JOY by Aysha Nalado

Author :  Aysha Nalado Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 23

3K to 6K   out of 68.8K words

sukayi cikin ido da sauri ya sauke kan shi ƙasa, a sanyaye
tace "Meke damunka." Bai yi mamaki ba don yasan yadda Ummi tasan shi ciki da bai
duk yadda taga sauyi a tare da shi sai ta gane.

Ba tare da ya dago kanshi ba ya ce "Ba koma Ummi jiya da zazzabin mura na kwana da
ciwon kai amma Alhamdulillah zuwa yanzu ya sauka na ji sauki dan nasha maganin tun
cikin daren." Cikin da nazarin yanayin shi ta ce "Ka tabbata." Ya gyada kai tare
da ce wa "Eh Ummi." Ta ce "Allah ya kara sauki." Ya amsa da "Amin Ummi." "Kazo ka
juye ruwa kayi wanka zaka ji karfin jikinka sai ka sha kunu ka kara shan maganin."
"Toh Ummi."ya ce tare da juyawa ya nufi inda botikin wanka yake ranshi duk a ɓace.


*********

Suna fitowa Fatima riko hannunta tare da maka mata harara cikin harshen nasara
Wanda shine yaren da Joy ta fi iyawa ta ce "why Bestie me yasa kike son saka kanki
cikin damuwa ne sabo da ni." Kallonta Joy tayi ta sakar mata murmushi Wanda har sai
da dimple dinta ya loza, cikin jin haushi Fatima ta ce "OK dariya ma na bakin ko."
Fari ta mata da idanu ba tare da ta amsa ba hakan ya ƙara hassala Fatima, take ta
hade rai kamar bata taɓa dariya ba sake hannun Joy tayi ta kama hanya zata wuce ta
barta, ganin haka yasa Joy saurin shan gabanta rike kunnayenta tayi cikin
marairaice fuska ta ce "sorry my Teetee." Jin sunan da ta kira ne yasa Fatima
kwashewa da dariya tare da kai mata dundun wasa, itama dariyar ta kwashe da shi,
tana kaucema dundun Fatima, sai da suka natsa, Fatima ta ce "kin san dai mun
makara, sai ki shirya amsan punishment." Ba tare da wani damuwa ba ta ce "Ai na
shirya." Fatima ta ce "OK I see." Da haka suka kama hanyar school hannunsu rike
dana juna suna fira suna kwasar dariya cike da nishadi hankali kwance, duk da ita
Joy tsoron al'ameen bawai ya gama sakin ta bane, da ka gansu zaka hango yadda suke
tsananin kaunar juna.

Kamar yadda suka tsammata kuwa sun tarar ana kama late comer a bakin get ana musu
bulala, sosai Fatima taji babu dadi a ranta dama abin sa take gujewa Joy kenan,
amma ta lura ita Joy din babu alamar damuwa ko nadama a fuskarta.

Koda suka Isa class har teachern da zai dauke su first period ya shiga class
kasancewar sa ba mai tsauri ba yasa excuse kawai suka dauka ya basu izini suka
shiga ciki.
Suna shiga idanun Joy ya sauka akan na David daya zubo musu ido yana kallo yana
gyada kai, harara ta maka mai tare da dauke kai daga kallon shi, sit din su suka
nufa Wanda yake a layin gaba suka zauna su biyu, dama bibbiyu ake zama a kowane
sit.

Haka sukai ta daukan karatu cike da himma da kwazo don dukan su ba baya ba wajen
kokari, wannan malamin ya shiga wannan ya fita har har zuwa break time, Joy ta
fito musu da su chocolate da biscuit din da ta zuba a jaka suka zauna a class suna
ci suna hiran karatu, sai jin tsayuwar mutum sukayi a kansu, kusan tare suka dago
suka kalle shi, harara ya fara watsama Fatima wanda itama bata yi kasa a gwuiwa ba
wajen ramawa kafin cikin wani yare wanda Fatima bata ji ya fara ce wa "dama nasan
gidan su wannan matsiyaciyar zakije kuma ki rubuta ki ajiye daga wannan karan kinyi
na farko kinyi na karshe don sai na gayawa papa halin da kike ciki a makarantar nan
kin san kuma abin da zai biyo baya, wannan ai zubar mana da Kimar family kike yi."
A harzuke ta ce da harshen turanci don shi tayi ji fiye da yaren su da David ke
mata magana da shi "David ka fita harkata babu ruwanka dani kayi harkan ka nayi
nawa a cikin makarantar nan." Ya ce "bazan fita a harkar taki ba, kiyi abin da
zakiyi." Kwafa tayi ta ce "to ka ci gaba da shiga zan yi maganin ka." "Ni dai ne
zan yi maganin ki, wawiya kawai Mara kishin kanta da addininta." Yana gama fadin
haka ya juya ya fice daga class din, joy taji zafin zagin ta da yayi hakan yasa a
zafafe ta mike zata bishi don ta rama, da sauri Fatima ta rikota tana bata hakuri,
batasan takamaimai abin da suka faɗa ba tunda da yare ne amma ta fahimci a kanta ne
suke wannan cacar bakin, kamar yadda ta bangarenta Joy ke fuskantar barazana da
kiyayya a wajen yayanta, haka take fuskantar kiyayya da kyamata daga wajen duk wani
ahlin Joy uwa uba iyayenta.

David dan uwan Joy ne cousin dinta ne, mahaifiyar shi kanwar papa ne uwa daya uba
daya.

Rarrashinta Fatima ta shiga yi tana bata hakuri, da kyar ta hakura ta koma ta zauna
don Joy akwai zafin zuciya idan ta fusata, basu fita ko ina ba har aka dawo break
aka ci gaba da lesson, har kuma akayi closing bata daina hararan David tana kwafa
ba, Fatima dai sai aikin rarrashi take kasancewar tasan halin kayarta.

Tare suka fito daga cikin school din kamar yadda suka saba hannun sakale da juna,
sarai Joy taga driventa peter yazo daukarta amma ta yi fuska ko kallon inda yake
bata yi ba saboda tana so ta jera da Fatima ,sau da yawa takance Fatima tazo su
Shiga mota su sauke ta amsa ƙememe take ƙi saboda gargadin ummi.

Peter bai damu ba don Inda sabo ya saba da hakan, rana daddaya ne idan yazo daukan
ta take yarda ta bishi.

A hanyar su sai da Fatima ta san yadda ta yi, ta mantar da Joy ɓacin ran da take
ciki na David, sai gata tana dariya har da kyakyatawa.

Wani me sai da yalo ne ya zo wucewa yana talla a bairo, har sun gifta shi Fatima
ta ce "laaa Joy bari na sai ma yayana yalo." Kafin Joy ta amsata har ta juya ta isa
gare shi, hamsin din da ummi ta bata ta mika mishi ya bata na hamsin.

Dawowa Inda Joy take tsaye tana jiranta tayi cike da farin ciki ta ce "nasan yayana
zaiji dadi sosai don yana son yalo kamar me." Taɓe baki Joy tayi tare da cewa
"Wanna yayan naki dabe dariya bashi da fara'a ko dan murmushi ni ban taba gani yayi
ba kullum yayita yiwa mutane muzurai, shine zaiyi wani farin ciki don kin sai
mai yalo, ni fa shi yasa yaya ko kani basa burgeni." Wani kallo Fatima ta mata
kafin ta ce "waya gaya miki yayana baya dariya, waya gaya yayana baya fara'a ina
jin duk unguwar nan babu wanda ya kai yayana iya murmushi." Joy ta ce "Au haka ne
fa."ta fadi maganar cikin sigar tsokana, fon ita bata yarda ba gani tke yi fatina
wasa take yi, Fatima ta ce "koma me zaki ce kice, kuma da kike cewa yaya ko ƙani
bass burgeki wlh don bakin hadu da irin yayana bane, ganin kamar fa da gaske take
yi, yasa Joy cewa "wai da gaake kike yi ko wasa." murmushi Fatima ta yi tana
girgiza kai, nan kuma ta shiga ba Joy labarin yayanta yadda yake kula da ita yadda
yake sonta da yadda baya kaunar bacin ranta, tun Joy na jinta sama sama har kuma
labarin ya fara shigar ta, nutsuwa tayi ya maida dukkan hankalinta tana sauraren
Fatima a ranta tana mamakin abubuwan da fatima tace al'ameen nayi, ji tayi a ranta
koda so ɗaya ne zata so taga murmushinsa,a haka suka iso kwanan gidan su Fatima
Wanda sai an wuce shi kafin a isa na su joy, ji tayi bata son su ru don bata gaji
da jin labarin ba, har kofar gida ta raka fatima sannan suka yi sallama ta kama
hanyar nasu gidan.

Tana tafe tana murmushi ita kaɗai tana tuna labarin yayan Fatima, da haka ta ƙarasa
nasu katafaren gidan, knocking tayi, jiki na bari me gari ya bude mata yana mata
sannu da dawowa, bata da wulakanci da girman kai ko kadan ita dai barta da tabara
da shagwaba, hakan yasa ta sakar mai murmushi tana amsawa ta sa kai ta nufi
entrance din gidan.

Fuskarta cike da murmushi ta turo ƙofar falon ta shiga, a bakin ƙofa ta taka birki
murmushin fuskarta na ɓacewa, lokacin da idanunta ya sauka akan mom da David da ke
zaune a falo, duk ido suka zubo mata, shaf ta manta da wani David da alwashin daya
dauka yau a kanta, ganin iron kallon da mom ke jifanta da shi yasa taji gabanta ya
fadi, a ranta ta ce shike nan na Shiga uku David ya gama dani......



Me bukatar Shiva group ya tuntubeni ta wannan lambar
09116099486
[12/29, 2:20 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

*BY*

*AYSHA NALADO*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

*LITTAFI NA ƊAYA*

*PAGE 3*


Fuskarta cike murmushi ta tura ƙofar falon ta shiga, ta na kwalama Mom kira, a
bakin ƙofa ta taka birki murmushin fuskarta na ɓacewa, lokacin da idanunta ya
sauka akan Mom da David da ke zaune a falo, duk ido suka zubo mata, shaf ta manta
da wani David da alwashin daya dauka yau a kanta, ganin irin kallon da Mom ke
jifanta da shi yasa taji gabanta ya fadi, a ranta ta ce shike nan na Shiga uku
David ya gama dani.

Sai da ta hadiyi miyau mukut! Kafin ta kirkiro murmushin dole ta sakar musu , cike
da fargaba ta nufi Mom don ta rungumeta kamar yadda Mom d'in ta sabar mata,
hankad'e ta Mom tayi saura kad'an ta fad'i Allah ya taimaketa ta dafa kujera, cikin
tsananin bacin rai ta ce "kar ki kuskura ki ta'ba ni Joy!!!" Ta karashe maganar a
kausashe.

A razane ta sauke manyan idanunta da lokaci d'aya suka tara kwalla a fuskar Mom,
cikin karaji Mom taci gaba da ce wa "kije na yafe musu ke,tunda sun fini a ajenki
kije kqai tunda ke kince baza kiji magana ba."daga haka ta mike a fusace ta bar
falon ba tare da kara kallon gefen da Joy take ba.

Lumshe manyan idanunta zuciyarta na wani irin tsinkewa, hakan da tayi ne yaba
hawayen dake kwance a idanunta daman zubawo, minti biyu ta dauka a haka kafin ta
waresu akan David dake kallonta yana sakin murmushin mugunta.

Gaban shi ne ya fad'i ganin yadda lokacin d'aya manyan fararen idanunta suka rine
zuwa launin jaa, take yaji wani shakkarta da tsoronta ya kama shi duk da kuwa ya
girme mata don ya bata kusan shekara daya a haihuwa.

Bai gama fita daga wannan yanayin ba ya tsinkayi muryarta a kunnayenshi, a
kausashe ta ce "David!!! Burin ka ya cika yau ka hadani da iyayena ko, nasan kaji
dadi ranka yayi maka fari ko? To ka rubuta ka ajiye na rantse da wanda ya busa min
rai da numfashi sai kayi nadamar wannan abin da ka aikata." Mikewa tayi ta kama
hanyar hawa upstairs.

Ji yayi duk ya muzanta ida ta wuce bai mayar mata da martani ba zata ga kamar ya
tsorata da furucinta ne haka yasa ya danne zuciyar shi tare da ce wa "Joy James."
Da karfi, dakatawa tayi tare da juyowa suka hada idanu, takowa yayi ya iso gabanta
ya tsaya, kamar zai fadi wani magana, sai kawai ya barke da wani mahaukacin dariya
mai ban haushi, wani irin yawun takaici Joy ke hadiya a jejjere, ganin kuka na
shirin kwace mata yasa ta juya a guje ta karkare hayewa saman bata zame ko ina ba
sai dakinta kan gado ta fada tare da fashewa da kuka da iya karfinta.

Mom koda ta shiga dakin ta kasa zama tayi safa da marwa kawai ta shiga yi ta kai
gwouro ta kai mari, hankalinta a matukar tashe, girgiza kai tayi a bayyane cikin
irin yaren da David yama Joy magana d'azu a school ta shiga ce wa " meke shirin
faruwa da ni ne ni Alice, kardai asirin da na rufe tsayin shekaru goma sha biyar ke
shirin tonuwa, tabbas ya kusa tonuwa." Bango ta kai ma duka kafin kamar zararriya
ta ce "Ina!!! Ba zan taba bari hakan ya faru ba indai na haifu cikin pastor Samuel
da Mrs Deborah." Da sauri ta rarumi wayarta ta danna ma wani lamba kira, ringing
wayar keyi amma ba'a daga sake kira tayi still ba,a daga ba jife tayi da wayar a
kan gado tare da zama da'bas tana tafa hannaye, can wayar ta dake kan gado daga
bayanta ya fara ringing da sauri ta raruma don duk a tunanin wanda take ne ya biyo
bayan kiran, ganin sunan me kiran ne yasa gabanta yankewa ya fadi, *Dr Hassan* ta
ambaci sunan a bayyane tana zare ido lallai bata ga ta zama ba wai an saci san
barawo.

Tafi awa d'aya tana kuka kamar ranta zai fita, gaba daya ta hargitsa suman kanta ko
takalmin school bata jire ba jakar ma jifa da shi tayi da shi can gurin kofar
toilet, jinta take yi wani iri ji takeyi kamar ta aikata baban zunubi tunda take da
Mom bata taba koda dungurinta bane, bata taba fushi mai tsanani da ita haka ba duk
kuwa iya girman laifin da zata mata, amma yau ita ce Mom ke hankadewa lallai ta san
ba karamin fushi Mom ta yi da ita ba, bata ga laifin Mom ba domin tun ba yau ba ta
riga ta san yadda Mom ta kasance mace mai kishin addininta, tana tsananin kyamar
addinin musulci, bata shan inuwa daya da musulmi, tana kyamarsu kamar me, ji tayi
baza ta iya jurar fushin Mom, hakan yasa ta mike dakyar ta nufi dakinta.



*******


KANO STATE


*Dr Hassan special hospital Amenity word room number 5*

Wani farin dattijo ne me kimanin shekaru 65 a duniya ke kishingide akan gadon
marasa lafiyar dake madaidaicin haddadden dakin wanda kwata kwata baiyi kama da
dakin asibiti ba, hannun shi sakale da karin ruwa, saman roofing dakin fuskar shi
ke fuskanta idanunshi a lumshe, idan ba ka kula da yadda yake motsa bakin shi a
hankali da kuma yadda yake danna caunter dake sakale a daya hannun shi da babu
Karin ruwa ba zaka dauka barci ya ke yi.

Daga gaban gadon wata dattijuwar mata ce zaune a kan daya daga cikin kujeru biyu
dake dakin, a kalla zata kai shekaru hamshin da haihuwa amma tsabar hutu jin dadi
jin iya kula da kai da yadda naira suka zauna zaka dauka batafi 38 to 40 ba, kallon
dattijon mutumin nan take yi fuskarta cike da matsanancin damuwa, hannunta plate ne
mai dauke da tuwon almaka da miyar alayyahu da nama, kasa ta yi da muryar a karo
na barkatai cikin sanyi ta ce "Alhaji ka tashi kaci abincin mana gashi na zuba
maka tun dazu yana hucewa." Bude lumsassun idanunahi yayi kafin a hankali ya ce
"bana jin yunwa bazan ci ba." Shiru ta yi tana ci gaba da kallon shi tana tuna
rabon shi da abinci tunda asuba da Dr yasa shi yasha tea lokacin da za'a daura
mishi drip, kallon agogon dake manne a bangon dakin tayi karfe biyar harda mintuna
biyu, ajiyar zuciya ta sauke, cikin son jaraba sa'arta ta sake ce wa "alhaji kayi
hakuri ka tashi ka ci abincin nan, lafiya bazai samu ba idan har haka cin abinci."
Wannan karan bai bude idanunnashi daya mayar ya lumshe ba kuma bai amsa ta ba, sai
ci gaba da yayi da motsa bakin shi alamar yana ci gaba da lazumin shi, ganin haka
yasa ta cigaba da yi mai magiya, jin ta dame shi yasa ya bude idanu tare da daka
mata tsawa "keee! Nace bazan ci ba dole ne wai." Ta ke alhini da tausayin dake kan
fuskarta ya bace bat lokaci daya bacin rai da bakin ciki suka maye gurbin su,
ranta ya kai kololuwar baci , a hassale ta ce "wai har sai yaushe ne zaka cire
wannan damuwar daga ranka? sai yaushe ne zaka dangana ka fawwalawa Allah
lamuranka?, yau fa kimanin shekara goma sha biyar kenan, sai yaushe ne, iyeee
alhaji na ce wai yaushe ne?" Ta karshe maganar cikin karaji tare da fashewa da
kuka.

Bude lumsassun idanun shi yayi ya kalleta kika take yi bil hakki, guntun murmushin
karfin hali ya saki, cikin muryar shi ta marasa lafiya ya ce " ya isa haka
Lubabatu kina son kisan sai yaushe ne ko?" Da sauri ta gyada kai tana sharar
kwallah, idanun shi ya saka cikin nata kafin yace a kausashe "sai ranar da asirin
wad'anda suka kashe ta ita da abinda ta haifa Tonu...."


Yau ba yawa kuma ba editing🙏


Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar
09116099486
[12/29, 2:20 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

*BY*

*AYSHA NALADO*


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

*LITTAFI NA ƊAYA*

*PAGE 4*


Mom na kallo har kiran Dr Hassan ya katse bata iya d'agawa, gaba d'aya a tsorace ta
ke, banda zufa babu abin da ke tsatsafo mata, ajiye wayar ta yi a gefen bed ta
rafka tagumi da hannu bibbiyu, wayarta ce ta sake d'aukar ringing kallon wayar ta
yi bata d'auka ba don duk daukarta Dr Hassan ne again sai dai ganin me kira yasa ta
zabura ta mi'ke, hannu na rawa ta yi received, tun kafin ta kai ga cewa komai ta ji
ya kece da wata irin mahaukaciyar dariya wanda sai da ta tsorata, kusan minti uku
ya kwashe sai da yayi mai isar sa kafin lokaci d'aya gimtse fuska.
Jin yayi shiru yasa Mom cikin rawar baki ta shiga kokarin yi ma shi bayani, wani
tsawa ya daka mata Wanda saura kadan ta saki wayar, cikin amon sautinsa mara dad'in
ji ya fara magana cikin irin yaren su ba ibo "kin yi sake! Kin yi sake! Na ce kin
yi sa ke Alice, tabbas abin da kike 'boyewa tsayin shekaru sha biyar zai bayyana
matukar baki raba alakar *jini da jini* ba." Kan Mom ya kulle take ta 'kara tsorata
jin ya ce asirin data binne tsayin shekaru zai bayyana, bata gane me yake nufi da
Kalmar *jini da jini* ba, sanin hakan da yayi ne yasa ya ce "kiyi gaggawan raba Joy
da ra'bar wadan nan ahlin musulman idan kuma ba haka ba." Sai kawai ya kara kecewa
da dariya kit ya kashe wayar ba tare daya mata cikakken baya ni ba ya barta tana
zare ido.

Hakan yasa da sauri ta sake dialing number shi, daga wa yayi bai bata damar yin
magana ya ce, "babu taimakon da zan miki idan har baki rabata da wadannan ahlil
ba, dama na gaya miki tun farko ai karkiyi sake, idan kuma kika yi sake tabbas jini
da jini ba karya bane." Daga haka ya sake kashe wayar bayan ya kwashe da dariya
kamar mahaukaci.

lallai bata ga ta zama ba, dole ta yi duk yadda zata yi domin taraba Joy da wadan
nan tsinannun talakawan musulman, tana son jin cikakken bayani tana son sanin me
Kalmar jini da jini yake nufi dan baza ta yi sake wani dan kankanin abu ya bata
mata aikinta na

2 / 23