Masifaffiyar Ƙauna Soyayyar da Ta Fi Komai Ƙarfi by M SHAKUR

Author :  M SHAKUR Category :  African Stories & Novels

Chapter   40 / 51

117K to 120K   out of 152.6K words

gudu ba" duk aka natsu yace "yarinyar nan yanzu xata shiga second semester ND two, tana final year, gaskiya zanso tagama school nan da 5month sanan ayi auren" da sauri Oba yace "muyi akidun nikka yanzu, mu daura musu aure but zata cigaba da zama anN a hannunku kawai zamuyi ne dan hankalinshi ya kwanta ya warke, but mu daura musu aure, in yaso bayan tagama makarantan nan da 5months ko 6 to be exact sai ashirya gangariyan biki na alfarma, kafin nan shima ya warke saiyazo gaisuwan iyaye ku ganshi akara sanin juna kun yarda" Granny tace "inhar hakan zaisa yasami lafiya ba matsala adaura auren kawai, ayi hotuna anunamai, Sarkin Kano ne cikin barkwanci yace "ashe nai basira dana taho da kayan daurin aure" yakira bafaden shi yace afara shigo da kaya, kafin kace me falo yacika da goro sweet tabarma da sauran su, Baba dudda bai soba haka aka sakashi waliyyin Zara, aka kira guards da all securities din suka shigo, Abba shiya daura aure tsakanin OluwaTobi Tajudeen Adewale da Fatima Zara'u Muhammad akan sadaki miliyan goma, wanda Sarkin Kano da Vice suka bada as tasu gudunmawar, Oba yakasa shiru sai murna bakinshi har kunne, take aka shafe fatiha securities suka fice bayan kowa ya debi su drinks dakomi son ranshi.





Ganin Fatima tashigo daki da gudu tana kuka gawata nabinta abaya yasa duksu Rahma suka juyo da Rayyana suna kallonsu, corridor tayi tabude kofan dakinta ta shiga da sauri itama Dami da sauri ta shiga ta maida kofan tarufe, tsugunnawa Fatima tayi agaban gado tana kuka sosai zuciyarta nawani irin rawa, ahankali Dami takarasa kusada ita hannunta tadaura akan gyalenta hakan yasa gyalen dake gabda zamiyowa yazamiyo tareda dan kwalinta gashinta yawani irin zubo dayasa Dami ta kalli kan takasa daurewa tace "Wow!" Saikuma ahankali tace "Is this your hair Fatima"? Saikuma gently tadago Fatimar takai hannunta tagoge fuskanta tass tace "Fatima i want to sincerely apologize to you kan duk abubuwan danamiki abaya, ki gafarceni, duk kishi ne da tunanin banza kan kanina yasa nai haka, haka and I know kinason Tobi dan haka kidena kuka I promise you I will take care of him xaiji sauki and he will come here and get you" ahankali tadaga kanta takalli Dami gyadamata kai tayi tace "i promise he will be fine" ita kanta batasan mesaba but samin kanta tayi da fadawa jikin Dami ta kankameta rungumeta back Dami tayi, tana feeling her brothers love in Zara's heart, aikowa akayi akirata hakan yasa ta tashi, itakuma Granny ta shigo rikeda babban mayafi ta kalli Fatima tace "muje ki gaida Baban mijinki" kallon Granny tayi cikeda rashin ganewa, Granny tayafa mata gyalen tareda lullube mata fuska sanan tafito da ita sukai falo, har gaban Baban Tobi takaita tace "ga matar kunan" ga mamakinta saitaga Oba yatashi yadagota tareda rungumeta sanan yabude gyalenta kadan yamata peck agoshi yace "welcome to the family daughter inlaw" aka shiga daukansu hotuna, dan satan kallon Babanta tayi taga yadauke kai daurewa tayi tahana kanta da kuka duk yanda sukai da ita binsu take tai zuru zuru haka aka yiyyi hotuna dabatasan adaddinsu ba bamatasan a ina aka samo masu hotunan ba...... kafin kaceme zokaga headlines da blog stories Son of Oba of Lagos ties the knot with a northern lady secretary, daddan sarkin Lagos ya auri bahaushiya yar arewa ba'a riga an sanar da ranan daza'ayi kayataccen bikin ba amman andaura aure secretly inda manya manya da sarakuna ne kadai suka hallaccidaurin auren.




Karfe biyu bayan anyi salla tarene suka tafi itakuma Fatima data kasa daina musu kuka sabida komima ciki harda yanda Baba yaki kulata harya tafi ko kallonta baiyiba akace ta tafi, sanan suka gyara zama a falon yace "I hope kunyi understanding decision dina, dudda banjin Imam nasan zai fahimcen" Ammi ne tace "wlh babu komi nidai awurina matar mutum kabarinsa Allah yayi batashi bane" duk ijiyan zuciya aka sauke sanan ya kwashe kudin sadakin 10m yaje har gaban Granny yace "Mama Zara yarki ce, ke kika kawo mana ita rayuwan mu, ga sadakin ta nan kirike, nida Ibrahim zamu mata kayan daki da kudinmu amatsayin mu na yaranki, wanan duk yanda zakiyi dashi kiyi" shiru Granny tayi tana kallon yaran nata saikawai tabudemai hannu shida Ibrahim din rungume su tayi tashiga musu addu'a don suncika yara yan halas, sanan tasake su ficewa sukayi abinsu falon yarage saura matan kadai, Granny ta kallesu tace "zamuma Fatima hadadden usulin gyaran jiki dag gobe za'a fara, wanan da bayerabe zata aura dole mu gyara yarmu" Ammi tace "hakane" sanan suka shiga planning yanda za'ayi za'a hado kayan shaye shaye tanasha daci, dana zama dana tsarki da turare, za'a hadamata ta tafidasu school ma, in yaso bayan tai final exam tadawo gida sai adauko yar Malaysia.




Karfe tara na daren ranan jirginsu Oba yasauka a lagos, motoci sukazo suka kwashesu sai gida, ana parking Dami tafito da gudu tana ihu, tun kafin takai flat dinsu su Mum suna fito dasu Dami suna lpy, cewa tayi "niku matsamin Tobi zan fara fadama good news dinan" tashiga falonsu da gudu suka biyota, ganin bata ganshi ba yasa tajuyo Mum tace "yana bedroom dina" da gudu tai stairs tabude dakin Mum dinta ta shiga Tobi tagani kwance akasa yay lakur kaman kamai kuka, wani irin ihu tayi tafada kanshi tace "Tooobiiii am so happy for you look at this" tadagashi da sauri tabude jakanta taciro wayarta ta cillar da jakan tabude gallery ta shiga pics din datama Zara dabama tasan tamata ba, takai wayan saitin fuskanshi tace "look is your Zara, she's alive, Zara is not dead, Zara is not dead Tobi look at her" ahankali ya karkatar da idanunshi ya kalli screen din wayan ganin Zara kan screen din takai hannu tana goge hawaye kusada babanshi yasa yawani irin fizge wayan da sauri yana zooming hoton yana kallonta da kyau kaman mahaukaci sanan ya kalli Dami yadaura hannunshi kan wayan yace "Zaaaa......ra"? Gyadamai kai Dami tayi ahankali tana hawaye tace "yes is Zara, and she is now your wife, anyi Akidun nikka" wani irin ihu su Mummy da Taye sukayi, Mum datake musulum musulum gatanan kaman chrismus batasan lokacin data zube akasa tai sujjada ba, saikuma ta tashi takama rigan jikinta tashiga rawa sosai tanajin dadi yaran suka shiga tayata Tobi kuma sai kallon hotunan Zara yakeyi.


Dakin Dad yabude yashigo Tobi yadaga kai yakalleshi shiru, ahankali Dad yakaraso gaban Tobi yazauna hakan yasa sauran suka natsu da rawa, hannunshi xaya Dad yakama sanan yakai hannunshi kan fuskarshi kafin ahankali yasakinmai peck a forehead yace "Tobi i know u can hear me, I am sorry for hurting you and for making your life this miserable, but karshen wahalan yazo" yanunamai wayan yace "you are officially Zara's husband, anyi akidun nikka, tana final year the main walima grand wedding will be after 5month from now bayan tagama exam, now what I want from you is" yadanyi shiru sanan yasake sakinma yaron peck a kumatu yace "your Dr daka kora will resume tomorrow, zai cigaba da maka treatment Zara can't see you like this zata iya guduwa, you need to be fine, be eating, kadena kwanciya akasa haka and change your clothes idan ka warke tass zan kaika har Abuja kaje kaga matarka okay" bin bakin Babanshi yakeda kallo yagane all abinda yace, for the first time after one whole year sukaga yay murmushi yafada jikin Baban hakan yasa suka fara ihun dadi sun murna sun dade ahaka har Tobi yay bacci aka kwantar dashi sanan aka shiga plan, Dad yacema Mum yanaso itadasu Taye zasuje Abujan to meet with Zara and her Family Dami kuma will stay d Tobi da Dr shi zaI fara zuwa gobe.


Washegari tun safe Dr yazo yaduba Tobi da yay wanka da kanshi, yamai allurai yabashi magani yasha kaman ba Tobin kwanaki ba dayakusa kasheshi da kyar aka ceceshi, sanan yama bayani Tobi will be fine, but treatment dinshi yawanci bacci ne, zai bacci for 72 hours, dazaran yatashi abashi healthy food da magani yasha yaci yakoma, haka aka fara, and Alhamdulillah akwai lot of changes....


Abangaren Fatima tuni aka fara mata kayan shaye shaye ciye ciye na kayan mata, ko kadan bataga chanji gun kowa agidan ba saima murna dasuka tayata, saikuma Text din Dr Imam datagani yaturo mata congratulations Allah sanya alheri, Dad yafadamin.


Ana gobe Sunday zata koma school dan 1week aka bata, Maman Tobi da yan biyunta sukazo Taye da Kende duk since atampopi shiga na mutunci dan sunsan North zasuzo, anmusu tarba na shataran arziki, sanan suka kara bama Fatima hakuri kan komi daya faru abaya, itadai bata cemusu komiba kawai bamurinta taga Tobi ko amata maganan shi amman babu wanda yamata, da yamma suka tafi washegari ta koma school bayan Granny tahadata da magungunan ta nasha tace kullum saita kira ta tambayetra kota sha, wasa wasa saida tadage sanan ta iya tafara karatu sabida Maryam datake sakata dole sabida tunanin Tobi tun bayan ganin video shi, ita mantawama take wai ita matan aurece kawai dai tunanin rashin lafiyanshi tayi, final semester is not easy wanan karanma bakoda yaushe take iya komawa gida weekend ba ga project ga fix lectures da ake hada musu asabar ko lahadi amman dudda haka bata fasashan magungunan da Granny kullum ke kiranta tasha ba, suna karewa zata aiko direba yakawo mata sababbi, kafin kace me tafara wani irin cika jikinta namata wani iri. Ahaka hartai 2months a school.





_Erotic Ideas group na matan aure zalla ne, group ne damuke program guda HUDU aduk sati, ranakun sune ALHAMIS, JUMMA'A ASABAR da LAHADI._


_Duk ranan Alhamis munayin program mai suna MARRIAGE LIFESTYLE, wato ZAMANTAKEWAN AURE, inda nakema mata lectures kan yanda ake zama da miji dakuma dabarun zama da miji, ranan jumma'a kuma muna program din damuke kirada TALK & HEAL wato yi magana ka warke, inda matan aure zasu gayamana matsalolin dasuke fuskanta agidajen mazajen su, zasu iya turamin ta pc idan basuson asansu nisainai forwarding group mu taimaka musu da shawarwari dakuma dabarun dazasubi su magance wanan matsalolin, sai ranan asabar shine ranan LECTURES, inda zan dauki darasi dake dauke da dombin ilimi abu wanda ya dace mata su iya dangane da aurensu, mu koya musu ayi magana akai sosai, sai ranan Lahadi zamuyi lectures akan ilimin daya danganci yanda zaki gamsar da mijinki sanan ki gamsar da kanki, kisaka mijinki ihu agado yana kururuwa yana sambatu, mukoyar dake yanda zakiyi spicing up sexlife dinki, and yanda zaki dinga rayuwa da mijinki kullum kaman sababbin aure._

_Idan kinason shiga wanan group din zaki turo 2000 to 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din, wata daya ne group din, idan kinason ki cigaba da zama duk wata dubu dayane 1500 ne subscription, sababbin zuwa kuma new member zakiyi register is 2k ne, don karin bayani zaki iya tuntubata a number ta 07012181461_
M Shakur ❤️







_NAFJAN COLLECTION_
_Nafjan Collection business ne na shahararriyan CEO dinan wato Nafisa, wacce ta kware akan sana'oi kala kala._
_Tana saida kowani kalan kaya dakuka sani, Riga, wando, lace, shadda, atampa, takalma, na maza, na mata, na yara, na manya, sneakers, cambas, sandals, flat shoe duka, handbags, bagpack, akwatuna, dogayen riguna, agoguna, tana shigo da hadaddun kayan daki daga kasan waje, kayanta arahansu zaisa kama rufe baki, dan tuntubarta ko magana da ita directly zaku iya saminta awanan number wayan 08160472711, kowani kalan abu kuke nema kawai ku danna mata kira dan tambayanta kuji kotana dashi kobatada shi_

_Dankuma magana da ita directly a watsapp zaku iya samunta ta hanyar danna wanan link din.👇_

https://wa.me/+2348160472711

_danyin sarin kaya awajenta da sallan nan, just chat her up_ https://wa.me/+2348160472711
7/17/21, 5:31 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

TALK TO ME M SHAKUR DIRECTLY BY CLICKING ON THIS LINK https://wa.me/+2347012181461

✍🏾M SHAKUR
_GGM THIS IS A BONUS PAGE INHAR THIS MADE YOU HAPPY INASO KUNUNAMIN KAUNA YAU, JUST CLICK ON THIS LINK, GO TO MY INSTAGRAM ACCOUNT AND FOLLOW M SHAKUR DINKU PLEASEEEEE._

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=s498eu8pt72t&utm_content=x8r5nr


EPISODE 6️⃣4️⃣ & 6️⃣5️⃣

Daga window falonshi Dad ya tsaya yana kallonshi yanda Tobi ke workout na fitina gashi yadauko wani sabon couch, dudda all this two months he has been on his drugs but yanzu yaji sauki sosai yakara wani irin kyau bakinshi yakara so pinkish, ga Dami da yanzu itace best friend dinshi zaune akan chair wajen itama sanye da kayan work out tana rikeda water bottle dinshi, tana kallonshi tana murmushi ita kanta muscles dinshi har tsoro suke bata sabida yanda suke.....

Dafashi da akayi yasa Dad yajuyo Mum ce tana murmushi sosai tace "our Son is back" ahankali Dad yace "oh yes he is" murya chan kasa Mum tace "amman yaushe zaka barshi yatafi yaje yaga matarshi kace when he's done with his medication kuma yakare yanzu ai" dan murmushi Dad yayi yace "am planning on giving him the news today, bari yagama workout ya shigo breakfast" rungumeshi Mum tayi saikuma tai kissing nashi abaya tace "I love you horny" ahankali yace "love you too, muje kasa" sauka sukayi dakanshi yahsiga tayata saita dinning.


TALK TO ME M SHAKUR DIRECTLY BY CLICKING ON THIS LINK https://wa.me/+2347012181461


Around 9 Tobi yashigo yana kamshi sosai looking damn huge, zama yayi yayyinshi ma duk suka taho aka zauna aka fara breakfast, saida suka gama breakfast sanan Dad yay gyaran murya yace "Son" dago kanshi Tobi yayi ahankali sanan ya kallai yace "yes Dad" ahankali Dad yasaki murmushi yace "private jet is ready, your new house na Abuja is ready, car is ready nachan, sanan direba na Abuja is ready sabida bakasan garin ba and this will be your first time in Abuja, so now the choice is yours anyday you are ready to see your wife Zara, shiryawa kawai zakayi kafita" jiyayi zuciyanshi na neman fita sabida farin ciki da sauri ya kalli Baban shi da Maman saikuma yace "Dad for real"? Sounding damn excited, gyadamai kai Dad yayi dawani irin sauri yatashi kawai ya rungume Babanshi saikuma yasake shi ya rungume Mum ya shiga kissing face dinta yace "I love you Mum Dad you guys are the best" ya kalli yayinshi yabasu high five sukayi sanan yace "okay bye am off to look good for my wife Dad" dukansu dariya sukamai Mum ta kalli Dad tace "hakafa kadinga rawan jiki kaima lokacin damukai aure" hararanta Dad yayi irin ya kina tonamin asiri gaban yara yaran ko suka kwashe da dariya.

Flat dinshi Tobi yawuce direct yana murmushi, kayan dake jikinshi yacire yawuce yashiga bayi, closet na shower essentials dinshi yaciro sanan yadauko wani kit na Bevel Shave System kit, kit ne na abubuwan shaving mai bala'in tsada, akwai pre shave oil, shaving cream, intensive moisturizing balm, brush, sai wani hadadden shaving stick dayay kama da machine, murmushi yayi yace "lemme make myself yummy for wife" pre shave oil yashafa agaba da hammata, saikuma yay applying shaving cream, kafin kaceme dudda bawani gashin kirki bane ajikinshi amman yashiga shaving wajajen nan yagama tass sanan yasake hadadden wanke feeling fresh, sanan yafito yashiga closet yashirya cikin 3quater da faran riga yadau car key yawuce yadauki wallet yafice, mota yashiga yaja, barbing saloon yaje aka gyaramai gashinshi ya aske tass yayi akamai hadadden low cut mai sanan aka gyaramai saje asalin gyaran fuska, bayan angama saida ya kalli kanshi ya yaba,yabiya kudi yafito yatafi Spa, wai namiji ne da morrocan bath, har body polish yayi, face treatment, lip treatment, lips dinshi suka kara taushi da pinkish sanan aka hadamai da deep tissue massage akamai gyaran kumba tass na kafa da hannu sukai haske sosai, sanan yay bacci sai bayan yatashi yatafi, awani asibitin hakori ya tsaya yaje aka wankemai baki sosai da hakora suka kara haske wlh ko amaryane shi sai haka, saida yagama gabaki dayan gyaran sanan yakoma gida around 9 nadare bayan ya tsaya yayi salla, yana kaiwa gida a flat dinsu yafara shiga duka iyayenshi suka bishi da kallo ganin yanda fatar jikinshi ke sheki kana ganinshi kaga dan gayu dan gata kuma, tasowa Dami tayi da sauri tazo gabanshi tana kallonshi hannunta takai ta taba lips dinshi tace "janbaki ka shafa ne Tobi" fari yamata da ido yace "stop touching my lips is for my wife" baki Dami tarike irin iyye basaban ba, sudai su Mum najinsu suna murmushi, yace "am hungry Dami give me food" zuwa dinning tayi tazauna kusada shi tana zubamai abinci tace "wai spa kajene kaga yanda kake sheki kuwa wanan askin yay kyau" murmushi yayi yakai hannunshi yashafa kan yace "I did it for my wife, nasan she will love it" hararanshi Dami tayi tace "nimadai aure zanyi stop intimidating me" murmushi yamata yakai abincin baki tace "yaushe zaka tafi"? "Gobe da sassafe, bari nagama muje kitayani hada kayana" gyadamai kai tayi tana zaune tana kallonshi yagama ci suka wuce suka fice Mum da Dad harcikin ransu Dadi sukeji yand yaransu ke shiri yanzu.




Yau tunda ta tashi sallan asuba bata komaba itada Maryam, dan test sukedashi gobe asabar mugun lecturer yamusu fixing test da lecture duk gobe, yau kuma Friday lecture daya kawai gareta dan dayan lecturer shine yace bazaizo yauba yamusu shifting lectures din Saturday.
Tayi kyau takara haske, tawani ciko, ita kanta Maryam takance wai kodai magungunan nan na Granny akwai wanda ke kara kyaune cikinsu dan tafadima Maryam ance an daura mata aure, dan ita har yanzu abin bambaram yake mata wai tai aure, ita matar aurece gashi gabaki daya an chanza mata gyaluluwanta zuwa masudan girma, sai 7 tagama karatun sanan ta tashi tacire kaya tashiga bayi da sauri dan 8 takeda class, wanka tayi tafito tabude box dinta, wani soft sky blue lace dinta dakeda zanen black flowers dashine saman kan kayan kawai ta dauka da black veil, sanan ta shiga shiryawa, kayan tasaka tazauna tana saka kwalli wayanta ya shiga kara da sauri ta dauki wayan dake kan gado ganin Granny ne yasa takai wayan kunnenta da sauri tace "Granny, harkin fara kewana, good morning" "morning diyar kirki, kinada lectures this morning ne"? Ahankali tace "eh, inada shi, but banda second

40 / 51