Author : ZAINAB FALALU Category : African Stories & Novels
wa'inna ilaihirraji'un"
Da damuwa a fuskar tace "An dena irin wannan auren fa Abban mus'ab, ni a iya zuwa gidan
nan da sakina keyi ban taɓa ganin wani abu ya haɗa ta da TK ba in ba gaisuwa ba, amma rana
tsaka ace an ɗaura aure"
Abba ƙ da shima haryanzu be fita daga mamakin al'amarin ba yace "To tunda mahaifin yarinya
yaji ya gani ai mu bamu data cewa zahra'u, in kika ga yarda junaid ya amsa ma Tkn ma zaki
sha mamaki wallahi, nasha Abbas zeyi magana shima naga yayi shiru daga baya ma ya bar
masallacin gaba ɗaya
Shi kuma junaid kafin na gama gaigaisawa da mutane na nemesa na rasa, kuma ya tashi ya
kashe wayoyi gaba ɗaya"
Ajiyar zuciya mama ta sauke sannan tace "Danƙari, tabbas akwai wani abu a ƙasa wallahi"
Goge zufar goshin shi yayi kafin yace "Yanzu abinda nake so dake shine, ki san yarda za'ayi ita
hajiya Asiyan kiyi mata magana ta fahinta kafin taji daga sama, daga nan se asan yarda za'a
ɓullo wa sakinar itama"
Jiki a mace mama tace "toh, bari naje"
Ta hauro sama, shi kuma ya fice ta ƙofar sirrin sa.
Mama na fitowa sukayi kiciɓus da hajiya Asiya data shigo a ruɗe
Da sauri mama ta tarbeta, bata jira komi ba gudun jan hankalin mutane garesu taja ta zuwa
bedroom ɗinta da ba kowa
Suna shiga ta danna key a ƙofa, kafin mama tace komi hajiya asiya tace "Ga dukkan alamu kinji
abinda na jiyo ko hajiya zahra?"
Jiki a sanyaye mama ta kamata ta zaunar da ita a gefen gado tace "Ki nutsu muyi magana haj
Asiya"
Da sauri maman sakina tace "Da gaske ne kenan?"
Cike da hikima mama tafara magana "Karki ɗaga hankalin ki akan abinda kika ji pls, Ya junaid
ba ze taɓa cutar da ƴarshi ba, ki riƙe zuciyar ki har sanda zakiji daga bakin mijin ki, nasan zaki fi
fahimtar zancen"
Fashewa da kuka tayi tace "wannan wani irin ƙaddara ne, aure ba shiri ba sanin uwa balle ƴar,
yanzu ya zanyi da sakina in taji wannan maganar bayan tana da wanda take so yake sonta,
innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"
Miƙewa da sauri mama tayi tace "ki zauna a nan kuma ki share hawayen nan, bari inje in tawo
da sakinar"
Ta fice da sauri har tana ɗan cin tuntuɓe.
Tun bayan shigowar Amal a gujen nan sakina taja can gefe tana amsa call ɗin saurayin ta dake
hanyar zuwa
Matsawa kusa da ita Amal tayi, seda tayi ƙasa da murya tace "wayar nan da kikeyi fa ta saɓawa
addini malama"
Ta ja gefe kamar ba ita tayi maganar ba
Seda sakina ta gama masa kwatancen gidan ta aje wayar kafin ta waiga inda Amal ke zaune
tace "Me kikace uwar ƴan shishshigi?"
Banza Amal tayi da ita, duk da taji me tace, amma tayi pretending kamar bata ji ba taci gaba da
firar ta
Ƙwata sakina tayi ta miƙe da niyar jan mumtaz zuwa sauya kaya mama ta faɗo ɗakin itama
Sama-sama ta amsa gaisuwar su kafin ta wurga idon ta can inda sakina ke tsaye tana wa
mumtaz magana
Da hanzari mama ta ƙarasa can, hannun sakina kawai ta kamo ta janyota suka fito daga palon
zuwa can sasan maman.
Suna fita Amal ta saki guɗa haɗe da karkaɗa jiki tana juyi
Kallon ta mumtaz tayi ta yafitota da hannu
Amal na dariya ta matso kusa da mumtaz
Kafin mumtaz tayi magana Amal tace "muje mu sauya kaya"
Mumtaz ta gane me take nufi, ba musu suka fice daga palon
Tacan bayan ɗakin ya faruk Amal taja mumtaz,
ido cikin ido Amal ta kalle ta tace "kin san wa ya Tk ya aura?"
Tsaki mumtaz taja kafin tace "wai wani ya Tkn kk magana akai?"
Cike da gulma Amal tace "Ya Tk na nan gidan, to wallahi na shiga ɗakin umma babba naji tana
waya da Abba b yana faɗa mata an ɗaura aure harda na ya Tk da sakinar uncle junaid"
Ido waje mumtaz ta dafe ƙirji tace "jakar ubancan kayyasa!!
Sakina fa kikace?"
Rai fess Amal tace "Rass sakinar da kika sani, kuma daga majiya me ƙarfin gaske naji"
Ai mumtaz bata gama tsayawa jin ta ba tayi hanyar sasan su da sauri kamar zata kifa
Direct bedroom ɗin mama ta nufa,
Murɗa ƙofar tayi tajita gam a rufe
Ƙwanƙwasa tayi, daga ciki mama tace "waye?"
"nice mama"
Sakina ce ta buɗe ƙofar duk tabi ta firgice
Mumtaz na shigowa tace "mama wai da gaske ya Tk an ɗaura mishi aure da sakina"
Dakatar da ita mama take, saboda sun kasa gaya ma sakinar, amma ina seda ta kai ƙarshen
tambayar ta kafin ta tsaya
A mugun firgice sakina tace "wai wace sakinar kike nufi?"
Shiru mumtaz tayi, ta nemi waje ta zauna ganin ɓallo ruwan datayi.
A tsorace sakina ta kalli maman ta dake kuka sannan ta waiga ta kalli mama itama tayi
zuru-zuru tace
"Dan Allah da gaske ni sakinar ake nufi wai?"
Yarda tayi magaanar mama taji wani mugun tausayi ya kamata,
Kamota tayi ta zaunar da ita tukun ta runguneta sannan tace "ki kwantar da hankalin ki sakina,
Dad ɗin ki kawai muke saurara muji tabbaci amma ba wani abun da zaki ɗaga hankalin ki bane
akai"
Da ƙarfi ta ture mama ta miƙe tsaye, cikin hargowa da rawar jiki tace "ku faɗa min gaskiya kafin
zuciyata ta buga, da gaske ni sakinar ake nufi ko wata ce daban?"
gyaɗa kai mama tayi sannan tace "ki nutsu abi komi a hankali sakina"
Wage baki tayi ta kurma ihun da seda ya janyo hankulan mutanen dake zaune a palo.
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA 👹
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg57-58
A guje mama da mamar ta suka tare ta ganin zata buga kanta a ƙasa
Kafin ta kai ƙasa suka tare ta
Cikin kuka maman ta ke jijjiga ta tana kiran sunan ta
Mumtaz dake tsaye jiki na ta kerma mama tace "kawo ruwa da sauri suma tayi"
Gaba ɗaya mumtaz ta ruɗe ta manta sam akwai toilet a ɗakin ta buɗe ƙofa ta fice a ruɗe zuwa
neman ruwa
Buɗe ƙofar data yi ne ya ba wasu daga cikin ƴan'uwan maman shigowa ɗakin
Ƙanwar mahaifiyar su maman ce tace "me ya same ta ne ni hassu, ina yanzun nan naga
gilmawar ta?"
Cike da kuka sa kuma ɓacin rai da ya fara bayyana a fuskar mum ɗin sakina ta waiga ta kalli
matar tace "inna hassu wallahi in dai junaid yayi sanadiyar rayuwar ƴata sena maka shi a kotu,
na san ba wanda ya isa ya gaya mishi yaji, amma ke tunda ƙanwar uwace a wajen shi ƙila yaji
taki maganar"
Bata ƙarasa ba inna hassu ta dakatar da ita cikin sauri tace "Kiyi ki kaini inda nake son zuwa kin
tsaya kina ta mana jaye jayen lukutar masifa"
Mama tayi caraf tace "ayi a hankali dan Allah, kunga akwai baƙin kunya a gidan"
Inna hassu tace "ku faɗa min me junaidun yayi?
Mama tace "aure ya ɗaura mata da ɗan gidan ƙanin megidana"
Kusan gaba ɗaya ɗakin aka hau salati da tafa hannuwa
Riƙe baki inna hassu tayi tace "shine wai abin ɗaga hankali harda suma?"
Sakatoo mum ɗin sakina da mama sukayi suna kallon ta da mamaki
mum ɗin sakina tace "aure fa ba shiri, babu jituwa ko wata sanayya tsakanin ta da yaro fa inna
hassu"
Ɗaya bayan ɗaya inna hassu tace kowa ya fita
Kowa ya fita ya rage daga ita se mama se mum ɗin sakina,
Se sakinar dake kwance ido rufe bayan ta farfaɗo daga suman wucin gadin data yi
Inna hassu ta kalle su duka tace "waye ke da haƙƙin aurar da ƴarsa?"
Ba wanda yace komi, da kanta ta ba kanta amsa tace "ina ubane ke da wannan haƙƙin"?
Ta ɗora da "mujira shi muji hujjar shi ta yanke wannan hukuncin da yayi ba wai ku zauna ku
ɗaga hankalin ku ba itama yarinyar ku ɗaga mata nata.
Yanzu abunda za'ayi shine, ke Asiya kamo ƴarki mu tafi can gidan naku ayi komi a can gudun
surutun mutane"
Ba yarda suka iya haka mum ɗin ta kamo sakina da banda kuka babu abinda takeyi, duk uban
kwalliyar da aka ɗauka ta caccaɓe da hawaye da majina, suka yi waje.
Kun san gidan biki, nan aka koma maganar da yarda abun ya kasance.
Mummy kam data ji batayi mamaki ba, dan ta san a halin mijin ta ze iya aikata komi ba tare da
sanin ta ba
Da Tkn ya shigo gidan ma rungume ta yayi yana murnar shima ya zama ango
Zaunar da shi tayi ta tambaye shi ra'ayin shi ne ko kuwa na iyayen shi ne
Da bakin shi yace mata ra'ayin shi ne, harda ƙarin cewa, daga tambayar baban ta yace kawai a
ɗaura yanzu.
a haka ya barta, ko ajikin ta taci gaba da sabgar jama'ar data gayyata.
Tsegumi na can sasan umma babba tunda ita ta fara jin maganar auren
Tayi-tayi taji wani abu game da auren a bakin ya faruk, amma yace mata be san komi ba akan
lamarin.
Inna hassu suna isa gidan suka iske uncle junaid baje yana bacci
Da mamaki sakina da mum ɗinta suke kallob shi,
Cikin kuka sakina tace "Gaskiya ba lafia ba mum, kalli a yarda dad ke bacci fa"
Ita kanta hajiya Asiyan jiki a sanyaye ta matsa kusa da mijin ta,
Ƙafar shi ta kama ta jire mishi takalmi sannan ta cire mai hular kanshi, da ƙyar suka haɗu su
ukun suka cire mishi malum malum
Inna hassu ta kalli haj Asiya tace "anya lafiar shi ƙalau kuwa?"
Shiru hajiya asiya tayi, tama rasa wani kalar tunani zatayi.
A gidan biki kuwa an ci gaba da shagali, masu janjanin magana nata yi, a haka ma wasu basu
san da maganar ba ana ta sha'ani
Wajen biyar da rabi na yamma masu ɗaukar amare suka fara isowa
Kaf amaren sun bar palon da suke zaune, ko wacce ta koma sasan su
Ya sabiha ta sasu Amal yin wanka kafin su Abba babba su ƙaraso
Haka Najwa itama ƙanwar mummy ta haɗa mata ruwan wanka da yaji turaruka masu ƙamshi.
Mumtaz kuwa tunda aka fitar da sakina jikin ta ya sake yin sanyi, ga azababbiyar faɗuwar
gaban da ta ƙaru fiye da na baya
Maman kanta dauriya kawai take wajen sallamar mutane dan kalli ɗaya zakai mata kasan duk a
firgice take, bata da sukunin zuciya
Mumtaz na nan kwance a kan gadon mama ta sake shigowa ɗakin
cikin faɗan dabata san daga ina ba tace "yanzun ma se nace kiyi wankan ne?"
Murya na rawa tace "a'a mama"
Mayafin ta tafara cirewa sannan ta cire sauran kayan
Ɗaya daga cikin akwatunan ta da ta haɗa ta buɗe, towel ta ɗauka sannan ta shige toilet tana
share hawayen da suka sakko mata.
Ta jima a ciki tana kuka kafin tayi wankan ta fito
Mai kawai ta shafa, se kayan ƙamshi, amma ko kwalli babu a idon ta
Wannan karon blue black ɗin atamfar me ratsin fari a jiki ta saka
Masha Allah, sosai ta fito a cikin ɗinki tayi ɗass abinta shigar ta dace da kalar fatar ta ƙwarai.
Buɗe jakar da ƴankunnaye ta ke aciki tayi har ta ɗauki ƴan kunne masu kyau zata saka ta fasa,
ƙananun barima ta ɗauka ta manna a kunnen ta, har zata rufe jakar ta hango wannan ɗan abin
hannun da ta sata ta, da sauri ta kai hannu ta ɗauke shi ta saka a hannun damanta,
first time da ta saka abun hannun kenan, shiru tayi ta tsaya tana kallon yarda ya dace da
hannun ta da kuma shigar data yi
Haka kawai ta tsinci kanta da yin murmushi.
Maida komi tayi ta rufe bayan ta cire sabon farin hijabi ƙar daga cikin kayan
Sassauke akwatunan tayi ƙasa, tukun ta haye gefen gadon tayi kwanciyar ta.
Gab da magariba su Abba b suka sallami ƴaƴan nasu bayan doguwar nasiha da suka sha
Tun ana jiran uncle Abbas har suka gaji suka sallami yaran .
Tabbas gida yana da daɗi, koda kai kaji kana son auren, amma ranar tafiya gidan miji se an
ɗaure
gaba ɗayan su kuka suke, kar ma kuzo kuga mumtaz, duk irin dauriya da kawar da kai irin na
Abba ƙ, kasa daurewa yayi, be bari an gama ba ya bar palon
Mama kam dama ko da aka kira ta ƙin zuwa tayi, da goggon safiya ta dameta se cewa tayi "ai ni
na gama mata faɗa, duk abinda taga inayi tayi shi bazata taɓa taɓewa ba"
Ba yarda goggo safiya ta iya, haka ta rabu da ita.
Ya faruk na cikin RANGE ROVER shi ƴar yayi, gab da babban palon,
Ko wacce an riƙota fuskar ta a rufe zuwa wajen motar
Duk da ba da son ranshi ze kaisu gidajen nasu ba ya sakko yace "Iya su biyar ɗin zan ɗauka,
ko wacce ta shiga wata motar"
Goggo safiya tayu caraf tace, "a ina ka taɓa ji amare sun tafi ba ƴan rakiya?"
Fuska ba yabo ba fallasa yace "bance kar kuje ba ai, ina nufin motar bazata ɗauke ku ku duka
ba"
Uncle ƙasim ya ƙaraso yace "su shiga mu gani"
Hafsat ta fara shiga, se najwa, sannan bilkisu, se Amal, kujerar
Bayan ta cika, uncle ƙasim ya rufe musu ƙofar
sannan ya buɗe ƙofar gaba yace "zo ki shiga nan mumtaz" tana shiga yace "matsa" sannan
yace "ya safiya shiga" ta shige tukun ya rufe ƙofar.
Tun kafin dama a fito da amaren, ƙawar ko wacce tabi motocin angon ƙawar ta
Haka dangi ma, wasu suce can zasu wasu suce nan zasu
Haka angwayen suka kwashe su tas
Tun farko sun san dama daga gida za'akai musu amaren nasu.
Ya faruk ya daidaita motar akan titi tukun ya kalli goggo safiya yace "gidan wa za'afara zuwa"?
Tana kallon hanya tace "a fara kai babba se ƙaramar ta zama ta ƙarshe"
Mumtaz najin haka ta sake lafewa a jikin goggo safiya tana sauke ajiyar zuciya, tun jiya dama
take roƙonta kar a fara kaita, kuma a al'adance in biki ya haɗe haka, ƙarama ake fara kaiwa
sannan babba.
Hakan kuwa akayi, hafsat naji na gani aka fara kaita,
Sannan bilkisu
Gidan najwa da Amal ba nisa tsakani, se anje gidan najwa kafin na Amal,
Nan ma seda aka kai najwan tukun aka zagaya da Amal, rungume juna suka yi da mumtaz
suna ta kuka, da ƙyar aka raba su tukun aka wuce da mumtaz
Kukan da mumrtaz keyi a yanzu yafi na ɗazu
Gaba ɗaya ya faruk na neman rasa nutsuwar shi
A cikin zuciyar shi yake jin kukan ta
Jiki a mace ya kai hannun shi jikin radion motar ya kunna karatun ALARAMMA AHMAD
SULEIMAN wanda yake karanta suratul mulk
Tun sautin kukan na tashi da ƙarfi har ya koma yayi ƙasa sosai
Shi kanshi karatun ya saka shi nutsuwa ƙwarai
Yarda suke tafiyar har yaso bawa goggo safiya mamaki
Laƙaƙai laƙaƙai haka suke tafia, da na kalla da kyau naga a 40 yake tafiyar
Kasa haƙuri goggo safiya tayi tace "wannan tafiya haka faruk, kamar baka so mu kai"
Se a sannan ya farga da yarda yake tafiyar
Duk haushin kanshi ya kama shi
Sunyi nisa sosai goggo safiya tace
"na mance, gidan sirikanta Za'a fara kaita kafin mu wuce gidan ta".
Cike da ƙosawa ya faruk yace "mijin ya kaita da kanshi, ina da abun yi ni kam"
Da sauri goggo safiya tace "wallahi baka isa ba, al'adar suce, kuma tunda har suka sanar mana
to ba zamuyi ƙaranta ba, dole muje"
Rai ɓace ya faruk yace, "nifa ban san gidan ba"
Itama rai a ɓace tace "bari na kira yayi maka kwatance"
Be sake cewa komi ba, se muryar kalid da yake saurar ta wayar goggon yana musu kwatance.
Har ƙofar gidan suka je, a can suka iske mota biyu ɗauke da mutum uku-uku a ciki, ciki harda
umma babba suna jiran ƙarasowar su.
Suna zuwa suka ɗunguma zuwa ciki inda ahalin mami ke jiran ƙarasowar su
Mami da kanta ta tarbi mumtaz da ƴan rakiyar ta har zuwa ciki
Tana rungume da mumtaz data lafe ajikin mamin, itama ta taro bayan mami da hannun ta na
dama ta riƙe ta
A haka suka taka zuwa ciki, ana ta ɗaukar su hotuna, ga guɗa nata tashi ta ko wace kusurwa
Da dai mumtaz taji ana ƙoƙarin yaye mata rufin fuskarta ta saka duka hannayenta ta riƙe hijabin
ƙam
Har seda mami ta aje ta a babban palon gidan, tukun ta kalli su umma babba tace, "marhabun
ku zauna bari nazo"
Hannun daman ta mumtaz tasa ta taɓo goggo safiya dake gefe,
Ɗiyar ƙanwar mami nata ɗaukan hotunan ta,
Khalid ya saka ta dama, seda ta ɗauka sosai duk da ba wani ganin fuskar ta ake ba tukun ta
fice
Ɗakin da sauran take takoma, sannan ta danna ma number khalid ɗin kira
Yana ɗagawa tace "duba whatsapp yanzu zan antayo maka pic ɗin, dan ma taƙi bari muga
fuskar ta"
Cike da jin daɗi khalid yace "Thank you, yanzu kuwa zan duba"
Babbar yayar mami da ke zaune kan dadduma tace "muga hotunan"
Miƙa mata wayar tayi ta ce "gama gani kafin na zo"
Aunty hajara(yayar mami) ta rinƙa duba pics ɗin da ƴar tata ta ɗauka
Tana ta scrolling taci karo da hoton da mumtaz ta miƙa hannu ta taɓo goggo safiya
Har ta wuce ta dawo da sauri,
kafe hannun mumtaz da ido tayi tana kallon abun hannun ta, daidai nan mami ta shigo da sauri
cike da annushuwa tace "ya hajara muje mana sun iso fa"
Yafito mami da hannu tayi, tace "zo kiga, kodai idona ne kemin bishi-bishi?"
Ɗan ranƙwafowa mami tayi ta amshi wayar ta kalli hoton
Dariya tayi tace "amaryar ce ai, muje ki ganta a zahiri"
Aunty hajara tace "ki kalli hannun ta, kamar abun hannun da inna ta baki ne"
Dummmm, haka mami taji gaban ta ya faɗi yin tozali datayi da shi.
Zooming hannun tayi da kyau, tana kallo ƙirjin ta na dukan uku-uku,
Da sauri ta fice daga ɗakin ta nufi nata,
itama aunty hajarar da sauri ta bita a baya tana ƙwala mata kira,
Tana shiga ta janyo laptop ɗin ta ta hau binciko videon data yi mushi ajiya me kyau
Tare da aunty hajara suka kalli ɗan gutun videon da fuskar mumtaz ce ɓaro ɓaro
Tsayar da videon tayi, a tare suka nufi palon da aka sauke su
Fuska ba yabo ba fallasa aunty hajara tayi musu sannu da zuwa ta tsallake su ta nufi mumtaz
dake ƙudindine a hijabi
Su goggo safiya sun sha duk a cikin al'adar su ne hakan
Ido suka zuba wa aunty hajara data ɗaga hijabin mumtaz fuskarta ta bayyana ma kowa.
BA LALE KU JINI GOBE BA, SHIYASA NAYI PAGES BIYU
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg59-60
Aunty hajara na buɗe fuskar mumtaz ta waiga ta kalli mami dake tsaye a bakin ƙofar palon
hannayen ta harɗe a ƙirji
Da ido tayi mata alamar itace
Gyaɗa kai mami tayi ta juya ta fice
Gaba ɗaya ranta a mugun ɓace,
Fuska ba yabo ba fallasa aunty hajara tace
"kuyi sallah se ku ci abinci muna zuwa"
Goggo safiya tayi caraf tace "a'a tafiya mu kam zamuyi, anan zamu bar muku ita ko kuwa zamu
dangane ta ga