Author : ZAINAB FALALU Category : African Stories & Novels
ni kam na riga da na gama haɗa komi da za'a
maka su a kotu, suje can su girbi abinda suka shuka"
Anan ya faruk ya sake fayyace musu kashe Abba ƙarami da suka sha kwatanta yi Allah baya
basu nasara
Da kuma irin ƙulle-ƙullen da suke shiryawa, har ma da auren Tk da sakina tayi, da shirin su na
warwarewa a maida auren mumtaz kan Tkn, kaf har accident da Abba ƙ sukayi duk shirin su
uncle Abbas ne.
Nan ma waje ya sake kiɗemewa
Basu ankare ba sedai ganin Abba ƙarami suka yi yana sassan ƙamewa idanun shi na
kakkafewa
gaba ɗaya kowa yayo kanshi banda umma ƙarama data fece, uncle junaid ma na ganin haka ya
fece, uncle Abbas na zaune ba um ba un un se idanu
A ruɗe uncle ƙasim yace Ahmad ɗakko mota bari mu sakko da shi
Mama kam faɗi take "shikenan sun ƙarasa min shi, sun kashe min shi, innalillahi wa'inna
ilaihirraji'un"
Ihun da mumtaz take ne ya raba hankalin ya faruk biyu, daga ƙarshe dai barin su Abba babba
yayi da ɗaukar Abba ƙarami, shi kuma ya rungume mumtaz da itama ke neman fita daga
hayyacin ta
Hankali a tashe umma babba ke faɗin "riƙeta da kyau faruk kar ta illata kanta ayi biyu"
Da ƙarfi ita da goggo safiya suka kama mama itama suka riƙe
Cike da tausayi umma babba ke faɗin "Sannu hajiya zahra'u(mama) nutsu kar kema kiji wa
kanki ciwo,
Akwai baƙin ciki amma kar ki bari hankalin ki ya gushe ya bar jikin ki"
Tana magana tana maimaita kalamar "hazbinallahu wani'imal wakil" da kusan kowa ke ambata
a palon.
Da mus'ab da uncle ƙasim ne suka ɗauki Abba ƙarami da gaba ɗaya baya numfashi
Abba babba da kanshi ya karɓi key ɗin motar daga hannun Ahmad ganin yarda jikin shi shima
yake rawa
Seat ɗin baya aka buɗe, uncle ƙasim ya fara shiga se aka saka abba ƙarami aka miƙar da shi,
kanshi na kan cinyar uncle ƙasim,
Mus'ab da Ahmad suka shiga gidan gaba a matse, Abba babba ya figi motar da gudu suka fice.
Cikin kuka mama ke faɗin "wannn wani iirin cin amana ne da yankar ƙauna, ƴan'uwan ka na jini
su rinƙa maka maƙarƙashiya saboda abin duniya da duk barin shi zamuyi a nan mu tafi"
Tana rungume jikin umma babba take wannan maganganun,
Umma b faɗi take " ya isa haka, kiyi addu'a ne, surutun kar ya jawo miki wata matsala"
Zabura mama tayi ta miƙe, gaban Tv stand taje ta ɗauki wayar ta,
Sam bata yi la'akari da cewa dare ne ba ta danna wa inna hassu kira dake gidan uncle junaid
Bugu biyu ta ɗaga, fashewa da kuka tayi tace "kizo inna hassu su ya junaid sub kasaarani sun
kashe man miji bayan mugayen manufofin su da basuyi tasiri ba se a yau"
Hankali a tashe inna hassu ta miƙe zaune tace "me kike nufi? Abubakar ɗinne ya mutu?"
Sam hankalin mama baya jikin ta, "eh" kawai tace kafin ta aje wayar
A kiɗime inna hassu ta fito palo ta nufi ɗakin mum Asiya da shigar ta kenan
A firgice tace "yanzu aka kirani Abubakar(Abba ƙarami) ya rasu
Salati mum asiya ta buga haɗe da dafa ƙirji
Hankali a tashe tace "mun shiga uku, wannan wani irin masifa ne daga wannan se wancan"
Da sauri ta rarumi hijabi ta ɗora akan kayan baccin ta tace "muje inna hassu, ai bamu ga ta
zama ba"
A tsohon daren nan suka nufi gidan Abba ƙarami.
Da suka zo kuma suka ji saɓanin abinda mama tace, nan hankali yafi na ɗazu tashi
Banda kuka babu abinda mum asiya keyi,
Cikin tashin hankali take faɗin "shine yasa min ƴa a cikin masifa, wallahi tallahi ba zan yarda ba,
sedai koma meye ya ƙare a kanshi shi kaɗai"
Inna hassu kam ba baka se kunne, dan abin ya wuce da tunanin ta sam.
Tuburewa mama tayi tace "se ta tafi hospital ɗin itama"
Umma babba tace "ai dole ko mu hankalin mu ai ba kwanciya zeyi ba muna a nan".
Goggo safiya, mama, umma babba, aunty(matar uncle ƙasim), inna hassu, su biyar umma
babba ta kwashe su a mota bayan ya faruk ya gaya mata asibitin dr jamal aka kaishi
Su umma babba na fita ya waiga inda su ya maryam sukayi cirko-cirko kowa hankalin shi a
tashe yace "ku kula da gidan, bari na bi bayan su"
Mumtaz na a jikin shi, seda ya zagaya ya saka ta a seat ɗin gaba sannan ya zagaya shima ya
shiga yaja suka tafi
Suna tafe tana ci gaba da kukan,
Da ƙarfi ya taka burki yace "wallahi zan fasa zuwa dake in bakiyi shiru ba, haka zamu shiga
cikin hospital ɗin kina rusa kuka?"
Da sauri ta kaɗa kai dan taji tsoro da birkin da ya taka
"To share hawayen ki, babu abinda ya same shi, shock ne kawai"
Da bayan hannu ta shiga share hawayen ta, ta hau sauke ajiyar zuciya.
Sanda su Abba suka isa har an tanaji streacher a wajen parking lot
Suna isa ba awani ɓata time ba aka shiga da shi ciki.
Nan suka tsaya cirko-cirko, basu kai minti talatin da isa ba motar umma babba ta iso
Ita da kanta ta riƙe mama har suka ƙarasa wajen da su Abban ke tsaye duk sun kasa zama
Cikin kuka mama tace "ya mutu ko?"
Cike da tausayawa Abba babba yace "be mutu ba zahra'u, addu'a zamuyi masa Allah ya tashi
kafaɗun sa"
Kamata umma babba tayi tace "zauna a nan karki faɗi"
Ba musu mama ta zauna haɗe da aza kanta a kafaɗar umma babba.
Su ya faruk na isowa mumtaz ta ƙwace hannun ta daga cikin nashi ta nufi inda mama ke zaune,
kusa da ita ta zauna itama ta ɗora kanta a jikin maman
Daga can gefe ya faruk na tsaye yana kallon su
Kan maman shi a kafaɗar umman shi, sannan kan mafi soyuwar matar shi a kafaɗar maman shi
Besan lokacin da ya hau furta "Alhamdulillah" ba, haɗe da sake jin ƙaunar ta na ratsa jini da
jijiyoyin jikin shi.
Suna a nan zaune har wajen huɗu saura na asuba dr jamal ya fito,
Cike da girmamawa ya gaishe da iyayen aminin nashi sannan yace "zaku iya tafia gida Abba,
zuwa da safe se ku dawo, mun samu numfashin shi Alhamdulillah ya samu bacci kuma"
Kai tsaye mama tace "zan tsaya ni kam, bazan iya komawa ba gaskiya"
Jinjina kai Abba babba yayi sannn yace "ku muje gidan, ita seta tsaya"
Hakan akayi kuwa kowa ya tafi, umma babba har ta miƙe ta dawo saitin mama tace "Me za'a
tawo maki da shi da safen?"
Murya a dishe tace "kaya marasa nauyi kawai"
Umma babba ta sake cewa "abinci fa?"
Shiru mama tayi can tace "anything"
Snnan umma b ta miƙe haɗe da faɗin Allah ya bamu alkairi yasa kuma muji shi, tabi sahun
sauran.
Ya faruk da mumtaz suka saka mama a tsakiya
Ahmad da mus'ab na tsaye suma
Ya faruk yace "ki kwantar da hankalin ki mama, ki dena kukan in sha Allah komi yazo ƙarshe"
Sake fashewa da kukan tayi tace "ya junaid fa faruk? ɗan'uwana ne fa in kowa zemin haka ban
taɓa tsammanin hakan daga wajen shi ba, wai harda hajiya sumayya da nafi kusanci da ita
akan kowa a cikin gidan nan"
Ta ɗora da "kai innalillahi wainna ilaihirraji'un, Allah ya sani sub cutar dani da alhalina, sub cutar
da zukatan da basu san komi ba se alkairi" kuka yaci ƙarfin ta takasa cigaba da maganar
Nan dai suka haɗa baki dukan su suka rarrashe ta
Kafin su rakata har ƙifar ɗakin da Abba ƙarami ke ciki
Kallon ya faruk mus'ab yayi yace "ka ɗauke ta kawai kuje, ni da Ahmad muna nan"
Murmushi ya faruk yayi, dafa kafaɗar su yayi yace "I trust u guys, nasan ba wani shege"
Dariya Ahmad da mus'ab sukayi gane me ya faruk ke nufi da ba wani shege.
daga nan ya wuce wajen dr jamal sukayi magana, kafin ya dawo yaja hannu mumtaz suka
wuce.
Titi tsit babu kowa saboda dare, haka ya faruk ya saki mota hankali kwance
Memakon mumtaz taga sunyi hanyar gida se taga sun ɗauke wata hanyar daban
har taso tayi magana ta fasa ta dai ci gaba da kallon hanya
Nasarawa taga sun nufa, a take gaban ta ya faɗi tunowa anan ne gidan ya faruk ɗin yake
Ta gefen ido yake kallon actions ɗinta, ganin ta dake itama ta basar yasa shima basarwa har kai
makeken gate ɗin gidan nashi sannan ya danna horn
Seda ya danna kusan sau uku tukun gate man ɗin yaji
Leƙowa yayi, ya faruk ya sauke glass ya leƙo da kanshi ya ganshi, sannan ya koma da sauri ya
tura gate ɗin ya shiga.
Ba can wajen da aka tana da domin parking ya nufa ba, gaban ƙofar da ze sada ka da cikin
gidan ya tsaya sannan ya kashe motar
kwashe wayoyin shi yayi, sannan ya fito, da kanshi ya buɗe mata ƙofar itama ta fito ya riƙe
hannun ta suka haura har ƙofar palon sannn ya saketa ya buɗe ƙofar tukun yace "bisimillah"
Da ƙafar dama ta shiga haɗe da sallama duk da tasan babu kowa a ciki
Ko wutar palon be kunna ba yaja ta zuwa bedroom
A gaban mirrow ya aje wayoyin shi da mukulin mota sannan ya kunna heater
Waigowa yayi ya ganta tsaye bata zauna ba
A hankali yace "baki gaji ba kenan?"
Zumɓura baki tayi ta zauna a gefen gadon da tunda ta shigo idon ta ke a kanshi
A ranta tace "choice ɗina"
Aircon ɗin ɗakin ya kunna, ya daidaita temperature ɗin ta sannan yace "ke zaki fara shiga ko in
shiga?"
Kallon shi tayi tace "ina?"
Kai tsaye yace "wanka mana, ko haka kike kwanciya bakya wanka" yayi maganar da alamun
tsokana
A fakaice ta murguɗa baki, duk da ya ganta basarwa yayi ya shige toilet
Be wuce minto sha biyar ba ya fito ɗaure da towel, ɗaya a jikin shi ɗaya a hannun shi yana
goge sumar kanshi
Da sauri mumtaz ta kauda kai haɗe da jin bugawar zuciya da ƙarfi
Firt time da ta taɓa ganin ya faruk a haka, tun daga wannan kallo ɗayan bata yarda ta sake na
biyu ba
Yana a gaban mirriow tsaye yace "kije ki watsa kema mu samu mu kwanta kafin asuba tayi"
Gajiyar dake jikin ta yasa ba wani musu ta nufi bayin itama
Sosai tayi wanka da ruwan ɗumi, duk ɗaɗɗaurewar da jikin ta keyi taji ya fara sakewa a hankali
Babban towel ta ɗauka ta ɗaura sannan ta mayar da hijabin ta tukun ta fito
Sanda ta fito shi har ya hau gado ya kashe hasken ɗakin
Hasken dake jikin aircon ke hasko mata shi
Matsowa tayi gaban gadon, a hankali tace "ya faruk babu kayan sawa ne"
Janyota kawai yayi, batayi aune ba taji ta faɗa gadon
A gajiye ya faruk yace "nima haka na kwanta, babu kaya anan"
Shiru tayi ta hau muzurai, can tace "bari na ɗakko wanda na cire na maida to"
Banza yayi da ita, sema ƙokarin cire mata hijabi da yayi ya rufa musu bargo.
Lamo mumtaz tayi tana jin yarda bugun zuciyoyin su suka ƙara sauri akan yarda suke bugawa
Shi kanshi ya faruk da niyar baccin gajiya ya kwanta, amma tunda ya riƙe mumtaz a jikin shi yaji
ya nemi baccin ya rasa.
A hankali yake shafa kanta har bacci-bacci ya fara ɗaukan ta,
Daga ƙarshe dai sabon al'amari ya kankama a wannan dare me ɗinbin tarihi da tsayawa a rai.
ASUBAH TA GARI YA FARUK DA AMARYA MUMTAZ 😎
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg84
Tunda ya samu tayi bacci bayan doguwar rigimar da yasha
Ya tashi yayi wanka ya fuskanci alƙibila yana me nuna godiyar shi a wajen ubangiji.
Har aka kira sallar asuba yana nan zaune, bini bini ya leƙa mumtaz da ke baccin gajiya da
rashin sabo
Haka har aka kira sallar asubah ya canza kaya ya fita zuwa masallaci.
Ya faruk na dawowa sallah ya tashi mumtaz itama
Haka yayi ta fama da ita har ta samu ta kintsa ta gabatar da sallah
A dudduƙe ta haye gado, ba wani ɓata lokaci bacci ya sake awon gaba da ita.
Ya faruk yaso ya ɗan rintsa shima, amma tunowa da yayi akwai sauran ƙura a ƙasa yasa ya
fasa,
Wanka ya sake yi ya shirya, be tashi mumtaz ba ganin yarda baccin ya ke mata daɗi kawai ya
fice.
Kafin yaje asibitin seda ya je gida,
Direct sasan umma babba ya nufa
Kowa yana nan jigum jigum kamar anyi mutuwa a gidan
Ɗakin umma b ya shiga a nan ya iske ƙannen shi, jiki a sanyaye suka hau gaishe shi
Kiran ya maryam yayi gefe,
Yace "umma fa?"
"Tana wajen Abba b"
"okay" kawai yace sannan ya ya ce "Ki shiga part ɗin mama ki duba ɗakin mumtaz ki ɗibo mata
kayan da zata ɗan iya amfani da su" yana maganar yana wani basarwa ganin kallon da ya
maryam ke masa
murmushi tayi tace "to ai mun kai mata kaya tun shekaran jiya da mukayi jere, suna nan mun
jere mata"
A ranshi yace "kash, me yasa ban duba ba"
Basarwa yayi yace "okay tanx"
ya juya ya fice
Yana fita suka saka ihu hale da shewa gaba ɗayan su
yana jin su, murmushi yayi ya gyaɗa kai kawai yayi gaba.
Sasan Abban ya nufa kai tsaye
Yana shiga ya iske umma ƙarama zaune a ƙasa dirshen, idon nan nata ya kaɗa yai jajir
Daga can ciki kuma yana jiyo muryar Abban nasa na tashi sama-sama
Ko kallon umma ƙ beyi ba ya ƙarasa ƙofar haɗe da yin sallama
be wani jima a tsaye ba Abban ya fito da shirin fita a jikin shi, umma babba na biye da shi a
baya
Kanshi a ƙasa ya gaishe da iyayen nashi, sannan yace "umma b me za'a kai hospital ɗin?"
Cike da annushuwa tace "tun wajen 8 aka kai musu komi, nima da na kammala abinda nake
zamu je"
Tunda yaji haka yayi musu sallama ya fice.
Abba babba na fitowa ya iske umma ƙarama zaune
Cikin fushi yace "ohhh bakiji me nace maki ba ko?"
Murya a dishe umma ƙarama tace "dan girman Allah ka tsaya ka saurare ni, wallahi sharrin
zuciya ne da kuma makircin Abbas da junaid"
Abba babba be bari ta ƙarasa ba yasa ƙafa ya tokareta da ƙarfi, zaro mata manyan idanun shi
na gado yayi, ya nuna ta da yatsa yace "fita, ba zan taɓa sauraron ki ba wallahi, kuma ba zan
taɓa hana hukuma aiki a kanki ba mara imani"
Da rarrafe umma ƙarama ta bar sasan riƙe da gefen kafaɗar ta inda Abba ya tokareta.
Ya faruk na fita be tsaya ko ina ba se wani resturant dake gaf da unguwar su
chips and liver sauce ya siya sannan ya ƙarasa gidan
Har lokacin mumtaz bata tashi ba,
Motsin shi ne ma ya farkar da ita, se kuma yunwar dake ƙwaƙular ta
Wanke baki kawai tayi ta hau kan abincin
Seda tayi nak tukun ta ture.
Cike da tsokana ya faruk yace "yau ma babu gaisuwa amaryar faruk?"
Banza tayi da shi ta kauda kanta gefe
Bugun duniyar nan yayi dan ta tanka mashi, amma mumtaz tayi banza, banda aikin
zumɓure-zumɓure babu abinda take.
Wajen sha ɗaya saura yace "tunda kinƙi kula ni bari nazo na fita"
Da sauri mumtaz tace "indai hospital zaka koma zanje"
Shima da sauri yace "a hakan kina ciccin maganin zaki bini?"
Ƙara ɓata rai tayi, badai tace komi ba
Murmushi ya faruk yayi yace "bama inda zaki bini yarinya, nan zaki zaman ki har sena dawo"
Kafin mumtaz tayi magana kira ya shigo wayar ya faruk
Ganin mus'ab ne me kiran yasa ya ɗaga da sauri haɗe da cewa "hope ba wata matsala?"
Daga can ya mus'ab yace "to Abba ƙarami ne ke son bamu matsala, yanzu haka ma shine yasa
na kira ka"
Gyara zama ya faruk yayi haɗe da janyo mumtaz ta dawo jikin shi, sannan yace "Abban ya
farka ne?"
Seda mus'ab ya aje numfashin takaici kafin yace "tun cikin dare ya farka, kuma muke ta fama fa
shi ba"
Gyaɗa kai ya faruk yayi yace "ina hanya yanzu kawai"
Ya aje wayar, gaba ɗaya mood ɗin shi na sauyawa, yasan sarai dama zasu sha fama da Abba
ƙarami akan case ɗin nan
A sanyaye mumtaz tace "Abba ya farka ne?"
"ya farka, sannan yace "shirya ki same ni a mota"
Gaba ɗaya bata wani jin ƙarfi, haka dai ta daure ta shiga ta watsa ruwa.
Har ya faruk ya sauka ƙasa ya tuna da be gaya mata akwai kayan sawa ba ya dawo
Daidai ta fito daga wankan,
walldrop ya buɗe, se ga kayan ta jere
Kallon shi tayi bata san sanda tace "kai yaushe ka ɗakko kayan"?
Murmushi yayi yace "dama suna nan"
Temaka mata yayi ta zaɓi wanda zata saka sannan yace "ina mota kiyi dauri ko in tafi in barki".
Tunda suka doso wajen goggo safiya ke kallon yarda mumtaz ke tafiya tana yatsina fuska
kamar warce ake ma dolen tafiya.
Murmushi kawai tayi haɗe da kauda kai, can ƙasan ranta tace "kamar dan junan su akayi su".
Umma babba, Goggo safiya da aunty ne kawai a wajen, se mama da zuwan su yasa ta fito
palon ta bar wa ƴan mazan ciki.
Cike da ladabi mumtaz ta rissina ta gaishe da umma babba da bakin ta yaƙi rufuwa saboda
fara'a
Cike da kulawa tace "tashi zo ki zauna a nan"
Ba musu ta zauna a inda ta nuna matan sannan ta gaishe da aunty da goggo safiya, tukun ta
gaishe da mama
A ɗan kunyace ya faruk ya gaishe su, sannan yayi ciki shima.
Yana shiga Abba ƙarami yace "yauwa zo nan faruk" ko gaisuwar da ya faruk ke masa be amsa
ba yace "Bana so a sake tada maganar su Abbas, yanzu ƙasim da su mus'ab ke min maganar
zaku shigar da ƙara a kan su,
To ni ban yarda ba, munyi magana da zahra'u(mama) itama tace abar magana, fitar maganar
ba mafita bace a garemu"
Rai ɓace ya faruk yace "Haba Abba ƙ, laifin su ya kai a hukunta su, hukunci me tsananin gaske
ma kuwa, be kamata a ɗaga masu ƙafa ba sam"
Cike da ƙarfin hali Abba ƙarami yace"ku barsu da haƙƙi ma, ko shi kaɗai ya ishe su, amma bana
son attention ɗin ƴan media sam"
Mus'ab da Ahmad na gefe suna haɗiyar zuciya tsabar takaici da baƙin ciki.
Tun jiya Abba babba shikam ya rasa tofa komi,
Tsabar takaicin da yake a cikin zuciyar shi kasa haƙuri yayi seda ya sanarwa da mahaifin su
maganar
Jijjigar da maganar tayi masa ne yasa ya kasa haƙuri shima ya bugo sammako yazo asibitin
Kafin kowa ya ƙaraso har ya gama ganawa da Abba ƙarami da mama ya koma.
Gyara zama Abba babba yayi sannan yace "Kaine ya kulle, ban san me zan ce ba, zalinci dai
an riga da anzalince ka, sannan kuma haƙuri abune me kyau, Allah ya ƙara mana haƙuri da
tsoron sa, Allah kuma ya hanamu cutar da kowa saboda son abun duniya"
Uncle ƙasim cikin ɗacin rai yace "Ai shikenan, bala'in dake a tsakanin su kawai ya ishe su"
Ya faruk kam kasa cewa komi yayi,