Chapter 22 Reading SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee READ HAUSA Novels

SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee

Author :  Khadija bee bee Category :  African Stories & Novels

Chapter   22 / 58

63K to 66K   out of 173.5K words

d'ina na ajeki domin hanyar nan akwai had'ari..."

Kamar gada tayarda kuma saitaga haksn shine mafita gsky domin bata ta'ba shiga maqwaftansuba bale su taimaketa da hakan...,yad'auko mashin nashi yasaka uniform nashi irin na yn banga d'innan ya aza trollyn gaba itakuma ta hau baya...,cikin ikon Allah tana nunamasa hanya har suka kai bakin gate nasu Iman yace bazayajeba har sai tashiga tukunna....

Wayarta tacire a hnd bag nata tafara kiran number d'in Iman tunda tasan mijinta bayanan saidai datakira Numbr busy takira har sau shida numbr busy gashi 1:30am amma iman waya takeyi....,gashi batada numbr umma tunda lkchn ai bata damu da itaba bale tayi numbr d'inta...

Baba mai gadi yafara knocking d'in gate d'in da qarfi amma shiru....

Iman suna magana da jabbar soyayya sukeyi wadda bata qaunar abunda zaisa wayar ta tsinke haka shima...,sun tsunduma suna sanya junansu farinciki...,wanda har musayar kiss akeyi acikin wayar shi yace.. "nafi iyawa.."
Itama tace...,nadai fika iyawa.."

Murmushi jabbar yayi har sautin dariyar tafito cikin dodon wayar yace... "Hmmm naji amma ai baza'aganeba sai nadawo sai ayi competition koh?"

"Hmm naji ni kasakan hakan idona sun fara qorafi sukeyi..."

Rufe bakinta keda wuya taji bugun gidan da qarfi.., tad'an jaye wayar kad'an a kunnenta har bataji abunda ogan nata yaceba..,sbd fargaba da tsoro 1:30 ana bugun gida koh lfy??

Jabbar cewa yayi...

"Toh haskenah..! Tunda kinfara barci toh *have a nyc dream wit me*.."

Amsamasa tayi amma cikin fargaba domin ba a daina bugun gate d'inba...,kashe wayar Iman tayi ta ajiye domin ta miqe taje d'akin umma ta tayar da ita taji...,fitar da zatayi sai ringing d'in wayarta yashigo..,dasauri tadawo tad'auka number farha tagani saida gabanta ya fad'i....d'aga wayar tayi acikin fargaba...

"Yaya farha..."

"Iman nice abud'emani don Allah..."

"Ok bari nafad'ama umma muna xuwa..."

Kashe wayar tayi takunna wutar d'akin sannan tayi hanyar d'akin umma kohda tashiga itama tana alamar fitowa domin dukan gate d'in bana wasa bane....

"Iman kinji abunda naji ashe..?"

"Eh Umma yaya Farhace koh lfy..?"

"Subhanallah bari nasaka hijab d'ina muje.."

Suka fito tare duk da akwai wuta koh ina amma dare ai abun gudune..,umma tabud'e gate d'in da addu'a..,farha tagani tsaye tareda wani da kayan aiki..,shigowa sukayi ciki shikuma yayimasu sai anjima zai koma gurin aikinshi...,sukayi godiya Iman taja jikkar zuwa ciki umma tarufe qofar da addu'a sannan tariqo farha datake kuka sukayo ciki....

Farha miqama ummar tayi takardar da Anwar yabata takuma fad'amata abunda yafaru tun farko da d'abi'ar da anwar d'in keyi na homosexual d'in duk tasanar da ita....sannan tace tareda share hawayenta wanda saida Iman itama tayi kuka akan jin lbrn abunda mijin na yr uwarta keyi Allah yasa itama bai halakataba domin masu irin wannan halin haka sukeyi da matansu....

Farha tace..., "Umma kinga sakamakon son zuciyar da na jawowa kaina koh...? Gashi baba bazai yrda nazauna dashiba sbd nayi rashin biyayya gareshi farko hakan zaitayi zaton zan cigaba..,bayan wlhy ba hakaba..,Umma naga jarabawa wlhy bazan qara gujema umurninsuba koh kad'an...."

"Yishiru farha Idan bai zauna dakeba ni xan zauna dake...,tunda ni kad'aice gidan sai ynx da yayanku yayi tafiya Imam take nan idan yadawo takoma sai muyi zamanmu tare...,ai farha dama kowa na kuskure a rayuwarshi tunda har kingane laifinki kin nemi gafara ai yawuce...,jarabawace Allah yad'auro maki kuma Allah yabaki ikon cinyeta...,kuje ku kwanta Iman riqa mata kayan saida safe..."

Farinciki gurin Iman ba acewa komai domin taji farinciki mara misaltuwa domin wlhy hakan yayimata dad'i domin haka yasa take k'aunar Uwar mijinta sosai kuma uwa gareta...,taja kayan suka wuce..,suka shirya kwanciya suka kwanta..,iman nayin barci farha tatashi tanata kukan dana saninta.......


Tabd'i zama gida guda farha da iman da jabbar...,chakwakiya🤕.........




🙏🏻🙏🏻🙏🏻afuwan banji garauba amma na warke gani gareku...,ina jiran comment naku.....



*b̈ëë b̈ëën̈ m̈äs̈öÿä*💞
[2/20, 6:47 AM] 0mmer Farouk: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧


©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com

My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*

*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋

★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★

*_masoyan💧sone dadilin hawayenah!💧Inajin dad'in comment naku..,masu bani shawara ta prvt da group gabad'aya ina godiya sosai..,saidai kowa yayi haquri kawai..,domin littafin true lyf ne yafaru kuma banison na karkace daga yadda lbrn yaxo,idan nayi hakan lbrn bazaiyi dad'iba..,kawai kusaka kunne ku bud'e idanu kuji yadda abunyake💁🏼soyayyar ciki kawai ce tawa amma karin lbrn nasu Iman ne da farha.., Ina godiya ina qaunarku kuma nidai d'ince taku💞duk inda buk d'ina ke zuwa group ne koh ma ina ne ina k'aunarku baki d'aya..._*

*Nayi mistake number jiya 3⃣4⃣🔛3⃣3⃣ agyaraman...*

Page...
★3⃣5⃣★


® Wayewar safiya Iman aftr tayi sallah..,tafad'a kitchen d'in umma domin gyaramasu break..,itakuma farha sbd rashin barci bayan tayi sallah assubahin barci yakwasheta nan inda tayi sallah..,umma kuma na d'akinta tana lazumin safe....

Ringing d'in wayarta dake gefenta tajiyo..,dasauri ta aje doyan da take ferewa taduba calling d'in....

" 'Dan halak d'ina shi baza'ayi tunaninshiba sai yaji jikinshi..."

Murmushi tayi sannan tad'auka tafara da cewa....

"Kakoyi barci..? Wannan kira daga sama hakan da wuri kai koh k'oshi bakayi..?"

"Hmmm morning dai haskenah...,yaza'ayi nayi barci bayan bamu kusa da juna..,jiya kin kashen jiki kuma kika tsere kika barni wlhy saidai natashi nayi sallah domin babu barci idona Ke kawai nake tunawa kuma kenaketa missing..,shiyasa naji gara naji muryarki ynx kafin na kwanta domin yau babu inda zamuje...,inama gidane da na 'barje gumina..."

"Ahh shikuma sanyinah bayada aiki sai hmmm da hmmm koh?"

"Eh lallai menene hmmm da hmmm..? Kice dai inada tanadi mai tsoka idan nashigo kisani ni koh abinci banaso naci kawai ki lula dani cen kad'ai nakeso..,kinyiman tanadin tarbona jibi domin bazan iya cika date d'innan ba zan tsero sbd gobe xa'a qarasa komai jibi zanbiyo hanya sauran aikin zan qarasashi a computer wlhy nakasa jure 3days d'in sucika..."

"Nipa aiki nakeyi gada umma ta fito ban qarasa break d'inba idan naqare zan kiraka naqara jinka tunda yau ranar tamuce..., _my honorable missing you so much..."_

Maganar qarshe d'inda Iman zatayi gabad'aya saida tawani karya murya tayi qasa da ita sannan tafad'i kalmar missing d'in acikin kunnenshi....,nantake jabbar ya rud'e kiran sunanta yayi baki d'aya...

" khadijah kinason namutune.? Wannan ai prvt voice ne amma kina yiman bayan kinsan bani kusa dake..,iman gada kijuyeni p..."

Dariya tayi harsaida sautin dariyar yashiga cikin dodon kunnenshi..,kashe wayar tayi domin tasan idan ba haka tayiba wlhy koh ita bazatayi aikin datakeyiba..,domin feeling mai dad'i take shiga idan tana tareda mujinta...,aje wayar tayi tacigaba da aikinta cikin qwarewa ta qarasa takai komai gurin zamanshi ta kai break d'in fallow sannan tatafi tayo wanka,fitowa tayi sannan ta tayar da yr uwar tata akan itama tashirya suyi break...

Bud'e ido farha tayi cikin mamaki yaushe barci ya d'auketa kuma.? Duba iman tayi kwalliya dai2 jikinta kuma saita burgeta sosai..,dubanta tayi sannan tayi murmushi tafad'a toilet d'in d'akin..,wanka tayi amma koh mai bata shafaba bale harta duba madubi...,domin inbanda haushi da kunburin fuska da jajayen idon kuka mezata gani a madubi..,doguwar riga kawai tazuba ta yafa gyalenta tafita...

Isko umma da Iman suna fira ga abinci gabansu amma kuma basuciba domin ita suke jira..,farha sun burgeta domin zaman amana sukeyi tsakanin uwar mijin da ita kuma sonta takeyi kamar raida ajali..,saida hawaye suka so fitowa amma sai taqi bari su xubo...,duqawa tayi tagaida Ummar kanta noce,ummar ta amsa sannan Iman tazuba mata nata karin...,faraci tayi kuma saitaji ta qoshi domin ba komai naci ke burgetaba sbd halin damuwar datake ciki tea d'in ne kawai tashanye amma sauran takasa tsaye tayi kawai tana tunani..,sukuma Iman da umma fira sukeyi suna dariya....

Farha hawayene keta zuba tana tunanin *SONE DALILIN HAWAYENTAH!* Gashinan takasa sukuni ganin wasu cikin farinciki har burgeta sukeyi gata itakuma duniya ta kad'ata.....

Juyowa da umma zatayi tayimata magana sai kuma taga farha na hawaye ga abinci gabanta takasaci tariqe kai tana hawaye nz baqin ciki...,da sauri ummar tace......

"Subhanallh farha menene kuma abun kuka anan..? Kizamo mai tawakalli a rayuwarki..,rabuwar aurenki da d'an iskancen ai abun farin cikine..,kid'auki cewa ita qaddara wata abuce da Allah kirubutoma bawanshi tunkafin a haifeshi...,an qaddaro haka rayuwarki zatayi don haka kidaina kuka kizauna damu cikin aminci da yarda da juna...,Na za'bi kizauna nan ne domin kisamu safsafcin rayuwa kinga kirageman kewar zama ni kadai nima naragemaki...amma kuma kinqi gane menene nufina......,nakira mahaifinki nafad'amasa ansakoki jiyan bayan kin koma kuma saki ukku..,shine yace ace kiyi zamfara cen gurin dangin mamarki kizauna domin gidanshi babu space na zamanki..,na amsa masane kawai kuma bansanar dashi nan xanbarkiba..,amma inkinfison zamfarar sai kishirya kitafi cen......"

Share hawayentah Iman tayi sannan tace....

"Yaya farha kiyi haquri ki rungumi qaddara...,kuma nima zamanki anan nake ganin zaifi sbd kinga kinfi sabawa da garinnan idan kika koma zamfara bazakiji dad'in zamanba gurin innaba...."

"Umma nagode sosai Insha'allah zan xamo mai tarbiya da kiyaye duk abunda akace bashida kyau..,domin naga Rayuwa rayuwa kuma taganni...,Ina godiya umma domin naqiku farko gashi ynx kice ginshiqina....,kuqara yafeman..."

"Bakomai komi ya wuce....,ki saki jikinki koh kinsamu jikinki yazamo naki...."

Murmushi sukayi dukansu...,Iman takwashe kayan tamaida kitchen wayarta nata qara amma saida takai kayan sannan tadawo tazauna gefen farha..,amma bata d'aukaba saida umma tace mata wayarta na ringing p..., d'aukar wayar tayi tayi hanyar d'akinsu...,tana murmushi da jin kunya...,ummar murmushi tayi domin tanason Iman rayuwarta sbd akwai kunya da sanin yakamatarta...,farha ma burgeta qanwar tata tayi domin tasan iman daban take a rayuwarta.....

'Daki tashiga tafad'a saman gado tana murmushi ta kwanta...,pillow tajawo ta'axa saman cikinta tariqe pillow d'in da hannunta d'aya..,hannun d'aya riqe da wayar picking tayi.....

"Hmmm sirrin ruhi..! Duka ynx hour nawa da wayarmu amma kuma harka kasa haquri kakira..."

"Eh dole nakasa haquri nakira nashaidamaki gobe insha'allah zamu dawo domin komai nawa yazama normal..,missing naki zai kasheni iman gara nadawo nadinga jinki a damana shine babban burinah..,wlhy kigyara komai naki gobe dana dawo zamuwuce part d'inmu nima kiji dani..."

"Kai amma nima wlhy nayi murnar dawo wanka domin nimapa nayi missing naka sirrinah..,eye lallai gobe gidanmu zai qara cika..,akwai fira kenan..?"

"Bangane gidanku yaqara cikaba...,bangane akwai fira ba sanar dani wayanne bak'i mukayi gidan namu wayanda firar zata qara yawa dani..?"

"Kaine dai baqon babu wani..,dani da umma ne agidan kawai...,idan kadawo ai munqara yawa koh..?"

"Hakane haskenah!"
Yayi dariya itama tayi..,sunanta yakira har sau ukku....

"Iman Iman Iman.."

Itama ta amsa sau ukku..,sannan yace..
"Wlhy missing naki har baya misaltuwa kifad'aman wanne farinciki kika shirya shayar dani shi gobe idan nashigo...?"

"Farinciki mara misaltuwa zan sanyaka hasken Ruhina..,ni takace nabaka dukan sirrinah..,zanyimaka tanadin farin ciki nishad'i da zance kala kala wanda nake ganin girman k'aunata zata saka a kar'baman akuma yadda dani acikamani burinah...."

Wani dad'i yakashe jabbar domin yaji dad'in kalamanta shima tsaye yake amma saida yasamu gurin zama sannan yasaita muryarshi iya sigar d'aukar hankalin matarshi yace.....

"Burinki buqatunki sun gama cika...,domin ni nakine kome kikeso zanyimakishi da hanxari ba guna guni...,domin nai tattali naso, nasan zaki kuladani goben dakuma k'arshen rayuwarmu insha'allah Ina way gobe 10:am ina tare dake...."

Dad'i Iman taji..,harda wani mirginowa tayi takifa cikinta saman gadon tana wasa da k'afafunta d'aya bayan d'aya....,sai murmushi takeyi ga shi duk Zance d'aya sai tayi shagwa'ba d'aya ciki...,shikuma kamar wanda ke ganinta sai rarrashinta yakeyi....,iman na wannan halin farha tashigo d'akin,itama datasan hakan zata iskota tana waya dabata shigoba..,domin iman kwatakwata bataji motsin qofa ba kuma koh qofar zatayi qara baji xatayiba domin ta tsunduma takai qarshe..., maganar da farha tajiyo taqarshe ita tasakata fita da sauri.....

"Ni takace..,kuma kasan batun yauba na mallaka maka kaina zaka iya shaidar da hakan tun daren dazaka tafi kasan Iman takace domin da miki kaje kabarni wanda sai dana sha gashi don hakama ni idan kadawo wancen wasan kad'ai zamuyi bada wannan mai zafiba...."

Farha najin wannan gabanta yafad'i ita tabani ta lalace..,anya zata iya zama wannan gidan kuwa..? Domin wlhy duk al-amarin duniya yaqarasha mata kai...,toh kuma idan tabar gidan taje ina..? Ita tabani ga qanwarta tafita komai ynx wanda ita take gani acen baya tafita komai..,gashi koh a soyayya kawai tafita komai wai ita Allahn ta....,
Dasauri tafito d'akin tajingina jikinta da qofar ta duqe nan tana kuka...,

"naga Rayuwar taurin kai ni farha...,gashi dana sani duk inda nayi don samun sauqi sai bina yakeyi..,gashi Allah yayima yaya jabbar babban sakamako gashi da qanwata yake more rayuwa ni kuma koh alamar hakan ban ta'bajiba bale har nagane me at cikin aure sai wahala tun ranar da aka kaini har yau cikin halaka nake...,Ya allah kagafar taman laifukana koh nasamu sanyi...."

Tana haka duqe sai jin tayi an riqota kamar daga sama domin tsananin kukan datakeyi ya hanata taji motsin mai fitowa....

"Yaya farha wai menene hakan? Koh yaushe kuka koh wanne lkch kuka gada ki halaka kanki p, kisama kanki ciwon zuciya...,ni nayi tunanin zamanki kusa dani zaisa kirage damuwa hakan yasa naji dad'in hukuncin umma data yanke na xamanki anan domin nima zanfi samun natsuwa..,tashi mushiga ciki, don Allah kiyi shiru hakan..,inbaso kikeyi nima na shiga halin damuwarba...."

Miqewa farha tayi tadubi fuskar yar uwar tata, kuma sai takawar gefe...,iman murmushi kawai tayi taja hannunta suka koma cikin d'akin bakin gado tazauna itama hakan...,farha tadubeta tace...

"Iman don Allah kitayani addu'a Allah yayayeman damuwata,kuma inason Idan yaya jabbar yadawo ki nemaman yafiyarshi may b sanadiyyarki ya yafeman Iman naci mutuncin yaya jabbar wanda nasan zaiyyi wuya yayafeman a gabanshi nake zagin mahaifanshi naci masu zarafi gashi mahaifiyar tashi ita tazamo gatana mahaifana nabijire masu suma sun bijireman ynx..,iman kixamo gatana duk da kema na muzguna maki farko..,kitayani neman gafararshi koh nasamu sauqin azabar rayuwa..."

Rufe fuskarta tayi da gwiwarta tana kuka..,iman kukan ne at bataso taga tanayi domin shi ke 'bata mata rai..,d'ago kan nata tayi ta riqo hannunta tace....

"Yaya farha riqa hannuna kamar yadda kike riqeshi a lkchn da muna zuwa islamiyya tare..,kiriqe hannuna kamar sadda kike riqewa idan munayin wasa..,ni qanwarkice tajini kuma bazan barki ba...,nasan k'addarar rayuwace takawo rabuwarmu farko kuma sai gashi taxamo itace taqara sakawa gashi mundawo guri d'aya..,kisaka aranki k'anwarki bata ta'ba bijiremakiba kuma bata ta'ba riqe abunda kikayiba a zuciyartaba don haka kisaka aranki ni nayafe maki har abada kuma komai yawuce hakan yasa nakeson ki manta da komai kikoma farharki tafarko gwana gurin kwalliya da gayu...,sannan zancen hubbinah kisaka a ranki ya yafemaki domin duk abunda nakeso yana yimanshi kuma zaiyimanshi..,don haka danuwa ki kawar kawai insha'allah gobe yana hanya da ya huta zamuyi maganar dashi..,koh ynx damuwarshi at banso baya kusa dani amma idan yadawo lfy komai normal kinji yayatah..."

Murmushi sukayi dukansu..,farha tace.., "ALLAH YADAWO DASHI LFY.."

Suka amsa ameen..,farha tayi toilet domin yin alwallal sallahr zuhuri domin an fara kira..,itama iman ita tayi sukayi sallah acikin d'akin iman naqarasa sallah tafito nema masu abincin rana....
Farha al-qur'an tad'auka tafara karatu...

A yinin yau haka tayini tanayi a d'akin..,idan iman taga zata takurata da wayar datake da oganta sai tayi waje cen su'barje guminsu duk da firar tafi dad'i a kwance amma gara tabarta tasamu sanyin rayuwa....,
Adarema haka sukayi dai.,babu wata mtsl farha idan tayi karatun tana samun sauqi..,hakan yabata damar turama rasheeda saqon sakin da akayimata kuma tana gidansu ummar jabbar koh da zata nemeta....

Wayewar safiyar da jabbar zai dawo..,iman taje part d'insu tagyara tasaka turare takoh wace kusurwar tagidan ta wanke toilet toilet nasu komai nagidan lfy qlau..,saidai dafa abincinne dole part d'in umma zatayishi domin zaifi sauqi d'auka..,sukuma yabar masu nasu anan...,hakan koh akayi umma kallonta kawai takeyi tana kaida kawo sbd taron miji...,inta wulga nan ta wulga cen sbd yace 10:am zai dawo nan take tafara aikin cikin qorewa gidan yafara amsa zuwan baqo...

Farha tataso domin riqama iman aiki..,amma iman tace tunda bata qarasa warkewaba kawai tabarta ita tayi ai tasaba..,umma ma tace taqyaleta taje tayi karatunta kawai...

Kasancewar ynx farha saida glass take ganin koh wanne karatu sbd bugun da Anwar yayimata afuska yaso ta'ba lfyr idon wanda likitan yace tafara using medical glass domin tasamu sauqin gani...

Tana zaune Iman taqarasa komai tad'auki nasu zuwa dashi part d'insu..,itakuma umma tace zataje mak'waftansu barka zata dawo kafin jabbar d'in ya iso.., Iman kwaso kayan da zata sakawa tayi daga part d'inta tayo part d'in umma anan zata gyara domin tasan dole nan zai fara sauka..,hankali kwance take aikinta domin duka ynx 9:am tayi amma zata shirya dai...,farha kallonta kawai takeyi wani lkch kuma sai tayi tagumi hannunta take sakawa ta tallabe fuskarta tana kallon iman har tawuce d'akinsu..,hakan yasa tazauna anan fallow d'in tana karatunta na qur'ani....

Jabbar tun 8:30 suka sauka don haka yawuduri yima iman bazata kawai basai yakirataba kawai taganshi..,9:05 dai2 yashigo gidan nasu...,part d'in umma yayo domin yasan cewa Iman nacen...,tsayawa yayi bakin qofar fallown koh zaiji d'uriyarta yafad'o kawai taganshi..,shiru yaji hakan yabashi damar turo qofar a hankali domin yabaro kayanshi a anan corridor d'in shigowa...,hangota yayi zaune ta done kanta da hijab jikinta da alama chatting takeyi injishi...axuciyarshi yake cewa.

"Haskenah har ynx ba a daina saka hijab d'inba duk da an tsufa gaban ummar amma kunyarta akeji ikon Allah.."

Ahankali yataka domin ya cire takalmanshi bale aji sautin takalmin..,saidai itakuma tadaina karatun tunani kawai takeyi tariqe fuska da hannunta...,da sauri yamatsa kawai yakai hannu ya rufe mata fuska....

Razana Farha tayi domin lalaba hannun namiji datayi a fuskarta ga qamshin turare na tashi takoh ina...,sai cewa tayi....

"Hasbunallhu wani'imal wakeel..,subhanallh.."

"Hmmm me kike tunani bayan gani nadawo kuma a bazata...."

Sakin fuskar yayi da sauri yaduqo yace..

"Sorry sanyinah..! Na razanaki koh..?"

Jin muryar da farha tayi yasata razana tareda nisanta numfashinta dogo..,amma bata juyoba saida yaqara yin magana tareda dafata....

"Nace sorry koh,kuma nasan za'a yafeman a juyo naga hasken annurin zuciyata..."

Dasauri farha tamiqe tsaye ta juyo...,idonshi na sauka fuskar farha sai ya had'e fuska..,tareda kallon tsana a fuskar da yad'ad'e da roqon Allah gada ya had'asu koh a mafalkine domin ya manta da tsarinta baki d'aya ya wani ja da baya tareda kare fuskarshi da hannunshi yace....

"Mtswww Subhanallh..,Allah dai ya'isa wlhy ta'baki kawai danayi...,shin ubanmi kika shigo gidan nan yi kuma...?"

Gaba yayi abunshi domin maganarta ma bayason ji bale amsarta....,hanyar d'akin da Iman take kawai ya banka qofar da qafa ya fad'a..,dai2 da fitowar Iman gurin wanka ganinshi tsaye rai 'bace yasa gaban Iman fad'uwa... Hijab kawai yajawo gefe yajefa mata tasaka..,sakawa tayi da sauri domin batagane kanshiba..,hannunta yaja kawai yafito da ita fallown farha na duqe na kuka jikin kujerar datake zaune...,

Jabbar hannun iman yaketa ja itakuma tana biye dashi babu sauqi tafiyar bud'e qofar yayi suka fita...

Sai lkchn Iman tagano mtslr datakawo hakan magana take yimashi amma banxa bayajinta yayi hanyar part nasu da ita.........



_ιnα godιyα мαѕoyαnαн dα тα αzιyαrĸυ αĸαιnα..,ĸυмα nαgα ѕo nαgα ĸ'αυnα ĸυмα nα αмѕα ѕυnαn тα мαѕoyα😍doмιn nαgα cαllιng nαgα мeѕѕαgeѕ nα cнαrт dα

22 / 58