Author : ZAINAB FALALU Category : African Stories & Novels
wata CCTV a office ɗin'
ya ɗan jima a wajen mamin kafin yayi mata sallama ya wuce ɗakin shi.
*****wajajen ƙarfe biyu da rabi na dare, ya faruk na kwance sam bacci yaƙi zuwar mishi ya rasa
mafita ga wannan matsalar da ke neman fin ƙarfin su
Yaji ana ƙwanƙwasa ƙofar shi kaɗan kaɗan
Nutsuwa yayi yaji da gaske nan bugawar ake
Seda ya tabbatar da bugawan ake, da sauri ya zira riga haɗe da kallon agogon wayar shi
lokacin da ya gani ne yasa shi jin faɗuwar gaba, haka ya dake ya matsa jikin ƙofar, a dake yace
"waye?"
Daga can akace "MUS'AB".
NAGODE DA CALLS ALLAH YA BAR ZUMUNCI ❤️
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
SHARE PLS.
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg 41-42
Babu inda jikin ya faruk baya rawa jin mugayen maganganun da mus'ab ke bashi labari,
Cikin kuka mus'ab yace "shiyasa na yanke shawarar nisantar su gaba ɗaya, dan muddin ina
kusa da su komi ze iya lalacewa".
Sam ya faruk ya kasa magana, ajiyar zuciya kawai yake saukewa yana tuna yarda uncle Abbas
ke gaggaya mishi magana akan sauya ma su Abba hospital da yayi
Da ƙyar maganar ya faruk ke fita yace yace
"Mus'ab zaka iya tunawa, bayan shi se wa?, baze taɓa zama cewa shi kaɗai ne ke wannan
aika-aikar ba"
Kan mus'ab a ƙasa, yaƙi yarda sam ya ɗago kanshi, ga alamar yana son cewa wani abu, amma
sam yaƙi ya furta
A zuciye ya faruk ya finciko shi, murya a murmurɗe yace "ka gaya min mus'ab, kar kaji
shakkata, se kuma wa ka gani?"
Ƙin cewa komi mus'ab yayi banda haɗiyar zuciya da yake ta faman yi
Sun jima a haka, har wajen asuba tukun mus'ab yace
"Zan tafi, tsayawa ta babbar matsala ce anan ya faruk"
Ya faruk be hana shi ba, sema dafa kafaɗar shi da yayi yace
"Ko shine silar zama ƙarshen numfashi na zan kare ahalin Abba ƙarami in sha Allah"
Mus'ab be seke minti ɗaya a wajen shi ba ya fice.
BAYAN SATI ƊAYA
Sosai jikin mumtaz yayi sauƙi dan suna saka ran sallama a yau ko gobe
A ɗan zaman asibitin da tayi wata soyayya suke zubawa ita da khalid da tuni yayi watsi da
maganar sakina
Ɗari bisa ɗari goggo safiya na goyon bayan hakan, itama ba ƙaramin son haɗin nasu take ba
Zuwan aunties ɗin shi biyu haɗe da shatara na arziki suna zuwa dubata
Wasa wasa, wani lokacin kafin khalid ya wuce asibitin se ya fara zuwa gaishe da mama har
gida tukun yake wucewa can
Mama tayi murna, ko ba komi ta yaba da hankalin shi, balle ma maganar da sukayi da Abba ƙ
akan aurar da su na nan maƙale a ranta, dan ma wannan tsautsayin da ya faru ne akayi shiru
da maganar, yanzu kam ta fara samun kwanciyar hankali.
Tafiyar khalid kenan ya faruk ya tura ƙofar ɗakin ya shiga
Da fara'a sosai goggo safiya ta tarbe shi, haɗe da faɗin
"Oh kana nan faruk? tunda aka sallami iyayen ka mu kuma ka ɗauke mana ƙafa"
Ɗan murmushi ya saki kafin yace "nima banji daɗi bane goggo, amma Alhamdulillah"
Ta gefen ido mumtaz ke kallon shi, tabbas ko be ce baya jin daɗi ba zaka hango hakan, ramar
da yayi ta nuna ƙarara a fuskar shi
Jajanta mishi goggo safiya tayi kafin tace "To ga kayan marmari a miƙo maka?"
Kallon tulin ledojin gaban su yayi yace "wannan shirgin fa"?
Cike da jin daɗi goggo safiya tace
"Hmm kaima dai ka faɗa, yarone mara ƙyashi wallahi, kullum in zezo baya zuwa hannu bibbiyu
se kaga ya riƙo wani abun yazo da shi, Allah dai yasa hat cikin gida ba maƙeƙe bane ba"
Idon ya faruk na kan wayar shi yace "wa kenan goggo?"
Baki buɗe, tace "khalid sunan shi, kuma wallahi baka ga yarda yake kula da mumtaz ba, abin
har birgeni yake"
A hankali ya faruk ke furta sunan khalid, be sake cewa komi ba yaci gaba da danne dannen shi
jin yayi shiru yasa goggo safiya tashi ta ɗauki komi bibbiyu ta aza akan plate ta tafi wanko mishi
Tana fita ya kalli mumtaz data juya baya yace
"Tunda har kin samu damar yin soyayya kina jinya kin warke kenan?, duk da na lura bayan
halayyar ki har rashin gaisuwa ma kin iya"
Bata ce komi ba, bakuma ta gaishe shin ba
Suna a haka goggo safiya ta dawo, kusa da shi ta aje plate ɗin sannan ta kabbara sallar isha'i
Ko kallon plate ɗin beyi ba ya fice daga ɗakin
Direct office ɗin dr jamal ya nufa, ba wani ɓata lokaci ya karɓi takardar sallamar da yasa akayi
ta dole.
Ya jima a cikin mota yana amsa wayar mus'ab kafin ya koma ɗakin
Goggo safiya na ganin shi tace "au nasha ka wuce ne ba ko sallama"
Kujera ya ja ya zauna tukun yace "a'a, nayi waya ne, ku haɗa kaya ku same ni a mota an
sallame ku"
Sakato goggo safiya tayi tana kallon shi bako ƙiftawa, can tace "yo haka ake sallama da dare
tsaka mutum ya gama sadaƙarwa kwana zeyi?"
Murmushi ya faruk yayi kafin yace "To mene abun ɓata rai goggo, ai komin daɗin asibiti gida yafi
shi ko? tunda naga kamar daɗin zama kuke ji" ya ƙarashe maganar yana kallon mumtaz ta
gefen ido
Be jira amsarta ba ya juya ya fice
Aikuwa suna haɗa kaya goggo safiya na mita, wai khalid zezo yaga basa nan
Mumtaz da se yanzu tayi magana tace "Rabu da shi goggo, zan kira shi a waya yanzu ma"
Saboda yawan kayan su seda goggo safiya ta kira masu goge goge suka taya su ɗauka
Suna zuwa wajen da yayi parking ya fito, ɗaya bayan ɗaya yake kallon kayan da suka jido
Beyi wata-wata ba yace wa warda ta tayasu ɗakko kayan "kwashi wannan da wannan ki tafi
dasu"
Nan tayi ta zabga godiya, goggo safiya na gefe tana zuba ƙorafi.
ƙofar baya ya buɗe mata ta shiga, sannan ya zagaya shima ya shiga
Mumtaz na tsaye ita bata shiga ba, sanin waye ya faruk yasa ya zagaya ta shiga gaba
Suna tafe yana ayyana abubuwa da yawa a ranshi, bin diddigin uncle Abbas da yake har yanzu
ya kasa gane komi, gani yake kamar ma incle Abbas ɗin ya gane yana bin diddigin shi
Dai dai wajen shagon da ake seda fura ya tsaya, sanin goggo safiya ta shaƙa da yawa yasa
yace "Bari na karɓo miki fura goggo"
be jira cewar ta ba ya fice a motar ya barsu a cikin raɓa.
Tunda mumtaz ta shiga motar idon ta ya sauka ga zoben azurfar da ya faruk ya aje domin ya
gwadata ya gani se kuma bandir ɗin ƴan dubu dubu guda uku dake gefen zoben
Ba wani dogon tunani mumtaz ta saka hannu ta ɗauke zoben nan, sannan duk a bandir ɗaya ta
zari goma goma a ciki ta saƙe a hijabin ta
Be daɗe ba ya dawo, kallo ɗaya yayi ma wajen ya ga babu, abunda bata sani ba saboda ya
gwada yaga ko ta dena halin ne yasa ya ajiye
Bece komi ba yashiga yaja suka tafi.
Goggo safiya na sauka ya waiga side ɗin mumtaz dake saurin sauka itama, fuska a ɗaure yace
"bani abinda kika ɗauka a nan"!
Duru duru tayi tana wani kauce-kauce, kunya da tsananin nadama na baibayeta
Gani kawai yayi ta sauke kai ƙasa ta fashe da kuka haɗe da ciro zoben da kuma kuɗin
Duk da yarda ranshi ke tafasa ganin yarda tayi yayi mugun ɗaga mishi hankali da kuma
mamaki,
Kasa ce mata komi yyi, da yaga bata da shirin sauka a motar yace "you can go, Allah ya shirye
ki ya kuma rufa miki asiri"
Jin yarda yayi maganar cikin sanyin rai da batayi zato ba yasa ta ɗago fuska da sauri tana
kallon shi
Kashe motar yayi, ya fice ya barta.
Seda ya ɓace wa ganin ta tukun ta fito bayan ta share hawayen ta tas, tayi cikin sasan su inda
take jin hayaniyar mutane sosai.
****Da asuba bayan sun dawo daga massallaci duk suna tsaye a harabar gidan Abba babba
yace
"Inajin zuwa gobe duka yaran su aiko da samarin nasu se asan abun yi ko?"
Amsawa sukayi da "hakane" Tukun suka ɗora da firarrakin su na ƴan'uwa
Sun ɗan jima sosai kafin kowa ya nufi sasan shi.
Uncle Abbas na shiga nashi part ɗin ya iske duka nashi ahalin a dinning suna breakfast
Amir ne ya fara gaishe shi kafin Najwa da Tk
Shima kujera ya ja ya zauna,
Mummy da kanta ta tashi ta fara haɗa mishi tea, tana haɗawa take faɗin
"Yaudai firar nan ta jima"
Seda ya kai mug ɗin bakin shi kafin yace
"Aikam" yana tsaka da cin abincin ya kirayi sunan najwa da ke gaf da barin dining ɗin
Kanta a ƙasa tace "na'am daddy"
Kai tsaye yace "ki sanar ma wanda ke zuwa wajen ki yazo gobe muna son ganin shi"
Duk da tasan da zancen amma hakan be hanata jin faɗuwar gaba ba, jiki a mace tace "to
daddy" haɗe da barin wajen.
Cike da jin daɗi mummy tace
"abun ya taso kenan"
Yace "ya taso fa, in sunyi daidai da ra'ayin mu ba za''a ɗauki wani dogon lokaci ba, kin san
bama saka biki da nisa"
Cike da jin daɗi mummy tace "hakane, Allah ya tabbatar mana da alkairi"
Uncle Abbas na gama cin abinci ya tashi ya nufi palon shi, kasancewar asabar ce ba ranar aiki
bace
Tsum ya Tk ya miƙe shima yabi bayan sa
Uncle Abbas na zama Tk ya shigo ya zauna kusa da uban nashi
Fuska ba alamun rahma Ya Tk yace "Daddy, na kasa gane me kake nufi gaskiya, na gaya maka
nifa ina son yarinyar nan, nace zanyi magana ka hanani da niyar kai zaka nemar min auren ta,
kuma ga ƙishin-ƙishin ɗin da nake ji na daban, nifa gaskiya an saka ni a duhu"
Murmushi uncle Abbas yayi tukun yace "Daɗi na da kai gajen haƙuri, akwai damar da nake jira
ne TK, kuma nafika sanin muhimmancin mumtaz a gareka, just trust ur dad, haƙƙata ta kusan
cimma ruwa soon!!!
Kamar wasu sa'anni haka suka tafa suna kwashewa da dariya.
Mus'ab na gama recording maganar yayi saving, har yayi niyar tura ma ya faruk ya fasa, ya
koma yayi kwanciyar shi haɗe da rufe fuskar shi.
😊
Sorry for the late update, kunsan jiki da jini
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
SHARE PLS.
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg43-44
Da yamma lis, yau baƙi masu zuwa gaisuwar sallah da kuma dubiya duk sun ɗauke ƙafa
Gidan an samu sauki mutane sosai
Mama da goggo safiya na zaune a palon ƙasa suna firar kayan sha tara na arziki da aka kawo
na saka ranar hafsa da bilkisu da kuma najwa
Goggo safiya tace "naji Ƙassim yace yau da daddare za'a kawo na Amal itama"
Mama tace "hakan Abban su ke gaya min kafin ya fita"
Can goggo safiya ta sake cewa "mumtaz fa? ko har yanzu ta kasa tsaida zuciyar ta akan yaron
kirki nan"
Gyara zama mama tayi kafin tace "a dai gaban ki jiya muka titsiyeta ya safiya, na kasa gane
kan yarinyar nan sam, ɗazu da safe da na sake mata magana ma fashe min da kuka tayi,
Na rasa yarda zanyi ni kam"
Da mamaki goggo safiya ta sake cewa "kuma fa naga kamar tana son yaron, nikam wallahi na
yaba da hankalin shi sosai, duk yafi min samarin sauran kamala da nutsuwa"
Ta waiga wajen da mumtaz ɗin ke zaune ɗazu taga bata nan
Altine ta yafito tace "shiga kira min mumtaz"
Altine na shiga ɗakin ta iske mumtaz tsaye gaban mudubi tana saka kwalli
Ta cikin mudubin take kallon ta, fuska a ɗaure tace "lafia?"
"ana kira" kawai tace ta juya
A fili mumtaz tace "munafuka kwanan ki sun kusa ƙarewa a cikin gidan nan, ki gama raɓe-raɓen
ki"
Seda ta gama tas abunda take tukun ta fito
Wannan karon harda umma ƙarama a palon
Kusa da mama ta zauna haɗe da faɗin "gani hajiya mama"
Yarda tayi maganar ya basu dariya, a da mumtaz akwai iya shege sosai, amma tunda ɗabi'ar
sarface-sarface ta kamata ta sauya gaba ɗaya.
Dundu mama ta sakar mata kafin tace "seda kika gama shanya mutane tukun zaki fito?
Ya safiya ke kiran ki bani ba" ta juya sukaci gaba da magana da umma ƙarama
Goggo safiya tace "shiru mumtaz banji kince komi ba, bana so kizo kina danasani daga baya"
Shiru tayi bata ce komi ba, umma ƙarama tayi tsulum tace "Ya safayi shifa yaro ba'a mishi dole,
in bata son wancan ta kawo wanda yafi kwanta mata mana"
Taɓe baki mama tayi, badai ta saka musu baki ba
Goggo safiya tace "haka maganar ki take sumayya, ni nagartar yaron kawai nake hangowa
wallahi"
Umma ƙ ta kalli mumtaz cike da kulawa tace " a cikin samarin naki wanne kk so tunda kamar
baki gama aminta da shi khalid ɗin ba"?
Kafin mumtaz tayi magana mama tace "ba se in akwai wasun ba, da bakin ta take korar su,
nasha zaunar da ita ina nuna mata illar hakan amma yarinyar nan ta maidani wata gani can dai,
to ga ranar maganata nan"
Zumɓura baki mumtaz tayi, duk maganganun su sun isheta,
Ga khalid ya jima da zuwa yana jiran ta, gashi su kuma sun titsiyeta a nan.
Suna tsaka da surutun su megadi ya ƙwaɗa sallama a ƙofar palon
Altine ce ta leƙa, ya faɗi saƙon ya juya
Tana komawa ciki tace "Tunɗazu baƙon na jiran ki wai mumtaz"
Salati goggo safiya ta saki haɗe da riƙe baki "yanzu fisabilillahi ajiye shi kikayi yana jira? to
gaskiya baki kyauta ba tashi kije"
Daman maganar su ta ishe ta,
Da sauri tayi waje ta barsu da binta da kallo.
Khalid na zaune a mota yaga fitowar ta,
Ajiyar zuciya me sanyi ya sauke ganin ta fito fuskar ta a sake ba kamar jiya da yazo ba
Da sauri ya fito ya tako zuwa wajen ta
Fuska a washe yace "barka da fitowar sarauniyar kyawawa"
Murmushin ta me kyau ta saki tana sunkuyar da kanta ƙatsa
"muje ciki" tace, tana gaba yana binta a baya har palon baƙi.
Da ƙyar da jiɓin goshi a ranar mumtaz ta yarje wa khalid turo manyan shi kamar yarda ya jima
da nacin tambaya"
Tsabar murnar maganar data yi yasa shi tashi ya fara juyi yana rawa yana mata waƙar "ta kusa
zama tawa, ta kusa zama tawa"
Ganin murnar da yake yasa yasata jin nutsuwa sosai a cikin ranta
Tun tana ɓoye fuska tana dariya har ta dena ta koma yin ta a fili,
Tsabar murna duk abinda aka jera mishi beci ba, time ɗin tafiyar shi ma beyi ba yayi mata
sallama ya tafi cikin zumuɗi da zakwaɗin sanar wa mami.
Tana komawa ciki kusan a tare sukace "har ya tafi?"
Mama tayi caraf tace "ko kuma ta koreshi ba"
Goggo safiya tace "Daɗina dake wani lokacin baki faɗin alkairi zahra'u,"
Murmushi mama tayi taci gaba da danna wayar hannun ta.
Mumtaz ko a jikin ta, seda ta shiga ɗaki ta ciro hijabin jikin ta tukun ta dawo palon, kusa da
goggo safiya ta koma ta zauna
Ƙince ma kowa komi tayi, seda ta mula ta mulmule tukun tace
"wallahi ji nake a raina dama ban amsa mishi ba"
Ta gefen ido mama ke kallon ta, ba dai tace komi ba dan kar tayi tunanin ta matsu taji
Goggo safiya ce ta gyara zama tukun tace "bana son iskanci mumtaz, duk kin bi kin saka mu a
duhu, shin kin ce ya turo ne koko wani taɗin kike yi na daban?"
Tura baki tayi gaba kafin tace "ai shine nace nayi danasanin cewa na yarda ya turo ɗin"
Kusan a tare umma ƙarama da goggo safiya suka saki wata narkekiyar guɗa wanda seda yasa
Altine dake baya shigowa da sauri
Mama kam ajiye wayar hannun ta tayi, haka kurun taji gaban ta na faɗuwa ba gaira ba dalili.
Tsabar haushi mumtaz barin wajen tayi
Kallon yarda mama ke binsu da ido goggo safiya tayi
Cike da murna tace "naga kamar kina wani basarwa zahra'u"
Kafin mama tace komi umma babba ta shigo itama, duk dan saboda yaya safiyar suke yawan
shiga sasan maman, duk da umma babba bada son ranta hakan ke kasancewa ba
Waje ta samu ta zauna, fuska ba yabo ba fallasa ta gaishe da yaya safiyar, sauran ko sannun
ku tace
Jin ana kamar magana me muhimmanci ne yasa taƙi tashi ta tafi
Kowa yasan bata jimawa in tazo, amma yau suka ga saɓanin hakan
Murna nata cin goggo safiya, bata so ci gaba da murnar a gaban umma b ba
Haka nan ta basar ta kalli mama data ci gaba da danna wayar ta tace "Kin dai gani in baki buɗe
ido kin tsaya ma ƴarki ba to ke kika sani, yarinyar da ba ƴar fari bace balle ace zaka ɗanyi
kawaicin wani abun, wasu ma da zasu aurar da na farin basuyi kawaici ba sam"
Kowa yasan da umma b take, dan tana maganar tana kallonta ta wutsiyar ido
Dan haka ki saki zuciyar ki kinuna ma ubangiji godiyar ki.
Umma ƙarama ta amshe da "gaskiyar ki kuwa yaya safiya, Allah dai ya tabbatar mana da
alkairin sa"
Cike da shewa goggo safiya ta taɓa umma ƙ tace "na taɓa ki da alkairi mutuniyar kirki"
Sosai umma babba ta ƙunsa, rai a ɓace ta miƙe tayi hanyar fita
Har ta saka ƙafarta waje ta waigo tace "Duk wanda yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake,
kuma wallahi ya safiya ki kama girman ki tun wuri"
tana gama faɗan haka ta fice fuuuu kamar zata tashi sama.
Umma babba na fita mama tace "kayya ya safiya ni kam bana son irin haka sam wlh"
Banka mata harara tayi, tukun ta waiga saitin umma ƙarama tace "Bazata taɓa sauya ba ita,
daga faɗin gaskiya kinga zata fara jero wa'azin nan nata "
Murmushi umma ƙ tayi kafin tace "zaman lafia yafi komi daɗi ai ya safiya"
Basar da su tayi taci gaba da murnar ta, harda faɗin "tafiya kam ba yanzu ba, se baba ya gani".
******Bayan isha, duka iyayen na nan suka tarbi masu kawo kayan Amal, aka tarbe su kamar
yarda aka tarbi sauran, sosai aka daddara kafin suyi sallama suka tafi.
Ta ɓangaren khalid kuwa yana barin wajen mumtaz gida ya nufa, duk da yasan mami bata nan,
hakan be yana shi komawa gida ba, gaba ɗaya yama rasa me zeyi
Waya ya ciro ya danna mata kira, amma har ta tsinke bata ɗaga ba
Maida kiran yayi ga kiran ƙanwar mamin, da ya sanar mata itama tayi murna sosai, a zumuɗin
ta har ta fara mishi lissafe-lissafen abinda za'ayi.
A daidai lokacin da call ɗin khalid ya shiga wayar mami tana