Chapter 42 Reading SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee READ HAUSA Novels

SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee

Author :  Khadija bee bee Category :  African Stories & Novels

Chapter   42 / 58

123K to 126K   out of 173.5K words

wajibi jan aji ya dawo baya, to ga Abdul-jabbar jan ajinshi ya zube da ganin cikar halittar farha, don haka yake jin kamar yanzu yake sabon so d'in.

Mik'ewa farha tayi, shima ya mik'e, ta juya zata tafi, ya saka hannunshi biyu ya lak'k'amo cikinta zuwa gare shi, yace.......

"Na yafe maki har abada, kuma komai ya wuce, zaki tallafi rayuwar marayan Allah?"

Juyowa tayi tana murmushi domin a rayuwarta wannan rana ita tafi mata ko wace rana dad'i, domin yanzu take jinta a sabuwar duniya, zata fara soyayya mai inganci, tace......

"Wannan kuma kaga zahiri, domin ni na kawo kaina, kuma na aminta nasama maka sauk'i, sannan gashi ka aminta dani da wuri, ka yafeni da wuri hakan, me zaisa bazan tallafi amintaccen mijina ba, na baka kaina baki d'aya yaya Abdul "

"Wani mugun farin ciki da yakamashi sai da yakai hannunshi saman kyawawan k'irjinta sannan ya shafasu ya lumshe ido, yak'ara juyo da ita gabanshi, ya zauna ya azata a k'afarshi, yace......

" naji banason ki barni, ki d'auko Ikram ku dawo sama"

"Ah ah cen zaifi mana kwanciyar hankali, domin banida maganin da zan baka, har sai ka k'ara aminta dani, ni takace, kuma ka tabbatar banida ciwon komai a jikina"

Mik'ewa tayi sannan tace....

"Sai da safe"

Fita tayi da sauri zuwa k'asa, shikuma mutuwar tsaye yayi tare da dafe kanshi, yana nanatawa.....

"Wallahi itace burina, amma kishin wani yayi mu'amalar aure da ita zai kasheni, wayyo ya zanyi, idan akace farha na d'auke da wata cutar, wallahi ko ma akwaita zanzauna da ita hakan, sai yanzu naji ashe sonta na nan bai fita zuciya ta ba, ya Allah kasa lafiyarta k'lau kamar yadda tace "

Komawa yayi bayan kujera ya zauna, yana lissafa kyaun halittar farha d'in, wallahi daban take da halittar Iman, farha tafi Iman cikar zati, sai yau ya tabbatar da hakan, bayan yaga yadda 'ya'yan fulaninta suke, gabad'aya a rud'e yake.

Farha tura k'ofar d'akin tayi, taga Ikram nata barcinta hankali kwance, ta gyarata, sannan ta cire kayanta zuwa toilet tayo wanka, tasaka rigar barci ta kwanta, amma barcin yak'i zuwa, tunanin yadda Abdul-jabbar keda saurin kamu hakan, ta lura yawan sha'awarsa kesa baya guje tayin da akayi masa akan hakan, sai yanxu farha ta yadda da maganar Iman akan cewa bayada wuyar kamu, idan anyi hak'uri da halinshi.

Lallai ta yarda, wajibi ta dage gurin ganin ta dawo farha d'inta ta da wacce yake k'auna, da wannan gud feeling d'in farha barci ya d'auketa da manyan buruka d'inta na alkhairi da take burin cikasu zuwa gareshi.

Dukansu kowa ya kwana da feeling mai dad'i ba kamar Abdul-jabbar, itama hakan ta kwana har safe....................





*~Ta masoya~*
*Bee Been masoya*💞
[3/22, 9:12 PM] 💖HASKEN MASOYA💞: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ÊųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com

My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*

*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋

★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★

*_ALHMDLLH! SAMUN MASOYA NA K'WARAI, KAN SAKA, TA MASOYA FARINCIKI, HAK'IK'A BEE BEE ALLAH YABAKI MASOYA NA K'WARAI, KOWA NAKINE, HAKAN YASA 'DAUKAKARKI DAGA ALLAH NE_*
*_MASOYANAH AKO INA KUKE FA'DIN DUNIYA KHADIJA BEE BEE NA GAIDA KU, SAK'ONKU NA ZUWA KUNNENA, ALLAH YA BARNI DA KU HAR K'ARSHEN RAYUWATAðŸ˜_*

Page...62


Dasafe farha tatashi jikinta duka babu k'arfi, domin ita bataga dalilin da zaisa umma tace abar Ikram ba, domin ita wallahi taji ko tafiyar bataso.
Daurewa kawai takeyi tana had'a kayan Ikram, amma badon tanaso ba.

Bayan yakai Ikram school ya dawo gida, amma baiga farha a palour d'in ba, don haka kamar ya wuce part d'inshi, kuma sai yaji baya iya wucewa sai ya shiga d'akin nata, domin ya k'ara shaida mata gobe ne tafiyar tasu 6:am.

Part nata ya shiga a palour nata baiji motsiba, hakan yasa ya zarce zuwa d'akinta.
Yauce rana ta farko da Abdul-jabbar ya ta'ba shiga bedroom d'in farha, turo k'ofar yayi a hankali tare da sallama, tana zaune gefen gadonta tana had'a kayan ikram a akwatunanta, shigowa yayi tare da jin wani k'amshi ya daki hancinshi, sai da ya tsaya ya shak'i k'amshin kad'an, tare da tsayawa bakin k'ofar.

Farha najin sallamarsa da sauri ta jawo hijab nata ta saka, domin kayan jikinta babu abunda ba'a bayyane yake ba, Amsa sallamar tayi tare da mamakin ganinshi, domin a k'alla yanzu zata bama 3 weeks baya a gidan, amma bata ta'ba ganin ya tako k'afarshi part nata ba, hakan yasa ko wace shiga zata iyayi domin babu mai shigowa.

Kallonta yayi tare da duba d'akin nata komai is need, komai gyare, sai k'amshi da sanyi A.C ke tashi, ta kowa yayi da sauri, ya zauna gefenta sannan yakai hannunshi a hijab d'inda ta saka da niyyar cireshi, nan take farha ta rik'e tare da cewa......

"Kayi hak'uri kabar man hijab d'ina jikina, gada na shiga hak'k'inka tunda baka son ana zama da kaya irin wannan, kabarni hakan please "

Kallonta yayi tare da kashe idanunsa duka yana kallonta, kuma bai saki hijab d'in ba, domin abunda ya hango da yashigo yake kwad'ayin k'ara hangowa, inda hali ma ya ta'ba yaji sanyi, domin shifa idan kan wa'yannan kayanne da yake gani jikinta, to yayarda ya fad'i jarabawa, domin ko a gurin wata yaga irinsu zai yi kwad'ayin yajisu hannunshi bare wadda aka mallaka mashi a matsayin mata, kuma first love tashi, hakan yasa ya yi harmar d'aga hijab d'in ba tare da ya tsaya jin k'orafin ta ba, idonsa kawai farha ta kalla tace......

"Na bani!
Cire hijan d'in yayi tare da jefar dashi ta gefe ya rik'e hannun nata yana kallon halittar jikinta kawai wadda Allah ya k'era mata, nan take idanunshi suka sauya daga yadda ya shigo.
Farha duk ta tsargu, domin ta rasa gane nufinsa akan hakan, jin ya saki hannuta d'aya yasata ajiyar zuciya, ashe wani gurin ya nufa da shi.

Hannunshi ya saka ya sa'bule gefen rigar har saida farha ta rike mashi hannu, kallonta yayi sannan yace......

" kece kika za'bi zama da ni a hakan, na ta'ba rayuwar soyayya dake, amma baki ta'ba sanin ni ko waye ba, nan kad'an zaki fahimci halina, ba duk mace irinki nake iya shafa ma lafiya ba, sai yanzu naji ma gwara da umma ta yanke hukuncin hakan a kanmu, ashe burina ne zai dawo, don haka ki koyi halina domin ni daban nake da sauran maza, kuma waya fad'amaki banason saka irin wa'yannan kayan? Ai sune best choice nawa a dressing d'in mata, don haka ki bari mu gana kad'an "

Bai bari ta bashi amsar tambayar da yayi mata ba, kawai taji hannuwansa duka cikin rigarta, chanja salon zancen yayi tare da cika hannunshi biyu da kyawawan halittun k'irjinta, wani irin ajiyar zuciya farha ta saki wadda sai da nishin yin hakan ya fito a fili, bai tsaya komai ba, sai da ya matseta son ranshi, tun farha nad'an jin dad'in hakan tana sharewa har takai abun ya fara bata tsoro, domin salo kala kala yake ai watarwa ga jikinta cikin sigar sha'awa.

A tunanin farha sai cewa takeyi a zuciyarta, "dama haka yake? Wai to ita haka maza suke, basa da wani jan aji kenan? Eh lallai macce na juye hankalin d'a namiji ta ko wace hanya, ji yadda ya dawo wani wawa akan jikina kenan, lallai abdul-jabbar bakada wuyar kamu a hannu "

Wani rik'o da yayi mata ba'a hayyacin shi ba, yasa farha yin wata k'ara tare da ture kayan Ikram da ke saman gadon ba tare da tasani ba, rik'e masa hannu tayi ta d'ago fuskarta cikin lumshe idanunta duka tace.....

"Ina shirin kayan Ikram ne, gashi kana yiman abunda ni ban saba yin irinshi ba, please kabarni hakan na k'arasa"

Hannunshi d'aya ya zame a nata hannun ya saka d'ayan hannun ya tallabo bayanta yadda k'irjin nata zai iya k'ara fitowa sosai, sannan ya matso da bakinshi a nata bakin, farha naganin ikon Allah sai ta bud'e idon nata alamar jin tsoron abun, domin bata ta'ba tsammanin wannan abun da wuri haka ba, mayar da idanun nata tayi tare da runtsesu tana jiran taji bak'on yanayi wanda ta mance dashi a rayuwarta, jin ya k'ara matse Boob's d'in nata, sai jikinta ya fara rawa, nan take yakai bakin shi cikin nata, aza bakin nashi ke da wuya a bakinta, da sauri kuma sai ya fitar tare da sakinta da sauri, kamar wanda a tsikara da allura, farha najin ya saketa da sauri ba tare da yayi abunda yaso yi a bakinta ba, sai ta bud'e idon nata, tare da jawo rigarta ta aza a k'irjin nata, ganinsa kawai tayi a bakin gadon ya dafe kai, alamar wata damuwa tare dashi, mik'ewa yayi tsaye tare da cewa....

"Ki had'a kayan nata idan zan d'aukota school, sai mu wuce da kayan, domin gobe 6:am insha'allah zamu bar kaduna "

Wucewa kawai yayi ba tare da ya k'ara juyowa ya ganta ba.
Abun yabawa farha tsoro, kuma bai tsaya ba bale ta tambayeshi abun da ke damunshi, amma ko ma menene, taji dad'in sakin nata da yayi, domin a tsorace take, irin yadda taga yana wani nishi tare da haukacewa a jikinta hakan kawai na bata tsoro, gyara saka rigarta tayi tare da kwashe kayan Ikram da aka zubar gurin murje murje, taci gaba da jerasu.

Fitar Abdul-jabbar d'akin, ya haye benenshi, tare da dafe kanshi yana taka step d'in yana tunanen, shin meke faruwa dashine? A duk lokacin da yaga farha gabad'aya rud'ewa yakeyi, har ya manta da wanene shi, shi yasan yayi rayuwa da Iman, kuma rayuwa mai inganci, amma wallahi baya jin irin abunda yakeji a farha, domin ganinta kawai nasa yaji sai ya ta'beta, wallahi yarasa meke faruwa dashi.
A haka ya fad'a d'akinshi tare da fad'awa saman gado, yana kallon yadda fankar d'akin ke motsi, iya abunda yake iya ganewa a tunaninshi shine, dama cen ba k'iyayyar farha yake yi ba, tsantsar kishintane yake sashi jin ya tsaneta, a halin yanzu ya fahimci son da yake yimata ne farko ke ambaliya a rayuwarshi, hakan kesa yana jin wani abu a duk lokacin da ya hangota ko ya kusanceta, amma ciwo da bak'incikin yadda zai zana alk'alaminsa a littafinsa kesa shi jin tsoron kamuwa da kalar cutar da tsohon mijinta ya mutu a dalilinta, ko tantama babu yasan alak'ar aure ta had'asu, don haka da yakai bakinshi a nata zaiji dukkan halittun da ke sadashi da feeling d'inshi zasu bud'e hakan kesa gaba d'aya ya rasa ya zayayi? Wajibi ya kaita domin gwada lafiyarta before, ya k'arasa nuna mata k'auna, k'asa tunanensa ya yi a kwancen, sannan ya duba agogon wayarshi 11:38, ya mik'e domin suje d'aukar Ikram, su kaita gidan umma, domin gobe dole ya bar garinnan zuwa abuja,kuma dole yacika umurnin umma.

Fitowa yayi don shaida mata tafito su tafi, dama tashirya fitowa kawai tayi, iya kyau farha tayi kyau, domin atamfa ta saka gyalenta kalar flower d'in da akayi zanen atamfar da ita, dressing d'in nata yayi, ganinta kawai da Abdul-jabbar yayi baisan sadda murmushi ya kufce mashi ba, da sauri ya rik'amata kayan hannunta suka fito abun gwanin sha'awa.

Makarantar su Ikram sukaje suka d'auketa, sannan suka kama hanyar gidan umma.
Shigarsu gidan da gudu Ikram ta fad'a d'akin umma, su kuma suka shigo tare da kayan a hannunsu, umma najin muryar ikram ta tamik'e daga kwancen da take, cikin murmushi tace.....

"To uwayen surutu an iso kenan?"
Kafin ta rufe baki har ta k'araso inda take zaune ta fad'a jikinta, tana murna, umma tace......

"Eh lallai d'iyar aunty farha andaina qyuya, da alama zamu dai-daita kenan?"
Dariya kawai Ikram take yi domin bata san menene nufin umma ba, don haka duk ta'aza wasarce kawai, tare suka fito zuwa falo d'in, duk'awa sukayi dukansu suka gaida umma, umma naganinsu a hakan farinciki ya cikamata ciki, domin iya dace sun dace da juna, don haka albarka kawai take saka masu da sanya alkhairi a d'aurewar rayuwarsu, sannan tace.....

"Gobe tafiyar na nan kenan?"

Farha ta kalli abdul-jabbar sannan tayi duk'ar da kanta k'asa, shine ya amsa ma umma da.....

"insha'allah gobe ne, yanzu ma bankwana mukazo da cika alk'awarinki "

Farha na ganin hakan ta d'auki kayan ikram tayi ciki dasu, hakan yabawa umma damar maganar da take son yi da Abdul-jabbar, Ikram itama tabi bayanta sukayi ciki, umma ta dubeshi tace.....

"Abbana, nasan na tilastaka auren farha bayan nasan cewa a farko itace ta k'i ka, to kasani nayi hakan ne domin na cika alqawarin mahaifiyarta ta rik'ata amana, Abdul-jabbar na duba a farko naga kai kafi chanchenta ka auri farha tun farko, sai dai wani ya kutso kanshi a cikin manema aurenta wato hisham, fasuwar hakan sai umurnina yacika, domin nasan kai kad'ai zaku zauna babu tsangwama duk da abun da tayi maka farko, sai dai kasani farha alkhairi ce gareka, domin ni na hango abun da kai bazaka hangoshi ba idan har kayi hak'uri tare da bin umurnina, Abdul na rok'eka da ka rik'e farha amana, ka zamo mai yafuwa a rayuwarka, ka zauna da ita cikin aminci da mutunci, ka karrama farha, nasan Allah kaima zai karramaka, idan kayiman hakan na yafe maka duniya da lahira, wulak'anta farha ko bayan raina ne banyafe maka ba, bare kuma tafiya wadda zakuyi zama bayan idon mu, kasani farhar da ba d'aya take da tayanzu ba, don haka Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, Allah yayi maka albarka ya raya maka ikram, ya kuma baka wasu masu albarka"

'Dago fuskarshi yayi tare da kallon umma cikin murmushi yace.....

"Insha'allah umma zan cika alk'awalinki, kuma na yarda da farhar da ba d'aya take ba da ta yanzu, insha'allah umma albarka kawai zaki ci gaba d'ayiman, domin bazan bar zancenki ba, sai dai ina neman alfarma akan ki umma "

Kallon sa tayi tace...
"Wace alfarma ce wannan?"

"Umma zan kai farha domin gwajin lafiyar ta, domin gudun ayi mutuwar kasko baki d'aya, kuma idan har na samu tanada d'aya da hakan, gaskiya umma zan k'ara aure "

Murmushi umma tayi domin ganin yadda abdul-jabbar ya fad'i maganar tare da duk'ar da kanshi alamar jin kunya, umma tace.....

"Na fahimceka Abbana, amma sai dai kaje ku k'ara yin gwajin da kanku, amma nasan farha bata da komai lafitarta k'lau, amma nayi maka alfarmar hakan "

Godiya yayi sannan ya ajiyema umma kud'd'i masu yawa, sannan yace zasu biya gidan baba kuma suyi bankwana dashi.

Umma godiya tayi, sannan ta shiga d'akin nata inda su farha ke ciki, shigarta ta taradda Ikram tayi barci, bayan farha ta bata abinci tayi mata wanka ta chanja mata kaya, anan barci ya d'auketa a k'afar farha.
"Ah tayi barci kenan? Lallai tafiyar za'ayita babu kuka, sai dai idan ta tatashi zanci uban kuka "

"Hmmm! Umma ni wallahi da anbarni naje da ita, domin zan samu kewa da yawa, akan rashin Ikram tare da ni, Umma ko ni na tsaya idan suka k'are exam d'in sukayi hutu sai muje tare "

"Farha kenan, ku daije, idan sukayi hutu sai yazo yaje maku da ita "

"To Umma"
Amma bai kai ciki ba amsawa.

"Yauwa farha, to acigaba da hak'uri, tare da yin biyayya gareshi ta yadda ya kamata, basai na k'ara maki da komai ba, domin nasan kinsan komai a rayuwar aure, sai wanda kinsanshi baki ta'ba aikatashi ba, wanda ni nasan da hakan, kece kawai bakisan nasan da cewa ke har yanzu matsayin budurwa kike ba "

Mayafinta farha ta jawo ta rufe fuskarta tare da jin mamakin ya'akayi umma tasan da wannan labarin, bayan Iman ce kawai tasan da hakan sai rasheeda, amma k'ila sune suka sanar da ita, kasa bud'e idon nata tayi sannan umma tayi murmushi tace.....

"Farha ni uwace gareki, kuma nayi maki kwad'ayin rayuwa ne da abdul-jabbar, domin nasan gareshi zaki samu jin dad'in aure sosai, shima hakan zai samu sakewa da ke, domin yanzu na fahimci yadda kike sonsa haka shima yanason ki, fatana Allah ya baku hak'uri da juna, ki tashi ku tafi, gada Ikram ta falka "

Sai a lokacin farha ta bud'e fuskarta, sannan ta mik'e ta shafa fuskar Ikram kamar tayi kuka, hakanan dai ta jure ta fita ba don taso ba, har takai bakin k'ofar fita, umma ta kirata ta dawo.

"Har zan manta, sak'o Aunty hafsart tace a baki, jiya aka kawo, to banason na bashi yaje maki da su, kinsan sirrine wannan, naga ta rubuta komai a takarda zaki fahimta, irin wa'yancen ne tace da ta baki "

Kar'ba tayi cikin jin kunya da godiya, ta fita.

Iskoshi tayi a motar, har zata shiga baya sai kawai ya harareta alamar rashin kyauta mashi, sai ta dawo gaba.

Gidan baba suka tafi yimasa bankwana, shima cikin murna da farinciki, harda hawaye sai da yayi, domin tuno baya da yayi, lokacin da farha ta bijirema aurenshi, amma ji yanzu yadda sukayi kyai, ALLAH kenan QADIRUN ALA MAN YA SHA'U, gashi burinsu ya cika, lokacin da basu shirya hakan ba.

Kud'd'i abdul-jabbar ya sakar mashi, sannan suka kama hanyar gidansu.

Tun kafin su k'arasa shiga ciki Abdul-jabbar ke kallon farha, kallo mai wuyar fassara, wanda ita bata gane me kallon ke nufi ba, domin farin shigace a wannan tarkon dole sai da k'auyanci kafin a waye.

Parking yayi suka fito baki d'ayansu zuwa cikin gidan

42 / 58