JOY by Aysha Nalado

Author :  Aysha Nalado Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 23

9K to 12K   out of 68.8K words

welcome back ba kenan, bari to ni naje na
ganta." Daga haka ya mike ya fice daga dakin.

Tun kan ya karasa dakin yake ce wa "baby where are u, I'm back, your Papa is
back." Yana maganar yana murda handle din dakin nata,yana shiga idanun shi ya
sauka a kan ta , zaro ido yayi kafin ya karasa da sauri ya haura kan bed din ya
shiga jijjgata yana kiran sunan ta, da kyar ta bude idon ta da suka kumbura, murya
a shake ta ce "Mom ki yafe Mom kiyi hakuri." Bai jita ba saboda shakewar da
muryarta ya yi, a gigice ya ciro waya ya dannawa Dr dake duba su waya, jin yadda
Papa ke gigice yasa, ya ce ya bashi fifteen minute gashi nan zuwa.

Yana ajiye wayan ya shiga kwala ma Mom kira, bata ji ba saboda tazarar dake
tsakanin dakunan, kuma gashi ko ina a kulle, ganin zai bata lokaci yasa yayi amfani
da telephone din dake dakin joy ya kira lambar dakin shi da shi.

Mom dake zaune ganin kira ta wayar tafi da gidanka abin ya bata mamaki, ta shi ta
yi ta dauka, jin yadda Papa ke magana a rude yasa taji gaban ta ya fadi da gudu ta
kwasa zuwa dakin Joy..........



Kuyi hakuri da jina shiru kwana biyu🙏 yawan comment yawan tsayin page😬



Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar
09116099486
[12/29, 2:31 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
*BY*

*AYSHA NALADO*


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

*LITTAFI NA ƊAYA*

*PAGE 6*


*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya
masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar
maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani,
maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai
domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu
cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar
miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin
yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar
naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da
wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k
kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI
MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon
Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki
number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da
boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin
mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin
Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA
KWARAI☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara
garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da
shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura
kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake
kasa._
*08089965176*
*07084653262*




Yadda Mom ta hango Joy a hannu Papa tana kakkafewa yasa ta 'karasa da gudu, a rud'e
take tambayar shi me ya same ta, cikin wani irin yanayin yace "Alice I don't no
nima haka na shigo yanzu na same ta." "Jesus!!!" Mom ta ce lokacin da ta d'aura
hannunta a goshin joy jin yadda ya dau zafi radau, "Mu kaita asibiti honey karmu
rasata." Ta fada tana shirin fashewa da kuka, "Na kira Dr solo ya ce yana zuwa
yanzu." Papa ya amsa mata, gyada kai ta yi tana share hawaye.

Wayar Papa ne ya dauki ruri, ganin Dr ke kira yasa ya daga da sauri, yana cewa "ka
iso ne Dr." Dan dakatawa yayi kafin ya daura da "OK ka karaso da sauri Dr ka hawo
sama tana dakinta." Cikin kankanin lokaci Dr Solomon ya karaso dakin Joy yana
d'auke da jakar kayan aikin shi, ganin yanayin da take ciki yasa ya nemi da su
Papa su bashi guri, da kyar suka fita suka tsaya a bakin kofar dakin, Mom rungume
jikin Papa tana kuka shi kuma sai bubbuga bayan ta yake yi idanu jajur,

Minti talatin Dr Solomon ya kwashe akan Joy, ya gano damuwace da yawan kukan da
tayi ya haifar mata da zazzabi da ciwon kai mai tsanani sai ulsanta daya ta shi
saboda rashin ci da sha, take ya bata duk taimakon daya da ce, ya mata allurai tare
da daura mata drip, barcin wahala ne ya kwasheta kasancewar a cikin alluran da ya
mata har da na barci, sai da komai ya daidaita sannan ya fito.


Da sauri suka yiyo kanshi suna rige rigen jero mashi tambaya, ajiyar zuciya ya
sauke kafin ya shiga yi musu bayanin abinda ya gano yana damunta, cikin kwantar da
murya ya daura da cewa "kuyi hakuri yanzu dai komai zai dai dai ta don na bata duk
taimakon daya dace na daura mata drip na mata allurai, yanzu haka barci ya dauketa
saboda alluran da na mata masu karfi ne kuma akwai na barci a ciki zaku iya shiga
shiga ku ganta."

Tare suka koma dakin da Dr , zama kusa da kanta Papa yayi ya kamo daya hannunta da
babu canula ya rike yana binta da kallon zallar kauna da tausayawa, Mom kuwa ta
wurin kafafunta ta zauna ta zuba mata idanunta mai dauke da danshin hawaye ganin
yadda ta rame ta kara haske a cikin yini guda.

Gyaran murya Dr yayi duk suka kalle shi ya ce "Mr and Mrs James ni zan koma
hospital dan na bar aiki sosai na taho nan, amma zuwa safe zan dawo na sake dubata
na kuma kawo magungunan da zata sha, sannan ruwan da na daura mata zai Kare nan da
sha biyu na dare, za kuma ta iya farkawa nan da hudun asuba idan ta ta farka Ku
tabbatar ta ci abinci kafin na iso." Godiya suka mishi Papa ya rako shi har parking
lot na gidan, tare da mai alkawarin kafin ya isa gidan zaiji alert kudin siyan
magunguna dana shan mai, shima godiya ya shiga yi, don yasan yau account din shi
zai kwana da nauyi.


Kusan a kanta suka kwana suna bata kulawa, cikinsu babu wanda yayi barcin kirki,
sha biyu ruwan ya kare kamar yadda Dr ya fad'a, Mom ce ta cire mata, bata farka
four kamar yadda Dr ya ce ba sai gurin six na safe har sun fara damuwa suna
tunanin kiran Dr ta farka.

Dishi dishi ta fara gani, kafin a hankali komai ya daidaita, tar ta ware idanunta
akan mahaifinta wanda zuwa lokacin shi kadai ne a dakin, da sauri ya karasa kusa da
ita ya kamo hannunta yana mata sannu, kura ma shi ido tayi tana kokarin son tunano
abin da ya faru,

Dai dai time din Mom ta turo kofar dakin ta shigo, motsin kofar yasa ta maids
idanunta gurin, idanunta ne ya sauka cikin na Mom, take abin da ya faru ya dawo
mata tsab, shesshekan kuka ta fara, ganin haka yasa Mom karasawa da sauri ta kama
daya hannunta, girgiza mata kai ta shiga yi, alamar kar tayi kuka, a hankali ta
bude baki hawaye na bin gefen fuskarta ta ce "Mom ki yi hakuri ki yafe min."

Hannu Mom tasa tana share mata haware, kafin ta ce "Ya isa haka daughter ki daina
kuka, kinga baki da lafiya." "Bazan daina kuka ba har sai kin yafe min Mom, bazan
iya jurar fushin ki ba." Dauke kai Mom tayi cikin dan bata fuska ta ce "zan hakura
amma sai kin mini alkawari babu ke babu wannan yarinyar." Ba tare da tunanin komai
ba don a lokacin mafita da sassauci kawai take nema ta ce "Na yi miki alkawari Mom
daga yau babu ni babu ita har abada." Murmushin farin ciki da nasara ne ya kwacewa
Mom ta rungumeta tana ce wa "nagode daughter ina son ki ina tsananin kaunarki."
Dariya ta saki mai sauti cike da jin dadi ta ce "I luv u 2 my Dear Mom."

Gyaran muryar da Papa yayi ne yasa Mom sake Joy, kallon tuhumar da yake mata yasa
ta yin murmushi, da ido ta mai alamar yayi shiru zata mai bayanin komai anjima, bai
ki ta tata ba, kawai yaja bakin shi ya tsuke.
Tea Mom ta hada mata, papa ya taimaka mata ta zauna, da kanshi ya ringa bata tana
sha har ta shanye, abinci mai saukin nauyi mom ta shiga kitchen da kanta ta samar
mata, ganin yadda Mom ta sake da ita yasa ta kwantar da Hankalinta ta ci abincin
sosai, kan kace koba sai gata ta gyagyije, da kanta tayi wanka ta shirya, cikin
riga pink mai hannun singlet da wando legis fari,

Karfe takwas Dr Solomon ya iso ganin yadda patient din shi ta gyagyije yaji dadi
sosai, magungunata ya bata ya musu sallama ya tafi.


*********


Sai da taci kuka ta koshi kafin ta mike jiki ba kwari ta kwabe kayan ta canza zuwa
dogon rigar atamfa, ta dauke dan madaidaicin hijabi ta sanya, ninke wadancen kayan
tayi ta kwaso ta fito dakin, ganin baya tsakar gidan yasa ta nufi hanyar zaure,
sallama tayi da yar siririyar murya, amsa mata yayi tare da bata izinin shigowa, a
bakin kafifar shi ta same shi zaune, har zuwa lokacin fuskarshi a hade babu rahma,
daga nisa ta tsuguna, cikin sanyin murya ta ce "Yaya kayi hakuri bazan sake ba." Ta
karashe tana mika misha kayan, bai amshi kayan ba kuwa bai amsa mata ba, ganin haka
yasa ta sake cewa "Yaya dan Allah da manzonsa ka yafe min, wlh tsautsayine na yi
maka alkawarin bazan sake ba" sai kawai ta fara shesshekar kuka.

Rintse idanu yayi, jin kukarta yake kamar saukar ruwan zafi a zuciyar shi, yana
jin Fatima a zuciyar shi fiye da tunani me tunani, yana mata so irin wanda kafin a
same shi tsakanin yan uwa sai an tona, kukanta yakan yi saurin raunata zuciyar shi,
matsayi uku yake takawa a rayuwarta UBA, DAN UWA, da kuma ABOKI, sun budi ido ne
daga shi har ita basu san kowa ba sai junansu sai kuma Umminsu, hakan yasa suke ma
juna wani irin so Mara iyaka, tunda ya fara girma ya fahimci basu da wani gata sai
Allah sai Ummi mahaifiyarsu da take tsaye a Kansu dare da rana, ya kudiri aniyar
zame mata gata, yadda yake maraicin rashin mahaifi ko wani tsayayyen dan uwa ita
bazai taba bari tayi shi ba matukar yana numfashi, a komai nata yana tsaye da
kafafun shi, ita macece mai raunice abar tausayi da riritawa.

Dakyar ya bude baki ya ce mata ya "ya isa haka Fatima na hakura share hawayenki."
Hijabin jikinta tasa ta share fuskarta da shi, gaban shi ya nuna mata yace "ajiye
kayan a nan." Babu musu ta ajiye, numfashi ya sauke kafin a tausaahe ya shiga yi
mata nasiha akan kula da mutuncinta matsayinta na diya mace, sosai ta nutsu tana
sauraren shi sai da ya dauke lokaci mai tsawo kafin ya dasa aya.

Godiya tayi kafin ta mike ta je kitchen ta dauko mai tuwon shi har zuwa lokacin
Ummi na tsakar gidan tana sauraren shirin tsalle daya a radio.


Ajiye tuwon tayi a gaban shi tare da ledar yalon da ke damke a hannunta tun dazu,
murmushi yayi ganin yalo, ya dago ya kalleta itama sai ta sakar mai murmushi, ya ce
"Nagode yar gidan Yaya Ameen" dariya ta saka cike da jin dadin yabawan da yayi da
kyautarta, wani dadi yaji ganinta cikin farin ciki sai ya tsinci kanshi da yiwa
marigayin mahaifinsu addua wanda har yau ko a hoto Ummi bata taba nuna musu shi ko
wani nashi ba, kawai abinda suka sani ya rasu da dadewa.

"Yaya sai da safe." Muryarta ya katsemai tunani, ya ce "har zaki tafi baza ki zauna
muyi hira ba, ko barci kike ji da wuri haka?" Ta girgiza kai, ya ce "kinci naki
tuwon ne ko?" Ta ce "A'a yanzu idan na shiga zanci." "Wanko hannu kizo muci
tare." Ta amsa da "to Yaya" tare da shiga cikin gidan danta wanko hannu kamar
yadda ya umarceta.

Cike da nishadi suka ci tuwonsu cikin kwarya daya suna wasa da dariya, a karshe ya
saka katon loma, kukan shagwaba ta saka tana dire kafa, cinyewa yayi ya kara kai
hannu da sauri ta dauke kwanan ta cinye guntun daya bar mata, tana tura baki, yana
mata dariya da gwalo kamar bashi ne dazu ya rufeta da fada ba, bayan ta kwashe
kwanukan wanko hannu tayi ta dawo, nan shiga bata labaran ban dariya yana cin yalo
yana yabawa ita kuma dadi kamar ya kasheta, daga karshe ya saurari haddarta.

Ummi na tsakar gida tana saurarensu, tsakanin Al'ameen da Fatima sai Allah,ko ita
data haifesu bata ce ga tsakanin subab, a haka bata san sanda ta fara gyengyadi ba.

Ba su suka ta shi ba sai gurin goma da rabi, shima ganin tana ta hamma yasa ya ce
taje ta kwanta, koda ta shigo gida ta samu Ummi tayi barci radio a kunne tashin ta
ta yi, suka wuce daki bayan sunyi alwalan kwanciya.

Washegarikamar kullum ta gudanar da aiyukanta na safe tayi shirin makaranta, tana
ta zuba idon ganin Joy sai dai shiru shiru har ta gama ta fito gida ta kama hanya,
yana ta tunanin ko zasu hadu a hanyar amma shiru har ta isa bakin get, bata kara
shiga damuwa ba sai da ta isa class ta tarad babu joy babu me kama da ita, haka ta
zauna jiki a sanyaye tana tunanin mekefaruwa ne yau, iya Sanin ta Joy bata fashin
makaranta, can sa'insar daya shiga tsakanin joy da David ya fado mata, take gaban
ta
ya yanke ya fadi rassss..........



Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lamabar
09116099486
[12/29, 2:32 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

*BY*

*AYSHA NALADO*


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

*LITTAFI NA ƊAYA*

*PAGE 7*



*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya
masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar
maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani,
maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai
domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu
cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar
miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin
yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar
naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da
wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k
kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI
MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon
Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki
number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da
boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin
mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin
Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA
KWARAI☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara
garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da
shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura
kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake
kasa._
*08089965176*
*07084653262*

Ranar haka Fatima ta wuni a school babu walwala, sboda rashin zuwan Joy, gaba ɗaya
jin school ɗin take yi babu daɗi a haka har suka yi closing, jiki a sanyaye ta
kamo hanyar gida cike da tunanin abin da ya hana joy zuwa school, fatan ta Allah
yasa dai lafiya.

A kulle ta iske gida alamar babu kowa, sai lokacin ta tuna Ummi ta ce mata zata dan
fita idan ta dawo ta karɓi key a maƙota.


Gidan da ke kallon gidan su ta shiga, shima dai kamar nasun ne, na y'ay'an mallam
shehu, sai dai yafi nasu girma da yalwar ɗakuna, sallama ta yi a ƙofar ɗakin Maman
Amira kamar yadda suke kiran matar gidan, Amira ce ta fito daga ɗakin tana amsa
sallamar, ganin Fatima yasa ta fad'ad'a fara'ar fuskarta, budurwace yar kimanin
shekara goma sha bakwai, sanye da wandon uniform dinta na girls day, ta cire rigar
ta bar farin singlet da alamar itama dawowarta kenan.

Murmushi Fatima ta sakar mata tare da cewa "Yaya Amira ina wuni." Cikin sakin fuska
ta amsa da "Ina gajiya Fatima kin dawo ya school." Fatima ta ce "Alhmdllh." "Shigo
mana tana ciki." Amira ta faɗa tana kauce mata a hanya, "A'a dama Ummi ce idan na
dawo na karbi key gurin Mama." "Ok bari na karbo miki." Ta koma ciki ba jimawa ta
fito da key din ta mikawa Fatima, amsa tayi ta fice, bayan tayi godiya, da kallo
Amira ta bi ta fuskarta dauke da murmushi a fili ta ce "kamar su daya sak! komai
nasu iri daya hatta murmushin, ya Allah ka mallakamin Yaya Ameen kasa ya zama
majibancin rayuwata, jin Mama kwala mata kira yasa ta amsa tare da komawa dakin da
sauri.

Ta tarar da gidan tsab kamar kullum, dakinsu ta bud'e ta shiga ta canza kayan
jikinta, ganin Ummi bata nan yasa bata tsaya watsa ruwa ba, don idan tana nan bata
yarda ta ci abinci sai ta watsa ruwa tayi sallah.

Kitchen ta bude ta dauko Kular abincinta, shinkafa ce garau garau da yaji, a nan
tsakar gida ta zauna ta ci abincin, tana gama ci ta mike ta kai kular kitchen, tana
fitowa Al'ameen na shigowa bakin shi dauke da sallama, amsa mishi tayi tana mishi
sannu da zuwa, murmushi ya sakar mata yana amsawa.

Idanunshi duk sun zurma kafafunta shi futufutu, takardun hannun shi ya ajiye kan
windon d'akin Ummi, ya ja kujerar ummi yar tsuguno ya zauna yana ce wa "Fatima bani
ruwa a buta." Da sauri ta dauki buta ta kai mishi bayan ta zuba ruwa, kafafunshi ya
shiga wankewa, Fatima dake tsaye daga gefe ta ce "Yaya tracking kayi ne?" Ya ce "Eh
kuma A'a kusan dai haka." Ya karashe maganar yana miƙewa don ya riga ya gama
dauraye kafar nashi.

Kofar dakin Ummi ya nufa, ganin haka yasa Fatima ta ce "Bata nan Yaya." Juyowa yayi
ya kalleta a mamakance ya ce "Bata nan, ina taje?" "Wlh ban sani ba ta dai ce min
zata dan fita da safe kafin na tafi school." Gyada ka yayi bai, kara

4 / 23