LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU

Author :  ZAINAB FALALU Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 25

15K to 18K   out of 73.4K words

cin ƴan'uwan nashi, se yaga saɓanin haka, tun daga nan jikin shi ya sake
yin sanyi zuciyar shi ta karye dauriya kawai ya ara ya yafa ma kanshi.



Yaso yayi furnishing gidan, wata zuciyar ta hana shi,
Mama kawai ya ɗauka suka je ta zabi komi da ya dace da gidan suka siya aka wuce dasu can



Sun riga kowa komawa, se uncle Abbas,

Abba babba be dawo ba har seda uncle ƙasim ya riga shi shiga da sabuwar amarya, yana can
yana fama da rikicin umma babba, ita allanbaran sedai ya barta a gidan hayan, dan ita wai
zuciyar ta bata mutu ba da zata kwanta ƙanin ta yayi mata komi



Ƙarshe dai seda abun ya ɗauki zafi sosai, dan har umma ƙarama ta koma da ƴar jinjirar ta da
bata wuce watanni ba tukun umma babba ta dawo

Tun da kuma ta saka ƙafarta a gidan ta hau danasanin ƙin dawowa da wuri da bata yi ba, a
cewar ta "wannan aljnnar duniyar"



Nan fa ƴan'uwa da abokan arziki akai ta zuwa taya su murna da saka albarka



Tunda suka tare kowa ya shiga saiti, harta da umma b da ke da matsala ta nutsu ta dena shiga
sabgar kowa, se kuma a lokacin ne take so ta kame girman ta



Haka ta ɓangaren sauran, kowa harkar gaban shi yake

Mazajen ma sun haɗa kai, komi da ya shafi cigaban su a tare suke shawartawa, se kuma
albarkar haihuwa da aka fara samu akai akai



Gaba ɗayan su sun riga mama hauhuwa, dan har seda matar uncle ƙasim ta haihu da kusan
shekara kafin mama ta samu cikin mus'ab, lokacin faruk na da shekara goma sha biya a duniya.

Randa mama ta haihun kuwa haka ya kafa ya tsare akan babyn,

Sosai yake nuna mishi so da kulawa, kullum da safe kafin ya tafi school se ya leƙa ya gan shi,
haka zalika in ya dawo se ya leƙa
Gaba ɗaya ma kusan tarewa ne kawai beyi a sasan mama ba, umma b tayi faɗan tayi dukan
har ta gaji ta haƙura.



Shekarar mus'ab ɗaya da watannin mama ta sake haifo Ahmad, hmmmm ga arziki yaci uban na
da ga kuma ƙaruwar ƴaƴa maza da ake ta samu ta ɓangaren su da Allah yafi rufa wa asiri



Tun daga kan Ahmad shiru mama bata sake haihuwa ba, haka akai ta tafiya, yau daɗi gobe
akasin hakan

Umma b seda ta haifi yara shida cif sannn haihuwar ta tsaya
Ya faruk, ya sabiha, ya maryam, ya fa'iza, se hafsa da auta Amal.



Umma ƙarama tana da yara uku, ya fauza, ya khairi da auta fadil.



Mummy na da biyu

Ya Tk, da Aliyu(amir)



Aunty na da uku, Abdul, muhammad da mahmud.

Mama na da uku, mus'ab, Ahmad da auta mumtaz.



WANNAN KENAN, IN DA WANI ABU KUMA KWAJI A GABA.

CIGABAN LABARI.




Ledojin da ya shigo da su ɗazu ya janyo ya bubbuɗe su yana ware kayan, sosai ɗinkunan suka
yi kyau



Seda ya gama tas ya matsar da su tukun ya janyo ledar ɗazu da ya gani a inda mumtaz ta
zauna, yana buɗewa yaga agogunan shi guda biyu data ɗauka ne a ciki



Shiru yayi ya kafe su da idanu kamar me nazarin wasu abubuwa, a hankali ya saka hannu ya
ciro ƴar ƙaramar takardar da ke ciki ya buɗe idon shi suka kai ga ɗan gajeran rubutun dake ciki

"Kayi haƙuri dan Allah kar ka faɗa wa mama ko Abba na"

Iska me huci ya fesar bayan ya ajiye takardar a gefen shi, dunƙule hannun daman shi yayi da
ƙarfi, dan zaka ga jijiyoyin hannun sun yi riɗu riɗu

Cike da tsananin ɓacin rai yace

"Who is behind this?"(waye me hannu a ciki?) Tabbas AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI"



INA ME BADA HAƘURI NA JINA SHIRU DA KUKA YI NA KWANA BIYU, ABUBUWAN NE
KASHI DA KASHI



❤️
INA MIƘO SAƘON GODIYATA GARE KU "LAUJE CIKIN NAƊI FANS" ADDU'O'IN KU MEANS
ALOTS TO ME, ALLAH YA SAKA DA KHAIRAN



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
SHARE PLS.
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg17-18



A daren bayan sallar isha'i Abba ƙ da aminin shi yayan mamar suka turo ƙofar ɗakin suka shigo,
a lokacin an maida wa mama drip tana ta bacci mumtaz kuma na kwance ita ba baccin take ba
kuma ba wani abun take ba, kwance take tana saƙa da warwara
Jiki a mace kamar ko da yaushe ta tashi zaune haɗe da amsa sallamar Abban nata da kuma
aminin shi kuma kawun ta.



Kanta a ƙasa ta gaishe su bayan ta sakko daga gadon zuwa gefen mama



Har mumtaz ta zauna ta tuno da dattijuwar likitar tace ta kirata in Abba ƙ ɗin yazo



Murya a sanyaye tace

"Abbana, dr tace in kirata in kazo wai"



Jin yarda take magana a sanyaye yasa Abba ƙ kafe ta da ido yana son ya gano mene matsalar
ɗiyar tashi



Jin ta sake maimaita tambayar a tunanin ta beji bane,

Still idon shi a kanta yace

"Je ki kirata"



Gyara dogon hijabin ta tayi tukun ta fice zuwa office ɗin likitar.



Tun sallamar farko da Abba ƙ sukayi mama ta farka, idon ta ne kawai bata buɗe ba jin yarda
sukayi mata nauyi



Ganin tana marmar da idanun yasa Abban matsowa kusa da ita ya zauna

Bayan hannun shi ya ɗora a kan goshin ta jim kaɗan ya cire



Murya ƙasa-ƙasa mama tace

"temaka min in tashi zaune"
Kara mata pillow yayi a bayan ta tukun ya jingina ta da bango



A hankali ta buɗe idon ta a kan yayan nata da yayi shiru yana kallon yarda ƴar'uwar tashi ta
koma



Murmushin ƙarfin hali tayi tace

"sannu da zuwa ya junaid"

Shima matsowa yayi tukun ya amsa da "ya kika ƙara ji?"

Kanta a ƙasa tace "Alhamdulillah" nan da nan idanun ta ya kawo ƙwalla, Abba ƙ na lura da
ƙwallar ya fara tapping bayan hannun ta a hankali, ita tasan me yake nufi, cike da dauriya ta
maida hawayen.




Tayi knocking a bakin office ɗin yafi a ƙirga, jin shirun da yawa yasa ta murɗa handle ɗin duk a
tunanin ta ba ze buɗe ba

Aikuwa tana murɗawa ya buɗe,

Leƙawa tayi ciki, ganin babu kowa yasa ta jayo ƙofar da niyar kullewa, amma sam zuciyar ta
taƙi barin azalzalar da lokaci zuwa lokaci takan ji hakan



Sam mumtaz kasa daurewa tayi seda ta biye wa azalzalar zuciyar ta taƙara shiga office ɗin



Memakon data shiga ta yi abinda aka aiketa,
Ina ta mance tunda ta ɗora idanun ta akan abin hannun data gani ajiye akan teburin likitar ta
nufe shi kanta tsaye, jikin ta babu inda baya rawa tsabar luguden data ke ji a cikin zuciyar ta

Tana kaiwa teburin ta dafe abun hannun nan dake ta walwali da ɗaukar idanu daga ganin shi
kasan dutse ne me mugun daraja

Tana ɗauka ta zira shi a aljihun doguwar rigar ta

Seda ta tabbatar da taji shi a jikin ta tukun ta sauke ajiyar zuciya me nauyin gaske, bata sake
kallon komi a wajen ba ta juya tafice da mugun sauri har tana harɗewa da ƙafafuwan ta.




Mumtaz na fitowa daga office ɗin dattijuwar likitar na shawo kwana,

Juyawar da mumtaz tayi yasa likitar bataga fuskar ta ba

Kafin ta ƙaraso mumtaz ta yi gaba,

Gaba kaɗan ta ƙara se ga Abba ƙ
Fuska a ɗaure yace

"daga kiran dr se kije ki shantake?"



Da sauri ta sadda kanta a ƙasa, duk a tunanin ta ze gane abinda tayi a cikin ƙwayar idon ta,
tace



"Bata cikin office ɗin, shine na tsaya jiran ta, da naga bata dawo ba shine na tawo"



"okay" kawai Abba ƙ yace ya juya suka koma ɗakin.




Su Abba na shiga ɗakin likitar ta turo ƙofa itama



Da fara'a sosai a fuskar ta suka gaisa da su Abba, sannan ta ƙarasa kusa da mama dake zaune



Mumtaz kam ƙasa tayi da kanta tana ƙara jin faɗuwar gaban ta na daɗa tsananta, a hankali ta
saka hannun ta cikin aljihu ta lalubo abin hannu taji yana nan
Ajiyar zuciya ta sauke wanda yasa daga mama har likitar kallon ta.



Murmushi likitar tayi, sannan tace

"wannan ajiyar zuciyar fa ƴammata"
Itama ƙaƙalo murmushin tayi, bata ce komi ba ta tashi ta shige toilet.




Kallon ta Abba ƙ yayi yace

"Yanzu mumtaz ke cemin kina son gani na"



Gyara zaman glass ɗin fuakar ta tayi tukun tace



"Eh, matar ka na son in sallame ta, ni kuma saboda yanayin jikin ta da na gani yasa nace ba
yanzu ba, ta zauna ta ƙara jin sauƙi, da dai naga ta nace yasa nace in kazo ayi min magana"



Kafin Abba ƙ yayi magana ya junaid yace



"Kiji wata magana se kace ƙaramar yarinya fa"




Murya a sanyaye mama tace

"Ni fa saboda tafiya ta umara nace a sallame ni, a can ne zan kai ma ubangiji kuka na yarda ya
kamata, kuma ko ba haka ba ai ina ganin dr Sanaa kuma ta san problems ɗina sosai"



Kallon ta Abba ƙ yayi yace

"Yaushe ne tafiyar to?"

A gajerce mama tace "next tomorrow"



Numfashi ya sauke a hankali tukun yace

"Ki yi discharging ta kawai, na manta sam da zuwan namu can ma"



Cike da fara'a likitan tace "yarda kuka ce ai, fatan mu a samu lafia ai"
Kafin goma na dare Abba ƙ ya gama da bills ɗin tas

Ankai komi mota, da kanshi ya kama matar shi ya riƙeta mumtaz na biye da su a baya
Ya junaid ya musu sallama ya tafi.



Seda Abba ya zaunar da mama a seat ɗin gaba kafin ya zagaya ya shiga

Mumtaz kuma na baya, yaja motar suka fice

Daidai gate mumtaz tayi ido biyu da khalid da suka taɓa haɗuwa a kasuwar seda gold



Tsaf sun gane junan su, da sauri khalid ya sauke glass da niyar yima mumtaz magana, kafin ma
ya gama saukewa ta kawar da kanta gefe, gaban ta naci gaba da bugawa haka kurin



Ganin ta kauda kanta yasa da sauri ya gangara gefe yayi parcking, kafin ya ƙaraso motar su
Abba yaja sunyi gaba



Mumtaz na ganin sun wuce ta waigo da kanta tana kallon shi ido cikin ido, shima yayi tsaye ya
kafe ta da nashi idanun har motar ta ɓace ma ganin shi.



SHARE PLS

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg19-20

Jiki a mace yace

"Tunda har Allah ya sake nuna min ke to tabbas zamu sake haɗuwa dake!"

Still jiki a mace ya juya zuwa inda yayi parking ya shiga ya ƙarasa shiga ciki



Office ɗin da mumtaz ta fito ɗazu naga ya sanya kai ciki, yana shiga ya iske dattijuwar nan
tsaye tana dube dube ranta a mugun ɓace

Sallama ya sake yi a karo na biyu tukun taji, bata waigo ba ta amsa



Da mamaki khalid ya ƙarasa kusa da ita haɗe da faɗin

"Lafia kuwa mami?"



Ƙaramin tsaki taja, tana aje book ɗin ƙarshe data ɗaga tace



"Hmm, bracelet ɗina na aje anan ɗazu da zanyi alwala, emergency call da na samu ne na
mance ban ɗauka ba na fita, amma abun mamaki na duba sama ko ƙasa ban gani ba"



Sanin muhimmancin abun a wajen Mami ne yasa shima ya zage yana taya ta nema,
Aikuwa abun hannu yace ɗauke ni inda kk aje

Abu kamar wasa seda mami ta koma har inda taje ɗazu amma babu shi ba alamun shi



In ranta yayi dubu to ya ɓaci, sosai ta ɗauki abun hannun nan da muhimmaci ba wai dan
tsananin tsadar shi ba, se dan daga hannun wacce ya fitone yasa tayi mugun ɗaukar shi da
muhimmanci a rayuwar ta



Kankace me idanun mami yayi jajir tsabar ɓacin rai, macece me sauƙin hali amma tana da
mugun fushi in abu ya kaita maƙura
Tsabar gajiyar da ta yi ne yasa ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake jere a office ɗin nata



Hannun daman ta tasaka ta tallafe kuncin ta na dama,

Shiru tayi tana sake nazari ko zata tuna ƙila ba anan ta ajiye shi ba

Amma tsaf iya tunanin ta me hasasho mata komi ba



Jiki a mace ta tashi bayan khalid ya haɗa mata hand bag ɗin ta da duk wani abu da ya san tana
tafiya gida dashi



Murya a tausashe khalid yace



"Kiyi haƙuri mami, tunda kaf garin nan bracelet ɗin irin shi ne kaɗai baze yi wahalar ba, in ma
ɗaukan shi akayi to ba ze wuce sedawa za'ayi ba,
Se mu bada sanarwar kama duk wanda aka gani ya kaishi kasuwa"



Ajiyar zuciya mami ta sauke, bayan ta gyara zaman ta a cikin motar tace

"har na ɗanji sauƙi a raina, Allah ya dubeni yasa a ganshi da gaggawa, kafi kowa sanin yarda
nasa shi a raina, infact ma a gaban ka goggo ta damƙa min shi gaf da Allah ze karɓi rayuwar
ta"



Sosai khalid ya kwantar mata da hankali, basu kai gida ba yayi ta making calls yana bada
sanarwa akan abun hannun.




Tunda Mumtaz ta shiga ɗaki take kallon abun hannun, sosai idanun ta suka cika da ƙwallar
rashin sanin ta mecece

Jiki a sanyaye tace

"Kodai inje in maida?"
Jitayi zuciyar ta na raɗa mata "banda abunki mumtaz in kika kaishi kasuwa ba ƙaramin kuɗi zaki
samu ba, se kiyi ta hidimar ki ba se kin takura mama ko Abba da tambayar bani bani ba"



Knocking ƙofar ɗakin da akayi ne ya katse mata tunani, da sauri ta mayar da shi cikin aljihun ta
tukun taje ta buɗe ɗakin



Altine ce tsaye a ƙofar, mumtaz na buɗewa tace

"mama na kiran ki"



Bayan ta tabi, ita tayi kitchen, mumtaz tayi can ƙaramin palon maman inda matar uncle
junaid(yayan mama) tazo se wasu daga cikin ƴan'uwan su



Gaishe su tayi kanta a ƙasa ta wuce inda mama ke kishingiɗe, manya manyan ledoji jube a
gaban ta

Seda ta zauna tukun tace

"gani mama"



Idon maman a rufe ta nuna wa mumtaz ledojin gaban ta tace

"hijabai ne, ki ware naki, nima ki haɗa min nawa a cikin babbar akwatin nan da na haɗa kayan
tafiyar mu"



Da "to" ta amsa, da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai ta ɗauki ledojin tayi sama da su

Seda ta gama haɗa wa mama nata tukun ta wuce da nata da se a yanzu ta harhaɗa kayan
tafiyar ta, duk uban shelar da mamar tayi mata kusan sati kenan amma bata haɗan ba se
yanzu.



A daren duk suka koma gidajen su da adduar samun lafiya ga mama, wanda har yanzu babu
wanda yasan sabab ɗin ciwon maman.
Mumtaz na kwance wajen ƙarfe ɗaya da rabi na dare ta fara jin ƙarar kunna motacin gidan



A mugun sukwane ta sakko daga kan gadon ta leƙa ta window



Su umma b, mummy, da aunty ne, se Amal, hasfa, Bilkisu yarinyar ƙanwar umma babba ce, se
najwa itama mummy ce ke riƙe da ita, da Amir ɗan gidan mummy se mahmud autan Aunty



Da sauri mumtaz ta janyo wayar ta tayi dialing no ɗin Amal

Bugu biyu Amal ta ɗaga tayi saurin yin ƙasa da murya dan kar hafsat dake kusa da ita taji ta
faɗa wa umma b



Mumtaz tace

"Ina zakuje da tsohon daren nan? nasha tafiyar se daren gobe fa?"



Murya ƙasa-ƙasa Amal tace "ɗazu naji umma b na cewa an raba tafiyar ne saboda jikin mama
wai, so kune zaku tawo gobe"



Daga can mumtaz ta taɓe baki, murya ciki-ciki tace

"Ta daiyi munafurcin data saba yi"

Daga can Amal tace

"banji ba fa," sake taɓe baki mumtaz tayi tukun tace

"se mun haɗu kawai" ta tsinka wayar ta

Murmushi kawai Amal tayi, dan yanzu sam ta dena mamakin sauyin ƴar'uwar tata kuma ƙawarta

Maida wayar tayi jaka ta juya ta shiga kusa da Bilkisu

Mota biyu sukayi zuwa airpot, wajen huɗu saura jirgin su ya ɗaga zuwa ƙasa me tsarki.
WASHE GARI

Mumtaz na ganin zuwan sakina ta bar mata sauran aikin da mama ta saka ta

Ɗaki ta nufa hijabi ta ɗauka se wannan abun hannun da zuciyar ta ke ta azalzalar ta akan ta
saida shi

Ta ƙofar da Abba ƙ ke shigowa tabi cikin sanɗa dan kar Altine ko sakina suji motsinta take tafia

Seda ta ɓulle zuwa gate tukun ta saki jikin ta tafara tafiya normal

Abunda bata sani ba shine, ya faruk ya ba me gadi lasisin kiran shi a duk lokacin da ƴammatan
gidan zasu fita, be ware sunan ta ba gudun zargi ko wani abun daban, se yace dukan su har da
wanda ake riƙon su a gidan kuwa



Yana ganin tunkarowar ta gate ɗin ya zaro wayar shi kuwa

Tana ficewa ya danna ma ya faruk kira, murya a ƙasa yace

"yallaɓai, yanzun nan hajiya mumtaz ta fita"



"nagode" ya faruk yace ya tsinka wayar, yana gab da shigowa layin gidan ne daman, tunda gate
man ya kira shi ya samu waje ya tsaya, be kashe motar ba yana zaune a ciki ya baza idanu
yaga ta ina zata ɓullo



Zaman kusan minti biyar yayi tukun ya hangota,

In wani ne da be san ta ba ya ganta zece a nutse take tafiyar ta

Amma shi da yayi mata farin sani kallo ɗaya yayi mata ya gane ba gaskiya tattare da ita



A ɗan gaba da shi kaɗan ta samu kekenapep ta hau



Beyi ƙasa a gwiwa ba ya bi bayan su a hankali,

sosai gaban shi ke faɗuwa dan sam be yarda da fitar ta ba
Haka zalika a dokar gidan ba'a aiken ƴaƴa mata ko nan da can hasalima basu hawa motocin
haya balle a kai ga kekenapep,

duk rintsi ana musu wannn alfarmar na kaisu duk inda suke so



Sannu a hankali yake binsu har suka dangane da bakin babbar kasuwa



A tsorace mumtaz tace

"sauke ni a nan kawai mlm"



Waigowa me keken yayi yace

"bamu zo ba ai hajiya, kasuwa gold na ɗan gaba wannan babbar kasuwa ce ai"



Dallaro mishi manyan idanun ta tayi tukun tace

"na sani ai ɗan'iya, a nan naga damar sauka"

Ta ciro ɗari biyar ta miƙa mishi sannan ta sauka.



Ya faruk na ganin ta sauka yayi saurin ciro wayar shi ya danna mata kira



Yana kallon sanda ta kalli wayar, memakon ta ɗauka sema murguɗa baki datayi, yana kallo tana
motsa baki alamun magana take, maganar ma yasan be wuce rashin kunya ce



Seda yayi mata kira uku bata ɗaga ba, kuma ta kasa shiga kasuwar sam

Sosai zuciyar ta ke ingiza ta, amma wani sashi na zuciyar yana dakatar da ita



Kome ta tuna oho, jikin ta har yana rawa ta tsaida wani me keken ta hau



Ya faruk na ganin haka ya juya yabi bayan ta again
Mugun mamaki ne ya sake kamashi ganin sun ɗauki hanyar gida

A fili ya furta

"bata da gaskiya, wani abun tayi niyar shukawa"



Kafin a kai gate ɗin gidan ya sauke ta taƙarasa da ƙafa.




Seda ya faruk ya bada tazara sosai kafin ya shiga gidan shima



Direct side ɗin mamar ya nufa, seda ya duba ta da jiki tukun

6 / 25