Author : ZAINAB FALALU Category : African Stories & Novels
suka shigar da su palo suka hau bubbuɗewa
Mami na daga gefe ta zabga uban tagumi tana kallon kayan
a cikin ranta tace "basu taɓa komi ba ma ashe".
Bayan sun koma gida mama taji abinda gidan su kalid ɗin suka ce, murmushi tayi tace "ku rabu
da su, Allah ya rufa mana asiri kawai".
***Umma babba tunda ya faruk ya barmata assignment take tufka da warwara, har ma bata san
time ya tafi haka ba
Duk in ta ƙulla se taga warwarar daga ƙarshe ba aibu bace ba kuma abar ƙyama bace sannan
kuma alamar tambaya ce me girman gaske.
Da dai tayi tayi ta gaji, haƙura tayi ta miƙe haɗe da faɗin "Allah ka warware mana komi cikin
sauƙi da salama, ka hanamu cutar da ɗan kowa albarka annabi muhammad"
Kai jama'a tun kafin lauje ya warware daga cikin naɗi umma babba tayi la'asar fa
Haka kawai take ji acikin jikin ta akwai wani ƙulli me girman gaske a lamarin.
Sanda labari ya iske Amal cewa aure ya koma kan ya faruk tayi matuƙar shiga ruɗu
bama ita kaɗai ba, harda sauran amaren da suma al'ajabi be barsu ba
Duk wanda suka tambaya kanun zancen sedai yace "haka kawai khalid ɗin ya sake ta aka
mayar da auren akan ya faruk"
Abun mamaki sanda hafsat ta kira umma babba dan taji dalilin hakan,
umma babba ta tsinci kanta da kasa faɗin komi game da mumtaz, abu ɗaya tace "Sauyin
ubangiji ne kawai hafsa".
Kusan hakan maganar take a kunnen kowa, takamaimai ka titsiye mutum kace meye dalilin da
yasa aka mayar da auren mumtaz kan ya faruk,?
Sedai suce "Ikon ubangiji ne".
TO HAKA UBANGIJI YAKE ABUN SHI, IN YA RUFA MAKA ASIRI TO BABU WANI MAHALUKI
DA YA ISA YA TONA SHI
SHIYASA AKO DA YAUSHE MUKE ROƘON UBANGIJI DA YA RUFA MANA ASIRI DUNIYA DA
LAHIRA, YA HANE MU AIKATA AIKIN DANASANI.
Goma saura na dare su Abba babba suka tara matan su da kuma ƴaƴan su kaf dake ma'aura,
da kuma wanda kenan cikin gidan banda wanda aka kai jiya,
Mumtaz na raɓe jikin mama taƙi yarda ta buɗe ido sam tsabar tsoro da kuma abinda take
tunanin ze kai ya kawo
Ƙafa ɗaya kan ɗaya umma babba ta ɗora tana zaune a gefen Abban ta dama, umma ƙarama
kuma na gefen shi ta hagu
Mama na kusa da Abba ƙarami da shima zaka ga annurin fuskar shi ya daɗu,
Uncle ƙasim ma aunty na kusa da shi.
Unccle Abbas da shima da ƙyar ya yarda ayi zaman yana zaune kuaa da mummy
Goggo safiya na daga gefe.
Yaran duka suna zaune a ƙasa
Ƴaƴan ta mata gaban su na ta faɗuwa dan sun san umma babba ba ƙaramin shiri tayi wa
zaman ba
Da addu'a Abba babba ya buɗe taron, sannan ya fara da ban haƙuri ga wanda suke tunanin
ba'ayi musu daidai ba
Nan Abban yayi nasiha me ratsa jiki kafin ya waiga ga umma babba yace "a matsayin ki na uwa
nasan ban kyauta ba da ban baki damar ki ba, amma ina me baki haƙuri"
Ido ɗaya umma ƙarama ta kashe wa uncle Abbas da gaba ɗaya hope ɗin su itace umma babba,
botsarewar ta kawai suke jiran ji
Amma ga mamakin su da Abban ya kai ƙarshen maganar shi, se ji sukayi umma babban tace
"ai kai da kaya duk mallakar wuya ne, Allah ya bashi ikon riƙe ta da gaskiya da amana, ya tsole
idon maƙiya"
JAKAR UBAN CAN 😳
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg73-74
Tsit palon yayi, wanɗanda kansu ke a ƙatsa duk suka ɗago tsabar yarda kunnuwan u suka kasa
gasgata abinda suka ji
Bama yaran kaɗai ba, kaf iyaye matan da mazan mamaki ne kwance a fuskokin su
Mama kam sakin baki tayi bilhaƙƙi da gaskiya tana kallon umma babba da tai mirsisi da
idanuwan ta
Ƴaƴan umma babba kaf idanun su ciccikowa da ƙwalla sukayi jin irin bazatan da mahaifiyar tasu
tayi musu
Abba babba shi kanshi maganar umman tayi mugun bashi mamaki, ta wani fannin kuma a take
yaji ƙimarta na daɗuwa a zuciyar shi, ko ba komai bata kunyata shi ba
A hankali mama ta maida kanta ga ya faruk dake gefe yayi folding hannayen shi ga ƙirji
A fakaice tayi mishi jinjina da hannun ta, dan ta san ba aikin kowa bane inba shi ba, duba da
sanin kafaffen hali irin na umma babba.
Mumtaz kam banda raba ido babu abinda take, dan ita har ga Allah bata yarda da abinda umma
b tace ba
Hajiya umma ƙarama kuwa ƙiri-ƙiri zaka hango rashin nutsuwa a tattare da ita, ga uwar zufa
data ke ta fama gogewa a fakaice
Goggo safiya ta gyara zama duk da itama mamakin ne kwance a fuskar ta tace "To se muyi wa
ubangiji godiya,
Nasan yarda nake cikin bazata haka kowa yake a nan" ta maida kallon ta ga umma babba da
har yanzu ƙafarta ɗaya na kan ɗaya tace "Kin kyauta ƙwarai da gaske hajiya Nabila haka
akeson babba ya kasance kullum cikin fahimta da fawwala ma ubangiji komi, wallahi dole mu
faɗa kin mana bazata, Allah yayi riƙo da hannayen ku wajen riƙe amana"
Da "Amin" kowa ya amsa, fuskar kowa da fara'a da annuri banda uncle Abbas da yayi mutuwar
zaune tunda yaji furucin umma babba
Ga Tk da ya gama ƙullin shi shima zaune, idanuwan nan kamar zasu faɗo ƙasa saboda
muguwar hararar da yake aikawa ya faruk.
Cike da farin ciki uncle ƙasim yace "magana ta ƙare anjima se a sada ta ga ɗakin mijin ta"
Ba wanda ya ankare se ji sukayi Tk yace "wallahi da sake babu wanda kuma ya isa ya sake
titsiye ni yace na saki matata alhalin warda ake jira aji ta botsare bata botsare ba"
A firgice umma ƙarama ta dafe bakin ta,
Uncle Abbas kuwa cikin zafin nama ya sauke ma Tk tagwayen maruka, cikin tsananin fushi me
haɗe da tsoro yace "Baka da hankali ne Tk, iyayen ka na magana kana magana, kodai kaje
kasha abinda ke maka saƙe-saƙe a cikin kai ne?"
Umma ƙarama na ganin hankalin kowa ya koma kan Tk ta samu ta saɗaɗa ta bar palon ta nufi
ɗakin ta.
Abba babba da yafi kowa zafi shima yace "Ku rabu da shi, maimaita abinda kace Tukur"
Ƙunƙuni ya hauyi, ya kasa magana
Tsintsinkewa kawai zuciyar Uncle Abbas keyi, karon farko da tsoro me tsanani ya kamashi
Tsawar da Abba babba ya daka mishi yasa shi faɗin "Ina nufin nima a anso min tawa matar
tunda kowa ana maganar shi amma anyi shiru da tawa"
A kusan tare umma ƙarama dake laɓe suka sauke ajiyar zuciya ita da uncle Abbas da ya silale
ya koma ya zauna
Sedai abinda basu sani ba shine ba ƙaramin yaro kaf a palon, maganar Tk ta farko abar
tunanice a ƙwaƙwalwa
Yarda umma babba ta zauna tana fasa maganar a kanta abun se ya baku mamaki
Daga haka dai iyayen maza suka sallami kowa ya rage se su kaɗai se kuma goggo safiya.
Ba ƙaramin mamaki umma babba ta shiga ba ganin yarda manyan ƴaƴan nata ke murna, masu
raguwar zuciya daga cikin su harda kuka
Nan ma zuciyarta ta sake yin sanyi
A nan palonta ta barsu su duka ta shige bedroom
Seda ta kulle ƙofar tukun t zauna tana sake fasa maganar da Tk yayi
Can data gama fasata ta kuma ɗauko maganar da ya faruk yayi mata a ɗazu ta haɗa, se ta ga
abun ya bata ma'ana ɗaya
Ta jima sosai a zaune tana nazari har lokaci yaja bata sani ba, daga ƙarshe a bayyane tace
"Tabbas AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI a maganar shi".
Abba ƙarami ne ya amshi maganar Tk da niyar gobe Ze kira aminin nashi ya sanar mishi da
zasu zo su ɗauki amarya sakina.
Da wannan maganar ta Abba ƙarami aka rufe taron, bayan faɗa me zafi da Abba babba yayi
masa.
Umma ƙarama data shiga ɗaki waya ta ɗauka ta kira uncle junaid da shima jarabar maman
sakina tasa ya kulle kanshi a ɗaki
Jiki na rawa umma ƙarama tace "wallahi junaid asirin mu na gaf da tonuwa, nidai na kasa
sukuni gaskiya ku kira malam kusa shi ya rufe mana bakin kowa gudun jin kunya"
Shiru uncle junaid yayi kafin yace "Baya ɗaukar wayata daga jiya zuwa yau, tuntuni naso ya
rufe min bakin sakina da mahaifiyar ta kafin mu samo bakin zaren"
Dogon tsaki uncle junaid yaja sannan yace "duk wannan wawan ne da ya sako mana ɗanshi a
tafiyar, wallahi ba dan ya sako sakaran ɗanshi ba da babu yarda za'ayi mu rinƙa shiga tashin
hankalin da ze sa har a farga da yanayin da mutum ke a ciki ba"
Still gaban ta na faɗuwa tace "kuyi magana da Abbas ɗin dai, shi ya kwatanta kiran shi, in ma
be ɗauka ba dole aje a same shi a daren nan kar wanki hula ya kaimu inda bamuyi tsammani
ba junaid"
Daga can uncle junaid yace "Bari nayi trying shi".
Ƙiri-ƙiri uncle Abbas na ganin call ɗin uncle junaid yaƙi ɗagawa, haka ya ƙaraci kiran shi har ya
haƙura.
A daren ranar bayan tashi daga zaman da akayi a palon Abba babba, ya faruk ya ɗauki
maganin da ya amso daga wajen Alramma ya nufi sasan mama
Ta can ƙofar baya ya shiga, har sama ya haura
A palo ya iske maman da goggo safiya se inna hassu da su kaɗaine sukayi saura a ƴan biki
Zama yayi suka gaisa da inna hassu, itace dama basu gaisa ba tukun ya matsa kusa da mama
yayi ƙasa da murya yace
"Mama na karɓo maganin tun ɗazu, ya kamata ta sha kar tayi wasa dashi kamar wancan"
Hankali kwance mama tace "shiga tana ɗakin ta"
Ɗan jimm yayi kaɗan kafin ya miƙe ya nufi ƙofar da zata sada shi da ɗakin nata.
Mumtaz na kwance ta kifa cikinta akan gado,
daga ita se ƙaramin baƙin wando da be wuce tsakiyar cinyar ta ba se vest fara ƙal da bata
ƙarasa rufe mata cibiya ba
Ga gashin ta da yasha gyaran biki ta baje shi, yarda take kwance haka gashin yabi lafiyar pilon
shima, kusan rabi ya rufe mata gefen fuska,
Wayar goggo safiya ce a hannunta, ta ƙuƙe se typing msg take
Gaba ɗaya hankalin ta da nutsuwar ta yana kan wayar, baka jin ƙarar komi a ɗakin se na
madannan wayar
Ya faruk ya turo ƙofar ya shigo bakin shi ɗauke da sallamar da bata kai ga fitowa ba ta koma
inda take
Tunda ya shigo ya ƙame a wajen kamar wanda aka dasa
Gaba ɗaya bugun zuciyar shi ya sauya daga yarda take, ta koma bugawa da sauri-sauri
Yarda yake a tsayen nan babu wani abu dake motsi a jikin shi se idanuwan shi dake bin ko ina
da ina na jikin ta da kallo.
Seda ya gama ƙare mata kallo ya saɗaɗa a hankali yakai hannu ya fizge wayar dake hannun ta
A firgice tace "wayyo Allah na" tana waigowa da sauri
Tana ganin waye a tsaye ta miƙe a guje ta sauka daka kan gadon ta ɓoye a bayan abun saƙale
jakunkuna ta tsaya
Fat-fat haka ƙirjin ta ke duka
Leƙo da kanta tayi taga ita yake kallo ko me, ga mamakin ta gaba ɗaya hankalin shi na kan
screen ɗin wayar da ya fizge daga hannun ta
Da sauri ta dafe ƙirji tunowa da tayi khalid fa take rubuta ma saƙo
Aiko mancewa tayi da kayan data saka ta fito da sauri tayi wuf zata ƙarɓe wayar
Cikin zafin nama ya damƙeta da hannun shi ɗaya sannan yaci gaba da karanta dogon saƙon
data rubuta ma khalid ɗin
Wutsil wutsil ta hau yi tana son ƙwacewa daga riƙon da yayi mata
Seda ya gama karancewa tsaf tukun ya maido da idon shi kanta
Jinjina kai yayi haɗe da ɗaga gira ɗaya yace "ohhh ashe har haddace number guntun can
kikayi"?
Zumɓura baki tayi sannan tace "Akwai no ɗin ai a wayar"
Ɗalle mata maki yayi da ɗayan hannun sannan yace "dan akwai number a wayar shine ya baki
damar yin magana da shi?"
Banza tayi da shi
Jin tayi shiru yasa ya sake matseta sannan yaja kumatun ta da ɗan ƙarfi yace "kin mance akwai
auren wani a kanki ko?"
Nan ma shiru tayi, tayi ƙwalƙwal da ido kamar me shirin yin kuka sannan tace "Haƙuri na bashi,
kuma na gaya mishi ni ba fasiƙa bace, bayan sata babu wani abu danake wanda be dace ba"
Nan da nan maganar datayi yasa yaji wani iri haɗe da tausayin ta na daɗa kamashi
A hankali ya samu gefen gadonta ya zauna, sannan ya janyota ta zauna akan cinyar shi
Seda ya ɗauki mintoci kafin yace "daga yau daga rana irin ta yau bana so na kuma jin kince
kina sata
Kuma kar na sake ganin ko da wasa kin sake ɗaukar waya da sunan zaki ma wani wawa da be
cancanci sanin ki ba sam msg, ki rabu da kowa"
Robar maganin da ya shigo da ita ya ɗakko, da kanshi ya buɗe murfin ya kai maganin bakin ta
Gintse baki tayi taƙi buɗewa,
Ware mata manyan idanun shi na gado yayi sannan yace "buɗe bakin ki kisha"
Duk da ɓata ran da take haka ta buɗe ya tuttula mata shi, seda ya tabbatar da tasha ya kai
adadin daya dace tukun yacire ya kulle
Jiki a sanyaye yace "da izinin ubangiji kin bar ƙara sha'awar kayan kowa daga yau"
Gaba ɗaya kunya ta rufeta
Hannayen shi nata zagaye a bayan ta kusan mintoci kafin ya sake cewa "gaya min abun wa da
wa kika ɗauka, kuma in kin ɗauka me kike yi da shi?"
Shiru tayi kanta a ƙasa, duk a takure take jin kanta
Seda ya sake maimaita tambayar tukun tace
"Tsaya in saka kaya to"
Buɗe idanun shi yayi sosai a kanta kafin yace "wannn su ba kaya bane?"
Banza tayi da shi, ta miƙe daga jikin shi
Shi kam be ma da energyn da ze iya hanata tashi, yana kallo ta ɗauki zumbuɗeɗen hijabi ta
saka sannan ta koma kan stool ɗin gaban mudubi ta zauna
Gyara zama yayi ya ɗan kishin giɗa a gefen gadon sannan yace "ina jin ki gaya min"
Kanta a ƙasa tace "agogunan Abbana nafi ɗauka, se na wani malamin mu guda ɗaya, se
agogon khalid da abun hannun mamanshi, se carbin umma babba, se kuma naka agogon"
Tana gaba faɗa ta sadda kanta ƙasa
Tashi zaune yayi yace "meyasa abun maza kawai kika fi ɗauka?"
Jiki a sanyaye tace "nima ban sani ba"
Gyaɗa kai yayi, a ƙasan ranshi yace "shima wannan akwai lauje cikin naɗi kenan"
Bayan ɗan shirun da yayi, can yace "to me kike da su in kin ɗauka?"
Still kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannun ta tace "Ba abinda nake da su, ajiyewa kawai
nake"
Bata gama maganar ba ta tashi daga inda take zaune ta buɗe wata jaka madedeciya ta miƙa
mishi
Ba musu ya karɓa, ya duba, a hankali tace "na baka naka, yanzu agogon khalid dana malamin
mu se kuma na Abbana ne kawai a cikin nan"
Hannu ya saka ya ciro carbin umma, kafin yace komi tayi sauri tace "se kuma carbin umma
babba"
Kallon carbin yayi yana tuna sanda ya ganshi ya faɗo daga jikin ta
Gyaɗa kai yayi ya miƙa mata jakar "ungo ajie, zuwa gobe in nazo kawo maki maganin ki se in
tafi da su"
Gyaɗa kai tayi
Ɗaukan maganin yayi ya nufi ƙofa,
Jiki a sanyaye ta bi bayan shi da kallo,
Kallo ne me ma'anoni da dama
Gaf da ze fita ya waigo karaf suka haɗa ido, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa
Murmushi yayi yace "Nafi wancan guntun kyau ko?".
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg75-76
Seda ya faruk ya jera kwana huɗu cif se bayan isha zezo da kanshi yabama mumtaz maganin
ta
A kwana huɗun nan shaƙuwar da ita kanta bata san ta yaya hakan ya faru ba ta shiga tsakanin
su.
****BAYAN SATI ƊAYA
Tsaf an gama gyaran gidan ya faruk inda mumtaz zata zauna
Haɗaɗɗu kuma tsadaddun kayan ɗaki Abba ƙarami ya zuba wa mumtaz tunda yaji labarin
abinda dangin khalid suka ce game da kayan
Dan kanshi yace a rabu da su kar wanda ya sake binsu.
Ƴan tsirarun dangin mama da kuma su ya sabiha ne suka je akayi jeren sabbin kayan da aka
siya
Duk wanda ka gani a gidan kasan ɗan'uwa ne duk wasu bare sun jima da tafiya.
Da yamma wajen ƙarfe biyar saura ya faruk ya nufi gidan da a yanzu can mus'ab ke zama
Da keys ɗin shi ya buɗe gidan ya shiga
Seda ya ƙare wa dattijon dake ɗaure a tsakiyar palon kallo sannan ya zauna a kujerar dake
kallon shi
Da ƙyar dattijon ya ɗago kai ya kalli ya faruk sannan ya maida kanshi ƙasa
Ya faruk bece mishi komi ba, sema wayar shi da kara a kunne, shirun da be wucw seconda yayi
ba kafin yace "uncle ƙasim ka shigo layin ne?"
Daga can yace "ina daidai gidan"
Fitowar mus'ab daga cikin bedroom kenan ya faruk yace "bari na shigo da uncle ƙasim"
zama mus'ab yayi yace "to"
Anan waje uncle ƙasim yayi parking, tukun ya biyo bayan ya faruk tambayoyi fal bakin shi.
Yana saka ƙafar shi a palon ya tsaya cak yana kallon mus'ab da ya tara ƙasumba a fuska
Raba kallon shi yayi,
ya kalli mus'ab da murmushi yaƙi barin fuskar shi, sannan ya kalli dattijon da yake a ɗaure a
ƙasa tukun maida kallon shi ga ya faruk da yasha baƙin gilashi fuskar nan a murtuke.
Ƙarasowa yayi a hankali idon shi a kan mus'ab yace
"Mus'ab yaushe ka dawo?"
Kai tsaye ya faruk yace "Ba inda yaje uncle, yana nan"
Da mamaki uncle ƙasim ya maimaita "yana nan fa kace?"
Be jira amsar su ba ya sake nuna mutumin dake ɗaure yace "shi kuma waye wannan kuka
ɗaure shi haka?"
ya faruk yace "calm down uncle ƙasim, dalilin zuwan ka nan kenan ai"
Be sake cewa komi ba se waje da ya samu ya ɗosana ya zauna, dan ya faruk da mus'ab sun
fara bashi tsoro.
Gyaran murya ya faruk yayi ya fara bashi labarin komi A-Z, sannan ya nuna mutumin nan yace
"shine tun shekarnjiya muka je na ɗakko bokan nasu na kawo shi nan.
Duk yarda zuciyar uncle ƙasim take da dakiya se gashi zaune dirshen yana kuka da idanuwan
shi
Kuka harda majina jin kalar cin amanar da ɗan'uwan shi da kuma matar ɗan'uwan shi suka ƙulla
Cikin su babu wanda ya lallashe shi, dan abin ayi kukane ga duk wanda yaji labarin cin amanar
nan
Uncle ƙasim yafi awa ɗaya kafin ya dawo normal, yayi shiru ya zabga tagumi yana kallon
mutumin da ya shirya dukka tuggun
Murya a dishe yace "all this while me yasa kuka bar abun a tsakanin ku baku fallasa maƙiyan
Allah ba?"
Haɗiye miyau me ɗaci ya faruk yayi sannan yace "Uncle ƙasim, in baka iya kama ɓarawo ba, to
shi se ya kamaka"
Ya faruk be gama rufe bakin shi ba wayar bokan tayi ringing a karo na