Author : ZAINAB FALALU Category : African Stories & Novels
ɗakin ta?"
Ɗan taɓe baki aunty hajara tayi kafin tace "ku jira ku wuce da ita muna zuwa"
Gaba ɗayan su jikin su yayi sanyi ganin yarda fara'ar su ta ɗauke lokaci ƙanƙani ta koma yaƙe
Farat ɗaya umma babba ta fara hasashen akwai matsala tsabar ƙwarewarta asa ido
Suna nan a zaune babu wanda a cikin su yayi yunƙurin yin sallar balle har su taɓa kayan
ciye-ciyen da aka jera musu
Mumtaz kam kanta na a cikin hijabi, gaba ɗaya ta nemi nutsuwarta ta rasa, tsananin faɗuwar
gaban datake ji ya zarce na ko wani lokaci gaba ɗaya ra kasa sukuni.
Aunty hajara da wata ƙanwar su suka iske mami a a ɗaki ta haɗa goshin ta da bango
Idon nan nata ya kaɗa yayi jajir
Kallon su kawai tayi tama kasa cewa komi
Amma kallo ɗaya zakai mata ka gane tana cikin tsananin ɓacin rai
Dafa kafaɗar ta aunty hajara tayi tace "Meye mafita?"
Cikin karayar zuciya tace "ban sani ba aunty hajara, gaba ɗaya tsanar yarinyar ta gama rufe ni,
banji ko ta zauna da khalid zanso ta ba, kuma ba zan taɓa sakin jiki da ita a cikin zuri'ata ba"
Gyaɗa kai aunty hajara tayi, tana ƙara jinjina wannan al"amari a cikin ranta
Can mami ta sake faɗin "Ɗa ɗaya tilo da Allah ya bani nake saka ran samun zuriya me yawa
daga tsatson shi kuma ya jarbce shi da auren ɓarauniya, wasu kalar ƴaƴa zata haifa mishi
kenan ni ƴasu?"
Ta fashe da kuka tana sake hango yarda mumtaz ta ɗauki abin hannun nan
Cike da jimami aunty hajara tace "dole khalid ya san wa ya aura gaskia, kuma tun farko inda
ansan haka halin ta yake bazamu tama yarda ya aure ta ba, kuma in kika kalli yarinyar bazaki
taɓa cewa zata aikata ba"
Zama mami tayi haɗe da dialing no ɗin khalid
Ringing biyu ya ɗaga,
Kafin yayi magana tace "kazo yanzun nan ka same ni"
Har ya buɗe vaki yace "lafia mami?" yaji ta tsinka
Da ɗan mamaki a fuskar shi ya kalli kamal yace
"Muje, mami na kira na"
Suna a mota dama, daga inda suke zuwa gidan ba wani tazara, cikin minti biyar suka ƙarasa
ƙofar gidan
Gab da ze shiga gidan ya faruk yayi mishi fitila
Dawowa khalid yayi, saitin ƙofar ya tsaya,
A hankali ya faruk ya sauke glass
Cike da fara'a khalid ya miƙa mishi hannu suka gaisa, sannan ya faruk yace "In ka shiga kace
musu muna jira fa suyi sauri"
Still da fara'ar shi yace "yanzu kuwa, ai yakamata ace sun gama komi zuwa yanzu, ina zuwa"
ya juya zuwa cikin gidan.
Direct ɗakin mami ya nufa, yana shiga yagan su wani iri
Da fara'ar shi ya shiga, amma ganin yanayin da mamin shi ke a ciki yasa jikin shi yin sanyi
Jiki a mace ya samu waje ya zauna haɗe da faɗin "me ya faru mami?"
Ganin shi da mami tayi yasa idanun ta sake cikowa da ƙwalla dan bata so yaji kalar ɓacin ran
da take ji a yanzu, kuma abu ne da bazata taɓa iya ɓoye mishi ba sam
Cikin ƙagara sa kuma tsoro da yafara kama shi yace "Dan Allah ku faɗa min meke faruwa, na
fara jin tsoro wallahi"
Kasa magana kowa yayi, se can mami tace "Ina zuwa" ta tashi ta fice
Palon da aka aje su mumtaz ta nufa
Ciki-ciki tayi sallama, tukun tace "zaku ɗan bani aron yarinyar ku pls"
Rassa, haka mumtaz taji a ƙirjin ta, bama ita kaɗai ba har su goggo safiya seda suka ji maganar
mami wani banbaraƙwai da ita, ba kara sam a maganar ta
Jin kowa yayi shiru ne yasa umma babba tace "Tashi mana mumtaz" ta yunƙura ra kamota
kamar da gaske
Ganin umma babban zata taso mumtaz yasa mami tace "Da kin zauna hajiya, ita kaɗai muke
son gani"
Baki sake kowa ke bin mami da kallo, gaba ɗaya ta sauya ba kamar da suka shigo ba, yanzu
har wani hare-hare take da kuma maganganu na gadara
Cak mumtaz ta tsaya taƙi yarda ta bi mami, gaba ɗaya tsoro ya gama rufar mata
Ba ganin fuskar ta take ba, amma ji take kamar ta san muryar kuma ta rasa a inda tasan
muryar.
Mami har ta kai ƙofa ta waigo jin mumtaz bata biyo ta ba
Ganin haka yasa ta dawo da baya tace "wanda suka fi kusanci da ita mutum biyu suzo muje
A fili umma babba tace "yau ko mun kawo kanmu gidan iko"
Goggo safiya da itama zuciyar ta na gaf, kawai tana basarwa ne ta miƙe tace "muje to"
Umma babba tayi tsalan tace "ai ba kyaje ke kaɗai ba yaya safiya, muje na rakaku nima"
Suka saka mumtaz a tsakiya suka bi bayan mami da tayi gaba
Har cikin bedroom ɗinta taja su
Khalid na ganin mumtaz a tsakiyar su goggo safia ya miƙe tsaye, da fara'a yace " sannun ku
gaggo, bisimillah ga waje"
Ya tashi daga kujerar da yake umma b da goggo safiya suka zauna
Ganin an bar mumtaz a tsaye yasa ya janyo mata kujerar gaban mudubi
Ganin taƙi zaman, kuma a cikin iyayen nashi ba wanda yayi yunƙurin cewa ta zauna yasa ya
rufe idon shi ya kama hannunta ya zaunar da ita,
Sannan ya tsaya ta ɗan saitin ta, da gangan ya rinƙa taka mata ƙafa yana mata waiwayi.
Jin shuru kowa ya kasa magana yasa goggo safiya faɗin "To mu kin ƙira mu bakuce komi ba ga
lokaci na tafiya dare na daɗa yi"
juyawa mami tayi ta kalli aunty hajara tayi mata signal da ido ta fara magana
Gyaran murya aunty hajara tayi kafin tace " faruk da kai zan fara"
Gyara tsayuwa yayi ya fuskance ta da kyau, dan wannan abun sabo ne a idon shi shikam
Shiru ta ɗanyi sannan tace "ku gafarce ni akan abinda zan faɗi hajiya, amma gaskiya an ha'inci
ɗanmu da ba'a sanar da shi cikekken halin ƴarku ba!"
Duuuuuum, haka ƙirjin mumtaz dana khalid da goggo safiya kai harma dana umma babba ya
bada wannan sautin a kusan tare
Da sauri khalid ya kalli yayar baban nashi yace "Wannan wace irin magana ce aunty"?
Goggo safiya ta ƙanƙance idanun ra tace "Me kike nufi da an ha'inci ɗanku??"
Gyara zama sosai ta sake yi sannan tace "eh hakan dai nake nufi, an ha'inci ɗanmu, kun san
sarai ƴarku na ɗan hali,baku faɗa mana ba, da akazo neman auren ta ai se ku faɗi ba wai ku
ɓoye ba, daga baya se anyi abu ta yi halin a inda ze tonu azo ana kai ruwa rana, ana wallahi
tallahi"
Bama ta kai ƙarshe ba mumtaz ta buɗe fuskar ta tana bin kowa dake palon da kallo har idonta
ya sauka akan mami da se a yanzu ta tuna da inda ta santa
Goggo safiya da umma babba kuwa a kusan tare suka miƙe tsaye,
salati suka hauyi haɗe da kallon aunty hajara da mugun mamaki da al'ajabi
Rai a ɓace goggo safiya tace "wannan wani kalar sharri ne daga kawo yarinya?
Umma babba tayi caraf tace "bayan sharri harda cin fuska ma wannan ai"
Khalid kam jin mugun kalamin bakin auntyn nashi yasa shi ƙamewa a wajen, ido jajir yake
kallon mamin shi da sauran, sam ya kasa cewa komi banda rawar leɓe dayake faman yi
Jiki a mace mami ta kalli mumtaz da gaba ɗaya bata san a wani kalar yanayi take a ciki ba tace
"Ya kike da suna, muga abun hannun ki"
Gaba ɗaya kallo ya koma kan mumtaz datake ta muƙumuƙu da hannuwa a cikin hijabi
Da sauri ɗayar ƙanwar mamin tace "zata cire ne fa"
Tsabar zuciya yasa goggo safiya matsowa gaba mumtaz ta yaye hihabin ta,
Aikuwa se gashi tana ƙoƙarin cire abun hannun
Khalid na tozali dashi yayi baya baya kamar ze faɗi, Allah ya temakeshi bango yayi mishi waigi
da ya sha ƙasa
Finciko abin hannun goggo safiya tayi kafin tace "wannan abun kike nufi ko me?"
Gyaɗa kai mami tayi, hannu ta miƙa da niyar karɓa ta fasa, can tace
"Kaf ƙasar nan ciki da kewayen ta wannan abun hannun ne kawai, ba zaki taɓa samun kalar shi
ba,
kai ko irin shi banjin zaki samu ba
Gaɗon shi naci daga wajen mahaifiya ta, itama daga wajen tata mahaifiyar ta gajeshi,
Bama wannan ba,
har sanda ƴarku ta saci abin nan ina da videon ta,
maganar gaskiya inda na san wannan ce yarinyar da ɗana ze aura bazan taɓa bari ba,
ba wai dan yana da muhimmanci a waje na ba,
se dan ba zan taɓa bari na haɗa jini da jinin sata ba"
Dafe ƙirji umma babba tayi
A yayin da goggo safiya kuma ta saki abin hannun a ƙasa tana wa mami kallon tuhuma da
kuma tsantsar rashin mutunci
Idon mumtaz kam ya gama soyewa, bakin nan ya bushe tsabar rashin isheshshen miyau a
bakinta
Khalid kam gaba ɗaya ya lula tunanin maganar da sakina ta faɗa mishi akan mumtaz kwanakin
baya.
Ido jajiri goggo safiya ke kallon videon da mami ke nuna mata
Umma babba ta gama yarda da sadaƙarwa, tunda har ga Allah bata yarda ba daga farko seda
taga videon tukun
Mumtaz na nan zaune idon ta a ƙasa tana kallon abun hannun da goggo safiya ta wurgar
Jiki a sanyaye ta duƙa ta ɗauki abin hannun ta matsa har gaban mami ta tsugunna
Se a sannan idanun ta suka kawo ruwa, murya na rawa tace "ki gafarce ni mami, kuma ki yafe
min, sannan dan Allah ku bani dama ta biyu karki yanke hukunci cikin ɓacin rai, wallahi sata ba
halina bane, haka nan na tsinci kaina da kwaɗaituwa da abun mutum in na gani"
Wani mari me raɗaɗi goggo safiya ta yarfa mata da ya hanata ƙarasa maganar data faro
Cikin tsananin fushi tace "Da gaske bayan wannan ma kin taɓa ɗaukar abun wasu mumtaz?"
Kafin tace komi khalid shima cikin tsananin ɓacin rai yace
"Munafuka halinta ne wallahi, ni kaina tamin sata amma na kasa yarda cewa itace saboda
yardar dana mata, sannan banyi mamakin satar da kike ba tunda dama duk me bin maza
bazaka taɓa rasa shi da ƴan ɗauke -ɗauke ba"
Ido a waje kowa ke kallon khalid jin abinda yace
Ita kanta mumtaz jin maganar khalid ba ƙaramin ƙaraa saka ta wani mawuyacin halin yayi ba
Amma kalmar bin maza da yace yasata saurin faɗin "Kar kayi min sharri khalid, eh tabbas
nasan ni na ɗauki agogon ka a airport, amma kar ka ƙara da abinda baka da tabbas akai"
Kamar ze maketa ya matso, da sauri mami ta riƙe shi, yace "Tunda baki da kunya ai zaki faɗi
hakan, kuma in kowa yayi maki ƙarya ina jin jinin ki SAKINA bazata munafurce ki ba"!
Mumtaz tace "SAKINA"!
Fashewa da kuka khalid yayi ya rungume mami da itama gata nan dai
Cikin kuka yace "wallahi mami bayan sata har maza take bi, ƴa'uwar ta musamman takirani ta
sanar dani amma ban yarda ba se yanzu, wallahi mami ba zan yarda da rufa-rufar da akayi min
ba se na bi kadi na"
Goggo safiya da umma babba kam basu da bakin magana tunda har mumtaz ta amsa da bakin
ta
Kunya kam ta gama saka su a cikin ta, dan ji suke ina ƙasa take su shige
Jiki a mace umma babba tayi hanyar ƙofa ta fice, goggo safiya bata da wata mafita itama tabi
bayan ta
Suka bar mumtaz a ɗakin a tsugunne riƙe da ƙirji.
Waigowar da khalid zeyi ya ganta durkushe, a mugun fusace yace
"Ki tashi ki bisu kafin su bar gidan nan, dan wallahi bazaki kwana a gidan nan ba"
Da sauri mami tace "kull kalid, bana son ka sake furta komi"
Da ƙyar mumtaz ta lallaɓa ta miƙe itama ta fice
Umma babba cikin ƙarfin hali tace ma sauran mutanen da suka zo tare su taso su tafi
Goggo safiya kan waje tayi tana kuka kashirɓan.
Ya faruk na hangota ya sakko ganin yarda ta fito a firgice ga kuma kuka
Gaban mota ya buɗe mata ta shiga, kafin yace "Halan haka kika barota itama tana ta kukan
ko?"
Bawan Allah besan abinda ke faruwa ba 🥹
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg61-62
Kukan goggo safiya yaso ba ya faruk dariya,
Yarda ta aza hannuwan ta duka biyu a kanta ka rantse da Allah wata gagarumar mutuwa akayi
mata
Ganin bata da niyar magana ga kukan dake ƙara yawa yasa shi ficewa a motar, haɗi da hango
su umma babba da fitowar su kenan.
Ganin jikin umma b a sanyaye itama kamar warce ta yi kuka yace "lafiya dai ko umma"
Murmushin takaici tayi tace "da sauki dai"
Bata gama rufe baki ba suka ga fitowar mumtaz da gudu tayi hanyar titi
Daga cikin mota goggo safiya ta hangota, a guje ta fito itama
A ruɗe goggo safiya ke faɗin
" ku bita kar tayi wani wajen, faruk ku bita, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! ku bita bata cikin
hayyacin ta"
Shima a kiɗime yace "wacece me akayi mata"
Kwata kwata beyi tunanin mumtaz bace tayi wannan fecewar
Umma babba ma a ɗan ruɗe tace "mun shiga uku, muntaz ce fa"
Umma b bata kai ga rufe baki ba ya faruk ya kwasa da gudu yabi bayan ta.
Kamal abokin khalid dake jiran shi a mota, jin ana a bita mumtaz ce, yayi saurin fitowa ya mara
ma ya faruk baya a guje shima.
Sauran matan da suka zo tare ɗaya daga cikin su ta kalli ɗaya tace "anya lafia kuwa, akwai dai
wani abun a ƙasa nake ji, wannan baza'a ce kukan rabuwa da gida bane gaskiya.
Da ƙyar ya faruk ya dafe mumtaz da saura ƙiris mota tabi ta kanta
Da wani irin speed ya damƙo ta gam ya fincikota baya
Allah yasa me motar ya ankare da yarda ta shiga titin ya taka birki da sauri
Ganin fizge-fizgen da take ne yasa ya haɗeta da jikin shi,
Shi kanshi jikin shi rawa yake dan ya sadaƙar da me motar nan ya take ta
Da ɗan fushi-fushi ya fara mata faɗa yace "Da hankalin ki da komi zaki je ki kashe kanki, inace
ke kika kawo mijin kika ce kina so ba dole akayi maki ba? to shine dan ankawo ki kuma bazaki
zauna ba se kiyi ta wa mutane hauka?"
Ƙanƙame shi tayi ta fashe da wani irin kuka me taɓa zuciya
Shuru ya faruk yayi, shi be tafi ba shi kuma be sake ta ba
Yarda ta ɓoye kanta a jikin shi yake jin yarda hawayen ta ke taɓa jikin shi yasa jikin shi sake yin
sanyi ga matsanaiciyar faɗuwar gaban dake damun shi
Tunda kamal ya hango ya faruk rungume da ita ya tsaya,
Wayar shi ya ciro ya danna wa kalid kira
Wayar tayi ta ringing be ɗaga ba,
Shima jikin shi yayi la'asar be ma yarda ya ƙarasa wajen ba ya juya.
Hangowa da ya faruk yayi
Ganin kowa jiran su yake yasa ya cireta daga jikin shi ya kama hannun ta ya fara janta
Tirjewa ta hau yi, taƙi yarda ta sake koda taku ɗaya ne
Da mmaki ya faruk ke kallon ta, beyi niyar cewa komi ba jin yarda kanshi ke mugun sara mishi,
duk saboda firgicin daya shiga
Amma ganin tirjiyar da take yasa ya tsaya yace "Talk to me menene mumtaz?"
Cikin kuka tace" na shiga uku ya faruk, wallahi ba da son raina nake sata ba, nima bana so,
kuma wallahi bana bin maza"
Kalmar farko ta sata data ce ba ƙaramin dukan zuciyar shi tayi ba
Ya tsorata ainun, duk da besan me ya faru ba
Dan ya kawar da kokwanton shi yace
"Nasan ba da son ranki bane ai, nutsu kiyi min bayani yarda zan fahimce ki"
Kasa cewa komi tayi taci gaba da kuka kamar ranta ze fita
Jin taci gaba da kukan kuma taƙi cewa komi yasa ya jata zuwa inda su goggo safiya da kuma
sauran mutanen suke
Amma deep down him yasan akwai matsala, ko daga ganin yanayin fitowar umman shi da
kuma goggo safiya da kukan ta yayi kala dana mumtaz.
Yana ƙarasawa inda ya aje motar shi yace "nan gidan za'a barta ko kuma gidanta zamu?"
Murya a dishe goggo safiya tace "ba wannan maganar ai, muje gida kawai kafin mu tara wa
kanmu jama'a"
Baki sake yace "kamar ya goggo, ban gane ba, kina nufin mu koma da ita gida wai?"
Muryar ta bata fita sosai tace "eh muje" kafin ma ta gama rufe baki mumtaz tayi wuf ta shige
mota
Ƙin shiga mota ya faruk yayi, kusa da umma da ke ƙokarin bude front seat ta zauna ya matsa,
da dan tsoro a fuskar shi yace "umma wai menene ke faruwa dan Allah"
Taɓe baki umma b tayi sannan tace "ai yau kunya da ƙasƙanci babu kalar wanda bamu gani ba,
ni wallahi ko maƙiyi na ba zanso ace an mishi kalar tozartar da ƴarnan tasa akayi mana ba"
Tsabar faɗuwar gaban da yake ji sam ta hana shi magana,
Kamar wanda beda lakka ya zagaya ya shiga motar
A cikin zuciyar shi yake jin sautin kukan ta, be waiga ba, murya na rawa yace "Seda kika bari
asirin ki ya tonu ko mumtaz"?
Daga umma b har goggo safiya sakin baki sukayi suna raba kallon su a tsakanin su.
Ba wanda ya sake cewa komi ya tayar sa mota yaja suka yi gaba
Baki a sake kamal yabi motar da kallo, ganin sun tafi da mumtaz,
Daga baya ya tuna ƙila gidan ta zasu kai ta kafin su wuce.
***UNCLE ABBAS
Tun baccin daya kwashe shi bayan ɗaurin auren sakina, se da akayi sallar magariba ya farka
Ganin shi kwance a gida yasa ya sauke ajiyar zuciya haɗe da hamdala, shi duk a tunanin shi
mafarki yake
Be kai ƙarshen tunanin da yake ba yaji muryar maman sakina bisa kanshi tace
"Tunda har ka farka se kazo muji da sakina, gata can jikin ta ya ɗume da zazzaɓi"
Da ƙyar ya miƙe zaune, dafe kanshi yayi kafin yace "Zazzaɓi kuma? ko daga gidan bikin ne ta
kwaso shi?"
Galla mishi harara haj Asiya tayi, ta cika kamar ta fashe dan takaici, tace "Hmm ka gama
kewaya-kewayar ka, kana nuna kamar babu abinda ya faru alhalin kasan silar zazzaɓin nata"
A ƙasan ranshi yace "da gaske ne kenan ba mafarki nake ba"
Hular shi ya ɗauka, se waya sannan makullin mota ya miƙe
Kai tsaye hanyar fita yayi, yana tafe yace "Ku jira ni, zanje na samu Abbas yanzun nan"
Ƙwata hajiya Asiya tayi ta koma ta zauna ta zabga uban tagumi
Fitowar inna hassu kenan daga sallar magrib, itama ta samu gefe ta zauna sannan tace "Fita
yayi?"
Haj Asiya tace "yaje warware abinda suka haɗa ne, ai kowa yaga abunnan yasan akwai wata a
ƙasa, anyi auren so da ƙauna ma ya aka ƙare ballantana auren haɗi"
Tana gama faɗin haka ta tashi tayi shigewar ta ɗaki.
****MAMA
Tunda aka saka ƙafa aka tafi da mumtaz t shige ɗaki ta kulle kanta, haka nan take son tayi kuka
ƙila Allah ya temake ta abinda ya tokare mata maƙogwaro ya wuce.
Mama bata fito ɗakin ba seda tayi sallar isha sannan ta sakko
akwai ƴan'uwan ta sosai a palon, ana ta fira da yaba ɗakuna
Nan mama take ji har suka baro gidan mumtaz ba'akaita ba
Ɗaya daga cikin ƴan'uwan maman