Author : M SHAKUR Category : African Stories & Novels
into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._
[25/06, 09:02] My Airtel2: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫
_MASIFAFFIYAR KAUNA_
✍🏾M SHAKUR
EPISODE 3️⃣2️⃣
Gyadamai kai kawai yayi batare dayace komi ba, yana tuki amman yana lura dashi zafi yakeji amman baison yanuna hakan yasa idanunshi nakan hanya yace "dazaran kaje gida kasha maganin nan within an hour zaka nemi zafin karasa, nan da 2 zuwa 3days zai warke, next time don't get into fight again I know it was fun" dan lumshe ido yayi yabude saikuma ahankali yace "I've heard" wayanshi ne yashiga ringing dake in between sit din gaban atare suka kalli wayan dan shima yazaci tashice dan ringing tone na iPhone ne ganin Dad dinshi ke kiranshi yasa yadanja tsaki yadaue kanshi daga kallon wayan, harta katse another kiran yashigo Mum, itama ta katse bai daukaba, saikuma Dad yasake kiranshi ganin baida niyyan dauka yasa ahankali yace "please pick up sunga dare yayi basu ganka bane" mika hannu yayi yadauki wayan daidai ta katse saiga wani kirin kuma yana shigowa hakan yasa yakai wayan kunne yace "Dad what" jim yayi yana sauraron Babannashi saikuma adan kubure yace "am on my way back home already" sanan ya katse wayan ya jefar yana maida kanshi jikin kujera yacigaba da nunamai inda zai bi har sukazo ta wajejen anguwansu amman ba'a kai layinsu ba sanan yace "dan gangara gefe kai parking" ahankali yace "but ai nan kan hanya ne" "don't worry am close to gida I can manage" gyadamai kai yayi Tobi yace "lemme call Uber yazo yadaukeka dan ana ganinka ansan you don't belong to the street of Lagos this ghetto Boys will rob u" yana maganan yana shiga app din yakira uber within 5min duk suna zaune acikin motan ya lumshe ido uber direba ya kira bude kofa yayi zai fita da sauri Dr Imam yace "no" dan murmushi yayi yace "i can manage" fitowa yayi yanama uber direba waving hannu hakan yasa yakaraso shima fitowa Dr Imam yayi, uber direban nazuwa Tobi yaciro kudi about 10k yabama uber direban yace "take my man to his hotel, idan y sauka just call me i will end the ride" sanan yadago yajuyo yana cizan baki, hannu Imam yabashi yace "I really appreciate this" gyadamai kai Tobi yayi, ahankali Dr Imam yace "please take care" I will yace sanan yajuya yashiga mota shima Dr Imam yashiga motanshi yanabin Tobi da kallo he's one the the nicest person yahadu dashi a lagos, jan motan Tobi yayi yamike sukuma suka juya suka fita daga layin.
Gidansu yashiga yana addu'a Allah karya hadu da iyayenshi sukaga riganshi da jini ai saisun sunyi panicking halama akara hanashi fita, saida yay parking yaga basa tsakar gida sanan yabude motan yafito, da sauri guards sukazo kafinma su iso yace "nobody should come here dissmiss" bacemai sukayi, sanan yabude boot ya kwaso abinda yasayo ma Boy, da ledojin yay amfani ya kare inda jinin yabata ariganshi yawuce flat dinshi yana bude kofa ya shiga yaga babanshi azaune akan kujera faduwa gabanshi yayi yawani batarai tareda saka leda yasake rufe wajen da kyau, Dad yajuyo yana binshi da kallo yace "iyye I can see anyi aski an chanza style, your face looks very fresh kaje spa ne" dauke kai yayi yace "uhn" sanan Dad yay murmushi yace "dakace kanaso damun kirasu home service suzo sumaka" shiru yayi yana tsaye inda yake baice kalaba Dad dake kallonshi yace "you look very dirty Tobi kaman wanda yaje yay dambe jibi kayanka" yanuna kayanshi da duk yabaci da kasa hakan yasa yace "are you investigating me newai Dad"? Da sauri Baban yace "no Son, just saying it ne sabida naga kai datti" tabe baki yayi yace "i played ball ne" gyadamai kai Baban yayi yace "i see meka sawo a ledojin nan" yanuna ledojin hanunshi, sake rungume ledojin yayi yace "is not mine, I actually got some clothes for Boy, sai gobe zan bashi" sosai Babanshi yay murmushi yace "Tobi u really like that boy, dats the first gift dana taba baka naga kanaso sosai" wucewa yayi yay stairs da sauri yace "i am sleepy when u are done ka kashe tv" binshi da kallo yayi yace "but Son i actually come muyi kallon match tare" "not interested Dad, gud night" night babanshi yace ahankali yana kallonshi, shiga dakinshi yayi yamaida kofan yarufe ya danna key da sauri yana cije lips yanabin dakin da kallo ganin Boy bai gyaraba kaman ma baima zobane kwata kwata ba yau.
Wanka yashiga yayi da hot water sanan yafito ya chanza wasu kayan zuwa pj, yarike magungunan shi yay dinning abincin daya gani wajen yabude yadan tsakuri amalan kadan dan bayawani so kuma yasan da gangan Mum takawomai tanason yay kibane yaci sanan yasha magungunan yatsiyaya juice a glass cup yadawo falo ya zauna yana kallon tashan news din dake aiki wanda ta tabbatar Dad ne yasaka danshi he hardly watch news, yana sipping din juice din yana chanza channel hakanan yake mamakin maiya hana boy zuwa yau aiki, but deep down yasan it will be something daya hanashi zuwa, dan tabe baki yayi sanan yay murmushi tuna irin fadan dayayi dazu, ba yana gayama su Dad yanada karfi basa yardaba just look at the gang he took down shi kadai dan dat Dr babu wani abun arziki daya tabuka. Sai wajajen one sanan ya kashe komi yawuce sama yafada gado sai bacci.
**
Awajen Boy wato Fatima tun jiya ta tashi dawani azababben ciwon mara, ciwon baya cikin kafa da ciwon kirji hakan yasa ta kulle kanta tacire komi ta ijiye dan yanda nononta ke ciwo da kirjinta yasa taji kaman ma zazzabi zazzabi take, nonuwan sunyi jajajir, sunyi wasu kala kaman kumburi kumburi sunyi mata wani irin strange tauri kaman wani maruru maruru tsabagen yanda take dauresu take nanesu, sunmata nauyi sosai idan zata mike tsaye wani zubin saita daura hannu tarikesu sabida ciwon dasuke mata kaman zasu tsage, abinda tsoro yasoma bata karya zaman mata wani babban ciwo danhar zugi suke mata kaman maruru kokuma wani dan kankare, toba doleba sumata ciwo duk uban cikan nononta danko kadan batada kananun nonuwa, boobs dinta are rounded full kaman kwallo, sumcious nd perky, white boobs gareta, ba irin wanan wasu girman haukan nanba, manya ne but daidai masu kan tasa, yanda take matsesu da silki yasa sukai tauri suke mata zugi sukai ja. Allah ne yarufa mata asiri head Guard baizo tashintaba jiya kaman yana wani aiki, dasafe taji muryanshi amman baizo dakinba sabida yaga kofan arufe hakan yasa yay tunani tana wajen aikinta ne, ko fitsari zata fito taje saitaji babu kowa acikin flat din, ko abinci bataci ba ranan daman bata iyacin abinci in tana mp, daga biscuit dasu sweet datakedashi da ruwa kawai takesha, jinin dan ficiline ma yazo as per the first day, haka tawuni tana ciwo har dare, gabaki daya bata runtsa ba daren jiya, jikinta yay mugun zafi, kanta ciwo maranta ciwo boobs dinta ciwo, babu irin kiran sunan Allah dabatayiba akan kar asirinta yatonu yau tana kwance akasa tana burgima dan tama kasa kwanciya agado taji anyi knocking. "Boy wake up and shower is 4 katafi wajen aiki" azabure ta tashi dama zani kawai ta daura, silkin taja jikinta na bari na zazzabi taja zanin kasa ta daura silkin tana runtse idanunta sanan tasa riga da wando da sauri daidai yana jijjiga kofan tabude da sauri tazube kasa, wani mugun kallo yake mata yace "wai how many times zan maka warning akan kadena kulle kofa" bakinshi na rawa tanadan haki tace "sorry head Guard" mugun kallo yasake jifanshi dashi yace "wuce kaje kai wanka fast fast" wucewa tayi bayinsu tai wanka tai brush sanan tasake maida komi tadaura tasaka kaya tafito tana tafiya ahankali da kyar maida kofan tayi tarufe tashiga shiryawa agurguje tasaka pad dinta da duka duka saura uku, daman shi bata wani damuba dan inya kare zata fara amfani da rigunanta tana yagawa dan bazata iya yaga zanin nanba shine hijabin sallanta, adaddafe tasaka takalmi tafito tana nema ta duke dan boobs din zuginsu janta suke sosai idan ta mike tsaye straight, ga maranta kaman ana murza kuli kuli aciki, dayake gari baiyi haskeba ko kadan Head Guard bai gane halin dayake cikiba balle yamaga idanunshi dasuka kumbura sukai suntum.
Ahankali yabude kofar flat dinshi ya shiga bayan head Guard yakawo shi, maida kofan tayi tarufe sanan taduke awajen ta tsugunna tana kokarin hadiye hawayen datakeji tanaso ta daure, kirjinta tasake tabawa dan bamatasan wanne yafi mata ciwoba cikin su biyun, takai sama da minti goma tsugunne awajen sanan ta tashi da kyar tana dafa kofa takai dayan hannunta ta taushe bakinta da sauri tana kokarin hana kanta kuka xafin datakeji yabaci, sai yanzu da aikinta yay nisa tana wata na hudu dan this is her fourth MP shine jikinta ke nema yagaza dan wanan ba ita bane, kirjinta na neman yagaja, ta mike tsaye kaman zata mutu takeji, kasa tsayuwan tayi straight ta duka kawai kaman tai ruku'u tana share hawayen daya zubo mata sanan tai stairs, stairs dinma kaman kara making ciwon worst yakeyi, aduken nan takai tabude kofar dakinshi ahankali ta shiga ta maida kofan tarufe tawuce direct ta shiga bayin shi dayay kacha kacha, kayanshi akasa ako'ina, tsugunnawa tasakeyi tana cijan lips hawaye suka shigabin kuncinta tana wani irin fuzarda iska inda xaka ganta zaka kusan yimata kuka ita karan kanta mugun tausayin kanta takeji but taga rayuwa.
Rarrafe tafara tajawo basket na kwashe kayan dattinshi ta shiga tattarewa tana sakasu a basket din tana kuka sosai mara sauti ko kadan, saida tagama tattare kayan tass sanan takama bathtub dinshi zata mike tsaye dan ihu tayi mai kara takoma ta tsugunna da gudu sabida yanda kirjinta yayi, lallabawa tayi tai kaye kayen bayin a tsugunne batare data iya ta wanke bayin ba, takara jingina da bango tana nishi sama sama, saikuma ta daura duka hannayenta biyu akan fuskanta kaman mai addu'a ta shiga kuka sosai, ita karan kanta she don't know abinda zatama kanta kirjinta ya daure ya rike, maranta ya rike, asalin kirjinta na mata zafi yana mata ciwo kaman wacce keda matsalan ciwon kirji na ulcer, ganin koma menene gwara tabar aikin taje dakinta ta kulle kanta tacire wanan silkin dake neman yasa numfashinta yadauke taita birgima akasa tana jinyan kanta da dandan sarki yagano wani abu game da ita anan, tun yanzu gwara tafice kafin ya farka daga bacci, tunanin haka yasa da rarrafe tazo ta murza hannun kofan sanan ta rarrafo tafito batare data kallo cikin dakinba ta daga hannu zata kama handle din kofan ta maida kofan tarufe kenan taji muryan prince yace "Boyy" awani zabure tajuyo ta kalleshi suka hada ido yana zaune bakin gado, ihun datayi abayi yatadashi yatashi ya zauna sai gashi kuma tafito, ganin yanda yake kallonta ganin rarrafe take yasa dawani irin sauri ta yunkura zata mike kirjinta yawani amsa yakafe kaman takasa wani igiya na kirjinta boobs dinta suka shiga mata wasu irin unbearable zugi, numfashinta yawani rike kaman mai asma takasa numfashi da kirji tafara wani irin neman numfashi tana wani irin nishi tana kokarin faduwa kasa kaman mai asma, da sauri Tobi yatashi yace "Boy!!!" Kafin yakarasa ta idasa zubewa flat akasa agaban bayin tana wani irin bude idanuwanta kaman wacce ke shirin mutuwa tana yi yi yi yi yi..... tana wuntsila hannu trying her best to breathe but takasa, dawani irin sauri yadagota yariketa yasa kanta kan cinyanshi yana kallon idanunta dasuka bude sosai tana kallon sama yace "Boy dama u are asmathic ne, do you have inhaler? Subhannallah whats wrong with you Boy" yay maganan yana gigixashi, da kyar idanunta suna neman kullewa tai grabbing hanannunshi tana kallon sama har lokacin takai hannunshi_ tai placing akan chest dinta tawajejen boobs dinta trying to tell him ya kwance mata abin nan karta mutu, karta mutu.
7/2/21, 9:10 AM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫
_MASIFAFFIYAR KAUNA_
✍🏾M SHAKUR
EPISODE 3️⃣3️⃣
Kallon fuskarta yayi sanan ya kalli inda ta daura hannunshi sabida kaman yaji dan tudu da alamun wata kalan fata dabata jikin mutum ba akirjin nata, sanan yasake kallon fuskanta yanda lips dinta ke kokarin motsi amman takasa gayamai metakeson cewa, takasa furta maganan datakeso tayi tana wani irin nishi idanunta na kullewa suna neman kafewa tana bubbuga hannunshi dake inda ta daura tana kokarin nishi takasa, dawani irin sauri ya daura hannunnashi kan kirjinta da kyau trying to understand abinda boy din is trying to tell him ya shashafa kirjinta tundaga ciki har wajen boobs din but baiji komiba sai fata wacce take kaman fatan takalmi ba fatan jikin mutum ba, saikawai yadage black rigan dake jikinta sama gaba daya zuwa wuyanya yaga wani brown silkin doki da yardin mai bala'in kauri da nauyi daure ajikinta tai wrapping kanta dashi, kirjinta ya kullu ya tamku gam gam da daurin dayaga kaman shiya hanata nishi danta daure kanta dayawa ahakama yana ganin yanda chest dinta ya matse, dawani irin sauri ya shiga kwance kullin kafin tashi daya dawani irin karfinshi na namiji ya fizge silkin futttttt yawani cillar sama daidai manya manyan boobs dinta dasukai jajir abunku da fara suka tamuke tsabagen kullesun da akayi suka bayyana before his eyes, dawani irin sauri yasaketa gabaki daya akasa yakoma baya kadan tsabagen shock!!!.
Wani irin nishi tayi tareda juyawa gefe ta kwanta ta side dinta har lokacin tana wani kalan nishi that is very strange dan numfashinta bai dawo daidaiba saikuma amai, waaaaaa ta kwaro aman duka biscuits da chocolate din dake cikinta tun jiya anan kasan carpet din tana wani irin nishi kaman ranta zai fita. Da sauri yatashi batare dayay komiba kawai key motarshi ya sunkuta yazo inda take take nishin har lokacin bata denaba dan she's really finding numfashi difficult, hannunta yadaga yakamota ta taho luuuu babu karfi kodaya ajikinta tai yaushi, kumatunta yabaci da amai harda kunnenta, kulle idanunshi yayi gam sake ganin boobs dinta akaro nabiyu dayayi, sai kawai yakai hannu yaja riganta daga wuyanta zuwa kasa ya dauketa kaman wata yar jaririya tai lakur akirjnshi ko'ina nata na lilo iska na kadashi sabida tsabagen rashin karfi, ko kadan bai damu da aman fuskanta daya share tass a kan pyjamas dinshi ba, yaki fuskanta ajikinshi ya rungume ta tsam ta yanda babu wanda zai gane wani abu gameda ita yawuce yafita hatta fuskanta nakan kirjinshi, ya sauko kasa da ita yana mamaki yanda ko kadan batada nauyi kaman ya dauki paper, sanan yakarasa yabude kofa yafito guards dinshi duk suka zube akasa suna gaidashi suna kallonshi sabida yanda sukaga ya dauki Boy a hannunshi dudda basa ganin fuskan boy din sunsan shine dan fuskanshi na kife a kirjinshi sai kafafunshi dake lilo akan hannunshi ko amsasu baiyi ba yawuce wajen motarshi baya yabude ya shimfideta abaya har lokacin tana wani irin nishi idanunta na juyawa, sanan yatashi ya maida kofan yarufe yakoma gaba da sauri yatada motar yafice lokacin babu wanda yatashi a family su danko 8 nasafe bataiba, yaja motar yafita daga gidan, agaban wani private asibiti yay parking yafito yazo baya yabude yadauketa chak yana kallon fuskanta har lokacin yay cikin asibitin da ita yana shouting Dr, Dr, wasu nurses dawata macen Dr dasuka fito daga wani dakine suka tareshi tanakan jikinshi likitan takai yatsunta wuyanta sanan tai ihu. "Get a bed her pulse is very weak" turo gado sukayi da sauri ya sauke musu ita akai ya kwantar da ita sanan Dr tace "just stay here, who are you to her"? Shiru yayi yakasa magana Dr tawuce tabisu ciki da sauri tana gyara stethoscope din dake hannunta tana makalawa a kunnenta.
Ahankali yasami waje yazauna yay shiru he don't even know what to think idan yace "a girl" saikuma da sauri yace "no he's a Boy, kawaidai hala yana growing breast tissues ne due to small health related condition, tsoron stigmatization daga mutane yasa yake kullewa yana boyesu" saikuma yace "how?" Shiru kawai yayi ya dakatar da tunanin yana zaune awajen har almost 2hrs saikuma Dr tafito kallo daya tamai tadauke kai tace "follow me to my office" tashi yayi kaman wani abu yamutu acikinshi yatashi yabita ahankali, yana shiga yasameta a zaune hakan yasa yamaida kofan yarufe yajuyo ya kalleta, cikeda fada sosai tace "kuna kallo sister ku na neman maida kanta Tomboy kunyi shiru kun kyaleta" dan ware ido yayi yana kallonta yana kokarin maimaita abinda Dr tafadi cikin harshen turenci dayamai kaman baigane ba tsabagwn yanda tai maganan, sister? Saikuma tacigaba da masifa tace "wanan wani irin musiba ne yasami Nigeria, mata naso su koma maza maza naso su koma mata irin su Bobrisky, James brown da sauran su, how could u allow this girl small girl that i don't even think she's up to 20yrs tana neman tamaida kanta namiji eh?" Ahankali yace "a man, a girl"? Sounding so confuse, gyadamai kai tayi with full assurances tace "yes, though dai banga asalin abinda ta kulle breast dinta dashi ba, but her breast sun matse iya matsewa, kanta tasaka bald cap