Author : ZAINAB FALALU Category : African Stories & Novels
ba adadi
Kallon wayar sukayi dukkan su, sannan ya faruk yace "calls ɗin su ya fi ɗari uku daga shekaran
jiya zuwa yanzu"
Cike da ɓacin rai uncle Ƙasim yace "ba amfanin hakan, so nake kawai yanzu ku tashi muje
gidan ayi wacce za'ayi kawai"
Karkaɗa kai ya faruk yayi sannan yace, "akwai abinda ban ƙarasa ba, kuma yanzu zan
kammala shi kafin mu dangane da gidan"
Shiru kawai uncle ƙasim yayi, dan abun yafi ƙarfin kanshi gaba ɗaya.
Juyawa saitin bokan ya faruk yayi, rufe ido yayi ya tsinka mashi mari me shiga jiki kafin yace "ka
haddace abinda nace ka gaya musu ko na sake maimaita maka maƙiyin Allah?"
Cikin rawar murya ta irin wanda yasha wiyar nan yace "wallahi na haddace ranka shi daɗe"
Da kanshi ya janyo wayar bokan yayi dialing no ɗin uncle Abbas
Tsit polon yayi, ringing ɗaya kamar dama suna a kan wayar uncle Abbas ya ɗaga,
Daga jin muryar sa zaka san a kiɗime yake, "Haba malam, haba malam, ina ka shiga tsawon
kwanakin nan muna neman ka amma baka amsa wayar mu?"
Cikin ƙarfin hali bokan yace "Ina wani aiki ne, ba gashi na kira da kaina ba"
Kamar me ƙinƙina uncle Abbas yace "dukan mu gamu a waje ɗaya, rikici na neman ɓarkewa a
tsakanin mu, in hakan ta kasance asirin mu ya gama tonuwa malam"
Buɗe mishi manyan idanuwan shi yayi, yayi mashi alama da ido
Bokan yace "Kuna jina dukan ku?" a tare su ukun suka haɗa baki wajen faɗin "eh malam"
ya ɗora da "abinda nake so da ku shine, ku tabbatar da ankai yarinyar nan komin dare ɗakin ta,
rufe bakin kowa da kukace nayi, to nayi,
kaita ɗakin ta shine rufar bakin kowa, daga nan ku bar min komi babu wanda ya isa yaga
bayan ku, kuma takardun campanonin da nayi muku alƙawarin cewa da kanshi ze tabbatar da
cewa ba mallakin sa bane shi kaɗai, akwai saka hannun jarin ku a ciki ze tabbata shima a daren
gobe, amma sharaɗin shine ku kai yarinyar nan kafin goben"
Yana gama faɗin haka ya faruk ya gintse wayar haɗe da tallaƙe ƙeyar maƙiyin Allah.
Da ƙarfi uncle ƙasim yace "HAZBINALLAHU WANI'IMAL WAKIL"!
Ya sake kaɗa kai yace "Mutum da dukiyar sa halalin sa gumin sa amma suke son ganin bayan
shi".
Tsuru tsuru sukayi gaba ɗayan su, maganar tarewar sakina sam uncle junaid beso ba, amma
jin kalaman bokan nasu na ƙarshe yasa yaji ranshi yayi fari
Uncle Abbas da umma ƙarama daman uncle junaid ne matsalar su
Suna jin yace "Na yarda ta tare ɗin" umma ƙarama ta daka wani uban tsalle kamar ƙaramar
yarinya ta rungume uncle Abbas da shima dariyar cin nasara da suke tunanin sun samu yake
(WA'IYAZUBILLAH)
A take umma ƙarama ta bar wajen ta nufi gida.
Uncle junaid ma ya nufi nashi gidan da yazama kamar gidan mutuwa a ƴan kwana biyun nan.
A yarda suka rabu dama uncle junaid ze kira Abba babba da kanshi ya sanar dashi tarewar
sakinar a yau
Aikuwa hakan ta kasance, ko gidan be kai ga shiga ba ya kira Abban
A mutunce suka gaisa, yayi masa bayanin komi
Abban yaso yaja maganar amma uncle junaid ya fahimtar da shi amfanin yin hakan tuntuni
A take Abba babba ya yarda, sukayi sallama sannan ya kira Abba ƙarami ya sanar da shi,
tukun ya kira uncle Abbas da dama call ɗin yake jira,
Sannan ya kira uncle ƙasim suma da suke zaune suna jiran kiran
Sanda uncle ƙasim ya yaga kiran Abba babba kuma yaji akan maganar da ya kira, abun ya
sake bashi mamaki ainun.
Murmushi ya faruk yayi jin komi na zuwan masu da sauƙi.
***TK
Sanda uncle Abbas ya kira shi ya sanar da shi tarewa sakina a yau ɗin nan, haka yayi ta
birgima yana murna kamar wani ƙaramin yaro
A take uncle ƙasim yace "Yanzun nan zan sa azo ayi shara da goge goge tunda gidan sabo ne
babu abinda yayi"
Cike da zumuɗi Tk yace "To daddy"
Kankace me maganar tarewar sakina ta baɗe sasan gidan gaba ɗaya
Abba ƙarami da kanshi ya kira mama ya sanar da ita, har da faɗin "ki shirya ki tafi can gidan
junaid ɗin"
Jiki a sanyaye mama tace "to, Allah yasa hakan shi yafi zama alkairi"
Mumtaz da inna hassu na gefe, har rige-rigen tambayar ta suke
Nan tace musu "yau ne sakina zata tare wai"
Riƙe baki inna hassu tayi sannan tace "shine ko junaidu ya kirani yasan da ina nan ban koma
ba"
Mama tace "ai bata ɓaci ba, yanzun ma shiryawa zakiyi mu tafi tare"
Mumtaz tayi karaf tace "mama nima zani dan Allah"
Ɗaga hannu sama mama tayu tace "ba ruwana, ki tambayi faruk"
Taɓe baki mumtaz tayi kamar gaske tace "to ara min wayar ki na kira shi"
Da hannu ta nuna mata inda wayar take haɗe da miƙewa zuwa ta shirya
Mumtaz na ganin mama ta shige ta maida wayar ta ajiye, haɗe da turo baki tace "wallahi ba zan
kira ba kuma se naje, kullum in zakayi abu se ace se ka kira wani can"
ALLAH KASA ANNABI YA CECE 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg77-78
Da gudu ta shige ɗakin ta,
Bata jima da watsa ruwa ba dama,
Rasa kayan da zata saka tayi, can idon ta ya kai ga baƙar Abaya
Da sauri ta cirota haɗe da mayafin ta
Roll on se ɗan body spray me daɗin ƙamshi ta fesa
Sannan ta saka rigar
Gashin ta da ke a wargaje ta haɗe shi ta saka ribbom ta ɗaure sannan tayi rolling da mayafin
mudubi ta kalla, ganin yarda ta fito ras a kayan yasa ta wani kashe ma kanta ido ɗaya
Har ta juya zata fita ta dawo da saurin ta zizara kwalli a idon ta, dan tasan sarai mama se tayi
magana in taga idon ta fari ƙwal.
Fitowar su kenan suka ga sisters ɗin mummy kusan su takwas sun shigo
Cike da mutuntawa aka gaisa suka wuce.
Miƙawa mumtaz key ɗin motar tayi sannan ta zagaya ta shiga gaba
Inna hassu kuma ta shiga baya, mumtaz na mazaunin driver.
Suna hawa titi mama ta kalle ta tace "Ba sauri muke ba mu kam, jamu a hankali wallahi"
Dariya mumtaz tayi, tace "Hajiya mama"
Daga can baya inna hassu tace "ah da gaskiyar ta wallahi, koni yarda naga kin fizgi motar seda
na zabura"
Haka sukayi ta wasa da dariya har suka kai gidan uncle junaid.
Suna shiga gidan suka iske ana buga danbarwa da sakina akan shiryawa
Kallo ɗaya mumtaz tayi ma sakina taji mugun tausayin ta ya kama ta
gaba ɗaya a ƴan kwanakin nan da akayi ta wani koɗe ta rame kamar warda ta shekara tana
jinya
Jiki a sanyaye tace "ina kayan nata?"
Ƙanwar mum ɗin sakinar ta miƙa wa mumtaz kayan, suka juya suka bar musu ɗakin.
Sakaya ƙofar mumtaz tayi tukun ta matsa kusa da sakina da ko ƙarfin kirki bata da shi tsabar
rashin cin abinci da ba tayi,
Kusa da ita ta zauna, dafa ta tayi tace "Haba sakina kina cutar kanki da yawa, jifa yarda kika
koma daga last week zuwa yau,
Ki ɗauki ƙaddara ki fawwala ma Allah komi, ko wannen mu yana da tashi jarabawar"
Cikin fushi sakina ta katse mumtaz tace "Kin faɗi haka ai bayan ke kin samu muradin ranki"
Murmushi mumtaz tayi sannan tace "nasan baki san khalid ya sakeni ba a ranar da aka kaini
gidan su"
Duk da rashin ƙarfin jikin da bata ji hakan be hanata waigowa da sauri ba haɗe da faɗin "Haba
dai?"
Gyaɗa kai mumtaz tayi
Can ƙasan zuciya sakina tace "Kaɗan kenan kika gani"
A bayyane kuma tace "To garin yaya hakan ta kasance, me kikayi mishi to?"
Taɓe baki mumtaz tayi sannan tace "shi ya san ma kanshi sakina"
mamaki mumtaz keyi ganin yarda sakina kamar fara'a take da jin labarin sakin da akai mata
Basarwa tayi taci gaba da bata baki akan muhimmancin bin iyaye,
Haka kurum ta tsinci kanta da kasa gaya mata an maida auren ta kan yaya faruk.
Biyar da rabi na yamma aka fito da sakina da, sam ba zaka iya tantance a wani yanayi take ciki
ba
Fuskar ta ba yabo ba fallasa, har cikin bedroom wajen maman ta aka kaita
Saboda yarda kuka yaciyo ta kasa cewa komi tayi, su mama suka taso ta suka fito
Motoci ne reras ba laifi, kusan guda shida, haka aka saka sakina idon nan nata ƙur tana bin
kowa da kallo har motocin suka ɗaga
Mumtaz ma na daga motar mama tana binsu a baya, wannan karon ita kaɗaice a motar.
Masha Allah, gida se ƙamshi yake zubawa kamar gaske, haka aka wuce da sakina har cikin
ɗaki aka zaunar da ita
Su mama suka sakata a gaba da nasiha da rarrashi tukun sukai mata sallama suka fito.
Ba su wani jima a gidan ba suka fito kowa ya kama gaban sa
Suna tafe a hanya mama tayi shiru tana ta kallon titi
Can ta nisa tace "wallahi sakina ta bani tausayi, Allah yasa dai ta sa ma kanta haƙuri da salama
ta zauna har su samu su fahimci juna"
"hmm" kawai mumtaz tace, taci gaba da tuƙin ta har suka je gida
Suna shiga gida taga motar ya faruk a pake
Duk a tunanin ta baya cikin motar, taje tayi parking a kusa da tashi
Yana zaune yana waya da mus'ab amma hankalin shi gaba ɗaya yana gareta
Mumtaz na parking mama ta fice tayi sasan mummy yi mata Allah sanya alkairin Tk
Ya faruk na ganin mama ta fice ya sallami mus'ab yayi wuf ya fito
Mumtaz bata ankare ba taji shi tsulum ya faɗo mata cikin mota, har seda ta ɗan firgita taja da
baya
Dalalo mata ido yayi yace "wa kika tambaya da zaki fita?"
Sosa kai ta hau yi, tana inda inda tace "ai ban same ka bane, kuma naga da su mama zamu fita
ai"
Ɗage duka girar shi yayi, sanna yace "Shiyasa kika ƙi tambaya kenan?"
Shiru tayi ta sunkuyar da kai ƙasa
a hanakali tace "to kayi haƙuri"
Murmushi yayi haɗe da faɗin "Ah lallai asalin mumtaz ɗin da na sani ta fara dawowa tunda har
ana iya faɗin nayi haƙuri"
Murmushi kawai tayi
Ya sake cewa "muje ki raka ni wani waje"
Taso yin gaddama, amma bata ga wannan fuskar ba.
Motar shi suka koma daidai fitowar mama daga sasan mummy ta hango fitar su, murmushi tayi
kawai ta wuce nata sasan.
Suna tafe yana mata hira, tun tana basarwa har ta dawo tana bashi amsa
Daidai ƙofar wani ɗan madedecin guda me kyau yayi parking
Kallon shi tayi sannan tace "gidan wa ne nan?"
Taɓe baki yayi yace "cewa akayi na kawo ki dan Allah, ki shiga minti goma na baki ki fito"
Ƙin fita tayi dan bata san ina ne ba,
Shima basarwa yayi yaja seat ɗin kujera baya yayi kwanciyar shi
Can ya waigo yaga itama idonta a rufe, zungurin ta yayi da hannu
Sannn yace "yarinya duk a cikin mintocin ki ne, ba ruwa na"
Yana gama faɗin haka ya janyo wayar shi yayi dialing no ɗin Amal, bugu biyu ta ɗaga, cewa
kawai yayi "Leƙo" ya aje wayar
Mumtaz na zaune taga fitowar Amal da gudu tayo kan motar
Da mugun mamaki mumtaz ta kalli ya faruk da ya basar tace "Innalillahi, wallahi ban yarda ai
faɗa min ya kamata kayi"
Bama ta jira me zece ba ta buɗe motar
Wani ihu suka saka seda ya faruk yayi saurin toshe kunnuwan shi
Cike da farin ciki suka rungume juna, ko ta kan ya faruk basu sake biba sukayi ciki rungume da
juna.
Karkaɗa kai kawai yayi yace "Bazasu taɓa girma ba yaran nan".
****Ango TK
Ana idar da sallar isha'i ya nufi gidan amarya sakina
Tana nan zaune inda aka barta, ba sallah ba salati, banda saƙa da warwarar mugun abu babu
abinda take tun tafiyar waɗanda suka kawo ta
A hankali ta tashi ta ƙarasa gaban mudubi ta tsaya,
ƙare ma kanta kallo tayi daga sama har ƙasa, a fili tace
"wallahi ba ajin ka bace ni Tk, ko ta halin ƙaƙa se na bar gidan nan ba tare da igiyar ka a kaina
ba wannan alƙawari ne na ɗaukar ma kaina! ta dafa ƙirjin ta haɗe da gyaɗa kanta.
KUYI HAƘURI NA JINA SHIRU, JIKI DA JINI 😊
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
WANNAN PAGE ƊIN SADAUKAR WANE GA DUK WANI MAKARANCIN "LAUJE CIKIN NAƊI"
ƘAUNAR KU TA DABAN CE A CIKIN RAINA ❤️
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg79-80
Tana nan a tsaye taji shigowar shi cikin gidan,
Rufe ko ina yayi sannan ya ƙaraso cikin ɗakin da take
Tk na tura ƙofar ya tsaya cak yana bin sakina dake tsaye a gaban mudubi da ido
Kamar maye haka ya hau lashe baki yana wani marmar da idanu.
Ta cikin mudubin take hango shi, wani tsana da ƙyamar shi kawai ke taso mata bilhaƙƙi
Ba sallama ba komi haka ya wuntsulo ciki,
Cike da zumuɗi yace "a ƙarshe dai kin yarda an kawo min ke amaryata"
Yana ƙoƙarin kai hannu jikin ta
A fusace sakina ta jiyo ta bige hannun shi, cikin fusata tace "Kar ka kuskura ka sake kai hannun
ka jiki na malam"
Dariya Tk ya saka haɗe da shafa ƙeyar shi, koma da baya yayi ya zauna a gefen gado sannan
yace "Halan iyayen ki basu ce maki gidan aure suka kawo ki ba?"
Banza tayi da shi ta buga tsaki ta shige toilet
Gyaɗa kai yayi haɗe da faɗin "gama ki fito, zaki gayan wanda kikayi ma tsaki yar gidan mugu"
Tun yana saka ido yaga fitowar sakina daga toilet har ya koma ya fara kallon agogo
Da dai yaga abin ya wuce gonabda iri ya miƙe haɗe da faɗin "ko kashin danƙo kike yi ai yaci
ace kin gama shi"
Tura ƙofar bayin yayi,
Da mamaki yake kallon sakina da tayi zaman dirshen a ƙasa
Ranƙwafowa yayi ya taɓata, da sauri ta buɗe ido haɗe da ja baya tace "miye haka?"
Ɗaure fuska TK yayi yace "baki da hankali ne zaki fara bacci a cikin toilet? nan wajen bacci ne
akace maki?"
Banza tayi da shi ta juyar dankanta can
Gyaɗa kai kawai yayi ya juya ya fice
Ɗayan ɗakin ya shiga ya gama duk uzirorin sa sannan ya shiga kitchen ya ɗakko cups da kuma
juice ya fito
a palo ya tsaya ya saka sleeping pills a cup ɗaya sannan ya tsiyaya juice ɗin a ciki ya nufi ɗakin
Daidai sakina ta gaji da zaman bayin ta fito
Kallo ɗaya tayi masa ta watsar,
Gefen gadon ta zauna haɗe da cire lulluɓin jikin ta
Kamar wani mutumin kirki Tk ya matsa kusa da sakina,
Cikin dabara ya fara magana,"ki fahimce ni mu nema wa kanmu mafita sakina, kin san nima ba
son ki nake ba, kamar yarda akayi maki dole to nima dolen akayi mani,
Abinda nake so dake shine, ki kwantar da hankalin ki muyi musu lamɓo kamar mun haƙura,
daga nan zuwa sati ɗaya nasan sun gama sakin jiki da mun haƙura da juna, ni kuma daga
wannan lokacin se in sake ki kije ki auri wanda kike so nima na auri wacce nake so"
Kafe ta da kallo yayi yaga a wani yanayi ta tarbi maganar tasa
Murmushi sakina tayi, tana jin sanyin nutsuwa na kama ta
Cike da jin daɗi da fara'a tace "Da gaske kake Tk?"
Gyaɗa kai yayi shima murmushi ɗauke da fuskar shi ganin yarda tayi saurin faɗawa tarkon shi
Gyara zama tayi ta fuskance shi da kyau tace "To muyi ma juna alƙawari"
Kai tsaye yace "alƙawarin me?"
A ido ta kalle shi tace "babu wani abu da ze taɓa shiga tsakanin mu har mu rabu"
Da sauri Tk yace "da me kike tunani?, ai ki saka a ranki yarda kike zaune a gidan ku haka zaki
zauna a nan, ba wannan maganar ma"
A take sakina ta ɗauki yarda ta aza wa maganar ta da Tk,
Shiru tayi tana ta saƙe saƙen abubuwan da ya dace tayi bayan rabuwar ta da TK.
Tashi yayi ya nufi ƙofa sannan ya waigo yace "nan ɗakin yayi maki ko can kike so?
Taɓe baki tayi tace "it's okay nan"
Har ya fice ya dawo ya ɗauki juice ɗin da ya watsa ma pills a ciki
Fuska ba yabo ba fallasa tace "nasha ni ka aje ma ai?"
A fakaice yayi murnushi ya yace "bari na kawo maki naki dai"
"to" kawai tace ta gyara kwanciyar ta
Tk na fitowa palo, ya nufi kitchen ya zubar da rabin wannan sannan ya sake ɗaukar me sanyi ya
cikasa cup ɗin tukun ya koma ɗakin
Ko kallon shi bata yi ba ta karɓa
Kofin ta kai baki, har wani lumshe ido take tsabar yarda sanyin juice ɗin ya ratsa ta
Tk na tsaye, seda ya ga ta kusa shan rabi tukun yace "mu kwana lafia"
Ko tanka shi batayi ba ta ci gaba da sipping juice ɗin ta.
*****Ya faruk
Wasa-wasa sedai ya bar mumtaz a gidan Amal yace zuwa bayan magrib ze dawo
Sam Amal kasa ɗauke ido tayi daga kallon mumtaz, saboda tsananin mamaki da kuma
al'ajabin komi da yaƙi barin ta
Faska mata duka a cinya mumtaz tayi tace "kar ki cinye ni malama, kallon ya isa haka"
Amal na sosa cinyarta tace "wallahi ganin abun nan nake kamar a mafarki mumtaz, wai ya faruk
ya zama mijin ki har kike masa yarda kika dama"
Kai tsaye mumtaz tace "To Allah ya kashe ya bani, ya son ranki?"
Ihu Amal ta saka tsabar ƙwaƙwalwar ta takasa riƙe jin daɗin da take a ciki
Cike da azarɓaɓi tace "wallahi kunyi mugun dacewa mumtaz, se yanzu na tabbatar da baku
wani dace da khalid ba sam,
nifa na jima da zargin dama ya faruk na son ki wallahi"
Taɓe baki mumtaz tayi tuno mata da sunan kalid da amal tayi, can tace
"Haka Allah ke abin shi, dama kana naka ne Allah na nasa, kuma na Allah shine daidai akan
namu"
Ko sallar basu tashi sun yi ba, mijin Amal ya shigo palon haɗe da kiran sunan Amal
Tashi Amal tayi ta fito zuwa palon, ya faruk ta gani zaune
Sam kasa ɓoye murnar ta tayi, cike da ɗoki tace "oyoyo ya faruk"
Murmushi ya faruk yayi yace "kuna lafia?"
Da sauri ta juya ta nufi kitchen ta haɗo mishi abun motsa baki sannan ta dawo
Ruwa kawai ya sha yace "kice ta fito mu tafi, akwai inda zani"
Ɗan ɓata rai Amal tayi sannan tace "Dan Allah yaya"
Be ma bari ta gama faɗin me zatace ba yace "no Amal, wani lokacin dai"
Jiki a saɓule ta koma ɗakin da mumtaz ke zaune, tace "ki fito zaku wuce"
Daga zaunen da take tace "ya dawo wai?"
"eh" tace sannan ta ɗauki hijabin ta dake aje a gefe.
Kan mumtaz a ƙasa ta gaishe da mijin Amal, ya faruk na ta satar kallon ta a fakaice har suka
fita.
**** Uku da rabi saura na dare Tk ya turo ɗakin da sakina ke ciki,
wata muguwar dariya Tk ya saka
Matsawa