Author : M SHAKUR Category : African Stories & Novels
bama a using dinshi mezasuyi dashi, budemusu dakinta sukayi tana kwance tajuyama kofan baya tagalabaita iya galabaita, dudda taji an shigo ko kadan bata juyoba, tsayawa a kofa Sarki da Otun sukayi shikuma Dr Imam yashiga ciki da sauri yay kanta yace "Fatima Zara" tareda dagota zaune, ahankali takallai da idanunta dasuka kode sosai sukai fayau irin idanun wanda ya wahalu iya wahakuwan nan, fuskanta dukya kumbura ga ciwo ga alamun cizon saura da cizon abubuwa da damama ajikinta abunku da fara, ahankali yashafa fuskanta yace "hey is me Dr Imam, am here to save you" shiru kawai tayi tana kallonshi, wani irin ihu Otun yamai yace "Malam kana batamana lokaci do abinda zakayi before mu chanza mind dinmu mu kasheta" sakinta yayi yadauki kwalban alluran da syringe yabude da sauri hannunshi na rawa ya zuko alluran daidai mil din daya kamata yamata pushing, sanan ya kalleta yace "you will be fine, I will take care of you Angel" yana maganan ta saman riga ya chaka mata alluran adaidai saitin heart dinshi duk tana kallonshi kaman bata hayyacinta sanan ya juye ruwan alluran tareda cirowa yatashi ya kalli Otun yace "done in the next 5sec jikinta zai fara slowing down, within 10min from now zata mutu heart dinta zai daina aiki" nunamai wani dakin yayi Otun yace "kaika boye anan sabida karya ganka yay suspecting anything" sanan ya kwalama guards kira yace "ataho da Tobi nan" itadai tana zaune tana jinsu sama sama dan kunnenta taji yamata nauyi sosai kaman an daura mata block din gini akai.
Sama sama take gani idanunta na mugun juyawa jikinta namata kaman ba nataba, taga an shigo da Tobi dayafice hayyacinshi tsabagen wahala, Babanshi ne yamai wani kallo ya dake yace "am doing this sabida kai d'ana ne, yanzun nan aka sanardani she has not been eating all this while, duk abinda aka kawo mata haka za'a zo afitar dashi, kaman she's dying i asked akawoka dan kagani da idanunka ku sakeshi" ya umarci guards din dawani irin gudu yashiga dakin, tareta yayi yasata ajikinshi yana shafa fuskanta tana kallonshi sama sama lips dinta sun bushe sosai kaman banata ba yace "Zara, Zara, noo no nooo, don't do this to me, niban mutuba sai ke, no, no, food, food, water, water, you are hungry, lemme feed you kisami energy nothing will happen to you I promise, somebody give us water and food" yay maganan da karfi yana jijjigata sosai, ganin yanajin yanda jikinta ke saki ajikinshi yasa gabanshi yashiga faduwa kaman zai fashe, ahankali tadaga hannunta na dama da kyar tana kallonshi da idanunta dake rufewa tanason ta taba fuskanshi but takasa, hannunta yakama yarike ga saikuma yafashe da kuka sosai yakai hannun kan fuskanshi yace "Zaara is me, your Ya Tobi, please don't die my life will be shattered wlh, wlh I love you morethan life itself, Zaraaaa, you are the first woman that makes my heart beat, that makes my heart skip, that makes my heart to skyrocket, you are the first woman I think of, Zaraaa don't do this to me this wasn't our deal pls, is not fair kitafi ki barni bayan nakamu da sonki, I said is not fairrrr Zara" sosai hawayenshi ke zuba a hannunta daya rike akan fuskanshi itama hawaye yagani yafito daga gefunan idanunta sunbi ahankali sun gangara sharr zuwa kunnenta kafin dip zuciyanta yadena aiki gabaki daya tasaki ajikinshi hanunta dake kan fuskanshi yafadi, chak shima ya tsayar da kukan dayake kaman wanda yatabu, yakai hannunshi kan fuskanta ya bubbuga yace "Zara, Zara, Jewel" saikuma chan yay wani irin ihu kaman zai fasa dungeon din gabaki daya. "Zarah!!!!!, Zara......." yama kasa kiranta sabida yanda kirjinshi yabuga kawai yasaketa yay gefe asume shima warwas, da sauri Otun yace "come out Dr" fitowa Dr Imam yayi dayaji komi dayafaru da kukan Tobi, Otun yace "dauketa kubar kasanmu har abada, direba is ready zai kaiku har airport we can do that for you just do that for you danmu nuna maka masarautannan munada kirki" shiga dakin yayi yana kallon fuskan Tobi dako amafarki bazai mantaba yaron daya taimakeshi, tsawa Otun yadakamai yace "I said carry her and leave this house for good" da sauri ya ciccibeta yadauketa suka fice har lokacin yana waiwayan Tobi akwance a sume, motan da aka ijiye musu yasata shima ya shiga sai airport, yana zuwa all he showed was Id card nashi na Dr, yabiya kudin ticket aka bashi wheelchair yasa Fatima dat was still uncountious, karfe 6 dot jirginsu yatashi sun isa Kano wajajen gab da isha'i yana isa yatare taxi ya shigar da ita yabama wanda yabiyosu mai aiki a airport din wheelchair yatafi dashi.
Har gaban gidansu Taxi yay parking lokacin duka duka baifi 10min tafarka ba dan alluran 6hrs ne, yabiya taxi yadauketa ya shiga cikin gidansu da ita, kofar flat dinsu yabude ya shiga da ita ciki da sauri kannenshi duka na falo suna kallo, dawani irin sauri yace "Ray yana get me a stethoscope daga dakina run" dagudu tafita, yace "Rahma get me ice" sanan ya kwantar da ita akasa, ya wurgan dakomi na hannunshi ganin 10min yawuce bata farka ba inbai tadataba zata iya rasa rayuwanta gabaki daya, sanan ya nannade hannun riganshi sama ya kalli Asma yake tsaye yace "fold this hand for me" linke hannun rigan tamai, sanan yadaura hannunshi akan kirjinta ya danne sau uku babu motsi bata farka ba, dasauri yafara no no no Fatima wake up, wake up, yanda yake ihu yasa Ammi dake sama tana hira da Maman mijinta data iso yau daga UK tadan zabura, tace "Granny kaman muryan Imamu nakeji" Matan da aka kirada granny wacce ta manyanta sosai amman kudi yasa bazaka taba ganewa ba, tahadu sosai tana sanye da glasses a idanunta hannunta rikeda supplement na diabetes tace "Imamu kuwa" "Fatima wake up!!" Wanan karan atare sukaji muryanshi hakan yasa itama granny tatashi da sauri itama sukai stairs suka sauka kasa daidai Imam yacire hannunshi dagakan kirjinta yakoma jikin kujera yazauna tareda dafe kanshi ahankali yana innalillahi wa inna ilaihi raji'un, chak Granny ta tsaya a stairs tana kallon Fatima that was lying there dead gabanta nafaduwa sosai saikuma ahankali takai hannunta kan glasses din idanunta tacire ta kalleta sanan tasake maida glasses din ta kalleta tace "Fadimatul Zara'u!!".
_Erotic Ideas group na matan aure zalla ne, group ne damuke program guda HUDU aduk sati, ranakun sune ALHAMIS, JUMMA'A ASABAR da LAHADI._
_Duk ranan Alhamis munayin program mai suna MARRIAGE LIFESTYLE, wato ZAMANTAKEWAN AURE, inda nakema mata lectures kan yanda ake zama da miji dakuma dabarun zama da miji, ranan jumma'a kuma muna program din damuke kirada TALK & HEAL wato yi magana ka warke, inda matan aure zasu gayamana matsalolin dasuke fuskanta agidajen mazajen su, zasu iya turamin ta pc idan basuson asansu nisainai forwarding group mu taimaka musu da shawarwari dakuma dabarun dazasubi su magance wanan matsalolin, sai ranan asabar shine ranan LECTURES, inda zan dauki darasi dake dauke da dombin ilimi abu wanda ya dace mata su iya dangane da aurensu, mu koya musu ayi magana akai sosai, sai ranan Lahadi zamuyi lectures akan ilimin daya danganci yanda zaki gamsar da mijinki sanan ki gamsar da kanki, kisaka mijinki ihu agado yana kururuwa yana sambatu, mukoyar dake yanda zakiyi spicing up sexlife dinki, and yanda zaki dinga rayuwa da mijinki kullum kaman sababbin aure._
_Idan kinason shiga wanan group din zaki turo 2000 to 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din, wata daya ne group din, idan kinason ki cigaba da zama duk wata dubu dayane 1500 ne subscription, sababbin zuwa kUma new member zakiyi register is 2k ne, don karin bayani zaki iya tuntubata a number ta 07012181461_
M Shakur ❤️
7/6/21, 11:57 AM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫
_MASIFAFFIYAR KAUNA_
✍🏾M SHAKUR
EPISODE 5️⃣3️⃣ & 5️⃣4️⃣
Granny takira sunan da karfi dayasa dukansu suka juyo suka kalleta kafin ahankali tabi ta gefen Ammi tasauko daga stairs din tazo inda Fatima take kwance akasa ta tsugunna tana kallonta yanda yarinyar tayi sanan tajuyoda kanta ta kalli Dr tace "Imamu a ina kasan yarinyar nan? A ina kasamo ta" motsin dataji Fatima tayi yasada sauri ta kalleta, Rayyana ce tace "Yaya tayi motsi" da sauri yazo wajen yasake maida stethoscope dinshi kunne yadura akan kirjinta jin heart dinta na beating yasa ya lumshe ido tareda furta. "Alhamdulillahi Rabbil Alameen, she's back" yafadi ahankali duk suna kallon fuskanta yanda take kokarin bude idanuwanta, bude idanun tayi ahankali sanan tadaurasu akan dukansu yan dakin har lokacin komina jikinta yamata nauyi, da sauri Granny tashafa kanta tace "Zara kin ganeni? Baabar kice" shiru tayi tana kallon Baban wani irin, kallon Ammi shi yayi yace "Ammi please amata wanka da ruwan zafi ta chanza kayan nan awanke kan nan nata, sai kubata tea tasha zanje hospital na kwaso magani nazo namat treatment i will tell you everything" gyadamai kai kawai Ammi tayi tana kallon Fatima itama, dasauri Granny ganin yasake zamane yana kallonta tace "wuce katafi mana Imamu" tashi yayi ya kalli Ammi yace "Ammi car key" gaban TV stand tanunamai, key motarta yagani hakan yasa yadauka yawuce yafita daga gidan.
Shadaya saura ya shigo gidan da katon ledan magani, Babanshi yagani da Granny dakuma Ammin shi afalo hakan yasa yadan tsaya yana kallon mahaifin nashi. "Are you standing there kozakaje kasaka mata abinda yakamata" Baban yay magana hakan yasa yawuce sama, adakin Granny yaganta kan gado an mata wanka ansaka mata doguwan rigan atampa light mara nauyi na Rayyana tana kwance kan gado idanunta biyu sai kallo su Rahma take har lokacin batace musu uppan ba, karasowa yayi yana kallonsu yace "tasha tea"? Rahma ce tace "kadan tasha bada yawaba amman" gyadamusu kai yayi ya shiga saka mata ruwa yay allurai a ruwan sanan yamata wani allura a vein ya tsaya chak yazuba hannu a aljihu yana kallonta kaman yanda yaga tana kallonshi da idanuwanta dake rufewa sanan idanun suka rufe tass bacci mai karfi ya kwasheshi yawuce ya sauka kasa kannenshi suka biyoshi, waje yasamu kusada Granny shi yazauna yace "when did you come back from UK Granny"? Murmushi tayi tashafa kanshi tace "nagaji da zama dasu wlh, ni nafison kasata Nigeria, abeg ciwo bata kisa sai in lokaci yayi nadai kwaso magungunana zanyi kwana biyu jibi zantafi Abuja gidan kanin Babanka achan zan zauna sabida consultant dina yahadani dawani abokinshi shima baturene dazai dinga dubani a anan Abujan" gyadamata kai yayi, sanan ahankali tace "muna jinka Imamu a ina kasamu diyata"? Dasauri yace "wai Granny itace Fatimar da idan nazo UK kike cemin kinyi kewa har kikasa naje wani gida anan kano dana dawo nadubo mikisu sabida you lost her father's contact akacemin sun tashi" gyadamaikai tayi tace "itace Fatima Zara diya ga Muhammad, a ina kasanta"? Nan yafara koromusu bayani right from ranan da aka kawota hospital dinsu tana rashin lpy yay admitting nasu har zuwa ranako irintayau. Sosai suka girgiza da Al'amarin, Abba yace "natausayama yarinyarnan wlh, Allah ne yaturaka exam dinan a lagos kawai sabida ka cetota amman cousil exam yawanci ma anfiyinshi a Abuja wanan karanne naga anyi a Lagos, am proud of you Son, shikuma Babanta! Hmm akwai Allah kawai" cikin fushi sosai Granny tace "wani irin akwai Allah Abubakar? First thing tomorrow in the morning tunda Allah yasa kasan gidan Imam zaka tukani nida ubanka ka kaimu gidan inaso naga Muhammad ido da ido ya maimaitamin abinda yafadin maka na gasgatar danni nasan yanda yaeson yarinyar nan tun tana yar karama, inyaso Maryam kesaiki zauna da ita anan gida" gyadamusu kai Ammi tayi tace "In sha Allah" nan suka cigaba da hirarrakin duniya daga baya Imam yatashi yahsiga yadubata har lokacin tana bacci sanan yawuce yasauko yamasu Dad saida safe yawuce yakoma flat dinshi.
WASHEGARI!!!
Karfe takwas Granny tashiga dannamai kira awaya, kiran wayan yasa yabude ido da kyar danyagaji yana dawowa daga sallan asubahi yakoma bacci, wayan yajawo yakara a kunnenshi ahankali yace "Granny" cikeda Masifa dan tanada fama sanan bata tolerating nonsense tace "kasandai kai nida father ka muke jirako" ijiye wayan yayi da sauri yasauka kasa sake dauro wani sabon wanka yayi yafito ya shirya cikin wata ash shadda bugagga yadauki hula yakafa aka yasanya takalmi yafito yana rikeda car key dinshi datun asubahi yacema gateman dinsu ya wankemai.
Flat dinsu ya shiga yaga daga Ammi sai Granny su awajen da alamun sun gaka break harsun watse, gaidasu yayi, Ammi tace "kajeka dubata ta tashi amman bata kula kowaba tea kadai tasha" gyadama Ammi kai yayi yazo zai mota ya shafa fuskar kakan tashi yace "Smile now Granny" hararanshi tayi takalli Ammi dake musu murmushi tace "danki yagama rainani wlh" cikeda wasa Ammi tace "ba'a shiga tsakaninku, keda jikokinki mu namu ido" hararan Ammi tayi tace "ai dama bamuce ku sakaba" dariya Ammi tayi tace "mezakici da dara" ahankali tace "fruits nakesha darana, da daddare kuma tuwon accha zakimin da miyan kubewa danya" gyadamata kai Ammi tayi.
Ahankali tabude dakin datake ciki yashiga babu kowa ita kadaine dansun tafi makaranta su Rayyana, idanunta biyu tana kallon hannunta kawai tai lamo kaman mara lafiya, karasawa bakin gadon yayi yazauna ahankali, saikuma yadauki stethoscope dinshi dake gefen gadon ya sanya sanan yadubata, tareda cire drip din yamakala mata wani har lokacin hannunta take kallo ko motsi batayi da ido yay allurai cikin ruwan sanan ya tsaya jim yana kallonta saikuma ahankali ya tsugunna ta yanda fuskanshi zai dinga ganin kwayan idanunta, murya chan kasa yace "Hey Fatima" saikuma yay shiru ganin batabar kallon hannunta datake kalloba hakan yasa yadaura hannunshi ahankali kan inda take kallo ahannunta, ahankali yace "nasan you can hear me perfectly fine dan yanzu fine, and u can see me, I want you to know that all of us here will support you, you have a full family anan yan uwanki yarenki dazasu taimaka miki, kin dawo daya daga cikinmu, Baabarki is here as well am sure kinganta, just take your time process all this emotions ki manta da duk wani abu dayasameki abaya ki daukeshi amatsayin kaddara sanan kigodema Allah and move on kema kifara makaranta kaman su Rayyana and Rahma, you are free now Fatima u can do anything you want, you have your life, so own it kitashi and be free you have three sisters already anan and let go off the past, now dayakamata kina farinciki karki bari emotions yarikeki na past dinki okay" yay maganan yana kallonta har lokacin tana nan yanda take batare datai motsi ba, gently yajanye hannunshi dagakan hannun nata yajuya yafita ahankali tareda rufomata kofa.
Afalo yasami Granny da Abban shi Ammi na kitchen dayar aikinsu yace "mutafi" gaba yayi suka biyoshi abaya suka shiga mota yajasu har zuwa unguwan su Baba, har kofar gidansu sukai parking dukansu su ukun suka iso, daidai lokacin wani yaro yafita daga gidan da sauri Granny ta tareshi tace "kai jekace ana sallama da Malam Muhammad" da sauri yaron yace "Baban su Habib"? Gyadamai kai Dr Imam yayi yaron yajuya da gudu yay cikin gidan, ba'a wani dauki lokaci ba saiga Baba yafito yaci gayu abinshi yay kyau kaman bashiba yana sanye da jallabiya fara mai kyau yar kanti, ganin Granny yasa yabude idanu cikeda mamaki yakaraso wajen yace "Hajiya, marhaban dasu lale" murmushi sosai Granny tamai tace "Malam Muhammad daman rai kan ga rai" dasauri yace "aikona kiraki baya shiga" anatse tace "wani ciwo nayi da aka hanani amfani da waya kwata kwata" "assha Allah sawake" yay maganan yana bama Abba hannu yana kallon Dr Imam irin kallon bana gayamaka karka kara zuwa gidana ba, ganin kallon yasa tace "jikana kenan Imamu, ga mahaifinshi nan" tanuna Babanshi tace "dashi da kanninshi na Abuja saikuma yata dake UK ne Allah kadai yabani aduniya, wanan ma a Abuja suke ai katuna lokacin yanda nake yawan zuwa Abuja basu wani dade da dawowa kano ba, asibiti babanshi yabude anan, idan kuma ina Abuja ina gidan kanninshi ne kasan anhanani zama ni kadai sabida ciwo" gyadamata kai Baba yayi saikuma ya murmusa yace "bismillanku ai bana barku anan tsaye ba" yay cikin gidan suna biyedashi har zuwa falonsu da babu kowa gashinan agyare kaman yasani yanzun nan yagama gyarawa dan ya tsani datti yara kuma duk sun tafi aiki banda Abida dake bacci da mamanta adaki, Granny ne tabishi tashiga falon Abba da Imam suka tsaya kasancewansu maza dole sai anbasu izinin shiga ai zasu shiga, da sauri Baba yadaga labulen yace "ku shigo dan Allah" sallama Abba yayi yashiga tareda Imam suka sami waje suka zazzauna shikuma Baba yashiga ciki da sauri yadan daddaki Mama dake bacci tana sanye da doguwan riga yace "tashi Ruka munyi manyan baki" da sauri tanude idanunta ta kalleshi, murmushi yamata yadauki hijabi yabata yace "Hajiya ce data taba bani achaba nai aiki aikin ganeta lokacin damuna amarya dani dake da Fateema muna zuwa wajenta" daure fuska tamau tayi tace "Baabar Fatima" da sauri yace "eh" kwafa tayi tanunashi da yatsa tace "saura inga anmaka maganab Fatima kafadi abinda bai kamata ba" daure fuska yayi yace "nace kidenamin maganan yarinyae nan" murmushi tayi tareda sauke ijiyan zuciya ranta fess ta karbi hijabi tasaka sanan ta sauka dagakan gadon, suka fito falon Mama tana kwasan pure water a hannu cikeda kunya kaman na gaske Mama tace "wanake gani haka Baabar Faty ido kanga rai dama" murmushi Mama tamata tace "Rukkaya" anatse tace "naam ina wuni ina gajiya" sanan ta gaida su Abba tace ga ruwa kusha duk sukace sun koshi sun gode akai shiru, sanan anatse Granny tace "Malam Muhammadu wata maganace muhummiya takawoni wajenka" anatse ya gyara zama yace "too too ina jinki Hajiya" gyara zama glass din kan idanunta tayi dake karamata karfin gani sanan ta kalli Baba takoromai bayani tundaga farko har karshe wanda Imam yafadi mata sanan tanisa tace "dudda abinda su mutanen lagos suka bama Imamu labari kace bakason yarinyar, da still yanda kafadima Imamu shima dayazo nemanta saisa nima natako takanas takano dannazo naji da kunnena dan yanzu ahak yarka na gidanmu