LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU

Author :  ZAINAB FALALU Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 25

66K to 69K   out of 73.4K words

tana son aikenta

Da mamaki tabi palon da kallo ganin jini a ƙasa

Da ƙarfi mom ɗin sakina ta ƙwala wa me aikin kira

Jiki na rawa ta fito, rissinawa

Idon ta akan jinin tace tace "meye wannan daga ina?"
Matswa me aikin tayi, seda ta kalla da kyau sannan tace "jini ne hajiya"

Kafin ta sake magana me aikin tace
"kamar da ƙafa aka tako shi, naga har ta can wajen ma gashi can" ta nuna hanyar da tabi zuwa
ɗakin sakina"



Da mamaki mom ɗin sakina tabi takun jinin, har seda ya dangane ta ga ɗakin sakina

Da sauri ta taɓa ƙofar

Jin ƙofar a kulle kuma ta san bata rufe ɗakin ba yasa tace "waye a ciki?"

Shiru ba amsa

Juyawa tayi da sauri ta koma palon tace "waye ya shigo gidan nan?"

"ina ciki ina aiki banji shigowar kowa ba hajiya"

Fita mom ɗin sakina tayi waje har wajen gate ta ƙwala wa megadi kira ta tambaye shi, nan yake
gaya mata yaga shigowar sakina a firgice ƙafarta duk jini.



Da gudu ta koma ciki,
Ƙofar ɗakin sakina ta tsaya a tsorace take ƙwanƙwasa ƙofar haɗe da kira sunan sakina



Sakina najin ta amma tayi banza da ita

Seda ta gaji da bugawa tukun sakinar tazo ta buɗe

A kiɗime tace "me yasame ki?" ta hau dudduba jikin ta



Ba wani wata wata ko ɓata lokaci sakina tace "Druging ɗina yayi sannan yayi amfani da ni ba a
cikin hayyaci na ba" ta tsaya a nan

Ido waje mom ɗinta tace "se akayi yaya?"

"tsautsayi ya ɗebe ni na caka masa wuƙa"

Da mugun ƙarfi uwar ta aza hannu bisa kai tace "na shiga uku na lalace ni asiya!!! wuƙa fa kika
ce sakina?

A guje ta fita ta koma ɗakin ta, jikin ta na rawa hannun na karkarwa ta janyo wayar ta, uncle
junaid ta danna ma kira daidai lokacin suna tare dukkan su a inda suka saba haɗuwa

Har wayar ta gama ringing be ɗauka ba

Ta kira ya kai sau uku amma ba amsa, da gudu ta sake komawa ɗakin sakina da har yanzu
tana a tsaye abin duniya ya ishe ta "ɗakko gyalen ki mu je"



Daƙilewa tayi a tsorace tace "ina zamuje mom?"

Falla mata mari tayi tace "dan ubanki har kina da bakin tambaya ta, to bari kiji wallahi in har kika
bari akazo aka ritsaki anan to kashin ki ya bushe"



Ba sake cewa komi ba banda fizgar ta datayi suka fice

A guje mom Asiya taja mota suka bar gidan.



*****Ya faruk na zaune a gaban Abba ƙarami call ɗin dr jamal ya shigo wayar shi,

Ɗagawa yayi, daga can dr jamal yace "sun iso fa, case ɗin babba ne wallahi, wuƙar ta shiga
cikin sosai fa"

Murya can ƙasa ya faruk yace "ban fa sanar ma kowa ba a gidan, amma bari na gaya wa su
Abba yanzu"

Da haka suka yi sallama.




******Har aka fito da Tk daga theater ba uncle Abbas ba dalilin shi

Hankali ya tashi ƙwarai da kowa yaji labarin abinda ya samu Tk, dama zargin da ake na sakina
ce tayi hakan, dan labarin bata gidan ya baɗe ko ina,

Ga mom ɗinta a gefe da take ta pretending kamar itama bata san inda sakinar take ba, alhalin
ita ta kaita ta ɓoye ta.
Wajen goma saura su Abba babba da ƙarami dama su goggo safiya, harda su mama da su
mummyn Tk suka koma gida, aka bar Amir ya kwana da shi.



Ta ɓangaren su uncle Abbas kuwa sun ƙagara lokacin ya cika,

miƙewa tsaye umma ƙ tayi, gyara lulluɓin ta tayi sannan tace "zanyi gaba se kun iso, zuwa
yanzu na san sun gama taron shirmen su"

Gyaɗa kai sukayo duka, duk sun bi sun ƙagara

Uncle junaid yace "nan da 30mins muna hanya muma"

Da haka sukayi sallama.




*****
Sanda suka shigo gida daga asibiti ba kowa a baƙi,

duk wanda ka gani ɗan gida ne, kowa sasan shi ya nufa, ga gajiyar hidima ga kuma gajiyar
tsayuwar hospital da sukayi



Abba ƙarami na zaune a palon shi bayan yayi wanka ya kimtsa mama ta kawo mashi tea,

Tana zaune a gefen shi suna firar abunda ya faru da Tk wayar shi tayi ringing

Mama tafi kusa da wayar, yunƙurawa tayi ta ɗakko, sunan Abbas ta gani a rubuce

Da sauri ta miƙa mishi haɗe da faɗin "ƙila se yanzu yaga calls ɗin da akayiyyi masa"

Gyaɗa kai Abba ƙ yayi haɗe da kara wayar a kunne

Duk a tunanin shi maganar Tk ze mishi, se yaji saɓanin haka



Da mamaki Abba ƙ ke sauraron shi, can dai yace "ba matsala ku ƙaraso ina palo na"

aje wayar yayi ya kalli mama yace "ki ɗauki mayafi su Abbas na shigowa"
Babban hijabi ta ɗora akan kaya jikin ta sannan ta koma ta zauna.



Kamar wasu mutanen kirki, uncle junaid da uncle Abbas sukayi sallama suka shigo, ɗauke da
wasu files a hannun su

Amsa sallamar sukayi

Da fara'a Abba ƙarami yace "bisimillah ku zauna mana"

Zama sukayi a kujerar dake kallon tasu

Kafin suce komi ya faruk yayi sallama ya shigo

Da sauri uncle Abbas ya kalli uncle junaid sannan suka kalli ya faruk dake murmushi kanshi
tsaye ya ƙaraso ciki

Basu gama mamakin ganin ya faruk ba se ga uncle ƙasim shima ya shigo goggo safiya biye da
shi a baya



Daga mama har Abba ƙ tsoro ne ya fara kamasu, ganin basu jima da rabuwa ba ai

Baki sake su uncle Abbas ke kallon su

Can suka jiyo ya faruk na faɗin "muna palon saman shi Abba babba"

Miƙewa Abba ƙarami yayi yace "wai lafia?"

Daidai shigowar Abba babba kenan shima ya ɗora da tashi tambayar "me ya faru kuma?"

Uncle ƙasim yayi karaf yace "Ku zauna mana, tunda kuka ga haka ai da magana ne"



A take uncle junaid ya fara jin tsintsinkewar zuciya
se wani mutsu mutsu yake kamar me basir.

Ɗaya bayan ɗaya sauran matan gidan ke shigowa harda manyan ƴaƴan

Kowa ya shigo se yayi turus yabi kowa da kallo kafin ya zauna

Ashe ya faruk ne yabi kowa da kowa ya tura mishi saƙon yana son magana da shi ta sirrin a
palon Abba ƙarami misalin ƙarfe goma da rabi.
Babu wanda yasan da an turawa ɗan'uwan shi saƙon, shiyasa duk wanda ya shigo se yayi
mamaki

Umma ƙarama ce kawai be turama ba, saboda itama yasan zata zo kodan shirin su.




Kowa ya nutsu ya zauna, cikin faɗa Abba babba ya kalli ya faruk yace "kai bana son shashanci,
meye haka ka wani tara mu anan kamar wasu sa'o'in ka?"

Kafin ya faruk yace komi, uncle junaid ya miƙe haɗe da faɗin, "ina jin abun na family ne, nikam
bari naje gobe na dawo muyi maganar data kawoni"

Karaf uncle ƙasim yace "ta shafe ka mana, aikama ɗan gidane, zaka iya zama"

Musu yaso yayi, amma amma ganin mus'ab ya ɗaga labule ya shigo haɗe da sallama yasa ya
tsaya cak, kamar yarda zuciyar shi data uncle Abbas ma ta tsaya.



INA MATUƘAR GODIYA DA ADDU'O'IN KU GAME DA ƁATAN ƘANWATA

ALHAMDULILLAH, KUMA TA DAWO LAFIA

MASU KIRA DA MASU TURO SAƘON JAJE DA ADDU'A ALLAH YA SAKA DA ALKAIRI,
MATSAYIN KU NA DABAN NE,

ALLAH YA BAR ZUƁUNCI

ALLAH YA TSAREMU DA TSAREWAR SA ALFARMAR ANNABI MUHAMMAD

INA MATUƘAR KAUNAR KU ❤️

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg82

Hannun Abba ƙ na karkarwa ya nusa mus'ab da ya bar ƙasumba sosai a fuskar shi yace
"Mus'ab!"

Cike da rauni mus'ab ya ƙaraso inda Abba ƙ yake ya rungume shi



Kowa mamakin ganin mus'ab yake a wannan lokacin duk da sun san cewa baya ƙasar(in baku
mance ba haka ya faruk ya faɗa ma kowa)



Abba babba yace "saukar yaushe mus'ab?"

Jin abinda Abba babba yace shine ya dawo da tunanin Abba ƙarami shima ya basar



Shigowar mummy(matar uncle Abbas) kenan ta ga uncle Abbas zaune,

Batayi tunanin komi ba ta ce "Dama kana nan nake ta faman kiran ka baka amsa min ba?"



Kallon ta kawai yayi amma ya kasa ce mata komi

Goggo safiya tace "ki zauna mana, ƙila wani abun ne ya tsare shi, tunda Allah ya taƙaita wahala
ai da sauƙi"

Taɓe baki mummy tayi kafin ta samu waje ta zauna.



Ta gefe kuma uncle junaid se zungurin uncle Abbas yake da ƙafa, shima yana zungurinnshi

Duk ya faruk da uncle ƙasim na lura da su.
Cikin ƙagara Abba babba yace "wai meke faruwa? wannan gangankon namene?"



Kai tsaye ya faruk yace "Na uncle Abbas da uncle junaid ne, se kuma umma ƙarama"



Da mamaki kowa ke kallon ya faruk, har da su waɗanda aka ambata ɗin



Cikin faɗa uncle Abbas yace "ohhh rainin da kayi wa kowa shine har ya fara gangarowa kaina
nima?"

Murmushi ya faruk yayi sannan yace "ku gafarce ni da abinda zan faɗa yanzu"

Tsuru kowa yayi yana sauraron ya faruk da ya shafa ma idanun shi toka ya ɗora da

"Abba ƙ ina neman alfarmar ka bar su uncle junaid da uncle Abbas gabatar maka da abinda ya
kawo su kafin akai ga jin komi"



Ɓata rai Abba ƙ yayi yace "meye haka kakeyi ne faruk?"



Kafin ya faruk ya ce komi uncle ƙasim yace "ya kamata su faɗi abinda ya kawosu a gaban kowa
da kowa a irin wannan lokacin"

Nan ma kallon kowa ya koma gareshi.



Cike da tsantsar rashin gaskiya uncle Abbas yace "me kuke nufi da hakan, ko kuna tunanin
wani mugun abunne ya kawo mu?"

Ba wanda yace mishi komi, Abba babba dai yabi kowa da kallo yana so ya tantance abinda ke
shirin faruwa"

Cike da rashin gaskiya ya hau buɗe files ɗin gaban shi, amma rawar da hannayen shi keyi sam
yakasa samun sukunin iya riƙesu da kyau.



Miƙewa tsaye mus'ab yayi, seda yayi ma kowa sallama kafin yace "A dena wani ɓoye ɓoye so
muke su uncle Abbas su fayyace mana meyasa suke cin dunduniyar ahalin Abba ƙarami!"
Mus'ab na gama faɗin haka aka hau kallon kallo

Nan da nan zufa ta rufe su uncle Abbas duk da sanyin aircon dake aiki a palon



Cikin ɓacin rai Abba ƙarami yace "baka da hankali ne mus'ab, waɗan nan ba iyayen ka bane
kake faɗin irin wannan munanan maganganun akan su?"



Shiru mus'ab yayi yana ci gabaa da haɗiyar zuciyar gado



Uncle ƙasim da shima fuskar nan a cukune take yace "tunda ba zasu ce komi ba, bari mu kawo
wanda zeyi ma kowa bayani"



Abu ya fara ɓaci fa, zama na neman gagarar su uncle junaid gaba ɗaya

Umma ƙarama kam saita ƙofa kawai take, dan ba zata taɓa tsayawa ta kunyata ba.



Kafin kowa ya dawo daga duniyar mamakin da suka shiga uncle ƙasim ya shigo da Altine da
idanun ta suka kumbura tsabar kukan data sha



Wiƙi wiƙi su umma ƙarama sukayi

Kunsa mara gaskiya ko a ruwa jiɓi yake.



Tallaƙe ƙeyar ta yayi sannan yace "munafuka faɗa ma kowa abinda kika shuka kafin na fasa
kanki"



Cikin kuka Altine ta kalli mama da gaban ta banda dukan tara-tara babu abinda yake tace
"ku yafe man hajiya, Wallahi duk abinda nayi maku ba da son raina bane, a bisa tirsasawar
hajiya sumayya(umma ƙarama) ne da kuma waɗanda ban sani ba wallahi"

Dafe ƙirji umma ƙarama tayi haɗe da faɗin "ku ji man wani sharri da tsohon daren nan, ina fatan
ba dai ni sumayyar kike nufi ba??"
Ido rufe Abba babba yace "dakata hajiya sumayya!"

Tsit umma ƙarama tayi ta koma zaro idanu

Altine taci gaba "wallahi da zuciya ɗaya na nemi aiki a gidan nan ba dan na cutar da kowa ba,
wata rana ina ƙasa a kitchen mama tace na ɗan fara ɗora mata ruwa a kan gas kafin ta sakko,
sega umma ƙarama ta shigo sasan ta iskoni har cikin kitchen tace min "kizo anjima da daddare
ki same ni, akwai maganar da nake son yi da ke"
tana gama faɗa min haka ta juya ta fice da sauri jin sakkowar mama daga sama.

Ban kawo komi a raina ba naci gaba da aikina, amma can ƙasan raina murna nake ƙila wani
abun zan samu daga wajen ta tunda ta saba min alkairi haka kurum.

Da nagama aiki na, kusan kowa ya kwanta na tashi naje na sami umma ƙarama a ɗakin ta

Maganar data fara min ba ƙaramin gigita ni tayi ba da naji tace aiki zan mata bakin raina

a tsorace nace "wani kalar aiki ne haka hajiya?"

Dariya tayi tace "ba wani aiki bane me yawa, hasali ma ba ze ɗauke ki minti biyar ba kin gama,
amma fa se kin sa kanki"

Kaina a ƙatsa nace "to hajiya, ina jinki"

Wani ƙulli ta ɗakko a takarda ta miƙo min, murya ƙasa-ƙasa tace "so nake ki zuba shi a abincin
Abba ƙarami, shikenan kin gama aikin ki, ba abinda ya rage sedai kija bakin ki kiyi shiru"

A firgice na saki ƙullin a ƙasa na miƙe tsaye, jiki na yana rawa nace "bani ke girka mishi abinci
ba umma ƙ, mama da kanta ke dafa mashi"

Tsugunnawa tayi ta ɗauki ƙullin sannan tace "kin yi babban kuskure tunda har kikaji sirrin mu,
kuma dole kiyi abinda nace ko kuma ki baƙunci lahira"

Na tsorata matuƙa da naji haka, a taƙaice dai dole tasa na karɓi maganin nan da niyar in anjera
wa Abba ƙ abinci a dining in fakaici ido na zuba mashi" ba yarda na iya haka na karɓa na fito
hankali na a tashe"

Shiru Altine tayi tana share hawayen ta,

Kaf mutanen dake palon banda kallo-kallo babu abinda suke aika ma junan su,

Umma babba kanta jin maganar take kamar a mafariki, dan bata taɓa tunanin hakan ba.
Goggo safiya tayi karaf tace "ci gaba algunguma'

Kan Altine a ƙasa ta cigaba "seda maganin yayi kusan wata a hannun na ban zuba ba,
Kuma a lokacinne nayi yunƙurin barin aiki, amma ga mamaki na se ganin umma ƙ nayi ita da
wani sun zo har cikin ɗakina sun min kakkausar gargaɗi akan duk inda naje se sun ga baya na

Ba shiri washegari na samu sa'a na zuba mishi maganin a cikin abincin,

Tsautsayi kuma a ranar Abba ƙarami be dawo ba,

Mama da kanta tace mumtaz ta ɗauki abincin ta kaiwa masu gadi,

Da naji haka shine nayi sauri na kwashe abincin na kai kitchen da niyar zan fakaici ido in zubar
dan kar wani yaci ya cutu,

kiran da mama tayi min kafin na zubar da abincin yasa har mumtaz ta shiga ta ɗiba taci

Ganin babu wani abu da ya same ta yasa hankali na kwanciya, amma duk da haka ban bari
wasu sunci ba na zubar da abincin.

Daga wannan ban san komi ba, seda aka jima sannan na fara ganin sauye-sauye a cikin
halayyar mumtaz da yasa na rinƙa bin diddigin ta dan nasan meke damun ta, amma bam samu
komi ba"

Tsit palon yayi baka jin motsin kowa sedai fitar numfashi na wasu yafi na wasu.



Abba ƙarami zuguɗin yayi yana kallon umma ƙarama dabkanta ke sunkuye takasa haɗa ido da
kowa har ƴaƴan ta da ke zaune hankalin su a mugun tashe.

Kafin kowa ya samu zarafin magana Ahmad ya taso ƙeyar bokan da ya faruk ya kamo tuntuni

Suna shigowa uncle Abbas ya miƙe tsaye da sauri haɗe da faɗin "na shiga uku"



Abba babba yace "waye kuma shi wannan"?

Kafin kowa yace komi bokan nasu yace "ni malamin hajiya sumayya da Abbas da kuma junaidu
ne"

Gaba ɗaya wajen suka hau faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!"

Dafa ƙirji goggo safiya tayi tace "yau ko munga lukutar masifa a cikin gidan nan, kai jama'a ana
zaton wuta a maƙera yauko gata mun ganta a masaƙa"



Gyaɗa kai umma babba tayi sannan tace "humm danƙari!!"



Fuska a ɗaure ya faruk yace "maƙiyin Allah, zauna ka gaya ma kowa abinda suka saka ka kayi
wa bayin Allahn da basu jiba basu gani ba"

Shima kanshi a ƙasa yace "Hajiya summaya itace ta haɗani da Abbas da junaidu inda suka
kawo min aiki na suna so a dankwafar da cigaban Abba ƙarami,

Dana buga ƙasata na gano cewa ba ta yarda za'ayi nayi kutse a lamuran shi sedai abi wata
hanyar

A take na fahimtar da su hakan, se suka ce min bari suyi shawara su dawo

Ina zaune suka fita, basu jima ba suka dawo, se ɗaya daga cikin ƴan mazan yace "tunda har
kace hakan ba ze yiwu ba, muna so ka kawar da hankalin ƴaƴan shi maza daga kan dukiyar
shi, sannan ka saka musu rashin jituwa tsakanin su da iyayen, shi kuma Abba ƙarami a saka
mishi halin ɓeraye gashi dai me arziƙi amma ya rinƙa sha'awar duk wani abu da ya gani a
hannun abokan kasuwanci, haɗe da muguwar azalzalar zuciya, yaji in be ɗauka ba ze iya rasa
ranshi.

Shine na basu magani nace a saka mashi a binci, daga nan shikenan.

Daga baya suka dawo min da zancen basuga yana komi ba, dan har gwada shi sunyi amma
basu ga komi ba

Dana bincika se na gano beci maganin ba, ɗaya daga cikin iyalan shine suka ci

Danayi musu bayani se suka sauya wata shawarar na cewa a kawar da shi.

nayi-nayi, amma Allah be ban sa'a ba, amma anci nasara da raba shi da ƴaƴan shi,

Se kuma in zasuyi abu nakan duba musu na faɗa musu lokacin da yafi dacewa su aiwatar da
abinda suke so, amma daga wannan wallahi babu wani abu da nayi, se wanda hajiya
sumayya(umma ƙarama) ta dawo ita kaɗai ta nemi alfarmar in mallake mata Alhj junaid da kuna
shi Alhj Abbas, akan duk wani abu datace mu suyi, to zasuyi shi kai tsaye ba tare da sun mata
musu ba"

Salati me ƙarfin gaske umma babba da goggo dafiya suka ɗauka
Sunayi suna tafa hannuwa

Mazan kam gaba ɗaya kansu na a ƙasa, bama kamar Abba ƙarami da gaba ɗaya rufe idon shi
yayi ƙam yana jin ƙirjin shi na mishi nauyi.



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg83

A tsananin firgice mama ke kallon uncle junaid da kanshi ke ƙatsa, zufa tayi mishi sharkaf

Kukan mummy ne ya dawo da kowa daga ɗimuwar da ya tafi

Cikin kuka ta cukumi kwalar uncle Abbas tace "butulu maƙiyin Allah, dama zaman haƙuri nake
da kai saboda baƙin mugun halin ka, wallahi ko ka sakeni ko ka tsammani sammaci daga kotu
inda zanje in tona maka asiri wallahi"



Duk zafin uncle Abbas kasa cewa komi yayi, jikin shi har wani rawa-rawa yake



Tashi uncle ƙasim yayi ya shiga tsakanin su

Da ƙyar aka ɓanɓare mummy daga jikin shi, ƙin zama tayi ta fice cikin kuka da nauyin zuciya.

Haka mama, kukan da take ta dannewa ta kasa seda ta sake shi, still idon ta na kan uncle
junaid da ya kasa kallon ta sam.
Abba babba shima ya kasa cewa komi tsabar yarda abun ya dake shi har cikin ƙwaƙwalwa



Gaba ɗaya wajen ma hautsinewa yayi, kukan ƴaƴan umma ƙarama gunin ban tausayi, Ya fa'iza
faɗi take "umma ƙarama kin cucemu innalillahi wainna ilaihirraji'un".



Kai tsaye ya faruk yace "Ku gafarce ni Abba,

23 / 25