JOY by Aysha Nalado

Author :  Aysha Nalado Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 23

18K to 21K   out of 68.8K words

yana aiki sai bayan isha'i ya maida
keken daga nan kuma kai tsaye ya nufo gida bayan ya tsaya ya sai ma Fatima Apple
sanin yadda take matukar son shi.

Suna zaune tsakar gida bayan sun idar da sallar isha'i, suna dan ta6a hira yayi
sallama, a tare suka amsa masa, Fatima ta mik'e kamar yadda ta saba kullum ta kar6i
ledan hannun shi, fuskarta ya kalla ganin bata cikin walwala kamar yadda ya saba
ganinta kullum ya ji babu dadi, a ran shi , duk da tayi kokarin boye hakan ta
hanyar sakar mishi Murmushi kafin daga bisani ta ce "sannu da dawowa Yaya."
Murmushi ya yi mata shima ya ce "yawwa yar gidan Yaya Ameen." Sunan da yake kiranta
idan yana cikin nishadi, dawowa tayi ta zauna ya biyo bayanta ya zuba a tabarma ya
gaida Ummi, cike da kulawa ta amsa shi tana mishi ya gajiya, ta kalli Fatima ta ce
" Binta daukowa yayanki abincin shi a kitchen." Da sauri ya ce "A'a Ummi bari na
watsa ruwa tukunna." Ya karashe maganar yana mikewa, ya nufi hanyar wajen drum don
ya dibi ruwan wankan , da sauri Fatima ta riga shi isa ta dauki boket ta zuba mishi
ruwan , kallonta yayi da Murmushi a fuskar shi ya ce "Nagode kanwata." Daki ya koma
ya rage kaya hadi da dauko kwandon soson shi da sabulu, har zai shige toilets din
ya tuna dagargadin likita akan wankan shi da ruwan sanyi saboda larurar shi,
dakatawa ya yi ya ce "Ummi a kwai ruwan dumi ne?" Ta ce eh akwai a flas, kafin ma
a umurceta ta mike ta dauko mashi flas din ya juye ruwan ya shige.

20 minute kacal ya kwashe ya fito sanye da jallabiya, dakin shi ya nufa ya shirya
cikin kana nan kaya ya dawo, abincin shi Fatima ta dauko mai, ya kalleta ya ce
"zauna muci tare." Ummi ta ce "yawwa kamar kasan yau ta ki cin abinci kwata kwata
dama jira name ka dawo ba gaya maka." 6ata rai yayi ya ce "me yasa Fatima." Tayi
narai narai da idanu, babu alamar wasa a sautinsa ya ce "oya let it." Ba musu ta
dauko cokali ta saka suna ci, ganin tana wasa yasa ya Shiga bata da kanshi a baki,
hakan ba sabon abu bane a wajensu dama, sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya dauko
Apple dinta ya bata, nan ta ke ta shi ga fara'a tana godiya, ya ji dadin gani yadda
ya sake take farin ciki,nan ta wanko ta ba ummi daya ta dauki biyu, tana ci yana
janta da hira, labarai masu ban dariya har da su tasuniyar gizo, Ummi ma ta biye
musu tana saka musu baki, kan kace koba Fatima ta wartsake duk wani damuwa dake
damunta ya kama gabanshi, sai lokacin take tunawa da batun Amira, kallon Ummi tayi
tana gatsar Apple ta ce "dazu Anty Amira ta shigo." Ga mamakinta gani tayi Ummi ta
washe baki ta ce "Allah sarki Amira yarinyar kirki, kai yarinyar nan tana da
hankali wallahi, na Dade banga budurwa mai natsuwa da hankalin ta ba." Fatima ta ce
"Hmmm Ummi ita fa ta share gidan nan ta cika drum da ruwa, ta zauna ta tayani hira
sosai, Ummi dama ta saba zuwa ne." Ummi ta ce " ta kan shigo jefi jefi cikin
kwanakin nan idan kuna makaranta da yake ita suna hutu kafin su fara zana waec,
tana shigowa idan babu kowa a gidan su ta kama mini aiyuka ta tayani hira har
wankin kayana tana yi min, kuma ko na ce ta bari bata bari, yarinyar ba dai
hankali ba. Haka Ummi ta yi ta yabon Amira Al'ameen na jin su, bai dai tanka ba,sai
gurin sha daya sauran suka ta shi.


Pls comment yan Amana, comment dinku shine karfin gwiwana wollah, idan kina comment
zaku ringa samun update a kai a kai😬
[12/29, 2:34 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀


*PAGE 11*


Yau kimanin mako biyu rabon Fatima da school, a cikin wad'anan y'an kwanakin
Al'ameen ya yi kokari sosai wajen ganin bai bar barta ta shiga damuwa ba, ya
zaunar da ita tare da sakawa ta daukar mai alkawarin akan baza ta sake zuwa gidan
su Joy, kuma daga yau babu maganar kawance a tsakanin su ya kashe har abada, da
farko ta shi ga damuwa amma daga bisani ganin yadda ya nunka kulawar shi a kanta
yasa cikin kwana uku ta ware ta nuna komai ya wuce ta hakura, sai dai na ciki na
ciki, kusan kullum sai ta shiga toilet ta sha kuka idan ta tuna da Joy, damuwarta
d'aya har yau bata san halin da take ciki ba, kewar ta take ji kamar kamar me.

A bangaren Joy ma kusan haka ne sai dai ma mu ce har gara Fatima. Sosai Mom ta saka
mata matakan tsaro bata zuwa ko ina, daga school sai school, kuma shima ita take
sauke ta da kanta idan an tashi ta biya ta dauko ta, duk wata kafa da zata bi ya
sadata da Fatima Mom ta to she shi, ga Papa ya yi tafiya zuwa Japan tun last week
dama shi ba cikakken mazauni bane da wuya yayi zaman sati biyu a k'asa ba tare da
yayi tafiya ba saboda harkokin kasuwancin shi, iya damuwa ta shige shi har ta kai
yanzu bata tsinana komai a class bata maida hankali kan karatu bata jan note ga shi
suna daf da fara mid term test.

Duk halin da take ciki Mom ta sani, tun cikin last week ta yi bincike ta gane
Fatima ta bar school din, hakan ya mata dadi kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha don
murna, da gangan ta hanata duk wata dama na fita ita kadai don kar ta samu damar
zuwa gidan su Fatima, uwa uba kuma security da ta saka Papa ya zuba musu a bakin
get, har guda hudu babu mai ikon shiga ko fita daga gidan sai da sanin Mom.


A haka makonni suka sake shud'ewa, ana sauran 1 week su fara test, Joy ta rasa
yadda zata yi, saga da marwa ta ringa yi a dakin ta, duk wani dabara da zata yi don
ta bar gidan ta gwada babu sa'a , wani tunani ne ya fad'o mata a rai, ta ke wani
farin ciki ya lullu6eta, da sauri ta dauko note book dinta da biro ta zauna a kan
bed ta shiga rubutawa Fatima letter, kalamai ne kad'an na ban hakauri tare da nuna
yadda take tsakanin kewa da kaunar ta, ta k'ara da batun fara test din su next
week tare da rokonta akan ta daure ta yi mata replay, a kasan tayi drowning din
hearts guda biyu daya cikin daya kasancewarta gwanar drowning take ya fito share
kaar ba hannu ya zana ba, a ciki ta rubuta sunayen su, a kasan hearts din kuma
ta rubuta friends forever cikin wani salo mai kyayatarwa.

Ninkewa tayi ta bude Jakarta ta dauki kudi kimanin dubu goma, ta boye a cikin
aljihun pencil wandonta ta sake rigarta mai hannu bes wanda ya kai mata gwiwa ta
fice daga dakin, sai da ta fara leka Mom ganin ta maida hankali tana danna system
yasa ta fice da sauri direct counpuond ta fito, ma'aika nata gaisheta, da fara'a
take amsawa tare da kiran sunan kowannen su, hakan na musu dadi, suna son Miss Joy
sosai kasancewarta mai fara'a da sakin fuska bata da wulakanci da izza ko kadan
sabanin mahaifiyarta da take ji kamar ita ce ma mai dukiyar ba Papa ba. In da ta
hango drivernta Peter zaune shida gardener na gidan ta nufa, da fara'arta, ganin
ta yasa Peter tasowa da sauri ya tare ta bayan ya kwashi gaisuwa ya shiga
tambayarta za'a fito da mota ne. Girgiza kai ta yi ta ce "Peter wani taimako nake
nema a wajenka, idan babu damuwa zan dan aikeka nan babu nisa amma bana son Mom ta
san da maganar." Washe baki yayi yana kallonta, saukin kanta na kara mata kima a
wajen shi, ji yadda take mai maganar don zata aike shi kamar ba zamanta yake yi a
gidan ba a yau idan ta ce ta sallame shi a aikin nan ya zaunu. A dan ladabce ya ce
" ki aike ni duk Inda kike bukata daga nan har abuja ni driven ki ne, kuma na miki
alkawain madam bazata san da wannan maganar ba." Cikin jin dadi ta ce "Ngd Peter,"
ya ce "never mind your Majesty." Waige waige ta danyi kafin ta fito da pepan daga
aljihunta ta mika mishi. Ta ce "Wannan nake son ka kaiwa kawata Fatima, nasan
kasanta ai?." Ya gyada kai cike da mamaki, don ranar a gaban idanunsu komai ya
faru, ta ce "Kasan gidan su?" Dan Jim yayi alamar tunani, ya ce "eh kamar na sani
ba gidansu na a wancen layin ba ne." Ta ce "yes." Tare da sake yi mai kwatance sai
da ta tabbatar ya gane sosai, sannan ta Ciro dubu goman nan data dauko ta mika
mishi, godiya ya shiga kwasa cike da farin ciki, ta ce "Pls ka kiyaye ka san me
zaka fadawa Mom idan zaka fita, sannan ka tabbatar ka amso min replay daga gareta
kar ka dawo kin ba tare da amsa ba, sannan ka tabbatar ita ka damkawa hannu da
hannu kar ka ba kowa idan ba ita ba." Ya ce "Am gama your Majesty." Daga haka
juyawa ta yi ta koma ciki, dakin ta ta haura ta dage labulayen window, tana kallon
sanda Peter ya isa bakin get a moto, sai da securities din nan suka kira Mom ta yi
magana da Peter ko mai ya gama mata oho ta dai ga an bude mishi get ya fice ajiyar
zuciya ta sauke ta koma da baya ta zauna a bakin bed ta rafka tagumi.

Peter bai yi dogon tafiya ba ya iso kofar gidan, tunda dama already ya san gidan
don haka bai sha wani wahala ba, daga nisa kad'an ya faka motar shi ya karaso da
kafa, babu kowa a wajen hakan yasa ya dan jingina yana jiran ya samu yaro ya aika
kiranta, sai dai ya kai kusan minti 30 babu yaron da ya gifta gaba daya duk ya gama
gajiya da tsayuwa, cikin wannan halin Al'ameen ya fito daga gida cikin shirin shi
na tafiya masallaci, don gabatar da sallan la'asar da ake kira, da sauri Peter ya
iso gare shi, ya mishi sallama a gurbace tare da mika mishi hannu, kollo daya
Al'ameen ya gane Arne ne, hakan yasa ya ki amsa masa sallman da ya mai kuma ya ki
bashi hannu, peter bai damu ba, a haka suka gaisa, Peter ya ce da gurbataccen
hausan shi "bros pls a gidan kake." Kollon uku saura kwata al'ameen ya mishi kafin
ya amsa da "yes." "Thank God!" Peter ya fada yana Ciro pepen daga aljihu, ya ce "
Miss Joy ne ta aikoni na kawowa Fatima wannan takardan pls ko zaka iya yi min
magana da ita." Ji Al'ameen yayi ran shi na tafasa, ya tsani duk wani Abu da zai
tuni mishi da ko sunan yatinyar ne balle abin da ya shafe ta, kamar ya fatattaki
Peter ya kora shi, sai dai wata zuciyar ta hane shi dakewa yayi ya ce " Sorry
Fatima bata gida yanzu haka sai dai ko ka kawo a ajiye mata. Ni dan uwanta ne idan
tadawo zan bata." Jim Peter yayi ga koshi ga kwanan yunwa, idan ya ba Al'ameen
wasikar zai zama babu replay din da zai kai ma Joy, kuma sai da ta ringa jaddada
mashi ya tabbatar ya tsaya ya amso mata amsa, dagowa yayi ya kalli Al'ameen dake
binshi da ido ya ce "Miss ta ce kar na bawa kowa kuma na tabbatar na amso mata
repley. " shiru Al'ameen yayi yana nazari kafin ya ce "I'm coming." Dakin shi ya
koma yq samu pepa da biro ya rubuta THANK U ya linke ya fita ya mikawa Peter tare
da cewa "ka bata wannan ka ce daga Fatima, kagaya mata cewa ka ba Fatima wasikar
hand to hand." Amsa Peter yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya ce "ok ngd
sai anjima." Al'ameen ya amsa da yawwa sai anjima.



Babu yawa.🙏
[12/29, 2:35 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀


*PAGE 12*


Al'ameen na tsaye har Peter ya shiga motar shi ya tayar ya bar layin, mayar da
kallon shi yayi kan pepen da ya bashi , kamar zai bude, jin ana kokarin tayar da
sallah yasa ya fasa bud'ewan, sakawa a aljihu ya wuce masallaci. Koda suka idar da
sallah bai bi ta kan pepan ba, hasalima ya manta da shi, kai tsaye Sayako ya nufa
gidan Alhaji Bala ko zai samu keke, don d'azu da safe ya je babu keke a k'asa.
Cikin sa'a kuwa yana komawa ya samu, singning yayi ya dauka ya kama aiki.


*******

A cikin y'an kwanaki kad'an Amira tayi namijin kokari wajen cusa kanta gurin
Ummi, har ta kai yanzu da sun zauna hira Ummi bata da wani zance sai nata, a
6angaren Fatima ma babu laifi don tana kyautata mata sosai tare da jan ta a jiki,
kun san kuma ita zuciya an halicceta ne da son mai kyautata mata. Sai dai fa har
zuwa yanzu uban gayyar bai san da zamanta ba, iyakar ta da shi gaisuwa, shi ma a
d'arare don bata sakin jiki idan yana waje ta dinga sunne-sunnen kai kenan, kunyar
shi take ji matuka gaya, babu wata sanayya mai karfi a tsakanin su, hasalima duk
sanda zasu gaisa da sunan d'aya daga cikin kannenta yake kiranta alamar bai
tantance ta daga cikin su ba, bare har ya kai ga batun bata wani matsayi na
musammam a zuciyar shi abinda ke matukar ci mata tuwo a kwarya.

Yau a islamiyya bayan an tashi su ka ke6e da k'awarta aminiyarta Zainabu wacce ita
ka'dai ce ta san halin da take ci game da soyayyar Al'ameen, haka duk abinda take
wa Ummi ita ta bata shawarar yin hakan kasancewar ta fita wayau da sanin duniya.
Cike da damuwa ta kalli Zainabu ta ce "Zainabu Ya zan yi Al'ameen ya so ni? ya zan
yi ya kalle ni da kallon soyayya koda rabin rabin wanda nake masa ne? na kusa
gazawa zuciyata ta kusa tarwatsewa da soyyayar sa, Babban b'akin cikina shine yadda
har yanzu ya kasa tantance ni a tsakanin kannaina bare har na samu wani matsayi
na musammam a wajensa, bazan yi ci gaba da jurewa ba Allah ya gani nayi Iya yina
wajen kare martaba da mutuncina na d'iya wajen ganin ban zubar da kimata na fara
furta mashi kalmar so ba, duk wani alama da zan mishi na ma shi ya kasa ganewa, ya
zan yi Zainabu ki bani shawara zuciyata zata tarwatse ki taimakamin plsss zeee."ta
karashe maganar tare da kama hannun Zainabu ta kamkame cikin nata da karfi. Cike da
tausayawa Zainabu ta ce "Na fahimci halin da kike ciki kawata domin nima na taba
tsintar kaina a irin wannan halin da kika shiga, dole zamu sake salo tunda munyi
mashi ta baya bai fahimta ba, ya zama dole ya san da zamanki don baza mu tsaya
kallon ruwa kwad'o ya man kafa ba." Nan suka shiga tsara next plan din su, wanda
zasu fara aiwatarwa a ranar ba sai gobe ba.


********

Lokacin da Peter ya koma gida, Mom na main parlour, hakan yasa bai nemi Miss Joy ba
bare ya samu ya bata sakon ta, har dare basu samu haduwa ba, Mom ta kasa ta tsare
kamar ta fahimci tana aikata wani abu. Wajejen karfe taran dare ta kasa jurewa,
dabara ne ya fado mata , da sauri ta dauki telephone din dakinta takira kitchen ta
bada umarnin a kawo mata juice daki, babu jimawa daya daga cikin ma'aikatan gidan
ta yi knocking, umarnin shigowa ta bata, bayan ta ajiye mata juice din zata wuce
Joy ta kira ta, juyowa yayi cike da ladabi ta tsaya, ta ce mata, tana son ta bin
ta kofar baya na kitchen ta je wajen Peter ta karbar mata sako,idan ta karbo ta
boye sosai yadda Mom ba za ta gani ba ta hado da bottle water ta kawo mata.

Haka ko aka yi, babu bata lokaci, maid din ta kawo mata, amsa ta yi ta mata godiya,
sai da ta maida kofar ta saka lock saboda tsaro, sannan ta koma ta zauna ta shi ga
warware pepen cikin wani irin yanayin mai wuyar fassaruwa, idanunta da hankali ta
kacokam na kan shi pepan Har ta gama warwarewa. Wani irin yankewa gabanta yayi ya
fadi lokacin da idanunta ya saka akan wani unique handwriting mai shegen kyau da
kayatarwa, a fili ta furta abinda ke rubuce a jikin pepan THANK YOU. Sake kure
rubutun tayi da idanu har zuwa lokacin gabanta bai daina faduwa ba, zuciyarta ta ne
ya bata ba rubutun Fatima bane, to amma kuma rubutun yayi kama dana Fatima, sai
dai yafi na Fatima kyau da kayatuwa, to idan ba rubutun Fatima bane na wanenen?
AL'AMEEN, zuciyar ta ya bata amsa, take wani irin tsoro had'i da firgici ya ziyarce
ta, zaro kyawawan idanunta tayi tare da sakin pepen ya fadi kasa.

A dai dai wannan lokacin Al'ameen ya fito daga masallacin unguwarsu, dawowar shi
kenan bayan ya mayar da keke ya tsaya yin sallah, yana isowa kofar gida ya tuna da
letter Joy, dakatawa yayi a kofar gida kasancewar a kwai wutar NEPA ko Ina na
wadace da haske, yasa ya lalubi dakalin dake Jikin gidan su Amira ya zauna tare da
zaro latter a aljihu. A hankali ya warware linkin da aka yiwa pepen, shina kamar
yadda ya faru da joy haka ya faru da shi ras ras! Gaban shi ya fadi,lokacin da
idanun shi su ka sauka akan wani dan rubutu da kwata kwata bai wuce layi goma ba,
babu abin da yafi daukar hankalin shi irin drowning din hearts din dake Kasan
rubutun, samun kanshi yayi da kasa dauke idanun shi akan hearts din. Bai san Iya
adadin lokacin daya dauka a haka ba, sai jin sallama yayi a gefen shi, firgigit
yayi tare da saurin kallon side din da ya jiyo sallamar, Amira ce sanye da dogon
hijabinta daya sha guga har kasa, tana tashin kamshi kamar wacce tayi wanka da
turare, idanun su na sarke wa tayi kasa da kanta teke duk wani jarumta da karsashin
ta ya tafi, jikinta ya d'an fara rawa.

Kallon ta ya yi, ganin tayi shiru ya ce "Aysha ya akayi." (Kanwarta dake binta)
wani bakin ciki ne ya ziyarceta take ta dake , cikin dan rawar murya ta ce "Amira
ce ba Aysha ba ce." Ya ce "Ooh sorry Amiran Ummi ko?" Dan murmushi tayi cike da
farin ciki, ya sake cewa " ya akayi ne?." Dan Jim ta yi kafin cikin dan. jin
nauyin tsareta da yayi da idanu, ta kara yin k'asa da kanta ta ce" Yaya Ameen dan
Allah dama nace idan babu damuwa zan kawo pass questions na waec and neco ka koya
min saboda muna daf da fara exam kuma

7 / 23