LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU

Author :  ZAINAB FALALU Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 25

24K to 27K   out of 73.4K words

ba, wai fisabilillahi baki gaya mishi fita zamuyi ba?"



Sakina da ke ɗaura ɗankwali a gaban mudubi tace "shap na mance ban gaya mishi ba, ko muje
ya sauke mu ne?"



Da sauri mumtaz tace "no, bari nayi wa drivern ku magana, in kuma yana da abinda zeyi zan
hau taxi"



Sakina batace komi ba, looks like kamar da gangan ma tayi hakan.



Mumtaz na fita ta iske an aiki drivern,

Dama ba kowa a gidan, mama asiya taje unguwa, daga su se masu aik.



Agogo ta kalla taga befi awa ɗaya ba su sauka,
Wayarta ta ɗauka ta kira bolt, minti biyar da kiran shi ya ƙaraso, "na wuce" kawai tace wa sakina
ta fice.



Saboda traffic ɗin hanyar, seda suka kai kusan minti talatin kafin suka kai

Daidai da zata shiga ciki call ɗin khalid ya shigo wayar ta
Jin cewa tana airport ne yace ta jira shi yana ta wajen ze ƙaraso, taso ta hana shi zuwa amma
ya kafe se yazo, rabuwa tayi da shi ya zo ɗin.



Bata jima a tsaye ba yayi parking a gaban ta,

Ganin da sauran time ɗin saukar su mama yasa ta buɗe gaba ta shiga

Fuska cike da annuri khalid yace

"Da za ki min buƙulun gaisar da su Abba ko?"

Murmushi kawai tayi, can tace

"yanzun ma ba ganin su zaka yi ba malam, suna sauka zan sauka kai kuma ka kama gaban ka"



Gyara parking yayi da kyau, sannan ya waigo ya fuskance ta, ƙasa da murya yayi kafin yace

"Gani nake kamar bakya so na mumtaz"

Ɗago manyan idanuwan ta tayi ta kalle shi sau ɗaya ta kauda kai, sannan tace

"mene dalilin ka?"

"gashi kuwa bakya so na ga su Abba, ko gidan su sakina da ƙyar fa kika yarda naje"



Kallon agogon wayar ta tayi taga time ɗin ya cika,

Cike da nutsuwa tace
"gobe ina gayyatar ka gidan mu to, Amma yau kam zanji kunya a Abba ya ganmu tare, in ma da
babban wanmu suka dawo wata maganar ce daban"



Marairaice fuska yayi, ba yarda ya iya dole ya haƙura,

Fita yayi da niyar ya buɗe mata ƙofa, yana fita idonta na kaiwa ga agogon shi dake ajiye, wuf
mumtaz tayi sama da shi, daidai ya buɗe mata ƙofar

Cikin ƙwarewa ta saƙe agogon nan tayi ciki wajen tarban matafiya, shi kuma ya shiga motar shi
ya tafi.
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg 31-32



BAYAN SALLAH DA KWANA BIYU




Tun safe da umma b ta fito daga wajen Abba b ta samu su Amal a ɗaki, duk da sun tashi amma
suna zazzaune

Wayace a kunnen hafsa, while Amal kuma handouts ne a gaban ta tana dubawa

Da sallama umma b ta shiga ɗakin,
Stool ɗin gaban mudubi taja ta zauna,

Sallama hafsa tayi da wanda suke wayar ta maido da hankalin ga umma b dake binsu da kallo

Amal ma juyowa tayi gaba ɗaya sukai shiru suna kallon ta.



Seda ta mula da kallon su tukun tace

"Dake zan fara Amal, Amir da faisal wanne yafi gwaɓi a cikin su?"

Bin ta da kallo Amal tayi, dan har ga Allah bata fahimci kalmar "gwaɓi" da umma tace ba
Ɗan shirun da Amal tayi tana nazarin kalmar, umma ta sake maimaita tambayar tana kafe ta da
idanu itama

Da gaske Amal tace "wallahi ban gane me kike nufi ba umma



Ƙafa ɗaya kan ɗaya umma ta ɗora sannan tace

"Bari nayi maki dalla dalla, ina nufin Amir da faisal wanne yafi wani a cikin su?"



Murmushi Amal tayi kafin tace "Amir ɗin dai umma"



Karaf hafsat tace "billahillazi ƙarya take, ko motar da faisal ke zuwa gidannan zata siya ta Amir
sau biyar umma"



Murtike fuska Amal tayi, cike da tsiwa tace "ba ruwanki a cikin maganar nan wallahi"



Da sauri Umma ta ɗaga masu hannu haɗe da faɗin "Ku dakata min" duka sukayi shiru suna
kallon ta, idonta ta maida ga Amal sannan tace "na san kece zaki fi bani matsala, daga yau
zuwa jibin da Abban ku yace zasu tara ku suji zaɓin ku na wanda kuke so, ina so ki fitar da
wanda yafi rigar arziƙi a cikin su, kuma kar naga ba abinda nake so ba"

Sadda kai ƙatsa Amal tayi jin abinda umman ke faɗa

Cike da zumuɗi hafsat tace

"umma wai maganar ta taso ne?"

Seda ta ɗan taɓe baki tukun tace

"Tunda me ƙumbar susa ya bada umarni ai dole a bi,"

Zaro ido Hafsat tayi ta ɗan sake matsowa kusa tayi ƙasa da murya tace

"Umma, to harda ƴar gaban goshin nashi ko mu kaɗai?"

Dariya umma b tayi sannan tace "hmmm, harda ita fa, da Bilkisu da Najwa ma"
Baki buɗe hafsat tace "jakar uba, to da wa za'ayi kenan?"

Wannan karon dariyar da umma b tayi tafi na ɗazu
Seda ta dara sosai tukun tace

"Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta"
Da ga nan tayi gaba ta ja musu ƙofar.

Umma na fita Amal ta kalli hafsat tace

"Mugunta fitsarin faƙƙo ce dai ya hafsa, har wani murna kike saboda wani dalilin ku mara tushe"

Kafin Amal ta rufe baki hafsat tayo kanta a mugun sukwane, dayake Amal ta san hali, dama
tayi readyn fita, aikuwa tana yunƙurowa ta kwasa tayi waje da gudu

Aikuwa hafsat kamar ta ari baki saboda masifa da take zazzagawa, seda ya fauza da basu jima
da zuwa gidan ba ita da khairi suka shiga tsakanin su tukunna.



Ya fauza da yake tana da faɗa sosai ta hau surfa musu bala'i, tace "kuna girma kuna cin ƙasa
shirmen banza"

A fakaice hafsat ta murguɗa mata baki ta juya tana gunaguni.



Kamar yarda umma b ta zaunar da yaran ta tasanar da su saƙon Abba b, haka ma mummy, duk
da Najwa ba ƴar cikin ta bace riƙonta take, hasali ma saboda son da take ma ƴa mace ne kuma
Allah be bata ba yasa yayan ta ya bata Najwa halak malak tun daga yaye

Najwa na kwance a kan doguwar kujera mummy ta sanar mata da umarnin su Abba

jin Najwa bata ce komi yasa mummyn cewa

"ya dai? ko akwai wani abunne?"

Can ƙasan zuciyar ta na zigata ta ce ya faruk take so, amma wani sashi na zuciyar yana ƙwaɓar
ta, murmushin dole ta ƙwaƙulo tukun tace

"nothing mummy, kawai naji maganar ne daga sama"

Shafa kanta tayi tace "mutuncin duka ƴa mace ɗakin mijin ta, tun da Allah yasa sadik na son ki
kema kuma kina son shi ba shikenan ba?"
Gyaɗa kai tayi, tana ƙara cire ya faruk daga cikin ranta dan har ga Allah bata son tayi auren da
ita kaɗai ke so.




******MUMTAZ

Kicin-kicin mumtaz tayi da fuska, jin me sakina ke gaya mata, bayan sun gama shirin tafia
airport tarban Abba ƙ da mama

"Gaskiya guy ɗinnan be iya zuwa ba, wai fisabilillahi baki gaya mishi fita zamuyi ba?"



Sakina da ke ɗaura ɗankwali a gaban mudubi tace "shap na mance ban gaya mishi ba, ko muje
ya sauke mu ne?"



Da sauri mumtaz tace "no, bari nayi wa drivern ku magana, in kuma yana da abinda zeyi zan
hau taxi"



Sakina batace komi ba, looks like kamar da gangan ma tayi hakan.



Mumtaz na fita ta iske an aiki drivern,

Dama ba kowa a gidan, mama asiya taje unguwa, daga su se masu aik.



Agogo ta kalla taga befi awa ɗaya ba su sauka,
Wayarta ta ɗauka ta kira bolt, minti biyar da kiran shi ya ƙaraso, "na wuce" kawai tace wa sakina
ta fice.



Saboda traffic ɗin hanyar, seda suka kai kusan minti talatin kafin suka kai

Daidai da zata shiga ciki call ɗin khalid ya shigo wayar ta

Jin cewa tana airport ne yace ta jira shi yana ta wajen ze ƙaraso, taso ta hana shi zuwa amma
ya kafe se yazo, rabuwa tayi da shi ya zo ɗin.
Bata jima a tsaye ba yayi parking a gaban ta,

Ganin da sauran time ɗin saukar su mama yasa ta buɗe gaba ta shiga

Fuska cike da annuri khalid yace

"Da za ki min buƙulun gaisar da su Abba ko?"

Murmushi kawai tayi, can tace

"yanzun ma ba ganin su zaka yi ba malam, suna sauka zan sauka kai kuma ka kama gaban ka"



Gyara parking yayi da kyau, sannan ya waigo ya fuskance ta, ƙasa da murya yayi kafin yace

"Gani nake kamar bakya so na mumtaz"

Ɗago manyan idanuwan ta tayi ta kalle shi sau ɗaya ta kauda kai, sannan tace

"mene dalilin ka?"

"gashi kuwa bakya so na ga su Abba, ko gidan su sakina da ƙyar fa kika yarda naje"



Kallon agogon wayar ta tayi taga time ɗin ya cika,

Cike da nutsuwa tace
"gobe ina gayyatar ka gidan mu to, Amma yau kam zanji kunya Abba ya ganmu tare, in ma da
babban wanmu suka dawo wata maganar ce ta daban"



Marairaice fuska yayi, ba yarda ya iya dole ya haƙura,

Fita yayi da niyar ya buɗe mata ƙofa, yana fita idonta na kaiwa ga agogon shi dake ajiye, wuf
mumtaz tayi sama da shi, daidai ya buɗe mata ƙofar

Cikin ƙwarewa a harkar ta saƙe agogon nan,



Sallama suka yi sannan tayi ciki wajen tarban matafiya,
shi kuma ya shiga motar shi ya tafi.
Mumtaz na shiga ta ga bala driver da sani driver zaune suna jiran ƙarasowar su Abban,

Tacan gefen su ta zauna, sam basu lura da ita ba

Bata jima da zama ba su mama suka fito

Da gudu taje wajen iyayen nata, Abba ƙ se murmushi yake haka maman ma

Ɗaya bayan ɗaya ta rungume iyayen nata tana musu sannu da zuwa

Gasu bala a gefe suna ta aika gaisuwar su suma cike da girmamawa .



Ganin mumtaz tare da su bala ne mama tayi tunanin tare suka zo.



Abba ya miƙa wa bala no ɗin dake jikin tag ɗinsu na kaya yace

"bala kai ka tawo mana da kayan, kai kuma sani muje"



A yarda suka zo bala ne ya ɗakko motar da ze ɗauki su Abba, amma jin Abban yace balan ya
tsaya ya ɗakko kayan su yasa sukayi sanjen mukulin motocin



Hakan kuwa akayi, bala ya tsaya shi kuma sani ya jasu zuwa gida

Abba da mama baya suka shiga, mumtaz ta shiga seat ɗin gaba,

Gaba ɗaya murnar ganin iyayen nata yaƙi ɓoyuwa akan fuskar ta.



Jingina da kujera mama tayi idon ta a rufe tanajin yarda Abba ke amsa calls akai-akai na
gaisuwar sallah

Mumtaz kam shiru tayi tana sauraron wani ɓangare na zuciyar ta for the first time yana ayyana
mata tayi daidai kuwa ɗaukan agogon nan da tayi?



Sosai bala ya shararo motar ganin yarda titin ba cinkoso, unexpected wani me keke napep ya
gifta musu
Da hanzari ya kai ƙafarshi kan burki, amma inaaa sam burki ya saki ya shafe gaba ɗaya

A firgice suka haɗa baki shi da mumtaz wajen faɗin "INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN"

Wajen ƙoƙarin kauce wa me keken, motar ta ƙwace tayi kan shagunan mutane dake gefen
hanyar gadan gadan



A firgice Abba ke faɗin " ka taka burki mana,"



Shima sanin a firgice yake kokawa da sitiyari haɗe da faɗin "wallahi ba burki yallaɓai"

mama kam salati kawai take, mumtaz tana ihu tana haɗawa da salati,

Abba kam bakin shi ya ƙi dena faɗin "Kamar ya ba burki, kamar ya ba burki" can kuma se ya
hau salati, haɗe da rungume mama ƙam a jikin shi ganin tsananin tashin hankalin da ta shiga



Mutane dake waje suna kallon mugun tashin hankalin nan wasu na salati wasu na ihu, wanda
motar ke tunkarar su kuma suna ta neman ceton kawunan su.

ALLAH YA TSARKAKE MANA ZUCIYAR MU, YA RABAMU DA HASSADA DA KUMA AIKATA
AIKIN DANASANI.

KUYI HAƘURI DA WANNAN PLS, JIKI DA JINI.

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
SHARE PLS.




LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg 35-36

Ya faruk suna tafiya Abba b yace

"Wasu a cikin ku su ragu aje wajen jana'izar sani, wasu se su tsaya"



Uncle ƙasim yace "Tunda Drn yace suna buƙatar hutu sosai kamata yayi ace matan duka su
koma gida, mu kuma har munje mu dawo basu farka ba nake tunani"

Ta gefen ido Abba b ya saci kallon kusan kowa kafin yace

"Hakan yayi" dukan su matan Abba ya ce su tashi su tafi,



Cike da nutsuwa da sanin yakamata umma ƙarama ta matsa kusa da Abba b, seda tayi ƙasa da
murya tukun tace

"Ya kamata ace ko ni ko hajiya nabila(umma babba) wani ya tsaya a cikin mu fa"



Kallon ta shima yayi kafin yace "ba'a buƙatar kowa inji likitan, gara ma kuje gida a shirya abinci
dan nasan zuwa anjima hospital ɗin nan ze cika da jama'a,"



Umma babba nadaga gefe tana cika tana batsewa ganin yarda umma ƙ ke wani shishahigewa
kamar itace babba.

Ya maryam dake kusa da umma b tace "kalli mutuniyar umma, ita ala dole so take ta ƙwaci
matsayin ki a idon kowa fa"



Taɓe baki umma b tayi kafin tace "ai bata birgeni ba, kamata yayi ace itama ta kwanta se asan
taji ciwon nasu sosai, amma wannan kwaɗifirin ba birgeni yake ba, shishshigi ba kwarjini"
Amal dake tsaye a gefe tana jin abinda mahaifiyar su da kuma ƴan'uwan ta keyi, sosai takaici ya
tokareta a wiya, ba'abin tayi magana ba su hayayyaƙo mata,
Rai a ɓace tace "Ya sabrina tafiyar ko kuma zaman?"



Dukan su suka kalle ta, cike da takaici umma b tace "ai fa, sabrina kin taɓo waƴanda tafi gani da
mutunci akan mu, bari muyi kaffa-kaffa kar muji duka daga sama"



Gefe Amal ta sake yi, bata ce komi ba sema ƙara ƙyamar irin halayar su datayi.



Dukan ahalin sun mimmiƙe da niyar tafiya, wasu zasuyi gida wasu kuma zasu wuce janaizar
sani kenan khalid ya iso wajen shi da wani abokin shi kamal



Ganin manyan shi na wajen aiki tsaye a ta gefen emergency yasa shi fasa wucewa ciki ya nufi
wajen su

Cike da girmamawa ya mimmiƙa musu hannu

Duk cikin su ba wanda ya sheda fuskar khalid se uncle Abbas

Khalid yace "Halan kun kawo wani ne sir?"

Uncle Abbas yace "megida da iyalan shi ne suka samu accident"



Cike da jimami yayi Allah kyauta, suna nan tsaye ya hango sakina dake nufo inda suke

Tana zuwa tace" sannun ku, ba'a bari a shiga wajen su fa"

Da mamaki khalid yace " its seems kamar yallaɓai Abbas na da alaƙa da su mumtaz ko?"



Murmushi sakina tayi kafin tace

"Halan bata gaya maka ƙanin ubanta bane uwa ɗaya uba ɗaya?"

Rungume hannun shi yaya a ƙirjin shi, idon shi a kanta yace "waye mahaifin ta a cikin su?"
Jin kamar ana kallon ta yasa ta juya, ido huɗu suka haɗa da Amal dake musu kallon ƙurilla,
Taɓe baki tayi tukun ta jiyo tace "Abubakar sule ƙaraye, shine mahaifin ta"



Shiru khalid yayi yana tuna haɗuwar su a makka da kuma sanda yake gabatar mata da kanshi,
Da kuma kallon data mishi da yace a ASK TXTL COMP, yake aiki

Murmushi me ƙayatarwa ya saki kafin a ranshi yace "shine taƙi sanar dani".



Ya ɗora da "Allah ya tashi kafaɗun su gaba ɗaya"

Da "Amin sakina da kamal suka amsa"



Sun ɗan jima, dan suna a nan kowa da kowa ya tafi, ya rage daga sakina se mama Asiya ne
kawai zaune a wajen

Suma basu ƙara daɗewa ba suka yi musu sallama da niyar zasu dawo zuwa jimawa.




****YA FARUK

leda ɗaya kawai aka ɗiba bayan gwaje-gwajen da ya dace ayi ma wanda ze bada jini



Cike da kulawa nurse ɗin tace "zaka iya kwanciya ka huta sir"

"Thanks" kawai yace

rufe idon shi yayi yama rasa wani kalar tunani zeyi a wannan marrar.




Gado uku ne a ɗakin, amma ko wanne ɓangaren gado akwai labulen da ya sakaya gadon

Gadon farko Abba ƙ ne akai, na tsakiya mumtaz, na can lungu kuma mama

Dukan su bacci suke, a fuskokin su zaka ga tabbacin baccin ba na daɗi bane
Abba ƙ an naɗe hannun shi na dama da bandeji, sannan ga drip an saka mishi

While mama drip kawai aka saka mata

Se mumtaz da ake wa ƙarin jini, saboda jinin data zubar,

Zamu iyacewa tafi kowa jigata tunda ta side ɗinta komi ya faru

Ga tsananin firgice da dukkan su suka shiga, in mukayi duba ga sani da ya riga mu gidan
gaskiya, shi bako ƙwarzane a jikin shi, zuciyar shi ce ta buga farat ɗaya, ya zama sanadi da
kuma lokaci.



Bayan nurse ɗin ta gama saka wa mumtaz jinin ta fice haɗe da sakayo musu ƙofar.




Ya faruk seda ya huta na kusan minti talatin kafin ya taso ya fito, sanda ya dawo bakin
emergencyn ya iske ba kowa da ya sani

Ciki ya shiga, cikin sa'a sega nurse ɗin data kaishi aka ɗiba jinin shi, da azama yace

"excuse me"

Waigowa tayi, fuskar ta da fara'a tace

"laa, anya ka huta ɗin kuwa?"

Shima fuskar shi ba yabo ba fallasa yace

"Zan iya ganin su kuwa?"

Da sauri tace "why not, duk da dai an sauya musu ɗaki, kuma bacci suke, amma zaka iya
shiga"



Gyaɗa kai yayi tukun yace "room number?"



Kai tsaye tace "muje na kaika sir" ta ƙarashe maganar tana wani far-far da idanu

A cikin zuciuyar shi yace "sakarya!"
Tana gaba yana biye da ita a baya har suka kai bakin ƙofar tukun ta tsaya, tace "shine ɗakin sir"

"nagode" ya sake cewa,

Ganin bashi da niyar ƙyasata yasa ta juya gwiwa a sace tayi gaba.



Ya faruk ya jima a bakin ƙofar tsaye, ya kasa samun ƙwarin gwiwar buɗewa ya shiga

Tsananin tausayin ahalin ya gama mishi rugu-rugu a zuciya

Fargabar shi ɗaya shine besan a wani yanayi ze shiga ya iske su ba

Yana nan a tsayen, hannu ɗaya a jikin handle ɗin ƙofar hannu ɗaya kuma a aljihin rigar shaddar
jikin shi

Ƙasa-ƙasa ya fara jin kakarin Abba ƙ na tashi, har yayi kamar ya juya ya kira likitan ya fasa, da
sauri ya murɗa ƙofar ya shiga a kiɗime

Ga mamakin ya faruk, Mutum ne tsaye da rigar likitoci a jikin shi, gaba ɗaya ya aza nauyin shi a
kan pilon da ya ɗora akan fuskar Abba ƙ

Ga karaya a hannu ɗaya, ga rashin ƙarfi gaba ɗaya, duk da haka Abba ƙ na neman ƙwatar
rayuwar shi a hannun wannan mutumin.



Lukutar masifar da ya faruk yayi tozali da ita ba ƙaramin gigitashi tayi ba

A firgice hankali a tashe ya faruk yayi kan wannan mutumi da gaba ɗaya fuskar shi da kuma
hannayen shi dik a rufe suke

Wata muguwar shaƙa da wawura ya kaimishi, duk da shaƙar da ya faruk yayi ma wannan
mutumin besa ya ɗaga Abba ƙ ba

Seda yaji azaba kamar ya faruk ze ƙwaƙule mishi maƙogoro tukun ya ɗaga Abba ya fara neman
ceton kanshi



Sosai tari ya sarƙe Abba ƙ bayan mugun ya sake shi

Akan idon shi ya faruk ke kokawa da mutumin yana son ya cire mishi mask ɗin fuskar shi,
Duk ƙwaƙwar shi na son ganin waye wannan mutumi haka ya haƙura, saboda mugun tokarin da
ya kai mishi ta gefen cikin shi

Akan idon Abba ƙ da mama da ƙarar kokawar su ya farkar da ita mutumin ya fece a guje

Ya faruk na duƙe riƙe da gefen cikin shi na dama.




Karkarwa kawai jikin Abba keyi,

9 / 25