Author : Aysha Nalado Category : African Stories & Novels
Cewar Ummi bayan sun gama gaisawa
da Fatima, jakarta ajiye a d'aki, ta amshi kudβin ta je ta siyo pure water mai
sanyi a shago ta kawo, ajiye ma shi ta yi, ta ce "Ummi bari na dubo Anty Amira."
"Yawwa Binta maza je ki, ni ma naso shiga da dazu sai ga Aliyu, amma idan na yi
isha kafin na kwanta zan dubota nima."
A zaure ta ci karo da Al'ameen, "Yayana oyoyoo." Ta fad'a tana amsar ledar
hannunsa, godiya ya mata, tare su ka shigo cikin gidan, d'akin ummi ta kai ledar ta
ajiye ta fice zuwa gidan su Amira.
Cike da d'okin ganin juna, suka yi musabaha, "Timekeeper kanawan dabo, gaskiya kano
ta kar6e ka abokina, kaga yadda ka yi wani k'ato." Cewar Al'ameen cikin sigar
zaulaya, dariya Aliyu ya yi ya ce "Na gode da zagi, kana ga duk na kanjame sai
kashin wuya kamar kai, ka ce wani na yi kato." "Allah ba sharri na ka yi dan gwa6i,
me ye sirrin." "Kai dai ka sani ni babu wani gwa6in da na yi, kowa cewa ya ke ba
rame na yi katon kai." Haka suka yi ta zaulayar juna, Ummi na yi musu dariya daga
bisani suka fito kafar gida suka zauna a dakalin gidan su Amira dake kallon nasu.
Jiki a sanyaye Aliyu ya dafa kafadar Al'ameen, juyowa ya yi suka kalli juna cikin
ido, damuwa da tsantar so da kulawa Al'ameen ya hango kwance a kwayar idanun
Aliyu, "Abokina mekefaruwa, ka rame Ustaz kamar ba kai ba ka taimake ni ka gaya
mini halin da ka ke ciki." Ajiyar zuciya Al'ameen ya sauke, ya ce " Ina cikin
matsanancin damuwa Aliyu! Damuwar da take neman ruguza mini rayuwa, ta hanani farin
ciki da kaanciyar hankali dani da ahlina." Ya karashe maganar a sanyaye, agogon
hannunshi ya kalla ganin lokacin sallah ya kusa ya ce , "maganar da yawa bari mu yi
sallah tukun na." Kafin Aliyu ya amsa suka ji sallama a kansu, a tare suka mai
sallamar jin muryar mace.
Kallo d'aya ta ma shi zuciyar ta ya bata cewa shine, tabbas bata ta6a gaskata
zantukan Amira ba sai yau da ta yi arba da shi, gaba daya duk wani karsashinta sai
ya nemi arcewa ya barta, dakewa ta yi ta karfafa zuciyarta, tuna halin data baro
Amira a ciki, duk da haka ta kasa kallon shi cikin ido , sai Aliyu ta kalla ta ce
"Barkan mu da yamma." Kamar yadda shi take kallo take magana haka zalika shi ya
amsa mata da cewa "Yawwa barkan ki dai." Ta ce "Sunana Zainabu, kaqar Amira, idan
babu damuwa ina son yin magana da Al'ameen." Sai lokacin ya sake kai kallonsa
gareta gabansa ne ya shiga faduwa jin ta ambaci Amira, kallon shi Aliyu ya yi, yana
jira ya ji ta bakin shi, ganin bai tanka ba yasa ya ce "Bismillah! Yana saurarenki
bari na baku wuri" ya fada yana kokarin mikewa, da sauri Zainabu ta ce "A'a ka
zauna zan yi maganar a gabanka ka zama sheda don naga kamar kai abokin shi ne." Ya
ce "Ya ce OK to shikenan." Shiru ta yi na yan sakanni kafin ta yi karfin halin
d'agowa ta sauke kallon ta a kan shi shima ita yake kallo har lokacin ta ce, "Shin
kasan cewa wannan ciwon da amira ke yi ciwon sonka ke ne? Kasan cewa idan ba ka
kawo dauki gaggawa a gareta ba tabbas soyyarka zata zama ajalinta? Nasan duk baka
sani ba, to yanzu na sanar maka, Wallahi Al'ameen idan ka rasa Amira ka yi asarar
masoyiya, ka dubi girman Allah ka amshi soyayyar ta kodon ceton rai, wallahi muna
gaf da rasata kuma idan ka bari hakan ta kasance sai munyi Sharia da kai a kotun
Allah." Ta karashe maganar tare da fashewa da matsancin kuka, kasa tsaywa ta yi da
gudu ta bar wajen ta shige gidan su Amira, Fatima da ta yi suman tsaye ne tun da ta
kunnayenta suka jiyo mata maganganun Zainabu ta fito zata shige gida ne, ta karaso
gaba su da sauri cikin kidima da rawar muryar ta ce "Ya Yaya da gaske ne ciwon
soyayarka ne ya mai kwantar da Anty Amira? " Kallon ta yake yi kamar mutum mutumi
ya kasa koda gyada kai ne, hawaye ne suka Shiga gudu a fuskarta, da sauri ta mike
tana girgiza kai sani kuma ta juya da gudu ta shige gida tana kwala kiran sunan
Ummi, sai lokacin ya Ankara da tashin ta "Fatimahhhh!" Ya kwala mata kira amma ina!
Tuni ta shige "Innalillahi wa inna ilaihinr rajiun." Ya fada yana dafe kanshi dake
Sara mishi kamar zai rabe biyu..........
09116099486.
[12/29, 2:45 PM] AyshaNalado: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*PAGE 32*
Tana kaiwa dai dai tsakiyar zauren gidansu ta jiyo muryar shi cikin wani irin sauti
kwala kiran sunanta, cak! Ta tsaya ta kasa ci gaba da gudun, sai dai kuma ta kasa
dawowa gare shi, sai samun kanta tayi da durkushewa a zauren ta sake fashewa da
wani irin kuka mara amon sauti, kukan tausayin Amira, dama ta dad'e tana zargin
wani abu a tattare da Amira game da Yayanta sai dai bata ta6a tunanin lamarin har
ya kai haka ba, take ranar da ta ga Amira ta fito daga d'akin Al'ameen tana kuka ya
shiga dawo mata.
A can kofar gida kuwa, dafa kafad'ar shi Aliyu ya yi, a hankali ya d'ago kaifafun
idanunsa da lokaci guda su ka canza launi ya watsa ma shi,kallon cikin idanun juna
su ka yi na y'an sakanni, Kafin Aliyu ya lumshe ido ya bud'e tare da cewa a sanyaye
"It's time 4 prayer, muje masallaci." Bai amsa shi ba, don baya jin zai iya bud'e
baki ya yi magana, mik'ewa ya yi jikinsa a matuk'ar sanyaye, su ka nufi masallacin
kusa da gidan.
Bayan sun idar da sallah, hannaye Al'ameen ya d'aga sama ya shiga kai kukan shi ga
mahalici, ya dad'a yana kwararo addu'o'i har sai da kusan kowa ya watse a
masallacin, bai sauke hannayensa ba. Aliyu na daga gefen shi yana amsawa da amin
duk da ba jin abin da yake fad'a yake yi ba don a zuciya yake yi.
A tare suka shafa addu'ar, shi ya fara mik'ewa ganin haka yasa Aliyu ya biyo bayan
shi. Tafiya suke yi a jere sai dai babu wanda ya ce wa d'an uwansa kanzil, daurewa
kawai Aliyu yake yi ya hana kansa magantuwa ganin halin da abokin nasa ke ciki,
amma bakinsa fal! yake da tarin tambayoyi, Kansa gaba d'aya a k'ulle ya ke.
Mazaunin su na da suka koma suka zauna, shiru ne ya gifta a tsakanin na wasu
mintuna, Aliyu dauriyarsa ya k'are don gabansa fad'uwa kawai yake, har ya bud'e
baki da nufin magantuwa, Ya tsinkayi muryar Al'ameen cikin wani irin amo mai nuni
da cewar tabbas maganar da zai fad'a mai girma ce, ya ce"Aliyu! Banda Allah
mahaliccina, bayan ni kaina da kuma likitan daya d'aurani a kan magani, Kai ne
mutum na uku da na za6a kasan sirrina, hakan kuma zai faru ne saboda na yarda da
kai, na dauke ka d'an uwa amini abokin kuka wanda hausawa kan ce ba'a boye masa
mutuwa." Gyada kai Aliyu ya yi cike da gamsuwa da bayanansa, shiru Al'ameen ya yi
na wani dan lokaci, kafin daga bisani ya sauke kakkarfar ajiyar zuciya a hankali ya
bud'e baki tiryan-tiryan ya shiga bawa Aliyu labarin ciwonsa tun daga lokacin daya
fara fuskantan matsalar har zuwa kan yanzu da larurar ke mataki na biyar a jikinsa.
Dagowa Ali ya yi idanunsa jajur yace "Wacece Amira? Menene alakar ka da ita." Nan
ma bai yi k'asa a gwiwa ba wajen zayyanewa Aliyu wacece Amira da alak'arsu tun daga
farko har zuwa yau , ya daura da cewa "Aliyu ban sani ba cewa akan soyayyata ne ta
ke wannan ciwon, ban yi zaton lamarin ya kai girman haka ba, abin da na sani kawai
bana son ta."
Shiru ne ya biyo baya, gaba d'aya jikin Aliyu ya yi la'asar, lamarin ya sosa ransa
fiye da zaton mai zato, gaba d'aya tausayin Al'ameen da ahlinsa harma da Amira ya
gama cika masa zuciya, a iya hasashensa babu wata mafita data wuce wacce Dr Abdul
ya fad'a, to amma ta yaya hakan zai kasance.
Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya d'ago ya ce "Abokina na tausaya maka kwarai, sai
dai naga zallar wautarka, shin me yasa ka za6i ka kassara rayuwarka akan ka yi
Aure, kula da Ummi da Fatima kadai bai isa hujja ba, ka gwammace ka mutu a tsaye a
kan ka yara sunnar ma'aiki, wallahi na tabbata idan Ummi ta ji wannan maganar sai
ta zubar da hawayen bakin ciki da takaici, kana fa da ilmin addini daidai
gwargwado, kana da tabbacin zaka iya rike kanka har zuwa lokacin da ka yanke wa kan
ka yin aure, kana da tabbacin kwayoyin maganin da kake sha zasu ci gaba da rike ka
har zuwa lokacin da ka d'ibarwa kan ka?" Girgiza kai Al'ameen ya yi ya ce "Ba ni da
tabbas abokina yanzu menene mafita." Aliyu ya ce "Da gaske ka dauke ni amini abokin
shawara kamar yadda ka fada?" Gyada mashi kai Al'ameen ya yi ba tare da ya iya
bud'e baki ya amsa shi ba, "To mafita shi ne ka jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya."
" Kamar yaya?" Ya tambaya cikin rashin fahimtar inda maganar Aliyu ya nufa, kallon
shi ciki ido ya yi ya ce "Ka Auri Amira." "Na auri Amira?" Ya maimaita maganar
cikin sigar tambaya, Aliyu ya ce "E ." girgiza kai ya yi ya ce "Bazan iya ba zan
dai taimaka mata ta wata hanyar." A harzuk'e Aliyu ya ce "Ya zama dole ka iya, dole
ka auri yarinyar nan Ameen." "Akan me zan aureta ba bayan bana son ta, ita fa
zuciya ba a yi mata tilas." Ya amsawa Aliyu shima a fusace, mikewa Aliyu ya yi ya
ce "Na sani Ameen zuciya ba'ayi mata tilas, amma ka sani a wannan ga6ar ba maganar
so ko kiyayya ake yi ba, magana ake ta ceton rai da rai " Yana gama fad'in haka
ya juya ya kama tafiya ba tare da ya sake kallon Al'ameen ba.
Da kallo Al'ameen ya bi shi, zuciyarsa na harbawa, shin ya tsayar da shi ne ko ya
k'ale shi? Ya fi minti goma yana bin haryar sa Aliyu ya bi sa kallo, a zuciyarsa
yana taraddadin mai Aliyu zai yi? Ya fi kowa sanin Aliyu, ya san dai tunda ya ce
dole yana nufin dolen ne, sai dai komai zai faru ya faru, fatan shi dai kar Ummi ta
ji wannan batu, Rass! Gabansa ya fad'i lokacin da ya tuno da Fatima, a hargitse ya
mike, shaf! Ya manta cewa ta ji, ya tabbata ya zuwa yanzu Ummi ta san da maganar,
da sauri ya nufi cikin gidansu, sai dai tuntu6en da ya yi da abu a zaure ya dakatar
da shi, kafin ya gama tantance da mai ya yi tuntu6e shesshekar kukanta ya cika
mishi kunne, "Fatima!!!" Ya ambata a tsorace, yana kokarin haska tocilar wayarsa,
itan ce kuwa kamar yadda ya yi hasashe, da sauri ya d'ago ta yana cewa; Menenen
Fatima me ya faru, ina Ummi?" A rud'e ya shiga jero mata wad'annan tambayoyin.
jikinsa ta fad'a tare da sake rushewa da kuka, k'ofar d'akinsa ya bud'e ya ja
hannunta a su ka shiga, ya mai da k'ofar net d'in ya rufe.
Zaunar da ita a bakin kafitarsa ya yi ya tsuguna a gabanta, ya ce "Fatima Menene?"
Cikin shessheka ta ce "Yayana Anty Amira, da gaske ne?" Gabansa ne ya fad'i, k'ura
mata idanu ya yi, kafin ya ce "Kin fad'awa Ummi ne?" Ta girgiza kai. Boyayyar
ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa; Kar ki gaya mata kin ji kanwata hankali ta zai
tashi sosai." Gyad'a kai ta yi alamar to, sai kuma ta hade hannayenta alamar rok'o
ta ce cikin kuka; Yaya dan Allah ka so ta, dan Allah ka tausaya mata ka kaunaceta
wallahi tana son ka matsanancin soyayya Yaya ina tsoron kar mu rasata ta dalilinka,
idan ka yi haka ka yi ceton rai, kuma na tabbata Ummi zata fi kowa farin ciki da
hakan, idan kuma ta samu labarin ciwon Amira na da alaka da kai na tabbata zata fi
kowa bakin ciki, Yayana don Allah karka ce A'a, ko dan ni da Ummi ka kaunaci Anty
Amira baza ka yi nadama ba.." Hannayenta dake hade ya kama ya rike gam! da
hannyensa yana jin maganganunta na ratsa kwakwalwarsa take idanunsa suna karasa
rinewa, cikin matsanancin kuka ta ci gaba da cewa "Don Allah Yayana, don Allah pls
kar ka ce A'a, ko dan ni da Ummi, ba baka da tam karmu muma bamu da ya kai."
Kalaman data yi ta maimaitawa kenan idanunta a rufe tana hawaye har sai da ta ji ya
ce "Is ok Fatima, is ok naji na Amince." Cak! Ta tsayar da sambatu da kukan da take
yi ta dago ta kalle shi idanu jaga-jaga da hawaye ta ce a sanyaye "Da gaske
Yayana." Ya gyada mata mata kai tare da sakar mata murmushin karfin hali. Fad'awa
jikinsa tayi tana sakin dariya mai sauti hawayen farin ciki da kaunar tilon dan
uwanta na kwaranya a idanunta, tallefe kanta ya yi shima yana jin kamar ya yi
wahayen.
Sun kusa minti goma a haka, tun tana shessheka har ta koma sauke ajiyar zuciya, jin
ana shirin tayar da sallar isha'i yasa ya sake ta, ya kalleta ya ce, "Ina rokonki
Fatima ki yara daren yau wajen taya ni neman za6in Allah, ni ma yau zan gabatar da
istikhara akan lamarin kome ciki Allah zai dafa mana." Gyada kai ta yi ta ce "In
sha Allah Yayana." Mikewa ya yi ya ce ki shiga gida nima zan ta fi masallaci.
Koda ta shiga gida bata nunawa Ummi komai ba, alwala ta yi ta gabatar da sallar
magriban da batta yi ba ta daura sa ishan da ake kira.
Kamar yadda Al'ameen ya roketa ranar daga ita har shi kusan kwana suka yi a bisa
sallaya suna kai kukan su ga Mahalicci.
Washegari
**************
Ajiyar zuciya Dr Abdul ya sauke bayan ya gama sauraren jawabin dan matashin yaron
da bai gaza tsaran Al'ameen ba ya gama yi masa, sake kallon yaron ya yi da kyau, ya
ce "Aliyu ko?" Gyada kai Aliyu ya yi, Dr ya sake cewa "Thank u Aliyu!" K'arara
mamaki ya bayyana a fuskar Aliyu, shi da ya zo ban hakuri da neman taimako ana yi
mishi godiya, goron ruwan faron dake kan table Dr Abdul ya dauka ya bude murfin ya
kur6a kadan ya mai da murfin ya rufe, kallon Aliyu ya yi ya ce "Nasan kana mamakin
dalilin da yasa na yi maka godiya ko." Aliyu ya gyada kai, Murmushi Dr ya yi yace
"Saboda ka rage mini aiki, sam! Ban yi fushi da Al'ameen ba domin da baka zo ba ina
daf da bin sahun shi, jira nake wa'adin dana d'aukar masa ya cika, sai ga shi kai
ka fanshe shi, na jinjina maka lallia ka cika Amini na kwarai kuma ina da tabbacin
zaka taimakeni a kan abin da na saka a gaba na alkhairi." Shiru ya yi kad'an kafin
ya daure da " Aliyu na fi ka son na taimakama Al'ameen, amma na rasa irin taurin
kan shi, sometimes na kan zauna ni kad'ai na dinga tunanin irin karfin hali da
taurin zuciyar shi, ko da yake ance ma gaji ma fiyi, ada ni kad'ai na me
gwagwarmayar nan yanzu gaka ka shigo ciki, don haka zamu had'a karfi da karfe!
Yanzu dai abin da ya kamata mu yi, shine mu samu ya amince da maganar auren domin a
yanzu shi ya fi komai mahimmanci, idan muka yi sanya, ina mai tabbatar maka daga
nan zuwa ko wani irin lokaci zai iya haduwa da mummunan attack wanda idan ba'ayi da
gaske ba zai iya shiga wani mummunan garari ko kuma ya rasa rayuwarsa ma baki
d'aya." "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!" Shine Kalmar da Aliyu ya furta a
baiyane cikin tsantsar tashin hankali, "Dr yanzu menene abin yi?" "Ka bi duk hanyar
da zaka bi wajen ganin ka tirsasashi ya amince da batun auren yarinyar nan." Cikin
tashin hankali ya ce "Zan yi Dr, zan tirsasashi ko zai amince' dole zai amince."
"To shikenan Aliyu zan kar6i lamabarka saboda ina son sanin duk halin da ake ciki."
Canjen lambar waya suka yi daga haka suka yi sallama Aliyu ya tafi.
***************
Washegari ya kama asabar babu school, misalin karfe tara na safe Al'ameen ya shiga
d'akin Ummi cikin shirin shi na tafiya wajen neman halalinsa ya sha kyau cikin wani
yadi milk, dinkin karamin riga mai guntun hannu da wando babu hula akansa don ba
abocin sakawa bane, duk suna falo Ummi ta maida hankali tana sauraren wa'azin Dr
jabir mai hula a tashar Afrika TV 3, yayin da Fatima ke zaune daga can sak'on
kujera, kallo daya zaka san tana tattare da damuwa, idanunta sun yi luhu luhu
alamar rashin barci, sallamar sa ne ya dawo dasu duk hayyacinsu. Ummi ta ce cikin
fara'a bayan ta amsa sallamarshi, "Amintacce har an fito." Murmushi ya yi ya ce "E
Ummi na fito a yi mini addu'a." Ya karashe maganar yana rage tsawo a gabanta.
Kan shi ta dafa ta ce "Ubangiji ya tsare gabanka sa bayanka ya yi maka albarka ya
saka maka Albarka cikin neman ka ya jikan mahaifinka." Cikin wani irin yanayi ya
amsa da "Amin Ummi." Tare da mikewa tsaye, ya kalli Fatima da itama shi take kallo
ya ce "Kanwata muje ki min iso na shiga na dubo jikin Amira." Daga yadda fara'a ta
fadada a fuskar Ummi ya tabbata ta ji dadin lamarin sai ya tsinci Kansas cikin
farin ciki shima, Fatima kam wuf! Ta yi ta mike fuskarta dauke da madaukakin farin
ciki........
Oum ummeetarh
09116090468
[12/29, 2:45 PM] AyshaNalado: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*PAGE 33*
No editing π€
Cike da zumud'i Fatima ta zura dogon hijabinta, bakinta washe kamar gonar auduga ta
ce "Yayana muje." Ya gyada mata kai tare da k'ara yin sallama da Ummi suka fito.
Tana gaba yana biye da ita har k'ofar gidan, a nan ya dakata ita kuma ta k'arasa
ciki bakinta d'auke da sallama, a tsakar gida ta tarad da Maman Amira da Aysha da
sauran k'annen Amira, Mama ta fara gaisarwa tare da tambayar mai jiki, sannan suka
gaisa da Aysha wacce suke kusan sa'anni, sauran yaran suka gaisheta.
Wuri ta samu ta zauna a dakali, ta kalli Mama ta ce "Mama Yaya Ameen ne yace na
mashi iso yana son ya shigo ya duba Anty Amira da jiki." Mama ta ce "Assha!
Aminullahi ne da neman iso dan zai shigo gidan nan, jeki maza ki ce ya shigo, ke
kuma Aysha gayawa Amiran zuwan Aminullahi." Kusan a tare Fatima da Aysha suka amsa
mata da to Mama.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bi bayan Fatima, da ta juya bayan ta isar masa da
sa'kon Mama, Bakin sa dauke da cikakkiyar sallama ya saka kansa cikin dan
madaidaicin tsakar gidan, dai dai lokacin Aysha ta fito daga d'akin Mama tana cewa;
"Mama Anty Amira fa ta samu barci." "Barci kuma? ikon Allah! Yanzu