LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU

Author :  ZAINAB FALALU Category :  African Stories & Novels

Chapter   19 / 25

54K to 57K   out of 73.4K words

ya
nuna umma ƙarama yace "umma ƙ!"

Gira ɗaya ta ɗaga mishi kafin ta miƙe tsaye, dariya tayi tace "kayi mamaki ko Tk?"

Murmushi ta sake yi sannan tace "anmin shigar sauri ne da tuni nice mahaifiyar ka"

Da ƙarfi uncle Abbas yace "Stop it sumayya"

Cikin salo da ƙwarewa a bariki umma ƙarama ta juya kaɗa mishi idanu tayi kafin tace "We will
come back to that my Abbas"
Daga can inda ya faruk da mus'ab ke zaune suna sauraron su ta wayar Tk ɗin,

Tsabar tashin hankali ya faruk kasa ci gaba yayi da saurare jin muryar umma ƙarama ƙurukuru
cikin gang ɗin su uncle Abbas

Sunan Allah kawai yake ambata dan tabbas ya shiga ruɗu, anan take maganar umma babba ta
faɗo mishi inda take cewa "Allah ka rabani da zama mutum me kan maciji"

A bayyane yace "La haula wala ƙuwata illa billah"



Murmushi mus'ab yayi yace "Anjima ana ruwa ƙasa na shanyewa".




Tk be gama fita a mamakin da ya shiga ba uncle junaid yace " Kai nake jira Tk, bani takardar
ƴata kafin ran kowa ya ɓaci a wajen nan"



Dariya Tk yayi ya hau tafa hannaye yana nuna su ɗaya bayan ɗaya, kafin yace "wallahi ba zan
sake ta ba, babban kuskuren da kuka yi shine bari a ɗaura auren, oh kuna nufin in sake ta
shikenan nayi biyu babu?"



Kanne musu ido uncle Abbas yayi, sannan ya matsa kusa da Tk ya dafa kafaɗar shi yace

"Baka yarda da baban ka ba kenan?"

Shiru yayi ya hau hura hanci

Cikin dabara uncle Abbas ya ɗora da "mu gata muke maka baka sani ba, taya za'ayi a baka
auren mumtaz bayan kana auren ƴar ɗan'uwan mahaifiyar ta?

Kai sakarai ne, kayi tunani akai"



Shiru Tk yayi yana nazarin maganar uncle Abbas, can yace "Kasan faruk ba ze taɓa sakin
yarinyar nan ba tunda ya samu ya dafe ta, balle na aure ta, kuma kowa yasan sarai yana sonta
dama"



Tsaki umma ƙarama tayi tace "Lallai da gaske sakaran ne kai, yanzu kai kana tunanin
mahaifiyar faruk zata yarda ya zauna da yarinyar da aka saketa a ranar da aka kaita gidan miji
ɗanta ya aura?

Har yau kenan baka gama fahimtar wacece hajiya Nabila ba, macece da bata son wani aibu ko
kaɗan ya shafi ƴaƴan ta, kuma kar ka mance a dalilin sata ne aka sako mumtaz har aka maye
gurbi da ɗanta, daɗin daɗawa ma a gaban ta akayi case ɗin komi"



Shiru Tk yayi, tabbas ya yarda da abinda umma ƙ kefaɗa,

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "na yarda in har faruk ya saki mumtaz to nima zan saki
sakina" yana gama faɗin haka ya fice



Zama suka yi gaba ɗaya kowa da saƙe-saƙen da yake a rai

Umma ƙarama ta katse shirun da "mu sake haƙuri mugani, muka yi haƙurin shekaru ma balle
yanzu na ɗan taƙin lokaci"

Tsaki uncle junaid yayi yace "Baki san taurin kai da tsaurin ido irin na faruk ba wallahi,
Shiyasa nayi mugun tsanar yaron nan"



Murmushi uncle Abbas yayi yace "Dole daman sedai a ɓullo mashi ta bayan gida"



Umma ƙarama tace "to ta yaya kenan"?

Uncle Abbas yace "habaici zaki koma ki rinƙa saƙa mata a fakaice, tunda har mun san inda
weakness ɗin ta yake, dole zata hasala tace zata yi mishi baki in be sake ta ba, shi kuma in ba
wawa bane ai ba ze yarda ya ɓalɓance a banza a wofi ba, daga nan ze sake ta, kuma at the
same time mun karya ƙwarin gwiwar iyayen da kuma ita kanta ƴar"

Dariya suka kwashe da ita duka, umma ƙarama harda kwanciya a kafaɗar uncle Abbas tana
wanu jinjina mashi.

Tas plans ɗin da suka shirya a kunnen ya faruk da mus'ab, seda suka gama naɗar komi kafin
suyi saving

Dialing no ɗin dr jamal ya faruk yayi, yana ɗagawa yace "na gama ji aboki, saura abu na gaba
kuma".



KUN SAN YAU INA HUTU, AMMA HAKA NAN NA DAURE NAYI MAKU
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg69-70

Duk wata hanya da ya faruk yasan ze haɗu da umma b ya kauce mata

A daren suka yi waya da ƴan'uwan shi suka ji dahir ɗin zancen auren a bakin shi, kuma suka
sanar da shi jiran da umma b ke masa,

Sosai suka taya shi murna, bama kamar ya sabiha datafi kowa sanin shi.



***MAMA

Murnar data ke ciki bata musaltuwa, ƴan'uwan ta kaf da suke gidan kowa yaji abunda ya faru na
auren mumtaz da ya faruk,

Da mamaki da yawansu ke tambayar ya akai hakan ta kasance

Kafin mama tayi magana goggo safiya tayi caraf tace "sauyin ubangiji mana, a daren tun kafin
mu kai ga isa da ita mijin ya kira yace ya sake ta akan dalilin shi mara tushe,

Aikuwa a cikin daren jiya iyayen ta suka ɗaura mata da wanda yafi shi komi"

Al'ajabin maganar kowa yake,
Sedai maganar data ke fitowa daga sasan umma babba daban da warce goggo safiya ke faɗa

Yawanci da magana biyu a zuciya suka bar gidan.




Tun a daren jiya da aka ɗaura auren ya faruk da mumtaz Abba babba ke neman umma babba a
waya amma wayar a kashe

Se kawai yayi la'akari da ƙila ta shiga ribibin mutane ne ya haƙura zuwa wayewar garin Allah

besan tana can tana tafasa ba.



Mutane na nesa nata shirye shiryen tafiya gidajen su ta ɓangaren mummy da aunty, tunda su
acewar su sun gama nasu bikin.



Mama kuwa a wannan safiyar tana tashi ta bada umarni a ɗora manyan tukwane a wuta

Inna hassu da ta baro gidan uncle junaid tun a daren jiya tace "anya basuyi yawa ba zahra'u?"

Murmushi mama tayi annushuwar fuskar ta na daɗa yalwatuwa tace "Basu yi ba inna, so nake
akai gidan marayu sannan a raba wa almajirai "

Gyaɗa kai inna hassu tayi, kafin tace "kice mu yanzu muka fara hidamar tamu"

Mama tace "ƙwarai kuwa, sabon ango sabuwar hidima"



Gaba ɗaya wajen suka saka dariya da guɗa

A hankali Altine tayi ƙasa da murya tace wa ɗayar me aikin da suke aikin hidimar bikin tare tace
"Rabon da naga baiwar Allah n nan a cikin farin ciki haka na mance wallahi,
Ki kalle ta da kyau ki gani, tunda aka fara hidimar bikin nan bata a cikin walwala sam, amma
daga jiya da daddare zuwa yanzu ko aljihun ki ze sheda da tana cikin murna"



Dariya matar tayi ta dafe lalitar ta taji zam kuɗin ta na nan, sannan tace "kyauta me tsoka fa
mun shata, mukam gaba ta kaimu wannan sauyin tunda ko ba komi mun sami alkairi"

Suna aiki suna hirar su, ko irin su nuna gajiyar nan, amma daka gansu zaka san cikin nishaɗi
da walwala suma suke aikin.
*****
Sha ɗaya da kusan rabi na safe yaya faruk yayi parking a harabar gidan nasu



Tunda ya tsaya be fito ba, yana ciki zaune yana ƙare wa jama'ar dake harabar gidan kallo ta
cikin baƙin gilashin motar shi

Seda ya gama kallon kowa tukun ya kwashi wayoyin shi dake ajiye a gefe sannan ya saka ƙafa
ya fito

Ma sha Allah! koni kallo ɗaya nayi mashi na tabbatar da lallai ya faruk ya zama ango da gaske

Banda baza ƙanshi da sheƙi ba abinda yake

Duk da faɗuwar gaban da yake ji hakan be hana shi murmushi ba



ya fauza dake ta kai kawo a harabar gidan ita ta fara hango shi

Ihu ta fasa tace "Angooooo"

Aikuwa akayo mishi caaa

Abokan wasa kowa na yagar shi, hatta da ƙannin shi yau basu barshi ba

Ba abinda yake se aukin murmushi da saɓa babbar riga



Ta window umma babba ke hango shi, ta ƙara ciki tayi fam ganin yarda yake wani zuba
murmushi yana amsa addu'o'in da ake mishi.



Da ƙyar ya kufce musu ya shige ciki wajen umma b

Zaune a palo ya iske umma ƙarama da wasu daga cikin baƙi

Be nuna komi a fuska ba yace "barka da safiya umma ƙarama"
ya gaishe da sauran sannan ya shige ɗakin umma babba
Tana tsaye jikin window dake kallon harabar gidan

A ɗan ɗarare yayi sallama ya shigo ɗakin

Ciki-ciki ta amsa, bata waigo ba bata kuma nuna tasan ya shigo ba

Gefen kujera ya ɗosana ya zauna, kanshi a ƙasa yace

"Ki yafe min umma na, wallahi tallahi ba'a tambayi ra'ayi na ba nima akan maganar"

Jin rainin da yake ƙoƙarin kawo mata yasa ta waigo a fusace tace "Dakata faruk, yanzu na sake
tabbatar wa da bani da wani matsayi me girma a wajen ka kai da mahaifin ka,

Na sha komin lalacewa ta tunda har ni na tsugunna na haife ka za'a nemi shawarata koda kuwa
ba zan yarda ba, nasan an fita haƙƙina an gaya min

Amma abun haushin sedai naji a gari, har wasu su sami damar yi min gori da habaici"

Tana faɗin haka ta hau share hawaye tana tuno da kalar habaicin da umma ƙarama ta yayyaɓa
mata ɗazu da safe



Gyaɗa kai ya faruk yayi, a ranshi yace "Tabbas sun gama sanin laggon ki umma na"



Jin bece komi ba yasa taci gaba da faɗin "wai kamar ni ace ɗan da shi kaɗai ne ɗa namiji dana
haifa ya ɓige da auren ɓarauniya, kai abin da ciwo wallahi"

Jin ta ɗan fara ɗaga murya, ga kuma mutane dake ta kai kawo yasa ya miƙe a hankali ya
sakaya ƙofar sannan ya dawo kusa da umman da ke ta sharar ƙwalla ya zauna



Kama hannayen ta yayi sannan yayi ƙasa da murya cike da ladabi da kuma sanin haƙƙin
mahaifiya yace

"Ki yafe min kuma ki yafe wa Abba na umma, wallahi tallahi muna sonki kuma kina da daraja a
waje na fiye da kowa a duniyar nan umma, kece kawai kika kasa fahimtar hakan"



Muryar ta na rawa tace "Yanzu kai kaji ka amince da auren yarinyar nan? wallahi faruk karka so
kaga wulaƙanci da cin kashin da mutanen can sukai mana saboda halin yarinyar nan

Ganin bazasu ɗaukar wa kansu jidali bane yasa ya sauwaƙe mata amma kai se ka kwaso mana
ita?"

Nutsuwa sosai faruk yayi yace "umma ke da akace maki mumtaz na ɗauke-ɗauke ya kika ji
zancen?"
Ya kafe ta da ido yana jiran jin amsar ta.



Shiru tayi can tace "gaskiya daga farko ban yarda ba"

"good" ya faruk yace sannan ya sake cewa "Tsakanin ki da Allah kuma baki ɗarsa komi a cikin
ranki ba, duba da ynayin yarda kuka bamu tarbiya daidai gwargwadon iyawar ku?"



Gyaɗa kai tayi tukun tace "Da wannan dan wannan kuma"

Murmushin gefen baki yayi ganin tun ba'aje ko ina ba matsalar shi ta kusa warwarewa.

Gyara zama sosai yayi sannan yace

"Umma in kika duba gatan da iyayen ta ke mata,

dan ban manta ba har maganar kin taɓa yimin cewa gatan da suke mata yayi yawa, kar su saka
mata girman kai a abubuwa, har kike cewa hakan yana da nasaba da ƙin kula samari da takeyi
saboda tana ganin ta wadatu da komi ta fi ƙarfin su"

Gyaɗa kai tayi tace "anyi haka"

Sannan yace "To umma kina ganin wanda ya wadatu da wannan gatan shine har wani abu na
wasu ze birgeta ta ɗauka?"

Ajiyar zuciya ta sauke a wannan karon, taci gaba da sauraron shi

Jin bata ce komi ba ya ɗora da " Tabbas in hakan da gaske ne to AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI
umma"

Shiru umma babba tayi tana nazarin maganar ɗan nata

a karo na farko da taji wani abu me kama da tausayi tausayi na son kamata game da ahalin
mama.

Cikin ido ya faruk ya kalli mama yace "Kiyi nazarin maganata umma, in har baki gano komi ba
to ina me tabbatar miki da a gaban ki zan saki mumtaz!."
Yana gama faɗin haka ya miƙe yace "na barki lafiya umma" ya fice.



Yana fitowa yaga juyawar umma ƙarama da gudu

Karkaɗa kai kawai yayi a ranshi yana faɗin "Baƙar macijya me kan mutum".



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg71-72

Yaso ya shiga sasan mama amma ya kasa, dan yau sasan nata yafi na kowa cika, a yarda yake
gani ma kamar sake yin wasu baƙin akai

Mota ya koma ya zauna, so yake yaga mama ya shawarce ta kafin ya aiwatar da ƙudirin shi

Wayar shi ya ciro yace "bari nagwada kira ƙila na same ta yanzu"



Mumtaz na kwance taji wayar maman na ringing

Calls ne ke ta shigowa na mutane daban daban

Jin wayar ta sake ringing yasa taja tsaki a gajiye ta kara wayar a kunne ko saurarawa bata yi ba
tace "Mamar fa na ƙasa tabar wayar a ɗaki"

Tsit faruk yayi da yaji muryar ta,
Can daga baya yace "Kuma bazaki iya kai mata ba?"

Durumm haka taji saukar faɗuwar gaba

Da sauri ta cire wayar a kunne ta kalli sunan dake kan screen ɗin

Daga can ya faruk yace "kar ki kashe man waya, ki sauka ki kai mata ina jin ki"



Zumɓura baki tayi kafin tace "wallahi akwai mutane da yawa, ni kuma kunyar sauka nake ji"



Murmushin da iyakar shi kan laɓɓa yayi tukun yace "saboda an miki auren dole da wanda bakya
so ko?"



Dafe baki tayi da sauri tana baza idanu,

Jin tayi banza da shi yace "Tunda baki da amsa ze ki kai mata"



Badan taso ba ta sauko,

Ta wayar ya faruk najin yarda abokan wasa ke warfarta suna tsokana, gummm yaji bakin ta dan
beji taba ko mutum ɗaya amsa ba.

Mama na cikin mutane mumtaz ta miƙa mata wayar

Ansar wayar tayi haɗe da tambayar ta "waye"

Zumɓuro baki tayi tace "yaron ki wai"

Dariya ya faruk yayi jin abinda mumtaz tace.

Tsinkayar muryar mama yayi tana faɗin "faruk ya akayi?"



Barin wajen hayaniyar tayi tana sauraron shi, da mamaki mama tace "Banjin ta sha ba gaskiya,
me yasa baka bani a hannu na ba? Riƙe wayar ina zuwa"

Da sauri mama ta haura sama zuwa ɗakin ta inda mumtaz ke zaune
Ya faruk naji tana tambayar ta "mumtaz ina maganin da faruk ya baki tun last month?"

Kai tsaye tace "akan mirrow na ajiye shi, da nazo zan sha kuma bangan shi ba"

Ajiyar zuciya mama ta sauke, jiki a sanyaye tace "bata sha ba faruk"



Daga can ya faruk yace "ba abin damuwa bane mama, yanzu zan koma wajen Alaramman
dama nayi waya da shi tun last week akan ya sake yin wani, nasan ƙila ya gama zuwa yanzu"

Mama tace "rubutu ne ko me?"

"Ba rubutu bane, ayoyin karya sihiri ne wanda ake yin shi da ganyen magarya, daga bayanin da
nayi mashi ne ya gane abun akwai sihiri a ciki"

Jiki a sanyaye mama tace "Allah yayi maka albarka faruk yasa ka gama da iyayen ka lafia, ya
albarkaci auren ku da zuri'a managarciya me albarka"



A hankali ya amsa da "amin" kafin ya ɗora da "ki kira Abba ƙaramin akan maganar kayan nasu,
dan be dace ace su sake kwana anan ba"

Murmushi mama tayi, tace "baka da matsala yaro na"

Da haka su kayi sallama ta aje wayar.

Kafin ya faruk ya tafi seda ya kira ya maryam ya sabiha da ya fa'iza yace "Ku lallaɓa ku saɓar
wa umma babba ku tafi can gidana dake nasarawa,

Ku cire komi da komi ayo waje dasu, nasa azo a kwashe su, za'ayi ma gidan sabon penti"

Ɗan baya ta maryam taja ta rangaɗa guda haɗe da tafa hannaye

Ganin zata jawo masu hankular jama'a yasa yayi saurin miƙa wa sabiha keys yaja motar ya fice.



Yana a hanya call ɗin Abba babba ya shigo masa, da sauri ya ɗaga haɗe da sallama

Abba babba yace "kasa an fara aikin ko kuwa shiririta kasa?"

Seda ya ɗan rissinar da kai yace "yanzun nan muka gama waya da su har sun iso masu
gyaran"
Abban yace "yauwa to, ka kyauta" ya aje wayar.



Seda mama ta je kiran da ake mata kafin ta dawo ɗakin ita da goggo safiya

Zaunar da ita mama tayi ta mata tace "kayan da can suka kawo ya kamata a maida masu kar
su sake kwana, nima a kwaso man furnitures ɗina"

Goggo safiya tace "hnn na taɓaki da alkairi, ai ni tsabar farin ciki yasa na mance da wasu kayan
su, gaskiya gara a maida musu, kira man ƙasim a wayar ki muji ya za'ayi"

Ba ɓata lokaci mama ta danno wa uncle ƙasim kira
Yana ɗauka ta miƙa mata.

A take suka gama arranging mayar da komi dan acewar su babu abinda zasuyi da kayan su.



Gaf da la'asar goggo safiya da matar uncle ƙasim se inna hassu da wata ƴar'uwar mamar suka
kwashi akwatunan aka loda su a mota ɗaya, su kuma suka shiga mota ɗaya suka nufi gidan su
khalid da su.



Babu kowa a gidan se ƴan tsirarun mutane, ba zaka taɓa cewa anyi biki jiya a gidan ba



Goggo safiya ce kan gaba, kwaɗa sallama tayi, sauran kuma suna ta shigo da akwatunan

Aunty hajara ce ta amsa musu haɗe da fitowa, cak ta tsaya tana binsu da kallo ɗaya bayan
ɗaya

Da sauri ta juya ta koma ciki, se gasu sun fito da ɗayar sister mamin

Suna tsaye har aka gama shigo da akwatunan sannan goggo safiya tace "sannun ku bayin
Allah, uwar kalid ɗin na ciki ne?"



Sister mamin tayi saurin faɗin "ku ƙaraso daga ciki mana kuka tsaya a nan"

Palon da aka tarbesu jiya a nan aka sake saukar su

Sun kai kusan minti goma a zaune kafin mamin ta shigo fuskar nan tata a ɗaure

Waje ta samu ta zauna, sama sama aka gaisa kafin goggo safiya tace "To bayin Allah, ga kaya
nan dai mun dawo dasu, tunda aure beje ko ina ba akayi saki, shine muka yanke shawarar
dawo muku da su
Kunga an ɗan rage mashi asara ko yaya ne"

Wani wawan kallo mami ta jefi goggo safiya da shi, bata yi magana ba har goggo safiya takai
aya tukun aunty hajara tace

"ai da kun bar mata kayan tunda har kun riga da kunyi jere, mu dama a al'adar mu in akayi
sakin aure kayan ɗaki ya zama na miji, kuma kunga yarda wannan auren ya kasance, se ku
koma da kayan kunga an raba asarar duka"

Matar uncle ƙasim tace "tohh, wannan wace irin al'ada ce ta son banza da yawa haka?"



Sister mami tayi wuf tace "kalar warce kuka ji yanzu"



Da sauri inna hassu tace "ku tashi muje, naga kamar abin ze zama da cin mutunci"

Miƙewar su kenan khalid ya shigo palon, kallo ɗaya zakayi mashi ka san ya zabge daga jiya
zuwa yau ɗin nan

Kanshi a sama yace "mami bani mukullin gidan, babu abinda zanyi da kayan nan, gara abari su
kwashe"

Sudai basu tsaya ba, ficewa sukayi gaba ɗayan su bama su tsaya jin amsar da mamin ke bashi
ba.



Aunty hajara da sistern mamin suka hau shi da faɗa, "sakarai in ba haka akayi musu ba kaike
da aasara, duk uban kuɗin da aka kashe wajen hidimar bikin, ba se ka fanshe da kayan ba"

Juyawa yayi ya fice haɗe da faɗin "nidai bana so".



Ganin sun bar akwatunan yasa

19 / 25