Author : Aysha Nalado Category : African Stories & Novels
ko tsammani ta jita a jikin mutum, turarensa ne ya tabbatar mata
da cewa shi ne, take ta ƙamƙameshi tare da fashewa da wani irin kuka mai ƙarfi.
Rintse idanu Al'ameen yayi zuciyar shi na tafarfasa, zai iya jurar komai amma
banda taɓa tilon kanwar shi, zai iya yin fito na fito da ko waye akanta, ita kaɗai
ce wacce zai iya bugu ƙirji ya nunawa duniya a matsayin ƴar uwarshi.
Lokacin da ta fito daga gida tana shan kwanan gidan su Joy yana ɓullowa bata
ganshi ba amma shi ya hango bayan, kamar ya kwala mata ƙira sai wata zuciyar ta
raya mishi cewa ba ita bace, tunda yasan ba nan bane hanyar haddarsu wata ƙila
daya daga cikin yaran maƙota ne da suke zuwa hadda ɗaya, sai dai shigan sa gida ya
tabbatar masa da ita ɗin ce, don gaba daya ya tarar da yaran makotan nasu a tsakar
gida wai sun biyo mata su tafi hadda, yana ji Ummi ta amsa musu da Fatima ta riga
ta wuce bata biya musu bane" Gabanshi ya faɗi, ke nan ita ɗin ce ina zata je??? ya
jefawa kanshi tambaya, tsoro ne ya shige shi lokacin da zuciyar shi ta raya ma shi
wani mugun tunani, ta ke ya kawar da shi ya na girgiza kai, kasa kwanciya hankalin
shi yayi hakan yasa ya biyo bayanta da sassarfa ba tare da ko Ummi ya sanar wa
mekefaruwa ba, kwata kwata bai kawo gidan su Joy aka ba, sai dai ganin ya shanye
kwanar ya shiga wata bai ganta ya fara zargin ko can ta je, take hirarsu ta jiya da
dare ya dawo mai, tabbas yadda yaga ta damu da rashin ganin Joy yasan zata iya zuwa
gidansu don ta duba lafiyarta, take ya kama hanyar gidan cike da yaƙinin ganinta
sai dai yana isowa Mom na hankaɗo ta waje kamar wata barauniya.
Sautin kukanta ne ya tilasta ma shi
buɗe idanun shi waɗan da suka rine kamar gauta saboda ɓacin rai ya sauke su a kan
get ɗin gidan, daidai lokacin da Mom ke banko ƙarami ƙofar bayan tayi nasaran tura
Joy ciki dakyar.
Hannu ya saka ya janyo hijabinta ya rufe mata kanta dake buɗe, a hankali kuma ya
shiga bubbuga bayanta alamar rarrashi ba tare da ya iya buɗe baki ya furta mata
koda kalma ɗaya ba.
A hankali sautin kukanta ya fara raguwa, daga bisani kuma ya dauke gaba ɗaya, sai
shessheƙa da ajiyar zuciya, ganin ta ɗan samu nutsuwa, ya raba ta da jikinshi tare
da kama hannunta suka bar ƙofar gidan ba tare da ya ƙara yi ma gidan kallo ɗaya ba.
A bangaren Fatima mari da hankadar da Mom ta mata bai daga mata hankali ba, kamar
yadda kalamanta suka daga mata hankali, tana jin Joy a jikin jinin jikinta da
bargonta, jinta take yi kamar wata bangaren na jikinta, kwatankwacin yadda take jin
Yaya Ameen haka ta ke jin Joy a zuciyar ta, shin me yasa Mom take son raba su, ta
karashe tunanin sabbin hawaye na silalowa daga idanuwanta.
A haka suke iso ƙofar gidan su ba tare da Al'ameen ya iya buɗe baki ya ce mata
ƙala ba, domin ran shi a maruƙar ɓace ya ke idan ya ce zai yi magana a lokacin
bazai faɗi alkhairi ba.
A zaure ya dakatar da ita, ya shiga ciki ba jimawa sai gashi da dayan hijabin
haddanta a hannunta shi, buta ya dauko ya bata ta wanke fuskarta, sannan ya bata
hijabin ta saka, ya sake jan hannunta, bai tsaya da ita ko ina ba sai haddarsu,
hakuri ya baiwa malamin su akan lattin da ta yi, sannan ya juya ya tafi ba tare da
ya kalli Inda take ba, sai lokacin shirun na shi ya fara daga mata hankali, ta san
sarai shirun nan na yayanta ba alkhairi bane akwai abin a yake shiryawa, magantuwan
shi yafi alkhairi sau da yawa fiye da shirun shi.
*********
A bangaren Joy dakyar Mom ta samu ta turata cikin gidan ta maida get ta rufe,
zubewa ta yi a wajen ta fashe da wani irin kuka, cikin kukan take cewa "why Mom me
yasa zaki yi mata haka, me yasa kika koreta Mom, me yasa kika daketa." Mom dake
wani irin huci ta dago ta watsawa ma'aikan gidan da suka yi cirko -cirko suna
kallonsu wani mugun kallo take duk suka dare kowa ya kama gaban shi, tsugunawa ta
yi gaban Joy a tausashe ta riko hannayenta ta ce "Ki daina kuma daughter ban yi
haka don na bata miki rai ba nayi ne dan kare martabarki data addininmu, na mata
haka ne saboda ta rabu dake don ke ba sa'ar kawancenta bane," katseta ta yi da
cewa "Amma ai na miki alkawarin ni da kaina zan rabu da ita, me yasa zaki
wulakantata." Mom ta ce "To naji kiyi hakuri ki share hawayen ki, kinga baki da
isasshen lafiya." Mikewa ta yi ba tare da ta kula Mom ba ta wuceta fuuu ta shige
plat din su haurawa sama ta yi ta fada dakinta ta bugo kofa ta murza key. Nan ta
silale bakin kofar ta ci gaba da rera kukanta ji take kamar ta yi tsunstuwa ta
ganta a gaban Fatima, me zata ce mata da wani ido zata kalle ta, uwa uba Yayanta
shin da wani baki zata fahimtar da su ce wa bata laifi.
Biyo bayanta Mom ta yi ta tura kofar dakin ta ji shi a rufe, knocking ta shi ga yi
tana kiran sunanta, tana ji taki tankawa, babu irin magiyar da Mom bata mata ba,
karshe dole ta kyale ta, gajiya ta yi da kukan ta mike ta shi ga toilet ta wanke
fuska ta dawo kan bed dinta ta kwanta, wuraren karfe goman dare ta jiyo muryar Papa
a bakin kofarta yana kiran sunanta, ta shi tayi ta bude tare da fadawa jikin sa ta
fashe da sabon kuka, rarrashinata ya shiga yi, cikin sigar nasiha ya ce "Akan me
zata damu kanta dan kawai wata Muslim kanwar ta tazo Mom dinta ta ce bata nan, ai
wannan ba abin damuwa bane Mom tayi haka ne don ta kareta daga sharrin terrorism.
Daga yanayin kalaman shi ta fahimci bai san ainahin abin da ya faru ba, kawai karya
da gaskiya da son rai Mom ta sanar mishi. Shi ya lallabta har ta dan sake ta samu
ta ci abinci.
A haka weekend days suka tafi duk bata cikin walwala, duk da irin kokarin da Papa
yayi na fitar da ita shopping da wuraren shakatawa a ranar Sunday ya kashe mata
makudan kukade hakan bai rage ta da komai ba, Allah Allah ta dinga yi gayi ya waye
ta je school ta hadu da Fatima ta bata hakuri, washegari kuwa 6am ya gama komai
har ta da breakfast ranar bata jira su Mom ba, daki ta bisu ta yi musu sallama
direbanta ya wuce da ita.
*********
Har akaci ranakun karshen mako aka sid'e Yaya Ameen bai ce komai game da abin da ya
faru ba, Fatima ta yi ta zuba ido ko zai mata fada amma bai yi ba kuma bai canza
mata a komai ba sannan bai gaya Ummi abin da ya faru ba, ganin haka yasa ta dan
saki jiki, safiyar litinin cike da wani irin shauki da zakuwa ta gama shirin
makaranta, duk da a ɓangare ɗaya zuciyarta cike take da fargaba amma hakan bai hata
ta sauri ba, tsab ta shirya da wuri tana cikin sallama da Ummi dake zaune a tsakar
gida Yayanta ya shigo, da fara'a ta kalleshi ta ce "Yaya barka da safiya." Duk da
kuwa sun gaisa ɗazu bayan asuba, kallon ta yayi ya na jin wani irin a zuciyar shi
game da hukuncin daya yanke ganin yadda take cike da farin ciki, dakewa yayi ya ce
"Ya ce Fatima ki je ki cire uniform din jikinki daga yau na cireki daga challenge
international school, zan canza miki wata makaranta." Wani irin zaro ido Fatima ta
yi ta sauke a fuskar shi, hankaɗinta a tashe gabanta na wani irin dokawa, Ummi ma
da sauri ta dago ka ta kalle shi, suka hada ido yayi saurin dauke kai, daga kallon
da take mishi, kafin ta ce wani Abu yayi saurin cewa "ki yi hakuri Ummi hakan shine
abin da zaifi mana kwanciyar hankali baki ɗaya." Ta san ɗanta yana da kaifin
hankali da zurfin tunani bata jin zai aikata abin da ba dai dai ba, amma duk da
haka zata so sanin dalilin shi, kallon Fatima da tuni hawaye sun game wanke mata
fuska tayi ta ce "Binta bamu guri, koma ɗaki ki cire uniform ɗin kamar yadda ya
fada." Da gudu ta wuce tana fashewa da kukan da tun ɗazu take kokawar rikewa, da
kallo duk suka rakata har ta kule.
Dawo da kallon ta kan shi ta yi, tare da yin gyaran murya, zama yayi a gefenta a
tausahe ya ce "Ummi kiyi hakuri da hukuncin dana yanke ba tare da neman shawarar ki
ba." Dakatar da shi yayi da cewa "Ba wannan nake son ji ba shin menene dalilinka na
canja mata makaranta, duk da nasan makarantar kuɗi ne ya fi ƙarfin mu amma ai ba mu
muke biya mata ba." Ya ce "Ummi dalili na mai karfi ne kuma shine kwanciyar
hankalin ta da nawa da kema baki gaba daya." Tsare shi tayi da ido ganin yana son
mata kwana kwana ta ce a dake cikin yananyi na rashin wasa "Dalilin naka na ke son
ji ko bankai matsayin da zan sani ba ne?" "Ki yi hakuri Ummi." Ya fada ganin kamar
ta dau zafi, kafin ya kwashe komai akan abin da ya faru ranar ya sanar mata, ya
daura da cewa "Ummi tarayyar mu da su ta ko,ina bai kyautu ba, na yanke shawaran
canzawa Fatima makaranta saboda rage karfin alakar dake tsakanin su, na san idan ba
ta hakan ba babu ta yadda zamu Iya rabasu." Shiru Ummi ta yi labarin ya girgiza ta
kuma ya bakanta mata, sai dai ita abin da ta dade da hangen a alakar Fatima da Joy
ba kowa ne zai iya hango shi ba, ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Amintacce wannan
lamari baiyi dadi ba, sai dai har kullum ina kara sanar maka tsakanin yaran nan
akwai wani boyayyen sirri wanda ni kaina bansan shi ba, mu bi komai a sannu don ina
ji a jikina wata rana wannan alakar tasu zata fitar dani daga kangin rayuwar
kadaicin da nake ciki na tsawon shekara da shekaru, duk da mafarki ba gaskiya bane,
ba abin yadda bane ni naga hakan a cikin mafarkina yafi sai shurin masaki, Allah ya
sani da fari nafi mahaifiyar Joy kiyayar tarayyarsu, kuma kai shaida ne babu ta
yadda banyi don na raba su ba, sai dai daga baya na fahimci cewa tsakanin su hadin
Allah ne, bazan hanaka canzawa kanwarka makaranta ba idan kaga hakan yafi maka
kwanciyar hankali shi kenan."
A ajiyar zuciya ya sauke dama fatan shi Allah yasa kar Ummi ta ki amincewa da
hukuncin shi.
Zamu dinga tsallaken rana daya idan nayi posting yau bazan yi gobe na sai jibi
insha Allah.
Ga me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar.
09116099486
[12/29, 2:33 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY*🌀🌀
*PAGE 10*
Miƙewa yayi daga gaban Ummi ba tare ya sake cewa komai ba ya bi bayan Fatima, bata
falo dama baiyi tsammanin ganinta a nan ba, bed room ya nufa kai tsaye , a kwance
ya same ta kan gado tana ta risgan kuka , jin motsin shigowar mutum yasa tayi sauri
ta juya baya ta fuskanci bango, yadda mai shigowan bazai iya ganin fuskarta ba ta
yi tsit! kamar mai bacci. Daga bakin ƙofar ɗakin ya tsaya ya rungume hannayen shi a
ƙirji yana ƙare mata kallo yana jin wani rauni na son ziyartar zuciyar shi, dakewa
yayi ya ce "Fatima kuka kike yi???" Da sauri ta girgiza kai, wasu sabbin hawaye na
sake wanke mata fuska. Ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da cewa "Kiyi haƙuri
Fatima idan hukunci na yayi tsauri da yawa a gareki, amma ki sani bazan iya jurar
ganin ana wulakanta ki ba, ya zama dole ki yanke alaƙa tsakanin ki da yarinyar nan
tunda iyayen ta itama basa so, bamu da ƙarfin ja da su ta kowanne fanni, shiyasa na
yanke hukuncin canja miki makaranta, duk da nasan zakiji babu daɗi, kiyi haƙuri ni
mai kare martabarki ne a koda yaushe." yana gama faɗin haka ya juya ya fice don
bazai iya jurar ci gaba da ganin kukanta ba.
Ummi na zaune yazo ya wuceta yayi haryar ɗakin shi, kiran sunan shi tayi ya juyo ta
ce "ka zo ka dauki kununka ka tafi da shi gaba ɗaya." dawowa yayi ya ɗauka ya
wuce . ajiye kunun yayi ba tare da sha ba ya zuba tagumi ya faɗa komar tunani,
sosai yayi nazari akan huƙuncin shi bai ga wani cutuwa a ciki ba, kuma hankalin shi
ya kwanta da hakan ɗari bisa ɗari, dama shi bai taɓa kaunar alakar su ba , saboda
Ummi kawai yake danne zuciyar shi. Sai dai zai iya kokatin shi wajen ganin ya duke
mata duk wata damuwa bazai barta ta shi ga damuwa a dalilin hakan ba alkawari ya
daukarwa kansa.
*******
Tunda Joy ta shi ga class idanunta na kan kofa, jira kawai take yi taga b'ullowar
Fatima amma shiru, har malamin da ke daukar su first period ya shigo, sai lokacin
ta ji haushin kanta na k'in biya mata su taho tare da tayi, duk da ta gwada yin
hakan sai dai kunyar Yaya Ameen da Ummi bazai barta ta iya zuwa gidan ba, da wani
ido zata kalle su, har gara Ummi akan Yaya Ameen da dama can ya lafiyar kura.
Sanin da tayi mata gwanar latti ce yasa bata d'aga hankalinta sosai ba, sai dai
ganin malamin yaci double period dinsa ya fice wani ya shigo ta tabbatar Fatima
bata zo school yau ba, kasa kwanciya hankalin ta yayi gaba d'aya ta daina fahimtar
darasin da suke yi, me ya hana Fatima zuwa school?, ta jefawa kanta tambaya. Kar
dai ace bata da lafiya, kar dai ace sanadin abin da Mom ta mata wani matsala ya
same ta, take taji zazzabi na shirin saukar mata, ta riga ta yi amannna cewar haka
ne, gaba daya ranar rasa kanta aka yi a class karshe kwanciya tayi akan desk har
akayi closing, da kudirin zuwa gidan su Fatima ta fito daga cikin school, dan ta
san zuwa yanzu Yaya Ameen baya gida, sai dai tana fito wa ta tarar Mom ce yau da
kanta tazo d'aukarta, babu yadda ta Iya haka ta kirkiro murmushi yak'e ta sakar
mata, tare da bude motar ta shi ga suka tafi gida.
Ranar haka ta wuni a kwance kamar ruwa duk bata cikin walwala, sai dai bata bari
iyayenta sun fahimci halin da take ciki ba gudun daga musu hankali, da tsoron kar
si fahimci ta samu da Fatima su kara karfafa mata tsaro da sanya mata ido.
*******
Fatima kam kuka tayi sosai har sai da kanta ya fara ciwo, tana jin sandaYayanta ya
yi sallama da Ummi ya fi ce daga gidan, bayan tafiyar sa Ummi ta kwala mata kira,
murya a dashe ta amsa, tare da mikewa ta kwabe kayan makarntar ta canza na gida
sanan ta fito, ta ce "Ummi gani." Kallonta Ummi ta yi ta ce "Kuka kikeyi Fatima
akan hukuncin da yayanki ga yanke akanki," da sauri ta girgiza kai, ta ce "Ummi ba
hukuncinsa na ke wa kuka ba," "to me kikewa kuka." Narai narai tayi da ido ba tare
da ta iya ba Ummi amsa ba, ganin haka Ummi tasan bata da ta cewa , don haka ta Dora
da cewa "Ni dai har kullum ina kara umartan ki,ki zama mai biyyayya a gare shi
domin shine jagoran rayuwar ki ko bayan raina." Gyada kai ta yi, Ummi ta ce "Tunda
kina gida yau ina so zan dan fita unguwa bazan dade ba zan dawo kiyi girkin rana
akwai tsakin shinkafa kiyi dambu ki tsinki zogale a ice ki ki gyara." Sake gyada
kai tayi. Ummi bata bi ta kanta ta mike ta shige daki ta shirya cikin shigarta na
mutunci ta fice daga gidan, ta bar Fatima cike da tunanin Inda take yawan zuwa a
y'an kwanakin nan.
Bayan tafiyar Ummi zama tayi ta rafka tagumu tana saka da warwara, tayi nisa cikin
tunani, ta ji an gaba ta firgigit ta yi ta dago, da Amira ta yi ido biyu, murmushin
yak'e ta kirkiro ta sakar mata, Amira dake tsaye a kanta tana mamakin irin zurfin
da tayi a tunani ta ce " Fatima tunanin me kike yi haka, tun dazu Ina ta sallama
baki ji ba." Bata amsa tambayarta ba sai cewa ta yi " Anty Amira Ina kwana."
Amira ta ce "lafiya kalau baki je school ba ne yau?" Ta ce "Eh bana jin dadi ne."
"Allah sarki Allah ya sauwake, ai ga idanunki nan ma sun nuna." Murmushi kawai
Fatima ta yi, Amira ta sa ke cewa "Ummi na ciki ne?" Fatima ta amsa da "A'a ta
fita." Kasa kasa Amira ta yi da murya cikin rad'a ta ce "Yaya Al'ameen fa?" Kallon
ta Fatima ta yi, cike da mamakin yin rad'ar tata ta amsa mata da s "Shima ya tafi
school." Ajiyar zuciya Amira ta sauke wanda ya tilastawa Fatima sake kallonta,
ganin tana kallonta yasa ta sakar mata Murmushi ta ce "Dauko tsintsiya na taya ki
sharar gidan tun da baki jin dadi." Cike da mamaki Fatima ta ce "A'a Anty Amira ki
barshi zan yi." Harara ta watsa mata, tare da wuceta ga mamakin Fatima ta ga Amira
ta nufi wani dan lungu da suke ajiye kayayyaki irin su tsintsiya da sauran tarkace
ta dauko tsintsiya da faka, ba tare da ta jira an nuna mata in da suke ba, da
alamar ta Dade da Sanin ma'ajiyar su, ta ke ta shi ga sharar ta hankalin kwance,
Fatima mikewa tayi ta koma falo ta bata fili, zuciyar ta cike da mamaki.
Tas Amira ta share gidan ta jawo ruwa a rijiya ta cika drum, falo ta dawo ta samu
Fatima kwance nan ta zauna ta shi ga jan ta da hira wanda duk rabin hirar akan
Yayanta ne, duk da Fatima bata cikin yanayin mai dadi, ta sake da Amira sosai suka
yi hiran Al'ameen wanda gaba daya Amira ce ta karkata akalar hirar cen, sai da ta
taya ta hura wuta kafin ta mata sallama ta fi ce, ta ce idan Ummi ta dawo ta gaisar
mata da ita.
Sai bayan azahar Ummi ta dawo zuwa lokacin fatima tayi girkin ta kwashe , sai dai
ko kadan ta kasa dandanawa, a kwance Ummi ta sameta a daki, sannu da zuwa tayi
mata, ta kawo mata abinci ta koma ta kwanta, Ummi bata takura mata ba sanin tana
bukatar space, sai ma janta da ta ringa yi a jiki tana mata hirarraki , hakan kuwa
ya taimaka sosai wajen rage mata damuwa da tunani makomar kaancenta da Joy.
Ranar Al'ameen bai dawo ba sai dare, daga school da ya tashi, gidan daya ke daukar
keke ya nufa, ya dauki keke ranar wuni yayi