LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU

Author :  ZAINAB FALALU Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 25

6K to 9K   out of 73.4K words

passports ɗin ya miƙe tsaye bayan ya ɗauki keys ɗin shi, da ido ya faruk ya
nuna ma Ahmad ƙofar fita



Ba musu ya juya sum-sum ya fice, ran shi baƙiƙƙirin



Akan idon su ya faruk ya rufe ƙofar shi ya wurga keys ɗin shi a aljihun wandon shi yayi gaba
abinshi ya barsu da ƙamshin shi me daɗin gaske.



SHARE PLS

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg6



Rai a ɓace mus'ab yace

"wannan ai mulkin kama karya ne wallahi, na gaji ƙarar shi zan kai wajen umma b wlh" yayi
gaba a fusace ze fita



Da sauri Ahmad ya damƙo shi, murya ƙasa-ƙasa yace



"Baka da hankali mus'ab ya faruk ɗin ne zaka kai ƙarar shi?
Malam ka dawo hankali ka"



Banda huci babu abinda mus'ab keyi



Hannun shi Ahmad ya kamo suka fito harabar gidan

Suna fitowa suka yi kiciɓus da ya faruk zaune a kan boot ɗin motar shi waya kare a kunnen shi
Kallo ɗaya yayi musu ya kauda kanshi gefe yaci gaba da wayar shi




Har sun gota shi Ahmad ya sake yin ƙasa da murya yace

"Ko dai muje mu bashi haƙuri ne?"



Tsaki Mus'ab yaja yace
"wallahi ba zanje ba, sedai kai kaje"
Yana gama maganar yayi gaba fuuu kamar wanda ze tashi sama.



Murmushi kawai ya faruk yayi, dan sarai yaji me mus'ab yace.




Mus'ab ne ya fara shiga part ɗin su fuska a ɗaure yana wani ciccin magani



Sakkowar mama da Abba ƙ kenan suka gan su a tsaye cirko-cirko kamar wasu zakaru



Rai a ɓace mama tace

"Lafia kukai mani tsaye a palo?"



A fusace mus'ab yace

"Gaskiya mama an fara saka mana ido a cikin gidan nan, kuma gaskiya ba zamu ɗauka ba"



Ba mama kaɗai ba, hatta Abba ƙ dake tsaye seda yaji wata mummunar faɗuwar gaba ta
ziyarce shi jin furucin rashin ɗa'a a karo na farko daga bakin ɗan nasu me kunya da tsananin
biyayya gare su"




Kafin Abba ƙ ya buɗe baki yayi magana mama ta rigashi faɗin



"Mus'ab me kake nufi da an fara saka muku idanu?
Mu iyayen ku ne ke saka muku idanu ko kuwa me kk nufi?"

Ta ƙarashe maganar tana zaro mishi idanun ta da suka kaɗa suka yi jajir.



Watsa hannayen shi yayi alamun oho ɗin nan, sannan yace

"Ai ba se na ambaci suna ba mama, kawai dai ku dena ɗaure ma ya faruk ƙarƙashi yana mana
abunda yaga dama bayan mun kauce mun bar mishi komi da ya dace ace mune akai"
Cikin zafin nama mama ta sauke wa mus'ab wasu mahaukatan maruka a kumatun shi



Mumtaz dake zaune itama mamaki ya gama kashe ta na jin abunda mus'ab ke faɗa,
kamar ƙiftawar ido taga tafiyar marin nan, muguwar zabura tayi taja baya tana dafe kuncin ta
kamar ita aka zabga wa marin,




Ahmad kuya ja da baya yayi ganin yarda mus'ab ya samu tsarabar tagwayen maruka



Ido jajir mus'ab ke kallon mama, har wani huci yake



Abba ƙ kam dafe kanshi yayi ya samu gefen kujera ya zauna.



Ganin kallon da mus'ab ke mata yasa ta matso kusa da shi,
Cikin ƙaraji da kuma fushi tace



"Kallon nan ba ze gamshe ni ba har se naji yatsun ka guda goma a fuskata tukun dan ubanka"



Dunƙule hannu mus'ab yayi, kamar ze kai wa mama duka, ya fasa ya fice daga palon a fusace,
a mugun firgice Ahmad yabi bayan shi



Mumtaz kuwa ganin yarda komi ya birkice yasa tuni ta fara kuka tana wa mama ɗan kira




Su mus'ab na fita mama ta juya da gudu ta koma sama



Tana shiga palon Abba ƙ ta fashe da kuka tana dafe kanta da take ji yana juya mata

Sunan Allah kawai take ambata jin yarda numfashin ta ke neman gagarar ta gaba ɗaya.
A daddafe Abba ƙ ya bi bayan ta, shima riƙe da kanshi.



A hankali altine ta koma da baya bayan ta sakayo ƙofar kitchen ɗin tana sauke ajiyar zuciya.




Se wajen bayan la'asar mama ta sakko, da ka kalle ta kasan bata cikin nutsuwa, ƙarfin imaani
ne kawai ke riƙe da ita



Tsabar yarda ta sha kuka yasa muryar ta bata wani fita can sosai,

Ɗakin su Mumtaz ta nufa, tana shiga ta iske ta kwance akan darduma bacci ya ɗauke ta

Seda mama ta gama ƙare ma ɗakin kallo tukun ta taɓa mumtaz tana kiran sunan ta



Seda tayi da gaske kafin mumtaz ta haƙura da baccin ta tashi zaune

A muryar bacci tace

"Wallahi ina jin azumin yau mama"



Juyawa mama tayi zata fita tace

"sannu uwar raki, ki taso ki taya Altine aiki bana jin daɗi"
Ta ƙarashe ficewa.



Seda Mumtaz ta sake ɓata lokaci kafin ta fito zuwa kitchen inda Altine ta fara aikin abincin buɗa
baki.




BAYAN AN SHA RUWA



Wajajen tara da rabi na dare, ya faruk na kwance yana ƙara nazarin maganar da suka yi da
mama da kuma Abba ƙ, abun na ƙara ɗaure mishi kai matuƙa

Waigawa yayi inda ya watsa passport ɗin su Ahmad yayi yaga suna nan
Daga can ƙasan ranshi yace

"Ƙila sunyi trying ɗaukar abun su fa"



A hankali ya sauka daga kan gadon shi ya nufi inda laptop ɗin shi ke ajiye

Seda ya koma gefen gadon ya zauna tukun ya buɗe

A hankali ya rinƙa kallon yarda mus'ab ke wani muzurai yana magana



Shiru yayi ya kafa wa screen ɗin idanu yana tuna irin kunya da kuma biyayya na yaran,
Seda ya gama kallo tas, kamar ance ya duba wasu vedios ɗin da CCTV CAMERAr shi ta ɗauka

A hankali ya rinƙa scrolling yana kallo,

Wata muguwar faɗuwar gaba ce ta same shi a take



Hannun shi har rawa yake wajen maida vedion baya, me idanun shi zasu gani?

Mumtaz ce a lokacin da ta shigo ɗakin shi ta ɗauki agogunan shi na diamond masu mugun
tsada

Tsayar da vedion yayi ya tashi da sauri ya nufi wajen safe ɗin shi

Sanin ba me shigo mishi ɗaki ne yasa be wani damu da rufe shi ba

Ilai kuwa, yana dubawa yaga babu waɗan nan agoguna da ya gani a hannun ta



Da baya da baya ya koma ya zauna haɗe da maimaita sunan ubangiji



A hankali ƙwaƙwalwar shi ke tuno mishi ganin ta da yayi tana abubuwa irin na marasa gaskiya



Da ƙarfi ya runtse idanun shi yana hasasho kirkin Abba ƙ da kuma maman kanta, kusan kowa
inuwar arzikin su yake sha a cikin gidan nan.
A bayyane yace

"Nata yafi muni akan nasu Mus'ab
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!! ya Abba ƙ da mama zasu ji in suka ji wannan mummunan
abun?" astagafirullah!"




A wannan dare ya faruk ya jima be rintsa ba, gani yake kamar wasa kamar kuma a mafarki
abunda ya gani



Alwashi kala-kala ya ɗauka a wannan dare, har barci mara daɗi yayi awon gaba da shi.



ALLAH YA ZAƁA MANA SHUWAGABANNI NA GARI.



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
YAWAN COMMENTS, UPDATE AKAI-AKAI 😎
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg7

Kusan kwana biyu kenan ya faruk ke fakon mumtaz da duk wasu motsin ta

So yake ko ta wani hali ya ritsata amma be samu zarafin yin hakan ba
Mumtaz kam kamar ta so ta ɗago ya faruk, sam taƙi yarda ta fita balle har ya ritsata, ko da
yaushe tana ɗaki kwance

Da mama ta matsa akan zaman ɗakin data tsira, shine tayi ƙaryar ciwon kai ne ke damun ta
Shiyasa mamar ta rabu da ita ba dan ta yarda ba.




Zaune ya faruk yake a palon umma b yana dudduba tickets yana siya ma kowa




Fitowar Umma b kenan daga side ɗin Abba b, da yake ita ke da girki shiyasa bata yi ma ya
faruk titsiyan da ta saba mishi ba



Tana fitowa yana gamawa, cikin nutsuwa ya ɗaga kanshi ya kalleta tukun yace



"Barka da fitowa umma"



Seda ta zauna tukun ta amsa da

"yauwa, kana nan ashe, su hafsa sun kawo maka kayan buɗa baki ko?"



Idon shi akan screen ɗin wayar shi ya amsa da "Nace a kai min ɗaki na"



Taɓe baki umma b tayi, so take tayi magana amma tana ɗan jin shakkar yi

Can dai ta daure tace

"Halan kayi banbancin da ka saba yi?



Da mamaki ya faruk ke kallon mahaifiyar shi, bece komi ba seda ya miƙe har ya kai ƙofar fita ya
ɗan dakata yace
"Gida uku na kasa ku umma, ko wani kashi ɗaya jirgi daban, be dace ace duka ahali ɗaya su
haɗe a jirgi ɗaya ba, babban kuskure ne,
Tunda har Allah ya hore yarda za'a rarraba ɗin ai gara a rarraba, ki duba na tura miki naki a
wayar ki"

Yana ƙarashe maganar ya fice yana jin ba daɗi sam a cikin ranshi na yarda umma b ke mishi.




Yana shiga ɗaki bayan ya zauna, wayar shi ya ciro ya kira mama dake zaune gefen Abba ƙ tana
yanka mishi apples a plate wayar ta tayi ringing

Seda ta kammala tukun ta kira shi

yana ɗagawa yace



"Mama yau akwai kunun gyaɗar nan kuwa?"



Murmushi mama tayi tana gyara zamanta kafin tace

"So sorry yaro na, na mance shaf ba'a kawo maka ba"

Kafin yace a ba mumtaz ta kawo mishi, mama tayi saurin faɗin



"Bari mumtaz ta kawo maka yanzun nan"



Godiya yayi mata suka aje wayar



Number mumtaz mama tayi dialing, bugu biyu ta ɗaga tana wani shaƙe murya kamar me ciwon
gaske, a tunanin ta wani aikin mamar zata saka ta



Ilai kuwa mama tace

"Ki duba kan dinnig flask ɗin yayan ku na nan ki ɗauka ki kai mishi yanzu"
Da sauri mumtaz ta wuntsulo daga kan kujerar da take kwance tace

"mama kuma kince nice zan kawo mishi?"



Tsaki mama ta ja tace

"in sakko inga baki kai mishi ba, zan baki mamaki ke da baki son a more ki sam"

Ta tsinka wayar ta, tana ci gaba da mammatsa wa Abba ƙ ƙafar shi.




Cikin marairaicewa mumtaz ta kalli sakina dake waya da saurayin tace

"Dan Allah sakina ki kaima ya faruk kunun shi"

Mumtaz bata gama rufe baki ba sakina tace



"caɓ, wallahi ba zani ba, salon inje ya rinƙa mun kallon wulaƙancin nan da ya saba"



Kamar mumtaz zatayi kuka tace

"Baki fahimce shi bane, haka yake shi, ni wlh jiwa nake gani shiyasa nace ki kai mishi"



Tsaki sakina ta sake yi, seda ta gyara kwanciyar ta tkun tace

"Haka nan zaki daddafa ki kai malama, thank God ba'a gidan nan nake ba da za'a kwashi ƴan
kallo dani"

Ta maida wayar ta a kunne taci gaba sa firar ta.




A zuciye mumtaz ta yayimi hijabin ta tasaka tukun ta ɗauki flask ɗin kamar shine me laifin, ƙiris
ya hana shi suɓucewa daga hannun ta tasamu ta taro shi
Tafi minti goma a tsaye tana jiran taga ko zata ga wani daga cikin yaran gidan ta bashi ya kai,
haka nan ta gaji da tsayuwar ta tayi shahada kawai ta nufi ɗakin




Ya faruk na zaune a gaban laptop ɗin shi, vedion mumtaz wanda ta ɗauki agogon nan ya kafa
ma ido yana kallo,
har yanzu ya kasa yarda da abun, se yake gani kamar ba nutsatstsiyar mumtaz ɗin da ya sani
bace



Knocking ɗin ƙofar da tayi ne yasa yayi maza yayi pausing vedion ya juyar da laptop ɗin zuwa
ɗayan ɓangaren da ba lale wanda ze shigo ya gani ba



Seda ya kimtsa tukun yace

"Come in"

A hankali mumtaz ta tura ƙofar kamar warce ƙwai ya fashe ma a ciki



Tunda ta shigo ya kafe ta da manyan idanun shi yana kallon ta,

Gaba ɗaya wani mugun tausayin Abba ƙ da mama ne suka lulluɓe shi, for the first time da yaji
kamar ya fashe da kuka tun bayan ya mallaki hankalin shi.



Tana sunkuyawa zata ajiye flask ɗin ya faruk yayi saurin tashi ya rufe ɗakin da key



Tana ganin haka ta juyo a tsorace tana niyar kware baki ta kurma ihu



Kamar yasan me take da shirin yi kuwa, manyan idanun shi ya zazzaro waje ya ɗora yatsar shi
ɗaya a kan laɓɓan shi yace

"shiii, kina fasa ihun nan zan sauya miki kamanni wlh"



Ƙut mumtaz ta haɗiye ihun ta, taci gaba da rarraba nata manyan idanun
Belt ɗin jikin shi ya zaro, tana ganin haka ta tsugunna ta dunƙule waje ɗaya tana ɓarin jiki




Rufe ida ya faruk yayi ya zambaɗa mata ɗaya a jikin ta

Kuma ya hana ta ihu



Sosai mumtaz ta tsorata da yarda taga ya faruk ɗin, a iya tsawon rayuwar ta bata yaɓa gani ya
ɗaga hannu ya daki wani a cikin gidan nan ba se yanzu, yanzun kuma a kanta




Cikin tsananin tsoro mumtaz tace

"Dan Allah ya faruk kayi haƙuri, wallahi mantawa nayi ranar da kace inzo in same ka ba da
gangan naƙi zuwa ba"



Bayan hannun shi yasa ya make bakin ta da ƙarfi, cikin fushi yace



"Rufe min baki maƙaryaciya, bayan sata har ƙarya kika koya kenan?"



Ƙwalalo manya idanun ta tayi waje, a lokaci ɗaya kuma kukan da take ya ɗauke ɗif



Jiki a sanyaye ta sauke kanta ƙasa tana sauraron yarda gaban ta ke dukan uku-uku




Sosai ya faruk ke kallo da nazartar yanayin ta,



Farko yaso yazo mata da mugun zafi, amma haka nan yaji zuciyar shi bata aminta da hakan ba



Unexpected muntaz taji murya ya faruk a kanta cikin nutsuwa yace



"Bayan ni akwai wanda ya taɓa kamaki?"
Shiru tayi bata ce komi ba, seda ya buɗe murya yayi kamar ze sake shauɗa mata belt ɗin tukun
ta girgiza mishi kai da sauri



Rai a ɓace yace "buɗe bakin ki kiyi min magana kamar yarda kika ji inayi"



Kanta a ƙasa tace "a'a"



Kallon ta kawai ya faruk yake, sam ya rasa ta ina ma ze fara, sosai yake jin ɗacin abun a ranshi



Can dai ya daure yace



"Me kika rasa da kika saka rayuwar ki a cikin wannan ƙazamar ɗabi'ar?"



Bata ce komi ba se sheshshekar kuka da take



Shima be buƙaci da yajin ba ya ɗora da



"Yanzu kina ganin kinyi wa Abba ƙ da mama adalci kenan? kina ganin suka san wannan abun
ba ze zama musu mugun tashin hankali ba?
Ashe baki da tausayi? imanin ki ragagge ne?
Baki jin kunyar Allah balle ace kunyar da zaki shiga duk ranar da aka kama ki?"



Kuka kawai mumtaz take, maganganun ya faruk nayi mata raga raga da zuciya



A tsawace yace

"ki min shiru, wannn kukan munafurci ne ai, gaya min tun yauahe kika fara satar"?



Kasa cewa komi tayi, banda aukin share hawaye
Wata tambayar ya faruk ya sake wurgo mata

"In kin saci kayan me kike da su?"



Kanta a ƙasa tace

"Ban taɓa ɗaukar ma kowa ba ai"

Bayan hannun shi ya saka ya make mata baki tukun ya waigo mata da screen ɗin laptop ɗin shi
yace



"Wannan wacece?"



Baki sake mumtaz ke kallon vedion kanta da kanta, da dai ta san ta kamu kawai se ta fashe da
kuka me taɓa zuciya



Cikin muryar kuka tace,

"wallahi wannan shine karo na farko da na fara ɗauka, nasha ganin abubuwa zan ɗauka amma
bana samun dama, kuma kaima yanzu zanje in ɗakko maka kayan ka"



Da mamaki ya faruk ke kallon ta,jin tace "tasha gani abu amma bata samun ɗauka"



"Da kika ɗauki wannan me zakiyi da shi da?"

"bakomai" tace cikin kuka



Da sauri ya faruk yace

"Ƙarya kike, kodai kina da saurayin dake saka ki ɗauke-ɗauke?"



Da sauri ta karkaɗa kanta, tana ci gaba da share hawayen ta da bayan hannun ta
Shiru ya faruk yayi, can dai yace "tashi kije"



Sosai tayi mamakin furucin shi



Tsaye tayi taƙi fita,



Da ƙarfi yace

"I said get out!!"

Da gudu ta fice tana ƙumshe kukan da ya tawo mata da mugun ƙarfi.



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

pg8

Memakon ta wuce side ɗin su kai tsaye se ta wuce can back yard ɗin side ɗin su

Suna ajiye kujeru haka a wajen dan hutawa wani lokacin
Zama tayi dirshen a ƙasa ta haɗe kai da gwiwa
Tunda ta shigo wajen mus'ab yaga shigowar ta,
Ya jima yana kallon ta bece komi ba, sema faɗuwa da gaban shi ke yi tunda yaji sautin kukan ta



A hankali ya taso daga inda yake ya matso kusa da ita

Dafatan da yayi ne yayi matuƙar razana ta, ƙiris ya hana ta kurma ihu, Allah yasa yayi saurin yin
magana



Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke ta saka hannun tana share hawayen fuskar ta



Sam taƙi yarda ta kalli mus'ab da ta san shima kallon ta yake

Abubuwa take na irin wanda suke a tsarge ɗin nan



Murya ƙasa-ƙasa mus'ab yace



"me ke damun ki? waye ya saka ki kuka?"



Muryar ta na rawa tace

'Bakowa ya mus'ab, kawai bana jin daɗin komi ne"



A hankali, yarda ba lale tajishi ba ya ce

"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!



Jin bece komi ba yasa tace



"Kai me kake yi a ban ya mus'ab?"



Ƙirƙirar murmushi yayi tukun yace

"Zafi ne ya fito dani"
Da sauri mumtaz ta ware manyan idanun ta da mamaki tace

"Zafi fa kace? Air con ɗin ɗakin ka fa?"



Shiru mus'ab yayi ya dafe kanshi, shi sam ya manta da wata aba wai air con,
Sam baya jin daɗi ji yake kamar ana iza mishi wuta a zuciyar shi, azalzala kawai yake ji, sam ya
rasa nutsuwa ko kaɗan
Bugu da ƙari ga abunda ya faru ɗazu, wanda shi kanshi seda ya bar wajen tukun yake tuna
rashin ɗa'ar da yayi"



Still bece komi ɗin ba,
Miƙewa yayi sannan yace



"Ki rinƙa addu'a ne, kuma kar in sake ganin dan abu ya dameki ki rinƙa fitowa wajen nan da
daddare, tashi ki wuce ciki"



Tashi tayi ta wuce jiki a sanyaye,

Seda mus'ab yadena hangen ta tukun ya koma ya zauna a wajen memakon ɗaki da yayi niyar
tafiya



Zabga tagumi yayi hannu bibbiyu yana maganar zuci da be san ta fito fili ba

"Allah na roƙeka kasa ba abinda nake ji bane yake damun mumtaz, Allah ka tsayar a iyakacin
kaina kar ka ɗora musu ya rabb, nima ka yaye min ya Allah".




Sanda mumtaz ta shiga side ɗin su kowa ya kama gaban shi dan har an kashe wutar ko'ina
Ɗaki ta wuce itama kai tsaye tunani kala-kala a cikin ranta



Abunda ya bata mamaki shine, titsiyen da ya faruk yayi mata ya sa taji tsanar kayan kowa,
amma tunda ta saka ƙafarta a side ɗin su taji damuwar ta ragun mata, tana ƙara jin kwaɗaituwar
sake tattara duk wani abu da yazo gaban ta koda kuwa na Abba ne ko mama
Murmushi tayi bayan ta sake yin ido biyu da agogunan ya faruk da sam ta gama ƙudirtar
salwantar da su ta ko wani irin hali a goben nan



A hankali ta saka hannu ta shafi laɓɓan ta inda tasha masga ɗazu

Jin sun ɗan tasa kaɗan yasa ta murguɗa baki tace

"Allah ya isa na".




2am

Karo na kusan biyar kenan yana fitowa daga wanka,

In ka kalli idon shi kamar an zazzago su tsabar

3 / 25