Author : Khadija bee bee Category : African Stories & Novels
su had'u itama take yi, don batason 'bacin rai yanzu.
Tashiga kitchen d'in ta duba babu abunda za'ace a dafa yanzu a ci nan take, don haka tafito cikin zullumi, dole tasha tea hakanan koh babu komai domin taji sauk'in wannan yunwar.
Jin ana knocking d'in k'ofa yasa gaban farha fad'uwa, kamar tayi d'akinta tayi shiru, kuma sai ta dawo ta bud'e, tare da lek'a kussuwar, malam bala tagani d'auke da abinci, da sauri ta qarasa bud'e k'ofar fallow d'in, suka gaisa ta kar'bi kayan ya wuce, tayi murmushi tace....
"Allah sarki Umma, dole nayi biyayya da abunda kike so, saboda kinyiman abunda uwa kawaice zata iya yima yarta, Alhmdullh kawai"
Ajiye foodflax d'in tayi akan dining ta gyara zaman kayan abincin tare da d'auko plate ta zuba tata wainar da tayi kyau har tagaji, ga miyar agushi, da dak'walen kaji, zubawa tayi ta d'auka zuwa fallown d'akinta, ta d'auko ruwa da lemo ta ajiye tafara ci hankalinta kwance, ta k'arasa da hamdala, sannan ta mayar da kayan zuwa kitchen ta wanke, takoma d'aki tayi wanka tare da yin kwalliya simple, tasaka doguwar rigar atamfa, tayi shegen kyau.
Farha mai kyauce koh babu kwalliya, bale kuma ita ma'abuciya son kwalliyace, anan kad'ai da award nata da mata zasu bata.
Fitowa tayi babban fallown gidan, tare da kunna kallo don gada tajita shiru, tun da har yanzu su Aunty hafsart d'in basu k'araso ba, ba laifi ta samu nishad'i da film d'inda take kallo, domin indian love story ne, soyayyar ta burgeta, amma kuma tana sha'awarsu ne kawai, domin ita tasan soyayya kuma sai lahira idan ana sake yin wata, domin tasan bazata ta'ba k'ara samunta ba, ga abokin yin soyayyar nata da aka bata, hakan kawai sai taji hawaye na cika mata ido, nan take sai ta tuno da tayi ma kanta alk'awalin cewa bazata k'ara saka rayuwarta a tunani ba, sai ta tsaya sannan zata ga takaici, amma idan bata tsaya ba, ai baza'ayi da ita ba, hakan yasa ta jawo farin cikin dake ziciyarta taci gaba da kallonta.
Jin motsin k'ofa alamar an bud'eta yasakata juyo da fuskarta da sauri zuwa inda taji k'arar k'ofar domin ganin waye?..........
_kuyi man afuwa🙏🏻, wallahi busy nake mai yawa,amma na fara samun saik'in shi, shi busyn ba, kuyi hak'uri da wannan ba yawa, yanxu hakan ina typig ina barci, saboda gajiya._
*Bee Been masoya*💞
[3/14, 7:10 AM] +234 810 918 8883: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
Page...
★5⃣8⃣★
Dum! Gabanta ya fad'i, domin ganin wanda ya turo k'ofar, gyara zamanta tayi, tare da duk'ar da idonta k'asa da sauri, d'an had'a idon da sukayi dashi, gabad'aya jikin farha rawa yakeyi, domin taga yadda fuskarshi take, ta rasa meke sata jin tsoronshi, domin ko ba komai, zai fad'amata maganar da zata 'bata mata rai,ita kuma a yanzu bata burin abunda zai ta'bi rayuwar ta.
Takunsa taji yana k'arasowa gaban t.v dake kunne, hannu yasaka yayi switching d'in t.v, sannan ya juyo zuwa gareta tare da nad'e hannuwansa a k'irji, ya had'e fuska yace.....
"Wasu sunk'i, ni kuma an manna man ciwo da mutuwa kusa dani, toh ki sani wallahi ki dinga nesa dani, domin banason zaman mu na yawaita guri d'aya saboda tsaro, sannan shigowa wannan fallow d'in, na hanashi idan ina cikinshi, ki tsaya a iya inda aka tilastani na ajeki, umhmm! Kina sane da gidana ne ba gidan kowa ba, don haka ki gane nufina "
Farha kamar tayi magana, amma kuma sai wata zuciyar tace "ah ah farha yi shiru, koh kin manta da alk'awalin hak'urin da kika d'auka jiya?"
Nan take sai farin ciki kuma yazo mata, d'ago fuskarta tayi tare da cewa.....
"Yi hak'uri, wallahi bansan da wannan dokar ba, saboda ai ni bak'uwace, kuma bansamu rules and regulations d'in gidan a rubuce ba, da bazan taka dokar zaunawa a yanzu ba,amma tunda yanzu naji wak'a a bakin mai ita, insha'allah zan kiyaye "
Koh kallonsa batayi ba, ta mik'e zuwa d'akinta, shigarta kenan ta share hawayen da batasan da zuwansu ba, jin ana surutu a fallow ne yasa farha saurin share idonta, domin batason kowa yasan damuwarta.
"Wai ina amaryar take ne? haka ake yi? Ango fallow amarya kuma bata kusa?"
Inji wata kakarsu Abdul- jabbar da tazo bukin.
Aunty hafsart rik'e da ikram a hannunta, taga mahaifinta amma bashine take son gani ba auntyn ta farha, tura k'ofar aunty hafsart tayi tare da rik'e baki, ikram da gudu ta fad'a jikin farha tana murna, rungumeta farha tayi tare da cewa.....
"Missing u my luvly Ikeey? Ya kika baro umma?"
"Shine kika zo sabon gida kika barni a cen ni kad'ai,ni ma bazan koma ba "
"Eh nima bazanbar Baby nah ta barni ba"
Dariya sukayi dukansu harda aunty hafsa d'in da ke kallonsu cikin burgewa, zaunawa tayi gefen kujerar fallown farha d'in tare da cewa.....
"Farha, wayace maki amarya na baro angonta shi kad'ai? Ai duk inda yasaka k'afa kema ki saka taki, wannan lokacin shine lokacin da xaki mori amarcinki,farha ki fara renon mijinki da kalar taki rayuwar, domin yanzu da tsohuwar rayuwarshi ta aure zai reneki, ki kusanci mijinki sosai farha, anan zaki fahimci kalar rayuwar da yayi farko da iman, in akwai na d'auka ki d'auka, sannan ki k'ara da naki farha, gada ki bani kunya, yadda kike da diri d'innan, gaki macce har mace,gada ki bari wata ta ribanci zuciyar mujinki kinji, ki daina barinsa shi kad'ai babu kyau "
Farha k'ara rungume ikram tayi, sannan ta kalli aunty hafsat tayi murmushi tace.....
"Aunty har kinsa naji kunya wallahi, tare fa muke dashi, yanzu, kinsan yadda zuwan namu auren yazo, dole sai a hankali, domin kunya bazata bari nan take a fara bayyanar da doguwar tarairaya ba, amma nan gaba kad'an aunty sai kinsha mamaki, farha fa ce "
"Nasani,kuma nasan jininmu bazai ta'ba bari wata maccen tafishi a gidan aure ba, tun daga gyaran jiki har gyaran makwanci, don haka turaren da nabaki, ki dinga using dashi, idan ya k'are zan k'aro maki wani, domin inason ki zama star a rayuwar aurenki, ki zarce iman a zuciyar shi, wanda sai dai ya bita da addu'a, saboda yanzu ke ce tashi "
"Insha'allah zan kiyaye"
"Toh mu zamu wuce,amma ki fito ku gaisa da kakar abdul-jabbar, saboda yau zasu koma "
Fitowa tayi, suka gaisa, ta kawo masu ruwa da drink,suka sha suka wuce, anan aka bar ikram.
Farha dad'i kawai take ji, na ganin Ikram, domin zata rage kewa da yawa.
A part d'inta, yinin ranar suka wuni, sai dai idan Ikram nason wani abu, farha ta bi ta baya, ba ta fallow ba, tayi abunda takeso a kitchen da sauri sai ta fito.
Kwana ukku yau da aurensu, farha bata k'ara ganin Abdul- jabbar ba, sai dai taji tashin mota da dawowar motar, A dalilin hakan yasa Ikram ta fara kukan son ganinsa, amma babu dama domin saboda farha, shiyasa itama ya hak'ura da ganinta.
A wani daren laraba, Ikram tayu barci, farha ta tuno da wayar da Umma ta bata ta Iman da tace a bata, saukowa tayi ta bud'e drower d'inta cikin hand bag nata ta d'auko wayar ta kunna, ta gama searching, tafara shiga gurin da document yake, taga an rubuta......
*"RAYUWAR AUREN IMAN DA ABDUL-JABBAR"*
Tasamu gefen gadon ta kwanta, tare da gyara kwanciyar ikram, itama ta jawo pillor tare da fara karantawa kamar hakan...........
_Masoya toh fa, sai hak'uri, domin wallahi busy nake, kuma ina shirin tafiyane, shiyasa zaku d'an jini shiru, amma idan nasamu chance zaku dinga ganin posting koh babu yawa, domin mu k'arasa da wuri, kuyi ma bee been ku afuwan da small page da zaku dinga gani daga gobe, har ranar monday insha'allah_
_ku sakamu addu'a, zuwa lafiya, dawowa lafiya, katsina on top,👍🏻 ranar friday._😂
*Bee Been masoya*💞
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAHðŸ˜ðŸ˜*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ÊųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
_so mai sonka, kabar wanda baya sonka, yi da mai yi da kai, ka share wanda ya share ka, duniya ce, Allah ka karemu da sharrin shaid'an, da miyagun k'addarori, da musibar zamani._
Page..59
*"RAYUWAR AURE NAH, NI DA YAYA ABDUL-JABBAR"*
_"Sak'ona nasan zai isa gareki yayatah, nasan ko ina raye ko bana raye, watarana dole zakiji hakan daga bakina, domin ko da baki samu sak'ona a wayata ba, zaki iya samunsa rubuce, domin na rubuta na ajiyeshi akanki yaya farha"_
Gyara kwanciya farha tayi tare da juyawa gefe d'aya, ta k'ara zooming d'in text d'in dai-dai, sannan taci gaba.
_"yaya farha, kece wadda yaya Abdul keso, kuma kece wadda zuciyarsa keso, kece first love tashi, kece zuciyarsa ke bege ko wanne lokaci, sai dai kash! Yaya farha duka baki gane hakan ba, domin rud'in duniya da haskenta yasa baki gane gaskiya ba har kika barshi"_
Hawaye suka fara zubowa daga idon farha, domin tafi kowa sanin wannan zancen na Iman, hakan yasa ta share 'yan qwallarta da suka zubo a fuskarta kad'an, taci gaba da karatun nata.
_"ki sani yaya farha, yaya Abdul-jabbar kece yake so bani ba, yazauna dani ne saboda tsananin biyayya da kyautatawata a gareshi, yafara sona ne, saboda yayi rashinki, a haka har sona yayi rinjaye a k'irjinshi, amma kisani sone kawai yaya Abdul keyiman, k'aunar duka taki ce yaya farha, yaya Abdul na sonki har kamar yadda baki tsammani, sannan duk wani abu da zai yi maki shi, zai yi shine saboda tsananin kishinki da kuma begenki, domin nafi k'arfin wata shidda a gidansa koh yaushe kece yake kira a cikin mafalkinshi, wanda na gane hakan nasamo dubaru wa'yanda zasu rinjayar dashi daga barin ambatonki izuwa ambatona, domin nice a gabansa lokacin, naci wuya kafin na sauya begenki a zuciyar yaya Abdul-jabbar ta hanyar sadaukar mashi da dukkan rayuwata, yaya farha gada na cikaki da dogon zance domin nasan kinsan wannan ba tun yanzu ba, sai dai wani sirri nake son bar maki wanda idan har abban Ikram kika aura, kika rik'e wannan sirrin, zaman aurenku zai yi dad'i sannan ke zaki samu mijinki hannu biyu, wanda ina yimaki fatar samun Abban Ikram a matsayin mijin aure yaya farha, wanda nake fatar sak'ona yazo hannunki tun kafin kiyi aure da wani bashi ba, kuma ina neman alfarmar idan Allah ya d'auki raina kuma bakiyi aure ba, yaya farha ki auri yaya abdul, domin nasan Ikram zata samu gata mai yawa a kan hakan, nasan Allah shike rayawa da kashewa, amma ni na dad'e da sanin cewa rayuwata ba mai tsawo bace, domin abun da nake ji nake gani a rayuwar tawa, ni nasan rayuwata bamai dad'ewa bace, don hakan tun daga ranar da kika dawo gida, bayan rabuwarki da tsohon mujinki, nake maki fatar samun miji na gari, kuma insha'allah a yanzu da bana raye, nasan idan kika bi tarihin kalar zaman da nayi dashi, yaya farha zaki samu yaya Abdul-jabbar, ko mai nauyin k'iyayyarsa gareki"_
"Nasani iman, wallahi nasan duk abunda kika fad'a gaskiyane, kuma nayi alk'awalin kasancewa dashi ta har abada, wallahi inason yaya Abdul, amma narasa yadda zanyi ne tun farko da na dawo gidan umma naga kalar rayuwar da kukeyi, tun anan naji sonsa nakeyi, kuma kishinsa nakeyi akan hakan, saboda nasan nawane ya dawo hannunki,amma kuma idan na tuna da babu aure tsakaninmu har abada,saboda aurenki,sai naji na tsani kaina, kuma na tsani rayuwata,hakan kuma sai Allah ya d'auki son Ikram ya sanya man arayuwa, domin nasan jininsa ce ita, Iman baki duniya a yanzu, amma wallahi zakiji dad'i a makwancinki na aminci, da zamowa da mijinki da 'yarki da zanyi, domin zanyi k'ok'ari akan na dawo da soyayyarshi a gareni da hak'uri da juriya"
Share hawaye tayi sannan taci gaba.
_"yaya Abdul ya kasance acikin maza masu mugunyar sha'awa, sannan shi mutun ne maison kyautatawa, yana da ra'ayin macce cikakka wadda take da cikar halitta, yanason macce mai sura irin taki yaya farha, a dalilin hakan lokacin da aka kaini gidansa, yake yimani d'aukar ni k'wailace,wadda batasan komaiba, wanda hakan shi ya bak'anta mani rayuwa,nayi yak'i da furucinsa domin nuna masa nima macce ce, nasan cewa yaya farha komai kin fini a rayuwa, domin ke koh a cikin mata daban ce, Allah ya k'eraki k'ira irin wadda yake bawa 'ya'ya mata kyautarta, ni kad'ai zan iya shaida maki gaskiyar ke wacece?,domin ni jininki ce, yaya farha inason idan har yaya Abdul yazama mujinki to zaki samu zuciyarshi cikin gaggawa domin irinki yakeso, kibi hanyar da yanzu ni zan fad'amaki sirrinsa, yadda zaki shawo kan zama dashi,kamar yadda muka zauna acikin so"_
Motsawar Ikram kenan, tare da yin kuka, da sauri farha ta jawota zuwa jikinta, tare da jijjigata ta koma barcin, da ikram jikinta ta k'arasa karantawa, tana lumshe ido, domin yanzu ne aka zo gurinda yayi mata dad'i, kuma sai taji k'aunar Abdul-jabbar na k'ara shiga zuciyarta, hakan yasa taji tsoronsa ya 'bace a zuciyar ta, taci gaba, domin shine page na k'arshe acikin document d'in da tayi zooming nashi.
_" yaya Abdul nada sauk'in kai, yana mugun son k'ananan kaya, yana son a dinga kulashi, ko da shi bai kulaka ba, yaya Abdul mutunne miskili, hakan yasa idan baka dage ba, zaka d'auka shi mutunne mai zafin zuciya, amma baxaka gane ba sai ka kusanci rayuwarshi sosai, yaya Abdul mutunne mai son adinga shagwa'bashi da riritashi a gabanshi, gada fushinsa ya girgizaki, domin zai iya cewa zaiyimaka abu kaza a cikin zafi, amma da ka iya tafiyar dashi komai zai wuce, yaya farha kisaka juriya a zaman aurenki, idan har Allah ya k'addara auren ki da yaya Abdul, domin nasan Allah ke ikonsa, amma nafison ki auri yaya Abdul, domin nasan shine dai-dai da ke, ina wannan rubutun ne tare da hawaye, sai dai kuma ina farin ciki, domin nasan banbar mujina a hannun wata ba"_
Share hawayenta tayi, sannan kuma itama tayi murmushi ta shafa kan ikram tace.....
"Allah yayi maki rahama k'anwata, Allah yasaki a aljanna firdausi, a hakan kad'ai kika tsaya my sistr na amfana, sauran aikin zan k'arasashi da kaina, kuma daga gobe bazan k'ara shakkun yaya Abdul ba, insha'allah "
Rufe wayar tayi, domin babu buk'atar son jin sauran labarin, domin tagane inda sauran zancen Iman ya dosa, don haka bata k'ara duba komai ba, ta kashe wayar, tare da gyara kwanciyar Ikram itama taja bargo ta rufe rabin jikinsu, sai safe kuma.
Safiya ta waye, farha ta tashi domin gyara ma ikram zuwa makaranta, duk da batasan wazai kaita ba, domin shi abban nata ba ganinshi take yi ba, amma bari ta gyara mata idan bataji motsinshi ha, takira driver umma yazo ya ajiyeta.
Gyaramata tayi, tare da shiga kitchen ta had'o mata duk abunda tasan zata nema a makarantar, ta gyara komai nata, sannan ta rik'o hannunta zuwa babban fallow d'in gidan, tana rataye da lunch box d'in ikram a kafad'unta.
Har zata kira umma ko driver d'insu na nan yakai ikram makaranta, kuma sai ta tsaya, domin umma zatayi doguwar tambaya akan hakan, sai ta changr shawara izuwa part d'inshi tayi mashi magana, duk yadda za'ayi sai dai kuma ayi yanzu, domin batasan ya za'ayi da zuwa school nata ba.
Ajiye ikram tayi a kujera tare da ajiye lunch box d'in a table d'in fallow d'in, tace ma ikram....
"Kijira nazo kinji"
'Dakinta taje ta d'auko hijab, domin kayan barcine jikinta, dama so takeyi, idan ikram ta wuce sai ta yi wanka, sanyo hijab d'inta tayi, sannan ta taka gidan benen izuwa part nashi, ganin k'ofar sake, ya sata yin sallama har sau ukku, jin ba'a amsa mata ba, sai tayi kamar ta juyo, kuma sai ta tsaya saboda taji an bud'e wata k'ofar dake gefenta.
'Daga idonta da zatayi, sai suka had'a idanu dashi, nan take taga towel ne d'aure jikinshi, sai tayi sauri duk'ar da kai tace......
"Don Allah kayi hak'uri yaya, dama Ikram zataje makaranta ne, bansan wanda zai kaita ba, gashi lokaci yana k'urewa, suna promotion exam ne"
Kallonta kawai yayi hankalinshi kwance, sannan ya tsuke fuska, tare da dafe nad'e hannunshi a k'irjinshi yace.....
"Amma saboda baki da hankali, shine zaki shigo d'akina kai tsaye ba tare da izini ba? Inace ni zankaita makaranta koh? Toh sai ki jira a cen inda aka ajiyeki idan banzo ba, sannan ki yanke hukunci, malama ki dinga tsayawa huruminki, ki daina zuwa inda ba'a kaiki ba"
Iya bak'inciki farha taji bak'incikin maganar tashi, nan take kuma itama sai ta mayar mashi da amsar ta cikin ruwan sanyi tace......
"Da farko ina baka hak'uri akan huruminka da na taka, duk da na nemi izini naji shiru, kuma ai ban shiga ba, sannan na biyu, kasani ni farha daga yau bazan k'ara saka hannuna a lamarin zuwa makarantar ikram ba, Ikram d'iyarka ce, haka nima d'iyata ce, sai dai kasani kafini iko da ita, idan ikram tayi karatu nasan zaka fini farin ciki, idan batayi ba, zaka fini bak'in ciki, daga yau bazan k'ara saka bakina akan zuwanta makaranta ba, kuma bazan k'ara shiga huruminka ba, kayi hak'uri, kuma ni bazan k'ara rik'on Ikram a hannuna ba, daga yau ka mayar da ita gurin umma,