JOY by Aysha Nalado

Author :  Aysha Nalado Category :  African Stories & Novels

Chapter   19 / 23

54K to 57K   out of 68.8K words

fa na barota
ido biyu." Cewar Mama tana kallon Fatima da ke tsaye tana jiran k'arasowar
Al'ameen.

Sallamarsa ne ya karad'e musu kunnuwa kusan a tare duk suka amsa, gefen Mama ya
risina cike tsantsar ladabi da kamun kai ya ce "Mama ina kwana." Da fara'a ta amsa
da "Ina gajiya Aminullahi, ya harkoki ya karatu." "Alhmdllh Mama ya jikin Amira."
"Hmmm! Jiki da sauk'i Aminu sai hamdala." Ta fad'a muryarta cike da rauni. "Allah
Ubangiji ya bata lafiya." "Amin ya rabbi, Mai jikin ma ta samu barci, idan ta farka
zan sanar da ita zuwan ka." Ya amsa da " Ayya ba komai Mama, a gaisheta idan ta
farka, idan na dawo da wuri zuwa dare zan sake shigowa in sha Allah." "To to!!
Aminullahi Allah ya kaimu daren an gode sosai, Allah ya yi Albarka." Da Amin ya
amsa tare da mik'ewa ya fice.

Fatima ma bata dad'e ba ta yi musu sallama ta tafi tare da Alkawarin sake shigowa
anjima. Kamar almara tana fitowa daga gidan ta yi kicibis da Joy.
Da fara'a suka tari juna, Fatima ta ce "ya akayi kika fito da sassafen nan, yau
Saturday." Murmushi ta yi kafin ta kai bakinta dai dai saitin kunne Fatima cikin
rad'a ta ce "Na zo ganin Handsome Yayana ne, na yi masa godiya a kan, turaren da ya
siya mana, yanzu zan koma kafin Mom ta nemi ni." Dariya Fatima ta yi, Idan da
sabo ta sabo da jin ire iren sunayen nan kala kala daga bakin kawar tata da take
kiran Al'ameen da su, sai dai bata ta6a daukarsu da wata manufa ba, ta bar hakan
a matsayi kirkin da yake gwada mata shima, yana kula da ita sosai ya daukesu duk
daya, sometimes har tsaraba yake musu a tare, tun bayan da hargitsin nan ya lafa
ta lura da irin yadda Joy din ke matukar girmama lamarin da ya shafe shi, ko fira
suke idan na shi ne ta fi maida hankali, kullum zancen ta Yaya Ameen kaza Yaya
Ameen kaza, takan yi mamakin yadda lamarinsu ya juye daga kiyayya da kushe juna
zuwa yabo da girmamawa hadi da tsantsar kulawa.

"Umh! Wato shi kadai ki ka zo gani ko banda ni, to kin mak'aro yarinya ya fita."
Narai narai ta yi da ido ta ce "Da gaske?" Cikin dariya Fatima ta ce "Ah swear!"
"Ok bari na tafi, idan ya dawo ki fara Isar min da sakon godiya, kice nace turaren
yana da kamshi wai tunda nake ban ta6a jin turaren mai dadinsa, kar ki sanarwa
Ummi zuwana pls zan dawo may be gobe." Fatima ta ce "Oh naso kuwa na baki wani
labari mai dadi, tunda kina sauri shikenan, kuma labarin ya shafi Yaya Ameen." A
d'okance ta ce "Pls ki fara fad'a min Teetee ko Kad'an ne." "A'a ki tafi kawai bana
son Mom ta miki fad'a, ranar Monday zan gaya miki a School." Riketa ta yi tamau ta
ce "Ban yarda ba, sai kin fad'a min." "Ok to sake ni." Sake ta yi ta ce "Oyo tell
me." Shammatar ta Fatima ta yi ta kwasa da gudu tana cewa; Sai Monday."
A jigace ta yunk'ura ta mike zaune, lamarin da ya kusa zautar da Aysha tsabar
mamaki, saboda rabon da ta iya mik'ewa ta zauna da kanta haka har sun manta, kullum
sai dai a kwantar a tayar, bata damu da irin kallon da Aysha ke mata ba ta ce da
muryarta wadda bata fita sosai saboda jigata "Da gaske ki ke Aysha Yaya Ameen ya
shigo gidan nan duba jikina?" Aysha ta ce "Ya shigo mana Anty zan miki karya ne."
Ga mamakinta wani Busasshen murmushi taga Amira ta saki wanda rabon da ta yi irinsa
har sun manta sai kuma ga hawaye shar yana bin kumatunta,, murya ciki ciki ta ce "
Tabbas ban yi farin ciki da wannan barcin da na yi ba, domin yayi mini shamaki da
ganin rayuwata." "Anty mai Ki ka ce? "Ban ce komai ba Aysha." Gyada kai Aysha ta yi
wani tunani na zuwar mata a kwakwalwa, da sauri ta d'ago ta kalli Amira ta ce "Yaya
ina zargin wani abu, kar dai kice min soyayyace silar damuwarki?" Kura mata ido
Amira ta yi, dai dai lokacin Zainabu ta yi sallama a k'ofar d'akin tare da kutso
kai, gaban Aysha ta tsuguna tare da dafa kafadarta ta ce "Kwarai kuwa Aysha
zarginki ingantacce ne, ranar wanka ba'a boyar cibiya." Ajiyar zuciya ta sauke,
tiryan tiryan ta shiga labarta mata komai, tausayin Amira ya saka Aysha kuka
kashir6an, cikin shessheka ta ce "Dama na dad'e ina zargin Anty Amira na son Yaya
Ameen, amma ban ta6a tunanin shine matsalar larurarta ba, da tuni na bankad' sirrin
kowa ya ji, dan bazan yarda na rasa yar uwata ba ina ji ina gani, amma ko yanzu
bata 6aci ba." Ta kai karshen maganar tare da mikewa a fusace, riko hannunta
Zainabu ta yi ta ce "kar ki yi haka Aysha abi komai a sannun." Komawa ta yi ta
zauna tare da dafe kai ta ce "Gaskiya Yaya Ameen bashi da tausayi, ko dubata bai
ta6a shigowa yi ba fa Anty Zainabu" "Kar kiga laifin shi Aysha bai san komai ba
sai jiya." Nan ta kwashe yadda su ka yi da shi jiya ta fada mata. Ta daura da "Tun
sa kika ga ya biyo baya ina ga akwai alamun nasara abin ba sai ya kai ga manya ba."
"Allah yasa" Cewar Aysha.

kamar almara ranar a zaune Amira ta wuni sa6anin kullum da take wuni kwance, sai
gata harda dan cin abinci, Tsabar farin ciki Mama da gudu ta garzaya ta sanarwa
Ummi don abokin kuka da shi ake dariya.

Hamdala Ummi ta shiga yi, ranar da wannan zancen ta wuni duk wanda ya shigo gidan
kuwa da maganar take fara taron shi.

Cikin sa'a karfe shidda Al'ameen ya dawo, da wannan zancen Ummi ta tare shi
fuskarta a washe, murmushi yak'e ya kirkiro ya yi tare da cewa "Alhmdllh kai na yi
murna Allah ya kara mata lafiya." Jiki a sanyaye ya juya ya koma d'akinsa, kimtsawa
ya yi, ya tafi masallaci, daga masallaci direct gidan su Amira ya nufa, a lokacin
duhu ya fara.

Sam ta ki yarda ta sake komawa barci tun bayan wanda ta yi da safe wanda ta yi
mishi lakabi da barcin shamaki, tun karfe biyar take ta zuba idon ganin shi amma
shiru, shidda ya yi da rabi ya wuce har magrib zuwa lokacin ta fara sarewa,
silalewa ta yi ta kwanta ta lumshe idanu hawaye na bin kumatatunta. Kamar a
mafarki ta tsinaka yi sallmarsa a cikin dodon kunnenta, kafin ta gama tantance a
wani hali ta ke ta sake jiyo muryar Mama tana cewa "Tana d'akinsu, Aysha yi wa
Aminullahi iso." Kur! Ta kurwa k'ofar dakin idanunta masu danshi ya yin da bugun
zuciyarta ya tsananta..........



Haka so yake d'iba ya maida kai bawa🎢🎢🎢🎢 Allah sarki Amira. Y'an term d'in sannunku
hwa 😬
[12/29, 2:46 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 34*
Har ya k'arasa shigowa d'akin jikakkun idanunta na kafe a kan fuskar shi, ta kasa
koda keftawa, gani take yi idan ta rintse ido ta bud'e zai 6acewa ganinta. Aysha ce
ta bashi wajen zama kafin ta fice daga d'akin ta basu guri. Sai lokacin ya samu
damar sauke idanunsa a kan ta, wani irin kwance-kwance gabansa ya yi ya fad'i, Inna
lillahi wa inna ilaihi rajiun! ya ambata a zuciya. hankalinsa ya yi k'ololuwar
ganin gaba d'aya yadda ta rame ta lalace, ta fice daga hayyacinta kamar na Amiran
daya sani ba, take tausayinta ya yi wa zuciyarsa kawanya.

Sassanyar Muryarta daya ratsa dodon kunnesa ya jawo hankalinsa, cikin maganarta
'kasa-k'asa irin ta majinyata take cewa; Yaya Ameen kaine da gaske! Ba gizo idanuna
ke min ba, A she zan sake saka ka a idanuna kafin na amsa kiran mahaliccina, nagode
sosai da ka zo gareni na yi farin ciki, nagode sosai." Ta karashe maganar tana
sakin murmushi, hawayen soyayyarsa na kwaranyo mata ba tare da tasan da kwaranyarsu
ba.

Jikinsa ne ya yi sanyi kalau! Gefe guda kuma wani irin kunyarta ya ji ya lullu6e
shi, sai ya samu kansa da kasa ci gaba da kallon idanunta. Lallai zuciyar so
makauniya ce, duk irin abin da ya aika ta mata Sam! bata ga laifinsa ba, bata yi
fushi ba, wata d'aya da kwanaki ta kwashe cur! Tana jinya saboda soyayyarsa, bai
ta6a koda aikowa bane yace ace mata sannu, amma take mashi godiya don yau ya shigo
dubiyar da bata kai zuci ba.

Dakyar ya d'ago idanunsa da ke kyallin hawayen tausayinta ya sake kallota, da wani
irin sassanyar murya ya ce " *Meerah* ya jikin ki."

Kusan suman wucin gadi ta yi, don lokacin da tattausar murya shi ya ratsa kunnenta,
cak bugun zuciyarta ya tsaya, kamar sabuwar makauniya haka ta kure fuskar shi da
kallo ba tare da ta amsa mishi ba.

Ganin haka yasa ya yi karfin halin sakar mata tattausar murmushi, abin da ya yi
sanidiyar lumshewar idanunta a hankali ta sake budewa a kan shi, still murmushin na
nan bai 6ace a fuskar ba, cikin k'asa k'asa da murya ya sake kira sunanta da cewa
"My Meerah."

Gudun wahayenta ne ya ninku, la66anta ne su ka kama rawa alamar tana son furta wani
abu amma ta kasa, gyada mata kai ya yi ya ce "Yess My Meerah, do u lik d name? Bata
iya amsa tambayar ba, sai kawai ta tsinci kanta da rintse idanu tare da furta "Ya
Allah na roke ka, kar ka farkar dani daga wannan daddadar barcin da nake yi, Ya
Allah ka dauwamar dani a cinkasa." Ta karashe maganar da fashewa da kukan da ita
kanta bata san na mai zata kira shi ba.
Bai san sanda ya isa gabanta ba, cike da tausayi ya shiga share mata hawaye, cikin
rad'a ya ke cewa; It's reality Meerah ba mafarki bane, nine Ameen d'in ki a
gabanki, bud'e idanunki ki kalleni." Samun kanta tayi da budewar kamar yadda ya
umarta, suna hada idanu ta mika hannu ta kama nashi ta rike gam! Cikin kuka da
fitar hayyaci ta ke cewa; Dan Allah Yaya Ameen kar ka barni, ka tsaya a tare dani
ka dauwama a tare dani, kar ka gusa kusa dani na roke ka, yin hakan daidai yake da
yankewar numfashi na, bazan iya rayuwa ba tare da kai ba, Ina son ka Ameen, ina son
ka ina son ka, kaine rayuwata farin ciki na, idan babu kai a duniyar Amira zan zamo
kamar mutum mutumi." Ta karashe da fashewa da wani irin kuka mai narka zuciyar mai
sauraro.

"Shiii! ya isa Meerah, ga Ameen a gabanki, na yi miki alkawarin zan rayu dake zan
zamo maji6ancin rayuwarki insha Allah." Ya fad'a cikin wani irin amo wanda yake
fitowa tun daga kasan zuciyarsa.

Sun dad'e a haka hannun shi, cikin nata, dakyar ya lalla6a ya zare hannunsa tare da
komawa mazauninsa ya zauna, yana ci gaba da gaya mata kamalai masu kwantar da
hankali, sai ga Amira tana dariya kamar wayiya, kallonta yake cike da tausayi tare
da kara tabbatar da cewa lallai shine farin cikinta.

kiran isha'i ne ya tayar da shi, kafin nan sai da ya yi mata alkawarin shigowa da
safe ya dubata kuma ya jaddada mata ta tabbatar ta ci abinci da yawa.

Cikin kwana uku da faruwar haka sai ga Amira ta gyagije ta mike tsaye kan
kafafunta, kamar ba itace a kwance rai a hannun Allah ba, lamarin da ya baiwa kowa
matukar mamaki banda Aysha Fatima da Zainabu da su ka san abin da ke ciki.

Al'ameen yana iya kokarinsa wajen ganin ya wanzar da farin ciki a gareta, kullum
yakan shiga ya dubata suyi hiran hakan ya jefawa Mama zargin wani abu a zuciyar ta,
Fatima kam kusan tafi kowa farin ciki don tsakanin ta da Allah har zuciyar ta take
kaunar Anty Amira, ba don warning din da Al'ameen ya mata akan kar fa fadawa Ummi
ba, da tuni ta fada, duk da haka takan yi su6utar baki wani bin.

Yanzu damuwar Al'ameen bai wuce Aliyu ba, tun daga ranar da wannan abin ya faru
basu sake haduwa ba ranar da damuwa yadda su ka rabu ya kwana, a zuciyar sa yaji
bai kyauta ma shi ba, ya je gidan su sau biyu baya samun shi, kiran waya kam ya
mishi ya fi sau shurin masaki amma baya d'agawa.


*********

Tun da Joy taje gida take ta tunanin albishirin da Fatima ta ce , zata mata a kan
Yaya Ameen, kasa juriya tayi don akan duk abin da ya shafe shi zuciyar ta azalzala
take, babu yadda bata so ba ta samu hanyar fita ran Sunday zuwa gidan sai dai babu
dama, don Mom tasata tayi a gaba tunda sassafe suke wuce church ranar acen suna
kusa wuni, haka ta kwana da daukin wayewar garin Monday, sai dai cikin rashin sa'a
ranar karatu ta yi musu zafi, kuma da aka yi closing Mom ce da kanta ta zo
daukarta, ba don ta so ba ta bita suka wuce gida da kudirin koma menene gobe baza
ta rabu da Teetee ba sai ta gaya mata......
[12/29, 2:46 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€


~FARHAT~


*PAGE 35*


Washegari tun six thirty ta gama shirin school saboda gand'oki, a gaggauce ta
sauko dining, a shirye ta same shi tsab! Kamar yadda ta tsammata, sai dai tea da
cake kadai ta iya sha shima kad'an, sake kallon agogon dake daure a tsintsiyar
hannunta ta yi, ganin bakwai saura yasa ta naima waje a parlour ta zauna tana
kallon cartoon a tv duk da kallon kawai take amma hankalinta baya gurin, karfe
bakwai dai-dai ta nufi upstairs, direct d'akin Mom ta nufa, tura kofar ta yi ta
shiga ba tare da knocking ko excuse ba. Mom bata falo dama bata yi zaton ganinta a
nan ba, kai tsaye ta nufi bedroom, muryar Mom da ya daki dodo kunnenta ne, ya
dakatar da ita daga karasawa cikin d'akin.

Cike da tabbatarwa ta ke cewa "Kar ki damu Esther bani da kowa a duniyar nan bayan
ke, ke kad'ai ne iyayenmu suna haifemu tare mu biyu kuma a yanzu basa raye, ki sani
ita d'in ba komai bace a gareni fa ce tsanin cikar burina, lokacin dana dibar mana
na daf da k'aratowa, sai na tabbatar da ya mallaka mata komai nasa daidai da tsinke
bai bari ba, zan kashe shi, sannan daga baya ita......" Sauran zancen ne ya mak'ale
lokacin da idanunta suka sauka a kan Joy rik'e da k'ofa, da alamar ta ji me take
cewa' Jikinta ne yaso daukar rawa, amma tuna wacece Joy yasa ta dake rainonta ce,
ta fi kowa sanin halinta bata da shiga sabgar da bai shafeta ba. "Excuse me." Ta
fad'a tare da sauke wayar daga kunnenta, sakar mata murmushi ta yi, cike da
wayancewa ta ware mata hannayenta tare da cewa; "Come to me my dearest princess."
Martanin murmushi ta mayar mata ta k'arasa ta fad'a jikinta suka jungume juna,
"Morning my lovely Mom." Joy ta fad'a tana zare jikinta daga na Mom, rike hanayenta
Mom ta yi ta na kallon ta cikin ido don son karantar yanayinta ta ce "Morning my
Happiness, har kin shirya? "Yes Mom har ma na yi breakfast." "Auh! Shine babu jira
ko gud." Dariya ta kyalkyale da shi, "I'm sorry Mom na tashi da yunwa ne." "Ok no
prblm." Mikewa ta yi tana cewa; "Bye bye! Mom till I came back." "Ok princess nima
yanzu zan shirya na tafi gidan antynki Esther, tana can tana rigima da Mr Moses wai
sai ya sake ta, yanzu ma da ita nake waya kika shigo Esther bata jin magana
lamarinta ya fara isa na." Ta karashe maganar tare da dafe kai cike da takaici,
"Ki yi hakuri Mom ki ci gaba da abin da kike yi na alkhairi zaki samu lada." Tana
gama fad'in haka ta fice, a parlour n k'asa ta dauk'i jakarta ta fito compound,
already Peter na jiranta basu 6ata lokaci ba, ta shiga ya tukata zuwa school.

Da biyu Mom ta fad'i wannan magana, don ta kauda hankalin joy daga zargi ne, hakan
kuwa ya yi tasiri, da farko kalmar kisan da ta ji a cikin maganganun Mom sun saka
ta a shakku, sai dai jin zancen Esther yasa ta yi watsi da lamarin don bata kaunar
abin da zai had,a ta da tilon kanwar uwartata, tun a bedroom d'in Mom ta watsar da
batun, ko kafin su isa school ta shafe babin batun a ranta.

Shiganta aji da mintuna kad'an Fatima ta iso, kasancewar babu teacher a ajin yasa
ta tashi da gudu ta tare ta suka rungume juna, dakyar suka saki juna suka k'arasa
sit suka zauna, sauran student na masu dariya masu jin haushin kawancensu kuma na
ta6e baki da zund'en su.

"Teetee tell me about him, ki gaya min mana sai ja min rai kike yi." Dariya Fatima
ta saka ta ce "Sai during break." Fushi Joy ta yi ta juya mata baya, magana Fatima
ta dinga mata amma ta share da gaske fushi ta yi sosai don harda guntun kwallah ta
share ba tare da sanin Fatin ba.

Abin da ya ba Fatima mamaki da kuma dariya ana ringing bell, Joy ta kalleta tare da
cewa; "Oya tell me." Dariya Fatima ke son yi, amma sanin halin Joy na saurin fushi
yasa ta danne, ta yi abinta a ciki, narai-narai Fatima ta yi da ido ta koma kalar
tausayi kafin ta ce "Zan gaya miki amma sai kin saki fuskarki, kinji my beautiful
friend." Murmushi ta saki, Fatima na dariya ta ce "Ba irin wannan ba gaskiya, idan
ba haka ba kuma bazan fad'a ba." Ga mamakinta sai ji ta yi Joy ta kyalkyale da
dariya. Gimtse nata dariyar ta yi tana binta da kallon mamaki, gira Joy ta d'age ta
ce "A kan Yaya Ameen komai zan iya yi domin nima a yanzu shine komai nawa." Rass
gaban Fatima ya fad'i da sauri ta kauda tunanin da yazo mata zuciya, jin Joy din ta
ci gaba da cewa; "Shine ya bani matsayin kanwa, ya zame mina Yaya dan uwa abin da
na nake tsananin kewa shekara da shekaru, ina jinsa har cikin bangon zuciyata."
Murmushi Fatima ta yi ta ce "Umm! Kaji masu yayyi muma Allah ya bamu." "Amin!" Joy
ta amsa mata a gatsile. Fatima ta ce tana murmushi, "To albishirinki." "Goro fari
kal!" Ta amsa mata, "kawo kunnenki kiji." Matso da kunnenta ta yi fuskarta a washe
yau dai finally zata ji abin da Teetee ke ja mata rai a kai kwana da kwanaki,
Fatima ta kama kunnen ta matsa da bakinta cikin rad'a ta ce "Yaya Ameen ya yi
budurwa very soon zai yi Aure, zai auriAnty Amira....." 6at tattausar murmushin
dake kwance a kan fuskarta ya ba ce within second, kamar saukar gudumar wuta haka
kalaman Fatima suka daki zuciyarta take idanunta suka fara juyawa, wani irin
dunkulallen abu ya tokare mata kirji, take numfashinta ya shiga sama da kasa kamar
mai cutar Asthma.

Jin shiru yasa Fatima kallon ta, a tsorace ta zaro idanu tare da furta "Na shiga
uku." A bayyane "Joyyy!"ta kira sunanta da karfi tana jijjigata, suuu! Ta ta tafi
zata fad'i, da sauri Fatima ta rikota cikin tashin

19 / 23