JOY by Aysha Nalado

Author :  Aysha Nalado Category :  African Stories & Novels

Chapter   17 / 23

48K to 51K   out of 68.8K words

ya dawo sai na tafi." Zaro ido
Fatima ta yi kafin ya ce wani abu sai gashi yana shigowa, fatima ta ce "Yawwa Yaya
zo kaji." Da sauri joy ta kai hannu ta rufe mata baki, tana zare ido, bata yi
zaton yana kusa ba, jingina ya yi da bango ya yi folding hannayesa a kirji ya ce
"Menene sister gayamin, gulma na FARHAT ta yi ko." Girgiza kai Fatima ta yi, ya ce
"To menene." Kallon Joy ta yi tana dariya da sauri ta girgiza mata kai, sai kawai
ta ce "Yaya babu komai." D'age kafada ya yi ya ce "Ku kuka sani Ku bani hanya na
shiga dakina." Kaucewa suka yi ya shige bayan sun yi sallama da Joy.

Har inda suka yi da David zasu hadu Fatima ta rakata, a wurin suka tarar da shi
shima isowar shi kenan, kallo Fatima ya yi yana murmushi ya ce "Fatima my
classmate." Harara ta watsa mashij, ya kyalkyale da dariya ya ce "Yau ina cikin
farin ciki don haka bazan kulaki ba, amma zamu jone, muje Joy time ya wuce sosai."
Ya karashe maganar yana kallon agogon dake daure a hannun shi...........


09116099486.
[12/29, 2:44 PM] AyshaNalado: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *JOY* ๐ŸŒ€๐ŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 30*



Ga link domin shiga group na Littafin *JOY* kai tsaye.

https://chat.whatsapp.com/EhPtIfeNaTtCC2GS6SvOnW


Tun daga wannan ranar k'awancen Fatima da Joy ya dawo d'anye sharrr!shak'uwa da
soyayya da sukewa juna ya sake nunkuwa, abin har mamaki ya ke ba Al'ameen sai ka ce
wasu tagwayen da su ka fito mahaifa d'aya. Kusan kullum sai Joy ta zo gidan su
Fatima daga school ba tare sanin Mom ba, yanzu bata da wata matsala ko shamaki da
yin hakan, dama can David ne matsalar kuma yanzu ta yi maganin shi ta hanyar sakar
mishi kud'i, tunda ta fahimci halin shi, sai ta ci maganin zama da shi. Daga ita
har Fatima yanzu hankalinsu a kwance ya ke sai walwalarsu suke kamar basu da
sauran damuwa. A halin yanzu zaman Fatima a gida shi ya fi tayar musu da hankali,
kullum cikin zulumin school d'in da Al'ameen zai kaita su ke yi. Joy har ta fi
Fatima shiga damuwa da tashin hankali a kan hakan, zama suka yi suka yanke shawarar
zasu same shi su bashi hakuri a kan ya barta ta ci gaba da zuwa tsohon school
d'inta kar ya canja mata.

Har daki suka same shi, karo na farko da Joy ta fara shiga d'akin shi, sosai ta
yaba da kyawun d'akin duk da ba wasu abin azo a gani ne a ciki ba, yar katifarsa
ce, sai karamin wardrobe na kayan shi, sai yar duruwar da yake zuba littafai, sai
hanga dake sama ta bangon gabas d'in dakin,sai ko dan tarkacen da baza'a rasa ba,
iyakarsu kenan sai dai ko ina tsab kamar ba d'akin namiji ba sai daddad'an kamshin
room freshener ke tashi.

Yana daga kishingide cikin damuwa, ya yi nisa cikin duniyar tunani, suka yi
sallama sanye yake da singlet da short kasancewar a kwai zafi a garin ga babu wutar
nefa, ga dai hadari d'ankare a sararin samniya, amma kuma rana ake kwallarawa
kasancewar daminar na gaf da wucewa, ganin su yasa ya yi sauri ya ja bargon dake
kan katifarsa ya rufe daga kwankwasosa zuwa k'asa, ya ta shi ya zauna da kyau
fuskarsa babu walwala saboda yanayin damuwar da ya kwana ciki. Bakin katifarsa
Fatima ta laluba ta zauna, Joy kuma ta zauna daga gefenta a k'asa, kallo d'aya ta
mishi ta d'auke kai ganin shi sanye da singlet gaba d'aya surar mazantakarsa a
bayyane ga wani kwantaccen bakin bashi luf a kirjinsa, duk sai ta ji wani iri a
jikinta, hakan yasa har suka gama gaisawa bata iya d'ago kai ta sake yi masa kallo
na biyu ba, sai da ta tsinci muryar Fatima na cewa; Yayana dama Joy ce ta ce na
rakota tana son yin magana da kai. A zabure ta dago jin kullin sharin da Fatima ta
mata, dai-dai lokacin ya mai da kaifaffun idanunsa kanta, carat idanuwansu ya
sark'e da na juna, da wani irin sauri ta kawar da kai don ji ta yi gabanta ya yi
wani irin fad'uwa, zuciyar ta kamar zata faso kirji ta fito, Fatima ta zungura da
itama tsabar kwarjinin shi yasa ta kasa fadar bukatarsu kai tsaye. Dagowa Fatima ta
yi ta kalleta, Suna hada ido ta watsa mata harara tare da yi mata kallon ya zaki
mini haka, alamar ki fad'a ma shi, Fatima ta mata da ido, ta sake watsa mata harara
tare da make kafad'a ta mata alamar ke ki fad'a.
Duk abin da suke yana kallonsu, ganin suna neman 6ata masa lokaci yasa ya yi gyaran
muryar duk d'ogowa suka yi suna kallon shi, idanunsa a kan Joy ya ce "Uhummm!
FARHAT ina jin ki." Cikin inda-inda ta ce "Daa da dama! Mun zo ne, mu rok'e ka a
kan ka yi hakuri kabar Fatima ta ci gaba da zuwa school, kar ka canja mata wani'
ko Fatima ai haka ne ko?" Ta fada tana kallon Fatima da sauri Fatima ta girgiza kai
ta ce "E, e, Yaya haka ne don Allah ka yi hakuri ka bar ni na ci gaba da zuwa can
d'in."

Duk da yanayin damuwar da yake ciki sai da suka so ba shi dariya; ji yadda suke abu
kamar uban wani ya turosu, ba su suka gama tsara abinsu ba, ji adanun Fatima kamar
wacce ta yi wa sarki k'arya, ita kuma kawar cin mushenta ji nata kwala-kwala kwalan
idanun kamar fitulun mota.

A zuciyarsa yake musu wannan tsiyar, dakewa ya yi ya ce, to shikenan na ji kuje sai
na yi shawara, har suna had'a baki wurin cewa "To Yaya mun gode."

Suna fitowa "ta zubawa Fatima dundu ta ce " Haka muka yi dake Teetee." Dariya
Fatima ta saka ta ce, "To ni kasa fad'a na yi yasin kwarjini ya min." "To kema
kenan ina ga ni, amma sai naga kamar bai dauki maganar mu da mahimmanci ba." Fatima
ta ce "Wallahi kuwa, tunda kika ji ya ce haka, amma nasan abin da zamu yi da Ummi
zamu hada shi nasan idan ta saka baki idan da yuwuwar ya bar ni zai bar ni."

Da kyar Ummi ta amince musu zata mishi magana, sai da suka yi ta magiya da bambaki!
A ranar kuwa daya dawo da dare ta tuntu6e shi da zance, kallon Fatima ya yi da ta
yi saurin yin k'asa da kai ya jefe mata kallon tuhuma, Ummi ta ce "Amintacce kai
na ke sauraro, idan da yuwuwar hakan don Allah ka barta ta koma can d'in su k'arata
tunda sun kusa kammalawa." Jim ya d'an yi kafin ya ce "To Ummi shikenan, ta shirya
zuwa Monday sai na rakata da kai na Allah yawa hakan shi ya fi alkhairi ya kad'e
fitina." Ummi ta amsa da "Amin ya Allah." Fatima kam washe baki ta yi tana dariyar
farin ciki, Al'ameen ya jefa mata hararar wasa, sake kyalkyalewa ta yi da dariya
tare da cewa; Thank u Yayana Allah ya faranta maka kai ma." A tare suka amsa da
Amin shi da Ummi.

Ummi ta ce "Wai ni kam Yaran nan ko kun ji mini motsin Amiratuwana, yau idan ban yi
karya ba kusan kwanan ta goma rabonta da gidan nan, Allah yasa dai lafiya."

Fatima ce ta dago da sauri tare da cewa "Yawwa Ummi tun ranar Asabar a hadda Aysha
ta ce min bata da lafiya wallahi na manta na gaya miki kwata kwata na sha'afa."

Tafa hannanye Ummi ta shiga yi tare da sakin salati. "Haba Fatima, yanzu tun ranar
Asabar aka gaya miki amira babu lafiya amma ki ce wai kin manta, Haba haba Fatima
amana bai ce haka ba, Amira ai ta wuce haka a gareki, don komin lalacewar giwa ta
fi karfin kwandon goro, wato yanzu kin samu Joy shikenan kin rabu da kowa ko?
Gaskiya banji dadi ba baki Kyauta min ba, ai hausawa sun ce ka gaida mai gaisheka
ko ba zai amsa ba." Haka Ummi ta yi ta mita tare da yi wa Fatima fad'a, can kuma ta
ce "Amintacce duba min karfe nawa idan dare bai yi nisa ba yanzu zan shiga na dubo
ta yarinyar kirki, ai ko iyayenta ma sai su zageni ba don Allah yasa mutanen arziki
ba ne."

Shikam Al'ameen shaf ya manta da batun wata Amira, zai iya cewa tun daga ranar da
wannan maganar ya shiga tsakanin su bai kuma saka ta a ido ba, agogon ya duba kamar
yadda Ummi ta umarta jin tana ta sake tambayar shi karfe nawa ya ce "Ummi goma da
rabi ta gota nasan yanzu sun kulle kofar gida ki bari da safe."

Badan ta so ba dole ta hakura, amma fa ranar Fatima taga fushin Ummi, itama duk ta
yi laushi jikinta ya yi sanyi tabbas bata Kyauta ba, gaba daya cikin yan kwanakin
nan Joy ta d'auke mata hankali ita ce kadai a rai da zuciyarta.
************


*AMIRA*


Tun daga ranar da Al'ameen ya nuna baya da ra'ayinta ta shiga matsanancin damuwa, a
ranar ta yi kuka kamar baza ta daina ba, har sai da ta kwanta zazza6i na kwana uku,
tun da ta tashi daga wannan zazza6in gaba d'aya ta canza, a hankali aka fara rasa
gane kanta, bata da aiki sai kuka sai tunani, kurmar karfi da yaji ta naimi komawa,
don tana iya wayar gari ta wuni ta kwana ba tare da ta cewa kowa uffan ba, lamarin
da ya fara d'aga hankalin ahlinta, wa'ec d'in da suka fara bada ita aka kark'are
ba, sosai Maman Amira ta shiga damuwa duk a tunaninta iskokai ne suka shigeta,
hakan yasa kullum cikin tofa mata addu'o'i take da amso mata taimako a wurin
malamai, amma a banza lamarin sai dad'a gaba ya ke yi, wani irin rama da mugun
haske ta yi cikin abin da bai fi wata guda ba, kusan sau uku suna zuwa asibiti
ganin likita maganar daya ce kullum; damuwa ce ke damunta." tambayar duniyar nan
ta k'i fad'awa kowa damuwar, sai dai ta ce ita babu wani damuwar da ke damunta, har
kuka mahaifiyarta ta yi mata ta yi magiyar ta yi nasihar ta yi fad'an akan ta gaya
mata matsalarta amma a banza, hakan yasa Maman ta k'ara gaskata zarginta na cewa;
Iskokai ne suka shigeta.


Da farar safiya Ummi ta yi wa gidan su Amira dirar mikiya, lokacin ko Al'ameen bai
dawo daga masallaci ba, wasu masallatan ma ba'a idar da sallah ba, itama tana
sallame nata ko tasbihi bata yi ba ta tashi, don jiya dakyar ta yi barci saboda
damuwa da tunanin halin da Amiranta ke ciki, yarinyar kirki, babban abin da ya
k'ara d'aga mata hankali bai wu ce mummunar mafarkin da ta yi a kan ciwon Amiran
ba, kwarai ta tsorata da lamarin, don ita kanta tana tsoron mafarke mafarken da
take yawan yi a cikin yan kwanakin nan.

Tsakar gidan babu kowa, duk su na d'aki, a k'ofar d'akin Maman Amira ta yi sallama,
Aysha ce ta fito tana amsawa, ganin Ummi yasa ta yi saurin risinawa ta gaisheta,
ummi ta ce "Ina gajiya Aysha ya mai jiki." "Alhmdllh Ummi tana samun sauk'i."
Kafin Ummi ta ce wani abu Maman amira ta fito daga d'akin sanye da hijabi hannunta
r'ike da carbi, murmushi ta sakar wa Ummi tare da cewa "Maraba da Ummi ke ce da
farar safiyar nan, ina kwananmu ya kwanan iyalai." Ummi ta ce "Ni ce Maman Amira,
ya mai jiki, wallahi ban ji sai jiya da dare, da nake cewa yara nikam kwana biyu
banga Amira ba, shine Fatima ke ce min wai bata da lafiya, wallahi hankalina ya ta
shi, ba dadon dare ya yi ba da a daren zan shigo na duba ta, a addafe na yi barci
jiya wallahi." Ta karashe maganar cike da alhini da tausayawa. Maman Amira ta yi
murmushin karfin hali ta ce "Allah sarki Ummi Kiyi hakuri wallahi nima harda laifi
na da ban aika miki ba lamarin ne da rikitarwa." Ta fad'a damuwa bayyana k'arara a
fuskarta ta, hakan ya k'ara daga hankalin Ummi, "Ki shigo daga ciki gata nan."
Maman Amira ta fad'a tana juyawa cikin d'akin da sauri tare da d'auke dan guntun
hawayen da ya zubo mata ba tare da ta bari Ummi ta gani ba.

Salati da sallallami Ummi ta saka a lokacin da ta yi arba da Amira kwance a kan
gadon Mama tana barci, wanda sai gabanin asubahin nan ya dauketa cewar Mama "Na
shiga uku ni Balkisu! Mai zan gani haka." Sai kuma ta fashe da kuka tana maimaita
kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, allahumma ajirni fi musabati wa aklifni
khairan minha!" Ganin tana neman fad'uwa yasa Mama saurin rikota tare da zaunar da
ita a bakin gadon.

Kuka Ummi ta yi sosai, Mama na rarrashinta cikin karfin hali da danne zuciya, bayan
ta tsagaita ta dago ta kalli Mama tare da cewa "Hafsatu mai ke damunta haka?" Take
Mama ta kwashe komai ta gaya mata ba tare da tare da rage ta da komai ba, itama dai
aljanan ta fi baiwa karfi, don ko kusa babu wanda zai kawo wani tunani makamancin
soyayya a cikin lamarin. Addu'a Ummi ta sauna ta dinga tofa mata har wuraren bakwai
na safe, har zuwa time din bata farka ba, sallama Ummi ta musu a kan zata je gida
ta dawo..........


Dan Allah Ku yi hakuri da jina shiru kwana biyu Mamana ce bata ji dadi ba, bana
samun zama bare nayi typing dan Allah Ku sakata a addu'a. Ku ci gaba da hakuri da
ni littafin Joy yanzu ya fara dadi, Ku dai Ku ci gaba da bibiya.

Yan group d'ina *Joy Novel Fans* ina Godiya da addu'o'inku ga Mamana Allah ya amsa,
Allah ya sake muku da alkhairi ina matukar Alfahari da ku.

Kar a manta da comment and share pls๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™


09116099486.
[12/29, 2:45 PM] AyshaNalado: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *JOY* ๐ŸŒ€๐ŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 31*




No editing๐Ÿ™

Ko da Ummi ta shiga gida da Al'ameen ta fara cin karo a tsakar gidan yana wanki, a
kid'ime ta fara labarta masa rashin lafiyar Amira, ta k'are da, cewa; Wallahi
Amintacce na tsorata da ganin yarinyar nan, hankalina ya tashi, da da k'arar kwana
da sai dai na ji mutuwar ta." Ta kai karshen maganar tana matsar kwalla, sosai ya
kid'ime da ganin hawaye na kwaranya a idanun ta. Ummi jaruma ce, abin da zai
sakata zubar da hawaye haka lallai ya kai abin tausayi, rik'e hannunta ya yi ya kai
ta falonta ya zaunar da ita, ya shiga bata baki a kan ta yi hakuri ta yi shiru cuta
ba mutuwa ba ne, ta ce "Yayan Fatima dole na koka, kar kaso kaga Amira."
Rarrashinta ya ci gaba da yi, har ya samu ta yi shiru, Fatima kam jikinta ne ya yi
sanyi tun lokacin da ta ji Ummi na labartawa Yayanta halin da Amira ke ciki, hakan
yasa ta lafe a kitchen ta kasa fitowa.

Ranar yini Ummi ta yi zirga-zirga tsakanin gidanta da gidan Maman Amira, babu irin
tambayar da Ummi bata mata ba a kan damuwarta amma kamar yadda ta saba ta k'i
fad'a, da Ummi ta dame ta da tambaya, sai kawai ta fad'a jikinta ta rungumeta ta
fashe da kuka, hakan ya k'ara sanyayar ma Ummi da gwiwa kwarai. Fatima ma ta shiga
ta duba ta, sai da ta yi kwalla itama.

Kamar yadda Al'ameen ya yi alkawarin ranar Monday zai kai Fatima makaranta hakan
ko aka yi, ranar ita da aminiyarta sun yi farin ciki kamar babu gobe, dan kar Mom
ta sani yasa Joy ta laftawa David kud'i, ai kam ji kake tsit! Mallam ya ci shirya.


A bangaren ciwon Al'ameen, babu abin da ya canza, sai ma sake ta6ar6arewa da
lamarin ya yi, kusan kullum a cikin damuwa ya ke, sai dai koda wasa bai bari Ummi
da Fatima sun fahimta ba , don baya son abin da zai d'aga musu hankali, haka ya ci
gaba da shan overdose d'in maganin shi, don a halin yanzu ba shi da wata mafitar
data fi wannan, abin da ya fi d'aga hankalinsa a yanzu bai wuce yadda, ciwon ke
yawan tayar mishi a kowani irin lokaci ba, babu dare babu rana babu safiya, hakan
na nufin ya kai stage 5 kenan a jikinsa, hakan yasa ko ina zai ce maganinsa na tare
da shi saboda tsaro.

Sau biyu Ummi na kama shi yana kokarin shan maganin, hakan ya firgita shi, sai dai
ya yi mamakin yadda bata tambaye shi na menene ba, itakam har ga Allah bata kawo
komai a ranta ba don ta yadda da tarbiyar da ta yi ma shi d'ari bisa d'ari.



Ana cikin wannan halin Aliyu ya dawo,
A ranar ya kira Al'ameen ya sanar mi shi da shigowar shi Niger, kuma a ranar yana
ajiye jaka a gidan ya yi wanka ya yi wa gidan su Al'ameen tsinke, don lamarin shi
ya tsaya ma shi a rai a kulli yaumin da tunanin shi yake kwana yake tashi.

Da yammaci ne misalin karfe biyar da rabi, Aliyu ya iso unguwar Abayi, bai tsaya an
yi mai iso ba, ya yi sallama ya shiga don yana son gaisawa da Ummi, babu kowa a
tsakar gidan Fatima na islamiyya, Ummi na d'aki.

Sake rafka sallama ya yi, daga cikin daki Ummi ta amsa mashi, tare da mikewa ta
fito tana cewa; Muryar wa nake ji haka kamar Ali gadanga." Ta karashe maganar tana
rike ha6a lokacin data yi arba da shi, risinawa ya yi yana murmushi ya yi ya ce "E
Ummi ni ne, Ina wuni." Cike da fara'a ta ce "ina gajiya Aliyu muatanen kano saukar
yaushe?." Ba tare da ya mike ba ya amsa da "D'azu Ummi." Ta ce "Masha Allah shine
barka zauna ka huta ba ka kamo hanya, to ya ka bari yan cen, fatan an iske mutanen
gida lafiya." "Lafiya kalau Ummi duk suna gaishe ki." "To madallah! Ina amsawa, ina
yawan samun sakโ€™on gaisuwarka wajen Yayan Fatima, har ya ce zai hadโ€™a mu a waya
Allah ba nufa ba." Ya ce โ€œAllah sarki! Haka ne dama komai sai Allah ya soโ€ "mikโ€™e
Aliyu ga kujera ka zauna, dโ€™aki zafi sun dauke wutar su." Ta karashe maganar tana
nuna mashi kujera yโ€™ar tsuguno. Zama ya yi, itama ta dโ€™auko tabarma ta shimfidโ€™a
ta zauna tana cewa; ga shi Fatima bata dawo makaranta ba da tsoro maka ruwan sanyi
amma nasan tana hanya.โ€ murmushi ya yi ya ce " Ba komai Ummi yanzu ma masha ruwa
kafin na shigo." Hira suka shiga yi da Ummi cikin sakin jiki da sabo, da alamar a
kwai shakuwa a tsakanin tun ba yanzu na, kusan rabin hirar ta Amira ce, Ummi ke
mashi, duk da baisan yarinyar ba ya tausaya mata sosai, ya yi mata addu'a da fatan
samun sauk'i.

Fatima ce ta yi sallama ta shigo ganin Aliyu yasa ta sakin fara'a ta ce "Laaa! Yaya
Aliyu Kaine a gidan namu yau." Murmushi ya saki a ransa yana mamakin girmanta ya ce
" Ni ne Zahra, kin dawo ya makaranta?" "Alhmdllh Yaya ya su Umma da su Aziza, da
sauran yโ€™an uwa?" "Duk suna gida na baro su k'alau." "Madallah! A gaishe su."
"Insha Allah zasu ji."

"Maza ki ajiye jaka ki amso mi shi ruwan sanyi."

17 / 23