Chapter 35 Reading SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee READ HAUSA Novels

SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee

Author :  Khadija bee bee Category :  African Stories & Novels

Chapter   35 / 58

102K to 105K   out of 173.5K words

gida, gobe zanshigo kaduna nasameki, yanzu akwai aikin da nakeyi gada contract d'ina ya rushe, domin tare nake da honourable, zanzo "

Turo k'ofar yayi yabarta nan tsaye, Ahakan ta kwashi bak'in cikinta ta koma kaduna, wanda takejin zuciyarta zata iya bugawa akan hakan.

Tunda hakan yafaru momyn bata k'ara neman Anwar ba kuma shima bai nemetaba.

*Bayan shekara biyu, da faruwar hakan.*

Anwar ciwo yake fama dashi, wanda duk wa'yanda ketare dashi duka sun gujeshi, Usman yad'an tsaya yana kula dashi, Amma daga lokacin da yaga Anwar wasu ruwa na fitar mashi daga cikin jikinshi masu wari, sai shima ya fara guje mashi, bayan yakaishi asibiti anduba ance bashida magani ciwonshi, kuma wanda duk yayi wata mu'amala dashi macce koh namiji ciwon na iya faruwa dashi, domin shima d'aukarta yayi jikin wani, tundaga nan Usman da jamila suka tsere suka barshi, ciwo nata cinshi shikad'ai wanda har tsutsa tafara fito mashi a jiki.

Watarana mai gadin gidan da Anwar yake, yaga kowa yashigo gidan gudu yakeyi, shima sai ya shiga yaga menene hakan d'in?
Shiga yayi domin duba halin da akeyima gudu, ganin anwar kwance tare da tsutsotsi a jikinshi, yasa mai gadin rufe hancinshi domin ya taimaka mashi.
Anwar number mahaifiyarshi yabada domin yasan ita kad'ai zata iya taimakonshi, mai gadin yakirata ya shaidamata halin da yaronta yake ciki, hartayi kamar gada tazo kuma sai soyayyar haihuwa tasata d'aukar mota domin ganin halin da dayake ciki.

Isowarta gidan taga yadda anwar ke wari ga ruwa nayi mashi zuba masu tsutsotsi da wari, sai hankalinta ya tashi, nan take ta rufe hancinta tana hawayen danasani, mai gadin ya rik'a mata aka wanke masa jikinshi sannan akasamu jallabiya aka saka mashi, tare da saka barguna da leda kamar ta 'yan haihuwa k'ark'ashin jikinshi ta dawo dashi asibitin nan kaduna, layin 'yan yoyon fitsari, domin su harsunfishi, don shi a duburarshi abun ke fita.

Kafin su kar'beshi federal hospital d'in sai da momyn Anwar ta zube masu 100k sannan suka bashi gado a wani wulak'antaccen d'aki.
Mahaifiyar Anwar takira mahaifinshi ta shaida mashi ciwon nashi, amma cewa yayi tacireshi a harkar Anwar domin shi baisanshiba, kuma naira d'inshi bazata shigo asbiti da sunan ciwon Anwar ba, momyn tayi kuka wanda yake kuka domin harda ita gefen 'bata rayuwar Anwar da mugunyar tarbiyya, su gasu masu kud'd'i yaronsu ya wataya yadda yakeso, toh yau ga k'arshen gata yazo, domin duk wanda yasan Anwar wallahi bazai ta'ba cewa d'an gayun yaron nan ne ba Anwar Naira, domin yakoma Anwar mutuwa.

_Toh Allah ka'iya mana, kabamu tarbiyya ta k'warai, da kuma 'ya'ya nak'warai, kabamu ikon yimasu tarbiyyar hali na k'warai ba tarbiyyar nuna jin dad'in duniyaba, ka karemu ka kare musulmi baki d'aya da rayuwa irin wadda Anwar yayi kuma yanzu yake ciki, ameen ya Allah.๐Ÿ‘๐Ÿป_

A Federal hospital anan aka kawo Anwar, doctor hisham shine likitan da ke duba anwar, shima yana iya k'ok'arinshi akanshi domin anzube masu kud'd'in aikinshi yadda ya kamata, mahaifiyar Anwar waya tabugama mahaifinta dake cen jidda akan yayi mata taimako da kud'd'i domin samama Anwar lafiya.
Kasancewar mahaifinta naji da ita batasamu mishkila anan ba nantake ya turo mata kud'd'i masu yawa domin samama jikanshi lafiya tunda jidda bazasu amsheshi ba koda yace azo dashi, don haka suka tsaya nan Nigeria, mahaifiyarshi na iya k'ok'arinta amma ciwo yak'i ci bale cinyewa.

Doctor Hisham ciwon na Anwar har mamaki yake bashi sosai, domin yasan ciwonshi na farko masu mu'amalar homosexual suke fama da kalarshi kuma idan dai za'a jure shan magani da cire kud'd'i asayi maganin toh may b a samu d'an sauk'i domin warkewa kuma babu, tunda a duburarshi ake mu'amalar, cuta kuma tarigada tashiga babu wani saf sauci ciki, amma abun mamaki sai ga wasu k'uraje damk'an acikin jikinshi sunfara fitowa, aka bada text a duba akaga Anwar d'auke da cutar H.I.V positive, wanda wanda kedashi sukayi tarewa ya lak'amashi shi, hakan doctor hisham yafad'amasu tare da basu result d'in sugani, ya wuce.
Momyn Anwar taci kuka har batasan metake cewa ba, haka shima mai ciwon sai yanzu yafara gane Illar abunda ya aikata,amma nadama yanzu ai bata aiki Anwar kabar girma tun ranar haihuwarka.

๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง

Farha anfara aiki a federal hospital, yanzu cikin 2 month take da farawa, Rayuwarta yanzu cikin jin dad'i da annashuwa, domin kuwa ta aminta da doctor hisham sone na tsakani da Allah yake yimata, kuma aure yakawoshi ba wasaba, domin yanzu ko wanne 'bangare na iyayensu sunsan da zancen neman Auren Doctor Hisham da farha, hakan yasa yanzu shak'uwar soyayyarsu nasaka farha mantawa da komai.
Ikram ta saba da doctor hisham, domin duk sanda zaizo, wajibine sai yayo mata tata tsarabar ta musamman,sannan kuma suyi fira da ita kamar ba 'yar shekara biyu da rabi ba, hakan nasaka soyayyar Ikram ga kowa wanda ke tare da ita, saboda wayo da kuma gane karatu, domin ansakata free nursery yanzu, idan farha zataje gurin aiki take ajiyeta sannan ta wuce, kasancewar yanzu umma ta tilastata akan tadinga d'aukar mota da kanta tana driving, saboda ai bata kowa bace ta ummar ce, hakan yasa yanzu take driving da kanta da sunan motar umma tunda ta iya dama.

Kamar kullum haka yauma tashirya fitar Ikram makaranta, sannan itama tashirya tata fitar, rataya jikkarta tayi sannan tarik'a lunch box d'in ikram a hannu d'aya sannan ta rik'a ikram d'in a hannu d'aya, suka shiga d'akin umma ta shaidamata sunwuce, umma tayi masu addu'a sannan tace....
"Ikeen Aunty farha harkar babu bye bye?"

Dariya Ikram tayi harda 'boyewa bayan Farha, sannan ta lek'o ta bayanta tace.....

"Idan uncle Hisham ya siyaman sweet da mota zan baki d'aya, nabawa Abban Abuja d'aya, motata kuma Aunty farha kawai zansaka tunda ita ke goyani "

"Ehhh, lallai Ikeen Aunty farha toh Adai yi karatu da yawa "

Farha dariya tayi sannan taja hannunta suka fita, sakata motar tayi, sannan tasaka lunch box nata da jikkarta a baya, tadawo gurin driving d'inta ta zauna.

Shigarta kenan wayarta ta fara ringing, kuma daji tasan mai kiran Hisham ne, picking tayi sannan tayi sallama.

"Amincin Allah ya tabbata agareka sanyi idaniyar teemah uncle d'in Ikram, antashi lafiya?"
"Wannan zance hakan? Ai sai kisaka nakasa fad'ar zancen dake bakina, plz ki safsautaman fa, akwai sauran time, toh qlau natashi, kefa?"

"Nima hakan"

"Toh Alhmdllh dear, dama so nakeyi kifito da wuri, domin akwai aikin da nakeso ki rik'aman na wani patient saboda aikin nad'aya daga cikin abunda nakeso ki k'ware a kai, sai dai nasanki da tausayi gada kizo kikasa fa"

"Hmmm naji zan daure ai, Ina onway ma, domin ikram kad'ai zan ajiye a school zan shigo yanzu "

"Ok kikular man da kanki kafin ki iso, sannan kibama ikram one kiss ga goshinta "

"Ank'are Oga "

Dariya sukayi dukansu, sannan ta mayar da wayar a jikkarta ta tayar da motar.
A bakin get nasu Ikram ta tsaya, tafito ta rufe motar tarik'o hannunta da lunch box nata, sai da ta tabbatar Auntyn tasu ta kar'beta sannan ta fito ta wuce.

Shigarta asibitin taje tasaka hannu a attendance ship, sannan ta duba komai wanda yakamata ta duba, sannan tafita zuwa office d'in doctor hisham.
Turawa tayi cikin sallama ta shiga, lokacin yana cike wata takarda a gabanshi, sai kuma ganinta yasa ya ajiye biron da yake rubutu yafara kallonta tare da cewa......

"Gaba d'aya nurses d'in asibitin nan, babu wadda uniform d'innan kema kyau kamar my teemah,wallahi keta dabance a jerin kyawawa farha, hakan yasa bazan bari wannan kyawon na k'arewa a duba patient's ba, har ni a dinga dubani, hakan yasa banji zan iya cika 2 month batare da anbani matata ba, don haka nashirya komai a hannuna, jiran kawai nakeyi a ce yau na iso "

"Wai kai Oga, koh yaushe sai kayi abunda zaisaka mutun dariya, gada ka manta kaga mata iri-iri a duniya, kazauna turai, ka auri shuwa'arab, don zaka Auri farha shikenan saikata zaro zance? Toh babu ruwana idan kyawawan nurses d'in asibitin nan suka jika "

"Farha kenan, dole na fad'a maki hakan, domin da sonki nake kwana nake tashi, k'arshe kuma ina burin najimu a inuwa d'ayane, kinyi auren farko nima nayi, amma wallahi jinakeyi wannan shine aurena na farko a rayuwa, don haka insha'allah a month d'innan komai zaizo k'arshe "

"Naji nidai oga tsoratani ma kakeyi, a yanzu saboda yadda kake zaro zancennan, toh mubar wancen zancen, ya batun patient d'inda za'a d'aura training d'insa akaina?"

"Hmm tunda ba kyason zancen nabari, amma ki shaidama umma next 2 week sadakin Hisham zai shigo hannun farha, sanna patient d'in anjima idan kin k'arasa aikinki zan kiraki sai muje tare koh? amma yanzu bangaji da kallonki ba, kibani 5mnt nak'are kallon flower ta "

"Haba! Wai oga menene hakan? Nifa yau tsoro kake bani, domin kafi koh yaushe rud'ewa akaina, inda da Ikram mukazo anan itama zata gane yadda ka koma fa"

Murmushi yayi sannan ya matso da sit nashi gaba, harda wani lumshe ido yayi sannan yace....

"Kinsan menake ji idan na ganki kuwa? Farha nasan kinsan menake ji, domin ke ba yarinya bace, kuma kinsan muhimmanci dad'ewar mutun bayada mata, bayan kuma yasan muhimmancin matar a rayuwarshi, toh wallahi ni kad'ai nasan yadda nake ji a kanki, hakan yasa nakeson na mallakeki a matsayin matata, mufito aiki tare, mu koma tare "

Duk'ar da kanta farha tayi, harda jawo hijab d'inta na uniform ta rufe fuskarta, domin yazo da sabon Al-amari zuwa gareta, tasan dai soyayya domin tayita amma batasan wani zance wanda yake fad'iba, domin bata ta'ba aikatashiba bale taji ya dameta tana nema, sai dai ita macce ce mai yawan sha'awa wanda tasan da wannan case d'inta tun kafin ta auri Anwar, da wannan zancen da oga hisham yayima farha, da zance ta rufe fuska ta bar office d'in nashi don kunya.
Kiranta yakeyi amma bata dawo ba, hakan ya k'yaleta tare da cewa.....

"Zan koreta ita kunyar a next month mai zuwa.

โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…

Watan Abdul-jabbar goma bai dawo gida ba, yana abuja zamansa, domin gudun fushin umma ya hau kanshi, tare da tilastashi abunda baiyi niyyar yiba, asashi yayi a halaka, domin duk wadda zai aura cutar ta kawai zaiyi, domin babu ita aranshi.
Hakan yasa koh yaushe cikin bugama baba waya yakeyi akan basu k'asar ne baki d'aya course aka turasu, amma da yadawo zai wucikke gida baki d'aya, kuma a gurin baban anan yake samun labarin gida da kuma yadda Ikram take, don har zancen shigarta school sai da yajiya gurin baba.

Baba yasan Abdul-jabbar zance ne kawai yakeyi, domin yasan yana nigeria, kuma shi yasan abunda yake ji akan rashin mata domin shima a tension d'in yake, don haka baya ganin laifin Abdul-jabbar, sai dai idan sunyi waya dashi yana jamashi kunne da nasiha akan ya kiyaye mutuncinshi, banda neman matan banza domin ba girman mutuncinshi bane, kuma idan yayi hakan bai kyautama kushewar Iman ba da Ikram, da kuma mahaifiyarshi, da hakan baba zai d'auki tsawon lokaci yana yima Abdul-jabbar fad'a, domin yasan yadda Abdul-jabbar ke da mugunyar sha'awa wadda tazamar mashi ciwo, sannan ya horeshi da yadaina umfani da pills d'in da yake sha, gudun gada su illatar mashi da gaba.

Idan baba yak'asa yima Abdul-jabbar fad'a, shima Abdul-jabbar d'in sai yayi godiya, sannan sai ya shaidamashi cewa, shi koh macce bayason gani bale har yaji suna burgeshi, insha'allah shi bayada niyyar tarewa da matar da ba muharramar shi bace, kuma zai kare mutuncin wa'yannan bayin Allah da ya ambata.

Kamar kullum yadda suka saba wayar, yauma Abdul-jabbar shine ya kira baban, lokacin baban yashigo gidan Umma tana shaida mashi zancen neman Auren farha da hisham yace zai kawo sadaki a cikin satinnan, baba yayi murna sannan yayi masu addu'ar dace na k'warai.

Yana cikin zancen cewa, shida yayan baban Abdul-jabbar zasu kar'bi sadakin insha'alla, kiran Abdul-jabbar shi ya katse zancen da baban keyi da umma.
'Daukar wayar yayi, sannan suka gaisa,hakan yasa baban kareshi da cewa.....

"Abdul-jabbar yau kenan kasamu sarvice d'in koh? Toh ga ummar ka ku gaisa, yanzu nashigo zancen auren k'anwarka farha "

Dum! Dum!!Dum!!! Gaban Abdul-jabbar ya fad'i, wanda yarasa menene dalilin fad'uwar gaban nashi hakan, amma yasan d'ayan zancen shine, idan tayi aure harda Ikram za'a bata? Toh wallahi bazai iya wannan aikinba.

Umma kar'bar wayar tayi kamar babu abunda yafaru, suka gaisa, ya tambayi Ikram, gudun gada ummar tace wani abu, harda farha d'in aka tambaya, Ummar tace "farha na gurin aikin, Ikram na makaranta"

Yace "alhmdullh"

Sannan ummar tace mashi, "Next month bukin Auren farha, don haka gudumuwar ka ga auren shine, kai zakayimata duk abunda uba keyima 'yarshi gurin aure, kuma umurnine ni nabaka, don haka koh a ina kake, k'arshen wannan watan kazo gida "

"Toh Umma insha'allah zanzo, kiyi hak'uri, kuma zanyi yadda kika ce, zan fara turo kud'in a fara sayamata abunda takeso goben"

"Toh Allah yayimaka albarka sai munjika "

Tamik'ama Alhaji Aliyu wayar sukayi sallama da Abdul-jabbar ya kashe wayar sannan yayi sallama da ummar ya wuce gida.

Sati d'aya dayin hakan mahaifin Doctor hisham ya kawo sadakin farha naira dubu d'ari, wanda saida baba ya nemi da arage sadakin domin yayi yawa amma mahaifin hisham yace su haka sukeyin sadakinsu, baba yayi addu'a tare da fatar Allah yasanya alkhairi a rayuwar auren, anan suka tsayar da ranar Auren 25 ga wata mai shigowa shine watan June, abu yayi dad'i domin iyayen Hisham sun tabbatar da uwayen farha mutanen k'waraine.

"Amarya kinsha k'amshi"
Furucin hisham kenan ga farha da yakirata a office nashi domin duba mashi patient nashi da case d'inshi yazamo mashi abun tsoro, shine tashigo yake zolayarta da kalmar "amarya kinsha mai, koh nace Amarya takusa shan mai "

"Hmm nifa banason wannan kirarinfa, gada kadinga hanani zuwa Asibitin nan, saboda tsoron zancen ka"

"Eyee, hakan kike burin yi ai naganoki, toh dake da hutu asibitin nan sai hutun cin amarcinki next month, yanzu dai kirik'aman takardun nan muje ki fara tayani aikin patient d'in nawa "

Kar'bar takardun tayi, tare da duba sunan patient d'in, nan take sunan ya hau saman idonta 'baro 'baro *ANWAR BALARABE NAIRA* Nan take tafara duba case nashi har da H.I.V ciki toh anan tafara shakkun ba wanda tasanin bane, sai dai duk wanda keda hankali zai fara tunanin wani abu akan rikicewar da farha tayu.

"Banason yawan tunaninki fa, gada ki sakani nima cikin damuwa, plz muje Nurse d'in doctor"

Murmushi farha tayi sannan suka jera zuwa shiga d'akin da Anwar yake kwance.
A nesa Hisham ya hango motar family nasu a k'ofar d'akin, nan take mamaki ya kamashi wanda sai da farha ta tambayeshi lafiyar hakan, yace mata "motar gidan mu nagani bakin block d'incen,shine nake mamakin faruwar hakan "

"May b sunsanshi, kaine baka sanshiba"

"Kuma hakane, mu k'arasa "

Shigarsu tabbas ya isko mahaifiyarshi da k'annensa guda biyu cikin d'akin, ga momyn Anwar nata rusar kuka.

Farha shigowa tayi, ta duk'a har k'asa suka gaisa da mahaifiyar Hisham cikin mutunci, itama nan take ta fahimci cewa itace farha d'inda aka kai sadakin aurenta, farinciki ya kama mahaifiyar hisham, domin farha ta ko ina tayi, tilon d'anta k'waya d'aya yayi dacen matar aure yanzu, domin ko ba komai daganin yarinyar akwai tarbiyya da kunya.

'Dagowar fuskar momyn Anwar sukayi ido biyu da Farha, ita firgita itama firgita, sakin bakin farha tayi tare da mamaki sannan ta koro mata tambaya cikin gaggawa, tacewa.....

"Waye bayada lafiya halan?"

Nuna mata Anwar tayi dake kwance baya gane kowa bale wanda ke tare dashi, hakan wanda yashigo idan yasan Anwar farko, A yanzu bazai ce shine ba, farha k'ara tambayar ta tayi cikin gidimewa.....

"Wai waye shi?"

"Anwar ne farha, yakoma hakan "

Cikin takaici da tuno wulak'ancin da yafaru da ita kala-kala wanda Anwar yajama rayuwarta, taja sunan tare da hawaye.....

"ANWAR! ANWAR!! kaine kazamo hakan? Toh Alhmdullh Anwar tun banje koh inaba naga yadda Allah kesaka ma bayinshi, ANWAR! Allah ya isarman tsakanina dakai sai Allah ya isa "

Mamaki ya kama mutanen gurin, hakan yasa shima Anwar d'in ya bud'e ido tare da kiran sunan "FARHA! Farha.......
Kash! yakasa k'arasawa domin zuciyarshi nantake ta buga, sai wani nishi mai k'arfi tare da ajiyar zuciya yace ga garinku nan.
Dasauri farha tafita d'akin tana kuka mai tsanani wanda batasan sadda labarin baya ya dawo mata farko ba.

Fara dubashi doctor hisham yayi, yagane ai Anwar ya rasu a dalilin shak'ewar da yayi, ya shaida masu sannan yafita da sauri zuwa gurin farha domin yaji wanene Anwar a rayuwarta da take yimasa Allah ya isa, kuma menene dalilin hakan?

Ko da yafito baiga farha ba, sai cen ya hango motar ta tafita asibitin da sauri, office nashi yakoma domin d'aukar wayarshi ya kirata.

Fitar Farha da Hisham yasa mahaifiyar Hisham tambayar Momyn Anwar cewa....

" Halan menene tsakanin Anwar da Farha wanda take jamasa Allah ya isa hakan, kuma shima da ganinta kawai gashi ya rasa rayuwarshi, meke tsakaninsu Hajiya ?"

Momyn Anwar saida tatsaya da kukan nata sannan ta d'ago tace.....

"Itace tsohuwar matarshi wadda suka rabu "

Mahaifiyar Hisham ta zaro ido, domin zancen yazo mata a bazata...........


Toh fa! Anwar anwuce da kaya bisa kai, Allah yajik'anshi toh, kuma ga wani rikici zai 'bullo kai.

Toh dai gamu ji da gani yanzu.


_Nagode da addu'oin ku, nasamu lafiya sosai, don haka gani gareku masoya na, ku 'ballani ga'ba ga'ba_๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ

_page biyu ne guri d'aya, na jiya da yau da gobe ma๐Ÿ˜_



*Bee Been Masoya*๐Ÿ’ž

๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ*
๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง

ยฎ *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ษฏษ› ษ–ฦกล‹ลง

35 / 58