LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU

Author :  ZAINAB FALALU Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 25

9K to 12K   out of 73.4K words

azabar raɗaɗin da yake ji a cikin zuviyar shi

A daddafe ya samu yayi sallar isha da se yanzu ya samu zarafin yin ta



Tunda ya idar ya janyo biro da takardar da ya ajiye tun ɗazu

Hannun shi na rawa idanun shu na zubar da rywa ya fara rubutu .....




Seda ya gama, ya ninke takardar tukun ya ajiye a gefe



Jeans da riga ne a jikin shi, se baƙar jacket da ya ɗora akai



Ya jima a tsaye kanshi jingine da bango kafin ya ɗauki takardar nan

Seda ya kalli agogo yaga huɗu saura, lokacin da yawa wasu sun tashi sahur



Fitowa yayi daga ɗakin ya wuce part ɗin su kai tsaye
Knocking biyu yayi Altine ta buɗe mishi ya shiga



Kallon stairs yayi yaga alamun mama bata sakko ba, dan ko hasken corridor ɗin ba'a kunna ba



Ɗakin mumtaz ya ɗan ƙonƙosa, tashin ta kenan dama taji knocking ɗin, ta aza mama ce ma,
shiyasa tayi saurin sakkowa ta buɗe ɗakin



Tana buɗewa taga mus'ab tsaye a bakin ƙofar



"lafia ya mus'ab?"



Muryar shi a dishe yace



"mama bata sakko bane?"



Gyaɗa kai kawai tayi tana ci gaba da kallon shi



Be sake cewa komi ba ya saka hannun shi a aljihun jacket ɗin shi ya ciro takardar ɗazu ya miƙa
mata



Hannu tasa ta karɓa

Kafin ma ta nemi ƙarin bayani yace



"Ki ba mama in ta fito, ni ba zan samu damar shigowa ba anjima, kice mata list ɗin data ce
akawo mata ne"

Yana gama faɗar haka ya juya ze fice



Da sauri mumtaz tace

"ya mus'ab"
Waigowa yayi yana ya kalle ta da jajayen idanuwan shi



Jiki a sanyaye tace

"Baka da lafia ne?"



Murmushi yayi mata tukun yace

"lafia lau nake, kawai ban samu enough bacci bane"



Yana gama faɗin haka ya ƙarasa ficewa.



Anan kan mirrow ta ajiye takardar ta shige toilet.




Wajen sha ɗaya da rabi na safe, Mama na zaune tana nuna ma Altine kayayyakin sallah da
za'a kai gidan marayu tana haɗe su a babban kwali



Dogon list ne a hannun ta na sunayen jama'a, sannu a hankali sukai ta fitar da na kowa, hatta
altine an cire mata nata rabon



Rabon yazo ya caɓe mata, ga shirin tafiya umara da zasuyi jibi shiyasa take so ta sallami kowa
da kowa dan ta tafi cikin kwanciyar rai




Mumtaz na zaune a gefe tana auna sarkar wuyan mama da tun fitowar ta take tsole mata idanu,
ta tuna da takardar da mus'ab ya bata ɗazu da asubah, kamar ba zata tashi ba can dai tace



"Akwai fa sauran ki mama, ɗazu ya mus'ab ya kawo wani list ɗin fa"
Bata jira cewar mama ba tayi ɗaki.



Hankalin ta na kab wayar da take daddanawa ta miƙa wa mama takardar har tana ƙoƙarin tsole
mata idanu




Daga mama har Altine sakato sukayi suna kallon Mumtaz da bata ma san me takeyi ba



Rai a ɓace mama tace

"Ki cire min idon se ki huta"



Ɗago kanta tayi, memakon ta gane abinda tayi sema dariya datayi tace

"Da abun yayi mana yawa ai mama, ga makanta ga kuma faɗa"



Da sauri Altine ta sauke kanta ƙasa tana ƙunshe dariyar dake cinta



Mumtaz kam ganin kallon da mama ke mata yasa tace



"Allah baki haƙuri, ni wasa nake miki" ta aje mata takardar a table ɗin gaban ta.




Seda mama ta gama da gaba ɗaya na hannun ta tukun ta ɗauki warda mumtaz ta ajiye mata



Haka kurin taji gaban ta na dukan uku-uku



A hankali ta warware, memakon taga sunaye ko gidauniyoyi se kawai taga an fara da

"Dear mamana da kuma Abba na"



Dummmm, haka gaban ta ya bata wani mugun sauti, ji tayi miyan bakin ta ya ɗauke, numfashin
ta na ƙoƙarin fin ƙarfin ta

Ido a waje take karanta takardar, gaba ɗaya hannun ta rawa yake



Tana kaiwa ƙarshe ta hau nanata kalmar "innalillahi wa'inna ilaihirrahi'un! da ikacin ƙarfin ta




Mumtaz da Altine sukayi kanta da gudu suna auna ma sunan ta kira



Dai-dai shigowar Ahmad kenan ya iske su a haka

Shima da sauri ya ƙarasa inda suke ƙoƙarin ganin sun tare mama bata kai ƙasa ba
Amma inaa jikin ta ya riga da ya gama saki ba wani alamun numfashi a tattare da ita.



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg 9-10

Ganin yarda Ahmad ke girgiza ta da ƙarfi yana kiran sunan ta yasa Mumtaz ficewa da gudu
tana faɗin

"Innalillahi mama bata numfashi, bala ka fito da mota".
Cikin bacci ya faruk ke jiwo kururuwar ta, kasaƙe yayi dan yaji me take faɗi



Jin muryoyi daban daban ciki harda na Umma ƙarama(kishiyar umma b)
Yasa shi saurin miƙewa yana lalubar jallabiyar shi

Da sauri ya fito, jin furucin Umma babba da tace

"Wannan gawa ce ai, ba wani alamun rai a tattare da ita"



A sukwane ya faruk ya ƙarasa palon sunyi cirko-cirko, mummy da umma b na faɗin ta mutu,
Aunty da umma ƙarama na faɗin a tafi hospital dai.



Gaba ɗaya ihun mumtaz yasa ba'a jin komi, seda ya faruk ya waiga ya daka mata tsawa tukun
ta lafa da iface ifacen,

Jiki a sanyaye Amal ta rungume ta itama tana ta ɗigar da hawaye



Kutsawa wajen yayi gaban shi na dukan uku uku hannun shi ya saka a wuyan mama, jin da
alamun numfashi a tattare da ita yasa ya cicciɓe ta yayi waje da gudu yana faɗin



"Fito da mota Ahmad, tana numfashi"



Ɗiii, haka suka biyo shi harabar gidan



Kafin Ahmad ya ɗakko motar har bala driver ya fito da ita



A bayan motar suka saka mama,

Fuska a ɗaure umma babba tace

"Ai kwa tafi da mace ko?"



Ya faruk na ƙoƙarin shiga motar ya dakata tukun yace
"Wani ya shiga muje to"



Kafin umma ta gama rufe bakin ta Aunty tayi parcking kusa da motar ya faruk, tace



"Faruk kuyi gaba, zamu biyo bayan ku"



Jan murfin yayi ya rufe, bala yaja motar a sukwane suka fice.



Seda suka fice aunty tace

"Ku muje mana"



Fuska a ɗaure umma babba tace



"Kuje, ai ba'a bar gidan ba kowa ba ko?"



Ba wanda yace mata uffan a cikin su, mummy ta buɗe front seat ta shiga, umma ƙarama kuma
ta shiga baya suka ja suka tafi.



Zaman dirshen mumtaz tayi a compound ɗin taci gaba da kukan ta, duk da ba sauti kamar na
ɗazu

Amal ce a gefen ta tana ta fama rarrashin ta, se sakina itama daci kukan har ta koma ajiyar
zuciya.



Umma B na ganin Altine ta koma part ɗin mama tace

"Bari inje in saka Altine ta haɗa abubuwan da za'a iya buƙata a hospital ɗin, dan na san
dawowar ta ba yanzu ba"



Tana gama faɗin haka ta juya da sauri ta wuce sasan maman.
Umma b na wucewa sakina ta taɓe baki, tana binta da harara gefen ido, dan har ga Allah ta san
ranta fes ne da abinda ya faru ga mama.




Mumtaz na nan zaune, Amal tayi-tayi da ita ta tashi amma taƙi



Can dai kamar warce aka tsikara ta miƙe zumbur tabi bayan umma b da mugun sauri



Ilai kuwa, tana shiga ta iske ta titsiye altine tana tambayar ta ainihin abinda ya faru,
Altine nata inda-inda dan itama takamai mai bata san me uwar ɗakin nata ta gani ya gigitata ba,




Sosai Mumtaz tasha kunu, ido cikin ido ta kalli Altine tace

"Bani takardar"



Ba musu ta miƙa mata ta juya ta bar wajen kanta a ƙasa.



Sosai umma b ke kallon mumtaz da ta nuna kamar ma bata san da tsayuwar ta a wajen ba



Seda ta ɗauki wayar ta tukun ta haura sama zuwa ɗakin mama.




Kusan a tare da su Abba ƙ suka isa hospital ɗin,

Ba wani ɓata lokaci akayi emergency da mama, duk da dai ta farfaɗo, amma sambatun da take
yi ne ya ƙara rikitar da duk wani masoyin ta dake wajen




Tunda Abba ƙ ya ƙaraso wajen yake tambayar me ya same ta a ruɗe
A sanyaye ya faruk yace

"Calm down Abba, kar ku zama ku biyu mana"



Sam Abba ƙ ya kasa zama, kuma kowa a wajen yace be san musabbabin ciwon ba



Suna a hakan Abba babba da uncle Abbas(mijin mummy) da kuma uncle ƙasim(mijin aunty
suka shigo hospital ɗin

Suma same tambaya da Abba ƙ yayi suka yi, amsa ɗaya ce ba wanda yasan me ya faru.




A GIDA

Tunda Mumtaz ta karanta takardar nan ta sake shiga mugun tashin hankali,
Kukan kam tayi shi kamar ba gobe, tausayin iyayen ta kam ba'acewa komi, da ta tuna actions
ɗin mama lokacin data gama karanta takardar hankalin ta ƙara tashi yake

A sanyaye tace

"Duk randa ta gane ni kuma sata na fara ƙila mutuwa zatayi"

Ta sake rushewa da kuka me taɓa zuciya.




HOSPITAL

Dukkan su suna zaune dr ta fito daga ɗakin da mama ke a ciki, sam ba wani walwala a tattare
da ita

Cikin nuna damuwa tace

"who is her husband"

Kasa cewa komi Abba ƙ yayi, se idanu da ya fito da su waje, yana jiran yaji me zata ce



Jin ba wanda yace mata uffan se ma idanu da suka bita da shi yasa taci gaba da maganar ta
"patient ɗin ku taƙi yarda sam muyi mata allurar da zata samu bacci dan a samu ƙwaƙwalwarta
ta huta,
Jinin ta yayi mugun hawa, amma duk da hakan taƙi bari ayi mata abunda ya dace, so zaka iya
zuwa kayi mata magana maybe ta tsaya a temaki rayuwar ta"



Da sauri Abba ƙ ya tashi ya nufi ɗakin, drn kuma ta wuce office, a hankali ya faruk ya sakko
daga inda yake ya tsallake kowa ya shiga ɗakin shima



A rungume a ƙirjin Abba ƙ ya iske mama, ita kuka shi kuka babu wani me rarrashin wani a cikin
su

Daman abunda yayi tunani kenan shiyasa ya biyo bayan Abba ƙ ɗin



Kanshi a ƙasa ya ƙarasa kusa da mama ya zauna, murya a tausashe ya ce



"Mamana me yasame ki? nasan ke jaruma ce, kina tarban ko wani kalan ƙalubalen da ya riske
ki, kece kika koyar dani dauriya da kuma fauwala ma ubangiji komi, amma wannan kukan da
kike yasani cikin kokwanto da kuma fargaba me tarin yawa a cikin zuciya ta mamana"

Shuru yayi yana haɗiyar zuciya, dan shima gaf yake da rasa jarumtar shi,




Sakin Abba ƙ tayi ta juya inda ya faruk yake zaune kanshi a ƙasa



Hannuwan shi ta ƙanƙame cikin nata,
Cikin kuka tace



"Yarona, Mus'ab ya gudu ya bar gida, yace yayi nisan da bazamu taɓa samun shi ba
Wai ba ze iya ci gaba da zama a cikin gidan nan ba saboda muguwar azabar dake damun shi,
yace tafiyar shi itace mafi alkairi gare shi, dan kuwa wata rana ze iya aikata mugun abun da
Allah zeyi fushi da shi
yace baya ƙaunar gani na ko Abban ku sam, in ya ganmu yana jin zafi me ciwo a cikin zuciyar
shi"

Kasa ƙarasa maganar tayi, kuka me tsanani yaci ƙarfin ta
Ya faruk kam, banda maimaita kalmar "innalillahi wainna ilaihirraji'un" ba abunda yake



Mamaki da kuma tsoro na neman lulluɓe shi, a iya sanin shi, tun yana ƙarami yasha kama
mama na kuka a ɓoye, in ya dame ta da tambaya se tace mishi wani abunne ya faɗa mata a
idanu, tun yana yarda har yazo ya fara wayo ya gane waskewa kawai take.



A sanyaye ya faruk yace

"Mamana ke kika koyar dani kalmar "innalillahi wainna ilaihirraji'un, kikace in har na tsinci kaina
a cikin matsin zuciya in yawaita karanta "LA 'ILA HAILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU
MINAZZALIMIN da kalmar HAZBINALLAHU WANI'IMAL WAKIL"

Bema gama maganar ba mama ta hau maimaita la'ilahailla anta subhanaka inni kuntu
minazzalimin da sauransu



Gefe Abba ƙ yaja yana kallon ɗan ɗan'uwan nashi da kuma matar tashi



Kafin wani lokaci mama ta hau sauke ajiyar zuciya tana lumshe idanu alamun bacci nason
ɗauke ta.




SHARE PLS



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg11-12

Seda suka tabbatar da bacci ya ɗauke ta tukun suka fito daga ɗakin da niyar kirawo dr



Suna fitowa Abba babba yayi saurin tarbar su da tambayar ya mamar take



Ya faruk bece ma kowa komi ba,
Abba ƙ ke basu amsa da "Ta saamu bacci"



Direct office ɗin dr ya faruk ya nufa,

Be jima da shiga ba suka fito a tare zuwa ɗakin da mama take, seda ya tsaya komi da yake da
buƙata ya kammala kafin ya fito daga ɗakin, a lokacin su umma ƙ da mummy se aunty ne kawai
a wajen, mazan sun fice massalaci sallar la'asar



Fuska ba yabo ba fallasa yace

"Tace zaku iyw shiga ai Umma ƙ"



Da "to suka amsa duk fuska babu walwala.




Allah-Allah ya faruk yake ya isa massalacin kafin liman yayi sallama, in be kai ga isa ba aka
sallame tabbas shirin shi ba ze tafi a yarda ya tsara ba



Jin ana zaman tahiyar ƙarshe yasa ya ɗan haɗa da ɗan gudu-gudu har ya samu ya ƙarasa,

Daidai kuwa an sallame mutane an fara futowa



Gefe ya tsaya daga can yana hango iyayen na shi suna tawowa inda yake
Ganin Uncle Abbas ya tsaida Abba ƙ alamun magana zeyi yasa ya faruk ƙarasawa wajen da
sauri



Kanshi a ƙasa yayi musu sallama, sannan yace



"Ina son magana da ku tun ɗazu, to abun nan da ya faru yasa kawai na yanke hukunci daga
baya in komi ya lafa na sanar muku"




Dukkan su kallon shi suke, suna jiran jin me zece



Uncle Ƙasim yayi saurin cewa

"Mu koma daga cikin mota mana, akwai jama'a a nan, bakuma musan me sauraron mu ba"



Sunyi na'am da abinda uncle ƙasim ɗin yace, dukan su suka nufi parking lots inda ba hayaniyar
mutane



Abba babba yace "ihum, muna jin ka"



Kan ya faruk a ƙasa hannuwan shi duka biyun ya maida su bayan shi yace



"Akan tafiyar nan tawa ta zuwa china, to abun ya haɗe min biyu ne, su daga can aka samu
clashing ɗin time, alhalin na gama budget ɗin se na dawo daga Turkey akan maganar kayan,
har in huta kafin time ɗin tafiyar tawa china, to se jiya da daddare na samu email ɗin su akan
dawo da date ɗin da suka yi a jibi, to ganin kar ayi asarar kayan yasa nayi replacing sunan
mus'ab memakon sunan tunda shi yana da visar ƙasar,
A taƙaice dai na kaishe airport wajen 2:30pm, itace maganar dama"



Tunda ya faruk ya fara maganar Abba ƙ ke kallon shi da mugun mamaki, amma can ƙasan
zuciyar shi yana jin wani sanyi na ratsa shi duk da dai yasan haɗa maganar yayi
Kicin-kicin da fuska Abba babba yayi, ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, yace



"Ba haka ya dace kayi ba ai, ga Tk ai yana gaba da mus'ab kuma nasan shima yana da visa
ƙasar, shi ya kamata ka tura ba mus'ab ba"



Kan ya faruk a ƙasa yace

"Ayi min afuwa, nayi kuskure"



Shafa kanshi uncle Abbas(Baban Tk) yayi yace



"An maka afuwa, kaje abinka, Allah yayi muku albarka ya ƙara muku ƙaunar junan ku"



Da "amin" suka amsa dukan su, dai-dai ze wuce ta saitin Abba ƙarami ya faruk yace a hankali
yarda ba wanda zeji se shi

"Ka duba inbox ɗin ka Abba".




A wayance Abba ƙ ke karanta saƙon ya faruk inda yace

"Abba, mu bar maganar a haka saboda mama, kasan mata ba sa raina abun gulma ko habaici"



Murmushi Abba ƙ yayi ya maida wayar a gaban aljihun shi.



Sanda ya faruk ya koma ciki har su umma ƙarama sun fito da niyar komawa gida saboda shirin
buɗa baki, duk da dai ba wacce bata da me aiki a cikin su, bayan masu aiki ga kuma yara.



Mummy ce ta amsa mishi da

"Bata farka ba, zuwa bayan magrib mun dawo yamma tayi"
Da "to" ya amsa musu, suka fice shi kuma ya koma ciki.



Kallo ɗaya yayi wa mama ya gane sarai ba bacci take ba,



Murya a sanyaye yace

"Mamana"

Seda ya maimaita so biyu tukun ta buɗe idon ta da yayi ja kamar gauta,

Kujera ya ja ya zauna a gaban gadon,

Hawayen da suka taru a idon ta suka gangaro ta gefen idon

Shiru ya faruk yayi ya barta tayi me isarta, tkun yace



"Mama, kinji kinji......."

Tas ya kwashe maganar da ya faɗa ma iyayen shi maza ɗazu itama ya faɗa mata

Sannn ya ɗora da

"A bar maganar a haka mama, se muci gaba da addu'ar Allah ya karkato da hankalin shi gida,
sannan kuma zan ci gaba da duba shi lungu da saƙo na cikin garin nan dama kewaye, ni dai
babban buri na shine ki kwantar da hankalin ki mu samu jinin ki ya sauka, kar ki bari maƙiyan ki
su yi nasara a kanki mamana"



Shiru mama tayi, can ƙasan zuciyar ta tana maimaita kalmar "maƙiya" da ya faruk yace

Can dai tayi murmushi, ta kai hannu ta shafa kanshi tace

"Allah yayi maka albarka faruk, Allah ya baka mace tagari warce zata kular min da kai"



Murmushi kawai yayi, bayan ya amsa a can ƙasan zuciyar shi
Shiru ɗakin ya ɗauka, can mama tace

"Ahmad fa?"



Se a lokacin ya faruk ya tuna da wani Ahmad, in be mance ba tun da aka shigo da mama
hospital ɗin be tsaya ba, kama gaban shi yayi, irin ko a jikin nan nashi.



Da sauri ya faruk yace,

"Na aike shi ne".



Shigowar Abba ƙ ciki ne yasa ya faruk tashi yace



"Bari inje gida in tawo da Mumtaz se ta zauna dake"

Gyaɗa kai mama tayi, har ya kai ƙofa ya waigo yace



"Da me da me zance ta ɗakko?"



A hankali mama tace

"Ta kawo min dogayen riguna marasa nauyi, se phone ɗina"




"Okay" yace ya ja musu ƙofar ya fice".




Altine kawai ya samu a tana kaikawo a ƙasan



Gaisawa sukayi tana tambayar jikin maman,

Sama-sama ya amsa mata, tukun yace

"Mumtaz fa?"
Kanta a ƙasa tace

"Tana sama tun ɗazu"

Ko rufe baki batayi ba ya haura saman

A buɗe ya iske ƙofar, duk da a buɗe take be shiga ba seda yayi sallama tukun

Tana kwance idanun nan nata a kumbure, jin muryar ya faruk yasa ta miƙe da sauri, duk a
tunanin ta agogon shi ya biyo



Sarai yaga tsoron haka a tattare da ita, fuska a ɗaure kamar be taɓa dariya ba yace



"tashi ki haɗa wa mama kaya marasa nauyi, sannan kema ki ɗauki naki, five minutes na baki
zan je in dawo"



Har ya kai ƙofa ya waigo yace

"Ina takardar da mus'ab ya baki?"



Jiki a mace ta ɗaga pillow ta ɗakko takardar ta miƙa mishi.

Seda ya karanta tas ya ninke ya saka a aljihu, tukun ya kalle ta ido cikin ido yace



"wallahi, wallahi ko da wasa naji maganar nan a bakin wani se na baki mugun mamaki, nasan
ko na tambaya ko ban tambaya ba kin karanta abinda yake a ciki"



Yana gama faɗa ya juya ya fice.




Kamar warda ta sa ana gadin shige da ficen shi

Yana fitowa Amal tayi saurin isko shi tace
"Ya faruk Umma babba na kira"



Badan ranshi ya so ba ya juya zuwa sasan ummah b



Fuska a sake tace

"Wai me ya same ta ne faruk?

Kanshi a ƙasa yace

"Hawan jini ne wai"



Riƙe baki tayi

4 / 25