LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU

Author :  ZAINAB FALALU Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 25

3K to 6K   out of 73.4K words

in maida ki gida a mota ta" yayi maganar yana nuna inda yayi parcking
motar shi da hannu.




Ko tsayawa me keken ya ƙarasa jin zancen beyi ba yayi gaba abun shi.




Seda ya ɓace ma ganin mumtaz tukun ta waigo da fuskar ta inda saurayin ke tsaye yana kallon
ta tun daga sama har ƙasa



Tana juyowa idanun ta suka sauka a cikin nashi,
Da sauri ta sauke kanta ƙasa tana wasa da hannun jakar ta dake cikin hijabi



Murmushi ya sakar mata,
Cike da ƙwarewa a magana yace



"im khalid, and u?"



Kanta a ƙasa kamar ba zata ce komi ba,

Har ya fitar da ran jin wani abu daga gare ta, can dai tace

"MUMTAZ"



can ƙasan numfashin shi ya maimaita "mumtaz"
Murmushi sosai ya sakar mata a wannan karon, sannan yace

"unique name"



murmushi itama tayi sannan tace "nagode".



Tana gama faɗin nagoden tayi gaba



Da sauri khalid ya bita a baya yace



"Ah ya zaki tafi kuma ki barni bayan bamu gama magana ba?"

Be jira cewar ta ba ya sake cewa

"ina ma zaki je tukunna?"



Yana mata wannan tambayar ta tsaya cak gaban na dukan uku-uku, sarai zaka ga hakan ga
fuskar ta



Kafe ta da kallon ƙurilla yayi yana jiran jin me zata ce



Ganin bata da niyar cewa komi yasa yace



"tunda ba zaki faɗa min ba, muje to na rakaki"



Da sauri Mumtaz tace



"na fasa, gida zan koma"



Shiru khalid ya sake yi yana kallon ta
Can yace

"Muje na sauke ki to"



Da sauri ta girgiza kanta tana yin gaba da sauri



Haka khalid yayi ta binta yana roƙonta akan ta tsaya ya sauke ta amma firr mumtaz ta ƙi yarda



Badan yaso ba ya sake tsaida mata ɗan keke



Yana ji yana gani ta tafi, ko arzikin number wayar ta be samu ba.




****Duk a tunanin mama mumtaz sun dawo tana ɗakin su,



Yau da yake a general kitchen za'ayi abincin buɗa baki yasa tun da akayi sallar azzahar matan
gidan suka hallara a babban kitchen ɗin dake ta can ƙarshen makeken gidan dake ɗauke da
ahalin gaba ɗaya



ko wacce mace da ƴan aikin ta, se ɗaiɗai ku na daga cikin ƴaƴan gidan da suke ɗan taɓa wani
abun a wajen.




Cike da haɗin kai suke aiyukan su,

Yawanci duka matan suna zazzaune akan kujeru suna basu order abubuwan da za'ayi



Sun jima suna aikace-aikacen su suna taɓa fira sama-sama

Ganin duka yaran gidan sun fito waje, mama ta kalla taga mumtaz ce kawai babu

Atine ta ƙwala ma kira daga can in da suke
Da sauri atine ta tawo tana amsawa



Kallon ta mama tayi tace

"Je ki taso min mumtaz, bacci ya isa haka"



Da "to" atine ta amasa tukun ta wuce part ɗin maman kai tsaye



Mumtaz na cire hijabi atine tayi sallama a ɗakin



Da sauri mumtaz ta waiga tana kallon ta,

Seda ta sauke ajiyar zuciya, duk a tunanin ta mama ce, tukun tace



"ya akayi ne?"



Atine tace

"mama na kira" ta juya ta fita.




Seda Mumtaz ta adana waɗan nan agogunan sannan ta gabatar da salla tukun ta fito zuwa
kiran maman.



A hanya kafin ta ƙarasa kitchen ɗin suka yi kiciɓus da yaya faruƙ da ya kafe ta da kallo tun
fitowar ta daga part ɗin su



Ita sam bata lura da shi ba seda ta kawo daf da shi



Fuska a ɗaure bayan ta kawar da kai gefe tace a taƙaice
"ina wuni"



Be bi ta kan gaisuwar ta ba yace



"After asham kizo ki same ni a ɗaki"



Ko kallon ta be kuma yi ba ya wuce abun shi.



Jin kalmar ta same shi a ɗaki ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, sosai tsoro da fargaba
suka kamata



Murya ƙasa-ƙasa tace

"ko dai ya duba bega agogunan shi bane ni mumtaz"?



Ta jima tsaye a wajen tana saƙa da warwara, can dai ta yanke hukuncin ƙin zuwa kamar yarda
ya umarce ta.



Ƙarasawa tayi inda su mama suke a ka ci gaba da aikin da ita.




Wajen biyar da rabi na yamma suka kammala, su Mumtaz, Najwa, Bilkisu da Hafsat ke ta
kwasan manyan kulolin suna kaiwa kan babban dinnig ɗin gidan suna jejjerawa,

inda lokaci zuwa lokaci ake haɗuwa duka iyalan aci abinci



Seda suka gama tas, tukun kowa ya koma part ɗin shi domin yin wanka kafin kiran sallah.



SHARE PLS.

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

p4

Ahalin gidan gaba ɗaya kowa da kowa ya hallara a babban ɗakin cin abincin da yake
musamman sabida lokuta irin haka dama



Cikin nutsuwa kowa ke cin abinci, baka jin motsin komi sai cokula, se kuma waya da wasu daga
cikin ƴan mazan dake amsawa lokaci zuwa lokaci.




Ba wani abincin kirki Mumtaz taci ba,

Ƙaramin bowl ta ɗauka ta zuba pepper soup ɗin cat fish ɗan madedeci ta fakaici idanun kowa
tukun ta fece zuwa part ɗin su, duk dan gudun kar su ƙara arangama da ya faruƙ

Bata san yana lura da duk wani motsin ta ba, duk da a zahiri zaka ce besan da wanzuwar ta ba
a wajen, amma kar yake kallon ta.



Tana fitowa ta sauke ajiyar zuciya, a bayyane tace



"Na sha a wannan karon, sallar ma a ɗaki zanyi ta tunda ba'ace dolen dolen mutum se yayi ta a
cikin jam'i ba"

Ta ƙarashe maganar haɗe da murguɗa baki.
Ɗan karkatawa Abba ƙarami yayi saitin kunnen mama yace



"Wani abun kika daka Mumtaz halan?"



Saitin ƙofa mama ta kalla sannan tace



"Ba abunda na saka ta, ƙila ta ƙoshi ne, kasan bata fiya zama taci abinci kamar yarda kowa keyi
ba"



Abba ƙarami ba sake cewa komi ba, sema ɗan yatsina fuska da yayi yana streaching wuyan shi
da kwana biyu yake ɗan sagewa, kamar irin be kwanta da kyau ɗin nan ba.




Ya faruƙ ne ya fara tashi,
Sannan ɗaya bayan ɗaya ƴan samarin suka fara watsewa daga teburin cin abincin suna ficewa,



Cike da isa Umma babba tace

"Hafsa, ku tashi ku kwashe plates ɗin nan, uwayen son jiki" Ta ƙarashe maganar tana miƙewa
haɗe da kara wayar ta dake ringing ga kunne




Tas su Najwa suka gyara wajen kamar yarda suka shirya shi a ɗazu, kowa da abinda ya ɗauka
yake yi, banda Hafsa dake ƙorafin bata ga Mumtaz ba, ai ba su kaɗai ya dace su rinƙa aikin ba



Da yake ƙasa-ƙasa take ƙorafin ta yasa Umma babba bata jiyo ta ba, dan ita ta mammake
mutum ba wahala yake mata ba



Macece me son iyawa da kuma kamewa, bata ɗaukar raini balle shashanci, kuma bata fiya
shiga sabgar mutane ba, in abu be shafe ta ba da wahala kuga ta saka baki, amma tana da
mugun kishin zamantakewa, se ka zauna da ita sosai zaka fahimci hakan.
Mama, aunty, umma ƙarama da mummy suma suka kama gaban su, kafin lokacin sallar isha
yayi, ko wacce tayi part ɗin ta suka bar iyayen maza kawai a babban palon da tun bayan gama
cin abincin suka koma cikin palon.




Cike da kulawa Abba babba ya kalli Abba ƙarami yace



"Ina lura da yanayin ka se streaching baya kake, badai ciwon bayan bane ya dawo?"



Murmushi Abba ƙarami yayi, yana lumshe idanun shi dake nuna tsabar gajiya tukun yace



"Ɗazun nan na fara jin alamun shi dai, amma ina tunanin gajiya ce, in nayi bacci zan warware in
sha Allah"

Da "Amin suka amsa dukan su



Seda suka gabatar da sallar isha'i suka ɗora da asham kafin kowa ya kama gaban shi.




Tunda ya faruƙ ya shiga ɗaki yaƙi cire riga saboda yana jiran Mumtaz



Ɗabi'ar shi ce sam baya son zama da riga, komin sanyi kuwa



Haka ya zauna tun yana kallon agogo har ya gaji da jiran ta

Se a lokacin ya fara recalling befa ganta a wajen salla ba



Ƙwata yaja tukun ya tashi ya cire rigar shi,

List ɗin da Abba ƙarami ya bashi ɗazu ya janyo ya hau duddubawa yana fitar da wanda ya
dace ya fitar ya bar wanda ya dace ya bari,
Ba shine ya gama ba, se wajen sha biyu saura, tukun ya kishingiɗa.




Tun da mama ta koma part ɗinta ta hau Mumtaz da faɗan rashin fitar ta salla da kuma tashi
data yi bata tsaya an gyara wajen cin abincin da ita ba




Marairaice murya Mumtaz tayi sannan tace



"kaina ne ke fa ciwo shiyasa ban fita ba mama"



Taɓe baki mama tayi, tace

"Da dai ban san halin ki ba, in bakiyi sharar masallaci ba ai kya yi ta kasuwa" ta juya tayi
ficewar zuwa palon Abbah ƙarami da shima shigowar shi kenan.




Direct kitchen ɗin palon ta nufa, butar shayi ta ɗora akan gas bayan ta zuba kayan ƙamshi da
ruwa

Seda ya dahu tukun ta juye a ƙaramin flask golden colour tukun ta ɗora a tray ɗan madedeci
bayan ta ɗora ƙananun cups biyu da kuma glass ɗin sugar akai, tukun ta fice zuwa palon Abba
ƙarami



Zaune yake ya kafa kai da gwiwa mama ta shiga, tana ganin a yanayin da yake seda gaban ta
ya faɗi

Jiki a sanyaye ta ƙarasa ciki, ajiye tray ɗin hannun ta tayi sannan ta zauna a kusa da shi

Jiki a sanyaye ta ɗora hannun ta a kafaɗar shi, bata ce komi ba se ɗan shafa bayan shi data ke
alamar rarrashi.




A jejjere Abba ƙarami ke sauke ajiyar zuciya, sun ɗan jima a haka kafin ya ɗago idanun shi da
suka yi jajir



Kafin yace komi mama ta rigashi faɗin



"Dukkan tsanani yana tare da sauƙi yallaɓai, tunda har warcan shawarar da na baka ba zatayi
aiki ba, dole mu rungumi haƙuri sannan mu ƙara ƙaimi wajen kaima Allah kukan mu, shine
yasan abunda muka sani da wanda bamu sani ba"



Murya a sanyaye Abbah ƙarami yace



"Maganar ki haka take, amma can ƙasan raina ina jin wani mugun yanayin da ke ƙoƙarin taɓa
min zuciya, faɗuwar gaban da nake ji sam bata barina na aiwatar da komi cikin salama, amma
ba komi ƙila dalilin hawan jinin nan ne yasa nake jin hakan" ya ƙarasa maganar yana ƙirƙirar
murmushi.



A hankali mama tace

"shima ze iya sawa"



Flask ɗin shayin ta janyo ta zuba mishi.




Suna a haka Ahmad da mus'ab suka shigo a tare bakin su ɗauke da sallama



Akan laɓɓa Abba ƙarami ya amsa musu yana jiran yaji me kuma suka zo da shi.



"Mus'ab ne ya fara magana cikin inda inda



"Abbah, dama akan maganar tafiya umarar ne, mun gama shiryawa ni da Ahmad gobe da
yamma zamu wuce"



Mama na gefe ta zuba musu idanu da mamaki sosai a fuskar ta
Abba kuwa murmushin da yafi kuka ciwo yayi, yasan ze iya jin abunda yafi wannan ba daga
bakin su, wannan zuwan ma da suka yi yasan ba da son ransu suka zo ba



Duk da haka a matsayin shi na uba be kamata yayi musu shiru ba akan muguwar ɗabi'ar rashin
shawarar da sam basayi da shi ko da mahaifiyar su ba



Gyaran murya Abba ƙarami yayi yana ajiye mug ɗin hannun shi a kan table ɗin gaban shi



Ɗaya bayan ɗaya yake kallon Ahmad da mus'ab da ke zaune kansu a ƙasa

Ɓacin ranshi keson fitowa fili, amma ya danne ya kalle su ya ce



"Yanzu kun kyauta akan wannn halin naku?" be jira cewar su ba ya ɗora da



"A matsayina na mahaifin ku ai naci arizikin a sanar dani kafin ku aiwatar da komi zakuyi,
dukkan ku ina lura da sabbin halayen da kuka tsiro da su,

So har kunyi arzikin da zaku iya biyan ummara, kuma har kk biya se zaku tafi muke da arzikin ji
ko?"



Kansu a ƙasa suka haɗa baki wajen faɗin

"a'a Abbah"

Murmushi ya sake yi sannan yace

"Yanzu nayi asarar kuɗin da na biya harda ku kenan?"



caraf mus'ab yace

"zaka iya sawa ayi refunding maka ai Abbah, mu mun riga da mun gama shiri"



Shiru yayi ganin mama na gaf da fashewa da kuka a gaban su yasa Abbah ƙarami saurin faɗin
"ku tashi kuje, Allah ya kaiku lafia"



Kamar wa ɗanda suke kan ƙaya haka suka tashi har suna gwaren fita.



Aikuwa suna fita hawayen mama suka ɓalle, sam ta kasa riƙe su tsabar yarda zuciyar ta ke
mata zafi



Abba bece komi ba, ya kamota ya rungume ta tsam a jikin shi yana shafa bayan ta alamar
rarrashi.



SHARE PLS

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
WALLAHI YAWAN SHARHIN KU YAWAN SAMUN UPDATE AKAI-AKAI 😎
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg5

Seda yaji mama na sauke ajiyar zuciya akai-akai tukun ya buɗe baki a hankali kuma cike da
rarrashi yace
"Kiyi haƙuri ina a kan umarnin hajiya ne, abu ɗaya na sani shine komi yana da lokaci"



Kasa cewa komi mama tayi, sema ɗan zamewa data yi anan kan kujerar ta kwanta haɗe da
lumshe idanun ta.

shayin da Abba ƙ be ƙarashe sha ba kenan, shiru yayi yana ci gaba da tunane tunanen da suka
aure shi tun shekarun baya.




WASHE GARI

Abba ƙ na zaune a ɗan madedecin palon shi na sama inda ba kowa ke shigar shi ba



Hankalin shi da na mama ya tafi ga tafsirin da akeyi a sunnah tv,

Baka jin motsin komi sena tv, se kuma air con da take aiki



Kusan 1hr suna sauraron tafsirin kafin a gama



Sama-sama suke ɗan taɓa hira, can Abba ƙ yace



"Miƙo min warcan yawar"



Tashi mama tayi ta ɗakko mishi duka wayoyin a inda ya aje ta kawo mishi



Yana karɓa kai tsaye dialing no ɗin ya faruk yayi.




Fitowar ya faruk daga wanka kenan yaji ringing ɗin wayar shi

Ganin sunan Abba ƙ a kan screen ɗin wayar yana yawo yasa yayi saurin ɗagawa ya kara a
kunne haɗe da sallama
Abba ƙ najin ya ɗaga yace

"In baka komi kazo ka same ni a palona"



Cike da girmamawa ya faruk yace

"To Abba"



Yanayin zafin da ake tsugawa yasa ko mai be shafa ba,

roll on kawai ya shafa se body spray, tukun ya saka kayan shi ya fice zuwa kiran da Abba ƙ yayi
mishi




Tunda ya fito daga ɓangaren su na samarin gidan Hafsata ta hangoshi ta windown ɗakin mama



Kamar zata kifa wajen saurin juya tace

"Umma, zo ki gani"



Fuska a ɗaure Umma babba tace

"me zan gani?"

Da sauri hafsat ta sake cewa "ze shige wallahi"




Da ɗan sauri umma babba ta ƙaraso jikin windown itama, akan idon ta ya faruk ya ƙarashe
shigewa part ɗin Abba ƙ



Ƙwata tayi ta koma ta zauna, fuskar ta ba yabo ba fallasa tace

"Bani waya ta hafsat"
Juyawa hafsat tayi ta ɗakko mata wayar, har ta miƙa mata ta tsaya tace



"karki kira shi umma"



Kallon ta umma Babba tayi tukun tace

"wa kenan?



Dariya Hafsat tayi, wani lokacin halin umma babba mamaki yake bata, wani lokacin kuma dariya



Kafe tan da ido da umma b tayi yasa tace



"na sha ya faruk zaki kira ai"



Tsaki umma b tayi taci gaba da danna wayar hannun ta.




Mumtaz na kwance taƙi tashi tayi komi wai azumin yau na bata wahala taji sallamar ya faruk



A guje Mumtaz ta miƙe tayi hanyar ɗakin su, sam ta mance da yunwar data ce tana ji



Tana shiga ta banko ƙofar da ƙarfi ta murɗa key tana maida numfashi da ƙyar



Gaba ɗaya seda hankalin su sakina ya dawo kanta, har altine dake kitchen seda ta leƙo jin
ƙarar ƙofar da aka buga




Karkaɗa kai ya faruk yayi, can ƙasan zuciyar shi yace



"Zanyi maganin ki, da gangan kenan kika ƙi zuwa kiran da nayi miki"
Sama-sama ya amsa gaisuwar su sakina, tukun ya nufi stairs ɗin da ze sada shi da palon Abba
ƙ.




Ya jima sosai a wajen Abba ƙ kafin ya sakko, da ka ganshi kasan ranshi a mugun ɓace yake,
amma in bakai mishi farin saniba ba lale ka fahimci hakan ba.



yana shiga ɗaki ko zama beyi ba, wayar shi ya ɗauka da niyar kiran Ahmad

Missed calls ɗin Umma b ya gani kusan biyar,

Saka wayar yayi a aljihu ya juya ya sake fita zuwa part ɗin Umma b.



Har bedroom ɗinta ya same ta, tana zaune riƙe da carbi a hannun ta tana ja yayi sallama ya
shiga



Zama yayi kan kujerar dake kallon gadon ta, Hafsat na zaune akan 1 seater dake kusa da
window tana duba handout ɗinta, kai kace gaba ɗaya hankalin ta na ga handout ɗin, da yake ya
faruk yasan halinta sarai, kuma yasan umma b babu ruwan ta duk maganar data ga damar faɗa
zata faɗeta koda kuwa a gaban ƙannen shi ne



Fuska a ɗaure yace



"Tashi kiba mutane waje"



Tasan sarai da ita yake,
Da sauri ta hau tattare takardun ta tanayi tana zumɓure-zumɓure ta fice a ɗakin




Seda yaga ta fita tukun yace

"Umma gani"
Juyawa tayi ta ajiye carbin hannunta ta fuskance shi da kyau,
Seda tayi gyaran murya tukun tace



"Tun last week nake jiran naga saƙon da kace amma shiru, banji daga gare ka ba"



Murmushi ya faruk yayi, a ranshi yana faɗin

"Taga shiga ta part ɗin Abba ƙ kenan"



Kafin yayi magana ta ɗora da



"Ni ba shiru na kira ka kayi min ba faruk, ko manzon Allah (SAW) yace uwa tana gaba da kowa"



Cike da kulawa ya faruk yace

"Haka maganar ki take umma, ban mnta da saƙon ba, zuwa anjima nake sa ran za'a kawo se a
fitar ma da kowa na shi dana mutanen shi"



Taɓe baki umma b tayi, kamar ba zata ce ƙara cewa komi ba, can dai tace



"In dai kana son ganin farin ciki na, to tabbas a fara girmama ni kafin waɗan da ke wahalar da
kai da sunan nuna kulawa"



Shiru ya faruk yayi ya sunkuyar da kan shi ƙasa, yana jin maganar da umma b keyi wani iri

Seda ta kai ƙarshen maganar ta tukun yace



"Toh, mu kasance masu yawan kyautata zato umma"



Da mamaki umma b tace

"Fassara abinda kk nufi faruk"
Murmushi ya sake yi, sannan yace

"Umma kenan, bari inje kar in rasa jam'i"



Kafin ta sake magana ya fice daga ɗakin ranshi a jagule.



Aljihun shi ya laluba yaji ko da key ɗin motar shi a jiki

Tsaki yaja jin be jishi ɗin ba, part ɗin su ya koma domin ya ɗakko, yana shiga su mus'ab na
ƙoƙarin fita,



Kauda kai gefe mus'ab yayi yace

"barka da rana ya faruk"



Ko kallon shi beyi ba, har ya tura ƙofar ɗakin shi ze shiga ya waiwayo yace



"Ku kawo min passport ɗinku kai da Ahmad yanzun nan".

Ya ƙarashe shigewa ɗakin.



Ya faruk na shigewa suka kalli juna shi da Ahmad



Murya ƙasa-ƙasa mus'ab yace



"mu gudu wallahi"

Tsaki Ahmad yayi yace

"Ba inda zamu, mu kai mishi ya gani, nasan in yaga yaune tafiyar ze bamu kayan mu"



Shiga ɗakunan su suka yi suka ɗakko passport ɗin su,
Mus'ab na fitowa ya miƙa wa Ahmad na shi yace

"ka kai ni bazan shiga ba"

Ansa yayi ya haɗa da nashi, knocking ƙofar ɗakin yayi

Seda ya bashi izini tukun ya shiga



Tsaye yayi bayan ya miƙa mishi passport ɗin yana jira ya gama dubawa ya bashi



Duk da ya faruk yasan me Ahmad ke jira hakan be hana shi faɗin



"Tsayuwar me kake yi kuma?"



Ido waje Ahmad yace

"ya faruk baka date ɗin bane?"



Kan gado ya wurga

2 / 25