Masifaffiyar Ƙauna Soyayyar da Ta Fi Komai Ƙarfi by M SHAKUR

Author :  M SHAKUR Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 51

18K to 21K   out of 152.6K words

signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number 07010439656 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._



EPISODE 8️⃣
_FREE PAGE_
*******
Washe gari!!

Yau Jumma'atu Babban rana sosai ta tashi da karfinta kaman ba itabace tai ciwon dako tsayuwa bata iyayi jiyaba lallai Dr nan yasan kan treatment, dan dakanta yau tashiga bayi tai wanka ta gyara kanta tsaf dan bataso wasu kattin mata sumata wanka, kayan datasa jiya da za'a kawota ta maida bayan tacire doguwan rigan, tadau hijabinta ta saka daya mata wani irin mugun kyau, gawani haske datayi buuu sabida ciwon datayi idanunta sun fada sosai sunyi fari kallll kaman anzuba nusu farin hoda babu kwalli ko digi acikin su sai lips dinta dasukai pink yirrr suka tattare suka tsuke suka bushe sabida har yanzu da dan zazzabi acikinsu da ita kanta, sai wani pimple kwara daya rak data farka tajishi akan goshinta daidai in-between giranta guda biyu kuma yaydan kato kanagani kasan pimple din period ne, tana kallon pimple din a madubin bayin taji tana tura baki dan yasa tai wani iri ga idanunta sundan kumbura sunyi nama irin na mara lafiyan nan, muryan Baba dayazo gaban bayin ne taji yana mata magana. "Zara'u me kikeyi kika dade haka abayi Dr yazo dubaki har an wuce gadonmu" kalman Dr da Baba yafadi hakanan saitaji gabanta yafadi takasa magana. "Zara'u kinajina ko zazzabin yatashi ne" jin muryan Baba adan rude yasa tace "nagama gani nan" tai maganan tana bude kofa tareda daukan kayanta data saka a leda tafito binta yayda kallo dan saiyau yakara ganin hijabin da kyau yace "a ina kika samu hijabi haka daya miki kyau haka Zara'u"? Yamata tambayan yana karban ledan hannunta da kayan data cire ke ciki, murmushi tayi tace "Baba wlh Maryam tabani, na islamiyyan mune ta dinko mana" dan tabe baki Baba yayi yace "iyye yar gatan Maryam, ba laifi Hijabin yamiki kyau kwarai" turomai baki tayi adan shagwabe tace "Baba balaifi nema kyan dayamin din?" Dariya yayi yace "nidai kinga tafiyata idan kuma kika bari Dr yatafi bai dubaki ba baza'a sallameki yanzu da safen nanba sai likitan rana yazo" Baba yay gaba abinshi dayake bayin abayan wani corridor dake cikin ward din yake, ganin harya fita daga lungun yay cikin ward dinsu yasa dadan saurinta tabiyoshi kanta akasa kafafunta na cikin wasu flat shoe baki irin yan dari biyar dinan.
Tana cikin tafiya dudda kanta na kasa ko kadan bata lurada bawon ayaba da yaron wata mata ya yar a tsakiyan ward dinba tana zuwa ta taka da kafarta, bawon ayaban yakama kasan takalmin ta daga kafan ta kai kasa zatai taking another step yawani yaja gaba zuttt tatafi tagaba gabaki daya zata fadi saikace anjawota da karfi ne kawai taji ta tafi ihu tayi sosai tana kokarin hana kanta faduwa tana watsa hannunta trying to stop kanta daga fadin. "Baaaaaaba......" shiru tayi batare data karasa kiran Baban ba jin ita bata fadi akasaba sanan ita batamasan a ina takeba takamaimai ammman dai bata jita akasa ba ta runtse idanunta gam tana nishi takara rike whatever hold her da kyau da fararen hannayenta ta rike gaban rigan ta daidai huge chest din da sauri da sauri kirjinta nawani irin mugun faduwa kaman zai rabe biyu, duka abubuwan nan sun farune aduka cikin sakanni dabasufi uku ba zuwa biyar, ahankali ta shiga bude idanuwanta dasuka shiga rawa kadan kadan kafin tabude su yan kadan, clean fararen kwayoyin idonta ne suka hadu dana Dr Imam dake sanye da fararen glasses yana cikin farin lap coat wanan karan ba stethoscope awuyanshi just him ne, gabaki daya tana cikin hannunshi yatarota, hannayenta duka biyun nakan kirjinshi tarike labcoat dinshi gam gam, yanda suka hada ido yasa ta maida idanunta ta kullesu da gudu gam gabanta nawani irin dukan uku uku daharshi kanshi yanaji ta kame kam tamakasa wani abu, duk cikin yan sakanni dabasufi goma bane akai abinanba daidai lokacin Baba ya iso wajen da saurin shi yan ward ma sukahau ihu. "Subhannallahi assha, waya yarda bawon ayaba akasa, zasu kara nakasa yarinyar dabata dade da farfadowa daga ciwo ba" Baba daya karaso wajen da sauri yace "Zara" kaman wacce aka mintsila tasaki riganshi da sauri ta tashi tareda kabarda hannunshi dake waist dinta kaman tana kabarda kyankyaso tafita daga jikinshi da gudu jikinta narawa sosai zatai wajen Baba dake kusada Dr ayaban dake kasan takalminta har lokacin yakara kwasheta tai kan Dr, harwani wuntsila hannu take sabida yanda take tsoron fadawa kanshi amman saida tafada kirjinshi dan at this time ta gwammace tafadi akasa shima dudda yanada daman a kauce tafadi akasan but bai kauceba fadowa tayi cikin kirjinshi fuskarta yay slapping chest nashi, chest dinta da nashi suka wani hadu suka buga juna yasake riketa ta hanyar kai hannunshi bayanta, da sauri Baba ya tsuguna kafinma tafito daga jikin Dr ya kama kafarta yacire takalmin sanan yadaye bawon ayaban yay wajen bin dake cikin ward din ya wurga sanan yadawo daidai itama tafito daga jikinshi ahankali ko'ina najikinta na bari kanta akasa yan ward namata sannu amman ko kadan she's not comfortable, hannunta Baba yakama yace "sannu kinji ciwone" girgizamai kai tayi jikinta narawa har lokacin bata dawo daidai ba, janta Baba yayi yace "Allah ma yakiyaye dabadan likita ba Allah kadai yasan irin faduwan dazakiyi muje ki zauna" yay hanyar gadonta da ita yan ward sai sannu suke mata dan babu wani wanda ya lura da abinda yafaru tsakaninta da Dr all abinda suka gani is Dr saved wanan kyakkyawar patient din daga fadi.


Har suka koma suka zauna a gado Dr Imam yakasa motsi daga inda yake, Zeena dake tsaye gaban gadon patient din dasuke dubawa daya barta yatare Fatima ne da bawon ayaba ya zamar da ita batare data kalleshi ba tace "komu dawo later mu karasa ward round dinne"? Dan juyowa yayi, saikuma ya sauke ijiyan zuciya yatako yazo wajen ya tsaya gefen zee din yana duba patient din yace "kin duba vitals dinta"? "Uhm" ta amsashi atakaice tacigaba da rubutun datake a folder sanan tamikamai karba yayi yaduba sanan yama matar alluran dazai mata sukabar gadon.

Tunda Baba ya zaunar da ita kan gadon take ba daidaiba kanta na kasa tana wasa da yatsunta dake nan dogaye ga kumbunanta farare fat dogaye masu bala'in kyau da kauri, kar kar dasu.
Muryan Baba taji yana "barka da zuwa likita" karban folder ta yayi daga hannun Zeena yana dubawa batare daya kalleta ba yace "any complain? Kinji sauki" gyadamai kai tayi ahankali da sauri Baba yace "yi magana mana Zara'una" adan hankali cikin siriryar muryanta tace "da sauki" matsar da folder yayi daga saitin fuskanta ya kalleta, kanta na kasa har lokacin tana wasa da yatsunta sai bantalar kunbunanta take da basu fito bama, pink lips dinta kadai yake iya gani, saikuma goshinta da gashi suka kwanta sukai lub lub ga zufa datakeyi a goshi sosai dudda ward din babu zafi dan akwai AC gakuma fankoki, duk kallonan yamata cikin yan sakanni ne sanan yarufe folder yamikama Zeena dake gefenshi yakarasa ya tsaya agabanta danhar kafafunta na gogan nashi, wani irin yawu tahadiye takasa dagokai har lokacin, hannunshi yasa a aljihu yaciro yar toculan shi ahankali yakirata kaman baison yakira. "Fatima" dagokanta tayi adan hankali hada ido sukayi idanunta sun cikada kwalla sosai, ahankali yakai hannunshi kan habarta ya kunna toculan ya haska idanunta yana kallonta murya chan kasan makoshi yace "crying angel" ayanda yay maganan daga ita sai shi zasu iyaji, juyowa yayi ya kalli Baba yace "zan sallameku Baba, zan baku maguguna dayawa, wanda every month dazaran ciwon maran zai fara zatasha, but nan da 7days zaka dawo da ita naduba ta" yay maganan yana bama Baba wata yar takarda yace "kabasu wanan zasu baka magungunan Allah kiyaye hanya" yay maganan batare daya jira maganan Baba ba yajuya yafice da sauri Baba yabishi har waje yanamai godiya dakuma addu'a daban daban.






Already Baba yariga yahada kayansu daman bawani abu garetaba banda kayan sawanta kala daya, daman abinci awajen mai shayi yake siyan mata, ledan kayan nata yadauka sanan suka shiga yima yan ward din sallama sukuma sunama Fatima Allah yakara sauki yasa kaffara ne fitowa sukayi yana gaba tana biyeda shi sukai hanyar pharmacy, ganin da dogon layi awajen yasa yajuyo yabata ledan kayan yace "rike ledan jeki sami kujera ki zauna chan na karbi maganin saimu tafi ko" gyadamai kai tayi tawuce ta tafi kujerun dake nan GOPD tasami wuri ta sauna a kujeran dake layin gaba inda mata uku ke zaune akan kujeran masu ciki sai ita data sami gefensu ta zauna tai shiru kawai kanta akasa danhar lokacin bata dawo daidaiba burinta kawai subar asibitin su koma gida, matan sai kallonta suke. Gabanta dataji ya yanke yafadi yasa tadan saki wani irin ajiyan zuciya kaman ance ta daga kanta suka hada ido da Dr Imam daya fito daga office dinshi wanan karan babu labcoat ajikinshi yana sanye da wata hadaddiyar bakar yadi mai digon fari fari, wanan karan ba cover ce akafarshi ba flat black Louis Vuitton takalmi ne akafan daya kara haska farin kafarshi, yay wani irin kyau bakin yadin yakara fito da hasken fatarshi, yanda kirjinta ke bugawa yasa ta janye idanunta da sauri ta saukar da kanta kasa ahankali ta shiga wasa da yatsunta tanajan hijabinta tarike gam, tadau kusan minti uku ahaka sanan ta sake dago kanta ta kalli direction din data ganshi hada ido suka karayi har lokacin yana tsaye awajen yay folding hannunshi a kirji yana kallonta dan baya komi ga mamakinta saitaga ya sakin mata wani cute smile da sauri ta dauke kai tanaji kaman numfashinta zai dauke saikuma ta mike zumbur ta zagaya ta bayan kujerun dan bamataso taje takusa dashi tawuce tafita daga GOPD gabaki daya da saurinta hartana neman fadi, iskan daya bugeta yasa tasaki wani hadaddiyar ijiyan zuciya tasami wani dan dakali ta zauna, hango Baba yafito yana nemanta yasa ta tashi da sauri tai wajenshi yace "me kikeyi anan" murmushi ta kakalo tace "Baba bansan asibitin nan mutafi gida" magungunan ta yamika mata a leda babba, karba tayi yace "gasunan birjik kiyita sha dazaran kin fara ciwon mutafi" wajen machine dinshi sukayi yatada ya dauketa sai gida.



_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number 07010439656 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._
6/23/21, 6:11 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_💫




_MASIFAFFIYAR SOYAYYA_


_THIS BOOK IS 500 IDAN KINASO PAY TO 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK, SAIKI TURO EVIDENCE OF PAYMENT TO MY WATSAPP NUMBER 07012181461_

✍🏾M SHAKUR



_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number 07010439656 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._




EPISODE 9️⃣

_FREE PAGE_

*****
Gidan nan babu wanda bai shigo yamata yajiki ba Maman Dady har wara takawo mata ma sabida ranan wara tayi ta karba cikeda kunya tamata godiya, Mama ma ba yabo ba fallasa tamata yajiki agaban Baba hakan yasa Baba yaji dadi, sanan yace taje ta kwanta adaki tahuta babu abinda zatayi yau shikuma Baba yawuce uwardaka wajen matarshi.


Da sallamaya shiga dakin zaune yaganta bakin gado tana fifita Abida datai bacci da mafici dan babu wuta tayi kyau sosai taci gayu tasa atamfarta mai kyau harda sarka awuya kaman wacce taje biki wanda abune dayasan bata sabayiba, zama yayi kusada ita tareda washe baki yace "wanan kwalliyan fa ni akamawa ne"? Wani banzan kallo ta jefeshi dashi sanan tace "kai asuwa, ni kaga dan Allah kabarni damuwan dake kaina daban Baban Habib" binta yayi da kallo yay shiru, dan yatsine fuska tayi saikuma ta nisa tace "uhm gwara ma nagaya maka, daga gidan Madam nake" yanda ya kalleta da sauri tareda sake natsuwa yasa ta gyadamai kai tace "gwarama kai salatin da kyau kaji, kirana tayi awaya tace nazo, nashirya naje nasameta tace min yaya ake ciki taji mijinta da mutanen nan namagana awaya ranan lahadi jibi kenan dan yau ai Jumma'a zasuzo, wai ya mun shirya mun gama hada kudin nace mata ko asi bakada shi balle chasi" wani gumi Baba yashare ahankali yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, wlh inda nasan haka abin nan zai kasance daban karba ba dukkece kika sani awanan ukuban" wani irin zaremai ido tayi tace "nice mene kace"? Kasa maimaita maganan yayi daya kalli kwayan idanunta saikuma ya saukar da murya ahankali yace "kiyakuri badake nakeba" kwafa tayi tace "Allah yasoka wlh dasaika raina kanka wlh mtswww" taja tsaki, ahankali yadafa kanshi saikuma ya buga tagumi saikuma ya kalleta cikeda damuwa yace "yaya zanyi yanzu Ruka kifadamin abinyi"? Shiru tayi tana kallonshi saikuma ta nisa tace "Mijin Madam yariga ya sanarda mu duk wasu ka'idoji da sharuddai na wanan lamarin ko kaje still maganardai itace zai sake maimaita maka, amman dudda haka yanzu katashi kaje kai wanka ka chanza kayan nan kasa wanan giznar danasa kasaya, ka feshe kanka da turare katafi chan sakateria office dinshi kasame shi kaje kuyi magana mai kyau, yafada maka idan dawata hanya dazakabi kome yagaya maka kadawo kasanar dani daga A zuwa Z sabida nasan yanda zamu bulloma lamarin daganan in lokacin Jumma'a yayi saika wuce kadawo gida karka biya ko'ina kadai jini ko" gyadamata kai yayi ta tashi tace "bari naje naduba ruwan dake murhu inyay sanyi kayi wanka da ruwan sanyi dan gaskiya sabida kai bazan hura wuta naci gayun nanba" tawuce tafita yabita da kallo yaji zafin yanda take gasamai magana amman yakasa cemata kala, kayan yacire yasa jallabiya yabi bayanta takaimai ruwan tadawo daki.

Fitowa yayi yadawo daki ya shirya tsaf yay mugun kyau kaganshi zaka dauka wani alhajine harda fesamai turare sanan tace "saura ka kalli wata mace" dan dariya yayi yaja hancinta yace "inada mace har mace irinki mezanyi da wata Ruka Baban Habib sai Maman Habib" murmushi tayi cikeda sonshi tace "nidai wuce katafi" tai maganan tana bashi key machine dinshi ta tasashi agaba har waje dudda yaso yama Fatima sallama dan taga yanda yake kallon dakin but bata bashi damaba haka yaja machine yatafi, murmushi tace "kwanaki kadan yarage kurabu" tawuce takoma daki, hijabi ta dauka tasaka sanan tafito ta shiga dakinsu Fatima, akwance ta ganta tana bacci, da kafa tasa ta hambareta da sauri ta farka harara ta balla mata tace "tashi kifita falo kizauna kimin gadin Abida tana bacci nikuma zan fita, in yarana sun dawo daga boko ki basu abincin dana dafa yana kula" gyadamata kai tayi ahankali Mama taja tsaki tawuce tafice daga gidan.



Wuraren goma Baba yakai sakateria yana kaiwa gate yay parking mai gadi yace "wajen Oga Abdul kazo ko" dasauri Baba yace "eh" ciki mai gadi yayi saigashi yadawo yace "yace kashiga" wucewa ciki Baba yayi yay knocking gaban wani dan madaidaicin office daga ciki aka amsashi "shigo Malam Muhammad" bude kofa Baba yayi ya shiga wani mutumi ne yana sanye da suit zaune akan kujera daga ganinshi kasan ba bahaushe bane banufe ne ya fadada murmushin kan fuskarshi yace "barka da zuwa Malam Muhammad" yamikama Baba hannu suka gaisa sosai sanan yakoma ya zauna yanuna ma Baba waje shima ya zauna sanan yace "ya ake ciki mutumina kahadama mutanen nan kudinsu kuwa"? Da sauri Baba ya girgiza kai anatse yace "saisa na shirya nazo wajenka Oga Abdu naga kana mutunci da mutanen nan saisa nazo ka taimakeni kadubi iyalina ka nemamin alfarma awajensu dan Allah, su dan karamin kwanaki zan biya wlh, ka taimakamin" hmmmm Oga Abdul ya fuzarda iska sanan ya kalli Baba yace "Malam Muhammad kasandai kai mutumina ne ko kuma tsakanina dakai babu boye boye, babu karya kowani abu, maganan gaskiya shine mutanen nan basusan menene alfarma ba wlh, saisa suke cewa mutum dakanshi yafadi yaushe zai biya back kuma duk ranan daya fadi ranan zai biya ko yabi sharadin daya yarda akai dazai ari kudin, mutumina idan baka da kudin nan bakada hanyar

7 / 51