Author : Aysha Nalado Category : African Stories & Novels
ji daga gareshi ba, shine ta ce idan ya dawo na tuna masa." Kallon Al'ameen
Ummi tayi dai dai shima ya kallota suka hada idanu, da sauri ya sauke kai. Ta ce
"Yayan Fatima idan da hali ka koya mata dan Allah, Amira yarinyar kirki ce." Shiru
yayi kadan kafin ya amsa da "Toh Ummi." Sannan ya dago ya kalli Fatima ya ce
"Fatima ki CE mata gobe idan na dawo da daddare tazo sai mu fara karatun." Yana
kallon Ummi ta gefen ido yadda fuskarta ta yalwatu da fara'a. Fatima ma taji dadi
don ba karya tana son Amira kamar dai Ummi.
*******
Washegari Sunday da sassafe Mom ta fito da trolley dinta, cikin shirinta na tafiya,
sai da ta daidaita komai batta driven da zai kaita airport yana zaune a mota yana
jiranta sannan ta nufi dakin Joy, tura kofar tayi da karfi, taga ya bude, bata
zaci a bude kofar ya ke ba, shiga ta yi, a kwance ta sameta idanunta a rintse kamar
mai barci sai dai ba barcin take yi ba, hasalima jin motsin mom din ne ya saka ta
rintse idanu, tsayawa a kanta Mom ta yi ta kare mata kallo, sai da tayi mai isarta,
sannan ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce "Daughter zan wu ce." Sai lokacin
Joy ta bude kumburarrun idanunta amma bata ce komai ba, Mom ta sake cewa "Ba yan
school ban lamunce miki zuwa ko ina ba, zuwa anjima Madame Esther zata zo ta zauna
dake kafin na dawo." Daga haka ta juya ta fice Joy ta rakata da kallo.
Bani da isasshen lahiya banyi editing๐
Ga masu bukatar shiga group Ku tuntubeni.
9116099486
[12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: ๐๐ *JOY* ๐๐
~FARHAT~
*PAGE 17*
Tana tsaye jikin windon d'akita tana kallo har motar Mom ya bar compound d'in
gidan, ko kad'an bata ji wani damuwa ko alamar kewa a zuciyarta game da tafiyar Mom
ba , sabanin hakan sai ma wani irin sanyi da farin ciki ta ji yana huda zuciyarta,
wani tsalle ta daka tare da fad'awa kan tattausar katifarta, yau jin ta take yi
kamar sakakkiyar tsuntsuwa, rasa irin murnar da zata yi yasa ta ci gaba da jumping
akan bed d'in tana tambul da adungure, sai da ta ji ta fara gajiya ta dakata tana
sauke numfashi, bayan ta dan huta daga tsalle tsallen murnanta, ta mik'e ta fad'a
toilet ta shek'a wanka, tana yi tana wake wakenta alamar cikin farin ciki take,
gaban mirror ta tsaya daure da mini tawul, tana kallon fuskarta, Zum6ura baki tayi
ta kwa6e fuska, bayyane ta ce "Ji duk yadda nayi baki kamar bani ba, duk Mom ta
gama ramar dani da jidalinta." Kwafa ta yi ta harari mirron kamar dai Mom d'in na
cikin madubin ne, kallon kayan kwalliyar dake shake kan mirron tayi sai kuma ta
saki murmushi ta ce "Bari nayi wa My Teemah kwalliya." Kujera ta ja ta zauna,
cikin gwanancewa ta shiga fesa kwalliya a kwakkwayar doguwar fuskarta.
Bata cika yin makeup ba, shi yasa duk sanda tayi yake zama special a fuskarta,
lallausar gashinta ta tattara tayi paking din shi gefe ta zubo da jelar ta gaba har
kafad'unta, ta yi kyau sosai matuk'a gaya kamar wata y'ar tsanar roba. Mik'ewa tayi
ta isa gaban wardrobe din ta ta wangale kofofin shi, tsayawa tayi tana kallon
kayyayyakin ciki, kaya ne shake a ciki ba na wasa ba, wasu ma batta taba sakawa ba
sai dai duk kanana ne babu wani na mutunci a ciki, idanuta ne sauke akan wani kaya
da Papa ya taba kawo mata daga America lokacin da yayi wani tafiya, kaya ne masu
matukar kyau da tsada irin ta yayan masu jajayen kunnuwa, bata taba sakawa tunda
ya bata ta jera su a sif, zarowa ta yi ta warware kayan. Straight skirt ne mai
dauke da dogon tsagu ta baya red colour da riga karami mai hannun bes White
colour mai V neck a gaban rigar an rubuta JOY cikin wani irin design mai kayatarwa
ya sha stone sai walwali yake, sai dan karamin jaket kalar skirt din, iyakar shi
kasan boobs yana da igiya daga kasa da za'a d'aure ta gaban.
A tsanake ta shirya cikin kayan tsab! Duk da kasancewarta bera dan yanzu take
shiga sha biyar hakan bai hana kyakkyawan surarta kayatuwa cikin shigar ba,
siririyace sosai sai tsayi, sai dai akwaita da faffadan gudu, hakan yasa take da
shape kayatacce, idan ka dauke hakan babu wani abu jan hankali a jikinta, dan y'an
boobs dinta basu fi girman lemon tsami ba samsam basu da girma shiyasa bata fara
saka bra ba.
Takalmi half cover ta saka fari ta daura agogo a tsinstiyar hannunta, daga haka ta
fito daga d'akin ta da sauri har tana had'awa da d'an gudu, direct get ta nufa ko
tsayawa ta yi breakfasts ta kasa, sai dai tana isowa, d'aya daga cikin security
d'in dake bakin get, ya ce "Miss kiyi hakuri madam ta ce kar a bari ki fita, in dai
ba school zakije ba." Bata san lokacin da ta kwaso wani irin mugun kallo ta watsa
mashi ba, take ta fusata kasancewarta dama gwanar saurin fushi babu wuya ta hassala
sai sai tana da saurin sauka. A tsiwace cike da gadara ta ce "Na ce Ku bud'e min
get zan fita." K'asa yayi da kai ya ce "I'm sorry Miss sai dai Ki kira madam ki
sanar mata." A tsawace ta ce "Bazan kirata ba! kuma ina umartanka da ka bud'e min
get kokuma yanzu wallahi a bakin aikin ka." Tsorata yayi ganin yadda ta ke huci yar
karamar yarinya da masifa kamar wata babba, shikam bazai so abinda zai raba shi da
wannan aikin daya samu mai maik'o ba, jiki na rawa ya shiga bata hakuri, ko kallon
banza bai isheta ba, dsauri ya bud'e mata karamin kofar yana mata a dawo lafiya
tana fita ya lalubi lamabr Mom don ya sanar mata, sai dai wayar tak'i shiga
kasancewar jirgin su ya riga ya lula.
Sai da ta fito gida sannan, ta ji wani tsoro na shirin kamata sabanin da da take
cikin farin ciki, da wani ido zata kalli Fatima, da Ummi, uwa uba Yaya
Al.......kasa karasa tunanin tayi don bata fatan hakan takasance fatan ta Allah
yasa zuwa yanzu baya gida, duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ta yi,
karfe goma har ta gota, ta tabbata zuwa yanzu ya fita, dakewa tayi ta ci gaba da
tafiya.
Tana kusantar gidan gabanta na faduwa, duk taku daya karfin bugun zuciyarta na
karuwa, sanda ta fara hango gidan ji tayi kamar ta koma saboda yadda zuciyar ta ke
luguden daka kamar zai fado kasa, ita kanta baza ta ce ga dalili ba, ta san dai ba
tsoron Fatima ta ke yi ba, haka Ummi akwai kyakkyawar alaka ta mutunci a tsakanin
su, dakewa tayi ta karasa kofar gidan, babu kowa a layin kasancewar shi karamin
layi.
A hankali ta tura kofar gidan ta shiga da sand'a kamar barauniya, a haka ta wuce
kofar dakin Al'ameen ta isa kofar shiga cikin gida, la6ewa ta yi jikin bango ta
kasa shiga, can ta jiyo muryar kamar na Fatima tana magana hakan yasa ta leka kanta
a hankali.
Al'ameen na tsaye a bakin kofar dakin shi cikin shirin shi na fita ya na makala
links a hannun rigar shi, ya ji an turo kofar gidan, shiru shiru ba'a shigo ba, ba,
a koma ba hakan yasa ya dago kai ya kallo waje ta raga ragar net door din dakin
shi, mamaki ne ya kusa kashe shi lokacin da idanunshi ya sauka a kanta tana tafiya
cikin sand'a kamar wacce ta shigo sata, kwafa yayi a ranshi lallai yarinyar nan,
uwar me ta zo yi gidan su bayan irin wulakancin da sukayi wa Fatima, kamar zai
dakatar da ita sai kuma ya dakata yaga Iya rashin kunyar ta, yana kallo ta la6e a
jikin bango ta lek'a kai cikin gidan.
Shiru shiru bata d'ago ba hakan yasa Al'ameen yin gyaran muryar daga bayanta,
kiriss! Ya rage ta saki fitsari lokacin da sautin muryar shi ya ratsa dodon
kunnenta, da sauri ta d'ago kai ta zubawa kofar dakin shi idanu batta hango shi
saboda duhun net amma shi yana iya ganinta.
Bud'e net door d'in yayi ya fito fuskar shi a had'e kamar hadarin gabas, Sai
lokacin ya samu damar ganinta da kyau, wani irin wulakantaccen kallo ya shiga wurga
mata ganin irin dressing d'in dake jikinta a rayuwarshi ya tsani yaga mace da
shigar banza koda kuwa arniya.
Shesshekar kukanta da ya ji yasa ya kai kallon shi ga fuskarta, zaraf idaunsu ya
sarke dana juna, a tare zuciyoyinsu ya yi wani irin girgiza, bude baki ta yi da
nufin yin magana, da sauri ya daura hannunta shi akan leben shi ya ce mata
"Shiiiii!!!." Tsit! tayi tare da hadiye shesshekanta tana wurwurga manyan idanunta
da suka kada saboda tsorata.
Ya sake yi mata alamar ta zo ta fice da hannu, baya son ya yi magana ne don yasan
su Ummi na tsakar gida zasu jiyo su.
Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta fara takowa, ta gaban shi ta bi ta fice
daga zauren, minti biyar ya dauka kafin bayanta yabi bayanta, tunanin shi zuwa
lokacin ta dan yi nisa da gidan, sai dai ga mamakin shi yana fitowa, ya tarar da
ita durkushe a kofar gidan tana sharar kwalla, ranshi yaji yayi mugun baci, wato
bata tafi ba kenan don rainin hankali, a hasale ya daka mata tsawa " keeee!" A
zarane ta dago ta watsa mai idanunta da suka fara sauya launi, take ya ji duk wani
karsashinsa ya tafi, kasancewar sa dakkaken namiji mai dakakkiyar zuciya yasa ya
dake ya ce "Me ya kawo ki gidanmu." Shiru ba amsa sai sabbin hawaye dake sake
shatata akan dakalin fuskarta, ya ce "Ok na gane yau ma kin biyota har gida ne ki
sake ci mata mutunci kamar yadda rannan kuka ci mata matunci a gidan Ku keda
mahaifiyar ki ko?" Da sauri ta shiga girgiza kai cikin shirin fashewa da kuka, ya
ce "Kul! Kar ki min kuka a nan. Kuma ki bud'e kunnuwar ki da kyau ki saurereni,
daga yau sai yau idan na sake ganin wadan nan kazaman kafafunta naki a gidan nan,
hmmmm! Sai na lahira ya ciki jin dadi. Oya kafin in bude idanuna ki 6ace daga kofar
gidan nan, daga yau babu ke babu Fatima har abada." Rushewa ta yi da kukan da take
ta kokarin rikewa tun dazu, cikin magagi ta ce "Pls Yaya Alemin karka raba ni da
Fatima wallahi ba laifi na bane laifin Mom dina ne idan ka raba mu, zan shiga
tasananin damuwa ku yi hakuri da abinda ya faru rannan Ku yafe min." Ya ce "Ok
baza ki tafi ba ko? Ina zuwa." Ya fad'a yana shirin juyawa zuwa cikin Zaure, caraf
ya ji ta riko kafafun shi, wani irin shock ya ji a jikin shi wanda tunda yake bai
taba jin irin shi ba, hakan yasa yayi wani irin fusgar k'afunshi da mugun karfi,
har saida Joy ta fad'i tare da bige goshi da wani dutse.............
Na gode da addu'o inku gareni, na j sauki sosai hannu ma da sauki alhmdllh ngd
kwarai da kulawa.
Me bukatar shiga group din joy ya tuntubeni ta wannan Layin.
09116099486.
[12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: ๐๐ *JOY* ๐๐
~FARHAT~
*PAGE 18*
Yauma ba editing a tai ta hakuri๐
Ba tare da ya kula da fad'uwar da tayi ba ya shige zaure da sauri ya bugo k'ofa.
Zafin buguwar da taji yasa ta saki yar k'ara "Acchh!" da siririyar muryarta , hannu
ta kai ta dafe goshinta dai dai gurin da ta bige, danshi da ta ji a wajen yasa ta
dubawa da sauri, zaro ido tayi a tsorace ta ce "Jini! wayyo my Dad." Sai kuma ta
fashe da kuka tana yarfa hannaye, rabon da jini ya fita a jikinta irin haka har ta
manta, ji tayi ranta ya mugun baci da abinda Al'ameen ya mata sosai ta kullace shi,
dama tun farko bata ta6a mishi kallon mai saukin kai ba, kallon wani irin
murd'add'en mutum mugu mara fara'a take mishi, sai gashi yau ya tabbatar mata da
hakan, mikewa tayi ta kakkab'e jikinta ta na hawaye ta kama hanyar barin kofar
gidan.
Duk abin da take yi yana tsaye daga cikin duhun zaure yana kallo, ji yayi zuciyar
shi ya sosu, haka kurum kukanta ke ta6a mishi zuciya, irin abinda yake ji a duk
sanda ya ji Fatima na kuka ya dinga ji, gaba d'aya tausayinta ya ji ya kama shi,
idan ya barta ta fice haka, anya ya kyauta kuwa, Annbin Rahama ya hane mu rama
sharri da sharri, ya gamsu da irin soyayyar da ta ke yiwa yar uwar shi kodan wannan
ya kamata ya raga mata, da sauri ya fito ya biyo bayanta, lokacin har ta riga ta
bar kwanar gidan, sunanta yake son ya kira amma ya kasa, sau uku yana gwada bude
baki sai dai ya mayar ya rufe, hakan yasa ya k'arasa da dan gudu gudu ya isa
gareta, jin karan gudu daga bayanta yasa ta juyowa da sauri har zuwa lokacin kuka
take, daai dai nan shi kuma ya iso inda take, kasancewar tana cike da haushin sa
yasa ko d'ar bata ji ba sai dai ta kasa kallon fuskar shi ko da gigin wasa, a
gabanta ya tsaya sai kuma ya rasa me zai ce mata, samun kanshi yayi da zaro
handkerchief daga aljihun shi ya mika mata, kin Karba tayi sai ta samu kanta da dan
zumbura baki.
Zaro ido yayi ganin abin da tayi, sai kuma ya samu kanshi da sakin murmushi wanda
shi karan kanshi bai san ta su6uto ma shi ba, yarintarta yake gani karara idan tayi
wani abin San Fatima yake ganinta.
A hankali ya kai hannun shi fuskarta da nufin ya share mata hawayen, a razane ta
dago idanunta ta karaf! Ya sauka cikin nashi, wani irin lamari ne wanda tunda take
a rayuwarta bata taba tsintar kanta cikin shi ba ya afku da ita cikin abinda bai fi
kiftawar ido ba, sakone na zuciya wanda ke shiga ba tare da neman shawaran
mamallakinta ba bare izini.
Samun kanta tayi da Kasa janye idanunta daga cikin nashi duk da irin duguden da
zuciyarta keyi, shima bai dauke idanun shi ba a haka kuma bai fasa goge mata
hawayen da yayi niyya ba. Murmushin daya Dakar mata ne ya fargar da ita yanayin da
da ta shiga, da sauri ta kawar da fuskarta daga gareshi, tana jan numfashi da karfi
don ji ta yi numfashinta na shirin daukewa, bata dawo hayyacinta ba ta tsinci
muryar shi a kunnenta cikin shigar rarrashi yana cewa "I'm sorry! Ban yi don na
cutar dake ba." Maimakon ta amsa mishi sai kawai ta juya da gudu gudu ta bar shi a
tsaye rike da handkerchief.
Ya fi minti goma yana bin inda ta bi da kallo, shi karan kan shi bazai ce ga abinda
yake kallo ba, Me yasa ta wuce ta barshi ba tare da amsa mishi ba, ko dai bata
hakura ba ne, "Ya ilahi!" Ya ambata a baiyane. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yayi
amfani da dakakkiyar zuciyar shi wajen yi fatali da abinda raunatacciyar zuciyar
shi ke shirin ingiza shi a kai.
********
Lokacin da Amira ta samu sakon Al'ameen, ruwa ne kawai bata zuba a kasa ta sha ba
saboda farin ciki abin har saida da ya ba Fatima mamaki, duk da karancin Shekarunta
sai da ta diga mata ayar tambaya.
A daren ranar kuwa bata ko daga kafa ba tana idar da sallar isha sai gata dauke da
tarin littafanta, Al'ameen din ma shigowar shi kenan daga masallaci yana dakin sa
ko abinci bai kai ga ci ba. Yana jin sallamarta ya bata rai shi har ga Allah zata
takura mashi.
A gaban Ummi dake zaune a tsakar gida ta zube cike da girmamawa ta ce "Barka da
dare Ummi."Fuska a sake Ummi ta ce "Yawwa Amira maraba, har kin shigo karatun
ne?"Eh wallahi Ummi." "To madallah! Allah yayi jagora, shima Yayan Fatiman yanzu
ya shigo gidan."
"Allah sarki, to ko na koma in dawo anjima kafin ya gama kimtswa." "A'a yi zamanki
yar nan idan ya ganki zaune zaifi maida hankali ya kimtsa da wuri."Ta amsa da "To
Ummi."dadi fall ranta don dama ta dai fada ne kawai ba don ya kai zuci ba.Dan
waigeยฒ tayi, kafin ta ce "Ummi Fatima bata nan ne.". "Tana daki ina ganin sallah
take."
Hira su ka shiga ta6awa da Ummi, a haka Fatima ta fito ta same su. Da fara'a ta ce
"Laaa! Anty Amira har kin shigo." Ta ce "wallahi Fatima ba shigo." "To bari na
sanarwa Yayan yana dakin shi." Duk yana jiyo su a ranshi ya ja karamin tsaki, ya
rasa me yarinyar ta taka da suke rawan jiki da ita dhi shiga harga Allah bata
kwanta mashi a rai ba.
Sallamarta Fatima ya katse mai tunani, a dakile ya amsa mata don haushin Amira ya
shafe ta, tura net door din tayi ta shiga, ta same shi zaune yana latsa waya, da
zumudi a muryarta ta ce "Yaya Anty Amira ta zo karatu." bai dago yakalleta ba ya ce
"Na sani, ki kwaso littafanki kema Ku jirani tare zaki dinga karatun." Ta amsa da
" To Yaya." Yana jin ta tana gaya musu sakon shi. Said da ya kwashe minti sha
biyar kafin ya taso. Ummi ya gaisar, kafin ya samu guri ya zauna, a sanyaye Amira
ta ce "Ina yini Yaya Ameen." Sai lokacin ya kalli side din da take, ya amsa mata
da "Lafiya." Ummi ta ce "Fatima kawo mishi abincin shi yaci tukunna kafin Ku fara
karatun." Da sauri ya ce "A'a Ummi bari mu gama tukunna." Bata ce komai ba, ya
kalli Fatima da Amira ya ce "Ku matso" Matsowa sukayi ya kunna fitilar wayar shi ya
haska, ya dauki daya daga cikin papers na past question da Amira ta zo da shi ya
bude ya dan dudduba sannan ya dan kalleta ya ce "Bismillah ko." Da kyar ta iya
dagowa ta saci kallon shi, ta re da gyada kai.
A tsanake cike da baiwa da basida ya shiga yi mata bayanin kowani question dalla
dalla, duk da kasancewarta ba mai kaifaffan brain ba, tsaka tsakiya take, hakan bai
hanata dan ganewa ba, wai damma ta fi maida hankali ta akan kallon kyakkyawar
fuskar shi, tana sakin murmushi tare da kiyasto abubuwa da dama a ranta.
Sai gurin goma saura ya dakata, tare da rufe paper ya dago ya kalleta ya ce "Zamu
dakata a nan said Allah ya kaimu gobe, idan kina da tambaya kiyi akan abinda baki
gane ba." Da sauri ta girgiza kai, ya ce "ok shike nan gobe idan muka karkare
subject din ni zan miki tambayoyi tunda kince kin gane ko?" Ya karashe maganar da
tambaya da sauri ta sake gyada ka ya ce "To sai da safe." Ba don ranta ya so ba ta
amsa da "To sai da safe Yaya Ameen nagode sosai Allah ya saka mata da alkhaiti ya
baka mata ta gari." Ummi da Fatima ne suka amshi, shi kuwa