LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU

Author :  ZAINAB FALALU Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 25

18K to 21K   out of 73.4K words

ya fito



Sakina na zaune ana mata kitso yace

"ina mumtaz"

fuska a ɗaure tace

"ƙila tana ɗaki"



Kai tsaye ɗakin ya nufa, seda ya ƙwanƙwasa kafin ya shiga



Zaune ya iske ta gaban mudubi comb a hannun ta ga gashin nan buzu-buzu kamar mahukaciya
sabon kamu, ido sharɓe da hawaye

Jin shigowar mutum yasa ta waiga da sauri tana tashi tsaye, ita duk a tunanin ta mamar ce ta
dawo kamar yarda tace



Ganin ya faruk ne yasa ta ja baya ta ɗauki hijabin ta zata saka



Yasan sarai me take wa kuka, sam bata ƙaunar kitso tun tana ƙarama,

Taɓe baki yayi sannan yayi ƙasa da murya yace
"wajen ubanwa kika je ɗazu, me ya fitar dake?"



Firgicin jin tambayar da yayi mata ne yasa ta saki comb ɗin hannun ta, ido a waje tace



"wallahi ba inda naje fa"

Cable ɗin wayar ta da ya gani a kan mudubi ya ɗauka, shima zaro mata nashi manyan idanun
yayi yace



"kin iya rantuwa akan ƙarya ko?, me kika je yi a kasuwa?" ya sake maimaita tambayar yana
ɗaga cable ɗin kamar ze tsula mata



Bata mance da haɗuwar su ta rannan ba, jiki na rawa tace

"wallahi abu naje siya, kuma ban shiga kasuwar ba na dawo"



Ƙara matsowa kusa da ita yayi, kamar ze shaƙeta yace



"ƙarya kike, abun wani kika sata halan zaki je ki ɓatar da shi?"



kasa magana tayi, se girgiza kai kawai tana sake ja da baya, murya na rawa tace wallahi ban
ɗauki abun kowa ba"



Jin muryar mama na kwala kiran sunan ta yasa ya shige toilet ɗin ɗakin da sauri, yana shiga
tana turo ƙofar



Tsaye tayi tana ƙare mata kallo ganin yarda take sharar hawaye wani na korar wani

A mugun fusace tayi kanta da faɗa

"Kitson kike ma wannan kukan mumtaz, saboda baki san darajar mutum be shine kika shanyata
tun ɗazu tana jiran ki?
To wallahi ko kukan jini zakiyi bazamu tafi dake a haka ba kai kamar na mahaukata, ni wlh
dama gashin ze kakkaɓe uban kowa ma ya huta ni kaina na huta da ciwon kan da kike sakani
duk sanda za'ayi miki kitso"



Tsaye mumtaz tayi bata ko motsa ba, ganin mamar tayo kanta ta fice da gudu hada ɗan
haɗawa da ihu



Haka mama tayi ta sababi kamar zata ari maki saboda takaici.



Ya faruk najin fitar su ya fito, ba komai ya sakashi ɓoyewa ba se sanin halin mama da yayi

Tsab zata zargi da wani a bu a ƙasa, shi kuma be shiryawa tambayoyin ta ba



Wayar mumtaz da ya gani akan mirrow ya ɗauka

tas ya bincike wayar ko da zega wani abun, amma bega komi ba, haka ya maida ya ajiye

Can ta ƙofar baya yabi ya fice ba tare da kowa ya lura da shi ba.



Seda mumtaz tasha faska a wajen mama kafin me kitson nan ta gama.



Ya faruk tunda ya shiga ɗaki yake saƙa da warwara,

tun lokacin da ya kama mumtaz da fara ɗauke-ɗauke yake shawara da zuciyar shi, se yau yaji
kwarin zuciya inda yayi alƙawarin zuwa bayan sallah in sun dawo daga umara ze faɗa ma
iyayen nashi dan a tunanin shi shine babban mafita, gwara duk a aurar da su kowa ma ya huta.



SHARE PLS

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
IN SHA ALLAH SE ZUWA BAYAN SALLAH ZAMU ƘARASA

ALLAH YASA MU FARA AZUMIN MU GAMA A SA'A, UBANGIJI YASA MUNA DAGA CIKIN
ƳANTATTUN BAYIN DA ZA'A ƳANTA

YA RABBI YA ZAƁA MAMU SHUWAGABANNI NA ƘWARAI
ALLAH YASA MU CIKA DA KYAU DA IMANI.

LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg-26-27

Ko second goma beyi ba ya ɗauke kanshi yaci gaba da wayar shi kamar be ganta ba.



Mumtaz kam tunda ta ja ta tsaya bata sake motsi ba seda taji maganar khalid daf da ita tukun ta
dawo hayyacin ta

Da mamaki khalid yake tambayar ta

"Are u okay?"



Ko kallon khalid bata tsaya yi ba ta ɗiba tayi ciki, ƙiris ya hana ta kwasa da gudu, tana kaiwa
ƙofar ɗakin su jikin ta na ɗan rawa ta ciro katin ɗakin ta kara a jiki, yana buɗewa tayi wuf ta
shige dan har seda ta ba Amal dake zaune tsoro



Ido a waje Amal tace "Mumtaz ina kika je?"



Banza da ita tayi, cire hijabin jikin ta tayi ta wuce toilet

Gaf da zata shige toilet ɗin Amal ta sake cewa
"Tunda bani da matsayin da zan tambaya ki bani amsa se ki tanaji amsar da zaki ba ya faruk da
su Abba ƙ"

Tana gama faɗin haka ta juya tayi kwanciyar ta mamakin mugayen halin mumtaz na daɗa cin ta
a ciki



Duk da mumtaz ta ɗanji tsoro da Amal ta ambaci su Abba, amma ji tayi zuciyar ta dake sam
tsoron babu shi,

Ƙaramin tsaki taja bayan ta watsar da komi hankalin ta gaba ɗaya ya ɗugunzuma ga agogon
hannun khalid, tunani take na yarda zata raba shi da shi har ta shiga toilet tana saƙe-saƙen ta.



Cikin farin ciki da zumuɗi khalid ya koma masauki, sedai murnar shi ta koma ciki, inda yayi ta
kiran layin Mumtaz amma shiru bata shiga

Ta ɓangaren mumtaz kuwa kashe wayar tayi, dan kar Abba ƙ ko ya faruk su nemeta.




Sam kasa rintsawa ya faruk yayi a cikin wannan dare, da ya tuno fuskar khalid se gaban shi
yayi mummunar faɗuwa

Sam kwanciyar ma gagarar shi tayi ya tashi zaune, duk da sanyi air con dake ɗakin hakan be
hanashi zufa ba

Zazzafan huci ya fesar, cike da kokwanto ya furta

"Allah yasa yarinyar nan bayan ɗauke ɗauke bata bin maza!"



Shi kanshi seda ya runtse ido da ya faɗi kalmar "neman maza" da yace

da sauri kuma ya koma faɗin "a'uzubillahi minashshaiɗanirrajim"

A haka har dare ya raba yana saƙe saƙen abubuwa a ranshi.



******

Hafsa ce ɗaure da towel zaune a gefen gado tana shafa mai, kunnuwan ta gaba ɗaya ta miƙa
wa najwa dake ta fama fallasa mata sirrin dake cikin zuciyar ta akan ya faruk
Seda hafsa tagama jin komi daga bakin najwa tukun tace

"Danƙari, lallai najwa zuciyar ki batai miki adalci ba wallahi, tunda muke dake kin taɓa ji ance ga
budurwar ya faruk?"

Bata jira cewar hafsa ba ta ɗora da

"To wallahi na taɓa jin ance aljanar dare ta aure shi da daɗewa, dan haka ki shafa ma kanki lafia
ki lallaɓa da ɗan sadik ɗin ki, in kuma baki ji ba kyaji da wulaƙancin shi ba ruwana"



Murmushi Najwa tayi ta matso kusa da hafsa da har a fuskar ta zaga gane batayi na'am da
maganar ba tace

"Haba hafsa, ke da zaki bani shawarar yarda zan fara tunkarar shi amma ke ce ma sage ni,
koma dai menene zaki fini sanin abinda yafi so tunda ciki ɗaya kuka fito dashi"



Taɓe baki hafsa tayi kafin tace

"To ko umma data haife shi ba zata iya tantance abinda ya faruk ya fi so ba wallahi, dama dai
mamace ko kuma warcan data ɗakko ma kanta dala ba gammo(tana nufin mumtaz) ƙila ki samu
wani abu da ze amfane ki"



Shiru Najwa tayi tana sauraran hafsa, can Najwa tace

"zan san yarda zanyi dai"



Sake taɓe baki hafsa tayi, taci gaba da shafe+shafen ta



Seda ta gama shiryawa tsaf tukun ta sake cewa

"Yanzu ya zakiyi da sadik da ya mutu a kanki najwa?"



Kai tsaye Najwa tace "haƙuri zeyi"
Bilhaƙƙi da gaskiya hafsat ta fuskanci najwa tace

"Ki bi a hankali najwa, karki fara da bawa sadik haƙuri baki damƙi dahir ba, wallahi tallahi zakizo
kiyi danasani nan gaba"

Tana gama faɗin haka ta ɗauki wayar ta da ƙaramar jakar hannun tace "mu wuce kar mu
makara sallah".




******

Kamar kullum yauma mumtaz wajen ta daban ta zauna, gaba ɗaya ta rasa sukuni ta rasa me ke
mata daɗi a cikin zuciya



Hand bag ɗinta ta buɗe ta zaro wayar ta da tun jiya take a kashe ta kunna

Few seconds ta gama booting, seda ta kalli wayar taga ashe data a kunne ne ma ta kashe
wayar jiya



Kamar jira khalid yake ta kunna wayar, nan calls ɗin shi sukai ta sintiri, mumtaz na kallon kiran
tana ignoring

Sam ta kasa samun courage ɗin amsa shi

Sauka tayi da niyar kashe data, kafin ta kashe message ɗin shi ya fito a saman notification,

"Dan Allah ki amsa mumtaz"

Hakanan ta samu kanta da replying shi "muyi chat, i cn't answer ur call now"



Cikin damuwa khalid ya ce

"kina ina yanzu, ina so in ganki pls".



Da ƙyar da jiɓin goshi mumtaz ta tura mishi live location ɗinta, ko minti shabiyar beyi ba ya
ƙaraso,
Abu na farko da mumtaz ta fara kai idonta kai shine hannun shi,

Ganin babu agogon data ƙwallafa rai akai taji ranta ya ɓaci, ɗan sakin data yi wa fuskar ta ma ta
koma ta ɗaure tamau



Da ƙyar mumtaz ta ɗan fara sakin jiki da shi, suka fara fira sama-sama



Cike da ƙwarewa khalid ya fara kafa gwamnatin soyayyar shi a zuciyar ta.



Sosai khalid ya saki jiki ya fara bata labarin shi

"Ni haifaffen ɗan kano ne, ɗa ɗaya tilo a wajen iyayen shi, babana tun ina secondry aji biyu ya
rasu, ya barmu daga ni se mamina taci gaba da kula dani

a yanzu haka ina aiki da A.S.K textile company"



Da sauri Mumtaz tace "A S.K company fa kace"?



Gyaɗa kanshi yayi kafin yace

"kin san wani a wajen ne?"

Murmushi kawai tayi, bata ce komi ba

A.S.K, textile company na Abba ƙ ne, shine kampani na farko kuma mafi girma a dukkan sauran
kampanonin shi guda takwas, shiyasa tayi mamaki jin a can yake aiki



Jin bata ce komi ba shi ya ɗora da

"Saura ke ranki shi daɗe" ya ƙarashe maganar yana murmshi



kan mumtaz a ƙasa tace

"nima ƴar kano ce, a sharaɗa phase 2, ina a 200lv a jami'ar bayaro ina karantar mass com"
Daga nan tayi shiru taci gaba da wasa da yatsun ta.



Girar shi biyu ya ɗaga haɗe da kallon yatsun ta datake wasa da su yace

"ma sha Allah, sauran abu ɗaya ne banji na"

Ɗan ɗagowa tayi kaɗan, tana sauraren shi

yace "Ni na gaya miki nine tilo, nine ɗan fari nine kuma auta"

The way ya ƙarashe maganar se ya baka dariya

Ilai kuwa seda mumtaz ta ɗan dara, tukun tace

"muna da yawa sosai a gidan mu, but a wajen Abba da mama nice ta uku, ina da yayu maza
guda biyu, se ƙanwa mace ɗaya, mama tace bata wuce 6month ba ta rasu"



Dariya khalid yayi yace 'kawai malama kice min kema autace"

Murmushi kawai mumtaz tayi, tana ɗan waigawa gefe, akwai wani feeling datake ji a jikin ta in
har ana kallon ta

Ɗayan gefen ta sake waigawa caraf suka sake yin ido huɗu da ya faruk dake kallon ta ko
ƙyaftawa babu, fuskar nan tashi a murtuke ba wani alamar sassauci



Da sauri ta waiga ta dena kallon side ɗin da yake

A ɗan tsorace, bama lale ka gane a tsoracen take ba tace

"ehnmm, tun da mun gaisa ka tafi, nima zan tafi ne yanzu"



Da kyau khalid ya kalleta, kafin yace

"ke dawa kukazo ne nake ganin ki ke kaɗai?"



Seda ta miƙe tsaye ta gyara hijabinta tukun tace

"muna da yawa sosai, kusan duka gidan mu"
Ganin tayi gaba da sauri ya sashi bin bayanta,

A ɗan ƙage ta juyo tace

"Kar ka biyoni pls, zamuyi waya kawai"

Sototo khalid ya tsaya ganin yarda mood ɗin ta ya sauya gaba ɗaya

Har ta ɓace wa ganin shi be motsa daga wajen ba.




***Ran ya faruk a ɓace ya ɗaga waya ya kira guy ɗin da yake sawa yana siyen mishi tickets duk
sanda tafiya haka me yawa ta taso



Sallamar shi kawai ya faruk ya amsa, ko ta kan gaisuwar da yake mishi be bi ba ya ɗora da

"sagir dan Allah date ɗin komawa gida nake so a sauya ma wasu daga cikin yaran gida"

Daga can ɓangaren wanda aka kira da sagir yace "to yallaɓai, yaushe za'a maida kuma da wa
da wa?"



Ya faruk yace "in har za'a samu jirgin zuwa anjima ma yayi, zan tura maka sunayen su yanzu"

"okay sir".




*****Mamace kaɗai zaune a masaukin su tana waya da yayan ta(baban sakina) mumtaz tayi
knocking ƙofar



Still wayar na a kunnen mama ta tashi ta buɗe mata ƙofar,

Da sallama mumtaz ta ƙaraso ciki, tana shigowa ta cire hijabi ta haɗa da hular kanta tacire,
agogon ɗakin ta kalla taga shida saura, ɗan tsaki taja ta zame a wajen ta kwanta, dai dai nan
mama ta gama wayar, kallon mumtaz tayi ganin yarda tayi ɗai-ɗai kamar wata mara lafia tace

"Ya dai? garin ko jikin?"
Turo baki gaba tayi kafin tace

"wallahi muguwar ƙishirwa nake ji mama, gashi yau lokacin baya gudu sam"



Kallon agogo mama tayi, tukun tace

"saura kaɗan ai"

Kamar an zunguri mumtaz ta miƙe zaune tace

"Mama Abayar dana ƙwallafa rai zan saka ranar idi ɗazu ina gyaran kayana ina buɗeta naga ta
gefen ta a ƙone"



mama tace "subhanallah, ko dai wajen guga ne aka ƙona?"

Taɓe baki mumtaz tayi tukun tace "Abba nake jira yazo ya ban kuɗi na siya wata kawai"



Cike da kulawa mama tace "ki duba acikin sauran mana ba zaki rasa wacce zaki saka ba ai"



Kafin Mumtaz ta sake magana wayar mama dake gefe ta fara ringing

Kallon screen ɗin wayar mumtaz tayi taga waye, sunan "YARONA" ta gani

Taɓe baki tayi ta waiga sanin ya faruk ne me kiran, ita duk a tunanin ta ze faɗa wa mama ganin
ta da yayi ɗazu tare da khalid



Jin mama tace "To, yau kuma?" da ɗan ƙarfi yasa hankalin ta komawa ga mamar



Can ta sake jin tace "Yau da jibin ai duk ɗaya ne, Allah yasa hakan shi yafi zama alkairi, bari inyi
sauri in gaya musu kuwa"

Daga nan mama ta aje wayar, ta maida kallon ta ga mumtaz datayi saƙe tanajiran jin me mamar
zata ce



unexpected cikin ƴar dariya mamar tace
"Yau me tafiya gida ce yarinya"



Da sauri mumtaz ta sake zama da kyau, ido a ɗan waje tace

"Ban gane ba mama?"



Sanin yarda Mumtaz ke ƙaunar yin sallah a garin makka yasa mama ke danne dariyar ta, dan ta
san sarai za'a kwasota da ita



Ɗan taɓe baki mama tayi tukun tace

"Tashi zakiyi ki samu su Amal da sauran ki faɗa musu yau zaku wuce gida, ku haɗa yanaku
yanaku"



Wani shegen ihu mumtaz ta buga wanda seda mama ta toshe kunnen ta da sauri

Duka hannaye mumtaz ta aza ga ƙirjin ta, ido waje tace

"Na shiga uku mama, waye yayi mana wannan muguwar muguntar dan Allah?"

Bata gama rufe baki ba hawaye suka wanke mata fuska

Kankace me mumtaz ta rushe da kuka me ƙarfi tun daga ƙasan zuciyar ta.



Galala mama tayi tana kallon ta, gaba ɗaya dariyace ta kamata ganin yarda haiƙan take rusa
kuka dan ance zasu tafi gida



Jin kukan na neman wuce gona da iri gashi ba'a gaya ma sauran ba yasa mama faɗin



"ke bana son shashanci, dama zama ne ya kawo ku ƙasar, ai dama dole ku koma"

Cikin kuka mumtaz tace

"Ai ba yau ne ranar tafiyar mu ba mama, kawai dan a ƙuntata mana ne wlh"
Cin serious mama tayi tace "faruk yace mistake aka samu, amma yaune ainihin tafiyar ku ba
washegarin sallah ba, ki tashi ki je ki gaya ma sauran"



Banza mumtaZ tayi da mama taci gaba da rera kukan takaici



Ganin time na tafiya yasa mama tashi da kanta ta saka hijabi ta nufi ɗakunan su Amal da su
hafsa



Dukan su zaka ga rashin jin daɗin maganar a fuskokin su, amma ba yarda suka iya, haka suka
hau shiri a take



Mama da kanta ta tsaya ta haɗa wa mumtaz nata kayan tukun ta koma nata ɗakin



A nan zaune ta iske ta, idanuwan nan sunyi ƙulu-ƙulu sunyi ja

Maman bata ce mata komi ba ta wuce toilet ta ɗauro alwala tukun ta fito

Murya a dishe hawaye na ɗiga mumtaz tace

"yanzu in na koma a wajen wa zan zauna mama?"



Shiru mama tayi tana nazarin maganar

Can tace "ki sauka wajen hajia sumayya(umma ƙarama), muma da anyi sallah in sha Allah da
kwana biyu zamu dawo".



Duk yunwar da mumtaz keji shayi kawai tasha da aka kira sallah,
Sallar ma da ƙyar ta tashi tayi ta, naci kam tayi shi har ta haƙura tayi shiru.



*****goma saura kwata ya faruk ya kira mama yace

"Su fito ga motar da zata fita dasu nan tazo"



Sanda mama ta je ɗakunan su duk sun shirya sunyi wanka sun sauya kaya, mumtaz ce kaɗai
ke ta nunkufurci, tsabar nunkufurcin ko wankan batayi ba ita

Haka mama ta haɗo kawunan su duka, suka fito



Suna fitowa mama taga Ahmad zaune a gaban motar kanshi a ƙasa yana danna wayar shi



Baki sake take kallon shi, rabon data saka shi a idanun ta tun ranar da zasuzo ƙasar nan,

Da mamaki sosai tace

"Wai Ahmad na ƙasar nan dama faruk?"



Kallon mama yayi yace "nima se jiya na ganshi, nasha ma ni kaɗai ne ban ganshi ba"



Hmm, kawai tace ta kawar da kanta daga kallon shi



A dabatance ya faruk ya fakaici idon mama yayi wa Ahmad magana

Abinda be sani ba shine ta ganshi sarai, basarwa kawai tayi

A ciccije Ahmad ya fito ya gaishe da mama

Tunda tace "lafia" bata ɗora ko kallama ɗaya a agaba ba ta juya tana ma su Amal da sauran
magana.



Kallo ɗaya ya fatur yayi wa mumtaz ya ɗauke kai, a ranshi yake cewa

"Tafiyar ce bata so kenan?"

Taɓe baki yayi, seda ya tabbatat da komi ya kammala tukun yace shiga motar



Ƙam ƙam mumtaz ta riƙe mama tana kuka, Hafsa, Amal, bilkisu duk sun shiga mota,

Mumtaz na manne da mama tana mata magana ƙasa-ƙasa cikin kuka, Najwa kuma ta tsaya se
fama iyayi yake wa ya faruk da mamaki ya gama kashewa
Cike da iyayi da sanabe najwa tace

"ya fatur ka dai yanke mana jin daɗi ba shiri" ta gefen ido ya kalle ta bece komi ba

Jin bece komi ɗin ba yasa najwa buɗe baki da shirin faɗo wata maganar, kafin ta kai ga furtawa
ya faruk yace

"Ke shiga mota, bana son rashin kunya"

dai dai mumtaz ta baro jikin mama ta nufo motar akai abun akan idon ta, duk da yarda ranta ke
a mugun ɓace hakan be hanata darawa ba



Sum-sum kamar munafuka najwa ta shige mota tana wani haɗa rai kamar zata kai duka.



Gaf da mumtaz zata shiga motar, ya faruk yayi ƙasa da murya yace

"kici gaba da ballagazancin a can in kin koma, kuma ki jirayi ƙarasowa ta shasha".



A ido mumtaz ke kallon ya faruk da bazaka taɓa cewa ya faɗi wani abun ba

Ganin ta tsaya yasa balaraben direban motar ya ce
"Time na tafiya fa" tukun ta shiga tana jin wani mugun nauyi na daɗa danne zuciyar ta,
musamman akan kalaman da ya faruk ya furta mata a yanzu.



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
SHARE PLS.

LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg 28-29

Har suka shiga jirgi mumtaz nai wa maganar ya faruk fashin baƙi

Da kanta ta tambayi kanta "wai bayan kallon ɓarauniya da yake

7 / 25