LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU

Author :  ZAINAB FALALU Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 25

27K to 30K   out of 73.4K words

a ruɗe cikin tsananin tashin hankali yake furta "innalillahi
wa'inna ilaihirraji'un, menayi musu ni Abubakar meyasa suke farautar rayuwata dana ahalina,
suwaye waɗan nan, inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un"



Yarda Abba ƙ ke magana ze tabbatar maka da ba a hankalin shi yake ba sam

Yarda jikin shi ke rawa haka jikin mama ke rawa, ko motsin kirki ta kasa yi

Ya faruk da zafin bugun da mutumin yayi mishi ya sauka ya miƙe, gaba ɗaya shima ruɗewa
yayi, ya rasa kan wa zashi, kan mama ko kan Abba fa ya gama girgicewa da tsananin azabar
da aka gana mishi

Ganin mamar ta sakko da ƙyar tayo kansu yasa shima ya faruk ɗin ya nufi Abba fa ke neman
cizge ruwan da aka sa mishi

Da sauri ya faruk ya dafe Abba ƙ, kasa cewa komi yayi

Abba ƙ kamar ƙaramin yaro haka ya ƙwaƙume ya faruk da shima ƙiris yake jira ya fasa kuka



Dukda jarumtar Abba se gashi yana kuka kashirɓan a jikin ɗan ɗan'uwan sa

Mama ma rashin madafar dafawa yasa ta matso, zama tayi kusa da Abban ta kutsa kanta kusa
da inda Abba ƙ ya saka na shi a jikin ya faruk, itama ta fashe da kuka



Haka ya faruk ya rungume su kamar shi ke sama da su



Suke kukan amma yafi su jin raɗaɗin abun a cikin zuciya



Ganin kukan nasu ya wuce ƙima yasa da ɗan ƙarfi yarda zasuji ya hau maimaita kalmar
"HAZBIYALLAHU WA NI'IMAL WAKIL!!!

LA'ILA HA'ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN!!"
ALLAHUMMA LA SAHLA ILLA MA JA'ALTAHU SAHLAN, WA'ANTA TAJ'ALUL HAZNA IZA
SHI'ITA SAHLAN!!!"

Haka yayi ta jero musu waɗannan addu'oin, yakai ya dawo, har mama ta fara yi itama, can
Abban ya ɗauka shima

Cikin hukuncin ubangijin bayi jikin su ya dena rawa, zuciyoyin su suka yi sanyi hankulan su
suka fara kwanciya



Abba ƙ ya fara sakin faruk ya koma ya kwanta, sannan mama itama ta kifa kanta a jikin bango

Ya faruk na ganin haka ya juya ya saka key a ƙofar sannan ya buɗe toilet ya shige ya kullo kan
shi a ciki

Yana shiga shima ya haɗe kanshi da bango ya fashe da kuka me taɓa zuciyar me sauraro.




Duk suna jih shi, banda mumtaz da har yanzu bata san inda kanta yake ba

Jin kukan ya faruk ba ƙaramin sake taɓa su yayi ba, amma ƙarfin kiran da suke ma ubangiji ya
nasu hope da juriya



Ya faruk seda ya kusa minti talatin a cikin toilet kafin ya fito

Be yarda ya haɗa ido dasu Abba ba yayi hanyar fita daga ɗakin

Da sauri mama tace "ina zaka ka barmu faruk?"

Be waigo ba yace "yanzu zan dawo mama"

Key ɗin ƙofar ya zare ya fita tukun ya rufo su ta waje

Seda ya ƙarewa wajen da yake tsit kallo tukun ya nufi office ɗin likitan



Shima ya ɓata lokaci sosai a wajen kafin ya fito,
Ta can baya ya zagaya, wayar shi ya ciro yayi ƴan danne dannen shi tukun ya kara a kunnen,
shima ya ɓata time yana waya kafin ya juyo ya dawo ɗakin

Shigar shi kenan mumtaz ta farka a firgice tana sambatun kiran sunan Abba na mamana!



Mamace a kanta duk da irin jirin da ke ɗibar ta,
Abba kam ya kasa koda motsi daga inda yake



Da sauri ya sake kulle ɗakin ya nufesu ganin mumtaz na neman dirowa daga kan gadon cikin
gushewar hankali har tana neman hankaɗe mama da ba ƙarfi sam a jikin ta

Da azama ya tallafe ta ya ɗaga ta cak ya mayar kan gadon
Tukun yace

"mama lallaɓa ki koma ki kwanta, bari na tare ta"

Ba yarda ta iya haka ta daddafa ta koma nata gadon ta kwanta.



Sosai mumtaz ke fizge-fizge tana sambatu

Ganin tana neman fin ƙarfin shi ne yasa ya rungume ta a ƙirjin shi ya hau tofa mata ayatul
kirsiyu da falaƙi da nasi.



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
SHARE PLS




LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg39-40

Sauke hannun Abba babba kenan daga kuncin ya faruk, goggo safiya na ƙarasowa baki sake
hannu a saƙale

Da mugun mamaki goggo safiya tace
"me zan gani haka Ali?, me yayi zafi ka sauke mishi wannn marukan kamar wanda akaiwa
turaren tsiya?"



Cikin fushi Abba babba yace

"ya safiya yaron nan yayi mana ɗiban albarka, banda bamu isa da shi ba ya za'ayi ace yaje ya
aiwatar da abu ba tare da masaniyar mu ba? banda ya raina ma mutane hankali"

Itama a ɗan fusace gaggo safiya tace "ɗiban albarkar me yayi?, ko me yayi be kamata ace da
girman sa mutum ya zama magidanci ace kayi mishi haka ba sam ga yara ta ko'ina"



Shiru Abba babba yayi yana maida numfashi, mutum ne shi me zuciyar tsiya, be raina abun
fushi sam



Uncle Abbas yayi saurin faɗin "Tunda haihuwar shi akayi ai befi ƙarfin hukunci ba"



Tunda Abba ya sauke ma ya faruk marin be yarda ya ɗaga kanshi ba se yanzu da uncle Abbas
yayi magana,

Da jajayen idanuwa ya faruk ke kallon uncle Abbas wanda daga ganin yarda yake magana
kasan harda zigar shi Abba b ya ɗauka



Be yarda yace komi ba ya juya da niyar barin wajen,

Taku ɗaya yayi ya jiyo muryar Abban ya sake faɗin
"Au tafiya zakayi baka sanar wa mutane inda ka kaisu ba?"

Murya a cunkushe ya faruk yace "Na kira wayoyin ku dukan ku a kashe, uncle Abbas kawai na
samu kuma be ɗaga ba, shine nayi dropping muku hospital ɗin da na sauya musu"



Be jira cewar su ba ya juya ya nufii ɗakin shi.



Tunda akai marin hafsat ta kwasa da gudu tayi ciki, cike da kwaratsi hafsat ke ƙwala wa umma
babba kira, faɗi take "umma, umma, fito kiji!"

Cike da tsoro umma b ta fito daga ɗaki jin yarda take ƙwala mata kira

Ido a waje umma b tace "lafia hafsa?"



Cike da gulma hasfat tace "yanzun nan Abba ya wanke ya faruk da zafafan maruka yasin"

Duk da taji kalmar marin banbaraƙwai, amma ga tunanin ta tasha ɗaya daga cikin wanɗa ke
hospital ne ya margaya



Fuska a ɗaure umma babba tace "mari fa kika ce, se kace faruk ɗin wani ƙaramin yaro ne?"

Taɓe baki hafsat tayi kafin tace "aikuwa yasha su da zafin su kam, dama yarda naga Abba ya
shigo gidan nan kamar da fushin kowa ya shigo".




Juyawa cikin ɗaki umma b tayi, wayar ta da ke kan mudubi ta ɗauka tayi dialing nombar ya
faruk

Wayar nata ringing be ɗaga ba,
Seda tayi mishi kira uku be ɗauka ba tukun ta aje wayar haɗe da faɗin "zuciyar gadon ta motsa
kenan".




Ta ɓangaren ya faruk kuwa yana shiga ɗakin shi ya shige wanka, yana wankan ne yaji kira nata
shigowa, sauri-sauri yayi ya gama wanka duk a tunanin shi calls ɗin daga asibiti ne

Yana fitowa yaga missed calls ɗin ummar har uku
Be kira ta ba seda ya gama shiryawa tsaf tukun ya maida mata da kiran



Umma b kamar daman jiran kiran nashi take ta ɗaga, kafin yace wani abu ta riga shi faɗin
"meke faruwa ne faruk?"



Cike da basarwa yace, "a ina umma?"



Sakatoo umma b tayi da baki tana sauraron rainin hankalin ɗannata, cikin ko in kula ta maida
mishi da "ohhh, hakane fa ba kai nayi niyar kira ba fa"

Murmushi ya faruk yayi jin yarda ta ƙule nan da nan, kafin ta aje wayar ta sake faɗin "ayi jinyar
kumatu lafia"

Wannan karon he can't hold it seda ya dara, duk da raɗaɗin da zuciyar shi ke mishi kuwa



Sosai ya faruk yayi nutsu cikin tunanin shi, gaba ɗaya ya rasa inda ze kama, ya kuma rasa da
wa ze tattauna akan wannan matsalar

Saƙon da'aka tura mishi a jiya ya buɗe ya sake karantawa "ya faruk kar ka bar su mama su
kaɗai"

A bayyane yace "waye wannan?"

Can kuma ƙwaƙwalwar shi ta koma ga likitan ɗazu da ya danne Abba da pilo

Gaba ɗaya kanshine ya hau hautsinawa yana juya mishi, alamar in mutum ya cika tunani.

Zumbur ya faruk ya miƙe, still a bayyane yace "wallahi AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI, dole ma"



Sanda ya fito harabar gidan ba mutane kamar ɗazu, dan har su Abba b da uncles ɗin shi duk
basa wajen

Ahmad ua hango can wani lungu zaune shi kaɗai ya haɗa kai da gwiwa

Tsayawa sosai ya faruk yayi yana kallon shi, duk a tunanin shi wayace a hannun shi

Ya kai kusan min biyu yana kallon shi kafin ya ƙarasa kusa da shi
Sam Ahmad beji zuwan shi ba har seda ya faruk ya dafa kafaɗar shi tukun ya ɗago da sauri

Zazzaro ido ya faruk yayi ganin yarda fuskar Ahmad tayi ruɗu-tuɗu tsabar kukan da ya sha

Cike da fargaba ya faruk yace "me ya same ka Ahmad?"



Murya na rawa Ahmad yace "ina son zuwa inga su Abba, amma sam na kasa ya faruk, zuciya
ta na min ƙuna da zafi duk sanda na kusance su"

sunkuyar da kai ya faruk yayi yana faɗin "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" yana tunowa da abinda
mus'ab ya rubuta sak da da abinda Ahmad yace a takardar shi lokacin da ze bar gida



Gaba ɗaya jikin shi yayi mugun sanyi,

Bayan kalmar innalillahi da ya furta be sake cewa komi ba,

Miƙewa yayi tukun ya kamo hannun shi ya miƙar da shi shima

Janshi ya hau yi har bakin motar shi, se a sannan yace "shiga ka jirani"

Ya juya yana amsa call ɗin dr jamal

Yana cikin amsa call ɗin dr jamal ya fauza(babbar ƴar umma ƙarama) ta fito ɗauke da manyan
kuloli

Yana a inda yake tsaye ya buɗe mata booth ta saka na hannun ta, sannan fadil ma ya saka
nashi.

Kaf a gidan babu warda suke zama suyi magana ta fahimta kamar fauza, tasu tazo ɗaya tun
suna yara

Ya faruk na gama wayar ya dawo jikin motar inda ya fauza ke tsaye tana jiran shi

Da ɗan damuwa a fuskar ta tace "ya faruk me yayi zafi wai ɗazu har Abba b ya mareka"?

Hannu ya saka ya shafi kumatun shi kafin yace

"nima dai nayi mamaki, daga na sauya ma su Abba ƙ hospital shikenan fa" har yayi niyar sanar
da ita abinda ya faru, ɓangaren zuciyar shi ya gargaɗe shi, waskewa yayi da maganar yace
"bari in dawo dai mayi magana"

Da "to" ta amsa, ta shige ciki, shi kuma ya shige mota.



Daga shi har Ahmad ba mece ma wani komi har suka isa asibitin

Har yayi parking ya fito bega Ahmad nada niyar fitowa ba

Kallon shi ya faruk yayi yace "fito"

Jimm ya ɗanyi tukun ya fito jiki sam ba ƙwari



Booth ya buɗe ya ɗauki kulolin da ya fauza ta saka

Yana gaba Ahmad na binshi a baya

Jiyake kamar yayi ta zunduma ihu tsabar zugin da ranshi ke mishi



Amir dake zaune a ɗan harabar wajen ya hango su, da sauri ya taso yazo ya karɓi kular hannun
shi yayi ciki da su

Amir na shigewa Ahmad yayi saurin faɗin "ya faruk ɗan riƙe min, fitsari nake ji"

Karɓa yayi tukun yaci gaba da tafiya zuwa ciki.



Ba wani fitsari da Ahmad keji, kawai yakasa riƙe kanshi ne sam shiyasa yayi haka

Ya faruk na shigewa, Ahmad ya zagaya ta bayan windows ɗin ɗakin,

Laɓewa yayi ya rinƙa leƙen iyayen nashi dake zaune bama zaka taɓa cewa sunyi accident ɗazu
ba, bama kamar mama ita ko ƙwarzane babu a jikin ta, Abban ma ƴar buguwace kawai a kafaɗa

Cike da so da ƙauna yake kallon iyayen nashi,

Abinda be sani ba tun da ya leƙo na farko mama taji ajikin ta ana kallon ta

A wayence ta kalli windon, ganin Ahmad ne ke leƙen su hakan ba ƙaramin karyar mata da
zuciya yayi ba.
Kusa da mama ya faruk ya zauna, cike da kulawa yace "mamana ya jikin?"

Murmushi mama tayi kafin tace "naji ƙarfi sosai yanzu, mumtaz ce har yanzu tun baccin daka
tafi ka barta tanayi bata farka ba, Allah yasa dai kan yarinyar nan be taɓu ba"

Da sauri goggo safiya tace "ah tuf da baƙin yawu, in sha Allah garas zata miƙe kamar yarda
kuka miƙe kuma"

Kowa seda ya murmusa wa yarda tayi maganar

Tsam ta taso daga inda take ta matso kusa da ya faruk, ƙasa tayi da murya tace

"waɗan nan masu kakin fa faruk?"

Kai tsaye yace "saboda tsaron lafiyar su na aje su goggo"

Taɓe baki tayi kafin tace "kamin daidai faruk, ni kaina ban gane ma wasu abunuwan ba wallahi,
tunda na iso garin nan na fara gane-gane masu ban tsoro wallahi"

Tsit wajen yayi jin abinda goggo safiya ke faɗi

Cike da son jin me tagani ya faruk ya ce "me kika gani ne goggo?"

Shiru tayi bata sake tanka kowa ba, daga baya ma miƙewa tsam tayi ta nufi gadon mumtaz
dake mutsu mutsu.



Se asannan mama tace ma faruk "In yasan ba ze shigo ba mene na zuwa yana leƙen mu?"

Da sauri ya faruk ya kalli window ido biyu suka yi da Ahmad dake laɓe

Da Ahmad yaga sun ganshi yayi saurin barin wajen yana jin azalzala acikin ranshi

Murya ƙasa-ƙasa ya faruk yace "mama akwai matsala babba wallahi, ban san daga ina take ba,
amma kowa ya kalli yarda abubuwan nan ke tafiya zaka san akwai wani abu a ƙasa,"



Murmushi me cin rai tayi sannan tace "Tabbas AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI FARUK, Amma mubi
komi a hankali mu dage da addu'a Allah ze warware mana komi"



Kafin ya faruk ya sake magana goggo safiya ta dawo tace "faruk zo ka kamamin mumtaz in
saka ta fitsari kar ta jiƙe shimfiɗar"



Dururu yayi, cikin ƙinƙina yace "ni kuma?, ah bari a kira nurse tazo ta tayaki dai"



Goggo safiya tace "kai bana son shashanci, yo kafin nas ɗin tazo ai ta gama fitsare wajen"



Murmushi mama tayi tace "muje na kama miki ita yaya safiya"

suna shiga yayi wuf ya bar wajen ya nufi office ɗin dr jamal.




*******KHALID

Yinin ranar yayi shine cikin rashin sukunin maganar da sakina ta gaya mishi game da mumtaz

wani ɓangaren na zuciyar shi yaso ya yarda, amma wani sashin ya gargaɗe shi da kar ya
kuskura yayi sake na dafe da mumtaz

Da ya zauna yayi tunani me kyau, yayi la'akari da irin yanayin rayuwar da akeyi a yanzu,
hassada, baƙin ciki, da zallar zagon ƙasa da yayi ma al'ummma katutu yasa ya dawo daga
rakiyar maganar sakina

Dan tabbas a rayuwar nan wanda kafi kusanci da shi se ya cuceka, ko kuma ya nemi ganin
bayan ka, kuma haka kurum siddan ragadan baka tare mishi komi ba, zallar hassada da
tsananin baƙin ciki ya ginu a tsakani.



Bayan wannan dogon tunanin da yayi ne yasamu sukuni a cikin ranshi

Beyi fushi ko zuciya ba ya sake kiran sakina, da ƙyar da ɗan wulaƙanci ya samu ta gaya mishi
asibitin da aka maida su



Aikuwa beyi ƙasa a gwiwa ba yaja abokin shi kamal suka nufi hospital ɗin

Sanda isa an shiga sallar isha, seda suka tsaya a masallaci sukayi kafin suka fito

Suna fitowa suka sake haɗuwa da uncle Abbas shima da fitowar shi kenan, cike da girmamawa
su khalid suka sake gaishe shi da tambayar masu jiki

Uncle Abbas da kan shi yayi musu jagora zuwa ciki

Inda Allah ya temakesu kenan, dan jami'an tsaron wajen bazasu taɓa barin su shiga ba saboda
tsaro

Direct ya wuce da su ciki

Abba ƙ kam be sheda shi ba, duk da yayi mishi bayanin a cmpnyn shi yake aiki

Ganin basu ga mumtaz a wajen ba yasa shi tambayar uncle Abbas "an sallami mumtaz ne sir?"



Uncle Abbas yace "ohh, gadon ta na ciki, ai tafisu jin jiki kam, ku shiga"



Suna shiga suka isketa zaune goggo safiya ta tasata a gaba tana cin abinci

Kalid na yin sallama mumtaz ta ɗago kanta da sauri, a take agogon data ɗauka a cikin motar shi
ya faɗo mata, da sauri ta sunkuyar da kai ganin yarda ya kafe ta da kallo

Murya ciki-ciki mumtaz tace "goggo bani hijabina pls"

Baki sake goggo safiya tace "Ah lallai kin fara dawowa hayyacin ki ƴannan da har kike neman
hijabi"

Ganin ba bata hijabin zatayi ba yasa taja ɗankwalin goggo safiyan dake ajiye a gefe ta yafa a
jikin ta



Hannu bibbiyu goggo safiya ta karɓi su kalid jin bayanin da kamal yayi mata

Nan suka zauna suna ta fira kamar irin sun saba ɗinnan

Ita kam komawa tayi ma tayi kwanciyar ta, sedai kaf firar da suke tana jin su.



Kiran da uncle ƙasim yayi mata ne yasa ta tashi a wajen

kamar dama jira kalid yake ta fita, matsawa yayi kusa da mumtaz data juya baya yace

"ya jikin naki?"
Ƙin amsawa tayi, in da ta waiga fuskar ta ya koma, ido huɗu suka yi
Da sauri ta rufe nata tana jumɓuro baki gaba

Murmushi kalid yayi kafin yace "nagode ma Allah da ya takaita abin nan a iya haka mumtaz,
yanzu kam zan iya bacci me daɗi tunda na ganki na kuma ga yanayin jikin ki"

"hmmm" kawai take cewa

Cike da damuwa yace "ina wayar ki?"

Se a sannan tayi magana tace "kamar an sace fa"

Yace "toh bakomai, gobe in zanzo zan tawo miki da wata, amma yanzu ba wani nonba da zan
same ki kafin safe?"

Girgiɗa kai kawai tayi,
Daidai nan goggo safiya ta dawo

Basu sake wani jimawa ba sukayi mata sallama, bayan sun aje ma goggo safiya 20k agaban
ta.



Sun fita kenan ya faruk ya shigo hannun shi ɗauke da takarda, kusa da Abba ya zauna, miƙa
mishi takardar yayi kafin yace "dan dai ka matsa ne Abba, amma da kun zauna kun sake
warwarewa tukun"

Cike da kulawa Abba yace "gara mu tafi gida tunda Allah yasa ba wani matsala, kuma na gaji
da tambaye tambayen da ake min akan waɗan nan ƴan sandan da ka zuba, kuma hankalina
baze taɓa kwanciya ba a nan"



"Hakane Abba, amma waze zauna da mumtaz?"

Se a sannan mama tace "Ya safiya zata zauna da ita mun gama wannan maganar, gwara muje
gida a sauƙaƙa ma jama'a dake ta sintirin zuwa"

Ba yarda ya iya, haka suka tattara suka koma gida aka bar mumtaz da goggo safia a asibitin.




****gaskiya ya kamata kije ki gaishe ta mami, wallahi taji jiki sosai
Cike da zolaya mami tace "ohh khalid bako kunya?, in na dawo daga tafiyar da zanyi gobe
zanje in gaishe ta,
Amma dai zuwa gobe ka samu binta da azima suje su dubata(binta da azima ƙannen mamin
ne)
Se su sake tabbatarwa da gaske kake



Cike da jin daɗi khalid yace "yauwa mami na, kin kawo shawara me kyau wlh"



Haka suka yi ta firar su irin na uwa da ɗa, sun jima suna fira kafin mami ta sako maganar abun
hannun ta data nema ta rasa "Wai khalid har yanzu shiru ba wani labari game da abun hannun
nan?"



"Mami, tunda kikaji har yanzu ba wanda ya kirani to wlh ba satar shi akayi ba, maybe ya faɗa
wani wajen ne, ki sake dubawa dai"

Taɓe baki mamin ta kafin tace "ko ɗazu seda na sake dubawa wallahi, ɓatan shi yayi min ciwo
sosai"

Da sauri khalid yace "mami ba akwai CCTV a office ɗin ba?"

Mami tace "akwai mana"

yace "ki duba to, ƙila kiga inda ya faɗa"

Da ɗan murna mami tace "aikuwa danaji daɗi, sam na mance da

10 / 25