Author : ZAINAB FALALU Category : African Stories & Novels
da ta naɗe kanta da jar laffaya
me tsaɗar gaske
Ɗaya bayan ɗaya suka samu waje suka zauna a kujerun gaba-gaba
Sosai shaika zainab mahmud Adam tayi shikekken wa'azi game da haƙƙin mace akan mijin ta
sosai wa'azin ke shiga dukkan mahalukin dake wajen, bama amaren kaɗai ba, harda waɗan da
sun jima a cikin auren dama wanda basu kai ga shiga ba
Shaika zainab mahmud ta ɗau lokaci me tsayi kafin ta rufe
Ɗaya daga cikin malaman da suka zo tare ta fara rero waƙa cikin harshen larabci,
Tana tafi tana waƙen,
wasu a ciki da suka iya suka hauyi suma
Anata tafi ana waƙen gunin ban sha'awa.
Note: waƙe ne da musulunci ya yarda dasu, don't come and attack me 😎
Sosai walimar tayi armashi, aka ƙaru sosai, waɗan da jikin su yayi sanyi saboda tsoratarwan
datayi duk suka warware wajen waƙe da kaɗa kai.
Shima gab da magriba aka watse, bayan an gabatar da hotuna, ciye ciye da shaye-shaye.
WASHE GARI
RANA BATA ƘARYA SEDAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA!!!
Tunbatsar da gidan yayi ba'acewa komi, mata ne ta ko'ina,
Tsabar cikar gidan har seda ta kawo da an buɗe makeken gate ɗin gida
Runfuna ne da kujeru ta ko'ina, karku mance biki ne na masu shi masu ƙubar susa
Matane hawa hawa, waccen wace wannan, wannan wace wancan
Kowa kaga fuskar shi zaka san yana cikin murna da farin ciki banda ƴan tsiraru daga ciki
Ciki kuwa harda mumtaz da mama da har shi Abba ƙarami da faɗuwar gaba ta same shi a
safiyar ɗaurin auren
Haka zalika kalid,
Daga wayewar gari zuwa yanzu ya ƙira mumtaz a waya yafi a ƙirga, kuma in ya kirata abu ɗaya
yake tambayar ta shine "Ba wani abun dai ko" har ma ta gaji da amsashi.
Sanda ya faruk ya tafi, se washegari ya buɗe jakar turarukan da mumtaz ta bayar a bashi
seda abun yaso bashi dariya da yaga duk turarukan mata ne
Ɗaya bayan ɗaya ya hau shinshinar turarukan, yanayi yana lumshe ido tsabar yarda sukayi
masa daɗi
Yana tsaka da jin daɗin shi zuciyar shi tace "Allah yasa ba satar su tayi ba dai"
Nan da na mood ɗin shi ya sauya haɗe da jin wata mummunar faɗuwar gaba.
HMMMMM.
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg53-54
Tunda garin Allah ya waye mumtaz ke zauna a bedroom ɗin Abba ƙ
Ita batayi wanka ba, ba ta kuma da niyar tashi tayin.
Kusan tashi uku mama na shigowa ɗakin, a inda ta barta a nan take isketa,
Har ita maman tayi wanka ta shirya duk mumtaz na nan zaune, ta muskata nan ta muskuta can
A shigowa ta huɗu ne mama tace "Kalli agogo fa mumtaz, sauran duk sunyi shiga ta bibbiyu
amma ke ko ɗayar bakiyi ba, ni shin gaya min gaskiya, kodai kina da wata damuwar ne da kika
kasa gaya min"?
Sadda kanta ƙasa tayi ta kasa cewa komi, se hawaye da suka fara tsere akan kumatun ta
Jikin mama dama a sanyaye yake, nan da nan ganin hawayen ɗiyar tata yasa jikin ta ya sake
yin sanyi
Kayan dake hannunta ta aje sannan ta matsa kusa da ita
A hankali ta janyota ta rungume ta, cike da tausayi da kuma ƙauna irin ta uwa ta fara shafa
bayanta, a hankali tace "Ki gaya min ko dai kun samu matsala da khalid ɗin ne?"
Tana cikin jikin ta ta karkaɗa kai,
Maman ta sake cewa "To gaya min menene?"
Cikin sheshekar kuka tace "Kawai bana jin daɗin jiki na, kuma gabana na yawan faɗuwa
akai-akai"
Murmushin yaƙe mama tayi ta ɗago da kanta daga jikin ta
Sosai ta fuskance ta tukun tace "Wannan ba wani abu bane mumtaz, duk amarya a ranar auren
ta takan fuskanci abubuwa makamancin waɗan nan da kike ji, daurewa ake da zaran an ɗaura
auren zakiji kin dena ji"
Mumtaz tace "Amma mama jiya a wajen walima seda na tambayi Amal ko itama tanajin hakan
tace min a'a"
Shiru mama tayi can tace "ai shine nace miki ya danganta, ta yuwu ita ba kalar naki take ji ba,
wani daban take ji"
Bata sake cewa komi ba,
Seda maman ta sauya kaya tukun tace
"Maza kije kiyo wanka, ga akwatin kayan ki nan, zan turo me kwalliyar zuwa palo se ki fito tayi
maki"
Ɓata fuska mumtaz tayi tace "yau ba zanyi kwalliya ba mama"
Kai tsaye maman tace "zakiyi, zance ayi maki light one" ta juya ta fice tana amsa call.
Gida ta ko'ina ba matsaka tsinke, kowa ka gani ya cike da murna da kuma fara'a
Wasu sunyi group ana ta fira wasu kuma suna ta harkokin su
Daga can gefe sautin waƙar gwanja ne ke tashi
Duk da ba rawa ake ba amma daga gani kasan sautin na kaima kowa
Ta ɓangaren amare kuwa ko wacce daga cikin su ta gaji da haɗuwa
Babban palo aka ware musu su da ƙawayen su,
Sakina ce keta tarbar ƙawayen mumtaz dabata fito ba haryanzu
Sauƙinta ɗaya ma ƙawayen nasu ɗaya ne da Amal, amma ko wacce in tazo bataga mumtaz ba
se ta tambaya
Da dai Amal ta gaji da tambayoyin yasa ta janyo waya tayi dialing no ɗin mumtaz
Ana tsaka da mata kwalliya call ɗin Amal ta shigo,
Ganin an kusa gamawa yasa bata ɗaga ba dan dama tasan ƙorafi ne.
Ta ɓangaren angwace ba'acewa komi, in ka kalli wannan sekace yafi sauran kyau, da ka kalli
wani shima se kaga kamar yafi wancan kyau,
Khalid na zaune kusa da kamal yana ɗaure igiyar takalmin ƙafar shi
Waya kare a kunnen shi yana sauraren mami dake ƙorafin kar ya wuce wajen ɗaurin auren ba
tare da sun biyo taga wankan shi ba
Murmushi kawai yake zubawa, sannan yace 'na san yarda mamina ke sona da kuma son nayi
aure tabbas zata so ta ganni for the last time a matsayin saurayi kafin na zama ango kokuma
ince magidanci"
Dariya da salati a tare mami ta hau yi kafin tace "naji ka dai zo in ganka" tana gama faɗin haka
ta ajiye wayar taci gaba da saka ɗankunne a ɗayan kunnen.
Khalid na aje wayar mami abokan shi suka hau tsokanar shi da mummys boy
Shidai murmushi kawai ya ke ta faman yi yana jin azalzalar ayi a ɗaura auren nan ko ya samu
nutsuwar zucia.
*****
A mugun fusace uncle Abbas ya sauke ma Tk mari a duka kumatukan shi
Cikin zafin rai yanuna shi da yatsa yace " Har kai ka isa ka nuna min ga yarda zanyi a al'amura
na? tun jiya nake lallaɓa ka akan ka bari ina da shiri na amma ka ƙi ji, na faɗa na kuma faɗa
mumtaz bata da wani miji da ya wuce kai a yau ɗin nan saboda ina da tabbaci daga majiya me
ƙarfi, ohhh shine zakazo kana min barazana da zaka faɗi gaske cewa ni na saka ka danne
Abubakar(Abba ƙarami) ka kashe shi, ko kuma ka sanar mu muka saka a tsinke wayar burkin
motar shi?"
Cikin zafin rai ya ƙara matsawa kusa da TK dake ja da baya ya ɗora da "to da kayi babban
kuskure a rayuwar ka, kallo na kawai kake a matsayin mahaifi amma kai kanka kawar da kai ba
wani abu me wahala bane a waje na, sakarai shasha"
Still a cikin fushi ya juya gefen gadon ɗakin hotel da ya kama saboda cinkoson mata a cikin
gida, ya janyo babbar farar leda me ɗauke da farar shadda aciki
Wirga mishi ledar yayi kafin yace "kaje ka shirya, kuma karkayi wasa da turaren da na baka ka
tabbatar da seka hango Abubakar(Abba ƙ) tukun zaka shafa a hannun ka, ka tabbatar da ko
yaya ne hannun ka ya taɓa jikin sa kafin a ɗaura auren, daga nan ka gama naka se kaja gefe
kayi kallo"
Duk da ya TK yaji marin da uban nashi yayi mishi amma jin wannan bayanin ya wanke mishi
zuciya, ko ba komi yanzu ze nuna ma ya faruk yafi kusanci da Abba ƙ da kuma duk wani abu da
ya mallaka
Seda TK ya ɗauki ledar tukun yace "sorry dad, nima ba da son raina nayi maganar ba" yana
gama faɗin haka ya juya ya fice ranshi fess.
KHALID
Ɗaya da kusan rabi ya shiga cikin gidan nasu inda shima a cike yake danƙam da mutane
Tunda ya shigo yaje gaishe gaishe
Guɗa ta ko'ina se tashi take
Mami nadaga can ta jiyo guɗar mutane, da sauri ta tawo dan ta san be wuce kalid ɗin ne ya
shigo
Tana zuwa kuwa ta rungume shi haɗe da fashewa da kukan murna da kuma tunowa da
mahaifin shi
Shi kanshi dauriyace kawai ya ara ya yafa ma kanshi, amma ƙiris da ya fashe da kukan
Mami na rungume da shi ta rinƙa jeho mishi addu'oi mutanen kusa da ita suna amsawa
Ta jima a haka, kafin kamal ya matso kusa da ita yace "mami time ya kusa wallahi, 2pm ne
ɗaurin auren fa"
Da ƙyar dai ya zame kanshi daga wajen ta suka ɗunguma zuwa babban masallacin dake
manne a jikin gidan amaren.
Fotowar mumtaz kenan taji ana ta guɗa a palon ƙasa, kamar ta fasa sakkowa take ji
Badan calls ɗin da ƙawayen su keta auno mata ba da bazata sakko ba
ISMAT ƴar ƙawar mama da bata jima da isowa ba, dataga alamun juyawa mumtaz zatayi yasa
ta taro ta, galla mata harara tayi kafin tace "Halin ki sak da na yaya mardiya wallahi, kuyi ta abu
kamar baku da gaskiya"
Mumtaz bata ce komi ba, dan tasan musu da ISMAT ɗin Ummu ba riba shiyasa ta lafe a jikin ta
suka fara takowa
Tana sakkowa daidai nan taga mama ta rungume ya faruk da yasha galleliyar farar shaddar shi
da ta amsa sunan ta
Yarda yake sheƙi da walwali kwa rantse da Allah shine angon
Sakato Mumtaz tayi tana kallon su
Sam fara'ar fuskar mama taƙi ɓoyuwa, gefen kumatun shi ta mangara tukun tace "ka kyauta
daka dawo yarona, a jiki na naji kamar wani abu da na rasa ya dawo"
Dariya yayi yace "wallahi saboda ke na aje komi mamana nazo, daga tafiyata na gane baki so
hakan ba, shiyasa ni kuma nace dole nayi suprising ki"
Kafin mama ta sake magana ta hango mumtaz, da sauri ta kamo hannun ta
Tsakiyar ita da ya faruk ta shiga sannan tace wa me hoto ya ɗauke su
Haka camera man ɗin nan yayi ta kashe su da hotuna
ISMAT kam wayar ta kunna itama tayi ta kashe su
Tajuddeen(me hoton) yace "Hajiya ɗan fita a yi musu au biyu"
Fita mama tayi, nan kuma tsakanin ya faruk da mumtaz aka tsaya kallon kallo
Ko a jikin Tajuddeen ya matasa kusa da su sannan yace
"yallabai matso kayi haka" ya nuna mishi ya dafa ta
Ganin zasu ɓata mishi time yasa ya ɗauki hannun ya faruk da kanshi ya ɗora a kafaɗar mumtaz
data ɗan sunkuyar da kanta
Ganin da sauran space a tsakanin su yasa ISMAT matsowa da sauri ta tura mumtaz jikin ya
faruk
Da yake Tajuddeen mayen hoto ne tuni ya samu ya hashaska su, kai kace shine mijin
Bayan ya gama ɗaukan su, ya faruk ya juya ya fice da sauri dan gaf ake da fara ɗaura auren
Ɗago kan da Tajuddeen zeyi yace "Kai ban taɓa ganin angon da sukayi mugun dace da
amaryar sa ba irin wannan"
Daga mama har mumtaz seda suka ji wata faɗuwar gaba dajin furucin Tajuddeen me hoto
Ganin ba wanda ya bashi amsa yace "next, se suwa za'a ɗauka"
ISMAT na dariya tace "muje ta can" sannan taja mumtaz suka ƙarasa ficewa zuwa babban
palon da amaren da kuma ƙawayen su suke.
Tunda ya Tk ya iso wajen yake kutsawa ya samu ya dangane da cikin masallacin
Duk inda ya saƙa be yarda Abba ƙ ya ɓace wa idanun shi ba
Cunkoso ne sosai a wajen, amma haka ya kurkurɗa har ya dangane da gaba gaba inda wakila
duka angwayen ke zaune
Can ta gefe ya hango Abba babba da Abba ƙarami se kuma uncle junaid yayan mama
Ta ɗayan ɓangaren uncle Abbas da uncle ƙasim se ya faruk a gefen su da kuma dr jamal a
kusa da ya faruk
Kusa da Abba ƙ ya matsa mutum ɗaya ne a tsakanin su, daga can uncle Abbas na kallon shi
ganin ya dangane da Abban yasa shi lumshe idanun yana sauke ajiyar zuciya
Cike da kula ya Tk ya sunkuyar da kanshi tukun ya zaro kwalbar turaren daga cikin aljihun shi,
da ƙyar ya kwance ledar duk dai yana bi a hankali kar ya tama kayan shi
Yana samu ya kwance ledar ya buɗe murfin shima da ƙyar tukun ya tsiyaya turaren a tafun
hannun shi, ya riƙe kwalbar da ledar da kuma murfin a hannu ɗaya
Tsabar mugunta seda ya wani runtse idanu tukun ya matsa a inda yake tunanin Abba ƙ ɗin na
zaune, a wayance ya shafe wannan turare da ya zuba kaf a jikin uncle junaid, wanda a tunanin
Tk a jikin Abba ƙ ya saka
Buɗe idon da zeyi ya hango Abba ƙ ya matsa can wajen da liman ke sallah yana amsa waya
A mugun tsorace ya ja baya, tsautsayi da baya wuce lokacin shi, aikuwa sauran turaren ya kife
a jikin ya Tk
Tsaf akan idon uncle Abbas da hankalin shi yafi na Tk tashi
A mugun tsorace uncle Abbas ya miƙe tsaye, har uncle ƙasim na tambayar sha da "lafia?"
Ko amsa be bashi ba, yafara ƙoƙarin cinma Tk dayayi mutuwar tsaye anan inda yake
Kafin uncle Abbas ya ƙarasa wajen Tk ya fara jin juyawar kai da kuma ɗarsuwar abu a zuciya
Ko tunani na biyu beyi ba ya matsa can kusa da Abba babba
Abba Abba na ganin shi yace "ya akayi ne Tk?"
Kanshi a ƙasa yace "Inaso ka nemar min auren sakina a hannun mahaifin ta uncle junaid Abba
b"
Da mamaki Abba b ke kallon shi, bama shi kaɗai ba har sauran dake gewaye a wajen ma sunyi
mamaki
Uncle junaid na gefe idon shi sun kaɗa sunyi jajir, ga wata muguwar azalzala da yake ji a cikin
ranshi
Uncle Abbas na ganin an tsaya saurarar Tk ya koma kawai ya zauna, dan yasan tunda
tsautsayi yasa har turaren ya taɓa shi to ba makawa se an ɗaura auren
Amma inda zaku duba kuga a wani irin yanayi zuciyar shi ke a ciki se kun firgita da mugun
baƙin da zaku gani.
Wasa-wasa magana ta zama babba,
Uncle junaid da kanshi ya amsa da ya ba Tk auren sakina
Ya faruk da gayya ya cire sadaki ya biya ma Tk
Har aka ɗaura auren Tk da sakina mamaki be bar zukatan kusan kowa dake wajen ba
Da gangan ya faruk yace a fara ɗaura na Tk dan ba'a san abinda ubangiji ya ɓoye a ciki ba
Aikuwa nasun aka fara ɗaurawa, sannan aka ɗaura na hafsa se Bilkisu sannan Amal se najwa
Kafin a ɗaura auren mumtaz ya faruk ya saɓar ya bar wajen cike da ƙunar zuciya da rashin
sanin abun yi kuma.
ALHAMDULILLAH aure ya ɗauru tsakanin khalid safwan da amaryar sa mumtaZ Abubakar
Haka maroƙi yayi ta kururuwar faɗar sunayen angwayen da kuma amaren
Khalid da suke tsaye ta can ya lumshe ido haɗe da godiya ga ubangiji jin anɗaura
Jikin shi har rawa yake wajen ciro wayar shi yayi dialing no ɗin mumtaz.
HMMMMM, AKAWAI FA LUKUTAR MASIFA JAMA'A!!!!!!
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg55-56
Mummy na cikin jama'a taga uncle Abbas ya shigo fuuuu kamar ze tashi sama
gaisuwa da mutane ke masa ko kallo basu ishe shi ba yayi ciki
Da mamaki mummy tabi bayan shi, sanda ta je har ya kulle ƙofar bedroom ɗin shi
Tsaye tayi a bakin ƙofar tana so ta gano abunda ya ɓata wa mijin nata rai har haka
A hankali ta fara kiran sunan shi tana ƙwanƙwasa ƙofar ya buɗe
Cikin tsananin fushi da hargowa uncle Abbas yace
"Wallahi da zaran kin ƙara taɓa ƙofar nan a bakin auren ki!!!"
A mugun bazata mummy taji furucin
Sakato tayi tana jin yarda bugun zuciyarta ya ƙaru daga jin furucin sa
Da yake tasan halinn zuciyar shi, a ranta tace "yanzu haka abinda akayi mishi be taka kara ya
karya ba yake wannan ɓacin ran," dawayewa tayi ta ja ƙafafuwanta ta bar wajen ta koma wajen
mutanen ta.
Tunda uncle Abbas ya kulle kanshi a ɗakin yake buga number malamin nasu,
Busy kawai ake ce mishi, amma ya ƙi haƙura ya manne wuta, da ta tsinke ya maida wani, daga
ƙarshe ma akace wayar akashe take.
Wurgi yayi da wayar sannan ya dafe kanshi da hannu bibbiyu ya kifa goshin shi a jikin bango ya
runtse idanu
Da ƙarfi ya ce "no! bazeyuwu ba billahillazi, ba zan ɗauki asara ba ban kuma santa ba" the way
yake magana da ƙarfi badan hayaniyar ƴan biki ba da babu abinda ze hana a ji shi.
Ganin yana neman zarewa a ɗan ƙanƙanin lokaci yasa ya janyo drower gefen gado ya zaro
kwalin sigari ya buɗe ya hau kunna musu wuta yana zuƙewa
A ƙanƙanin lokaci ya zuƙe kwalin tas sannan ya fara samun ɗan sukuni a ranshi.
Amare da ƙawayen su suna a nan anata shewa
Amal ta shigo palon da gudu tana haki
Kusan kowa kallon ta yake da mamaki
Hafsat ce tayi tsalan tace "oh Allah ya kyauta miki kedai, kar ki manta kin dai zama matar aure
tun ɗazu"
Dariya da shewa sauran suka saka, banda mumtaz data kafe ta da ido
Seda Amal ta zauna ta mayar da numfashin gudun data kwasa tace "Gulma da ɗumi ɗumin ta
na kwaso yasin"
Bata jira amsar su ba ta ɗora da "Ya TK shima ya angonce"
Ido a waje Najwa tace "Amma ba ya Tkn da na sani ba ko?"
Dariya sosai Amal keyi bayan ta kalli sakina dake ta wani taɓe baki irin ko'ajikin nan nata
Cike da son tabbatar da gaskiyar zancen mumtaz tace "a ina aka bashi auren tunda dai naga
alama kin koyo gulma kema"
Dariyar ta kawai take kwasa, lukutar masifar data hango a fuskokin mutanen gidan kawai ya
isheka sanin cewa AKWAI LAUJE A CIKIN NAƊI!
Ganin Amal taƙi basu amsar tambayoyin su ne yasa suka shareta dan maganar dama batayi
kama da warce za'a yarda da ita ba.
A waje kuwa, ana gama ɗaurin aure uncle junaid ya bar wajen saboda yarda yake jin kan shi na
jujjuyawa.
TK kam ya shiga sahun angwaye bakin nan nashi har kunne yake gaisawa da mutane ana
masa murna da sam barka.
Wurin a hautsine yake bama ka iya gane inda kowa yake
Ɗaurin aure ne ba na mutum ɗaya ko biyu ba
Shiyasa cinciridon jama'ar yayi yawa.
A haka dai aka rinƙa ragewa ana watsewa
Duka angwayen ko wanne tawagar shi sun bishi zuwa reception da suka shirya
Sam khalid beso tafiya ba, yaso se yaga fuskar amaryar tashi, bata samu amsa wayar shi ba,
ga gidan kuma ba ze shigu ba a yanzu, haka nan ya shige mota kamal yaja suka nufi wajen
reception.
Ba abinda mama ke maimaitawa se kalmar "innalillahi