Author : Khadija bee bee Category : African Stories & Novels
ciki, sannan sauran ya ajiye a nan falo, ya mik'ama ikram d'in makullan part nasu yace....
"Ki kaima aunty "
Sannan yafito ya kira wanda zai kaishi air port d'in, sbd adawo da motar gida, yazo suka wuce.
Farha ta amshi kayan da makullan ta ajiye su in da ya kamata, domin karatu zata yi gobe akwai exam mai zafi, a haka ta yini cikin karatu, ikram na gurin talatu tana yimata wasa.
★★★★★
Alhmdullh sun sauka lfy, wanda kuma sun samu jana'izar, inna hajiya tasamu jama'a domin dama mujin ta tsohon malamin makaran ta ne a nan zamfara d'in, hakan yasa kowa yaji rasuwar, kuma tasamu shaidu na k'warai wanda kowa yaxo zai yabi halin boyar Allah d'in, ga karamci ga managarci ga tsoron Allah, da haka kad'ai inna hajiya ta yi dace rayuwar ta, sai dai juyayi na d'iya da jikoki domin sunyi rashi, ahakan dai suka sami dangana da hak'uri a rayuwarsu.
Kwana ukku da addu'a umma da baba suka shirya dawo wa sbd shi ga aiki, ita kuma umma tunanin ta akan farha da yarinya da tabaro gida, hakan yasa mama tace su wuce, har da iman domin ita zata tsaya har mutane su k'arasa zuwa in yaso idan aka kwana biyu sai tadawo.
Kowa ya aminta da hakan, sai umma ta buk'aci da iman ta tsaya sai su dawo tare, tunda koh banxa tayi yaye, kafin su koma ta manta da nonon baki d'aya, baba shima ya ga hakan d'in yayi idan suka koma sai ya cika alk'awalin shi na tura ta gurin mujinta, kuma zaman zaisa ta k'ara gane wasu, domin sun fi sanin farha akan ta.
Aka zauna akan hakan, kuma itama taji dad'in hakan,kuma yayen ikram ciwon nonon komai batayi ba domin cikin da at gareta, don haka da sukayi waya da Abdul-jabbar shima yace hakan yayi kyau.
Su umma suka iso lfy k'lau, ikram murna kamar kace me, taga abokiyar wasar ta tadawo, talatu kuma umma tace tunda ba yara gare ta ba tayi zamanta kawai, tun da da wuri,a haka suke zaune cikin jin dad'i, ikram tunda tayi kukan nono sau d'aya bata k'araba, sbd bai dame taba, da ta nuna alama aka bata madara shikenan ta manta da komai.
💧💧💧💧💧
Sati d'aya da gama amsar gaisuwa, kowa ya watse, har k'anne mama d'in sun watse, sai k'anwar su k'waya d'aya wadda bata yi aure ba, mama tace da ita zatazo, aka shirya tafiyar da ita da kayanta.
Abdul-jabbar najin da wowar su, yabuga ma wani driver waya akan yaxo gida ya amshi mota ya d'auko su, domin bai yadda iman ta shiga motar kasuwa ba, hakan akayi shi ya d'auko su, suka kamo hanya.
Ba'a 2 mnt abdul- jabbar bai kira iman yaji ina suke ynx ba, har yakai chaging wayar tata duka ya k'are, sai neman tambayar ya tsaya.
Sunata shan hanya duk da 2hour ne tsakanin kaduna da zamfara, amma akwai xama, ga tafiyar ta d'anyi marece sbd 3:pm suka taso, kuma sai da iman ta kira farha ta shai damata sun taso, don Allah talatu ta taimaka ta share mata gidan kafin tazo, ta fad'ama farha ita kuma ta fad'ama umma sbd gada rainin yayi yawa, taga ba a kyauta mata ba, umma ta fad'amata ba musu ta je ta gyara gidan lfy qlau.
Sun kawo, zaria anan aka fara kiran sallah la'asar, mama tace a tsaya suyi sallah sannan, nan sukayi sallah sannan suka kama hanya.
Barci ya d'auki iman, kuma taji dad'in barcin, acikin barcin taji ana kiran.....
"Innalillhi wa'inna ilaihirra'un! La'illaha illallah, muhammadan rasulullahi sallahu alaihi wasallam!!!"
Muryar mama kenan da ta tayar da ita,koh da ta bud'e ido kawai zata iya tunawa, amma sauran zancen bata sanshi ba, domin wata k'atuwar mota burkin ta ya katse aguje ta tunkaro motar su,hakan driver d'in yayi k'ok'arin kaucewa, itama wata k'aramar motar tayi gudun tsira, sai d'ayar motar ta bugi motar su Iman gaba d'ayan su suka fad'a wata gada dake tsakanin zariya da jaji.
Tun da mutane masu wucewa suka hango hakan nan take aka kai d'auki cikin ramen da mota biyun ta fad'a, ita kuma babbar motar jejin ta mik'a ta bugi icce ta kama da wuta.
Da sauri mutane suka fara fitar da mutanen da abun yafaru da su, driver d'in su iman da mutanen motar su gaba d'aya sun rasu nan take, saka makon bugun da kansu yayi a wani babban dutsi.
Mama da ihsan duka sun ji jiki, domin basu san inda kansu yake ba, samira k'an war mama itama allah yayi mata cikawa itama, nan take wani ya jawo jikkar da yagani, ya duba last call na wayar mama, yakira Alhaji Aliyu yake shaidama shi su had'u assibitin shika, domin ita ce kusa, kuma ya fad'amashi hatsari ne ya faru su had'u assibitin.
Nan aka kwashe su a motar assibiti tare da yn sanda, zuwa emergency, domin duka in ba ka sansu ba bazaka shai dasu ba.
Baba sauri yayi, yaje ya d'auki umma ba tare da ya fad'amata komai ba, suka kama hanyar assibitin.......
_Ubangiji Allah yabaku lfy, ya jik'an wayan da suka rasa rayuwar su, kamar sameera k'anwar mama da driver d'in su, da mutanen d'ayar motar, da ake ganin family guda suma, Allah kabama iman lfy da mamar ta_😭😭😭😭😭
*Bee Been masoya*💞
[2/24, 10:46 PM] +234 803 932 4068: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
*Asragfirullah, wa'atubu ilaihi,Astagfirullahu lazee man lazee la'illaha illah huwa alhaiyyul k'ayyum wa'atubu ilaihi*🙏🏻🙏🏻
Page...
★4⃣7⃣★
Abdul-jabbar a tsiyace ya kawo zaria, assibitin yashiga tare da neman gurin, nan take aka nuna masa, nan take ya gane, ta hanyar hango umma zaune ita kad'ai azuciya yace "mutuwa mai yanke zumunta, ji umma ita kad'ai "
Dasauri ya k'arasa tare da tambayar ta gurin da iman take, koh gaisuwa babu sai tambaya, sbd baya a hayyacin shi, umma kar'bar ikram tayi sannan tace yabata wayar shi, ya mik'amata ya kama hanyar d'akin, sai da yatafi sannan takira layin wayar ta, cikin sa'a wayar na hannun farha, kamar kada ta d'auka domin numbr da tagani kuma sai wata xuciyar tace bari ta d'auka, tana d'agawa taji muryar ummar, bata tsaya amsa sallamaba, tace "kina ina?"
"Ina assibiti gurin aiki?"
"Kinada kud'i a hannunki?"
"Eh ki hawo transport muhad'u dake assibitin shika"
"Toh zanzo ynx umma,amma zan koma gida na d'auko ikram "
"Ah ah gata nan tare dani kidai zo
Jikin farha har rawa yake yi, da sauri ta shirya ta nemi transport nan take.
Shigar abdul-jabbar d'akin yadinga dube dube domin baiga mai kama da iman d'inba, yadawo ya tambayi umma ta biyoshi suka shigo tare, inda yavari nan daine iman take, kuma itace wadda bai ganeba, kuka umma Abdul-jabbar kuka....
"Umma kina nufin haka iman ta koma!?"
"Eh Abdul qaddarawar ubangiji kenan d'in, su nan da sauk'i sauran duka babu rai "
Ashe idon iman bud'e kuma tana jinsu nan take tace...
"Kaji umma! waye yace maki nima ina raye? Ai burina kawai nake son yacika sannan mala'ikan dake kusa dani ya wuce dani gidan da aka ginaman wanda yafi wannan a aljannah,Alhmdullh umma Alhmdullh, zan rasu ina mai farincikin zan koma hannun ubangijina kamar yadda mama ta koma masa, dama inajin duk abunda ake yi,Abdul karik'e man amanar Ikram, duk matar da zaka koma aure gada ka bari ta cutar man da ita, domin nasan dole d'iyarka zata koma hannunka wata rana,ni kuma zanje maka da wannan babyn sabon gidan mu na aljannah, sannan kacikan dukan alk'awarina bayan raina "
Kuka Abdul-jabbar yasaki mai k'arfi wanda sai da ikram itama ta fashe da kukan haka umma da ita tashin hankalin da tagani ai batasan iya karshi ba tunjiya har izuwa wannan tym d'in, Abdul-jabbar ya matsa kusa da ita da sauri tare da rik'a fuskar iman wadda banda aka fad'amasa itace da bazai yar da ba, amma duk'awa yayi a fuskar ya dubi iman yace cikin sanyi wai shi ya kwantar mata da hankali, amma kuma kuka yake yi.....
"Ah Ah iman ai ba haka mukayi da ke ba fa, munyi alk'awalin zamu rayu tare zamu mutu tare, kawai don ciwo ya sameki sai kice man wai zaki tafi kibarni? Nima so kikeyi na bi bayanki kenan mubar ikram ita kad'ai? Toh ki daina,ai kin fara samun sauk'i gobe gida zamuje tare,kin manta zamu koma sabon gidanmu na abuja iman? Zuwan da nayi kenan muwuce, kuma zamuje kidaina fad'in hakan don Allah, ki duba nine fa, nine Abdul-jabbar d'inki, ki tuno da farincikin da kike sakani idan muka kasance tare, iman kece ke sani nishad'i ya za'ayi kuma ki tafi ki barni duniyar nan iman?"
Umma tagane shima hankalin nashi ya gushe, domin baisan ma me yake cewaba, kar'bo ikram yayi ya azota gefenta yace...
"Duba ikram na ganinki kuma tanajinki kina fad'amata zaki tafi ki barmu, toh ki fad'amata wasa ce kikeyimuna zamu koma gida tare "
Iman dariya tayi ma ikram sannan tace...
"Haskenah kenan! Ikram ina kika baro Auntynki?"
Itakam kallon farin bandeji kawai takeyi a fuska, domin batasan waye anan gurin ba, idan ita kad'aice tserewa zatayi, amma hannun abbanta take.
Umma kar'barta tayi sannan tace.... "Kataso muje"
Iman tareqe masa hannu tace...
"Kayafeman kuma kacika alk'awalina, kuma wayata na mallakama yaya farha abata, domin inada sak'o da yawa ciki wanda na ajiye domin ita,sauran naka sak'on ka........."
Bata k'arasa ba sai ta sarqe da miyon bakinta, umma da gudu ta kira likitan, amma abdul-jabbar rik'e yake da hannun iman ga gam sai sannu yake ce mata, "nabaki ruwa?"
ta d'aga kai ya jawo d'ayar gorar ya bata tasha sosai, sannan tace barci nake ji, dai² da shigowar likitan yace abata guri ta huta, da alama tayi magana doguwa, suka fita amma banda abdul-jabbar, umma goya ikram tayi sukayo waje.
Kusan awa d'aya Abdul na zaune jinya bai san cewa Iman tayimai nisan kiwo ba, sai sun had'u kuma, hango ruwan da aka saka mata yayi jini na dawowa ciki sa sauri ya rik'a hannunta tare da kiran sunnanta amma da gani barcin yayi nauyi inji shi.
Yafita kiran doctor d'in, suka dawo tare dubata yayi sannan ya cire ruwan yace.....
"Sai hak'uri aboki nah, Itama tabi mamar ta, gidan gaskiya "
"Menene ma hakanan?"
"Hak'uri kuma assabru, kuma sorry duka kagane ako wane yare "
Kameshi abdul-jabbar yayi yace....
"Haba likita daga cewa ka dubata sai kace wai nayi hak'uri, idan bazaka iyaba nakaita wata assibitin a dubata koh da a tsirara zan tafi "
"Toh abokina, nasan kai musulmine mai imani da k'addara mai kyau koh mara kyau don haka ka yarda matar ka ta rasu kusan 30mnt da suka wuce "
Fad'uwa kawai likitan yaga yayi tare da rik'e kai, dai_dai da shigowar umma da farha, umma da sauri ta k'arasa kusa tare da tambayar lafiya?
Doctor yak'ara nuna iman kuma ya fad'a masu ta rasu.
Ai kafin ya k'arasa fad'i, tuni farha tabi sahun k'asa itama a sume, nan take imanin umma yak'aru ga ikram sai kuka take yi, ga rashin iman ga su sukuma a kwance.
Shikenan duk sun mutu sun barta, ya zatayi? 'Dauki likitoci suka kawo, umma koh hawayen ta nema ta rasa,waya ta d'auka ta kira baban don shaidamashi, shikuma............
😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭
_Innalillhi wa'inna ilaihirraji'un._
_kullu nafsin za'k'atul maut._
Duk mai rai zai d'an d'ana azabar mutuwa.
Mai kudd'i, talaka, almajiri, mawadaci, yaro, babba, mara lfy, mai lafiya, masoyi da masoyan shi,duka wata halitta zata d'an d'ana azabar mutuwa.
Muji ya rasa matar shi, mata tarasa mujinta, koh uwa tarasa d'anta koh d'an yarasa uwar, idan dai baka ta'ba d'an d'ana zafin rashi ba, toh zaka sameshi wata rana.
*KULLU MAN ALAIHA FAN,WAYABQA WAJHI RABBUKA ZUL JALALU WAL'IKRAM*
Kunga kuwa baza'a bar wani don wani yaji dad'iba.
Ina typing d'innan damuwa feel a zuciyata, hakan yasa nakasa turo shi,amma nasan dad'in hak'urin rashin iman zai sa musamu farinciki gaba.
😭😭😭😭😭😭
★★★★★★★★
💧 *masoya nah da mabiya buk d'ina, sak'o gareku.....*💧
Kusani labarina yafaru da gsk, kuma wayanda abun yafaru da su suna biye da ni, idan nace iman bazata rasa ranta ba, sak'on da nake son isarwa ba zai zoba.
Kusani ni kaina wlhy naji mutuwar Iman domin khadija mutunce, duk wanda yasan rayuwarta yasan ita ta dabance, alokacin da nake rubuta wannan page na mutuwar tata labarin sai yazamo man sabo bisa ga lokacin da aka bani labari, domin ina rubutawa ina zubar da k'wallah wanda hakan yasa yau gabad'aya naji har tsoron posting nake yi wlhy.
Idan da labarin nawa ne, kuma nice na k'irk'irashi, toh banga abunda zai sa na kashe iman ba, ni bee bee bani na kashe iman ba, daga Allah ne hakan yazo.
Duk mutun na k'warai zai so ace ya mutu yana cikin soyayyar jama'a da yawa domin hakan babban dace ne, sbd kowa zai fad'i alkhairin ka kuma zai samamaka tsira koh da a shaidun k'warai ne, iman ta cika da imani, domin a tafarki tsira taje lahira, tana da aure, kuma mijinta na yaba halinta, kuma itama tana yaba halinshi,kunga wannan kad'ai dace ne, don haka da ita da mahaifiyarta anayi masu fata da zaton sunyi dace.
A halin yanzu idan kana son iman addu'a kawai zaka bita da ita domin koh tanan ta samu dace mai girma.
*Fatima Aliyu Abbas (Farha)* kuwa kusani itace tabada labarin domin a rubuta shi, wanda a halin yanzu hakan da labarin yak'ara kawowa wannan part d'in,gaba d'aya farha cikin damuwa take.
Masu cewa farha ta sa'bama iyayenta farko, tabbas hakan yake kuma ta nemi gafara, tare da gyara halinta tazama tak'warai,wanda laifinta rashin jin maganar iyaye da kuma mummunar soyayyar Anwar da tasaka ma kanta, wanda kuma sai Allah ya nunamata ishara a hannunta, aka had'ata da wanda gara mazinaci dashi, tasha wahala, tabugi wahala, wahala kuma ta ganta.
Wanda duk yayi laifi, yagane kurensa har yanemi yafiya ba a yafe mashi ba, ai cikar imanin bai kaiba, ansan cewa idan kayi laifi a nuna 'bacin ran abunda kayi, sannsn dga baya a yafeka.
Idan ana yima Allah babban laifi ya yafe idan taubatun nasuha ce, mezaisa za'ayima d'an adam yak'i yafewa? Don haka kowane mai rayuwa ake sonsa da kalmar hak'uri, domin samun zaman lafiya sanadin hak'urinnan, don haka farha tayi laifi kuma ta gyara, sannan mutuwa kad'ai tazamar mata ishara a rayuwa, rashin uwa ba k'aramin jidali bane ga rayuwa, da rashin yar uwa ta jini, anan ku fad'aman waye farha ynx?
Don haka inason a bayanina yan uwa kufahimci cewa.....
*WAMAN K'ADARALLAHU, HAQQAN K'ADDIRIHI*
Babu mai wuce zanen da aka rubuta mashi a *lauhul mahfuz* don haka imani da k'addara khairan wa sharan.
Fatana kubini a cikin littafinnan domin akwai nishad'antarwa gaba, tare da gargad'i mai amfani, insha'allah, akwai duk wata soyayya wadda babu ita a baya gaba zaku sameta, albishirine daga gareni.
Sannan ina taya d'aukacin masoyan iman ta'aziya baki d'aya, Allah yayi mata rahama, yasa mutuwa hutuce gareta da mahaifiyarta da mahaifanmu baki d'aya, muma allah ka gafarta muna laifukanmu kuma kasa mucika da imani.
Nidai d'in ce taku, ta masoya, jinin soyayya, tambarin ruwan soyayya,insha'allah a cikin soyayya zamu wuce😍.
Allah kabarmu da soyayyar Allah da manzonsa, ka kuma barmu da masoyan mu.
Ina cikin alhinin rashin iman, amma kuma ina cikin farinciki, domin nasan ita tayi mai kyau, sai addu'ar Allah yabama Abdul-jabbar hak'uri, da musaya mashi mata wadda tafita.
Akwai show fa👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻
*Bee Been masoya*💞
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
# ;*” ”*;.
‘*;._
, ‘*-;
*:, .;* ORRY!
This is a special SORRY 2 u my fans! Allah 4give all our sin's.
Page...
★4⃣9⃣★
Ringing d'in wayar baba yaashigo amma tana a silent lokacin, saboda yana gaban k'abarin mama yana jero mata Addu'a da nema mata gafara gurin Allah, ya shafa k'abarin tare da shafe hawayen shi ya fito mak'abartar, duka anwatse shi kad'ai ya rage, don haka sai ya kamo hanya shi kad'ai don dawowa gurin ta'aziyyar.
Fitowar shi kenan, ya k'ara jin _vibration_ na wayar tashi na motsi a aljihunshi, dubawa ya yi sannan ya amsa kiran domin yaga numbr abdul-jabbar ce, kafin ya d'auka gaba d'aya imani ya gama shiga jikin shi domin yasan baya wuce iman itama ta tafi ta barsu.
_Picking call_ d'in yayi, tare da tare da yin shiru, sannan muka yaji ance....
"Iman itama lokaci yayi! idan kun k'arasa azo a d'auki gawar itama a suturta ta,kuma ga yaran dukan su sun fad'i a sume "
Kalma d'aya ta fad'o mashi a bakin shi, domin itace garkuwar shi koh ina, ita kad'ai ke rik'e da nauyin imanin shi yace tare da hawaye.....
*_"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Allahumma ya muk'allibal qulube sabbit qalbe Allah Deenika, Allahumma ya musarrifal qalube wal'absari, sarrif qalbe Ala d'a'atika"_*
Jin zuciyar shi tayi sanyi, yak'ara bashi qwarin gwuiwar yin sauri zuwa gidan nashi.
Shigar shi aka fara yimashi ta'aziyar matarshi, anan ya amsa yace masu zai koma domin kar'bo gawar 'yar tashi, saboda itama Allah ya amshi aburshi, anan mutane nat fara rud'ewa suna kuka, sai Allah yabama baban k'arfin hali da k'warin gwuiwa domin jin hakan yake yi ba wani abu bane yanzu, tun bayan karanta addu'ar da yasan itace dogaron shi, nan take ya shiga basu hak'uri tare da fahimtar da su girman hak'uri da imani da abunda Allah ya saukar, sannan suka kama hanya shi da aunty hafsart k'anwar mahaifiyar su farha don zuwa assibitin kuka kawai takeyi, baba nabata hak'uri da nuni da bazata da wo ba har abada.
Likitoci ukku kan abdul-jabbar amma yayi nisa sosai, hakan yasa suka sanya mashi abun jawo numfashi a hancinshi saboda taimakon rayuwar shi, suka bashi _30mnt_ su gani koh zai