Author : ZAINAB FALALU Category : African Stories & Novels
yayi ya ɗaga hannuwan ta
Ya ɗanyi mata cakulkuli yaga ko motsawa batayi ba
Sake ɓaɓɓaka wata dariyar yayi sannan yace "an gaya maki kowa sakarai ne irin ki, ai ko zan
sake ki bazan bari ki tafi hakanan ba ya mori sadaki na ba"
Hmmmm!! daga nana labari ya sauya,
Tk dai ya saɓa alƙawarin da suka yi shi da sakina
A daren ranar ya hakke ma sakina da sam bata cikin hankalin ta.
Abun da Tk yayi ya wuce hankali sam,
Kusan zamu kira abun da fyaɗe kai tsaye
Tunda ya gama hankalin shi ya dawo jikin shi yabar ɗakin ya koma nashi ɗakin yayi kwanciyar
shi nan da nan bacci yayi awon gaba da shi.
Asubar fari sakina ta farka daga mugun baccin datayi,
Jan ƙafarta na farko datayi ya tabbatar mata da ba haka ta kwanta ba
Da ƙyar da dabara ta tashi zaune, alamomin data gani da kuma tsantsar azabar da take ji ya
tabbatar mata da abinda Tk yayi mata
Hankali a tashe ta samu ta lallaɓa ta sakko daga kan gadon, sam tsayuwa na neman gagarar ta
Tana tsaye dafe da bango Tk ya buɗe ɗakin ya shigo
Ido cikin ido sakina ke kallon shi
Tsabar yarda take jin bushewar zuciya yasa idanuwan ta bushewa ƙamas
Da ɗan sauri TK ya matsa kusa da ita
Cike da duniyanci yace "ashe kin tashi amarsusu"
Maganar shi ji tayi kamar ya daɓa mata wuƙa a ƙirji
Yarda take jin zuciyar ta kamar ta shaƙe shi har se ya dena motsi
Matsowa yayi daf da fuskar ta yace "kin ɗauka kowa ma wawa ne irin ke da ubanki?,
Be jira cewar ta ba ya ɗora da "in ma zakiyi ɗammarar zama dani to kiyi, in ba haka ba ke zaki
wahalar da kanki a banza a wofi?" Yana gama faɗin haka ya juya yayi ficewar shi ko duba da
yanayin datake a ciki beyi ba ya balle ya temaka mata.
Tk na fita sakina ta durƙushe a wajen ta fashe da kukan baƙin ciki
Karkuce kuka na hankali, kuka take na fitar hankali da kuma tsanar duk wani wanda ya shafi Tk
Cikin hargowar kuka tace "wallahi, tallahi sekayi mugun danasani na wannan aika aikar da kayi
min".
A ranar seda sakina tasha baƙar wahala kafin ta samu kanta.
Ta can ɓangaren su mama kuwa ana ta shirye shiryen miƙa mumtaz gidan nata mijin
A hankali kamar kuma da wasa gida ya fara cika kamar ba last week akayi biki ba
Duk da gidan be kai ko tabin cikar wancan taron ba, amma ba laifi ƴan'uwa nata halartowa
domin shedawa da idanuwan su
Abun har yaso ba kowa mamaki
Da safe wajajen sha ɗaya saura warce zata yi wa mumtaz kitson amarci ta iso
Kun san dai gwanar taku basa shiri sam da kitso
Seda mama tayi kamar zata maketa kafin a gama kitson
Ana gamawa me ƙunshi tazo, ta yarfa mata shi a farar fatar nan,
Masha Allah, ba'acewa komi.
Ya faruk kam ya bar mus'ab da uncle ƙasim wajen tsare bokan su uncle Abbas, shi yana can shi
da su ya sabiha da ya maryam wajen haɗo wa mumtaz kayan da zatayi fitar buɗar kai da umma
babba da kanta ta shirya hakan a gobe kafin ango ya ɗauki amaryar sa su tafi.
Sosai umma babba ta sanar da taron buɗar kan babban ɗanta a gobe
Duk wata ƙawar ta da tai tasan da zaman taron a gobe
Haka mama ba'a barta a baya ba, itama ta gayyaci ƙawayen ta sosai
Wasa wasa, gida ya kacame da sabuwar hidima.
Su umma ƙarama da sauran sun samu kwanciyar hankali tunda sukaji abinda bokan nasu ya
sanar da su
Haka itama umma ƙarama ta saki jiki sosai a ka shiga hidima da ita harda ƴaƴan ta ba'a barsu a
baya ba.
*****Khalid
A fusace mami ta tura ƙofar ɗakin shi ta shiga
Kamar koda yaushe yana kwance idon shi a rufe duk da ba bacci yake ba
Bakar shi tayi a ƙafa ya buɗe idanun shi da suka kaɗa sukayi jajir
Jiki a sanyaye ya tashi zaune yace "lafia mami?"
Galla mishi harara mamin tayi tace "wallahi khalid na gaji da wannan halin da ka tsirar ma
kanka,
Tunda kaji labarin an aura ma yarinyar nan ɗan'uwan ta ka wanu susuce ka fita hayyacin ka,
Ina kai ka sake ta da kanka ba wanda ya saka ka?"
Shiru kalid bece komi ba kanshi a ƙasa
Mamin ta ɗora da "wallahi na gaji to, ka dena fita sam, aikin ma ka dena zuwa, abinci se nayi da
gaske kafin kaci saboda ka ɗora ma kanka wahalar banza data wofi
Shiyasa tun farko nace karka sake ta, kawai dai zaka nemi warce zata haifa maka ƴaƴa na gari
amma bance ka sake su ba,
Dole ko ka ƙi, ko ka so kacire ta a ranka tunda har Allah yasa ta zama mallakin wani, kuma mu
gode wa Allah ma ba seda aka fara tara ƴaƴa ba tukun muka san halin ta
Gwara da aka sani tun wuri"
Can kuma ta sausauta murya ta koma rarrashi.
Tun ranar da mumtaz ta ɗauki wayar goggo safiya tayi mishi msg khalid ya rasa sukunin kanshi
bayan ya karanta saƙon ya biyo da kira, a lokacin wayar na hannun ya faruk, nan kuwa ya karta
mishi warning me zafin gaske da fayyace mishi abubuwa da yawan gaske a game da satar da
mumtaz keyi
Da yake yayi nisa bejin kira yasa yace "ai da bayani za'aimin tun farko na fahimta ba wai kaje ka
aure min mata ba"
Ya faruk be wani tsaya ya saurare shi ba ya kashe kiran haɗe da blocking number shi daga
wayar goggo safiya.
*****RANA BATA ƘARYA..
Tunda garin Allah ya waye masu decoration suka iso
Gidan yana da girman gaske kamar yarda na faɗa a baya
Shiyasa zeyi wahala in ana biki kuga sun fita wani waje da sunan kama hall.
Ma sha Allah su ya sabiha sun tsaya tsayin daka wajen ganin komi ya kammalu
Ba ƙarya an shirya wajen yayi kyau matuƙa
Baloons ɗin da akayi kwalliyar wajen da su su kansu abun kallo ne
Kala uku sukayi using, sky blue, baƙi se fari
Haka kujerun wajen gaba ɗaya farare ne, se ɗan kwalliyar baƙi da sky blue a saman teburin
Ko wani teburi da sunan wanda ya dace ya zauna a wajen
Side ɗin abokan ya faruk daban abokanan umma babba daban sanan na mama daban
Se wajen da ango da amarya zasu zauna shi kanshi wajen abun kallo ne,
Sannan wajen da ƴan'uwa da abokan arziki da zasu zauna daga can gefe.
Mumtaz kam bata gayyaci ko mutum ɗaya ba acewar ta ai biki ɗaya ne.
Tun kafin azzahar me makeup ɗin da zata yi wa mumtaz ta iso, wannan karon babu wani cewa
banaso, da kanta tace "ki tsatso ni infi kowa fita fa"
Yarda tayi maganar seda taba kowa dariya a wajen
Ita kanta seda ga baya taji kunyar abinda tace.
Abun mamaki umma babba itama musaman ta sa aka kira mata me kwalliya har gida.
Ta can ɓangaren yaya faruk shi zamu iyacewa taron shi ya fi na kowa,
Tunda ba ɗaurin aure, shiyasa ya yi gayya sosai wannan karon
Gaba ɗaya abokab shi wankan blue shadda sukayi se baƙin takalmi da baƙar hula
Shikuma yayi wankan farar shadda ƙal da baƙar hula.
Ma sha Allah, ku hango tsarin da kanku ku gani 😊
Biyar saura wajen ya ɗinke sosai da mutane,
shigowar iyayen amarya da ango ake jira sannan shigowar amarya da angon.
Mamace ta fara isowa bayan MC ya sanar da shigowar ta, tana a tsakiyar ƙawayen ta da ko
wacce ka kalla zaka san nera ta zauna ba ƙarya
Gaba ɗaya maman wankan blue black lace tayi ta amsa sunan shi.
Seda suka sami waje suka zauna, sannan MC ya sanar da shigowar hajiya umma babba da
nata tawagar
Ba ƙarya itama itama a tsakiya suka sako ta, bakin nan nata kamar gonar audiga saboda fara'a
Wankan ta itama yayi kyau ba ƙarya, inda ta saka farin lace me ratsin baƙi a jiki
Itama ta samu waje ta zauna.
Seda kowa da kowa ya nutsu ya zauna sannan MC yayi sanarwan shigowar ya faruk da
mumtaz da har yanzu ya faruk ya kasa yarda cewa ita ce saboda yarda shigar fari da baƙi yayi
mata masifar kyau
Da gudu ya sabiha ta ƙaraso da sky blue ɗin net sharara ta rufa wa mumtaz akan goggoron ta,
sannan tace "yes, zaku iya shiga
Tunda suka fara takowa, wajen ya ruɗe da tafi, wasu na guɗa wasu suna sowa
Mama kam ta kasa ɗauke idanun ta akan su, banda murmushi da hamdala babu abinda take
Umma babba kam miƙewa tayi ta tarbosu har seda ta dangane dasu da gujerar su
Tajuddeen me hoto na gaba gaba yana haske su ta ko wace kusurwa.
(ƘANI NA YANA PICS ƊIN BIKI, SUNA, BIRTHDAY, DA KOMI MA, KUMA A KO WANI GARI
👉 😊
KUKE, A CIKIN FARASHI ME SAUKI DA RAHUSA, ZAKU IYA TUNTUƁAR SHI TA WANNAN
NUMBER 09078408747, KU GWADA BABU DANASANI A CIKI )
***TK
Tun da rana da ya leƙa sakina ya aje mata abincin da yayi musu order yace mata "ki shirya
anjima zamu je buɗar kan ya faruk da mumtaz"
A mugun firgice da kuma mamaki ta ɗago, murya a dishe tace "wacce mumtaz ɗin kake nufi?"
Har ya saka kanshi ze fice ya dawo yace "Mumtaz nawa kuke da su a dangin ku?"
Ganin kamar bata fahimce shi ba ya tsaya yayi mata bayanin auren mumtaz da ya faruk dalla
dallah sannan ya fice haɗe da faɗin "kar kuma ki ɓatan lokaci"
yana ficewa sakina tayi jifa da ledar abincin haɗe da gwara kanta da jikin gado
Cikin kuka take faɗin "ya za'ayi ma na ƙare akan TK mumtaz na auren faruk,
Wallahi baze taɓa sakuwa ba"!
Fuuu ta tashi ta fice daga ɗakin
Bata tsaya ko ina ba se kitchen, sharɓeɓiyar wuƙa ta ɗakko ta fito, direct ɗakin Tk ta nufa ido
rufe
Tana shiga tayi kanshi, kwata kwata beyi aune da wuƙar dake hannun ta ba sedai jin shigarta
yayi a cikin shi
Wani wawan ihu ya fasa haɗe da faɗuwa wanwar.
Hmmm
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg81
Cikin raɗaɗin sukar da tayi mishi yace "sakina wuƙa kika caka min fa"
Ganin yarda jini ke bin jikin shi a lokaci ƙanƙani yasa ta firgice ta fice daga ɗakin da gudu tayi
nata.
A hankali ya fara matsawa inda ya aje wayar shi
Amma da yayi motsi kaɗan zeji kamar wuƙar na sokar wani abu a cikin shi
Yunƙurin da ya rinƙa yi wajen janyo wayar sa yasa jinin ƙara yawan fita
Duhu duhu ya fara mamaye idon shi, amma duk da haka besa ya fasa yunƙurin kaiwa ga inda
wayar shi ke ajiye ba
Cikin yardar Allah ya samu ya ɗauki wayar amma sam baya iya kallon meke ciki saboda yarda
duhu ya mamaye shi
Shafa wayar yayi, ganin ba iya kiran ze ba, ya saketa a wajen
a hankali ɗakin ya fara juya mishi.
A inda ya yasar da wayar yaji kira ya shigo
Duk da ba gani yake ba, kuma hankalin shi na gaf da gushewa ya janyo wayar
Janyowar da yayi ya ɗauka ba tare da ya sani ba
Muryar abokin shi yaji
Cikin fitar numfashi Tk ya ce "Ta caka min wuƙa, kazo, kayi sauri kazo zan mutu"
Daga can abokin Tk ke jin shi cikin mawiyacin hali
A kiɗime yace "Guy me kake faɗa ne wai, ina waje fa, waye ya caka maka wuƙa, kana ina"?
Duk a ruɗe yake zubo mishi tambayoyin haɗe da ƙoƙarin fitowa daga motar
Daidai nan sakina ta fito a kiɗime tayi hanyar titi bako suturar arziki a jikin ta
Juyawa yayi da niyar binta, ya fasa ya shiga gidan da ta barshi a buɗe da gudu haɗe da ƙwala
kiran sunan "TK."
Ɗakin sakina ya fara shiga, began shi ba, sannan ya leƙa ɗayan ɗakin da Tk ke kwance cikin
jini baya numfashi
A kiɗime yayi kan TK da be san a inda kan shi yake ba
Sam be lura da jinin dake fitowaa ta cikin sa ba yayi kanshi ya rarime shi haɗe da jijjiga shi yana
ambaton sunan shi
Maida shi yayi ya aje da niyar kiran uncle Abbas a waya
Se a sannan idon shi yakai ga wuƙar dake cikin shi
A tsorace yaja da baya yana bin jinin dake a ƙasa da kallo
Da ƙarfi yace 'inaaa, wallahi bazan taka sahun ɓarawo ba" yayi waje da gudu ya faɗa motar shi
ya jaa.
*****waje yayi waje fa,
Fuskar kowa ka kalla kasan yana cikin annushuwa da farin ciki
Da ɗan damuwa mummy ke kallon kowa, taga kowa da kowa harda amaren wancan satin da
mazajen su amma bata ga TK da iyalin shi ba
Waya ta ciro tayi dialing no ɗin shi, amma har ta katse be ɗaga ba
A ranta tace "maybe suna hanya, ko wani abun ne ta tsaida su"
Anyi bajinta a wannan taron ba ƙarya, duk da ba'awani shirya mishi ba,
amma kai da ka gani zaka ce an jima ana shirin taron tsabar yarda komi ke tafiya akan tsari da
tsaruwa.
Bayan an gwangwaje, anci an sha, sannan akazo akayi cinikin fuskar amarya a tsakanin dangin
mama da dangin umma babba
Ƙwarai da gaske abun ya ƙawatar, dan an ta zabga ciniki cike da barkwanci har aka daidaita a
kuɗi adadi masu nauyin gaske kafin aka buɗe fuskar amarya kowa ya ganta
Tunda ya sabiha ta ɗaga net ɗin fuskar mumtaz bakin kowa be huta ba wajen faɗin "ma sha
Allah, tubarakallah", shi kan shi ya faruk seda ya furta "Tsarki ya tabbata ga ubangijina me
kashewa da kuma rayawa, tabbas wannan shi ake kira da sakin wawa"!
Hakanan ya tsinci kanshi da murmusawa game da maganar da yayi ta "sakin wawa"
Waigawa ya faruk yayi ta inda su ya sabiha ke zaune, yafito ta yayi da hannu
Da sauri ta taso taje
ya faruk yace "na gaji da hayaniyar nan fa, akwai kuma abinda zanyi kisa ya taƙaita abin pls"
Gyaɗa kai tayi tukun ta sauka zuwa wajen MC dake ta ɓaɓatu yana kwasar nera.
Biyar da kusan kwata abokan shi suka fara mishi sallama suna tafiya haɗe da mishi fatan alkairi
da zama lafia.
😂
A taƙaice aka rufe komi duk da can na hango fuskokin LAUJE FANS ba haka suka so ba, dan
basu gaji da gwangwajewa ba aka katse su LOL
Su o'o da o'o kam kamar su fashe saboda haushi.
Lalubo hannu mumtaz ya faruk yayi ya miƙar da ita tsaye tukun ya ja ta suka fice ta can bata
hanyar da kowa ke fita ba
Seda ya dangane ta da sasan mama tukun yace "zanje na dawo, ki shirya komin dare in sha
Allah yau zamu wuce gidan mu"
Sunkuyar da kai ƙasa tayi tana wasa da stones ɗin jikin kayan ta
Murmushi ya faruk yayi, yatsar shi ƴar manuniya ya saka ya tallafo gemun ta ya ɗago da fuskar
ta sama
Ɗayan hannun yasa ya zunguri hancin ta sannan yace "ko baki shirya hakan ba?"
Da sauri ta ƙwace fuskar ta ta sake yin ƙasa da kai, kunya duk tabi ta cika ta
Daga can ta hango Amal nata nunosu tana kwasar dariya, tana nuna mata irin meye haka take
yi
Murguɗa mata baki mumtaz tayi, shi kuma ya faruk se yayi tunanin da shi take
Folding hannayen shi yayi, still murmushi a fuskar shi yace "eyee harda murguɗa min baki ma
kike?"
Da sauri mumtaz ta dafe baki haɗe da zaro ido tace "Amal ce fa" ta nuna wajen da Amal ke
tsaye
Waigawa yayi daidainan Amal ta juya kamar ba ita ba
Murmushi kawai yayi ya kaɗa kai, sannan yace "Ki taya ni addu'a akwai abinda zan aiwatar a
cikin daren nan in sha Allah"
Kafe shi da ido tayi can tace "me zakayi ya faruk?"
Kallon ta kawai yake yama kasa ce mata komi
Ta sake faɗin "gaba na yana faɗuwa tun ɗazu, bana son yarda nake ji ɗin nan"
Kafe ta da kallo yayi, can ya basar yayi murmushi yace "kazar amarci zan je siyowa fa, wasa
nake maki"
Yana faɗin haka ta rufe fuska ta juya da gudu tayi ciki
Murmushi kawai ya sake yi sannan yace "i have to do this for Abba ƙarami's sake, barin bara
gurbi a cikin zuri'a shi kesa wasu taɓuwa" ya juya ya fice.
Duk sha'anin nan da akayi umma ƙarama bata cikin gidan nan sam,
Har abun ya ba ƴaƴan ta haushi, ganin kowa na nan amma ita bata nan, kuma bata ce ma kowa
ga inda taje ba
A wannan lokacin su suna can suna jiran lokacin da bokan su ya basu ya cika yarda zasu sami
Abba ƙarami su titsiye shi akan maganar hannun jarin da suke da shi a cikin dukiyar sa.
***Tunda abokin Tk ya fice daga gidan saboda firgita da yayi ganin halin da Tkn ke ciki
Beyi nisa ba ya dawo, ya sake komawa ciki
Da ƙyar ya iya saka shi cikin mota yayi rushing zuwa asibiti
Ganin halin da yake a ciki ne yasa suka ce ba zasu karɓe shi ba seda ƴansanda
Hankalin abokin Tk a tashe ya hau kiran uncle Abbas a waya
Haka wayar nan tayi ta ringing amma shiru be ɗaga ba
A ruɗe ya maida akalar kiran ga ya faruk
Ya faruk na zaune a cikin mota yana waya da mus'ab kiran abokin Tk ya shigo
Seda ya faruk ya gama wayar shi, sannan ya amsa kiran
A kiɗime yace "na kawo TK hospital sun ƙi karɓar shi"
Hankali kwance ya faruk yace "nutsu kayi min magana mana, me ya samu TKn? sannan
meyasa basu karɓe shi ba?"
A ruɗe yake mishi bayani
Ido waje ya faruk yace "ɗauke shi maza bari na tura maka address na hospital ɗin dr jamal, zan
kira shi a waya yanzu"
Seda ya faruk ya tura mishi sannan ya kira dr jamal,
Daga nan shiru yayi da bakin shi be gaya ma kowa ba yaja motar shi ya fice.
Sanda sakina ta fice daga gidan bayan aika-aikar da tayi
Gida ta wuce direct
A firgice ta afka ciki, babu kowa a palon se me aiki da ke kitchen
Sakina bata tsaya ko ina ba ta ware ɗakin ta haɗe da rufo ƙofa harda murɗa key
Jin motsin ƙofa da me aikin ta jiyo yasa ta leƙo, ganin bata ga kowa ba ta koma taci gaba da
aikin ta.
Se can wajen magrib mom ɗin sakina ta fito dan taga ko me aikin ta kammala