Masifaffiyar Ƙauna Soyayyar da Ta Fi Komai Ƙarfi by M SHAKUR

Author :  M SHAKUR Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 51

15K to 18K   out of 152.6K words

kirjinta yacigaba da faduwa sosai da sauri ta janye idanunta ta saukesu akasa tareda sa hannu takama rigan jikinta tawajajen cinya ta rikegam, ahankali yajanye nashi idanun shima ya kalli Baba yace "Baba kadan bamu wuri zamu dubata" da sauri Baba yace "to" zaro manyan idanunta tayi dasauri kwalla yataru a idanun tabi Baba da kallo harya wuce yabar wajen nurse din dake tareda shine rikeda tray din injections tace "ba cinyeki zamuyi ba yanzun nan muna gamawa zai dawo kinji" gyadamata kai tayi ahankali idanunta na shining sabida kwallan daya cikashi, batare daya kalli nurse dinba yace "ja labule" jan labulen daya zagaye gadonta tayi na both side dana gaban gadon hakan yasa babu wani na cikin ward dazai iya ganinsu, ahankali yakai hannunshi zai kama habarta da sauri taja kanta baya, dan dariya nurse din tayi tace "matsoraciya" wani kallo yama nurse din hakan yasa tai shiru tana hade hannayenta biyu alamun sorry sir, juyoda kanshi yayi yasake zubama Fatima shanyayyun idanunshi yakai hannunshi for the second time ahankali zai kama habarta komar da kanta baya tasakeyi shar hawayen kwayar idonta na dama ya zubo na haggun shima yacika fam yana shirin zubowa, da yatsa ta nuna nurse din tace "k....ki.....ra....min Baba dan Allah" sai alokacin Nurse din tasake magana tace "toki tsaya Dr yadubaki bazai daukemu 2min ba sai Babanki yazo" bayan hannunta takai ta share hawayen sanan ta saukar da hannun tasake kama jikin riganta kanta akasa, ahankali for the third time yakai hannunshi yakama habarta yadago da kanta sukai eye to eye, hawayen kwayar idanun haggunta ne suka zubo sharrr sukabi kumatuntu sukai wuya.



_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da saUran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_
6/23/21, 6:09 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫



_MASIFAFFIYAR KAUNA_




✍️M SHAKUR


_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_






EPISODE 7️⃣
_FREE PAGE_

Toculan hannunshi ya kunna yana kallonta still, ahankali yabude bakinshi kaman wanda baiso yabude softly yace "stop crying" gyadamai fuskarta dake hannunshi tayi yana kallonta tahadiye kukan gabanta na faduwa sosai, haska duka idanunta biyu yayi sanan yasaki habarta yace "meke miki ciwo yanzu"? Kasa jure kallon dayake mata tayi tasake saukar da kanta kasa murya chan kasa tace "kaina" "damene kuma"? Dagokai tayi ta kallai saikuma tasake sauke kanta kasa takasa magana, karban folder hannun nurse din yayi sanan yace "raise her gown cover her legs with the bedsheet" sanan yajuya musu baya yana rubuce rubuce abinshi acikin folder ta. Fashewa tayi da kuka ganin yanda Nurse din ta kwaye mata riga ga namiji awurin, riganta har saman cikinta, saitaja bargon gadon tarufe mata cinyoyinta har zuwa kasan maranta, tundaga cikinta har maranta abude sanan tajuyo tace "angama Dr" ahankali yajuyo yamika mata folder yana kallon cikin nata dayay lakur kaman batacin abinci sai maranta dayadan kumburo, handglove yasaka sanan yakai hannunshi yataba maran yakalli fuskanta motsi yaga tayi tareda runtse udamunta gam alamun tanajin zafi, ahankali yace "zafi"? Murya chan ciki dake rawa sosai danduk a birkice take jin namiji nataba mata ciki tace "eh" dagowa yayi yadauki kwalaben allurai 3 dake tray injection da nurse din takawo ya fasa ya zuko alluran a syringe guda biyu da karami da babba sanan yadaga alluran sama yana saitawa kaman ance tabude idanunta tabude alluran data gani yasa tawani irin tsandara ihu. "Babaaaaa! Baba wlh naji sauki kazo mutafi gida ni kar amin allura" da sauri yajuyo ya kalleta kwaye zanin da aka lullube ta dashi tayi tawani zabura zata sauka hannu daya yasa yariketa dan faduwa zatayi tana tashi yamikama nurse din alluran, kokarin kwace kanta tayi tafashe da kuka sosai tace "wlh wlh naji sauki ku kiramin Baba mutafi Allah kuwan, inkanama Allah karkamin alluran nan dan Allah Doctor, dan Allah dan Allah" ayanda take kuka take rokonshi he could feel her fear tundaga heart dinta and is not a good condition ama patient allura haka, da hannu daya yariketa yakai hannunshi daya kan bakinshi yana kallonta yace "shiiiiiiii inbakiso namiki alluran kiyi shiru bake kadai bane a ward dinan ba am I clear"? Gyadamai kai tayi tana wani irin nishi tana neme nemen alluran taga batagani ba, hakanan saiyaji tana tunamai Rayyana haka take itama batason allura, juyawa yayi ruwan goran daya gani kan kantarsu yadauka yamika mata yace "sha ruwa and calm down" yabude mata goran tareda bata karba tayi takai baki tana kalle kalle kurba tayi kadan tabashi da idanu yama nurse alamu taje ta bayanta, ahankali yace "ya isheki"? Gyadamai kai tayi yace "to kwanta" yanda yake mata maganan sosoft ysata natsu, kwanciya tayi ahankali yaja zani yarufa mata kafa batare daya kalleta ba, hannunshi yamika ya karbi allura daya yace " ki kalli bakina kome nafadi kifadamin test zanmiki okay inaso nagane daga wani lobe ciwon kanki ke zuwa" gyadamai kai tayi, ahankali yake mata wasu alamu da baki yakai alluran yamata daya gabaki daya batasani ba dan haka Allah yayishi baida zafin hannu ko digi, yamata dayanma, murya chan kasa yace "mena fadi"? Ahankali tace "banjiba" murmushi nurse tayi tace "cewa yayi yagama miki alluran" tanuna mata empty syringe din, da sauri takalli syringe din saikuma ta kalleshi abinma mamaki yabata, danharara yasakin mata yace "katuwa mai tsoron allura" ahankali tasaki murmushi dan yanda yace katuwar was a bit funny, da sauri yadauke kai yakama hannunta yamaida mata da karin ruwan sanan yawuce yafita daga wajen aka yaye labulen nata ya shiga duba sauran patient din da Zeena bata dubaba tai shiru tana binshi da kallo tanajin ciwukan datakeji ajikinta na sauka kadan kadan tana mamakin inda Baba yaje saikuma tai tunani yatafi salla, juyowa Dr imam yayi yakalleta kaman ance ta kalli gadon dayake hada ido sukayi da saurinta ta dauke kai gabanta nafaduwa kawai saima ta lumshe ido.



Wuraren 10:30 nadare yagama komi zai tafi, fitowa yayi rikeda jakan laptop dinshi a hannu, hanyar ward dinsu Fatima yayi, awajen kofan ward din ya tsaya yana kallon ciki batare dasun lurada shiba danbai bude kofaba, yanabi bed by bed yana kallo haryakai gadon Fatima, zaune ya ganta Baba yasa filo abayanta yana rike da plate da indomie keciki da soyayyan kwai yana ganin plate din yagane namai shayin gaban hospital dinsu ne, indomie Baba yadeba da cokali zaikai bakinta, makemai kafada tayi tadan turo baki idanunta dake cikeda ciwo sukadan juya ahankali tace "ni Baba nakoshi" da sauri Baba yace "yakuri ci wanan shine na karshe, aini bansan akwai ciwon dazakiyi ki tsani indomie kiba, oya ci ci ci Zara'una" yakai cokalin bakinta yana mata murmushi, washe cute white teeth dinta tayi zata bude baki tai magana Baba yasamata indomie aciki dariya tahauyi tana taunawa shima Baba yahau dariya yace "yaushe aka haifeki yarinya bagashinan kinci ba" batarai tayi tana taunawa saikuma tahau dariya ahankali dan bata da karfi.

Ahankali yasaki dan murmushi yana kallonsu yana tunani who ever says money shine happiness karyane, happiness kauna ce, just look at this father and daughter gwanin ban sha'awa. Kaman ance Baba yajuyo yaga Dr Imam tsaye da hannu Dr Imam yamishi alamu dayazo batare da Fatima ta gansu ba, tashi yayi ya ijiye plate din yace "ina zuwa Zara'u" hanyar kofa Baba yayi hakan yasa ta kalli kofan hada ido sukayi da Dr Imam da sauri ta dauke kai, abakin kofa Baba yasameshi yabashi hannu suka fara tafiya sukai hanyar waje Dr yace "Baba daman i wanted to see you kafin natafi ne, akwai abinda nakeson na tambayeka" da sauri Baba yace "menene likita"? Dan jim yayi kaman wanda baison yin maganan saichan yace "Baba naga tabon duka, fresh shaidan bulala ajikin Zara'u, waye yamata wanan dukan Baba?"


_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_


Shiru Baba yayi yakasa cewa komi yama kasa cigaba da tafiya hakan yasa shima Dr ya tsaya kaman mai nazarin shi saichan ya nisa yace "Baba shirun dakamin ya tabbatar da kasan wanda yamata dukan kenan wanda nina tabbata bakai bane, ayanda naga kakeson yarka nasan bakaine zaka mata wanan dukan ba, Baba yarinyar nan bama wanan dukan bane na farkon dukan da aka mata ba dan jikinta da tabo dayawa, koma waye ke dukanta Baba hakkinka ne amatsayin ka na mahaifinta ka kareta, ka tsareta, mace ce tanada rauni sosai, abu kankani zai iyasa rayuwar ya mace yabaci dan haka dole ka kula, idanma rashin ji take bada duka zaku gyarata ba ai" ahankali Baba yace "bantaba ganin salahar yarinya mai biyayya irin Fatima ba, ko kadan batada rashin ji sai dumbin biyayya da girmama nagaba da ita" Shiru Dr Imam yayi yana kallon Baba ahankali yace "mahaifiyarta ke dukanta"? Girgizamai kai Baba yayi yace "batada mahaifiya" shiru Dr yayi saima yakasa magana, ganin haka yasa Baba yace "ni fulanin Maiduguri ne, mahaifiyarta buzuwar Maiduguri ce amman dukanmu dagani har mahaifiyarta rainon kauyene muba yan burni bane, a kauye mukai aure muka kuma tare cikin dangi da yan uwa da abokan arziki harta haifamin diyata Fatiman nan dakake gani ayau, bazan manta ba, lokacin Fatima nayar shekara biyu da watanni zan fita kiwo da safe tahau kuka zata bini, haka takemin and muddin tabini tosaina siya mata plantain chips da ake saidawa a bakin gari nadawo da ita gida sanan zata barni nafita kiwo, haka na dauketa nace bari naje nasaimata wanan plantains chips dinan abakin express sabida tanason abin sosai, kauyenmu nakan express road ne na zuwa asalin cikin garin Maiduguri, kuma masu saidawa anan bakin titin kake ganinsu (hawkers) na dauketa namata makawuya da nufin innaje nasayo mata mukoma nafita kiwo, muna fita bakin titi nakira mai plantain zan siya mata, na karba daya nasa mata a hannu nasa hannu zan ciro kudi a aljihu nabashi bangama cirowa ba mukaji wani irin kara da girgizan kasa dabansan lokacin dana dauki Fatima data rusa ihuba na kankame ajikina, kafin kasani naga ana ihu ana gudu, ga hayaki wuta natashi daga cikin dajin dana fito...." yadanyi shiru tareda lumshe ido, yanda Baba yay shiru yasa yagane end of the story, ahankali cikin wata murya dazai nuna asalin damuwa yace "Allah ya jikansu" ajiyan zuciya Baba ya sauke yace "Ameen, hadadden bomb yan boko haram sukai amfani dashi suka tada kauyenmu tass wai warning sukama gwamnati, dagani sai Fatima muka rayu a kauyen mu gabaki daya dasu bomb din yatashi dan safiya ne basuriga sun fita ba, nida Fatima mun wahala aduniyar nan, neme neman aiki, kwadago, da leburanci shine yakawoni nan Kano, inda nasami wata baiwar Allah matar nada kirki sosai tabani machine ina express tana tayani rainon Fatima dan tanason Fatima sosai matar Fatima ke kirada Baaba, yaranta duk suna waje, da aikin danake nasamu nahadu da wata budurwa dake saida mana da abinci a tasharmu na yan achaba Rukkaya, naji ina sonta namata bayanin kaina tace taji tanaso na, nadauki Fatima na kaimata tanason Fatima sosai, Fatima na yar shekara biyar mukai aure, Hajiya tabamu yarmu tabarmin machine din cewa zasubar Kano, ranan Fatima tai kuka amman ta hakura, a kasan waje take zama bata cika dawowa Nigeria ba, amman duk intazo Fatima na zuwa wajenta" ahankali yace "step Mum din Fatima tamata dukan nan"? Gyadama Dr kai yayi ahankali saikuma yace "da farko dana aure Ruka tana bala'in son Fatima sosai, dayake bata haihu dawuri saida mukai kusan shekaru biyu Fatima na shekara bakwai ta haifi Habib to daganan kaman asiri son datake ma Fatima yakoma ki, kodan taga son danakema Fatima mai karfine oho, bawai bansan sauran yarana bane a'a kawai dai son Fatima dabanne araina, sabida tun tana yar yarinya take wahala bata taso gidan gatan uwa ba kona kakanni duksun rasu, ina matukar tausayama Fatima, yanda kuma nake sonta haka Fatima take sona, ko ciwon kai yakamani yarinyar nan saikaga kaman zata haukace sabida damuwa, ina iyakan kokarina wajen kareta, ni kaina bansan da dukan ba sai dazu danaje gurin aikinsu d'ana Habib a samin iska a machine yake gayamin ai dukan da Mama ta mata yatada mata da ciwo" Ajiyan zuciya kawai Dr Imam yasauke sosai yaji Baba yabashi tausayi ainun, ahankali yamikama Baba hannu yace "Baba ka koma wurinta saida safe, gobe idan nazo taji sauki zan sallameku saita cigaba dashan magani, ka kulada ita" gyadamai kai Baba yayi Dr yawuce yatafi yabar Baba anan tsaye, Baba yadade tsaye awajen yana wani irin dogon tunani, da idan Ruka tama Fatima duka kowani abu yana tsawatar mata amman yanzu baya iyawa, dazu da Habib yafadi mai abinda yafaru ranshi yabaci ainun yatafi gida but yanazuwa daya kalli fuskarta kasa mata maganan yayi, ko kayan salla yace zai sayama Fatima tace mai bazaka siyamata ba zaiji rashin yabaci amman kuma saiya kasa mata magana, bazai kuma siyan ba, jiyayi kanshi na ciwo hakan yasa yahakura da tunanin yawuce yakoma ward.

_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_




Kwance yaganta kan gado tana kallon kofa kaman dama shitake jira ya shigo tana ganinshi tawani sauke ijiyan zuciya mai karfi, murmushi yamata yakarasa yaja kujera yazauna yana kallonta yace "jirana kike daman? Nadauka kinyi bacci Zara'una" dan karamin bakinra tabude tace "a'a" shiru yayi yana kallonta, kallonshi tayi itama sanan tace "Baba rigan nan dakasaimin nada kyau sosai ina sonshi" ahankali yadan duko da kanshi zuwa saitinn kanta anatse yace "maisa baki gayamin dana dawo da daddare Mamanki ta dakeki ba eh"? Yadanyi maganan ranshi abace, ahankali tace "Baba" cikeda dan bacin rai yace "duk randa tasake dukanki ko aka miki wani abu baki gayamin agidan nanba sai ranki yabaci Zara" ganin yanda ran Baba yabaci yasa taji hawaye sun cikamata ido murya chan kasa tace "kayakuri Baba" ganin yanda tai wani iri yasa yay murmushi yace "yawuce, na gwada kiran lambar Baabar ki bata shiga bata kasar hala" gyadamai kai tayi ahankali, ganin har lokacin damuwa ne akan fuskanta yace "baki taba tambayana ya suffan mahaifiyarki yakeba Zara'una, ingaya miki"? Da sauri ta gyadama Baba kai, murmushi Baba yayi yace "Mamarki doguwar mace ce sosai dan tafini tsawo saisa nai mamaki yanda baki wani dauko tsawonta ba, kuma shine abu na farko danakeso game da ita, inason doguwar mace saikuma yahadu da sunanta danake so shima Surayya, Mahaifiyarki nada yar doguwar fuska kaman taki anan, sanan fuskar nada dan fadi, tanada wasu irin idanu exactly irin idanun nan naki, zakiga acikin mutane idanunta dabanne, idan ta kalleki ne zaki kara ganin tsabaragen kyawun idanun, tanada dogon gashi baki kirin sanan yanada cika, kinga yanda kullum bakison tsifa sanan akama samu kikayin baki iya tajewa balle ki kulle haka gasjinta itama yake, tanada dan goshi dakuma jan lebe inda kika banbanta da ita kenan, ke kin dauko lebena pink itakuma nata jane kaman tasa jan jambaki, mahaifiyarki batada losewan kumatun nan naki ni kika biyo da wanan, saikuma sanyin hali da hakuri dakuma juriya da kunya Fatima dukkin gado mahaifiyarki, saisa nake alfahari dake, dukmai hakuri da juriya yanacin riban rayuwa wata rana komin daren dadewa ki rubuta ki ijiye" ahankali tace "saisa bana fadamaka kome Mama tamin agida, Baba Mama tana matsayin uwace agareni, tabani kannai danake so sanan tarike ni cikinsu Baba bawai bazan iya fadamaka bane, kokuma bazan iya ina mata wasu abubuwan ko rashin kunya ko makamancin haka bane a'a, kariga ka koyardani hakuri dakuma juriya, banson tasanadiyata kana fada da Mama kullum, babu abinda nakeso aduniyan nan samada farin cikin ka, Baba kanada hawan jini banson abinda zai dagama hankali, kome nayi Baba nasan menakeyi wlh niba yarinya bane kawai kadinga mini addu'a kaji, nagama makaranta nafara aiki na kula dakai dasu Habib da dukanku" for the first time yau saiyaji Fatima tai magana kaman wata yar shekara talatin, hannunshi yakai kan kumatunta yana murmushi yace "Allah yacika miki burin ki, Allah yamiki albarka Zara'una, Allah yabaki miji nagari" murmushi tayi taja zani tarufe fuskarta tace "saida safe Baba kaina yafara ciwo mani" murmushi kawai yayi baisake cemata komiba idan sabone yasaba da kunyanta duk randa zai mat hiran aure ko magana suke karshen maganan yazo kenan dan guduwa zatayi.


_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da saUran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_
6/23/21, 6:09 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_💫



_MASIFAFFIYAR KAUNA_


_FOR DIRECT MAGANA DA M SHAKUR A TUNTUBENI TAWANAN NUMBER NAN 07012181461_


✍️M SHAKUR


_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna

6 / 51