Masifaffiyar Ƙauna Soyayyar da Ta Fi Komai Ƙarfi by M SHAKUR

Author :  M SHAKUR Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 51

24K to 27K   out of 152.6K words

gida yake gayamin shekara uku yace kinga fadan dana mishi saikuma na share muka biyamiki kudin makaranta kika fara ss1, kanenki ma haka, muka chanza gida, yasai machine ya gayaramana daki yasai mana katifu kujeru da komidai dakika gani na wanan dakin ahaka kudi suka kare wanda har yau dadan ragowan chanjin muke rayuwa yanzu haka gobe ne ranan biyan bashi ko bada d'a Fatima ko akulleshi, ke yarinya ce Fatima mai basira ilimi dakuma fikra kinsan Habib yay karanta daza'a kaishi aikatau, Habib baidama hankali balle ya tsare kanshi saisa ubanki ya yanke shawaran kezaikai amman zamu maidake namiji" tunda Mama tafara maganan kanta akasa sai alokacin ta dago kanta ta kalli Mama shima Baba ita ya kalla sabida shairin dayaji tamai, wani mugun kallo tama Fatima tace "kobazaki rufama mahaifin naki asiri bane butulu? Dakuma nace maidake namiji ba ina nufin nane miki tsuliya ko yanke miki mama nake magana ba a'a zadai mu boye hallitunkine, ga kayan damuka siyomiki nan na maza" tanuna mata ganamasgon sanan tace "ke kinsan bantaba miki karya ba, inhar baki yardaba kulle ubanki za'ayi kuma kinsan mahaifinki baida kowa dazai iya biyamai miliyan ukun nan, saidai agana mishi azaba agidan yari karshenta ma akashe shi achan, kafin yay signing duk angayamai sharuddan nan kuma ya yarda ya amsa, idan yanzu suka tafi dake aikatau din zai dage da nema Oga Abdu yamin alkawari zai samomai aiki dudda baiyi makaranta sosai ba zamu dage nima zan fara sana'a cikin wata biyu ko uku mubiya mu madawo dake, zaki iya hakuri kiyi rayuwa namiji ki boye macen ki aciki na watanni dabasufi uku ba dan rufama wanan mahaifin naki daya miki komi asiri? Mahaifinki dake wahala dake tun kina yar tatsitsiya ya raineki shi kadai mutuminnan, yay achaba, yay faskare, yay leburanci duk sabida ke, yanzu lokaci yayi dazaki nuna mishi baiyi haihuwan banzaba kema yar halak ce zaki iya"? Ahankali ta kalli Baba dataga kanshi akasa dan hakanan yaji ayau yana kunyar yarshi bai chanchanci zama mahaifinta ba, tuna tun tana yarinya yanda yake wahala da ita tayi da wanan rashin lafiyan datayi, dakuma yanda yakeda hawan jini, aduniyan nan da'a kulle mahaifinta gwara an kulleta so dubu, da mahaifinta ya tozarta aduniyan nan gwara ta to tozarta sau dubu, da'aci mutuncin Abban ta gwara acinci nata, da ubanta yamutu gwara ita ta mutu, da Baba yasha wahala gwara tasha wahala. Cikin fushi Mama tace "kinmin shiru" ahankali takai hannu ta goge hawayen dasuka zubo mata tace "Mama babu abinda bazan iyama Abbana ba koma menene aduniyan nan, zanje zanyi aikatau din koda Baba bai sami kudiba zanyi aikin koma na tsawon shekara nawane dazai dauka bashin yakare, Baba kadena damuwa kaji karka fara ciwo" tai maganan ahankali tana kallon Baba dayaji jikinshi yadawo kaman kankara, wani hadadden murmushi Mama tayi tace "kaga yarinya yar albarka maison mahaifinta, duk diyar data rufama iyayenta asiri Allah zai rufa mata itama, cikin dare zan tadake na shiryaki anjima zamuyi kitso, dau kayan gwanjon kije ki wanke kinji ki shanya su bushe yauko mekikeso ninezan dafamiki dakaina yar albarka, me zakici"? Murmushi ta kakalo ta girgiza kanta tace "bakomi" cikeda farinciki Mama tace "ai ina saina saimiki tsiren dare yau" daukan ganamasgon tayi tafita dashi kayan tacire tadau omo ta tafi makwarara wanki, Mama ta kalli Baba dahar lokacin kanshi akasa tace "dalla me haka sokake tadauka akwai wani abu akasa ne iyye saki ranka jor mutuwa zatayi komene nifa banson haka, tashi kahau gado muyi baccin rana" tashi yayi yahau gado haka dan dolenshi tasashi yay bacci.


Wanke kayan tayi tass tana kallonsu itace yanzu zatasa wanan kayan mazan wandunan ma kaman sun mata tsawo dayawa, komawa tayi daki ta zauna, itakuma Mama saida ta tabbatar Baba yay bacci sanan tafito tace "xomuyi kitson" babu musgunawa haka Mama ta zauna ta zuba mata zane yan kanana masu kyau gashi har tsakiyan bayanta data gama ta tupke bakin gashin tace "cikin dare zamusa hulan fatan, nasiya miki always dayawa zan saka miki a kasan jakan duk wata karki bari kowa yasan kinayi kitafi da magungunan ciwon mara karki sake kibari asirinki yatonu dan kashe babanki za'ayi kinga yanda baida lafiya hawan jini yamai raga raga" kaman ba Maman data sabada itaba yau tsabagen dadi zama tayi tana koyama Fatima duk yanda zatayi harda koyamata muryan dazata dinga yi da kalan tafiya dakomima ranan bata bari tai girki ba ita tayi.





Cikin dare Mama tashigo ta tadata ahankali gudun karsu tada yara fitowa falo sukayi Mama ta zaunar da ita, tasanya mata bald cap dinan bayan ta zuba gum da ake sa bald din dashi ta shigar da gashinta tass ciki abin yabame bam gashi tasayo daidai kalanta fari sabida farace, kan yay kato amman ba chan chan ba, sanan tasamata fatar daya rufe hujinn kunnenta shima, cikedajin dadi Mama tace "tashi ki kalli kanki a madubi" ahankali ta tashi taje ta tsaya gaban madubin falonsu tana kallon kanta badadan atampan dake jikinta ba zaka rantse namiji ce ita, ahankali tadaura hannunta ta shafa saikon kannata hawaye taji zasu zubomata hango Baba datayi ta madubi yafito ya tsaya abakin kofa ya rungume hannunshi yana kallonta yasa tahadiye kukan tajuyo tareda murmushi tace "Mama yay kyau nayi kaman Habib ko" dan dariya Mama tayi tamika mata kallabinta tace "ungo daura karki bari su Habib suga kan, da sassafe gobe zan kadasu hadda karfe tara zaku tafi keda Babanki jekiyi kwanciyarki" wucewa tayi ta shige dakinsu itakuma Mama ta watsamai harara tace "wuce ciki" ciki yayi ba musu, daren cikinsu babu wanda ya runtsa ita Mama farin ciki yahanata Bacci zata rabu da ķaya Allah yayi fatanta Allah sa nan gaba agane mace ce asirinta yatonu su kasheta tahuta gaba daya dan ta tsani yarinyar nan, Baba kuma damuwa ainun yasan yacuci yarshi sosai, guilt yahanashi ya runtsa, itakuma Fatima kuka tayi sosai na tausayin Babanta yanzu bazata gansu ba sainan da wata uku, tana tausayin Babanta sosai tana addu'a Allah yabashi aikin yi sabida karyaje yasake karbo wani bashi dazai sakashi a matsala irin wanan.


Tun karfe biyar Mama ta tashi tadaura girki tana gamawa ta tadasu Habib tamusu wanka, kowa yafito yay wanka bakwai daidai ta kadasu babu yanda sukaso suka tafi haddan tun kafin 8, tacema Fatima taje tai wanka wanka tafitayi hakan yabata daman balbale Baba da masifa kan yasaki ranshi, hakuri yabata sanan ta barshi Fatima nafitowa daga wanka Mama tabita dakinsu.



Yau duk yanda takejin kunya saida Mama taganin mata nono, silkin doki Mama ta dauka da akama igiya ta bakunan guda biyu tace "kullum wanan zaki dinga daure nonon ki dashi sabida kar agansu" nannada mata tayi sanan ta daure tamau harsaida tai yar kara sabida azaba takasa tsayuwa da kyau, Mama tace "ahaka zaki rufama baban naki asiri tsaya da kyau jor" tsayawa tayi da kyau da kyar Mama tace "sannu duk idan zakiyi bacci kidinga kwancewa kadan" sanan tabata singileti tasaka sanan takawo rigan mazan navy blue shirt mai gajeren hannu tasaka Mama ta kulla boturin ba laifi nonon sundan boye sabida rigan dama burgujeje ne baka ganinsu sanan tasaka Jean din daya mata yawa mama ta nannade kafan suka kama kwankwason jeans din da igiya, sanan Mama tabata kamvas tasaka, Mama takoma baya ta kalleta batada banbanci da namiji kaman irin yaran nan maza da yanzu suka fara balaga dinan, kawai kyaune da ita sosai ga pink lips na bala'i which is normal daman sunsan babanta kakkyawa ne jini fulani da buzu ce yarinyar, ran Mama shar ta kwalama Baba kira tace "zokaga diyarka" shigowa dakin yayi shima ya shirya kallo daya yamata yadauke kai yawuce yafita, Mama tace "yanzu saka hijabi sabida kar yan gidanku su gane sai kunyi nisa sosai saiku cire babanki ya karba yaboye" hijabinta tasaka har kasa, Mama tahada mata jakanta fess saikuma tabata jakan goyon makarantan Habib tazuba mata abinci a flask tasa mata cinyan kaza da biskit guda biyu, da ruwan gora dakuma lakasera guda daya, karba tayi tana godiya, Mama ta kalli Baba daya zauna tace "tashi kutafi takwas da rabi" tashi yayi yawuce yafita Mama bata damuba tadau jakan tarike suka fito ta kwalama yan gidan kira tace "Fatima zataje hutu wajen Baabarta" sallama suka mata Maman Dady tabata 200 suka mata rakiya har waje, Baba yajuyo yana kallonsu agaban machin tasamai gana masgon itakuma tahau baya tana rikeda jakan Baba yatada machine din suka tafi.



Tafiya mai nisa sosai sukayi kasancewa hotel din dazasu da nisa dan hanya fita daga kano ne, sunyi tafiya mai mugun nisa sanan yay parking akan hanya ya sauka itama ta sauka hannunta yarike suka shiga wani uncompleted building dake kan hanyar har lokacin yakasaa kallonta, suna shiga ta kallai ahankali tace "Baba hijabin ko"? Da sauri ya gyada matakai yana juyamata baya, ahankali tacire hijabin tarike a hannu tana kallon bayanshi tasan yadamu hakan yasa ahankali tazagaya ta gabanshi ta kalleshi gani tayi idanunshi sunyi jajir kaman wuta, ahankali tace "Baba menene?" Kaman jira yake saukar da guiwowinshi yayi kasa ya rike hannuwanta biyu fuskarshi yadaura kan kafafunta baitaba kuka ko hawaye gaban yaranshi ba amman wanan karan yakasa daurewa saiga hawaye sharrr da sauri ta zube akasa itama ganin fuskarshi da hawaye yana kuka yasa tafashe da kuka sosai zatai magana yadaura hannunshi kan bakinta cikin wata irin murya mai rauni sosai yace "Fatimatul Zara'u kiyafeni, ki gafarceni, ki yafema mahaifinki, tunda na haifeki baki tabajin dadina aduniyan nanba, niba uba nagari bane, jibi abinda nasa kika zama, namaidake namiji sabida kawai na rufama kaina asiri, Fatima na cutardake dayawa aduniyan nan, dan Allah kiyafemin, kiyafema Babanki" wani irin kuka takeyi tashiga girgizamai kai tace "Baba kaine uba nagari dana sani aduniyan nan, da ace akwai wata rayuwa bayan wanan still kai zan zaba kazamto mahaifina Baba, kaizan saba danni kaina nasan I am so lucky da Allah yabani kai amatsayin ubana, Baba dan Allah kayakuri kadena kuka, bakamin komiba kaji, koma kamin nayafe maka duniya walahira nima kayafemin Baba" kamota kawai yayi yarungumeta tafashe da kuka sosai ajikinshi ta kankameshi dan yasa taji wani iri yanda taga Babanta nakuka, sun dade sosai ahaka sanan tace "Baba tashi mutafi zamuyi latti" tana maganan wayanshi na ringing sakinta yayi yana duba wayan yaga Oga Abdul ne bai daukaba ya maida aljihu yatashi tareda karban hijabin ya share mata fuska sanan ya ijiye hijabin awajen suka fito yahau machine itama tahau yatada suka shiga titi, tunda tai wayau bata taba fita ba hijabi ba ballema har ba dan
Kwali yau itace iska ke daka yana ratsa tundaga kanta, kunnuwanta da wuyanta haka, haka suka karasa hotel din mai suna Prestigious, yana shiga yaga Oga Abdul yaci suit sai kallon agogon dake daure a hannunshi yake, yana ganinsu yataho dagudu murya chan kasa yace "kayi latti sosai sokake kasamu a amtsala" ya kalli Fateema yace "good, from now sunanki Khalid understood" gyadamai kai tayi, yace "any question dasuka miki answer them da turenci, sukaga u are educated zasu yanka miki albashi mai yawa nan da nan agama biyan bashin babanki" tasake gyadamai kai, ya shiga gabansu da saurin shi yace "let's go" jikinshi har rawa yake hakan yasa taji gabanta na dukan uku uku, shiga hotel din sukayi sukai upstairs, wani babban hall suka shiga ga security guards gardawa aciki, hall ne da aka jera kujeru hadaddun gaske, ga maza manya magidanta amman irin talakawan nan haka kusan su 100+, ga yara samari maza agefe dabazasu wuce sa'oninta ba zuwa yan 22yrs suma zaune kan kujeru adayan bangaren kusan su 63 ko morethan ma, saikan hadadden stage din da akai decorating da flowers aka zuba wasu arnayen kujeru wasu hadaddun manya manyan lawyers ne da baristoci sunci suit suna rubuce rubuce ga laptops agaban su, da printers, kallon Baba Oga Abdul yayi yace "kujirani anan lemme talk to them nazo dan ankira sunanka yafi sau uku" stage din yayi zuwa wajen wani babban Barrister dan tsoho nema dukawa yayi yamai magana a kunne sanan yadawo yaje wajensu Baba kujera yanuna musu yace "kazauna za'a kiraku" zama Baba yayi yana rikeda hannun Fatima itama ta zauna a kujeran kusada shi, saishima Oga Abdul yazauna kusada Baba yace "yanzu nan police suka tafi dawani mutumi thank God kayi tunani mai kyau da....." "Muhammad Alhasan Muhammad" shiru Oga Abdul yayi jin ankira Baba, faduwa gaban Baba yayi haka itama Fatima dan yanzu saitaji tanajin tsoro sosai dan ga dukkan alamu wanan babban organization ne baba yaci kudinsu duk azatonta tazaci is just a small something, hannun Fatima yarike sukai stage, cikeda girmamawa ya gaida lawyoyin da duk suka zubamai ido suna kallon yanda danshi yay kama dashi, yace "yallabai bangama hada kudin ba amman ga......" kafin yagama maganan Barrister ya kalli Fatima yana gyara glasses din idanunshi yace "young Man akwai turenci" gyadamai Fatima tayi ahankali, yace "whats your name" gyara muryanta tayi ba yabo ba fallasa dudda muryam baiyi kaman na namiji ba hakama baiyi kaman na mace ba tace "ahhhm Khalid Muhammad" ajiyan zuciya Oga Abdul ya sauke, Barrister yace "how old are you"? Anatse tace "i am 19yrs old" documenting sukayi sanan yace "what level are you in school" ahankali tace "I just write waec this year" gyadamai kai yayi yace "what are you good at Khalid? What can you do what are your skills?" Shiru tayi saikuma ta kalli Baba taga kanshi na kasa sanan takalli Barrister tace "only house work" da sauri Barrister yace "don't you go to work" gyadamai kai tayi tace "only school and islamiyya i go" gyadakai yayi cikeda gamsuwa dan yaga yaron na kokari turenci shi dai ba laifi normal turenci yaro dan arewa dayaje school, juyawa yayi ya karbi wani bracelet dataga anciro daga wani akwati an rubuta 65 ajiki yace "give me your hand" bashi hannunta tayi ya nada mata bracelet din sanan yakalli Baba yace "because your son is educated and can communicate da English, salary dinshi every month will be 120,000 naira, yakama zaimana aikin watanni ashirin da biyar (25) shekara biyu da wata daya kenan" ya kalli Fatima da gabanta ke wani irin mummunan faduwa yanuna mata bangaren yaran yace "go and sit there with your mate, Abdul take her luggage to the car" gana masgonta Oga Abdul yafita dashi aka nunama Abba wajen zaman manya yawuce yaje ya zauna yakasa dagokai.

Wuraren 12 suka gama, sanan aka shigo da abainci yaran aka rabamawa hadadden fried rice da chicken da salad da ruwa da juice Barrister yace "eat Boys" yara sai dadi sukeji ganin abincin da basaci agida nan da nan suka cika hall din da hayaniya sanan akai dismissing iyayen su, security guards na fitarda su suka fara fita, da sauri tadaga kai ta kalli Baba kin kallonta yayi harya fita tareda Oga Abdu yaki juyowa ya kalleta saidai yana tafiya ahankali kaman baida jini ajiki, ahankali taji hawaye yazubo mata kaman daga sama taji an rungumota takafad. "Dalla karkai kuka saikace wani mace eh guy" da sauri ta daga kanta wani saurayi tagani dabazai wuce 20 ba yana sanye da riga da wando shima kabar da hannunshi tayi cikin sabon muryanta tace "dalla malam karka kara tabani" taja kujeran ta ta matsar tabude jakan bayanta tasa takeaway aciki ta ijiye jakan akasa ta kafa fuskarta akan kafafunta kawai ta shiga kuka mai taba zuciya.




_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._
6/23/21, 6:12 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫


_MASIFAFFIYAR KAUNA_




✍🏾M SHAKUR



EPISODE 1️⃣2️⃣
_FREE PAGE_


Sauran yaranne sukahau dariya though not all dan wasuma sunyi shiru sun natsu daga gani suna kewan iyayensu, shikuma yaron wani hararan shi yayi yafaracin abincishi kawai, takai kusan 20min ahaka, sanan ta tashi tagoge fuskarta tas da idanunta tass, ahankali taduka tadau jakan budewa tayi tadauki takeaway ta tabude ahankali tashiga turama kanta abincin sanan ta ijiye acikin jaka duk suna zaune wajen su kadai sai hayaniya yaran suke har wajajen karfe uku sanan securities suka shigo sukace "kutashi kuyi layi masu son amfani da bayi suyi, ga bayi nan anbude muku night journey zakuyi so get ready, prepare use 10min to do everything" bayika hudu dake dankareren hall din suka bude musu, ahankali ta tashi ta goya jakanta tai hanyar bayin wasuma nabinta abaya, shiga daya daga cikin bayinka tayi tarufe harda key sanan ta tsaya ta kalli kanta really fa batada banbanci da namiji da sauri ta dauke idanunta daga madubi dan bataso tana kallon kanta, fitsari tayi kaman tasani ta soke wani pad a aljihun wando dudda bata wani heavy flow dan gobenema zata gama amman saida ta dauka wanan dataji night journey zasuyi yasa ta chanza ta gyara kanta tareda flushing old one din ta shirya tsaf sanan tafito goyeda jakanta, tana fitowa security yanunata yace "kai kagama?" Gyadamai kai yayi hakan yasa security yanuna mai kofa yace "jemota ajeraku" fita yayi ahankali ya sauka kasa tareda wasu yaran, wani babban luxurious bus tagani kaman irin nasu landstar wanan hadadden bala'i kaman ma sabo, security dake tsaye gaban mota yace "oya zoka shiga" karasawa tayi ahankali

9 / 51