Author : Aysha Nalado Category : African Stories & Novels
a gareta
Allah yana nan kuma bazai ta6a bari su wulakanta ba, a karshe haka Ummi ta kamo
hanya gida, babu nasara sai tarin bakin ciki da ta k'unso tare da tayar mata da
tsohon mikin da ta dad'e da lullu6eshi a can karkashin zuciyarta.
Su hudu ne y'an uwan marigayi mijinta Al-husssain. Mata biyu maza uku Yaya Tanimu
wanda suke kira da yaya babba kasancewar shine babba a cikin su, sai Hassan sai
hussain da yake mijinta, sai mata biyu wadanda ke gidajen mazajensu kowacce ta
tara nata iyalin.
Kaddarace ta jeho ta cikin ahlinsu ba tare da ta san sanda ta giffa a gare ta ba,
ta yi gwagwarmaya sosai a lokacin duk da karancin shekarunta, ta kowane bangare ta
fuskanci kalubale rayuwa, duk don kasancewarta tsintacciya mara galihu, Mara gaba
Mara baya wacce bata san inda ta dosa ba.
Tanimu mutuncinta yake nema ido rufe yake so ya keta mata haddi tun kafin su yi
aure da marigayi, ta dauka aurenta da dan uwansa zai sa, ya rabu da ita , sai dai
hakan babu abinda ya rage a kan irin bibiyar da yake yi wa mutuncinta saboda rashin
tsoron Allah har da igiyar aurenta, igiyar aurenma na dan uwansa, sai dai har
mijinta ya kwanta dama bai samu galaba akanta ba hakan ya haifar mata da mummuna
tsana da tsamgwama daga gareshi, zata iya cewa shine ya fara hura wutar kiyayya
tsakanin sauran kannensa da marigayi wanda suka dauki karan tsana suka dora mata
acewarsu itace silar mutuwar dan uwansu, yayinda kiri-kiri suka sheganta mata
y'ay'a, y'ay'an da bata san daga ina suke ba, kawai ta bud'e ido ne ta ganta a tare
da su.
Ta dauka zuwa yanzu Tanimu ya saduda, tunda shekaru sunja, bata ta6a tunani ko
hasashen cewa zai kuma tayar da wannan maganar ba, sai gashi yana sake baiyana mata
har yau yana nan da muradin tarayya da ita, wa'iyazubilla.
Ta yi kuka ta yi bakin cikin wannan lamarin don sai da ta kwashe kwana uku tana
zazzabi a tsaye saboda jimamin wannan lamari, bata cewa Al'ameen komai a kan
lamarin, haka shima bai ce mata ba, sai dai shirun shi ba yana nufin bai damu bane,
daurewa kawai ya ke, kullum suna tare da Aliyu shine ya ke don karfafa masa gwiwa
da bashi baki, a bangare daya kuma suna nan suna wani shiri shi da Dr Abdul wanda
Al'ameen din bai san da shi ba, don tun ranar da Aliyun ya mishi maganar shi suka
rabu baran-baran bai kuma ambaton sunan shi ba, wannan kuma umarnin Dr din ne.
Da misalin karfe biyar na yamma yaro ya yi sallama, tsakar gidan Ummi ya sanar da
ita wai wani mutum na sallama da ita a waje, a lokacin ita kadai ce a gidan Fatima
na islamiyya Al'ameen kuma na gurin sana'arsa, cike da madaukakin mamaki, ta ce
"Balkisu aka ce ka kira ko dai Fatima." Yaron ya tabbatar mata da Balkisu ake
kira, har ta ce ya je ya ce wanene, sai kuma ta ce ya barshi, ya ce wa mutumin ya
shigo daure ya kirata tana zuwa, ta dade zaune tana sake-sake , kamar ta fasa fitar
don hankalinta bai kwanta ba sai dai ta dake ta mike ta sanya hijab dinta ta
fitan........
Oum ummeetarh
09116099486
[12/29, 2:50 PM] AyshaNalado: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*PAGE 43*
Mikiya Writers Association
*Masu facebook ku yi following wannan account Ιin domin samun damar cin giveaway
Ιin da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa*
https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL
βA'uzu billahi minashshaidanir rajimβ Ummi ta furta lokacin da ta yi arba da baβkar
fuskar Tanimu a matsayin wanda ke sallama da ita. Dakatawa ta yi daga bakin k'ofa
ta kasa k'arasowa cikin zauren, sai bin shi take yi da wani irin mugun kallo, mai
cike da tsana tsaba. Zuciyarta cike take fal da tsoro, amma a zahiri sam babu
alamar hakan a kan fuskarta. Shu'umar murmushinsa ya saki yana jan dogon gemunsa
yana binta da wani kallo, irin ta gogaggun y'an duniya tare da ce mata "K'araso
mana Balkisu mai gadon zinare, Alheri ne ke tafe sa ni, na canza shawara domin
daren jiya na kasa barci kyakkyawar surarki ce ta dinga yi mini gizo zuciyata ta
sake kwadaituwa da son tarawa da ke, yayinda gangar jikina ke sake fallasa mini
muradinta na son yin nitso a kogon ni'imarki, shine
na ji a raina gara na zo mu sasanta, idan hagu ta ki sai a koma dama ko na haka ba
yar shilata." Ya karashe maganar yana fitar da wata sautin murmushi mai cike da
zallar iskanci.
Had'e girar sama da ta k'asa ta yi babu alamaun fara'a ko sassaci ko miskala
zarratin a fuskarta, ta ce "Ta Allah ba taka ba mugu fasiki dan Akuya, da yardar
Allah baza ka ta6a cin galaba a kaina ba, baza ka ta6a cimma mummunar nufinka a
kaina ba har lokacina ya cika na bi bayan mijina, kuma ka fita kabar mini gidana
bana bukatar taimakon daga wajenka ko wani naka, Allah da na rike zai kawo wanda
zai tallafa mana." Takowa ya shiga yi gareta yana fadin "Haba mana balkisu, ya
zaki yi mini haka, wannan harkar fa cudanni in cudeka ne, kan ki kawai zaki mallaka
min na rana d'aya, ni kuma na jiyar take dad'in da babu wani namijin da ya ta6a
jiyar take irinsa a duniya, tun daga kan kwaratanki har zuwa kan mataccen mjinki,
iye yan mata kar ki yi mani rowa mana, nasan ai kema kina da muradi." Ya karashe
maganar yana kokarin kai hannusa jikinta.
Da sauri ta ja baya hankali tashe take fad'in "Tanimu kar ka ta6a ni, ka fitar mini
daga gida ni ba fasika bace irinka." Dariya ya kece da shi, ya ce "to muje cikin
gidan mana ai nasan babu kowa daga ni sai ke sai Allah, kinga sai na cika tsohon
muradina a kan ki ko ta karfi ne." Yana maganar yana dariya.
Jin hakan ya matukar daga mata hankali, take ta sake k'amk'ame hijabinta tana sake
ja da baya, yayinda shi kuma ya ci gaba da biyota har suka shiga cikin gidan.
Zuciyarta ta dinga bata shawarwari shin ta juya ta runtuma da gudu ne zuwa dakinta
ta datse kofa ko kuma ta nemi makami ta illata shi ko kuma dai ihu zata yi mashi.
Kamar ya shiga zuciyarta ya ga abinda take kitsawa sai ji ta yi yana cewa " Kina
tunanin yi mini ihu ko? To bismillah, idan kika yi mini ihu na rantse miki da Allah
k'aik'ayi ne zai koma kan mashek'iya don sai kin gwammace mutuwa da irin Sharrin
da zan kulla miki."
"Mugu azzalumi dan Akuya Allah ya fika." Murmushi ya yi ya ja gemunsa ya ce
"Balkisu taurin kai! Ni wallahi ko a yanzu kika bani kan ki na minti ashirin na
miki Alkawarin a yau zan je na nemawa dan ki aure kuma na tsaya masa babu wanda zai
san shege ne balle ayi masa gori, ba sai munje da nisa ba a tsakar gidan nan ma sai
mu yi mu ta shi don ni ba bakon zafi bane." Ya fad'a yana murmushi tare da bin
tsakar gidan da kallo.
Wannan kalle kallen daya tafi ne ya bata damar zarar wuka a jikin rufin din kitchen
Inda suke ajiyewa, cikin zafin nama ta kai mishi yanka cike da shammata, da sauri
ya saka hannu sa ya tare yankan hakan yaba wukar damar yankarsa a tafin hannu mugun
yanka kuwa, take jini ya balle, razananniyar kara ya saki tare da rike hannun,
tuni idanunsa sun kada sunyi jajur, rigar jikinsa tuni jini ya bata shi kaca-kaca.
Ganin yadda mini ke zirara kamar an yanka karamin dabba yasa jikin Ummi ya fara
karkarwa take ta sake wukar dake hannunta, don ta tsorata ainun, tunda ta taso ita
mai taushin zuciya ce ko kiyashi bata kashewa da gangan balle ace wai yau ita ce ta
yanki mutum da wuka haka jina na zuba, hakan ya tayar Maya da hankalin ainun.
Bata yi aune ba taji ya shaki wuyar hijabinta tare da hed'e ta da bango kafin ya
shiga wanka mata mari a fuskarta, karfi ya saka ya yage hijabinta jikinta ya damk'i
wuyarta ya shake, a zuciye cikin zaro jajayen idanunsa yake cewa " Ni zaki jiwa
ciwo! Ni za ki yi wa lahani! Wato don kinga ina bin ki ina da lalla6a ki ko, to
bari na turmushe ki ta karfi da ya ji muga ta tsiya." Yana maganar ne cikin fitar
hayyaci da tsananin fusata, yayinda ya shiga kokarin keta dogon rigar atamfar dake
kijinta.
Babu zato wani irin wawan naushi ya sauka a gefe fuskasa wanda sai da jini ya yi
tsartuwa daga bakinsa ya famtsama a fuskar Ummi, babu shiri ya sake ta tare da
tallafe gefen fuskarsa ya furzar da miyan bakinsa mai gauraye da jini, saiga hakora
uku turame sun biyo.
Kafin ya gama tantance meya faru, Al'ameen ya yi wa wuyarsa wata irin muguwar
shaka, idanunsa a waje cikin tsananin fusata ya shiga dukansa ba tare da ya tsaya
tantance wanene ba.
Cikin yan dak'ikai ya hada mishi mi shi jini da majina, nan ya zube kasa warwas
kamar gawar sababi, bai bar shi ba ya zauna a ruwan cikinsa ya ci gaba da duka yana
fadin "Mahaifiyata, Uwata ita za ka yi wa fyad'e kai waye, wallahi wallahi, sai na
kashe ka, ni Muhammadul-Ameen yau sai an kashe ka."
Jin shirun Al'ameen ya yi yawa yasa Aliyu dake jiransa a kofar gidan ya miko masa
sak'o, ya gaza hakuri ya kutso kai cikin gidan, tun daga Zaure ya fara jiyo
sambatun Ameen hakan yasa ya k'arasa cikin gidan a guje, abinda ya tarar ne ya saka
shi zare ido tare da runtumawa da gudu ya shiga kokarin bambare hannun Al'ameen a
wuyar mutumin da yake duka kamar Allah ya aiko shiz sun yi kokawa sosai kafin ya
samu nasarar daga shi daga kan mutumin.
Jijjigashi Aliyu ya shiga yi , yana fad'in" Ameen menene haka ka dawo cikin
hayyacin mana." Sam Al'ameen ba ya jinsa, sai yunkurin kwacewa ya ke daga rikon da
Aliyu ya yi masa yana kokarin sake kaiwa Yaya babba cafka, ganin haka yasa Yaya
babba mikewa a daddafe ya fece daga gidan ba tare da ya tsaya ko neman takalmansa
ba.
"Ka sake ni Aliyu, wallahi sai na kashe shi , bazan barshi ba, sai na raba shi da
numfashin sa." A tsawace Aliyu yace "Ka nutsu Ameen, ka kalli halin da Ummi ke
ciki."
Jin haka yasa shi saurin juyawa gareta, a kwance take sharaf a kasa kamar bata
numfashi, da wani irin sauri ya karasa gareta ya dagota yana jijjigata tare da
kiran sunanta, da kyar ta bud'e idanunta dake lumshewa ta kalle shi a kan la66anta
ta furta "Ka kula da Fatima Ameen na bar maka ita amana nasan za ka iya.... Bata
karkareba idanunta suka lumshe numfashita ya dauke cak! " Ummi!!!!!!!! Ya ambata da
Iya dukkan karar muryarsa..............
Kunfa rage comment mutanen Joyπ¬
Oum ummeertah
09116099486
[12/29, 2:51 PM] AyshaNalado: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*PAGE 44*
Mikiya Writer's Association
Cike da tsananin tashin hankali Al'ameen ke safa da marwa a bakin d'akin bada
agajin gaggawa na karamar asibitin dake unguwarsu, in da suka yi gaggawar kai Ummi
bayan sun fahimci suma ta yi ba mutuwa ba, tunda suka kai ta kimanin awa hudu a
tsaye yake kamar mashi, a k'ofar d'akin sallar magriba da ishsha ne kadai ya kau
da shi daga wajen, Fatima na zaune a kan d'aya daga cikin bencinan da a ka tanada
domin zama, sai kuka take yi idanunta sun kumbura sun yi jajur, dawowarta daga
hadda ta tarar da wannan tashin hankalin ko gida bata kai ga shiga ba ta ga an fito
da Umminta a sume kamar gawa, hakan ya daga mata hankali, a guje ta kutsa kai cikin
napep din da aka sanya Ummi ta kamkameta tana kuka, tun lokacin take rusar kuka har
zuwa yanzu da ake neman karfe goman dare. Yau dai kam kasa rarrashinta Al'ameen ya
yi, Aliyu da Maman Amira wacce ta biyo su asibitin daga baya ne suke kokarin bata
baki idan suka ga kukan nata ya yi yawa.
Likita ne ya fito daga d'akin , da sauri suka yi caaa! A kan shi kowanne na jeho
mishi tambayar da ya zo bakinsa duk a game da Ummi, kallonsu ya yi cike da
tausayawa ganin yadda hankalinsu ke tashe, murmushin kwantar da hankali ya sakar
musu, ya daura da cewa "Ku yi hakuri yaran Ummi, Ummi tana lafiya, firgicine ta
shiga shine ya haifar mata da daukewar numfashi ta yi, dogon suma, yanzu dai
Alhmdllh mun bata taimakon da ya dace ta farfado tun dazu,sa dai mun yi mata
allurar barci domin kwakwalwarta ta samu hutu, zuwa safiya in dan Allah ya kai mu
zamu sallameta.
Hamdala Aliyu da Maman Amira suka shiga jerowa, Al'ameen ku wa rintse idanu ya yi
shima yana jero hamdala a zuciyarsa, wani irin farin ciki da kwanciyar hankali na
maye gurbin fargaba da tashin hankalin da ke dankare a zuciyarsa. Yayinda Fatima ta
rungume Mama ta na shessheka tun da dama cikin kuka take.
Aliyu da Ameen ne suka kwana a asibitin, Mama da Fatima kuma suka tafi gida, bayan
sun shiga sun duba Ummi, tana barci kamar yadda likita ya fada.
Bayan tafiyarsu ne Al'ameen ya samu damar baiwa Aliyu labarin abin da ya sani game
da abinda ya faru, yana ba shi labarin zuciyarsa na kara daukar zafi yana sake cin
alwashi a kan kassara rayuwar koma waye wannan mutumin, shi kan shi Aliyu ran shi
ya baci, zuciyarsa ta tashi har yaso yafi Ameen daukar zafi a kan lamarin, ko da
wasa bai ta6a kawo hakan a ransa ba, ya ciji yatsa ya fi sau shurin masaki a kan
rike Al'ameen da yayi har mutumin da ko sunan sa basu sani ba ya samu damar guduwa,
karshe Ameen ne ya koma tausarsa.
Washegari karfe goma a ka sallami Ummi, a lokacin Fatima da Amira ne ke tare da ita
don Aliyu tun wuraren bakwai ya tafi gida da zummar kimtsawa ya dawo, Al'ameen ma
ganin sun zo yasa ya tafi gida don yin wanka.
Sosai makota da abokan arziki sukai ta shigowa yi wa Ummi sannu, yinin ranar bata
samu kanta ba, kallo daya zaka san bata cikin walwala amma haka ta daure ta saki
fuskarta ta dinga amsa gaisuwar yan dubiya.
Ranar da matsanancin damuwa Al'ameen ya kwana, bai iya rintsawa ba, burinsa ya ji
daga bakin Ummi 'shin wanene wannan mutumin, domin baya jin har duniya ta nade zai
iya yafe mishi.
Washe gari da safe ko da ya je gaisheta bata ce masa komai game da batun ba, haka
ya shirya ya tafi makaranta jiki babu kwari, da yamma tare suka shigo gidan da
Aliyu ya biyosa don ya sake gaida Ummi duk da jiya ma yazo, kuma mahaifiyarsa da
matar kawunsa harma da kannensa sun zo suma a jiyan.
A falonta suka same ta zaune a kan dadduma, carbi a hannunta tana lazumi, zama suka
yi suna jiranta, itama ganin shgowarsu yasa ta yi sauri ta kai karshen lazumin,
Aliyu ne ya fara gaisheta da jiki ta amsa cike da kulawa, Al'ameen ma ya sake
gaisheta.
Daga haka duk zama suka yi jugum-jugum daga yanayin fuskokinsu ta fahimci da magana
a bakunansu, ajiyar zuciya ta sauke dama ta san ko ba jima ko ba dad'e wannan
ranar zata zo, bata gama tunanin da take yi ba ta tsunkayi muryar Al'ameen yana
cewa.
"Ummi don Allah da manzonsa ki gaya mini wanene wannan mutumin? Kallonsa ta yi sai
kuma ta yi shiru, ba tare da amsa shi ba, ganin haka yasa Aliyu kar6ewa da " Ummi
don Allah ki daure ki sanar da shi, domin yana cikin matsanancin damuwa ni shaida
ne, saboda ni amininsa ne, muna da kusancin da bazai iya boye min duk wani
damuwarsa ba, nine na ba shi shawara a kan ya zo ya tambaye ki, shi kuma ya ya
dauko ni don na taya shi rokon ki, Ummi don Allah ki fad'a masa menene hadin ki da
shi."
Ajiyar zuciya ta sauke a karo na biyu, ta ce "Dama ko baka tambayeni ba Yayan
Fatima yau ne na yi niyar sanar maka su wanene ahlin Alhussain a gare ku da nima
baki d'aya." Aliyu ya ce "Alhmdllh Ummi, Ameen ya dade yana tsumayen wannan ranar
tsayin shekaru." Ya k'arashe maganar cike da tsantsar farin ciki kamar shine Ameen
d'in. Murmushi Ummi ta yi tana sake jinjina amintar dake tsakanin Aliyu da Ameen,
kamar dai Fatima da Joy.
Fatima ce ta shigo d'akin daga hadda take, ganin yayyinta yasa fara'ar fuskarta
k'ara fad'ad'a, ta gaishesu baki d'aya a ladabce, ta wuce uwar d'aka ta ajiye
hijabinta da jakar haddarta ta fito zata wucesu, har ta kai bakin k'ofa, Ummi ta
dakatar da ita ta hanyar cewa "Fatima! Kema zo ki zauna." Bata musa ba ta dawo ta
samu guri kusa da Yayanta ta zauna, zuciyarta na tsinkewa haka kurum take jin
gabanta na fad'uwa.
Mikewa Aliyu ya yi, da nufin tafiya gida don ya basu waje, Ummi ta dakatar da shi
da cewa; Dawo ka zauna Aliyu, domin kuwa kaima d'ana ne, tamkar Al'ameen haka nake
jin ka." Bud'e baki ya yi da nufin yi mata musu, sai dai ganin yadda ta tsare gida
yasa ya kasa, sai dai bai koma ya zaunan ba kamar yadda ta umarceshi, idanunta ta
watsa mishi, irin kallon da take yi wa Al'ameen idan tana son ladaftar da shi,
babu shiru ya koma ya zauna.
Sauke kai Ummi ta yi kasa ta yi shiru duk ido suka zuba mata falon ya dauki shiru
na tsayin mintuna biyu, a hankali ta dago idanunta da suke cika taf da kwallah
cikin wani irin murya mai sanyi wacce basu ta6a junta da irin shi ba ta fara
cewa..............
Oum ummeertah
09116099486