Author : ZAINAB FALALU Category : African Stories & Novels
ta hau salati,
"itako me yayi mata zafi haka?"
Can dai ta taɓe baki tace
"Mugun nunkufurci ne ze halaka ta wlh, mace sam baza ka taɓa jin cikin ta ba, sedai tayi ta
barin abu yana damun ta a cikin rai, to Allah ya tsayar a kanta"
Ya faruk bece uffan ba, seda ta ƙaraci ƙorafin ta dan kanta tayi shiru tukun ya sallame ta ya
wuce.
Mumtaz ta jima tana jiran shi a wajen motar shi, duk da ba wani fira suke da Amal ba, amma taji
daɗin tsayawar ta a kusa da ita ko ba komai tsayuwar ba zata dame ta ba
Suna tsaye a haka ya faruk ya iso, tun kafin ya iso ya danna remote boot ya buɗe,
Jakar hannun kayan ta saka a ciki, Amal kuma ta saka basket ɗin abincin hannun ta
Murya ƙasa-ƙasa Amal tace
"Ya faruk dan Allah nima zani"
"muje" kawai yace
Front seat ta shiga, mumtaz ta shiga baya ya ja suka tafi.
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg13-14
Sanda suka shiga ɗakin mama na zaune dattijuwar likitar na cire mata drip ɗin da aka saka
mata
Mumtaz da Amal suka gaishe ta a ladabce ta amsa musu da fara'a
Can gefen da fridge yake suka ajiye kayan hannun su, kujera Amal taja ta zauna, Mumtaz
kuma ta koma gefen mama
Drn na gama cire mata ta juya ta fice, tukun ya faruk ya ƙaraso ciki
Be wani jima ba yace wa Amal
"ke muje"
Sosai mama ke mishi addu'ar gamawa lafia, dan ya faruk mutum ne.
Suna fita mama ta kalli Mumtaz da har yanzu idanun ta basu sauka da fushin da suka yi ba tace
"Kunna min heater can in watsa ruwa, kayan nan sun min nauyi da yawa"
Jiki a mace Mumtaz ta tashi, duk mama na lura da yanayin ta, ba se an faɗa mata ba dama
daga ganin idanun ta kasan ba ƙaramin kuka ta sha ba
Tana kunna heater ta koma ɗayan gadon da aka aje shi domin me jinya ta kwanta haɗe da
lumshe idanu, tanajin shigar mama toilet ta sakko ta hau bincike gadon da mamar ta tashi
Seda ta bincike ko'ina bata samu komi ba tukun ta koma ta zauna
Koda mama ta fito tayi mamakin ganin yarda shimfiɗar gadon tayi, bata kawo komi a ranta ba ta
waiga tace
"Kakkaɓe min gadon kafin nayi sallolin da suka wuce ni"
Seda ta fakaici idonta ta zumɓura baki kafin ta nufin gyara gadon.
Suna shiga gida ana kiran sallar magrib
Shigewa Amal tayi cikin gida
seat ɗin baya ya faruk ya buɗe ya kwashe ledojin siyayyar da yayi tun shekaran jiya be kwashe
ba
Seda ya kwashe har ya ja baya ze rufe motar yaga wata ledar a ajiye a inda Mumtaz ta zauna
ɗazu
Haɗe ledojin yayi a hannu ɗaya sannan ya ɗauki warcan, be tsaya dubawa ba saboda kiran
sallah da akayi, seda ya kai kayan ɗaki tukun ya ɗauro alwala ya fito
Seda ya ratsa cikin cincirindon maza da mata dake danƙare a wajen ana ta rabon kayan buɗa
baki, sam wasun su bama ta sallar suke ba, ta cikin su suke, a haka ya samu ya wuce da ƙyar
TUSHEN SU!
Alhj sule me awaki shararren attajirin ƙauye ne, mutum ne me dattako da sanin yakamata,
a lokacin Iyaye sukayi shawara aka haɗa shi aure da matar shi ta farko wato Balki, sun kwashe
tsawon shekaru Allah be basu rabon haihuwa ko ɗaya ba,
Kusan shekarar su Goma sha bakwai da aure kafin Allah ya ba balki rabo, sosai sukayi murna
suka ji daɗi da rabon da Allah ya basu
Haka Balki tayi ta rainon cikin ta cike da kulawar ko wani ɓangare, Alhj sule ya kan fita
kasuwannin kusa dana nesa a ranakun kasuwa ya seda dabbobin sa, haka yake raba jama'a
zuwa ko wacce kasuwa a wannan lokacin.
Hanun shi a buɗe yake sosai, shiyasa be samu matsala da yawanci waɗanda ya aza akan
dukiyar shi ba
A haka wata rana da dare naƙuda ta kama balki,
Daman jiran ta ake, Inna(kishiyar maman Alhj sule) itace tsaye kan Balki har Allah ya sauke ta
lafia ta haifo ɗanta namiji me kama da Alhj sule,
Suna daga can waje suka jiyo guɗar inna har uku, nan fa akayi ta murna ana ma juna sam
barka, dan balki ba ƙaramar wahala ta sha ba
Tas aka gyare balki da ɗanta aka miƙa wa Alhj sule, anan yayi mishi huɗuba da suna
"Aliyu"(Abba babba) so ɗaya Balki taba Aliyu nono, sedai aka tashi washegari da gawar ta, cikin
dare jini ya ɓalle mata, kafin ayi wani yunƙuri rai yayi halin shi
Sosai aka shiga tashin hankali, masu kuka sun yi kuka,
Wasu kukan su duk akan jaririn data bari ne saboda tausayi
Kar kuso kuga Alhj sule, shi kanshi ya shiga ɗimuwa ƙwarai, ya yabi kyawawan halayyar balki
ƙwarai da gaske.
Duk nonon da aka baiwa Aliyu baya kamawa, akwana biyu duk wanda ya kalle shi se ya
tausaya mishi, dan yunwa sosai ta fara bayyanar mishi
Kamar da wasa, ƙanwar balki me suna Abu na zaune tace a miƙo shi,
Tana karɓan shi tayi bisimillah ta kafa mishi nono, aikuwa cikin hukuncin ubangiji Aliyu ya karɓa,
Yana sha yana sauke ajiyar zuciya
Tunda mahaifiyar Alhj sule ta ƙyallara ido taga an samu ya karɓa tace "a barmata shi ta shayar
da shi"
Abinda akayi kenan, A wannan dalili na shayar da shi datayi yasa mijin ta yayi fushi ya sake ta,
haihuwar su ɗaya dama
Haka ta tattara ta dawo, sosai rayuka suka ɓaci ta dalilin komen da ake so tayi
Ganin abun yaƙi yiwuwa yasa aka haƙura
Ko sati bata rufa ba da gama idda aka ɗaura auren ta da Alhj sule ta maye gurbin yayar ta balki.
Cikin hukuncin ubangiji tana shiga ta samu ciki,
Haka Abu ta rinƙa rainon Aliyu da kuma cikin ta duk a lokaci ɗaya,
Wata tara cif ta haifo ɗanta me kama da Aliyu dak
Lokacin data haihu Aliyu ya cika shekara ɗaya da wata huɗu a duniya, a ranar kuma ta cire shi
daga nono.
Yaron data haifa aka saka mishi sunaa "Abubakar".
Bayan shekara uku ta sake haihuwar Abbas, sannan tayi ƙasim, ta rufe da Auta Aisha.
Sosai suka haɗa kai suka rinƙa ba yaran su tarbiya, yara dama dole se da saka idon iyayen su
Sam sauran yaran basu taɓa sanin cewa ba Innaa Abu ce ta haifi Aliyu ba seda suka girma
kowa ya mallaki hankalin sa tukun.
A lokacin innaa Abu na iyakacin ƙoƙarin ta wajen ganin sun haɗa kansu,
Kana naka Allah na shi, Aliyu ne yaso ya fita zakka, Allah yayi shi mutum ne me zuciyar tsiya,
ga saurin hannu, abu kaɗan ze ɗaga hannu ya kai wa Abubakar duka, shikuma be iya ramawa
ba wai dan bashi da ƙarfin ba, seda koyar da su da innaa Abu keyi kullum akan bin na gaba da
su
Yawan doke-doken da Aliyu ke yi ne yasa wata rana Innaa Abu ta dake shi shima, tayi ta mishi
faɗa daga baya ta ɗora da nasiha akan yaja ƙannen shi a jikin shi.
Duk da haka dai ba wani jituwa me ƙarfi a tsakanin Aliyu(Abba babba) da Abubakar(Abba
ƙarami).
Anan ƙauyen sukayi makaranta muhammadiya da kuma primary da aka buɗe
Duk a cikin su Abubakar yafi nuna son karatun zamani, sauran se sun ga dama zuwa wani
lokacin
Bayan sun gama primary, Alhj sule da kanshi ya ɗauki Aliyu da Abubakar ya kaisu makarantar
gaba da primary, wanda sauran su basu kai ga gamawa ba
A haka dai, yau daɗi gobe akasi hakan, har Allah yasa suka kammala, Aliyu ya tsunduma
harkar kasuwanci irin na mahaifin su, inda shi Abubakar ya tafi makarantar gaba, anan ya fara
karatun shi na jami'a a fannin kasuwanci yana gaf da gamawa, Abbas ya fara nashi karatun a
fannin mass com daga baya ƙasim ma ya biyo shi, inda anjima da aurar da Aisha ga wani ɗan
me garin garin da suke, inda shima ya ɗauke ta ya bar ƙauye da ita suka fito gari.
A lokacin da Aliyu ya cika shekara 25 yayi aure,
Ya auri matar shi me suna Nabila, iyayen ta na da rufin asiri daidai gwargwado, nan inda yake
kasuwancin shi a nan ya kama gida suka zauna
Abubakar kam seda ya gama degree, a lokacin ba kowa ke samun wannan damar ba, sanda
ya gama ya samu aiki a wani babban company ana biyan shi sosai da sosai
Lokacin shi ba nauyin kowa a kanshi, iyaye ne kuma Allah yayi musu rufin asirin da ba se sun
dogara da kowa ba
seda ya shekara uku da fara aiki, a shekaru ukun nan kaf haka ya rinƙa tara albashin shi, tunda
ko gidan zama ma bashi akayi, ba shi da wani buƙata sedai abunda ba'a rasa ba
To da waɗan nan kuɗi beyi shawara da kowa ba yaje ya siya wani mahaukacin fili me girman
gaske, lokacin wajen daji ne ma ba gida ko ɗaya, sedai an yanyanka filayen, haka ya siya ya
adana takardun shi, filin kuma yayi banza da shi yaci gaba da aikin shi,
Duk sanda ya samu lokaci yakan kaima iyayen shi ziyara, kuma ya kai ma ɗan'uwan shi Aliyu
ziyara haɗe da sha tara ta arziki
Nan Nabila(umma babba) ta rinƙa ma ƙanwarta campaign a wajen Abubakar, shi kam tuni ya
ƙyallara idanu akan ƙanwar aminin shi.
SHARE PLS
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg 15-16
Duk sanda su Nabila(umma babba) zasu tare shi da zancen ƙawarta yakan basar da zancen ya
nuna be gane inda suka dosa ba
Ba yarda suka iya, dole suka rabu da shi.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, yau fari gobe baƙi
Duk asabar ɗin duniya Abubakar(Abba ƙarami) ke zuwa wajen Zahra'u, sosai suka fahimci juna
sukayi sabo me wahalar mancewa
Da yake yana da ƙafa a gidan, yayan ta aminin shi ne sosai yasa be wani sha wahala ba, kuma
da Allah yayi cewa ita ɗin rabon shi ce.
Bayan shekara biyu da kusan rabi da auren Aliyu(Abba babba) shima Abubakar aka ɗaura
nashi, an yi shagali dai dai gwargwado a wannan lokaci, amarya ta tare a gidan ta da ya kama
haya
Zama ne na fahimata da kuma ƙaunar juna
Takan leƙa Nabila wani lokacin, duk da ba wani fira ce ke shiga tsakanin su ba se dai harare
harare daga ɓangaren Nabila
Da dai zahra'u taga take taken ta se tasha maganin zama da ita, tsaf ta ɗauke ƙafar ta daga
zuwa wajen ta, in ba dai abun murna ko Allah kyauta ne ya faru ba
Wannan kenan.
Tsakanin auren Abubakar da Abbas ba wani tazara,
shima ya haɗu da matar shi me suna hauwa,
a ranar bikin Abbas ɗin ne matar Aliyu wato Nabila ta haifo santalelen ɗanta me kama da baban
shi sak, ranar data zagayo yaci suna Umar faruk, shine suke kiran shi da faruk, sosai Zahra'u
ta ɗauki son duniya ta ɗora ma faruk, da ta ɗauke ƙafa daga gidan, amma haihuwar faruk yasa
take zuwa a kai akai, Nabila tayi ta yada mata magana son ranta amma haka nan take basarwa
dan son da take masa
Cikin hukunci ubangiji haka buɗi yayi ta buɗe ma kowa a cikin su,
Saboda nema haɗuwa ta fara musu wahala, a wannan ɗan tsukin ne, Aliyu ya sake rarimo wani
auren na biyu
Sosai hankalin Nabila ya tashi, ta shiga nan ta shiga can, to da yake duk abunda Allah ya
ƙadarta se ya faru ba makawa, haka akai auren nan kamar ba za'ayi ba
Haka itama ya kama mata gida daban, Sumayya macece me haƙuri da sanin ya kamata itama
bata da matsala ko kaɗan.
Lokacin da Aliyu ya ƙara aure faruk be wuce shekara biyu da rabi ba
Haka sumayya ta ringa janshi a jiki, ganin hakan yasa Nabila ta hana ta gwammace gara ta
rinƙa barin Zahra'u na ɗaukar shi akan ace kishiyarta ke ɗauka
Wannan dama da ta samu ne yasa sukayi mugun shaƙuwa da faruk, inda bakin shi ya buɗe da
kiran ta da "MAMA" Abubakar kuma yana ce mishi "Abba"
Da faruk ya ƙara wayo ne yake banbance sunan iyayen da Abba babba da Abba ƙarami
kishiyar mahaifiyar sa kuma ya laƙaba mata "Umma ƙarama" mahaifiyar shi kuma "Umma
babba"
Sosai sunayen nan suka yi wa Umma babba ciwo, tasha ta rinƙa mammake mishi baki, amma
haka nan ta haƙura ta rabu da shi badan ta so ba.
Abu kamar wasa har umma ƙarama tazo ta haihu amma mama shiru babu alamun ciki
Sam basu saka wata damuwa a zukatan su ba, sun san Allah ne meyi, duk da habaicin da
umma babba ke yawan yi mata a duk sanda suka haɗu a wani taro ko sha'ani bata taɓa saka
abun a ranta ba balle ya dame ta.
Ta ɓangaren matar uncle Abbas kam bata fiya shiga sabgar kowa ba, saboda take-taken umma
babba data gani
Sun ɗan fi zama da mama suyi fira ma, sukan ziyarci juna lokaci zuwa lokaci.
Sosai rashin lafia ya kama Inna Abu, hankalin kowa ya tashi,
Lokacin da Abba ƙarami yaje yaga halin data ke a ciki hankali a tashe ya ɗakko ta suka shigo
asibitin cikin gari
Sosai sirikan nata ke bata kulawa, babu warce ta rainata a cikin su,
A cikin jinyar ne Inna Abu ta lura da sam sirikan nata ba wata jituwa a tsakanin su
Batayi musu magana ba, seda gaba ɗaya ƴaƴan nata suka hallara tukun tace
"Kuji tsoron Allah kuso junan ku da amana, kar ku bari asamu ɓaraka a tsakanin ku balle har na
kusa da ku su gane su shigo da nasu son rai, ku sani duk abu ɗaya ne yayi ku, baku da
banbancin komi a tsakanin ku, bana so ko so ɗaya wani daga cikin ku ya ɗarsa wani abu mara
daɗi a cikin ranshi, ku zama tsintsiya maɗaurin ta ɗaya wanda ko ƙasa ta rufe min ido zanyi
alfahari daku"
Can ta fashe da kukan tausayin kanta da ma su yaran nata
Sosai hankalin su ya tashi sukai ta banbaki har tayi shiru
Ɗakin yayi tsit, maganar inna Abu ta katse shirun da
"Abubakar, maganar filin nan da kayi min ɗazu nace ka ban lokaci, to na yanke shawarar ka
gina ɗin kamar yarda ka fara faɗi, alabarshi se ku haɗe iyalan ku duka a waje ɗaya se fahimta
ta sake shiga sosai a tsakanin su
Ku kuma zumuncin ku na nan sema ƙarfi da ze ƙara"
Tana rufe baki uncle ƙasim yace
"Kar kice haka inna, ni anawa tunanin se inga zama a waje ɗayan nan ba shine zefi ba, kamar
za'afi zumunci in kowa na muhallin shi"
Da sauri Abba babba yace,
"Yarda tace haka za'ayi ko muna so ko bama so, ballantana banga wani aibu a cikin maganar ta
ba"
Abba ƙarami bece komi ba, duk da shi ya fara kai wa mahaifiyar shi shawarar yin hakan, amma
daga baya ya gane ya tafka babban kuskure, kuma tunda yanke shawarar hakan bashi da
kuma bakin da ze iya hanawa.
Ta ɓangaren uncle Abbas kam cewa yayi
"bani da choice ni kam, dan ba lale ayi amfani da abinda kace ba"
kKowa seda ya kalle shi jin furucin bakin shi, inna Abu tace
"Ni dai ga abunda nace, kuma duk wanda yayi watsi da wannan maganar ban yafe ba"
Tsit wajen yayi, kowa da abunda yake saƙawa a ranshi, in ka kalli fuskar Abba babba zaka ga
kamar me murmushi.
Abba ƙarami kam baka gane a wani yanayi yake a ciki ba, kanshi na ƙasa.
Uncle ƙasam ne ma yace
"Allah ya baki haƙuri, ai abun be kai ga haka ba hajiya Inna" ya ƙarashe maganar da
barkwancin shi.
ganin dare yayi ne kuma suna ta zama yasa tace
"zaku iya tafiya dare yayi, Allah yayi muku albarka yasa duk ku gama da duniya lafia"
Gaba ɗayan su suka amsa da amin, ɗaya bayan ɗaya suka yi mata sallama suka fice
Abba ƙarami ne na ƙarshen fita, har ya kai ƙoma yaji inna Abu tace
"zo nan Aliyu"
Jiki a sanyaye ya dawo ya zauna still kanshi a ƙasa
Kanshi ta dafa tace
"Ka daure kayi hakuri da Aliyu, da sauran ƴan'uwan naka, sannan kaba zahra'u haƙuri itama,
zaman ku a tare ze saka ni farin ciki, duk da bakayi magana ba nasan baka so hakan ba, amma
kuyi haƙuri kuma na yafe muku gaba ɗayan ku, tashi kaje Allah ya sada mu da alkairin sa"
Murmushi yayi jin zolayar da tayi mishi,
Sanda ya fita duk sun kama kansu, shima ya haye babur ɗin shi ya tafi gida.
WASHE GARI
Wajen shida saura suka ji bugun gida, mama na kitchen tana dafa ruwan wanka ta shiga ɗaki ta
taso Abba ƙarami
Yana fita ya dawo yana salati duk yabi ya ruɗe
Anan take jin rasuwar Inna Abu,
Hankali ya tashi sosai, ko wanka basu samu yi ba suka ɗunguma suka tafi asibitin
Sosai ahalin nan suka shiga damuwa,
mota aka samo aka sakata, sannan wasu daga ciki suka shiga
Sauran kuma suka samu wata motar suka bi bayan su zuwa ƙauyen su
A nan aka sallace ta aka rakata zuwa gidan ta na gaskiya.
Bayan bakwai kowa ya kama gaban shi yin harkokin sa.
Tunda inna Abu ta rasu Abba ƙarami da maganar inna Abu yake kwana yake tashi
Sam ya kasa samun sukuni a zuciyar shi
Wata safiyar Asabar ce yana zaune suna ɗan taɓa hira sama-sama da mama, faruk na kwance
a gefen ta yana bacci Abba ƙarami yace
"Zahra'u bari in daure inje in duba filin nan inga ta ina zan fara"
"Okay to, Allah ya kiyaye, ai gara kaje ka duba ɗin tun wuri".
Da Abba ƙarami yaje wajen da ƙyar ya iya gane wajen, seda ya nemo me unguwar da kusan a
hannun shi dama filin yake tukun ya gane
Sosai Abba ƙarami yayi mamakin cikar wurin, gidaje ne a tsare reras manya-manya gabas da
yamma kudu da arewa,
Be bar wajen ba seda ya tabbatar da ya daidaita abunda ya dace.
Tsayawa yayi tsayin daka aka fitar da zanen gidan cikin kwana kaɗan
flat biyar aka zana, ko wanne duplex,
Flat ɗin Abba babba anyi shi dan zaman mace biyu, a ido yafi ko wanne girma, sama ɗaki biyar,
ko wacce biyu se na Abba ƙarami ɗaya
Ƙasa kuma akayi ɗaki biyu, se babban kitchen da store
Flat ɗin uncle Abbas da na uncle ƙasim na tsarin mace ɗaya kuma iri ɗaya, sama ɗaki biyu ƙasa
biyu se kitchen da store
Flat ɗin Abba ƙarami mama yaba wuƙa da nama ta faɗi yarda ta ke son ya kasance
Aikuwa tayi tsarin da yafi na kowacce kyau da haɗuwa
Dan ita hada palo tace ayi mata a sama, Sosai tsarin ɓangaren ta ya babban ta da na sauran.
Gadan gadan aka fara gini, Alhamdulillah, da yake ya tara shiyasa nan da nan komi ke sauri
A cikin shekara ɗaya gam aka kammala gidan, dai-dai lokacin uncle ƙasim shima ya samu mata
Sanda Abba ƙarami yaje musu da maganar komawa sabon gida memakon yaga murna a
fuskokin wasu daga