Author : ZAINAB FALALU Category : African Stories & Novels
min harda na ballagazanci ma
ashe?"
dafa goshin ta tayi ta hau furta "LA'ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU
MINAZZALIMIN"
Idonta a lumashe, laɓɓanta ne kawai ke motsi, Alhamdulillah, ko ba komai ta fara jin sauƙin
nauyin kirjin ta.
Seda jirgin su ya lula sararin samaniya, komi ya daidaita dan har hasken ciki an kashe Hafsat ta
dafa kafaɗar najwa dake kujerar kusa da ita tace
"me na gaya miki?, in har baki fita sabgar ya faruk ba to tabbas abinda yayi miki ɗazu kaɗan ne,
ko baki faɗa ba nasan kinji haushi dan gashi nan ya nuna ƙuru-ƙuru a fuskar ki"
Yaƙe najwa tayi sam bakin ta ya mutu murus, dan bata taɓa zaton hakan ba.
Haka hafsa ta gama ban bakin ta har ta gaji tayi shiru.
*****KHALID
Tunda aka kira sallar magariba yake neman mumtaz be samu ba
Duk ya bi ya damu ya susuce na rashin ji daga gareta
A hankali ya taka har zuwa wajen da yake tunanin ganin ta, amma wajen wayam bata ba
alamar ta
Jiki a mace yayi typing mata "Call me as soon as u see this pls"
Ƙura wa saƙon ido yayi kamar zega ta buɗe, haka nan ya ƙaraci tsayuwar shi ya haƙura, bayan
ya bar masallaci seda ya jima sosai a bakin hotel ɗin da suka sauka, nan ma ya ƙaraci tsayuwar
shi har ya gaji ya tafi.
****
Ƙarfe huɗu da rabi na asuba jirgin su ya sauka, tun kafin su taso dama ya faruk ya sanar wa da
bala driver yaje ya ɗakko su.
Sanda suka shiga gida har an fito daga sallar asuba a masallatai, Allah ta temake su sunyi
sahur a cikin jirgi
Kowa na fitowa daga cikin motar ya nufi part ɗin su,
Amal ce kawai bata kai ga tafiya ba tace wa mumtaz da tayi tsaye
"muje part ɗin mu mana"
Murya a dishe mumtaz tace
"no, kije kawai"
Da yake akwai gajiya sosai yasa Amal ko jan maganar batayi ba ta juya ta shige ta barta nan a
tsaye
jiki a mace ta waiga ta kalli ko ina na gidan, a hankali ta furta "tabbas mahaifa babban garkuwa
ne ga ƴaƴan su"
Tana nan a tsaye kusan minti sha biyar bata ga tsuntsu bata ga tarko taji muryar Abbah babba
yace
"waye nan a tsaye?"
Kai tsaye tace "nice Abba b"
Da mamaki yace
"me kike jira baki shigo ciki ba?"
Still jiki a mace ta waiga inda akwatinta yake ta janyo shi tukun tace "yanzu nake shirin
shigowa"
"to" kawai yace ya juya ciki.
Tana ɗaga kai taga ya bar balcony ta juya ta fasa shiga can ta wuce part ɗin su kai tsaye
Duk da bata da tabbacin ganin keyn ƙofar, haka ta ƙarasa wajen data san suna ajiye spare
incase ko wani abun ze kama
Da ƙyar ta ɗaga tukunyar flower dake aje ta gefen part ɗin, luckey enouhg kuwa taga makullin,
ɗauka tayi ta nufi ƙofar palon kai tsaye ta buɗe
Seda ta buɗe tukun ta koma ta janyo jakar kayanta sannan ta shige
Da mamaki tabi palon da kallo ganin ba'a kashe wutar gidan ba, motsin data ji daga wajen ɗakin
mama yasa ta ƙarashe firgicewa,
Duk da tsoron data ke ji hakan besa ta fasa kurɗawa ciki ba
Saɗaf-saɗaf, haka yake tafiya har ta ƙarasa inda tafi jin motsin
Ga mamakin ta mutum ne a kwance kan doguwar kujerar ɗakin, ya kifa cikin shi kan kujerar,
Idanun shi a rufe yana bacci
Mumtaz na tozali da wanda ta gani ta ja da baya ta kurma uban ihu, hannun ta na karkawa
bakin ta na rawa take nuna shi
Jin ihun ta da mutumin yayi ne ya farkar da shi shima da sauri ya nufeta a mugun sukwane.
HMMMMMMM!
RASHIN SHARHI KE HANANI TYPING ME YAWA 🙄
AYI MANAGE DA WANGA 👆
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
SHARE PLS.
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg30
A mugun sukwane ya nufi mumtaz ganin tana neman fita daga hayyacin ta
Ƙam ya riƙeta a jikin shi, muryar shi ta irin wanda ya jima da fara bacci yace
"Relax mumtaz, kar kisa a san da zamana a cikin gidan nan mana"
Sam ta kasa riƙe kukan dake cinta, cikin kukan tace
"Dama ya mus'ab kana nan?, ina kaje ina ka shige dan Allah, mama har kwanciya a asibiti tayi
saboda tafiyar ka, hankalin duk wani masoyin ka ya tashi"
Nan da nan idanun shi suka kaɗa sukayi jaajir tsabar fushi da yarda yake jin raɗaɗi a cikin
ziciyar shi
Kasa furta ko kalma ɗaya yayi, sema janta da yayi zuwa kan kujera ya zaunar da ita
Ya kai kusan minti biyar yana haɗiyar zuciya kafin yace
"Na sani mumtaz, ina tare da ku a koda yaushe, zamana a cikin ku babbar illace a gareki,
Ahmad, mama da kuma Abba, na gano abinda be kamata na gano ba sam, naji abinda ya
hanani zama a cikin jini na mumtaz, banso kika ganni ba a halin yanzu gudun kar kema kishiga
matsala makamanciyar tawa"
Shiru yayi yana sadda kanshi ƙasa
Cike da mamaki da kuma kokwanto mumtaz ke kallon shi, ji take kamar bata gane yaren da
yake, duk da yaren hausa ne
Cike da tsoro tace
"Ya mus'ab me kake nufi ne wai, nifa sam ban fahimce ka ba"
Murya ƙasa-ƙasa yace
"Bana so ki fahimta ne ai, abu ɗaya nake so dake shine, ki zama very vigilant a gidan nan, karki
yarda da kowa sannan karki yarda da kowa a kusa da mama,
Sannan ban san ko yaushe ne za'a tattara ku ba a kan maganar fitar da mazan aure, amma ko
yaushe ne ki tabbatar da kin tsaya a kan ra'ayin ki, kada ki kuskura ki yarda da ra'ayin kowa,
kuma duk yarda za'ayi kisa mama ta kori Altine daga gidan nan koda kuwa ta hanyar ƙulla mata
sharri ne"
Da sauri mus'ab yayi shiru yayi kasaƙe da kunnen shi, ko second goma beyi ba ya miƙe zumbur
Mumtaz na ta binshi da kallon tsoro da tuhuma
Har ya kai ƙofar kitchen ya dawo, be yarda yaci gaba da magana kamar ɗazu ba, saitin kunnen
ta ya ranƙwafo yace
"zan tafi badan naso ba, kar ki kuskura ki nuna ma koda mama ne in sun dawo cewa mun haɗu,
amma kisa a ranki ina nan a tare da ku ako wani irin hali"
Har ta buɗe baki zatayi magana yayi saurin rufe mata baki da hannun shi, sannn ya sake ƙasa
da muryar shi yace
"Kome kika furta a yanzu ze iya zama ajalina ko naki ko kuma na iyayen mu da sukai saura
basu dawo ba, ki adana maganar ki har sanda muka sake haɗuwa, shima se Allah ya nufa"
Kitchen ya nufa da saurin gaske,
Shiru-shiru mumtaz na zaune tana jiran taga ya fito, tun tana kallon agogo har ta gaji ta yunƙura
da ƙyar ta shiga kitchen ɗin, amma ga mamakin ta ba mus'ab ba dalilin shi, bakuma taga wata
ƙwaƙƙwarar hanya da za'a ce mutum ya wuce ba
Nan ma tsananin tsoro ya kamata, jikin ta har karkarwa yake wajen kunna wayar ta
Allah-Allah take ta gama booting, tana gamawa tayi dialing numbar sakina(ɗiyar yayan mama)
seda ta kusa tsinkewa tukun sakina ta amsa da
"Barka da sauka mumtaz"
Bata tsaya jin komi ba tace
"Sakina dan Allah kizo yanzu ki ɗauke ni a gida, ba se kin shigo da motar ba, kawai ki kirani in
kin ƙaraso"
Tambayoyi ta fara jero mata, cikin zaƙuwa mumtaz tace
"kedai ki zo zakiji komi pls" kit ta kashe wayar ta koma ta dunƙule waje ɗaya, tana jin wani
mugun zazzaɓi na kamata.
20mins drive ne ya kawota sharaɗa phase2, dialing no ɗinta tayi
Mumtaz na ganin call ɗin sakina ta tashi da sauri, akwatin data zo dashi shi ta sake ja ta fice,
sam ta mance bata da rufe ƙofa, seda ta kusa gate ta tuna ta dawo da gudu ta rufe
Gaf da da zata fita gate taga ya TK da wani friend ɗin shi sun shigo gidan
Sama-sama ta gaishe su tayi gaba
Haka abokin nan ya kafeta da ido kamar wani tsohon maye, dan seda ya Tk ya zungure shi da
ƙafa kafin ya dawo daga lulawar da yayi
Warda akeyi domin ita bama tasan yana yi ba, tayi waje abinta.
Sakina na zaune cikin mota taga fitowar ta,
fitowa tayi ta taya suka saka kayan
Kafin sakina ta gama saka zakar hannun ta har mumtaz ya shiga motar
Sanna itama ta zagayo ta shiga mazaunin driver taja suka tafi.
Jin mumtaz ta mata shiru batace komi ba yasa tace
"kin tsira ma waje ɗaya idanu bayan kin san jiran jin ki nake"
Mumtaz tayi niyar suyi maganar, amma haka nan taji ranta be aminta da tayi zancen da sakina
ba,
Busashshen murmushi ta yi sannan tace
"Dan kizo ki ɗauke ni fa kawai, amma bakomaai"
Murmushi sakina tayi kafin tace "in tayi wari maji, yaushe kuka dawo?"
"Ɗazu" tace ta maida idanuwanta ta lumshe.
****
Biyu da rabi na rana umma babba ta sakko zuwa ɗakin ƴammatan ta dake ta baccin gajiya tun
da suka dawo
Tura ƙofar ɗakin tayi ta iskesu sunyi ɗai-ɗai, taso tashin su kome ta tuna? oho, ta juya ta fita
zuwa kitchen inda masu aiki ke ta soye-soyen kayan flour
Nan ta gama bada umarni umarnin yarda za'a shirya komi kafin ta koma bedroom ɗin ta.
Kamar yarda ake ta hada-hada a sasan umma babba haka sauran sasan aunty da mummy ma,
wasu daga cikin su ma har sun fara karɓan baƙin ƴan'uwansu da zasuyi sallah a nan.
***MAMA
Tun da ta tashi take neman layin mumtaz amma shiru bata ɗauka, farko tayi tunanin ko baccin
gajiya take, amma har bayan la'asar data sake neman ta shima shuru ba amsa
Sauya akalar kiran tayi ga layin umma ƙarama, bugu biyu umma ƙ ta ɗaga, cike da fara'a da
mutunta juna suka gaisa
Can mama tace "Ehn, dan Allah hajiya sumayya mumtaz nike so ki ɗan haɗani da ita, ina ta
kiranta bata picking"
Da mamaki umma ƙ tace "Ah, wai mumtaz ta dawo ne itama?"
Mama tace "tare suka dawo duka ai, nasha tana nan wajen ku"
Umma ƙ tace "to banƙi ta taki ba, bari na dubota ko tana wajen su Amal, riƙe wayar"
Da "to"maama ta amsa
A kunnen ta taji umma ƙ na tambayar Amal inda mumtaz take
Daga can ta jiyo Amal tace "ban sani ba umma ƙ"
Umma ƙ tace "kamar ya baki sani ba?"
Da ɗan ƙosawa tace "da muka dawo a waje muka barta, nace tazo muje tayi banza dani, daga
nan ban san inda tayi ba"
Umma ƙ na tsaye a ɗakin su Amal, umma b ta shigo jin maganar su,
Ba yabo ba fallasa tace "hajiya sumayya lafia?"
Mama na jiyo su daga can, kafin umma ƙ tabawa umma b amsa mama tace
"ko tana part ɗina ne?"
Umma ƙ tace "bari inje can to"
Taɓe baki umma babba tayi ta juya tana faɗin
"Gulmamammu kawai, shishshigi babu kwarjini" ta ƙarashe ficewa.
Can ma wayam bata, nan ne fa hankalin mama ya fara tashi, farat ɗaya tafiyar mus'ab ta dawo
mata kai
Cike da zullumi tace
"ko dai tana gidan Abbas ko ƙasim?"
Kafin umma ƙ tayi magana, mama taga call ɗin mumtaz na shigowa, da sauri tace "gashi tana
kirana bari naji".
Seda taji daga wajen ta tukun hankalin ta ya kwanta, duk da tayi mata faɗan rashin gaya mata
datayi.
Da suka gama wayar ta kira umma ƙ ta gaya mata taje gidan ya junaid ne ashe.
*****KHALID
Daga yinin jiya zuwa na yau duk yabi ya susuce rashin ji daga wajen ta, msgs kam ya tura mata
su kamar me
Bashi da aiki se duba waya akai akai,
Bayan sallar isha haka ya sake wankar ƙafa ya koma hotel ɗin da suka sauka, haka yasha
zama kamar jiya amma bata da dalilin ta.
Zuwan shi na jiya dana yau duk akan idon ya faruk, yasan khalid farin sani tunda a ƙarƙashin su
yake aiki,
Yasan yana da kirki, amma ba ze iya cewa ga hallayyar shi ba, a fili yace
"Zanci gaba da sa maka ido naga dame kazo".
Mumtaz na kwance a ɗakin data sauka, baka jin motsin kowa alamar dai dare ya ratsa
Juyi kawai take tana farfasa maganganun da ya mus'ab yayi mata ɗazu,
Gaba ɗaya kanta ya kulle ta rasa wani kalar tunani zata yi akan maganar, dama tacika damun
kanta taji ya fara sassara mata,
Haka ta tattara ta watsar da zancen, abu ɗaya ne ta ɗauka shine bazata bari kowa yaji ba har
sanda ya dace
Khalid ne ya faɗo mata a rai lokaci ɗaya, sam ta mance da babin shi daga jiya zuwa yau, se
yanzu daya faɗo mata
Wayarta dake gefe ta janyo, kunna data tayi ta hau whatsapp, kan kice me saƙonnin shi suka
rinƙa antayowa
Tsuru tayi ta kafe wayar da ido
Seda suka gama shigowa tas tukun ta buɗe ta fara bin saƙonnin ɗaya bayan ɗaya tana dubawa
A karon farko tun jiya da tayi murmushi, ita kanta bata san sanda hakan ta kasance ba
Se tsintar kanta tayi da replying shi, ta rubuta "whats wrong"? akan saƙon shi da ya rubuta "ina
cikin wani hali" da manyan baƙi.
Khalid na ganin saƙon ta, hannun shi har rawa yake wajen danna mata kira
Tana ɗaga wayar ta kara a kunne tayi shiru tana sauraren shi
"Baki da wani excuse da zaki bani, kina ina?"
Murmushi mumtaz tayi kafin tace "ina nan mana"
Cikin zaƙuwa yace "meyesa ban ganki a masallaci ba? har hotel ɗin da kika sauka naje nasha
jira amma banga ko me kama dake ba mumtaz" yaja sunan ta daga ƙarshe
Zumɓuro baki tayi kamar yana ganin ta kafin tace
"kai dai bari, Allah ne ya haɗamu da ɗan baƙin ciki yasa aka auno mu gida"
Yarda tayi maganar dole ya baka dariya, seda khalid ya dara kafin yace
"who was that person?"
Seda ta taɓe baki again kafin tace "a dangi yake, ataiƙaice dai ina ƙasarmu ta gado"
Duk da khalid beji daɗi ba, amma ya samu relief ko yayane, nan suka raba kusan daren gaba
ɗaya suna fira,
Abun mamaki sosai mumtaz ta saki jiki da shi se gashi tana neman kunci da damuwar data
shiga sam ta raaa ta, ji tayi ma kamar kar ya kashe wayar su dauwama a haka.
A ranar daga khalid har mumtaz baccin farin ciki sukayi da alƙawarin haɗuwa a ranar sallar da
ze dawo da yamma,
Saɓanin wasu ƴan tsirarai masu mugun nufi da suke kwana da yini wajen tarwatsa rayuwar
bayin Allah da yawa wanda basu jiba basu gani ba, saboda tsabar son zuciya da rashin rabo!!!!.
SHARE PLS
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg 31-32
BAYAN SALLAH DA KWANA BIYU
Tun safe da umma b ta fito daga wajen Abba b ta samu su Amal a ɗaki, duk da sun tashi amma
suna zazzaune
Wayace a kunnen hafsa, while Amal kuma handouts ne a gaban ta tana dubawa
Da sallama umma b ta shiga ɗakin,
Stool ɗin gaban mudubi taja ta zauna,
Sallama hafsa tayi da wanda suke wayar ta maido da hankalin ga umma b dake binsu da kallo
Amal ma juyowa tayi gaba ɗaya sukai shiru suna kallon ta.
Seda ta mula da kallon su tukun tace
"Dake zan fara Amal, Amir da faisal wanne yafi gwaɓi a cikin su?"
Bin ta da kallo Amal tayi, dan har ga Allah bata fahimci kalmar "gwaɓi" da umma tace ba
Ɗan shirun da Amal tayi tana nazarin kalmar, umma ta sake maimaita tambayar tana kafe ta da
idanu itama
Da gaske Amal tace "wallahi ban gane me kike nufi ba umma
Ƙafa ɗaya kan ɗaya umma ta ɗora sannan tace
"Bari nayi maki dalla dalla, ina nufin Amir da faisal wanne yafi wani a cikin su?"
Murmushi Amal tayi kafin tace "Amir ɗin dai umma"
Karaf hafsat tace "billahillazi ƙarya take, ko motar da faisal ke zuwa gidannan zata siya ta Amir
sau biyar umma"
Murtike fuska Amal tayi, cike da tsiwa tace "ba ruwanki a cikin maganar nan wallahi"
Da sauri Umma ta ɗaga masu hannu haɗe da faɗin "Ku dakata min" duka sukayi shiru suna
kallon ta, idonta ta maida ga Amal sannan tace "na san kece zaki fi bani matsala, daga yau
zuwa jibin da Abban ku yace zasu tara ku suji zaɓin ku na wanda kuke so, ina so ki fitar da
wanda yafi rigar arziƙi a cikin su, kuma kar naga ba abinda nake so ba"
Sadda kai ƙatsa Amal tayi jin abinda umman ke faɗa
Cike da zumuɗi hafsat tace
"umma wai maganar ta taso ne?"
Seda ta ɗan taɓe baki tukun tace
"Tunda me ƙumbar susa ya bada umarni ai dole a bi,"
Zaro ido Hafsat tayi ta ɗan sake matsowa kusa tayi ƙasa da murya tace
"Umma, to harda ƴar gaban goshin nashi ko mu kaɗai?"
Dariya umma b tayi sannan tace "hmmm, harda ita fa, da Bilkisu da Najwa ma"
Baki buɗe hafsat tace "jakar uba, to da wa za'ayi kenan?"
Wannan karon dariyar da umma b tayi tafi na ɗazu
Seda ta dara sosai tukun tace
"Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta"
Da ga nan tayi gaba ta ja musu ƙofar.
Umma na fita Amal ta kalli hafsat tace
"Mugunta fitsarin faƙƙo ce dai ya hafsa, har wani murna kike saboda wani dalilin ku mara tushe"
Kafin Amal ta rufe baki hafsat tayo kanta a mugun sukwane, dayake Amal ta san hali, dama
tayi readyn fita, aikuwa tana yunƙurowa ta kwasa tayi waje da gudu
Aikuwa hafsat kamar ta ari baki saboda masifa da take zazzagawa, seda ya fauza da basu jima
da zuwa gidan ba ita da khairi suka shiga tsakanin su tukunna.
Ya fauza da yake tana da faɗa sosai ta hau surfa musu bala'i, tace "kuna girma kuna cin ƙasa
shirmen banza"
A fakaice hafsat ta murguɗa mata baki ta juya tana gunaguni.
Kamar yarda umma b ta zaunar da yaran ta tasanar da su saƙon Abba b, haka ma mummy, duk
da Najwa ba ƴar cikin ta bace riƙonta take, hasali ma saboda son da take ma ƴa mace ne kuma
Allah be bata ba yasa yayan ta ya bata Najwa halak malak tun daga yaye
Najwa na kwance a kan doguwar kujera mummy ta sanar mata da umarnin su Abba
jin Najwa bata ce komi yasa mummyn cewa
"ya dai? ko akwai wani abunne?"
Can ƙasan zuciyar ta na zigata ta ce ya faruk take so, amma wani sashi na zuciyar yana ƙwaɓar
ta, murmushin dole ta ƙwaƙulo tukun tace
"nothing mummy, kawai naji maganar ne daga sama"
Shafa kanta tayi tace "mutuncin duka ƴa mace ɗakin mijin ta, tun da Allah yasa sadik na son ki
kema kuma kina son shi ba shikenan ba?"
Gyaɗa kai tayi, tana ƙara cire ya faruk daga cikin ranta dan har ga Allah bata son tayi auren da
ita kaɗai ke so.
******MUMTAZ
Kicin-kicin mumtaz tayi da fuska, jin me sakina ke gaya mata, bayan sun gama shirin tafia
airport tarban Abba ƙ da mama
"Gaskiya guy ɗinnan be iya zuwa