Chapter 3 Reading SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee READ HAUSA Novels

SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee

Author :  Khadija bee bee Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 58

6K to 9K   out of 173.5K words

samun sonki gareni...Nabiyu kuma yau nayi interview d'in fara aiki insha'allah...ina burin nanda shekara kizamo a hannun damata...,domin ni banason mu dad'e ban mallakekiba...,sone nakeyimaki na har abada nadad'e da sonki farha banji zankai 2years ban samekiba insha allah ina fara aiki kece farkon mallakina...,hope kema zakiyiman kalar sonda nakeyimaki domin muqarfafa zumuncinmu....."

"Congratulated broz ina tayaka murnar samun abubuwan guda biyu...,kuma ina fatar samun aikin da arziqi mai yawa..kuma insha'allah zakasamu yadda kakeso...,saidai sai kayi haquri dani domin kasan ban iya soyayyaba takace farko dole sai kana koyardani zan iya....."

Yayi murmushi tareda qara riqa hannun nata...

"Farha nah insha'allah zaki fini qwarema domin nima ai banta'ba soyayyaba..,gareki zansan zafinshi dakuma sanyinshi har kibani gurin kwana...."

Dasauri tarufe fuskarta kuma...qamshin turarenshi shine ke bimata hanci har yanasa tanajin sonshi nad'an qara shiga....

"Hmmm farha kidaina kunyata inason mugina soyayyarmu ta hanya mai kyau da inganci sannan su abba da baba su sani..., domin ke tawace insha allah nasan bamuda mtsl da iyayenmu zasu ji dad'in hakan damukayi....."

Murmushi takeyi...hakan yasata d'aga fuskarta takalleshi...,shikuma lumshe mata idanun nashi shanyayyi yayi...,da sauri tajuyar da kanta domin abunda taji jikinta yayi wato sanyi tareda jin baqon al-amari jikinta duk ya mutu sbd kallon da yayimata....,
Gane abunda yayimata yasashi yin murmushi amma bai saki hannun nataba...,d'ayan hannun nashi yasaka ya d'auko handout nata...,yace...

"juyo muyi karatun koh..? Nima ayi dani..."

Batace komaiba kuma bata juyoba...suna hakan iman ta turo qofa da sallama tashigo...,sai suka burgeta irin yadda tagansu da alama soyayya akeyi....

"Toooh ashe kune at ciki...bari naje d'akin mamah nachangr kayana nayi sallah inkun qarasa firar nadawo..."

Iman nafita yadubi farha yace.... "Iman tasan komai kenan..."

Farha ta gyad'a kai alamar eh....
Yace... "Shiyasa nakeson sistr iman domin akwai wayewa da wuri kinga har ta fahimcemu p......"

Murmushi kawai tayi tace.... "Zata dai tonamaka assiri gurinsu mamah ba..."

"Shikenan kowama ai sai yasan jabbar nason qanwarshi farha....kinga sai su fahimchemu kawai su fara shiri...next month subani ke kawai cen muqarasa love d'inmu da karatunmu inda zasu kaimu...."

Murmushi kawai take yimashi...hakan yasashi miqewa don ankira sallahn magrib..ya sunkuyo tareda cewa....

"Fad'aman wani abu dazai zama garkuwata kafin nakai masallaci.."

Rufe fuska tayi tace mashi "I LUV YOU.."
"LUV YOU TOO MY FARHA..."

yafita d'akin nasu bayanshi ta zubama ido tafiya yakeyi cikin sigar burgewa...sonshi na nan zuciyarta...,wanda tafara daga daren jiya zuwa ynx....,tacire gyalen datasaka takoma takwanta a kujerar tana jiran qanwarta tashigo.....

Iman nashigowa d'akin da sauri..,domin taji fitarshi...,tafad'a jikin yr uwarta tace....

" 'Ya'ya farha kinga yadda kukayi kyau kuwa...,wlhy wani farin ciki duk yakamani domin da waya garan koh..,wlhy dasainayimaku pic... 'Ya'ya farha nayi maki murnar samun brox jabbar domin rayuwarshi rayuwace ta burgewa..,ni nasan wlhy ya iya soyayya mai inganci...daganinshi wlhy zai bar tarihi a zuciyar masoyiyarshi 'ya'ya farha kema wlhy nasan kin iya luv kidinga kashe brox yasan akanshi aka fara..,amma kuma an iya..."

"Innalillhi Iman ina kika iya wayannan surattan banxar..? Eh lallai soyayya kikeyi a 'boye cen school d'in taku babu wanda yasani kenan...,toh lallai ke yakamata ayima aure baniba ma...,wato har kinsan a kashe mutun da kalam luv...toh koyaman naji sbd ni bansan komaiba...."

"Haba 'ya'ya wlhy ni banta'ba soyayyaba...,kawai dai kinsan idan kana zaune da mutane mabambanta kuma kana shiga cikinsu zaka qaru da wani abun...,kinga school d'inmu har matan aure nazuwa sbd gyara exam d'insu..,toh nikuma kinsan akwai shiga mutane anan in aka fara fira sunayi nakan kashe kunne naji...tunda bansan inda zanjiba..gareki ne kekuma 'ya'ya bakison mutane shiyasa komai bamu saniba gamu zaune kawai...,ga kyau ana shaidamuna ga diri amma komai bamu saniba..."

"Iman kenan menene ranar zama da mutane kata surutu...,kenifa bakowa nake iya zama nayi fira dashiba...,sai kakai irin mutumen danakeso....ke iman rashi totally baiyiba...,ni da ace arziqi garemu wlhy ni da sai anga bubud'awa domin sai kakai irin wanda nakeso zan fira dakai...ke ynx bamuda shi ma bandamu da kowaba a school d'inmu bare munadashi...kedai Allah yayimuna arziqi mudinga shiga waccen mufita wannan...."

Nan take Iman ta changr fuska..ta miqe jikin yr uwar tata....
"Wlhy 'ya'ya farha raina arziqin da Allah yayimaki kawai shi ke had'ani dake...,kituna munada suturar da duk inda muka shiga za a kallemu..,sannan mu masu surace mai kyau wadda kowa zaiyi murna da farincikin kasancewrshi taredamu...,munada lfy gamu cikin gata uwa da uba na raye..,sannan iyayenmu nayimuna duk abunda mukeso muci mai kyau musha mai kyau karatunmu mai tsa'bta duka school namu damukayi prvt ne da akwai da babu iyayenmu zasu biya muna...,amma duka har ynx kina ganin akwai wayanda sukafimu gata a duniya..mumafa munfi wasu wasu sunfimu dogaro ga Allah yafi komai domin watarana zai wadatamu muma..."

Miqewa tsaye farha tayi tareda riqe hannun qanwar tata....
"Haba Iman d'ina daga magana kuma sai fushi..? Toh zauna kinsan banison 6acin ranki iman insha'allah baxan qara cewa hakanba kuma inason brox jabbar sosai...."

Sukayi murmushi tareda zaunawa iman takalli yr uwar tata tace...."Allah ya tabbatar da alkhairi toh.."
"Ameen.."

★★★★★★

Soyayya mai qarfi ke shiga tsakanin farha da abdl-jabbar..., saidai abdl-jabbar yafi farha nuna soyayya qarara domin koh wacce rana idan bai shigo gidanba zai kirata susha soyayyarsu wadda koh dare da hakan suke kwana..,iman najin dad'in hakan domin yr uwarta tafara maida hankalinta gurin d'an uwansu...ynx koh ina suke suna tare maqale a waya..,wanda tarubutamashi my love..💖shikuma yasakamata my happiness💞 soyayya mai gamsarwa sukeyi wanda farha takai bata jure rashin jinshi....,hakan shima idan sunyi waya dole ne yazo yaganta....

Iman sunqarasa neco d'insu..,ynx tadawo gida koh yaushe tananan jiran takardu...,hakan yasa Iyayensu suka fara fahimtar wani abu tsakanin abdl-jabbar da farha..,mamah takasa haqura ta risqi autar tata domin shan lbr domin wannan irin kallo da yarancen keyima juna nabata mamaki....,

"Iman wai meke tsakanin 'ya'yarki da abdl...?"

Tayi murmushi tareda komawa kusa da mamar tata...tace...

"Mamah gada kice ni nafad'amaki zamuyi fad'a 'ya'ya farha...,wlhy soyayya sukeyi tsakaninsu...,ynx sunfi wata biyu a hakan..."
Mamah tayi dariya domin tadad'e d fahimtar hakan don koh ganin farha tayi ance za aje gidansu abdl-jabbar d'in sai tace batajin dad'i domin gada taje su had'u aganesu....,"toshikenan ai abun yayi kyau Allah had'a hankullansu...zan sanar da babanku kawai..."
💧💧💧💧💧

Abdl-jabbar yafara aiki a federal ferma ba laifi yanasamun albashi mai d'an qarfi..,domin yasamu lavel 5 agurin aikin kuma ba laifi yana rage wahalhalun mahaifinshi...domin ciki yake sayamasu abinci dakuma abunda ba a rasaba....,hakan zaisai kayan make up masu tsada yakaima farha..,tareda sayama iman nata....
Hakan dayakeyi yasa duka ynx iyayen sun gane cewa akwai soyayya mai qarfi tsakaninsu...sukaji dad'i sosai.....

Albashinshi nafitowa yana rage wani abu ciki domin son yakeyi zuwa next year yanada farha hannunshi....acikin kud'in yasayi mashin d'in zamani dashi wataran yake kai farha school duk da batason ana ganinta a mashin amma batason sa'bamashi..amma kamarta da yn jami'arsu kemata d'aukar d'iyar masu kud'd'i sbd takunta da wankanta...domin school d'in kowa nason ace qawarshice koh kuma budurwarshi....amma duka farha bata bada damaba....
Shiyasa idan yakawota aget suke tsayawa gada aga abunda ke ajeta.....

Ahaka dai aketa wannan soyayya...,shi yana yima farha soyayya taji da fad'i itama tanayimashi soyayya da zuciya biyu .... Domin tanasonshi iya matuqa amma kuma da yanada abunda yafi hakan da sonshi ya wucenan a zuciyarta......

Oh nie bee bee nace farha rayuwarki tayi..,kuma batayiba domin sannu bata hana zuwa saidai adad'e ba akaiba....,Allah katsayar da zukatanmu gurin da akajemu...,ka yayemuna dogon buri....ameen👏🏻👏🏻



~Ummul Ilham~
*Bee Been masoya*💞
[12/31/2017, 2:51 PM] Bee Been💞 Masoya: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧


©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com

My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*

*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋

★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★

*_YA HAYYU YA QAYYUM...BIRAHAMATIKA ASTAGISU...,ASLIHLIE SHA'ANIE KULLAH...WALA TAKILNIE ILA NAFSIE 'DARFATA AINIE....AMEEN ALLAH AMEEN....👏🏻👏🏻_*

Page...
★6⃣★

® Mamah ke shaidawa baban farha d'in cewa akwai soyayya mai tsanani tsakanin 'ya'yansu fa..., baban ke nuna mata ai yasan hakan tun aftr 1month baya yadad'e dasanin hakan...,amma yabarsune yaga koh shi Abdl d'in zai tuntu'beshi amma tunda baiyi maganaba shi zanji daga bakinshi ya abun yake....

2days da hakan yaje har gidansu domin ganin malam dabayada lfy sosai..,yakai mashi magani tareda gaidashi...fitowarshi keda wuya suka had'u da abdl d'in...nan yake shaida mashi anjima yazo yana nemanshi...

Dare nayi kuwa abdl bai sa'ba lkchn da yabashiba...,da wuri yaje.,kohda yaje baban baya nan bai dawo masallaciba...,hakan yaxauna sunata fira da mamah da iman...farha nacikin d'akinsu kwance...

Babah yadawo yake shaidama abdl su had'u d'akinshi... Acen kuwa suka zauna shi a kujera shikuma abdl a qasa yazauna suka gaisa cikin girmamawa...,babah yafara magana kamar hakan.....

"Abdl-jabbar naji wani lbr gurin mahaifiyarku nacewa dakai da qanwar taka akwai fahimtar juna tsakaninku..toh shiyasa naga yakamata nafara ji daga bakinku shin dgsk ne koh kuma shaquwarce tayi yawa domin nasan yadda kakeson qannenka...., dgsk akwai soyayya ta aure tsakaninka da qanwarka....?"

Abdl-jabbar yad'aga kanshi yadubi baban nasu yace....

"Eh baba akwai soyayya tsakaninmu kuma inason farhane domin na mallaketa a matsayin mata idan kun yarda da hakan...'

Babah yayi murmushi domin babu abunda yakai mashi wannan zancen dad'i a rayuwarshi..,domin yana d'aya daga cikin burinshi dayaso yacika akan hakan....amma bayason ya takura kowa daga cikinsu amma tunda hakan yafaru babu komai Allah ya tabbatar da akhairi kawai.... Afili kuma yacema abdl....

" Toh abdl-jabbar Alhmdllh Allah yasa wannan shine mafarin shigarmu aljanna baki d'aya..zanji daga bakin yr uwar taka sannan zanje nayima 'ya'ya malam maganar insha allah adaidaita komai..."

"
Toh babah ngd Allah yaqara arziqi da wadata mungode..."

Yamiqe yafita yakoma pallor da murnar da batada adadi domin babu abunda yakaimashi farinciki kamar ace yau farha mallakinshice ta halak...,domin koh yaushe da ita yake barci da ita yake tashi domin idan suna tare jin yakeyi kamar yayi abunda baidaceba...saidai yana tsoron gada ya wuce guri..,yayi haquri har Allah ya mallaka mashi ita hannunshi....,bai dad'e gidanba ya wuce gida domin abbanshi babu lfy sosai...,domin gobe dole sukoma assibiti dashi...,hakan yasa bai tsaya yaga farha ba domin yasan zasu had'u a waya....,

Hakan kuma baban yacema mamah ta kira mashi farha domin itama yaji tabakinta...itama tashigo d'akin ta zauna yayi mata tata tambayar....

"Fatima dama nakirakine kema domin naji tabakinki domin ynx kin mallaki hankalin kanki zaki iya fahimtar komai na rayuwarki...don koh khadija tasan hakan bale ke....,dama son nakeyi naji kema kinason 'ya'yanku a matsayin mujin aure....?"

Dum Dum gabanta yafad'i domin batasan amsar daxata bayar ba.,kuma batada wata mafita bale hujjar daxatace Ah Ah...,ba yanx ba...hakan yasanyata yin imani da qaddara ta fuskarta duqe tacema mahaifinta.....

"Eh babah hakane..."
Amma a xuciyarta tunanine na shin da yayi wannan zumud'in haka...ina yaga kud'in da zai d'auki lalurata...,iyayenmu suci da kansu suci damu kenan🙄...

"Toh mamanah Allah ya tabbatar da alkhairi kuma nafi kowa jin dad'in hakan data faru tsakaninku...,insha allah yau zanuyi maganar da 'ya'ya malam, kije kawai dama shine dalilin kiran...."

Tamiqe jikinta babu qwari...tayi hanyar d'akinsu..,domin itafa tanasonshi amma kuma tun ynx da wuri za ayi auren...toh menene abdl yamallakane da zai tsiri aurena tun ynx.....? Bataba kanta amsaba saidai tashiga d'akinsu ta cire hijab tareda kwantawa kujeran d'akin...Iman naganinta da sauri tamiqe tsaye....

'Ya'ya farha lfy kuwa..? Naga kinshigo jikinki babu qarfi koh dai babah ya fad'amaki wani abunne mara dad'i....?"

Kallonta kawai tayi tareda lumshe idanunta...domin tasan qanwar tata ynx da ta fad'amata abunda ke zuciyarta..,zata fara kawo mata hujjar banza bayan bazata gane menene burintaba....

"Iman babu komai...ina tunanin wata sabuwar rayuwane...,da alama antsayar za a tsayar da zancen aurenmu da broz jabbar ne..,shine nake tunanin sabuwar rayuwa...."

"Kai haba 'ya'ya ai ni jikina duka yayi sanyi domin wlhy nayi tsammanin wani abunne...,haba 'ya'ya farha yau celebrated xamuyi cikin d'akin nan domin naji dad'i...."

"Wai ke meyasa kike haka ne wai...? Ke baki gajiya da abun fad'a koh yaushe...toh kiyi celebrated sbd zaki rabu dani koh...,? Toh kiyi ina sauraronki...."

Tayu murmushi ta koma gefenta ta zauna "inbanyi murna ba nayi me toh Allah dai yakawo ranar kusa...."

"Naji tashi zubamana abinci kawai yunwa nakeji..."
Tamiqe tafita da sauri don cika umurnin yar uwar tata.....
★★★★★
Haske da yalwa nashigo babah Aliyu abbas domin wayanda suka damfareshi a baya sune..,allah yabasu ikon dawo mashi dadukan dukiyarshi murna ba acewa komai domin kuwa farha tafi kowa farin cikin hakan da yafaru....,
Ganin ciwon babansu abdl-jabbar na yawane babansu farha yad'aukeshi domin zuwa dashi assibitin qwararru dake abuja haka suka shirya suka tafi su ukku da ummar abdl dashi baban farha d'in da kuma abdl..,balaifi ansamu sauqi suka dawo gida...dawowarsu keda wuya baban farha yasayamasu gida wanda qaramine amma kuma babu laifi yanada kyau kuma yafi wanda suke ciki...murna ba acewa komai....
Suma su farha d'in yasayamasu wani gida babba mai kyau a cen suka koma...farha anqara samun girma girman kai da kuri yaqaru saura....

Acikin wannan faragar ne baban farha yake shaidama 'ya'ya malam cewa akwai soyayya tsakanin farha da abdl don haka ga sadaki nan shi yabiya dakanshi..,saidai shi 'ya'ya malam d'in yakira yn uwanshi na gombe domin sukawo sadakin..,don tabbatar da shaidu....

'Ya'ya malam yaji dad'i domin shima yaso hakan..,saidai ciwone ya hanashi fad'a...,yayima d'an uwan nashi godiya kuma amininshi wanda bayada kamarshi duk duniya haka shima a gurinshi...kiran mahaifiyar abdl d'in yayi ya shaidamata itama tayi murna da addu'a aciki tayi godiya domin an fifita rayuwarsu kuma anyimusu karamci....
Baban farha shima yake shaidamusu ai kafin yayi shi akayimawa bazaya ta'ba mance alkhairinsu gareshiba.....

Sati d'aya dahakan 'yan uwan malam ibrahim na gombe sukazo ganinshi yabasu kud'in auren abdl 50k domin sukai gidansu farha..,haka akayi kuwa kowa cikin farinciki haka suka rabu....

Farinciki a zuciyar abdl ba acewa komai domin koh ba komai yasan ynx farha takusa zama mallakinsa...
Kamar kullum yashirya domin xuwa gurinta zance...haka yauma yayi kwalliyarshi taji da fad'i idan kaganshi bazaka ta'ba tunanin bai mallaki wasu manyan dukiyoyiba sai inka ganshi a mashing d'inshi sannan ka tabbatar....

Isowarshi bakin get nasu hakan ya sauka yabud'e get d'in sannan ya shiga da mashing d'inshi...,shigarshi gidan mamah na kitchen dayake had'e yake da pallor nasu...tanajin muryarshi tafito suka gaisa...take shaidamashi suna ciki mana ya wuce....

Yashiga tareda tura qofar tasu...shigarshi iman tagaidashi tare da janshi wasa kamar yadda suka saba....
"Brox ango 'ya'ya amarya..."

"Kekuma uwar gida..."

Sukayi dariya har farha d'in tafita tabasu guri...,dasauri yakoma gurinda farha d'in take zaune ya zauna...,sai ya cije le'benshi na qasa....

"Yatake yr mata...? Komai natafiya yadda mukeso..,yaudai ankawo kud'in aurena pa don haka fatiha kawai ta rage a kira..,naganki gefen damata..."

Gaban farha yayi mummunar fad'uwa domin batasan meke sawaba idan aka ambaci sunan aurensuba sai gabanta yafad'i...,da sauri ta d'aga idonta ta kalleshi sai farin ciki yakeyi....

"My farha plx be happy p...wlhy a ynx nan nikad'ai nasan menakeji azuciyata daza ace kawai a d'aura yau danafi kowa farinciki...domin sonki da k'aunarki bazaki ganeba sai ranar tazo...."

'Duqar da kanta tayi tana wani tunane mara amfani..."wai anbiya kud'in aurena..! tab meke faruwa hakan wai....?"

Riqa hannunta yayi tareda d'ago kanta da sauri hawayene ke bin fuskarta da sauri ya sauka kan kujeran ya koma gabanta...

"My farha menene hakan...? Idan farinciki yasamu mutun godiya yakeyima Allah ba kukaba don haka plx kidaina...,koh kinaso nima nayi..? Sai mu rarrashi junanmu...?"

"Ah Ah.." Tajuyar dakanta gefe...,yajawota gabad'aya jikinshi... "toh kiyiman murmushi naji dad'i matata..."

Hannunshi yasa yana sharemata hawayen danaxxubo fuskarta..yana duban kyawawan la'bbanta wanda yakeji kamar bakinshi yakai kansu amma babu dama...

Murmushin tayi baikai zuciyaba... _lamarin farha p akwai mamaki...shin sone babu k'auna ciki..? Koh koh sonne kawai...,domin abun da d'aure kai...,mudaije zuwa zamu fahimta in munkai_

Haka yaketa nunamata soyayya wadda tunda yafara furta yana sonta baita6a nunamata yasantaba...idan tajuyar da kanta ya juwota shima...shi burinshi su had'a idanunsu guri d'aya akwai wani sirrin saqo dayake son isar mata aciki amma taqi bari su had'u...
Dahakan dai yaqyaleta yamiqe domin yasan tsananin kunyane ke hanata sakewa....

"Toh zan tafi domin nabar aiki da yawa gida na office ban cikeba kinga dakina kusa zanfi saurin qarasawa domin zanji d'uminki kusa dani...amma tym is coming..."
Dubansa kawai tayi tayi masa murmushi yajuya yafita itama tabi bayansa da kallo..tace...
"Akwai kyaufa...saidai hmmm...."

Tajawo wayarta don cigabada typing nata wato chart kenan...
★★★★

Ciwon mahaifinshi yayi tsanani wanda aka kwantar dashi a assibitin nan garin kaduna..yn uwan malam ibrahim duka sun halarta..,domin gabad'aya nufashinshi yayi sama sosai wanda har ansakamashi abun numfashi wato (oxygen) kenan shike riqe mashi numfashi...hakan yasa umman jabbar babu abunda takeyi sai kuka haka mamah domin dukansu suna assibitin....

Likitocin sunga taron yayi yawa hakan yasa sukace kowa yafito..,amma jabbar bai fitaba domin ganin yakeyi idan yatafi zai rasashi....
Hakan malam ibrahim yayi nuni da akiramashi baban farha d'in domin d'amqa mashi amanar jabbar....

Shigowarshi yakama hannun jabbar dana baban farha guri d'aya tareda azamasu takarda hannunsu...,domin baya iya cewa komai...nan take yakoma yakwanta....nufashin na tafiyarshi...komai rashin imaninka dole kayi kuka idan kaga yadda yakeyi...hakan yasa baban farha ya matsa yana bashi kalmar shahada har ya amsa shima yanabi...cen kawai sai numfashin nashi yatsaya...,na urar oxygen d'in tatsaya hakan yasa jabbar fita dagudu domin kiran doctors d'in..zuwansu kawai sai suka cire oxygen d'in suka lullu'beshi da zanen assibiti doctor d'in yace....
"Toh pa sai haquri domin yarigamu gidan gasky kuyimasa addu'a kawai....."

Nan take jabbar ya riqe kanshi domin baimasan mezaiceba...baban farha d'in shine yariqashi yana fad'amashi "innalillhi wa inna ilaihirraji'un...kafad'i wannan kawai abdl domin malam yasamu kyakkyawan qarshe..,Allah yabamu kalar tashi shahadar..."

Fitowarsu d'akin umma tafara kuka...

"Innalillhi wa inna ilaihirraji'un...malam katafi kabarmu Allah yayimaka rahama yasa nan yafiyemaka nan shikenan mun rabu...,malam na yafe maka nayafema...!"
Mamah na sharar hawaye ta riqata sukayo gida...aka d'auko gawar malam anan gidanshi akayi mashi wanka..aka kaishi maqabarta tareda yn uwanshi na gombe...baban farha shi yagabaci komai a qarasa....

Kwana bakwai da addu'ar rasuwar malam yan uwanshi suka fara shirin komawa gida..sukace toh idan ummar abdl taqare iddarta zasu dawo suwuce da ita gida....

Baban farha yace "ah ah komai wahalhalunsu shi zai d'auke kuma idan tabar gidan waxai zauna zan riqe jabbar kamar ni nahaifeshi..,kuma wasiyyar malam ibrahim dayabari hannuna..yanemi da na riqe jabbar amana kuma nabashi kyakkyawar d'abi a duk da ya girma ya mallaki hankalin kanshi...,kuma dukiyar da malam ibrahim yabarma jabbar zata zauna hannuna...idan Allah yanunaman nacika alqawalin aurenshi da qanwarshi kuma yaqara hankali zan mallakamashi aburshi duka...,kuma komai na aurenshi ynx nad'auke ni zanyi insha allah..,zanje hajji wata mai zuwa ina dawowa komai zai kammala.... Sannan sbd ita mamar tashi zata zamo ita kad'ai sai yazauna nan gidan tare da ita..,sbd iddarta zatafi agidan mujinta..,dasai takoma cen gidan amma yazauna nan da ita komai zan kula dashi koh bani nan..."

Sukayi murna da godiya Allah sarki daza a samu mutanen kirki irin Aliyu abbas da duniya babu marayu duniya sukayi sallama suka tafi.....

Umma kukan farinciki da murna takeyi domin koh ba komai tasan jabbar ba marayabane ynx yanada gata....
Tayi godiya suka watse.....


*bee been masoya*💞
[12/31/2017, 2:51 PM] Bee Been💞 Masoya: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧


©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com

My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My

3 / 58