Author : Aysha Nalado Category : African Stories & Novels
yi
sallama d'auke da abincin karin kumallon shi a hannu, ga mamakinta a tsaye ta same
shi yana bin bango zai fito waje har ya kai bakin k'ofa.
"Subhanallah! Yaya ina zaka je?" Murmushi ya sakar mata, ya ce "Na gaji da zaman
d'aki ne k'anwata zan fita tsakar gida in sha iska." Kwa'be fuska ta yi ta ce
"Shine baka kirani in taimaka maka ba, idan ka fama ciwon ka fa?." Ta karashe
maganar tana k'ok'arin rik'e shi, ya ce "No Barshi Fatima zan iya, ki je ki
shimfid'a mini tabarma a tsakar gida." Cike da mamakin karfin halinsa ta ce "To
Yaya." Ta fi ce.
Kici kicin shimfid'a tabarman da ta ke yi ne yasa Ummi dake kitchen lek'owa "A'a
Fatima ya haka kuma?" Cewar Ummi sanin ba wai sun saba zaman tsakar gida da safe
bane.
"Yaya ne ya ce na shimfid'a mi shi zai fito yasha iska wai ya gaji da zaman d'aki."
Kafin Ummi ta ce komai sai gashi ya shigo da bin bango da dabara ya ke lalla6awa,
da sauri Ummi ta zo ta rik'e shi, ta na cewa "haba Amintacce, ai da ka yi magana
sai a taimaka maka." Da murmushi ya ce "A'a Ummi zan iya ai."
Ita dai bata yarda ba sai da ta rik'e har kan tabarman da Fatima ta gama
shimfid'awa ya lalla6a ya zauna, yana rintse ido lamar yana jin azaba, cike da
tausayawa Ummi ta ce "Sannu Yayan Fatima Allah ya sauwak'e, ka yi k'o'kari ma
wallahi zaman da'ki babu dad'i ga namiji, zaman dak'i ai sai mata, Allah dai ya ta
shi kafad'a yasa kaffara ne." Ya amsa da "Amin Ummi."
Kayan tea Fatima ta jera a gaban shi da flask d'in ruwan zafi ta shiga had'a mi
shi, kallon ta ya yi ya kalli Ummi ya ce "Ummi yau kuma tea zamu sha, babu kamun
ne." Ta ce "A kwai naga baka da lafiya ne, kamar zaka fi son shayin shiyasa na bada
kudi ta siyo buredi da sauran kayan hadin tunda shi kokon naga kayan fitsari ne."
Yamutsa fuska ya yi alamar baiso ba, amma bai ce komai ba, sai kallon Fatima da ya
yi ya ce "Sister ka d'an za ki hada shayin." Ganin yanayin shi yasa Ummi cewa "ko a
dama maka kunun ne? Naga kamar baka son shayin." Baya son bata wahala , sai kawai
ya ce "A'a Ummi ki barshi kawai zan sha." Kafin Ummi ta ce wani abu Aysha kanuwar
Amira, ta yi sallama a tsakar gidan.
A tare suka amsa mata, ummi ta ce "Aysha ke ce tafe." Ta ce "E ni ce, ina kwana
ummi ya mai jiki. " "Alhmdllh da sauki." Juyawa ta yi bangaren Al'ameen shima ta
gaishe shi tare da yi masa ya jiki, ya amsa da "
Alhmdllh."
Basket mai dan girma dauke da kuloli da flask ta fito da shi daga hijabinta, ta
ajiye gaban Al'ameen tare da ce wa "Yaya Ameen wai gashi, in ji Anty Amira ta ce na
kawo maka wai tana gaishe ka da jiki."
Share Aysha ya yi kamar bai ji abinda ta ce ba, wani banbarakwai ya ke jin lamarin,
amma yarinyar nan bata da hankali mai take tunanin Ummi da Maman Amira zasu zata
idan suka ga haka.
Ummi kam murmushi ta yi ta ce "Lallai an gaida Amira harda hidima haka ki ce mata
Amintacce yana godiya." Fatima murmushi take yi a ranta tana lallai Anty Amira kin
zurma da yawa Allah dai ya tabbatar da wannan lamarin.
Sallama Aysha ta yi musu Ummi ta ce "Tsaya ki amshi tukwuici." Tana kwance habar
zani da sauri Aysha ta yi hanyar waje ta na cewa "A'a Ummi wallahi ki barshi
nagode."
Yi ya yi kamar bai san an ajiye wani basket a gabansa ba, ya yi kicin kicin da rai,
Ummi ta kalle shi, sai kawai ta yi murmushi, ta ce "Fatima bude abincin nan mu
gani." Barin hada shayin ta matso ta fara cirowa kula guda biyu ne tuwo da miya,
sai jug, babban kulan ta fara budewa kosai ne an yi shi manya manya jan suya gwanin
sha'awa, ta bude karamin shi kuma farfesun kayan ciki ne a ciki da romo kadan sai
turiri yake da kamshin kayan yaji jug din kuwa kunun tsamiya ne hadadde shima da
zafin shi.
Rike haba Ummi ta yi, ta ce "Umm! Lallai Amira, to angode Allah ya yi albarka."
Kollonta ta kai kan shi ko kallon side din abincin bai yi ba, ta ce "Amintacce ga
abin kari in ji Amira." Ya ce "Angode kuci kawai Ummi, Fatima mikomin shayin da
kika hada."Ummi ta ce " Baza ayi haka ba Yayan Fatima, Binta dauko kofi da plate
ki zubawa yayanki abinci."
Mikewa tayi ta shiga kitchen ta dauko ta zo ta zuba mishi kunun da kosan zata zuba
farfesun Ummi ta ce "Bar wannan Binta ya ci anjima." Ta amsa da "To ummi." Tare da
mika mishi abincin gaban shi.
Dakyar da takurar Ummi ya dauki kosai daya ya yi bismillah ya kai baki ya gutsira,
babu laifi yaji dadin shi sosai bai san sanda ya tura guntun a baki ba, daga haka
ya shiga ci yana kora kunun sai ga Mallam Aminu ya kar kunu da kosai tas.
Ummi da ke mishi dariya a ranta ta ce "A kara ne?", yamutsa fuska ya yi ya ce "A'a
Ummi Alhmdllh."
Ummi da Fatima ne suka ci sauran ragowar kunu da kosan, farfesun kuwa Al'ameen aka
ajiyewa da rana aka dumama mi shi ya sha.
Makota na ta shigowa yi mi shi sannu da jiki baga mata da matasa tsararrakinsa ba
har da dattijan unguwa, domin shi din mutumin mutane ne, yana da kirki da yawan
gaisuwa, Maman Amira ma ta shigo haka kafatanin yan gidan gaba daya.
*************
*JOY*
Allah-Allah ta dinga yi gari ya waye ta je ta ga halin da Al'ameen ke ciki idan ba
haka ba zuciyarta zata iya tarwatsewa, sai dai gaba daya Daren ranar ya mata nisa,
dakyar ya iya jumirin jiran har bakwai da rabi ta yi.
Duk da tarin ciwon kan da take fama da shi, hakan bai hanata tashi ba, cike da
karfin hali ta yi wanka ta shirya cikin riga da wando kanana as usual, sakkowa ta
yi dining ko Mom bata jira ba ta yi breakfast din ta ita kadai duk da iya tea ne
kawai ta iya sha.
Dakin Mom ta nufa, ta tarar bata tashi ba, ji ta yi baza ta iya jira har sai
lokacin da ta farka ba, hakan yasa ta zauna a bakin godon ta shiga dan bubbuga
pillow, Mom ta bude idanu cike da barci ta kalleta, ganin yadda idanunta suke har
zuwa yanzu a rine gashi sun kara kankancewa fiye da jiya, saboda kwanan da ta yi
kuka yasa ta mikewa zaune cike da damuwa ta ce "Daughter, me yasame ki?" Ta kai
hannu tana tattaba jikinta, rike hannunta ta yi ta ce "Babu komai Mom tun kukan
jiya ne da na yi." "Amma Daughter ya kamata ace tunda kin yi barci kin farka
idanunki su dawo daidai ba wai su kara rinewa ba." Shiru ta yi ta rasa me zata ce
don kare kanta. "An ya kuwa lafiyar ki kalau, idan kina jin wani damuwa ki sanar
min muje asibiti." Girgiza kai ta yi, ta ce "I'm ok" "Well!" Mom ta faa tana gyara
kwanciya.
Langwabe kai ta yi ta ce "Mom ina son zanje landmark bookshop na duba wani story
book da nake nema, da ma wasu books din wadanda nake da su duk na gama karantasu."
Tsare ta da idanu Mom ta yi na yan wasu sakannni tana nazartanta, Hankalinta bai
kwanta mata da fitar ba, hakan yasa ta ce " Da sassafen nan haka? Ki barshi kawai
ba sai kinje ba, ki fadi sunan book d'in zan saka a naimo miki." "Ok Mom Thank
U." Ta fada tare da mikewa ta fice a dakin gudun kada kwallan daya ciki idanunta su
zubo a gaban Mom.
Sarai Mom ta ga yanayin da ta shiga hakan yasa ta kara gaskata zarginta akanta.
Da gudu ta fada kan gadonta ta rushe da kuka, ya ya zata yi? Ina zata saka ranta
ta ji sanyi? Wani hali Al'ameen yake ciki, shin kodai ya mutun ne da gaske kamar
yadda ta gani a cikin mafarkinta, yin wannan tunanin yasakata mikewa zaune zumbur!
Zuciyar ta ne ke Ingizata akan ta saci hanya ta tafi .
Da sauri ta mike tsaye da nufin tafiyar , sai kuma tsoro ya kamata, idan asirinta
ya Tonu Mom ta sani mai zai biyo baya, ta tuna sanda Mom ta juya mata baya lokacin
da ta gane tana mu'ala da Fatima, ko kadan baza ta so su koma gidan jiya ba, don
baza ta iya jura ba da wanne zata ji.
Komowa ta yi dabass ta zauna a bakin bed ta ci gaba da kuka.
Wani shawara ne ya fado ranta wanda ya sakata mikewa da sauri kamar an tsikareta,
da sauri sauri gudu gudu ta dinga saukkowa stairs, tana fitowa direct boy quarters
din gidan ta nufa, bangaren da wasu daga cikin ma'aikatan gidan suke kwana, a kofar
dakin Peter ta tsaya ta shiga knocking, da sauri ya fito ko amsa gaisuwar da yake
mata bata yi ba ta ce "Peter, ka taimakeni." Ta fada tana hade hannaye hawaye na
bin kumatunta, rudewa Peter ya yi, cikin rawar bani ya ce "Miss me ki ke bukata
kiyi hakuri ki daina kuka ko meye zan miki matsawar baifi karfina ba." Tunda ta
fara zayyano ma shi bukatar ta na tana son ya je gidan su Fatima ya dubo mata wani
hali Al'ameen ke ciki, ya ke bin ta da kallon tausayawa ji yake kamar ya zubar mata
da kwallah wannan wacce irin jarabta ce, a raunace ya ce "ki yi hakuri Miss na miki
alkawarin zan je na dubo miki shi, yanzu dana gama abinda nake yi."
Haka suka rabu da Peter ta koma cikin gida tana jiran tsammani.
Kamar yadda Peter ya yi mata Alkawari karfe goma sha daya a kofar gidan su Fatima
ya mi shi, kasancewar gidan ana ta shiga da fice na masu zuwa gaisuwa bai sha
wahala gurin sanin halin da Al'ameen ya ke ciki ba, shi kanshi ya tausayawa yaron
da fargaban yadda zai sanarwa uwar dakinsa wannna bakin labarin ya koma gida, bai
samu haduwa da ita ba a lokacin, sai wuraren karfe shiddan yamma suka hadu. Kallo
daya ya mata ya sauke kai, gaba daya ta fice a hayyacinsa kamar ba Miss Joy daya
sani ba, "I'm sorry Miss labarin babu dadin ji." Ya fada a sanyaye.
Wani irin Kwalalo ido waje ta yi tare da safe kirji a razane ta ce "Ya mutu
ko."............
09116099486.
[12/29, 2:42 PM] AyshaNalado: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*PAGE 27*
Wani irin gwalalo idanu waje ta yi tare da dafe kirji a razane ta ce "Ya mutu
ko?" Girgiza kai Peter ya yi ya amsa da "Bai mutu ba." "To mai ya same shi?" Ta
fad'a cikin shirin fashewa da kuka, Shiru ya yi yana nazarin mai zai ce mata don ba
k'aramin tausayin ta yake ji ba, baya so ya fad'a mata abin da zai tayar mata da
hankali, muryarta ne ya katse mishi tunani "Na rok'e ka kada ka boye min komai
Peter, sanin halin da yake ciki shine kwanciyar hankalina." Ba yadda zai yi hakan
yasa ya yi k'asa da kai ya ce "Na samu labarin cewa sanadiyar kad'e shin da muka
yi, ya samu targad'e a kafar shi ta hagu sannan......" Shesshekar kukanta ya saka
shi dasa aya, da sauri ya dago yana kallon ta, dama yasan za'a rina, an saci zanin
mahaukaciya.
Cikin muryar rarrashi cike da girmamawa matsayinta na uwar dakinsa ya ce "I'm sorry
Miss ki daina kuka zai samu sauk'i soon, naji labarin tun jiya an gyara kafar an
d'aure." Cikin kuka ta ce "Saboda mai ka ke cewa kar na yi kuka, bayan nice sanadin
raunatar shi? Me yasa bazan yi kuka ba? Kasan yadda na ke ji a zuciyata kuwa?" Ta
fad'a tana ta6a saitin zuciyarta, kasa ya sake yi da kai, tare da cewa "I'm sorry
Miss." Zuciyarsa gaba d'aya ta raunana, anya zarginsa bai zamo gaskiya ba kuwa? Ko
dai uwar d'akinsa ta fad'a soyayya da wannan yaron ne, domin lamarin ya fi gaban
tausayi kad'ai.
Daurewa ya yi dago ya kalleta tare da jeho mata tambayar da ke kai kawo a ransa,
"Miss Joy ar u in luv wit him?" Ya fad'a a d'arare.
Tsittt! Kukan ta ya d'auke, ta zuba ma shi rinannun idanunta na yan sakanni, can
kuma ta girgiza kai ta ce "Noooo! Babu wani abu makamancin haka a zuciyata game da
shi, kuma kar ka sake yi min irin wannan tambayar." Daga haka kuma ta juya da sauri
sauri gudu gudu ta bar gurin.
Ajiyar zuciya ya sauke ya san ta fad'i son ran ta ne kawai amma shakka babu tana
son yaron nan, shi daga ita har yaron tausayi suke ba shi, yasan wannan abu ne da
ba zai ta6a yiwuwa ba ko a tastuniya balle a zahiri. Alice fa! jinin Alice da
soyayya da musulmi tabbas akwai k'ura, shi dai zai saka su a addu'a shine k'adai
taimakon da zai iya mu su.
Ta d'auka sanin halin da yake ciki zai sama mata sauki a zuciya, amma ina! Babu
wani sauki sai ma k'ara mata damuwa da tashin hankali da ya yi. kamar jiya daren
ranar sai barci 6arawo ne ya sace ta bayan ta gama tsara yadda za ta yi gobe ta
samu fita ta je ta gan shi ko a sace ne.
********
*AL'AMEEN*
Kasancewar sa jarumi kuma sam ba shi da k'an jiki yasa nan da nan ya fara samun
sauki, a Washegari rana ta uku da samun tsautsayin ya soma taka k'afarsa, tuni
kumburin ya sa6e sai dan abin da baza a rasa ba.
A ranar ma haka Amira ta sake had'o lafiyayyan karin kummalo ta aiko ma shi. Sam
bai ji dad'i ba, a ganin shi ta cika zak'ewa, hakan yasa ya kuduri aniyar taka mata
birki, yau kam bai ci abincin ba duk irin magiyar Ummi, ya fake da cewa shi ba
cimarsa ba ne, shi kunun zai sha, kasancewar Ummi tasan hakan yasa bata tsaurara
masa dole sai ya ci ba. Wainar shinkafa ce da miyar taushe yaji tantakwashi da man
shanu, Ummi da Fatima ne kad'ai suka ci.
Yau kam a d'aki ya yi zaman shi bai fito tsakar gida ba kasancewar akwai wutar
nepa.
Wuraren karfe goman rana Amira ta yi sallama tsakar gidan, direct cikin gida ta
nufa don bata za ci yana d'aki ba, a kitchen ta samu Ummi, kamar kullum a mutunce
ta gaisheta tare da tambayar mai jiki.
Ummi ta amsa da "Mai jiki Alhmdllh yana samun sauki, sannu da hidima Allah ya saka
da Alkhairi Allah ya yi Albarka." K'asa ta yi da kai tana d'an murmushi ta ce "Amin
Ummi."
D'aukar tsintsiya ta yi ta tattare hijabinta tana "Ummi bari na tattara gidan naga
ba'a riga an share ba." Kallon ta Ummi ta yi ta ce "Kun gaisa da mai jikin ne?" Ta
girgiza kai tare da cewa "A'a Ummi." Ummi ta ce "kije Ku gaisa yana d'akin shi."
Ajiye tsintsiyar ta yi ta kama hanyar d'akin ,zuciyarta na dokawa da mugun gudu.
A sanyaye ta yi sallama a bakin k'ofa. Ya amsa mata yana daga zaune a bakin
katifarsa, duk a tunaninta zata tarar da Fatima a d'akin kamar ran nan sai dai ga
mamakinta shi k'adai ne zaune a sanye da singlet da dogon wando, kallo daya ta yi
masa ta yi saurin yin kasa da kai, take jikinta ya dauki rawa, kasa zama ta yi don
gaba daya gani take ya cika dakin tsabar kwarjini.
Shikam a tsanake yake kare mata kallo, Sam! Bata da makusa sai dai ita zuciya
ba'ayi mata tilas.
Ganin bata da niyyar yin magana gashi ta doje a bakin k'ofa ita ba ta koma ba ita
ba ta k'arasa shigowa yasa ya yi gyaran murya.
A diririce ta dago su ka had'a ido sai kawai ta zu6e gwiwowinta a k'asa a nan inda
ta ke tsayen cikin dan rawar murya ta ce "Ina kwana Yaya Ameen ya karfin jiki."
Maimakon ya amsa gaisuwarta sai ya cewa "Amm! Amira." Da sauri ta dago tare da
amsawa da "Na'am." Ya ce "Na ga sa'kon ki nagode, sai dai ina rok'on ki daga yau
kar ki sake wahalar da kanki wajen aiko min da wani abu ko yi min girki please
bana buk'ata, wani irin tunani iyayenmu zasu yi idan suka ga haka, to dan Allah
wannan ya zama na karshe, and maganar wasika shima daga yau na kashe please kar na
sake gani bana so, sannan ina mai jan hankalinki da ki zama mace mai kamun kai
domin mazan yanzu basu da tabbas wani zai iya yin amfani da wannan irin damar ya
sabauta rayuwarki.
Wani irin tafarfasa zuciyarta ya shiga yi, tun kafin ya dasa aya tuni hawaye sun
gama wanke mata fuska. Meye laifinta don ta nuna masa soyayya, dama duk tsawon
lokacin nan aikin banza take, Ashe kallon sakarya mara kamun kai yake mata, ji ta
yi zuciyar ta ya dake duk wani tsoro da kwarjinin daya cika mata ido ya kau. Dagowa
ta yi ta kalle shi, ta ce "Shin laifi ne don na nuna maka soyayya da kulawa, ka
sani nima ba yin kaina bane kuma bani na daurawa kaina ba, don Allah na rokeka ka
daina min kallon sakarya mara kamun ka wallahi ba haka na ke ba, sannan don Allah
ka ta ya ni da addu'a Ubangijin daya sanya mini soyayyarka ya yaye min, na maka
alkawarin daga yau bazan sake gwada maka wani abu makamancin soyayya ba, zan yi
kokarina na taushi zuciyata, amma ka sani bazan daina sonka ba har karshen
numfashina." Ta kai karshen maganar tare da fashewa da wani irin kuka wanda ya taso
mata daga can k'asar zuciya, to she bakinta tayi da hijabinta saboda kar sautin
kukanta ya fita har Ummi ta jiyo ta da sauri ta mike tare da ficewa daga dakin da
gudu.
Karo suka yi da Fatima a k'ofar d'akin, bata tsaya ba ta ra6a ta gefenta ta fice
daga gidan.
Kur!: ya kurawa hanyar da ta bi idanu, rana ta farko da wani abu mai kama da
tausayi game da ita ya tsirgar ma shi a zuciya, me ya aikata kenan ya salam! Ya
fad'a tare da dafe kai.
************
*JOY*
Safa da marwa kawai take yi a d'akin ta ganin karfe ukun rana ya gota babu wata
dama da ta samu na fita, babu irin tunaune da bata yi ba ciki har da da haura
katanga, sai dai ta san ko cikin maye take bazata iya ketare katangar gidan ba. Cak
ta tsaya lokacin da zuciyar ta ya hasko mata mafita "David." Ta fad'a a saman
lab'b'anta, da sauri ta rarumi wayar ta, ta lallatsa tare da karawa a kunne.
πππ kunya duk ta isheni na rasa da bakin da zan baku haΖuri ma yasinπ¬ π¬π¬ in sha
Allah hakan bazai sake faruwa baπππ Ku tayani da addu'a aljanun kiwar yin typing ne
su ka kusa sauka a kainaπππ
09116099486
[12/29, 2:43 PM] AyshaNalado: ππ *JOY* ππ