Chapter 20 Reading SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee READ HAUSA Novels

SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee

Author :  Khadija bee bee Category :  African Stories & Novels

Chapter   20 / 58

57K to 60K   out of 173.5K words

cigaba da gani...,Allah yayimaku albarka bakid'ayanku..."

Suka amsa da amin baban ya miqe zuwa d'akinshi..,sukuma suka shirya fita domin zuwa rakiyar farha d'in dagacen suwuce gida...

Gabad'ayansu sukayi sallah suka fito domim rasheeda xata kaisu dagacen ta ajiye su Iman gida....

Haka sukayi dukansu sukafito banda mama domin iya ynx son uwa da yarta yasa mama jin babu dad'i domin taga halin da farhar keciki amma babu yadda zatayi domin mijinta akan wannan mtslr ta farha bazai saurari kowaba.,dole tayi shiru domin farha ita tasiyoma kanta babu yadda ta iya.....

Suka shiga motar dukansu su..,Umma ce gaba rasheeda ke driving momyn rasheeda da iman da farha baya...,suka kama hanya don mayar da ita gidan..

Isarsu bakin gate qato mai kyau...,sai gaban farha yafad'i domin tafi qaunar lahirarta da wannan makeken gidan....

Yaune rana tafarko da iman ta ta'ba zuwa gidan yr uwar tata...,"tap lallai yaya kina cikin daula amma mara amfani gida har gida domin wannan shi ake cema gari guda..."

Azuciya Iman ke zancenta saidai tunaninta bai qarasa isaba saida taga harabar gidan....

Motocine baquwar fuska mota tayi ukku jere guri guda Farha batagane motocinba domin bata ta'ba ganinsuba hakan yasa takawar da zancen suka shiga ciki...,a fallow d'in suka zauna anan suka qarayima farha d'in nasiha datayi haquri...,sukayi sallama suka wuce gida tayimasu godiya...,sannan taqaracema Iman tayefeta bakin qofar fita..,cikin farin ciki Iman tacemata tadaina damuwa komai yazo qarshe......

Dawowa farha tayi tazauna fallown tana nazari da tunane iri iri amma babu yadda ta iya dole tazauna ta rungumi qaddarar da son zuciyarta yasiyomata, taxauna domin tasan bazata ganshiba kuma bason ganinshi takeyiba.....


Rasheeda ta kaisu Iman gida suka bud'e gate suka shiga...,sukuma suka kama tasu hanyar..

Iman nashiga tafad'a toilet domin watsa ruwa sannan tajira kiran mijinta domin duk yau basu gaisaba sbd exam dasuka shiga amma tasan ynx kiranshi na iya shigowa kuma ya hanata aikata komai domin kashemata jiki kawai zaiyi gara tayi shirin kwanciyar baki d'aya...

โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…
Zaman fallow d'in ya ishi farha da tunane tunanenta da hawayenta duka guri d'aya domin ita tasan ynx gara maraya da ita domin shi za'a tausaya mashi domin bayada iyaye...,itakuwa ga iyaye amma babu gata wanda akayimata farko kuma ai yatafi ynx....

Tashi tayi domin shiga part d'inta koh tasamu sanyi gadama yashigo gidan taganshi baqinciki yacikamata zuciya domin ynx 10:30pm yana bisa hanyar shigowa 11 koh 12 kuma batason ganinshi baki d'aya....

Hanyar d'akinta tamiqa saidai tatsaya domin gani takalma na mata da na maza.,tayi kamar takoma baya kuma sai ta tsaya tafara nazari..,toh ai bataji motsiba may b koma suwaye ba anan sukeba...,tura qofar kawai tayi tashiga...

"Innalillhi wa'inna ilaihirraji'un..,la'illaha illallh mohammadar rasululluh (s.a.w)..,subhanallh..."

Tsaye farha tayi domin ganin wani mugun sa'bo saman gadonta, gadon da take kwana amatsayin gadon aurenta yau shine d'auke da yn iska tsirara suna iskanci irin na halaka saman gadon..,nan take kuka yakamata tafara kiran...

"Astagfirullh Allah Astagfirullah Allah..,Allah kagafartaman wannan mugun gani danayi Ganin da ban ta'bayiba rayuwataba sai yau..,Ni farha naga takaina...."

Duk iya wannan tsayin datayi duka basu san tanayiba domin dukansu suna cikin wani hali..,mace biyu ce kwance d'ayar nasaman jikinta tana lasar ganta itakuma namijin na cikin jikin da'yam ma'ana tabayanta yashiga ba tagabantaba shikuma anwar yashiga ta bayanshi yana iskancin irin nasu gabad'aya sun nutse a kogon shaid'anar da Farha bata ta'ba gani irintaba sai yau.....

Imani yakamata tarasa abunyi...,kawai walqatawa tayi tagefen gadon zuwa drower tata domin ta d'auki wayarta data bari tun ranar idan tana nan....

Wani nishi sukeyi wanda farha batasan koh na meneneba tunda bata ta'ba kwatanta wani abu makamancin hakanba...har tad'auki wayar tata basu saniba...,juyowar da d'ayar zatayi daga cikinsu nan taga farha tsaye gefen drower itama farhar juyowa tayi xata fita kawai saitaga fuskar tsohuwar aminiyyarta jamila....

Kuwa farha tayi sbd tsananin gid'ima...,nan take dukansu suka juyo don ganin menene hakan...?

Anwar yataso da sauri zindir haihuwar uwarshi haka suma dukansu suke cikin wannan hali Farha rufe fuskarta tayi domin tsoroma yabata....,hankalinshi kwance zuciyarshi zaune d'an iska ina ruwanshi da kunya...kamo farha yayi ya mareta son ranshi yace....

"Ubanwa yabaki ikon shigoman gida har ki shigo d'akinnan...?"

Ita farha tsoron ganin halittarshi da tsoron ganin k'awarta a cikin d'akin yahanata iya attaka komai sai kuka da rufe ido kawai takeyi domin batason ganinshi hakan....qara fisgota yayi wanda saida tafad'i qasa yace...

"Badake nake maganaba..,uban waye yadawo dake gidannan? K'awarki Rasheeda tafad'ama mahaifiyarta abunda nayimaki hakan itama taje tasanarda mahaifiyata abunda yafaru itakuma tasanar da mahaifina wanda natsani yasan cewa bandaina abunda nakeyiba qarshe mahaifiyata tasanar dashi duk da ba sonki takeyiba...,ynx hakan mahaifina yakirani yace nakama gabana domin bashi babuni a rayuwarshi wanda hakan yasa mahaifiyata kuka..,toh kisani yadda iyayenah suka qini akan ki kema dole na d'an d'ana maki azabar abunda naji wlhy...."

Muryar jamila kawai sukaji tanacewa...

"Haba sweet menene abun tsayawa gabanta kana wasu maganganu marasa dacewa..,gashi tasaka jindad'inmu ya yanke idan har bazama iya jure zama da itaba kawai kasallameta..."

Usman ma dake gefe shima haka yace....

"Ni wlhy bangama dalilin dayasa yayi wannan aurenba gashinan tunda ya aureta koh yaushe cikin matsala yaketa shiga gurin mahaifinshi gashi ynx yace bashi babu shi...,tunda hakane daka ajeta tana 'batamaka show kawai kasaketa shine abu mafi sanyi xuciyarka...."

Nan take yaji shawarar yin hakan itace dai2 axuciyarshi domin gara ya saketa tabarmashi gidan yatara abokan harka kawai....

Juyawa yayi zindir haihuwar uwarshi yajawo wani note buk yafara rubutu...,iya lokacin farha bata gane komai domin cin amanar da jamila tayimata yafi mata komai baqinciki hakan yasa idanunta gabad'aya suka bushe domin tasan qarshen sakamakonta kenan da zata samu domin zamanta dashi bazai yuyuba koh da bai saketaba dole wataran taguje ma wannan gidan....
Juyowa yayi da takarda hannunshi na sakeki saki ukku kuma duk wani abu dakikasan mallakinane a hannuna yafito wanda nabaki banison komai domin ni ba matsiyacibane irinki..."

Kar'ba farha tayi kuma sai hawaye suka zubo mata..,juyawa tayi tajawo trolly d'aya dake jere cikin d'akin tazuba kayanta daduk abunda xata buqata mai mahimmanci da takardunta na mkrnt takama hanyar fita ranta da dad'i kuma babu d'ad'i ciki...,jawo jikkar tayi tayo waje koh waiwayen gidan batayiba....,mai gadin yana ganinta tanajan jikka kuma ga hawaye tanayi sai yataso da sauri domin ynx 12:00am...

"Hajiya lfy zaki fita ynx cikin daren nan,bayan kinsan babu kowa a unguwar nan iya ynx sai kar nukka da miyagu a hanya...?"

Batace masa komaiba kuma baidaina bata haquriba har takai bakin gate d'in sannan tatsaya tace...

"Baba maigadi daganin wata rayuwa gara naje duk abunda zai saman yasaman...,nan dakake ganina wlhy bansan inda zanjeba domin gidanmu bazasu barni na zaunaba domin qaddara tasaka nasa'bamasu kuma sun yafan amma bazasu barni zama gidanba..,kakoga gara namutu koh zan samu sauqi a xuciyata..."

"Hajiya wlhy nima nayi mamakin auren wannan mara mutuncin yaron dakikayi domin iskancin danasan gidannan yana faruwa nakusa da gidanma zai iya qonewa..,nima wlhy hanya nake nema nabar gidan nan amma nakasa samu domin tanan nake ciyar da iyalinah a gadin...."

Share hawaye farha tayi kuma tarasa ina zata dosa domin badai gidansuba wlhy...,kuma ynx idan taje gidansu rasheeda tayi hauka...,cen kuma dubara tafad'omata taje gidan Ummar jabbar kawai..,gobe saitakaita gida may b mahaifinta ya yarda tazauna gidan...,zuciyarta tabata taje cen kawai domin ita kad'aice wadda xatayimata gata ynx kuma gashi jabbar bayanan bale taji nauyin xuwa..,hakan kawai zatayi domin cen kad'ai za a sammata gurin kwana inba jeji xatajeba.....

"Ngd baba maigadi zan wuce.."

"Ah ah hajiya bari nasaka kayan aikina na tsaro saina d'auki mashin d'ina na ajeki domin hanyar nan akwai had'ari..."

Kamar gada tayarda kuma saitaga haksn shine mafita gsky domin bata ta'ba shiga maqwaftansuba bale su taimaketa da hakan...,yad'auko mashin nashi yasaka uniform nashi irin na yn banga d'innan ya aza trollyn gaba itakuma ta hau baya...,cikin ikon Allah tana nunamasa hanya har suka kai bakin gate nasu Iman yace bazayajeba har sai tashiga tukunna....

Wayarta tacire a hnd bag nata tafara kiran number d'in Iman tunda tasan mijinta bayanan saidai datakira Numbr busy takira har sau shida numbr busy gashi 1:30am amma iman waya takeyi....,gashi batada numbr umma tunda lkchn ai bata damu da itaba bale tayi numbr d'inta...

Baba mai gadi yafara knocking d'in gate d'in da qarfi amma shiru....

Iman suna magana da jabbar soyayya sukeyi wadda bata qaunar abunda zaisa wayar ta tsinke haka shima...,sun tsunduma suna sanya junansu farinciki...,wanda har musayar kiss akeyi acikin wayar shi yace.. "nafi iyawa.."
Itama tace...,nadai fika iyawa.."

Murmushi jabbar yayi har sautin dariyar tafito cikin dodon wayar yace... "Hmmm naji amma ai baza'aganeba sai nadawo sai ayi competition koh?"

"Hmm naji ni kasakan hakan idona sun fara qorafi sukeyi..."

Rufe bakinta keda wuya taji bugun gidan da qarfi.., tad'an jaye wayar kad'an a kunnenta har bataji abunda ogan nata yaceba..,sbd fargaba da tsoro 1:30 ana bugun gida koh lfy??

Jabbar cewa yayi...

"Toh haskenah..! Tunda kinfara barci toh *have a nyc dream wit me*.."

Amsamasa tayi amma cikin fargaba domin ba a daina bugun gate d'inba...,kashe wayar Iman tayi ta ajiye domin ta miqe taje d'akin umma ta tayar da ita taji...,fitar da zatayi sai ringing d'in wayarta yashigo..,dasauri tadawo tad'auka number farha tagani saida gabanta ya fad'i....d'aga wayar tayi acikin fargaba...

"Yaya farha..."

"Iman nice abud'emani don Allah..."

"Ok bari nafad'ama umma muna xuwa..."

Kashe wayar tayi takunna wutar d'akin sannan tayi hanyar d'akin umma kohda tashiga itama tana alamar fitowa domin dukan gate d'in bana wasa bane....

"Iman kinji abunda naji ashe..?"

"Eh Umma yaya Farhace koh lfy..?"

"Subhanallah bari nasaka hijab d'ina muje.."

Suka fito tare duk da akwai wuta koh ina amma dare ai abun gudune..,umma tabud'e gate d'in da addu'a..,farha tagani tsaye tareda wani da kayan aiki..,shigowa sukayi ciki shikuma yayimasu sai anjima zai koma gurin aikinshi...,sukayi godiya Iman taja jikkar zuwa ciki umma tarufe qofar da addu'a sannan tariqo farha datake kuka sukayo ciki....

Farha miqama ummar tayi takardar da Anwar yabata takuma fad'amata abunda yafaru tun farko da d'abi'ar da anwar d'in keyi na homosexual d'in duk tasanar da ita....sannan tace tareda share hawayenta wanda saida Iman itama tayi kuka akan jin lbrn abunda mijin na yr uwarta keyi Allah yasa itama bai halakataba domin masu irin wannan halin haka sukeyi da matansu....

Farha tace..., "Umma kinga sakamakon son zuciyar da na jawowa kaina koh...? Gashi baba bazai yrda nazauna dashiba sbd nayi rashin biyayya gareshi farko hakan zaitayi zaton zan cigaba..,bayan wlhy ba hakaba..,Umma naga jarabawa wlhy bazan qara gujema umurninsuba koh kad'an...."

"Yishiru farha Idan bai zauna dakeba ni xan zauna dake...,tunda ni kad'aice gidan sai ynx da yayanku yayi tafiya Imam take nan idan yadawo takoma sai muyi zamanmu tare...,ai farha dama kowa na kuskure a rayuwarshi tunda har kingane laifinki kin nemi gafara ai yawuce...,jarabawace Allah yad'auro maki kuma Allah yabaki ikon cinyeta...,kuje ku kwanta Iman riqa mata kayan saida safe..."

Farinciki gurin Iman ba acewa komai domin taji farinciki mara misaltuwa domin wlhy hakan yayimata dad'i domin haka yasa take k'aunar Uwar mijinta sosai kuma uwa gareta...,taja kayan suka wuce..,suka shirya kwanciya suka kwanta..,iman nayin barci farha tatashi tanata kukan dana saninta.......


Tabd'i zama gida guda farha da iman da jabbar...,chakwakiya๐Ÿค•.........




๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿปafuwan banji garauba amma na warke gani gareku...,ina jiran comment naku.....



*bฬˆeฬˆeฬˆ bฬˆeฬˆeฬˆnฬˆ mฬˆaฬˆsฬˆoฬˆyฬˆaฬˆ*๐Ÿ’ž

[2/20, 6:47 AM] 0mmer Farouk: ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ*
๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง


ยฉยฎ
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com

My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*

*I LUV YOU ALL MY FANS*
๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹

โ˜…TRUE LYF STORYโ˜…
โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…

*_ASTAGFIRULLAHULLAZIE...,MAN LAZIE LA'ILAHA ILLAH ANTA...,ASTAGFIRUKA WA'ATUBA ILAIHIE...๐Ÿ˜ญ_*
*~YA ALLAH KAGAFARTAMUNA XUNUBBANMU WAYANDA MUKA SANI DA WAYANDA MA BAMU SANIBA BAKI'DAYA ALBARKAR MA'AIKI {S.A.W}~*๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป

Page...
โ˜…3โƒฃ3โƒฃโ˜…


ยฎ Likitoci suka gurfana gurin ceto rayuwar farha...,Allah yabasu ikon shed'arta tadawo..., likitocin suma sunyi mamakin wannan abu domin ba hatsaribane...,wanna dukane na bala'i...,

Kiran rasheeda sukayi suka shaidamata cewa yr uwarta na d'auke da ciwon zuciya mai tsanani wanda bai fi 5days da kamataba...,kuma idan ba'ayi hattaraba zata iya rasa rayuwarta ko wanne irin lkch...,sannan suka tambaya wanne irin ibtila'i ne tafad'a haka da har akayimata duka hakan...,?don wannan dukane kuma idan yn fashine sukayimatashi toh marasa imanine naqarshe...,yakamata kisanar da iyayenku idan suna gari....."

Rasheeda hawaye nat zubo mata domin tasan Farha ita tasiyoma kanta musiba da bala'i...,"lallai Anwar shine yayimata wannan rashin Imanin kenan...,rayuwa kenan Farha kinganta....,gashi mahaifanki suma sunjuya maki baya nikad'ai naragemaki mai dubanki... Nima danaso dazan qyalekine..,amma babu aminci idan nayi maki hakan sbd inasonki...."

Azuciya Rasheeda tace hakan...,doctor yadubeta yace..,kinata tunani kitashi kije kisanar da iyayenku domin sud'auki mataki da wuri...."

"Ah ah doctor ynx nikad'ai naragema farha...,domin ita tayi laifinta ynx laifin yajuyo mata....,wannan dukan mijintane yayimatashi...,kuma naje iyayenta sunce bazasuzo ganintaba domin itama ta bijeremasu farko tace sai shi takeso tabar za'binsu dakuma son zuciya....don haka sunce bazasu zoba jiya natafi...."

Likitan yajinjina kai yace..., "lallai rashin biyayya ga iyaye ba khairibane gashi da wuri taga sakamako...,amma kizama jigonta gurin nemamata yafiyarsu domin tana cikin wani hali wlhy wanda 'bacin ran nasune yata'bata..,kuma nima zanyi qoqarin ganin hakan na taimaketa gurin ganin iyayen nata...."

Rasheeda tayi godiya sosai...,kuma taji dad'i...,kasancewar zataje gida amso abincin da akace idan tafalka aba...,sai ta'bar yr aikin gidansu domin koh jiya itace takwana gurinta..,itakuma takoma gida...,fitowarta gate d'in assibitin acikin motar ta..,ta hango ummar jabbar da Iman napape ta ajesu bakin gate d'in....,

Hango iman rasheeda tayi...,tayi bala'in kyau ga haske datayi ga cika datayi...,kamar ba 'itaba....,parking tayi bakin gate d'in tafito...,iman yakira har sau biyu...,sannan tajuyo hangota da iman tayi da sauri tazo suka rungume juna....

" 'yaya rasheeda nan kike aikine...?"

"Ah ah Iman inadai da patient ne anan..."

Sannan umma tajuyo suka gaisa...,
"Dama ynx nake tunanin kiranki domin bamusan gurinba..."

"Eh umma nima da zaxanje gidane...,toh sai na hangoku shine natsaya...,muje koh duk da bata falkaba har ynx tun jiya barci takeyi domin takwana 5batayi barciba inji likitan..."

"Subhanallh da sauqi dai koh...?"

"Eh dasauqi kowanne lkch tana iya falkawa ynx sukace...."

Suka kama hanya amma iman p batasan waye ba lfy ba...,tunaninta yn uwan rasheedan ne kawai....

Suna shiga Farha na falkawa...,yr aikinsu rasheeda na riqe da ita tana kuka tanacewa....

"Anwar Allah yasakaman...,kayi sanadiyar dana bar iyayenah...,nabar kowa da kowa dayazama shine gatanah...,amma gashi kaci amanata..,ashe kai fasiqine..,dazama dakai gara zama da mazinaci...."

Rasheeda najiyo sautin kukan farha tarugo da gudu..,ta rufemata baki...,kuka kawai farha keyi ga ruwan da aka jonamata a hannu har jini yafara dawowa ciki....,

Shigowarsu Iman kenan gabanta yafad'i domin qafafun farha kawai ta hango..,bataga koh fuskartaba....,amma tagane itace...,baki tasaki tasaki tana matsowa zuwa gadon...,rasheeda matsawa tayi gefe riqe da hannunta.....,Iman abun mamaki yabata domin farhace koh mai kama da ita...?
Tsaye tayi tana lissafi domin ta bushe ta rame tayi baqi ga kunburin bugunan fuskata tako ina kwancin belt ne.....

Farha naganinta ta ambaci sunanta...
"Iman...! Rasheeda Iman ne koh gizo takeyiman...?"

"Itace farha.."
Farha 'balle allurar ruwan dake jikinta tayi taqwace hannunta ga rasheeda ta diro saman gado...,ta rungume iman.....,iya lkchn Iman komai takasayi domin bata yarda farha bace..,jin ta ambaci sunan nata sannan ta yarda...,rungumeta tayi itama ta rushe da kuka....

" 'yaya farha kece kika koma haka...?"

"Eh Iman nice..,kinga yadda haqqinku yamaidani koh...,nabar haske nad'auki duhu...,gani yau ina cike da zullumi kaina yabuga yayo d'umi...๐Ÿ˜ญ narasa kowa gatana adalilin so mara umfani gareni...,narasa hankalina lkchn da yakamata ace inada hankali...,naqi sauraron kowa naqi gane kowa..,gani cikin duhu haske yayayeman bansan ynx hakan a ina natsayaba....,iman naqi gane maganarki lkchn da yaci ace nagane kece jinina ta haqiqa...,nad'aukeki mara hankali nice mai hankali...,gashi ynx ina danasani tun kanda aje koh ina....,nagane cewa rayuwata batada amfani...,sbd naqi bin umurnin iyayenah bayan sunyi tarbiyyata da gata da so da k'auna...,sunsoni sona haqik'a amma sai nasakamasu da butulci...,nasan haqqinsune ke fita tunbanje koh inaba gashi *SONE DALILIN HAWAYENAH๐Ÿ˜ญ* Iman kiyafeman kiyafeman naqiki lkchn da yakamata ace nasoki amma nakasa hakan domin son zuciya da rud'anin shaid'an bayan nasan bakiman komaiba...,iman kiyafeni kuma kitaimakeni iyayenmu su yafeni domin nasan bazasu saurareniba koh kad'an.....,hasali kunyarsu nakeji ynx kitaimakaman koh nafita a dajin duhun danake ciki...."

Rungume juna sukayi dukansu suna kuka...,iman tarasa gane kan 'yar uwar tata domin dagani bugune ga fuskarta...,wanda gabad'aya ta kunbura suntul...,d'agowa tayi tadubeta tace.....

"Yaya me yafaru dake har fuskarki ta kunbura hakan...?"

Fashewa farha tayi da kuka sannan tashafa fuskar tace cikin kuka...

"Komai ma yafaru dani Iman....,ynx hakan bansan waye yakawoni nanba...,abu d'aya kad'ai zan iya tunawa a rayuwata danasanin auren anwar...."

Ganin lbrn zaiyi nisa yasa rasheeda zuwa takama farha domin hannunta jini yakeyi sakamakon allurar data cire..,gashi ynx tafalka...qin sakin iman tayi tariqeta sosai itakuma kuka takeyi mai tsanani damuwa biyu guri guda ga mijinta baya kusa gashi halin da tasamu 'yar uwarta ciki...., Umma zuwa tayi ta kamo Iman ta rungumeta itakuma rasheeda riqe take da farha.....

"Haba farha bakida lfy p..,amma sai qara sakamakanki damuwa kikeyi...,ynx nan kika falka...,kibari kisamu relief before kiyi abunda zakiyi...."

"Rasheeda waye yakawoni assibitin nan...?"

"Nice farha..,kikwanta kifuta duba hannunki jini yakeyi p....."

"Rasheeda meyasa kika ceci rayuwata..,? Meyasa baki barniba namutu..,aftr kinemaman gafararsuba....,rasheeda rayuwata batada amfani mudun dangina da dangin jabbar basu yafemanba...,uwa uba shi..,domin shima nacutar dashi....,mutuwata tafiman komai ynx rayuwata....."

Umma sakin Iman tayi taje gurinda su rasheeda suke...,ta dafa kafad'ar farha...,nan take farha tajuyo da sauri...,ganin ummar jabbar ce...,sai kuma tadone kanta qasa taqara gunjin kuka....

"Ah ah farha kidaina kuka kibari kisamu lfyrki sannan...,ynx hakan bansan bakida lfyba jiya nakeji shine mukazo dubaki....,kidaina kuka kinji duba hannunki duk jini...,rasheeda kikira likitan yaduba....."

Tafiya rasheeda tayi ummar ta riqata...,hakan yasa farha sauka daga gadon tad'uqa tana hawaye....,

"Umma kiyafeni...,umma na cutar daku naqi aminta da abunda kukaga shine alkhairi kaina...,Umma kiyafeni kitayani roqon baba da mama su yafeni...,kuma ki roqaman 'ya'ya jabbar ya yafeni....,don nasan bazasujiniba koh kad'an don nasa'ba masu farko....."

"Tashi yawuce ni nayafemaki...,kuma suma zasu yafemaki tunda har kinyi nadama...,Allah yayafemu baki d'aya...."

Shigowar likitan tasa umma gyarama farha kwanciya ta matsa gurin...,duba hannun nata yayyi yasaka bandeji kawai ya d'aure yace basai an qara wasuba sbd dama data falka zasu cire....

Farha tanemi da likitan yabata sallama domin ta warke don Allah...,yace tayi haquri har xuwa gobe..., fita zaiyyi yayima ummar magana akan yanason ganinta office nashi....

Ummar taje..,iman gefe take kawai tana kukanta ita kad'ai...

Likitan yafara magana tareda cema umma....

"Kece mahaifiyar mara lfyr...?"

"Eh likita nice..,"

"Toh don Allah kurabata aure da wanda take aure..,domin takai stage d'inda zuciyarta zata iya bugawa koh wanne lkch...,kuma zai iya kasheta wlhy domin dukan dayayimata shekaranji zai iya sakawa yayi kisa...,toh da ayi ba'aji dad'iba gara tunda wuri arabata dashi...."

"Toh insha'allah za'a duba...,kuma gsky ni yr uwar mahaifiyarta ce..,kuma mahaifin yarinyar nada tsauri..,domin tasa'ba mashi farko...,amma xamuyi qoqarin ganin komai yagyaru domin gada tahalaka...."

Likitan yaji dad'i...,sosai kuma yace ataimaka mashi da number mahaifinta zasuyi magana....,ummar tabashi tayi godiya tatafi....

Itama riqo Iman tayi suka fito...,domin farha tasamu barci...,suka bar yr

20 / 58