JOY by Aysha Nalado

Author :  Aysha Nalado Category :  African Stories & Novels

Chapter   22 / 23

63K to 66K   out of 68.8K words

ce "Tabbas na tabbar da idanuna na hango tsantsar soyayyar
Arniyar yarinyar na kwance a cikin kayan idanunsa dan Allah Zainabu ki bani shawara
ya zan yi wallahi zuciyata zata tarwatse."............



Afuwan masoyaπŸ™




Oum Ummeetarh
09116099486
[12/29, 2:49 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 40*


Mikiya Writer's Association


*Masu facebook ku yi following wannan account Ι—in domin samun damar cin giveaway
Ι—in da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa*

https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL



Kwantar mata da hankali Zainabu ta yi, tare da ba ta shawara a kan ta yi kunnen
uwar shegu da abin ta cire shi daga zuciyarta ta yi kamar bata fahimci komai ba
tunda dai hasashe ta ke yi bata da tabbas a kan lamarin. Cikin kuka ta ce "Wallahi
Zainabu da idona na gani ya rik'e hannayenta, suna bin juna da wani irin kallo,
kollon da bai ta6a yi mini irin shi ba, irin kallon da nake fatan samu daga gare
shi koda a mafarki ne. Ta6e baki Zainabu ta yi ya zuwa yanzu lamarin Amira ya fara
bata haushi, cike da jin haushi, ta ce " Ke dai Wallahi an yi raguwar banza, yanzu
haka ma fa ba abin da ki ke tunani ba ne shegen kishinki ne yasa ki ke ganin hakan,
ta yaya Ustaz kamar Al'ameen zai tsaya soyayya da wata arniya mai fistari a tsaye,
ai ruwa ba sa'an kwando ba ne, ni kam ko duk jikina kunne ne ban yarda ba."
Murmushin takaici Amira ta yi, ta na kallon Zainabu a zuciyarta tana cewa; Hmm!
Zainabu don dai ba ki san so ba ne shiyasa ki ke cewa haka, "Kallon fa?" Zainabu ta
fad'a tana dan zaro mata ido had'i da d'an hararanta, girgiza kai ta yi tare da
sakin murmushin yak'e wanda ya fi kuka ciwo.

Amira ta dauk'i shawaran Zainabu don kuwa koda wasa bata yarda ta yima Al'ameen
maganar Joy ba haka ma Fatima duk irin yadda abin ya tsaya mata a rai kuwa.

A haka tafiya ta mik'a a ka kwashe satittika, har zuwa lokacin kuwa Al'ameen bai
tura magabatansa wurin kawunnan Amira ba kamar yadda suna buk'ata kuma bai ce musu
komai ba, ganin shirun nashi ya yi yawa yasa d'aya daga cikin k'annen marigayin
mahaifin nata kiran Al'ameen har gida.

Tare suka shirya da Aliyu suka tafi gidan nasa bayan sallar isha'i, d'aya daga
cikin samarin gidan ya musu iso har falon kawu Basiru kamar yadda suke kiran shi,
bayan gaisuwa aka gabatar musu da ruwa da abin motsa baki, sai da suka d'an ta6a
hira da Aliyu kasancewar kawun mutum mai yawan magana sai dai mafad'aci ne na
karshe, haka ma Alin shima magananne ne ba laifi idan ya samu waje. Al'ameen kam
kansa na k'asa yana saurarensu gabansa na fad'uwa ya k'agu ya ji kiran me a ka yi
masa.

Sun dan d'auki lokaci a haka kafin kawu Basiru ya yi gyaran murya ya ce "Am!
Aminullahi." D'agowa Al'ameen ya yi ya kalle shi tare da sake yin k'asa da kai cike
da surukuta, "Abinda yasa na kira ka, mun ji shirunkaya yi waya, yau kimanin wata 3
da aka yi maka magana ka turo magabatan ka amma har yanzu shiru, to mun gaji da
gafara sa kuma har yanzu bamu ga k'aho ba, domin dai yarinya cikin y'an uwanta wani
ya ganta kuma ya nuna yana so , to kaga gida bai k'oshi ba ba'a kai waje ba, sai
dai kasancewar mu ba k'ananun mutane bane yasa jiya muka zauna ni da y'an uwana, a
kan maganar, yanzu dai an umarceni kasancewar nine k'arami a cikinsu suka wakiltani
a kan na kira ka na shaida maka, an baka nan da sati d'aya idan har da gaske ka ke
muji wani motsi idan kuma ba haka ba, to gaskiya komai zai iya faruwa, wannan shine
mak'asudin kiran da na yi maka da fatan ka fahimce ni."

Tun kafin kawu Basiru ya kai aya a maganarsa, tuni gumi ya tsatsafowa Al'ameen a
gaban goshi, banda dukan uku-uku babu abin da zuciyarsa ke yi, sai Aliyu ne ya yi
karfin halin amsawa kawu Basiru da cewa; Na'am kawu mun fahimta." Ya ce "Toh dama
kiran ke nan idan kuna da abin fad'i kuma ku fad'i ina saurara." Aliyu ne ya sake
amsawa da "A yi hakuri kawu, in sha Allah zaku ji mu kafin satin." Da haka suka yi
sallama da kawu basiru, Aliyu ya ajiye masa naira dubu uku suka fito.


Daga Alin har Al'ameen an rasa mai karfin halin cewa wani abu, har suka yi nisa da
k'ofar gidan, shi Aliyu ganin halin tashin hankalin da abokinsa ya shiga ne ya
sanyayar masa da jiki hakan ya tabbatar masa da akwai wata matsala, yayinda A
bangaren Al'ameen yake hasaro irin tashin hankalin da Ummi ta shiga ranar da ya
fara sanar mata da cewa; Iyayen Amira sun nemi ya turo, wannan na d'aya daga cikin
abin da yasa har yau bai sake tayar da maganar ba, bawai don ya rasa naira dubu
goman da za'a kai a matsayin kudin gaisuwar ba, kwarai ya hangi firgici da tashin
hankali a cikin kwayar idanunta, wanda har ya kai ta ga son yin su6ul da baka a
gabansa ta furta wasu kalamai da suka hana shi rintsawa a daren ranar.

Aliyu ne ya katse shirun da cewa; Abokina ya kamata fa ka yi wani motsi a kan
lamarin nan, ka dai ji abinda kawu ya fad'a, kar ka yi sakacin da zaka rasa Amira
domin na lura kiris suke jira shi yasa suka yi maka wannan daurin talalar, duk da
nasan kai ko da ta subuce makan ba damuwa zaka yi ba tun da ba wani sonta kake yi
ba" Ajiyar zuciya ya sauke, da wani irin sanyin murya wanda Aliyu bai ta6a jin ya
yi irinta ba ya ce "Aliyu ina son Amira, wallahi ina kaunarta ina fatan ta zame
mini uwar y'ay'ana, sai dai ina jin tsoron wani abu, ina ji a jikina a kwai
gagarumar matsala." "Wacce irin matsala? Aliyu ya jefa masa tambayar cikin dan
tashin hankali, cike da wani irin k'unci ya ce " Dangin mahai...." Sai kuma ya yi
shiru ya girgiza kai, Aliyu ya dafa kafadarsa ya ce "Dan girman Allah kar ka boye
mini matsalarka abokina, idan kamin haka zaka saka zuciyata cikin zullumi." Shiru
ne ya ratsa tsakaninsu na yan sakanni, kamar bazai ce komai ba, can kuma ya sauke
nannauyar ajiyar zuciya, kafin ya kwashe komai ya fad'awa Aliyu, shi kan shi Aliyu
abin ya so girgiza zuciyarsa, sai dai bai nuna hakan a fili ba, ya ce "Wannan ba
hujja ba ce da zai ka kasa sake tunkararta da wannan maganar, Ameen ka sani anzo
gabar da dole ne kusan su wanene ku." Wani irin kallo ya shiga bin Aliyu da shi
kamar ranar ya soma ganin shi a duniya, domin ya sosa masa inda ya dad'e yana masa
k'aik'ayi." Basu rabu ba sai da suka tsara yadda lamarin zai gudana.

Bai iso gidan ba sai wajajen k'arfe goma da rabi, kamar yadda ya zata a tsakar
gidan ya tarad da su, Fatima na kwance barci ya kwasheta yayinda Ummi ke
kishingid'e tana sauraran redio, ta amsa masa sallama tana mik'ewa zaune, tare da
gyara rik'on carbinta da gyangyadi yasa ya kusa subucewa daga hannunta.

"Barka da gida Ummi." Ya fad'a yana zama a gefen tabarmar, dan tsira mashi ido ta
yi ganin kamar yana tattare da damuwa kafin ta amsa masa da "Yawwa barka da dawowa
Amintacce." Ganin irin kallon da take binsa da shi yasa ya yi saurin yin kasa da
kai, gabansa na faduwa, ya ce "Fatima ta yi barci kenan." Ta amsa da "E ta yi da
kyar bayan ta gama dakon jiran ka, kazo ka ji mata hadda." Murmushi ya yi idanunsa
kan kanwar ta shi tare sa cewa; "Allah sarki yar uwata." Lamarin da ya saka Ummi
sakin murmushi ba tare da ta sani ba.


Bayan ya ci abinci ya fusakanci Ummi gabansa na wani irin dokawa yace "Ummi kawun
Amira ya kirani d'azu a kan yana son ganina." Dakatawa ta yi da kokarin canza
channel din da take kokarin yi ta zubawa fuskar shi manyan fararen idanunta masu
cike da kwarjini...........



Har kullum Afuwan shine abin da zan iya cewa gareku masoyaπŸ™



*Pls a ta6a comment domin shi ke saka min karsashin yi muku typing ko da ban yi
niyya ba*




Oum ummeetarh.
09116099486
[12/29, 2:49 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 41*


Mikiya Writers Association
*Masu facebook ku yi following wannan account Ι—in domin samun damar cin giveaway
Ι—in da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa*

https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL




Bayan ya ci abinci ya fuskanci Ummi gabansa na wani irin dokawa yace "Ummi kawun
Amira ya kirani d'azu a kan yana son ganina." Dakatawa ta yi da kokarin canza
channel din da take yi ta zubawa fuskar shi manyan fararen idanunta masu cike da
kwarjini, da sauri ya yi k'asa da nasa kan, tare da ci gaba da cewa; Ya bani nan da
sati d'aya in turo magabatana idan har da gaske na ke yi, idan kuma na wuce hakan
to za su aurad da ita ga wani dan uwanta wanda yake son ta." Har ya dasa aya bata
iya dauke idanu daga kallon shi ba, yayinda shi kuma ko da wasa ya kasa d'agowa ya
kalleta, Ajiyara zuciya ta sauke mai nauyin gaske, cikin sanyin murya ta ce, "Kar
ka damu yayan Fatima in sha Allah, gobe zan je na samu yan uwan mahaifinku duk da
sun min kyakkyawar kashedi a kan babu ni babu su kar na sake na sake ra6arsu yanzu
lokaci ya yi da dole na neme su domin su sauke hakkin nauyin daya rataya a
wuyansu." Ta karashe maganar cikin karyewar harshen, tare da sauri d'auke kwallar
da ta ciko mata idanu.


Hankali tashe ya d'ago ya kalleta, suna had'a ido ta yi saurin d'auke kai, don
bata son ya fahimci kuka take yi, sai dai tun a yanayin sautin muryarta ya fahimci
kukan ta ke yi, bata son ta ba shi damar da zai jeho mata wata tambaya hakan yasa
ta mi'ke da sauri ta shige d'akinta ba tare da sake kallon gefen da yake ba.

Gaba d'aya duk wani ga6a na jikinsa ya mutu, haka ya dinga sauke wani irin nunfashi
mai hade da kunci, ya yi zama ya kusa na awa d'aya a tsakar gidan nan ba tare sa ko
kwakkwaran mosti ya iya yi ba, shin dole sai sune zasu nema masa aure? Tun bai
mallaki hanakalin kansa ba ya san cewa; Yan uwan mahaifinsu basa kaunarsu, a she
dama dalilin da yasa Ummi bata yi musu zancensu kuma ta hane su da yin zancen su
kenan, me yasa zasu ce kada su ra6e su shin su d'in ba jininsu ba ne, shin ita Ummi
ina nata dangin suke? Tambayoyin da ya dinga kai komo kenan a cikin kwanyarsa, sai
dai bashi da mai bashi amsarsu.

Ya dade sosai a zaune kafin ya yi karfin halin mikewa ya tashi Fatima ta wuce daki
shi ma ya nufi nasa dakin bayan ya nade tabarmar.

Daren ranar ya jima kafin ya iya rintsawa, yayinda a bangaren Ummi yadda taga rana
haka taga dare, ta yi kuka sosai bayan shigewarta d'aki, rayuwarta ce ta baya ya
dinga dawo mata filla-filla, tabas ta yi rashin masoyi na hakika Al-hussain ya
kaunaceta ya tallafeta ya nuna mata hakikanin soyayya duk da irin yadda gaba d'aya
kafatanin danginsa su ke kin ta, kamar mujiya a cikin taron jama'a, sun yi mata
korar wulakanci tana tsaka da alhinin rabuwa da masoyinta, sai dai dole haka zata
sake tunkararsu a wannan ga6ar domin bata sa wadanda suka fisu bata san kowa ba sai
su.

Ta yi kuka sosai wanda rabonta da yin irin shi tun rasuwar marigayin mijinta,
dakyar ta danne zuciyarta ta mike ta dauro alwala, a kan darduma ta karkare wayar
gari ranar, Da safe haka ta wayi gari idanunta sun yi jajur sun kumbura, Fatima ta
tsorata da ganinta, sai dai yadda ta tsare gida sai ta kasa tambayarta me ya same
ta, hankalin Al'ameen ba karamin tashi ya yi da ganin ta ba, sai dai kamar yadda
Fatima ta kasa tambayarta haka shima ya kasa,jiki babu kwari ya shirya ya fice daga
gidan zuwa wajen harkokinsa.

Karfe goma da rabi ta gama shirinta tsab cikin riga da zani na atamfa ta sanya
hijab dinta gogagge mai matsakaicin tsayi, fes ta fito a matashiyar mace kyakkyawar
gaske mai cike da haiba da kamala, sallama ta yi wa Fatima bayan ta bar mata
sallahun abubuwan da zata gudanar a gidan kafin ta dawo.

Tafiyar mintuna ashirin a cikin a daidata sahu ya isar da ita unguwar mak'era, a
hankali ta dunfari babangidan mai dauke sa babbar k'ofa hadi da babban zaure.

Family hause ne mai dauke da dakuna masu yawan gaske, kai tsaye ta nufi cikin
gidan gabanta na fad'uwa sai dai ta dake, don babu alamun hakan a fuskarta.


Kasancewar safiya ce yawancin matan gidan na tsakar gida kowacce na gudanar da
sabgar gabanta, sallamar da ta yi ne ya janyo hankalin mafi aksarin jama'ar dake
tsakar gidan.

Kamar wata sabuwar halittta haka wasu daga cikin matan suka Shiga kallonta
fuskokinsu dauke da tarin mamaki, yayinda bakin fuskoki a gare ta ke binta da
kallon rashin sani.

D'aya daga cikin matan ne ta kasa jurewa sai da ta maganta, cikin tu'ajjabi ta ce
"Wa nake gani haka Lamar Balkisu? Na kusa da ita ce ta amsa da " Taya ni fada dai,
ashe ba gizo bane. Tsaki d'aya daga cikin su ta ja tare sa cewa; Allah ya wadaran
naka ya lalace, dai dai lokacin kuma d'aya daga cikin mazan gidan ya sawo kai jin
kananun maganganu na tashi daga matayen nasu wadanda dama kullum basu rabo da
hakan.

Turus ya yi da farko lokacin da ya yi arba da ita, sai dai daga bisani ya wani irin
hade rai kamar hadarin gabas, a kausashe cikin zare jajayen idanunsa ya ce "Meya
kawo ki gidan nan Balkisu, Ashe ba mun yi miki kashedi sake rabar inuwarmu ba, shin
ke mayya ce, to wallahi wallahi billahillazi la'ilaha illah huwa idan kika kara,
minti biyu a cikin gidan nan sai na yi miki mummunar lahani.

Wannan haniyar ta Yaya Al-hassan kamar yadda suke Kiran shi ita ta janyo hankalin
kafatanin sauran muatane gidan dake dakunansu, suka Shiga firfitowa d'aya bayan
d'aya.

Gyaran muryar da aka yi daga bayansu yasa duk suka maida hankali gurin, sabanin
Hassan fuskarshi washe ta ke da wani irin shu'umar murmushi, ............




Oum ummretarh

09116099486
[12/29, 2:50 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 42*


Mikiya Writers Association


*Masu facebook ku yi following wannan account Ι—in domin samun damar cin giveaway
Ι—in da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa*
https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL



"Ka barta Hassan, ka barta mu ji da me ta ke tafe." Yaya babba ya fad'a a
gadarance, cike da umarni, Al-Hassan dake huci kamar kububuwa ya juya ya kalli
inda sautin muryar d'an uwan nashi ke tashi, ya ce "Yaya ka yi hakuri ka barni in
ci mata mutunci, in wulakantata, kamar yadda na yi mata alkawari duk ranar da na
sake ganin kafarta a cikin gidan nan zan yi mata.

" Ka bari na ce Hassan" cewar Yaya babba, bayan ya k'araso kusa da Al-hassan d'in,
daga haka ya juya ya nufi falon shi ba tare da sake cewa komai ba, wani irin huci
Al-hassan ya dinga furzarwa yana bin Ummi da wani irin wulakantaccen kallo mai
dauke da tsantsar tsana, daga bisani ya juya ya bi bayan dan uwansa a fusace.

Jiki babu kwari Ummi ta k'arasa madaidaicin falon mai d'auke da satin kujeru da
k'aramar TV, guri ta nema ta zauna daga can gefe bayan tayi musu sallamar da
cikinsu babu wanda ya amsa mata.

Shiru ya ratsa falon na y'an wasu dak'ik'ai, Yaya babba ne ya katse shirun ta
hanyar cewa; Ke muke saurare Balkisu me ya kawo ki garemu, bayan mun riga mun gaya
miki babumu babu ke har abadan da'ima."

Dagowa ta yi ta kalle shi idanunsa kem a kan ta, yana binta da wani irin mayen
kallo kamar zai cinyeta da ido, da sauri ta d'auke kanta a zuciyarta tana neman
tsari daga sharrin shi, domin bata manta waye Yaya babba duk da shekaru sun ja.

Cike da fargaba da tsananin fad'uwar gaba, ta samo gabatar musu da abin da ke tafe
da ita, tun kafin ta k'arasa Al-hassan dake binta da mugun harara ya daka mata
tsawa, a kausashe ya ci gaba da cewa "Ban ta6a sanin ke dabba ba ce, a cikin
dabbobin ma tunkiya marar hankali ba sai yau Balki! Kina nufin ni ko d'aya daga
cikin ahlina ne za mujelup nemar wa shegun y'ay'anki aure? Lallai kwakwalwar kan ki
iri d'aya ne sak dana jaka shiyasa ta baki wannan shawaran na ki tunkare mu da
wannan maganar. To ki sani har gaban abada babu gamin mu da shegun y'ay'anki,
y'ay'an zina tsintattun y'ay'an kwararo........

" Ya isa Hassan ya isashe haka!!!" Ummi ta fada da wani irin murya mai kaushin
gaske, tuni idanunta sun juye sun yi jajur, ga hawaye da tuni ya gama wanke mata
fuska, Mikewa tsaye ta yi ta ci gaba da cewa a tswace "Kada ka kuskura ka sake
sheganta mini y'ay'a, kada ka kuskura na ce maka, y'ay'ana ba shegu ba ne ina ji a
jikina y'ay'ana y'ay'an halak ne tsarkakku!!! Ta k'arashe maganar tana nuna shi da
yatsa idonta kem! Cikin nasa babu alamar tsoro ko shakkarsa a ciki sai ma tsagwaron
tsana a cikinsu.

Mikewa ya yi a fusace ya iso gabanta yana cewa " Ni kike nunawa yatsa, ni kike
yiwa ihu Balki! To na sake fad'a cewa y'ay'anki y'ay'an zina ne shegune me zaki
yi??? Saukar miyan bakinta a fuskarta ya dakatar da shi daga hargagin da yake yi, a
fusace ya daga hannu zai wanke mata fuska da mari, caraf! Yaya babba ya rike
hannayensa ta baya, "koma ka zauna Hassan." Yaya babba ya ba shi umarni, bai zauna
d'in ba sai kawai ya fice daga d'akin yana kwafa, zuciyarsa na tafarfasa

Bayan fitar Hassan, Yaya babba ya maida kallonsa ga Ummi data durkushe a wajen tana
kuka mai tsuma zuciya, shu'umar murmushi ya saki, kafin ya bita ya tsuguna shima ,
cikin kasa-kasa da murya kamar me rada, ya fara cewa "Duk da shekaru sun ja, kina
nan a balkisunki kyakkyawar mace fara kal, d'anya sharaf mai dauke da tarin
baiwarwaki, kwata kwata baki tsufa ba balki, har yanzu ina nan da kudirina a kan
ki, ki amincemin koda sau d'aya ne na cimma muradina a kan ki ni kuma na miki
alkawarin zan tsaya miki da ke da y'ay'anki har duniya ta nad'e muddin ina
numfashi.
An yi ta babu dad'i sosai a gidan, domin sun yi musayen maganganu a tsakanin
su,Ummi ta kauda ido ta wanke Yaya babba tas ta kira shi da fasiki dan akuya,
kasancewar Tana cikin bakin ciki da bacin an sheganta mata y'ay'a da Hassan ya yi.

Sosai ran Yaya babba ya 6aci, Inda ya dauke mummunan kudiri akanta idea da shegun
y'ay'anta, ita kuma ta kalli cikin idanunsa ta sanar masa ta Allah ba yasa ba da
Allah ta dogara, da su nemarwa yayanta aure da kar su nemar musu duk daya

22 / 23