Chapter 43 Reading SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee READ HAUSA Novels

SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee

Author :  Khadija bee bee Category :  African Stories & Novels

Chapter   43 / 58

126K to 129K   out of 173.5K words

nasu, bud'e k'ofar ke da wuya farha tace.....

"Allah sarki my Ikram zanyi missing d'inki a ko wane hali na motsa "

Rungumota yayi ta bayanta, hannunshi duka saman cikinta ya azo kanshi a wuyanta yace......

"Waya fad'amaki zaki dauwama a kad'aici? Ki dawo da duka kulawar Ikram akaina, da ga yanzu nine baby Ikram, kinga zan samu gata kenan, Umma tace bazata yafe man ba, idan naci amanar ki, toh kinga ya kamata ki saki jiki dani domin nasamu cika burin umma anan "

Ajiyar zuciya farha taja tare da busar da iskan, sannan tayi dubarar da ta juyo zuwa gareshi, amma kuma bai saketa ba, hakan d'in yaqara d'uro masu wani sabon so a k'wayar idanunsu, domin idanunsu sun nuna situation d'in da suke ciki.
Farha murmushi tayi sannan tayi magana kamar wadda tayi gudu ta gaji, cikin saukar da murya tace.......

"Insha'allah yaya nah bazan k'ara guje maka ba, fatana ayi gwajin jinina a shaida maka ni ko waye, sannan zanfi samun k'warin gwuiwar gabatar maka da nawa burin, domin yanzu akwai shakku da tsorona a gareka, bazaka samu walwalaba kamar yadda kake so "

Yaji dad'in maganar ta, sannan ya k'ara matsowa da ita jikinshi, wanda sai da farha ta rufe idonta, don ganin abun da yake hari a jikinta, hakan kuwa akayi, domin a kujerar palon ya zauna itama ya d'aurata jikinshi, nan take ya aza kanshi saman k'irjin nata, domin turaren jikinta kawai yake shak'a.

Hannunshi zai kai a zip d'inta na baya, da da sauri ta rik'e mashi hannu tace......


"Lokacin sallah "

Ta sauka jikinshi ta ruga da gudu, shi yarasa gane wannan abun, farha fa tayi aure kuma tasan yadda abunnan yake, domin babu wanda zai ajiye kamar farha bai moreta ba, amma tasan yadda akeyin wannan wasar ko ita bata ta'ba fara nuna zata yiman ba, tun ranar da tasama man sauk'i, to me hakan ke nufi? Da nafara wasa da jikinta sai jikinta ya fara rawa, ko kuma ta tsere, ko me kesa hakan?????.??.??


_Toh readers ku bashi amsar wannan tambaya tashi, ni dai bangane ba, kuma ya tambayeni😂_




*~Ta masoya~*

*Bee Been masoya*💞
[3/24, 6:09 PM] 💖HASKEN MASOYA💞: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ÊųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com

My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*

*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋

★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★

_عن أبي هريرة رضي الله عنه قال : "جاء رجلٌ إلى رسول الله -صلى الله عليه وسلم- Ùقال : يا رسول الله، من أحق الناس بحسن صحابتي؟، قال: *(أمك)* ØŒ قال: ثم من؟ قال: *(أمك)* ØŒ قال: ثم من؟ قال: *(أمك)* ØŒ قال: ثم من؟ قال: *(أبوك)* متÙÙ‚ عليه، وزاد ÙÙŠ مسلم : *(ثم أدناك أدناك)*_
*_ya Allah kabamu ikon kyautatama iyayenmu mata sau ukku, sannan mu kyautatama iyayen mu maza, ka bamu ikon yimasu biyayya baki d'aya, da 'yan uwan mu musulmi baki d'aya_*

Page...63


Asubar fari farha ta tashi ta domin samun abun da zatayi kari dashi da gyara sauran kayan ta na tafiya.
Kitchen ta shiga ta fere doya tare da dafata, ta dafa iya wadda tasan zata iya cinyewa, kad'a k'wanta tayi ta soya doyar, source tayi na tattasai da attarugu domin yima doyar mahad'in ci, sannan ta aza ruwan zafin tea.
Sanin cewa Abdul-jabbar ba ci zaiyi ba, yasata dafa iya wadda zata cinye, nan take gidan ya d'auki k'amshin soyar da takeyi, k'arasawa tayi tare da juyewa a foodflax sannan ta shiga zuwa gyarawa kafin ya fito.

Abdul-jabbar ya shirya tsaf, ya fito parlon don ganin idan ta tashi, k'amshi ya daki hancinshi, nan take ya nufi gurin da yaga abincin rufe, dubawa yayi tare da jin sha'awar yaci girkinta ko da sau d'ayane, amma bari yaje yaga me takeyi.

Shiga yayi d'akin nata kai tsaye, tana zaune dressing mirror tana shiryawa ya shigo, gurin da take ya tafi kai tsaye, ganinshi da farha tayi da sauri ta mik'e tsaye don samun abun da zata rufe jikinta da shi, domin towel d'in jikinta k'arami ne sosai, mayafinta ta jawo, shi kuma har ya iso inda take tsaye ya rik'e mayafin tare da jefar dashi inda ta d'auko shi, qudundune jikinta farha keyi domin gabad'aya halittar jikinta a bayyane take, saboda towel d'in k'aramine zai iya faccewa.
Hannunshi ya saka, tare da jawota jikinshi, ya bud'e hannuwan nata yana kallon k'irjin nata, yana lumshe ido yace.....

"Me zaisa don na shigo ki dinga yunk'urin 'boyeman abunda ke halat d'ina? Ki barsu mu gana sosai, domin ina sonsu "

Hannunshi yakai ya shafasu duka, sannan ya lumshe idonshi ya k'ara cewa....

"I like this part k'anwata, wannan yana d'aya daga cikin favorite d'ina da nakeso a jikin macce, sannan inason macce mai wadatar wannan halitta, farha Allah ya baki wannan halitta wadda nakeso naga ina wasa da ita ako wanne lokaci, me zaisa idan kinganni ki dinga sanya mani hijabi tsakanina da su?"

Kallonsa kawai tayi ta duk'ar da kanta, hannunshi ya saka ya tallabo fuskar yace.....
"Ki daina jin kunyata farha, domin ni banida kunya a gefen abunda nake so, farha inasonki, yanzu ma nake jin sonki na shigata sabo, ki saka kayanki muje ki bani break d'in da hannunki, domin daga yanzu ciyarwata ta dawo hannunki, lokaci na k'urewa, 6 ta kusa"

Kasa k'arasa shafar tayi, domin yayi tsaye jiranta yake yi, tsaye tayi gurin drower tata alamar ciro kayan da zata saka, taciro wata doguwar riga tare da gyalen da zata saka ta ajiye a gefen gadon, kallonta kawai yakeyi duk abunda takeyi, domin rik'e yake da wayarshi amma ita yake kallo.
Farha duk ta da burce, domin pant da brah d'inta take so ta saka, amma yak'i fita, hakan taga kamar ba kallonta yake yi ba, ta kwashi undis d'inta zata tsere toilet ta saka, da sauri ya tareta tare da jawota jikinshi, domin yagane nufinta, kallonsa tayi tace.....

"Toilet zanje"
"Me zakiyi ciki?"

"Zanyi wani abu ne ciki"

"Oya bari ni nayi maki abunda zakiyi a cen"
"Ah ah zan iya yi da kaina yaya Abdul, ka bari na shiga kawai "

Kayan hannunta ya kar'ba tare da ce mata....
"Hmmm! Ni zan iya saka maki da kaina"

Rik'e masa hannu tayi, domin har ya fara warware nad'in da tayi masu, da sauri ta k'ara rik'e mashi hannu, hakan ya bashi damar kamota baki d'aya jikinshi ya matse sannan yace mata a kunnenta....

"Ki bari kawai nasaka maki baki d'aya, kinga time ya kusa,gada muyi loosing d'in jirgi"

Runtse idonta tayi, sannan taji alamar zai warware towel d'in, domin har ya fara jawoshi, da sauri farha tace...

"Wayyo Allah na! Wallahi banida komai a jikina, please gada kayiman tsirara bansaba ba "

Kallonta kawai yayi yaci gaba da abunda ya ke yi, sance towel d'in yayi daga sama, ya tsaya na 2 mnt yana kallon ikon Allah, domin farha hannunta tasaka duka biyu ta kare k'irjinta,jaye hannun yayi sannan yace.....
"Alhamdulillah"

Ya shafa sannan ya saka mata brah d'in, ya sanyata lafiya k'lau, domin dama ai ya saba da iya aikin mata tun a Iman, mamaki ya kama farha,amma kuma in ta tuno ba gareta yafara hakan ba, sai tayi shiru, domin tasan zai iya hakan tunda yayi rayuwa da iman cikin so da aminci, itama tana kwad'ayin Allah ya bata ikon kasancewa da shi cikin so da k'auna.

Jin kawai tayi ya ajiyeta gefen gadon ya jawo k'afarta d'aya alamar ta saka pant d'in, bud'e idonta tayi domin taga da gaske sanya mata zaiyi? Haka ko akayi domin k'afar d'aya ya jawo ya saka mata ya jawoshi zuwa gwuiwar,sannan ya mik'ar da ita tsaye ya k'arasa pant d'in zuwa cinyarta, da sauri ta rik'e ta k'arasa sakawa da kanta, hararta yayi yace.....

"Waya sakaki karambani k'arasa sakawa?"

Komai bata ce mashi ba, ya jawo rigarta ya saka mata, sannan yace ta k'arasa sauran aikin yana jiranta parlo, sauri tayi ta k'ara shiryawa tare da mamakin Abdul-jabbar, da irin yanayin rayuwarshi, sai taji nan take ya burgeta, domin bata ta'ba tsammanin zata samu wannan kulawar ba ga ko wanne namiji, amma gashi da wuri ta fara ganin rayuwar da batasan me akeji ba aciki ba.

Fitowa tayi tana k'amshi ta ko wace kusurwa, Abdul-jabbar na zaune ya hangota, nan take ya taro sabuwar gimbiyarshi izuwa dining.

Murmushi kawai tayi mashi, suka zauna a dining sai kunyarsa kawai take ji, saboda abunda yayi mata yau, hakan dai ta daure ta zuba abun karin, ta had'a masu tea.
Matsowa yayi da kujerarsa ya kalleta yace.....

"Ki ciyar dani, kamar yadda kike ciyar da d'iyarki Ikram "

Haka akayi kuwa ta ciyar dashi, shima idan ta bashi sai ya rage ta bakinshi ya bata, har suka ciyar da junansu, aka kwashe sauran abincin aka bawa driver d'in umma da zai kaisu air port domin har yazo.

Fitowa sukayi cikin farin ciki, babu kamar farha da mafalkinta yake ta zamowa gaskiya, jinta takeyi cikin wani good feeling na farinciki wanda batasan ya zata misaltashi ba, shi kuma da ya juyo ya kalleta sai yayi murmushi a zuciyarshi yace "Allah kenan"
Shi gabad'aya ya cire ransa a sake rayuwa da farha, amma gashi cikin k'ank'anin lokaci ya nemi k'iyayyar da yake yimata ya rasa, sai wani haskenta yake gani, tun kafin su d'auki wani lokaci na zamantakewa kenan, ina ga sun yi nisa kowa yasan dad'in kowa, Addu'ar sa itace Allah ya cire mashi kishin da yake ji akanta game da rasa fara bud'eta a matsayin mace, domin hakan kawai nasaka shi jin wani bak'in ciki, sannan yana rok'on Allah yasa bata d'auke da ko wace cuta, domin ita kad'ai zata iya sakashi k'aurace mata, cen kuma sai zuciyarshi kuma tace "anya zan iya rabuwa dake farha, a ko wanne hali kike ciki? Domin wallahi tsohon sonki fitowa yake yi"

Farha kallonsa kawai take yi, domin tasan tunani yake yi kuma mai zurfi, ta'bo hannunshi tayi ta dubeshi, shima ita ya kalla nan take ya sakar mata murmushi, dai-dai da tsayawar motar air port kenan, shima ya rik'a hannunta harda matsashi.

Zuwansu kenan jirgi na shirin tashi, gyara komai sukayi suka shiga, nan take jirgin ya tashi sai abuja........


*RAYUWAR FARHA DA ABDUL-JABBAR A ABUJA, TARE DA KYAKKYAWAR SABUWAR SOYAYYAR SU*

_ku dai biyoni donjin yadda tsantsar soyayya ke tashi a zukatan masoya guda biyu, tare da yiman uzuri domin ina fama da ciwon idone sai slow typing d'in, domin sai na saka glass nake typing, kuyiman afuwa masoya na, inaji daku sosai, a duk inda kuke bee bee na tare daku a kyakkyawar zuciyarta ta soyayyaðŸ˜_



*~TA MASOYA~*
*Bee Been Masoya*💞
[3/25, 10:17 PM] 💖HASKEN MASOYA💞: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ÊųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com

My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*

*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋

★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★

*_اللهم إني أعوذبك من علم Ù„Ø§ÙŠÙ†ÙØ¹...ØŒ ومن قلب لايخشع...ØŒ ومن Ù†ÙØ³Ù† لاتشبع...ØŒ ومن دعوة لايستجاب لها._*
امين يااللهðŸ‘ðŸ»ðŸ‘ðŸ»ðŸ‘ðŸ»

Page...64


*BIRNIN TARAIYYA ABUJA*

Isar su a airport, suka tarar da Abdul-hafeez yazo d'aukar su da motar Abdul-jabbar d'in.
Abdul-hafeez ya sha mamakin ganin amininshi da sabuwar bak'uwa, domin bai fad'amashi cewa yayi aure ba, bai tambayeshi ba, shima bai ce mashi k'ala ba, sai da suka kama hanya sannan Abdul-hafeez ya dubi Abdul-jabbar yace.....

"Aboki kuma sai ka tafi daga kwana biyu har kusan 3weeks, kullum kareema cikin damuwa akan rashin dawowar ka, ga tulin aiki da ka bari "
Gaban farha ya fad'i dum! dum!! Nan take tafara jin wani iri a zuciyarta, game da sunan da taji ance tana cikin damuwa, daurewa tayi domin jin yadda zancen zai kai k'arshe, amsar Abdul-jabbar kawai taji yana cewa....

"Ai na fad'ama oga cewa akwai abun da ya tsayar dani, sai dai zanci uban aiki wallahi, domin jiya ya kirani akan na dawo hakanan, shiyasa ma na dawo yau "

"To masha allah, kace harda bak'uwa kazo mana?"

"Eh k'anwata ce "

"To k'anwar mu ya gida?"

Farha sai da ta had'iye miyan bakinta, sannan tace....

"Lafiya k'lau, ya muka sameku?"

Hafieez ya amsa mata cikin girmamawa,yana driving nashi, sannan ya cigaba da cewa...

"Tun jiya da kareema taji zaka dawo taketa hidima, sannan ta amshi keys d'in gidan da kanta tayi shara ta gyara gidan, ni dai fatana Allah yasa wannan abun yayi, domin yarinyar nan na sonka sosai "

Farha mutuwar zaune tayi, domin wallahi ta girgiza, har k'walla sai da suka zubo mata, juyar da fuskar ta tayi tana kallon garin abuja, amma wallahi baza ta iya tuna menene take kallo ba don tunani take yi akan abun da take ji yanzu.

Abdul-jabbar yayi murmushi, sannan yace ma hafieez....

"To ai gani na dawo,sai ta daina damuwa, sai dai ina ganin sai dai na bawa kareema hak'uri domin k'addara ta riga fata hafeez "

Dai-dai da shigowarsu get d'in gidan su Abdul-jabbar, tare da yin parking a gurin ajiye motoci, anan hafeez yayi parking, Abdul-jabbar ya fara fitowa sannan ya bud'ema farha marfin k'ofar baya ta fito, ranta babu dad'i, ambaton sunan wadda akayi kawai, ji take yi kamar ta mutu.

Suna gaba tana baya biye da su, da gudu masu yimasu aiki maza suka fito da kayan da suka zo dasu a motar zuwa shiga da su ciki.

Masha'allah, gida har gida, domin gida ne naji da fad'i aka tsara, domin sabon gyara Abdul-jabbar yayi ma gidan lokacin da ya tashi dawowa tare da iman, sai kuma Allah bai k'addara ba.
Gidane wanda ya tara gurin more rayuwa naji da fad'i, Abdul-jabbar ya k'era gidan ne da tsarin rayuwar da ya shirya da Iman, amma Allah baiso hakan ba, hakan yasa duk lokacin da zai shigo gidan sai yaji ranshi ya 'baci, amma a yau da zai shigo rayuwarshi na da haske acikin ta, ko me yasa hakan?
Amma yana tunanin sabuwar rayuwar da yazo da itace tasaka hakan.

Abun mamaki yak'i k'arema farha gurin gani, domin wani abun bata ta'ba ganin irinsa ba, har zamanta gidan Anwar naira, bata ta'ba ganin abunda take gani a wannan k'aton falon ba, kujerin ciki kawai zasu iya saka ka rud'ewa domin sun tsaru sosai, duk da wannan burgewa da farha ke gani, bai hanata jin kishin wadda taji ake ambato ba acikin mota, hakan yasa ta samu gefen d'ayar kujeran falon ta zauna jiki babu k'wari, jin muryar Abdul-jabbar kawai tayi yana cewa....

"Kin gaji koh? Tashi na nuna maki part naki, sai ki watsa ruwa ki fito muci abinci ko?"

Kallonsa kawai tayi, tare da sauya idanunta, ya shiga gaba ta biyo bayanshi har zuwa wani had'add'en d'aki wanda k'amshi ke tashi ga sanyin A.C ya garwaye d'akin, amma kuma duka wannan gyaran bai burge farha ba, domin taji wadda tayi wannan gyaran,shigowa tayi tare da cire mayafinta da zaunawa kujerar da ke gefen gadon.

Abdul-jabbar kuma sai yaga jikin farha duk yayi sanyi, ba kamar yadda suke acikin jirgi ba, duk'awa yayi gaban ta, ya dafa gwuwayyunta, ya dubi cikin idon ta yace.....

"Ko da ban dad'e da ke ba a cikin wannan yanayin, nasan cewa akwai abunda ke damunki, ko zan iya sanin matsalarki?"

Kallonsa da farha zatayi, sai hawaye suka k'arasa zubowa, domin dama dama cike suke a idonta, da sauri ya mik'e zaune zuwa gefen ta, tare da rik'ota jikinshi baki d'aya, yace da sauri.......

"Subhanallah! Farha me kuma nayi maki na kuka daga isowar mu yanzu? Nasan dai lafiya muka baro gida, kuma har cikin jirgi lafiya k'lau, please ki fad'aman damuwarki banason na sa'ba alk'awalin umma na rik'eki amana, kuma ko ba haka ba, farha ina sonki, so mai tsanani, me kuma kike zubar ma da hawaye?"

'Dago idonta tayi ta dubeshi cikin wani irin kallo, wanda sai da tsikar jikinshi ta tashi, tace.....

"Waye kareema kuma?"

Murmushi Abdul-jabbar yayi sannan yace mata, dama firarta tasakaki shiga wannan damuwar, har da zubar da hawayenki? Toh daina kuka, kareema budurwa tace, wadda kesona sosai, ko k'uje kareema batason ya ta'beni idan muna tare, sannan batason damuwata ko kad'an, kuma idan don ita kike wannan hawayen ki daina "

Farha jaye jikinta tayi da sauri, tare da matsawa gefe tak'ara k'arfin kukanta tace.....

"Nashiga ukku! Wayyo Allah!!

Da sauri Abdul-jabbar ya matsa gurinta tare da kamota jikinshi, tureshi takeyi tana nufin ya matsa gurinta, wani mahaukacin kishi k'arara, nan take ya gano kishin farha babba ne, to dama haka take? Ya tambayi zuciyarshi, murmushi ya k'arayi sannan ya k'ara jawota jikinshi, mik'ewa zatayi tsaye, ya jawota ta dawo jikinshi matseta yayi, sannan ya kwantar da ita a kujerar yabi bayanta ya haye, domin wannan tsiwar tata ta burgeshi iya matuk'a, danneta yayi ta yarda bazata iya tashi ba, yana murmushin k'eta, itakuma runtse idonta tayi tana zubar da hawayenta son ranta, bakinshi yakai fuskarta da niyyar yin abun da baita'ba tsammanin zai yima farha ba bayan ya auri iman, amma yau gashi ga cikar burin da ya d'auka tun kafin yasan menene rayuwar aure, halshenshi ya saka a fuskarta ya lashe hawayen baki d'aya, wani irin yanayi farha ta kutsa ciki, domin ko a soyayya bata ta'ba

43 / 58