Author : ZAINAB FALALU Category : African Stories & Novels
daɗi yace
"Tun da akwai shedu har sama da mutum shida a ɗaura shi a yanzu kawai"
Abu kamar wasa ya zama gaske a take!!!
Da ƙarfi ya Ahmad yace "Allahu akbar"
Mama da ya faruk kusan a tare suka yi sujudushshukur, banada mumtaz data kasa ɗauke
idonta ga kowa dake palon.
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg65-66
Saɗaf-saɗaf Abba ƙarami ya tashi daga palon yayi sama,
Tsabar sauri bema san a bibbiyu yake taka matakalar benen ba
Yana shiga ɗaki ya kalli gabas ya kabbara sallah
Nafila yayi ta godiya ga Allah,
Acikin addu'o'in da yayi yake faɗin
"ya Allah ban taɓa tsammanin wannan abu ba, ada munso hakan amma ganin waɗanda
mukeyin dan su basu da ra'ayi, haka muka danne zuciyoyin mu muka haƙura, ashe akwai shirin
da kayi mana Allah, Allah na gode maka, kacika mana burin mu nida nagartacciyar matata
alokacin da muke tunanin an mana tozarci mafi muni a rayuwar mu,
Allah ikon ka ne kuma yardar kane ya rabbi, kai kayi mana kuma mun gani, Allah ka ƙara tsira
da aminci ga shugabanmu kuma masoyin ka annabi Muhammad"
Haka Abba ƙ yayi ta wa ubangiji godiya da wannan sauyi da yayi musu a lokaci ƙanƙani.
Mama na ɗagowa daga sujjadar datayi ta rungume ya faruk da shima ɗagowar shi kenan
Jin yarda jikin shi ke rawa yasa tayi ƙasa da murya tace
"Bi a hankali yarona, kar ka kunna kanka fa"
Dariya yayi, a karo na farko da kunyar mama ta kamashi a kaf rayuwar shi
Ƙeyar shi ta mangara sannan ta yunƙura ta tashi, har gaban Alhj sule taje ta tsugunna
Gwiwowinta a ƙasa haka zalika kanta a ƙasa tace "Nagode Baba, Allah ya ƙara girma, arziki da
wadata"
Murmushi yayi yace "Amin, Allah kuma yasa ace gara da akayi, ya kaɓe sharri da fitina"
Da "amin" ta amsa, sannan ta tashi.
Uncle Abbas na fita dama uncle ƙasim yabi bayan shi da sauri ganin abinda yayi be kyauta ba,
dan kamar raini ne ace mahaifin su na zaune dan ba'ai mishi abunda yake so ba se ya tashi ya
fice
Yana fita ya iske shi zaune a mota yana waya cike da tashin hankali a fuskar shi
Uncle ƙasim na ƙarasawa wajen yayi saurin datse wayar yaci gaba da muzurai yana wani ɓata
rai
Jinjina kai kawai uncle ƙasim yayi sannan yace "Yanzu ka kyauta abinda kayi Abbas?,
Ai ko baka ɗaga ma kowa ƙafa ba ka ɗaga wa Baba da shine silar zuwan ka duniya"
Cikin hargowa uncle Abbas ya fara magana daidai kuma Abba babba da ya faruk sun sako Alhj
sule a tsakiya zasu maida shi masaukin shi suka ji yana faɗin
"Ai ɗaya bayan ɗaya zan same ku, banda toshewar basira irin taku ai wani kusancin yafi wani,
kuma komin lalacewa kusanci na da Abubakar yafi kusanci shi da Aliyu"
Cak Alhj sule ya tsaya jin wannan furuci da uncle Abbas yayi
Kafin Alhj sule ya magantu, Abba ƙarami dake bayan su yace "ka tafka babban kuskure Abbas,
akan abinda be taka kara ya karya ba kake wani tada jijiyoyin wuya haka?
To bari kaji abinda baka sani ba, wanda kake cewa kafi kusanci dani akan shi, shi ya fara shan
nonon mahaifiyar mu kafin mu musha, haihuwar shi ce kawai inna batayi ba, amma tundaga
shayarwa zuwa raino, cin kashi da fitsarin shi duk itace
Sannan kuma abinda yayi mahaifiyar Aliyu shi yayi inna in baka sani ba na sanar da kai
Kuma wallahi inda inna zataji wannan furucin daga bakin ka tabbas da zaka ga mummunan
fushin ta"
Waigowa Alhj sule yayi yace "wannan bayanin ma ya ishe shi haka Abubakar, kuma har gobe
ina alfahari da jinin Bilkisu da Zainab(Bilkisu itace mahaifiyar Abba babba, zainab kuma
mahaifiyar su Abba ƙarami)"
Shiru uncle Abbas yayi yana muzurai har su Abba suka bar wajen shi yana nan tsaye.
Cike da fargaba mumtaz tace "mama haka ake ɗaurin auren wai?"
Daga mama har goggo safiya kwashewa da dariya sukayi
Goggo safiya tace "Kinga yardar ubangiji ko?"
Gyaɗa kai mumtaz tayi hawaye na sakko mata tace "wallahi kashi na ya bushe in dai da gaske
an ɗaura min aure da ya faruk"
Sakin baki suka yi suna kallon ta, goggo safiya tayi ƙarfin halin cewa "Kamar ya mumtaz, mudai
kiyi shiru kar ki janyo mana wata lukutar masifar bamu jima da fita a wata ba"
Mama kan kafe mumtaz tayi da ido tana nazartar ta.
Tsaki Ahmad yaja kafin yace "yo ya faruk befi wancan sakaran ba so ba adadi?"
Cikin kuka mumtaz tace "To wallahi baku san halin ya faruk ba, ku rubuta ku aje kullum se ya
narkeni tunda ba dena ɗauke-ɗauken nayi ba"
Gaba ɗaya jikin kowa yayi sanyi, harda shi kanshi ya faruk ɗin da dawowar shi kenan daga kai
Alhj sule masauki yaji ma kunnen shi.
Jiki a saɓule goggo safiya tace "Allah ze rabaki da ita in sha Allah, kema ki daure ki rinƙa kai
zuciyar ki nesa dan Allah mumtaz"
Shiru mumtaz tayi tana share hawayen fuskar ta,
Amma tsoro na nan danƙare a zuciyar ta, bayan tsoro ga tsananin mamakin wai an ɗaura mata
aure da ya faruk.
Murya ƙasa-ƙasa goggo safia tace "Ni ba kowa nake ji ba se tijararriyar uwar faruk wallahi"
Tagumi mama tayi kafin tace "babban damuwa ta da kikace a gaban ta akayi komi a can gidan"
can ta nisa tace "mu bar ma Allah kawai, kuma ina fatan zuciyarta tayi sanyi ta karɓi abun da
hannu bibbiyu".
Ɗan komawa da baya ya faruk yayi, kamar zuwan shi kenan yayi sallama
Da sauri mumtaz ta juya baya tana dafe ƙirji jin yarda gaban ta ya yanke ya faɗi
Yana lura da actuons ɗinta, basarwa yayi yace "mama ku taso na maida ku gida"
Kallon shi mama tayi cike da fara'a tace "su Abban naku fa?"
Yace "Alhj ya tsaida su duka"
Tashi tayi tace "ku muje to"
Ita ta fara fita sannan goggo safiya, se Ahmad dasu fadil
Mumtaz kuma ta tsaya neman warin takalimin ta da ya shige ƙarƙashin kujera
Duk tabi ta ruɗe jin kowa ya fita se ya faruk da ya rage
Daga inda yake tsaye yana hango takalmin, Daburcewar datayi ne ya bashi mamaki
Dan ya sake tabbatar da ta ruɗen ne ya matso kusa da ita ya tsaya ta bayanta
Da hannu ya zungureta, aikuwa a firgice ta juyo jikin ta na ɗan rawa
Da baki ya nuna mata inda takalmin ya shige
Da sauri ta janyo shi tayi hanyar fita har tana cin tuntuɓe da ƙafarshi
Karkaɗa kai kawai yayi tukun ya bi ya kashe wutar gidan sannan yaja ƙofar ya rufe ya ƙarasa
motar
Ganin mama zaune a gaba yasa ya ɗab waiwaya baya, can ya hango mumtaz maƙure a gefe
Be san sanda murmushi ya suɓuce mishi ba,
Duk abinda yake ta gefen ido mama ke kallon shi,
Farin cikin da take ji be misaltuwa dan rabon dataji irin haka ta mance.
Motar tayi tsit baka jin motsin kowa, dukansu da saƙe-saƙen da suke
Sun ɗanyi nisa kaɗan, jin shirun yayi yawa ya faruk ya kunna radio, rabi idon shi na titi rabi
kuma yana kan radio
Canza radion yayi da bluetooth sannan yayi searching waƙar Naziru "IN RABO YA TSARO DA
KAI, KUMA ABUN YA TABBATA DA KAI, RABBI NE YACE SE DA KAI EM SE DA KAI KAWAI
SEDA KAI...." har ƙarshe
Cikin shauƙi da annushuwa yake bin waƙar duk da a hankali yake bi amma hakan be hana
mama jin shi ba
Murmushi sam yaƙi barin fuskar ta.
Suna zuwa ƙofar gida yace "mama ba zan shiga ba nan zaku sauka akwai inda nake son zuwa"
Agogon motar mama ta kalla tukun tace "its late fa faruk"
Murnushi yayi tukun yace "Bazan jima ba ai"
Ganin mumtaz na son riga kowa fita yasa shi saurin faɗin "Mumtaz tsaya ke ki wuce da
wannan" yayi maganar yana wani faskewa
Ranƙwashi goggo safiya ta kai mishi haɗe da faɗin "algungumi, kaji dashi dai" ta fice, mama ma
na dariya ta fice
Suna fita ya saka lock a motar
Idin shi na kansu mama har suka shiga gate, sannan ya waigo ya kalle ta
Daga sama har ƙasa yake kallon ta, itakam taƙi yarda ko sau ɗaya ta kalle shi, ta takure a waje
ɗaya
Seda ya gama kallon ta tas tukun yace "Da kin shiga gida ki tabbatar da kin cire waɗan nan
kayan jikin naki, ki ɗauki naki na gida ki saka, ko da wasa kar in sake ganin ki da kayan da
wancan guntun ya kawo"
Mancewa ma tayi da tsoron ta saki baki tana kallon yarda ya faruk yasha mur yake bata umarni
Hannu ya kai ya tsokale mata manyan idanunta da sauri ta rufe idon da hannu haɗe da faɗin
"wayyo Allah"
Murya ƙasa-ƙasa yace "nan gaba ƙwaƙulo daƙwa daƙwan idanuwan zanyi tunda baki iya amsa
ni ba sedai ki kafe ni da idanu kamar ansoya tasoyu"
Murza idon take, amma hakan be hanata zumɓuro mishi baki ba
Murmushi yayi ya kauda idon shi tukun yace "jeki, shine saƙon dama"
Ko ƙarasa rufe baki beba tayi wuf ta fice, ki waiwaye batayi ba, tana tafe tana faɗin "daɗin abun
ma ai idanun ka sun fi nawa girma"
Seda yaga ta shige tukun yaja motar yayi gaba.
Wayar shi tayi ringing ya ɗaga yace "on my way" ya sauke yaci gaba da tuƙi.
A parking lot na gidan dr jamal yayi parking, direct ciki ya shiga inda ya iske mus'ab da dr jamal
na zaune ko wanne da yana ɗauke da mug me ɗauke da coffee a ciki
Yana shiga toilet ɗin palon ya shiga ya ɗauro alwala sannan ya fito
Anan palon ya kabbara sallar shi,
Ya jima yana addu'ar neman sassauci daga wajen ubangiji akan umman shi, haɗe da godiyar
kyautar da ya bashi a sanda ya riga da yacire rai gaba ɗaya
Seda ya gama tukun ya dawo palon ya zaune haɗe da cire hular kanshi yana faɗin "wash"
Cike da damuwa mus'ab yace "kun mayar da mumtaz ɗin ne?"
Karkaɗa kai yayi haɗe da kallon dr jamal ya ce "guess what?"
Girar shi biyu dr jamal ya ɗaga sannan yace "kasan im not a good a guessing abu, kawai mlm
ka gaya mana"
Murmushi ya faruk yayi yace "Da gaske nima yau ango ne"
A mugun bazata suka ji maganar, sedai basu yarda ba
Dr jamal tsaki yaja yace "karo na farko da naji kayi ƙarya kenan wallahi, Halan tsinko matar
akeyi a bishiya?"
Dariya kawai ya faruk keyi
Mus'ab da yasan waye yayan nashi yace "Sunyi galaba akan mu ko mu mukayi ya faruk?"
Tashi ya faruk yayi, ya zagaya ta side ɗin mus'ab yace " akoda yaushe Allah na bayan me
gaskiya mus'ab, a yau Allah ya mallaka min mumtaz a matsayin matar aure"
Da gudu mus'ab ya rungume ya faruk, tsabar murna da yarda yake ji ya hana shi magana,
banda "Alhamdulillah, Alhamdulillah" babu abinda yake faɗa, dan ya san babban burin yayan
nashi kenan, kuma babban burin iyayen shi.
Tasowa dr jamal shima yayi baki buɗe yace "are u for real guy?"
Gyaɗa kai ya faruk yayi, shauƙin abun na daɗa tasiri a ranshi.
Ɗakin da Tk yake kwance suka nufa
Yana nan a kwance kamar yarda suka aje shi
Ya faruk yace "Ina ganin ba zamu bari se da safe ba, kawai mu fitar da shi tunda abun yazo da
sauƙi"
Mus'ab yace "hakane, ina ta ganin calls ɗin uncle Abbas harda na uncle junaid ma, amma ba
wanda muka ɗaga daga baya ma kashe wayar muka yi"
Murmushi ya faruk yayi yace "su ya shafa wannan, mu saka shi a mota mu maida shi"
Su ukun suka cinciɓe shi sukayi waje da shi
A bayan motar da mus'ab ke basaja da ita aka saka shi
ya faruk ya shiga tashi motar, mus'ab da dr jamal suka shiga motar mus'ab ɗin suka fice kusan
a tare.
a inda suka ɗaukeshi nan suka koma, mus'ab ya ciro key ɗin motar TK ya buɗe, sannan suka
kamo shi suka saka shi a motar shi
Dr jamal yayi mishi allurar da zata dawo da shi hankalin shi cikin minti biyar, sannan suka bar
wajen gaba ɗaya.
****** Tunda su mama suka shiga gida goggo safiya ke rafka guɗa a tsakar gida
Irin guɗar nan me shiga kai har ƙwaƙwalwa
Da kusan gudu mama ta shige sasan ta dan ta san jan maganane goggo safiyar ke ƙoƙarin yi
Jama'ar gida jin guɗar taƙi ƙarewa yasa aka hau firfitowa, abinka dama da gida na a cike da ƴan
biki
Dangi su goggo safiyar ma tun kafin suji komi suka hau tayata da guɗar
Umma babba na ɗaka tana ba su ya sabiha labarin abinda ya faru a gidan su kalid suka jiyo
hayaniya gidan gaba ɗaya ya ƙaure da iface iface da guɗoɗi
Su ya sabiha hankalin su a matuƙar tashe jin mummunan labari daga mahaifiyar tasu suka
mimmiƙe, dan a yarda suke jiyowa kamar ma faɗa ne aje a wajen
Ya maryam ce ta banko ɗakin da gudu, ta ƙanƙame umma babba tace "Allah mun gode maka,
Allah ya kiyashe mu jin kunya duniya da lahira, ga goggo safiya can na faɗin an ɗaura auren ya
faruk da mumtaz yanzu"!
Wata wawiyar hankaɗa umma b tayi ma ya maryam har seda ta kusa wuntsilawa, a mugun
firgice tace "Na shiga uku na Nabila, waye ke shirin ganin bayana"!
Tayi hanyar fita da gudu!
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg67-68
Cikin zafin nama ya sabiha ta tare umma babba da gaba ɗaya idanun ta sun rufe tsabar tashin
hankali
Jiki na rawa ya sabiha tace "Dan girman Allah umma ki nutsu kar kije kiyi abinda zaki zo kina
nadama daga baya"
Ya maryam itama tace "ga gida bamu kaɗai ba, baka san waye ze tafi da kai a baki ba umma"
Ya fa'iza kam na ganin umman zata fice tayi wuf ta fice ta rufe main ƙofar palon da key tayi
gaba.
Cikin tsananin fushi umma b tace "sakeni sabiha kafin kiji mugun furuci daga bakina wallahi"
A hankali jiki a saɓule suka ja baya suka zuba mata ido
Yarda ta fito da zafin ta tana zuwa ƙofar palon taja tajita a garƙame
Kallon ƙofar tayi taga ta waje aka rufe
Fuuu ta koma ciki, a yarda ta barsu a haka ta iske su, zazzare musu ido tayi ta hau nuna su da
yatsa tace "ubanwaye a cikin ku yasa aka rufe ƙofar?"
Kusan a tare sabiha da maryam suka sauke ajiyar zuciya, sanin aikin fa'iza ne
Cikin tsawa umma tace "ba magana nake muku ba wai"
Nan ma a tare suka haɗa baki wajen faɗin "bamu sani ba umma"
Yaraf ta faɗa a kan kujera, tama rasa me zatayi, can ta zabura tace "Ku miƙo man wayata"
Sanin zata nemi wayar yasa suka kasheta suka ɓoye"
Kamar da gaske suka hau neman wayar
Sama ko ƙasa ba'a ganta ba, duk suka yi tsuru-tsuru ganin kallon da umman ke musu
Seda ta gama kallon su tsaf tukun tace "na gama gane rainin hankalin ku, to ku rubuta ku ajiye
ba zan taɓa yarda da wannan abun da akayi man ba, dama sun mallake man ɗanne dan sun
san abinda suka shirya ko?"
Da sauri ya sabiha tace "karkice haka umma, dan girman Allah ki nutsu kar ki kawo wani abu
can da be da alaƙa da wannan"
Da ƙarfi umma b tace "ku dakata man dan ubanku, na lura kallon mahaukaciya kuke man a
gidan nan, to bari kuji na jima da sanin faruk yana son mumtaz shiyasa tun wuri nayi ma tufkar
hanci na gargaɗe shi, da yake munafuki ne shima se yayi man wasa da hankali ya nuna min
bema san wacece mumtaz ba da har ze so ta
ohhh shine yanzu dan su nuna min ban isa ba yasa aka tafi can aka gama ƙulle-ƙullen tukun
zanji, banma ji daga matushiya me ƙarfi ba se a saƙar gari"
Gefe da gefen ta sabiha da maryam suka zauna
Cike da lallami suka fara nusar da umma b da gaba ɗaya ta gama haɗa zufa tsabar bala'i
Ya sabiha tace "Umma kar muyi ma ubangiji shishshigi a cikin ikon sa fa, wallahi tsanani akan
abunda akwai rabo yakan kai mutum ga kushewar sa fa"
Wannan maganar da ya sabiha tayi ta sake tunzira umma b,
Dole suka haƙura suka rabu da ita, haka tayi ta surfa bala'i a cikin ɗaki, su kuma suna gefe sun
zuba wa sarautar Allah ido
Amma fa sunyi babakere sun hanata fita ko nan da can.
****Da mamaki Tk ke kallon gari yarda yayi duhu
Da sauri ya janyo wayar shi dake yashe a kusa da shi ya danna yaga har sha biyu na dare ta
kusa
Da mamaki yace "Ahh gari da sauran haske fa na tsaya a wajen nan,
To bacci nayi ko me?
Bashi da me bashi wannan amsar,
Missed calls ɗin uncle Abbas dana uncle junaid har ma dana mummyn shi da ya gani tururu a
wayar shi ƙara bashi mamaki
Da sauri yayi dialing no ɗin uncle Abbas,
Kamar jira yake, ringing ɗaya tayi ya ɗaga, cike da zafin rai uncle Abbas ya fara surfa mashi
banbamin bala'i, shiru Tk yayi yana sauraron shi yana wani ɓata rai
Daga can uncle Abbas yace "To gidan ubanwa kaje ka ajiye wayar ina ta neman ka, kai duk
abinda aka haɗa da kai suka ba mutane matsala, kazo hotel ɗin da nake ka same ni yanzun
nan shashashan banza" be jira cewar shi ba ya kashe wayar shi.
A guje TK ya taka motar ya bar wajen, cikin ƙanƙanin lokaci ya isa hotel ɗin.
Ƙwanƙwasa ƙofar yayi, ko cire hannun shi beyi daga ƙofar ba akace "shigo"
Tura ƙofar yayi ya shiga, kanshi a ƙasa dan be san da wacce kuma uncle Abbas ɗin ze tarbe shi
Still kanshi a ƙasa ya samu waje ya zauna, muryar uncle junaid da yaji ne ya sashi saurin ɗaga
kanshi
Fuska a ɗaure Tk ke kallon uncle junaid da sam shima babu alamun rahma a tattare da shi
Ɓata rai Tk yayi yace "Banji me kace ba"
Miƙewa tsaye uncle junaid yayi, cike da hargowa yace "Ka sakar min ƴa nace!"
Dariyar gefen baki Tk yayi sannan yace "shine kiran dama?"
Daga gefe uncle Abbas yace "Dole ka saketa yanzun nan kafin mu fuskanci matsalar dake
shirin tunkaro mu"
Cike da hargowa uncle junaid yace "ni kam yanzu na haƙura da komi, kawai ka saka ɗanka ya
sakar man ƴa daga nan ku ƙarata can ku kuka sani, shekara da shekaru muna akan abu ɗaya,
har yau ba nasara, da munga alamun nasara lokaci kaɗan kuma muga akasin haka,
To ni na janye na fita a ciki tunda har abun na neman taɓa min gida"
Daga can gefe umma ƙarama ta cire nose mask ɗin fuskar ta, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tace
"Baka isa ba Junaid, tunda aka soma da kai to tabbas da kai za'a gama"!.
Bani kaina ba har Tk da ke zaune seda ya miƙe ganin warce betaɓa zato ba, da mamaki