JOY by Aysha Nalado

Author :  Aysha Nalado Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 23

30K to 33K   out of 68.8K words

kasa amsawa yayi don
jin addu'an yayi banbara kwai.

Bayan tafiyar ta ya yi wa Ummi sallamarta tare da umarta Fatima ta kawo mishi
abincin shi daki, daga haka ya wuce dakin shi.......



***********


Tashin hankali wacce ba'a saka mata rana, a bangaren Joy ranar kusan yadda taga
dare haka taga rana, duk da bata san so ba, zata iya kiran abinda take ji game da
AL'AMEEN da zazzafan soyayya wanda tayi wa zuciyar ta daurin goro a farat daya...




Wata sabuwa inji yan caca hmmmm! Joy ina raraki da, kinsan dai Mom kamar yunwar
cikin ki, atoh ni dai babu ruwana, masoyan Joy Ku bata shawara.

Pls kuyi ta manage da guntayen page insha Allah komai ya kusa dawo min normal muyi
mu gama book din nan don ni na fara gajiya da shi saboda rashin comment dinku.
yasin.


Ga masu bukatar shiga group
Ku tuntubeni kai tsaye
09116099486.
[12/29, 2:38 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

DAGA ALƘALAMIN 👉 *AyshaNalado*

ƘARƘASHIN JAGORANCIN 👉 *Mikiya Writer's Association*
*PAGE 19*

Washegari Monday da shirin school ta tashi hakan ne ya d'an d'auke mata hankali
daga tunanin Yaya Ameen data kwana yi, jiki a sanyaye ta gama shiryawa, sai kuma ta
nema waje ta zauna ta rafka tagumi, ta yaya zata je ta zauna ta zana jarabawa ita
kad'ai ba tare da Fatima ba? ta ina zata fara? Me zata rubuta? Ko dai ta je gidan
su ne, wata zuciyar ta bata shawara, yayinda wata zuciyar ta hane ta da aikata
hakan. A karshe hankalin ta yafi karkata akan ta bari idan sun yi closing ta je,
Haka tayi ta zaman gawon shanu har na kusan 30 minutes ba tare da ta ankara ba.

Ringing d'in wayar ta ne ya dawo da ita hayyacinta, da kyar ta mik'e ta isa
ma'ajiyar wayar, sunan Mom ta gani yana yawo a fuskar wayar, gabanta ne ya yanke ya
fad'i, tunda Mom ta wuce basu yi waya ba.

Jiki a matukar sanyaye ta kara wayar a kunne ta ce "Gud morning Mom." Daga daya
6angaren Mom dake cikin matsananin tashin hankali ta ce "Morning." A dak'ile ta
d'aura da "Thank u 4 what u did, nagode sosai kin nunwa duniya ban isa dake ba, na
ce karki je ko ina amma sai da kika fita saboda ke mai kunnen k'ashi ne, to baki
isa ba, kin yi karya, kin yi kad'an, ni na haifeki ba ke kika haifeni ba don haka
baki isa ki juyani, kuma zan nuna miki." Cikin rawar murya ta ce "Kiyi hakuri Mom "
Mom ta ce "No don't sorry me, sorry 4 ur self akwai ranar karbar result yana nan
tafe. Kuma me kike yi a gida har yanzu, ko ba yaune kika ce zaku fara test ba?" A
sanyaye ta ce "Yau ne." "To zaman me kike yi?" "Kiyi hakuri mom na shirya yanzu
zan wuce." "Da kyau, ki fita waje driver na nan da zai kai ku kuma zai jira har ku
tashi ya dauko ku, idan ki ga dama kar ki bishi,Duk abinda kika yi zan samu
labari." Kit ta kashe wayar ta. Wayar ta bi da kallo kafin ta ce "Zai kai mu ni da
wa?" Bata da mai bata wannan amsar hakan yasa ta saki ajiyar zuciya a bayyane ta ce
"kiyi hakuri Mom ba yin kaina ba ne." Jiki a sanyaye ta jawo jakarta ta sakko
downstairs, babu kowa a main parlour, ko kallon 6angaren dining bata yi ba don
bata jin zata iya saka koda ruwa ne a cikin ta a halin yanzu.

Tana fitowa compound idanunta ya sauka akan wata bak'uwar mota fake a gaban plat
din Mom daf da kofa, bata gama mamakin su wanene a ciki ba aka bude kofar motar,
David ne ya fito sanye da uniform d'in shi irin nata fuskarshi dauke da murmushin
mugunta, kafin ta gama mamaki aka bud'e d'aya 6agaren mahaifiyar shi ce ta fito Mrs
Esther fuskarta a had'e kamar hadarin gabas! cikin wani irin takun isa da tak'ama
ta iso gaban Joy, kallon sama da k'asa ta mata kafin a gadarance ta nuna mata motar
data fito, da hannu ta mata alamar ta shiga.

Sai lokacin ta fahimci jam'in da Mom keyi d'azu wata ita da David za'a kai school
tare me hakan ke nufa? Kar sai Mom Anty Esther ta fito ta zaua da ita kafin su dawo
da kuma ta shiga ukunta.

Sai da ta hadiyi wani busassshen yawu kafin, ta kimkimi jakarta jiki a sanyaye ta
nufi motar ta bud'e baya ta shiga, David dake tsaye shima ya bud'e inda ya fito ya
koma ya zauna, driver yayi ribas ya fice daga gidan.

A rayuwarta tana matukar tsoron Anty Esther, macece masifaffiya ta karshe, uwa uba
kuma bata kaunarta ko miskala zarratin, tun bata mallaki hankalin kanta ba ta
fahimci hakan, ko kadan jininsu bai hadu ba.


Bata san school ba sai da ta ji k'arar bud'e kofa David, dagowa tayi yana tsaye
daga jikin windon suna had'a ido ya d'age mata gira tare da sakar mata murmushin
keta ya ce "Muje ko." Harara ta watsa mai kafin ta 6alle murfin motar ta fito a
fusace ta nufi cikin school ba tare data kula shi ba, tana jin shi yana biye da ita
yana fito kasa-kasa.
Ko a class kasa concentrating ta yi akan abin da ke gabanta, tana kallon sauran
student na d'aukan notebooks din su suna dubawa kafin shigowar invigilator, amma
ita ko kwakkwaran motsi ta kasa, har zuwa lokacin da aka shigo yi musu first paper
wanda English ne, bayan suna babu abinda ta iya rubutawa a script dinta, ajiyewa
tayi akan desk ta rafka tagumi, ta fada komar tunani, rintse idanu tayi take
kyakkyawar fuskarsa ya shiga yi mata gizo, komai nashi na dawo nata dallah-dallah,
especially moment din su na jiya a tare.

Bata san iya adadin time din data kwashe ba sai sai ta ji ana cewa everybody
submint, tana kallo aka d'auke script din ta ba tare da ta iya rubuta koda kalma
d'aya ba.


Koda suka fita break kasa fita tayi, kwanciya ta yi kan desk, duk da irin yunwar
dake nukurkusarta.

A haka har lokacin second paper yayi, shima dai kamarna farkon babu abinda ta
tsinana, da ta kai hannu ma sai ta samu kanta da yin drowning din hearts da arrow
ba tare da ta farga ba, a haka lokaci ya tafi, ta yi submit ba tare da ta goge ba.


Kasancewar suna test sha biyu suka ta shi, ga mamakin ta David ta ga yazo ya tsaya
akanta, a hasale ta ce "what?" Yayi murmushinsa dake kular da ita tare da cewa
"Nothing, just let's go." Tsoron Anty Esther ne kawai yasa ta bi bayan shi suka
wuce, kamar kuwa yadda Mom ta fad'a a bakin get suka tarar da driver'n daya kawo su
yana jiran su, kai tsaye gida ya wuto da su ba tare da ta samu damar zuwa gidan su
Fatima ba kamar yadda ta tsara.

Cike da fargaba ta bi bayan David suka shiga plat din Mom, a hakimce ta tarar da
Anty Esther a falo kafa daya kan daya, ta tara duk ma'aikata gidan a gabanta, ko me
take gaya musu oho! A haka suka karasa ciki David dake gaba ya ce "Good afternoon
Mama." Ta amsa da "Fine Son kun dawo." Ya ce "Yes Mama." Tare da neman waje
gefenta ya zauna yayi balance kamar gidan uban shi. Idanunta ta dawo da shi kan
Joy, ta shiga binta da wani shegen kallo mai cike da tsana.

Jikinta ne ya d'an dauki rawa lokacin da sukayi hada idanu rasa abin yi yasa ta
samu kanta da maimaita abin da ta ji David ya fada ita ma, a d'arare ta ce "Good
afternoon Anty." Harara ta watsa mata kafin ta ce "Afternoon." A dakile daga haka
bata kara ce mata komai ba sai tsarabar hahara.

Ganin haka a sukwane ta kimkimi school bag din ta, ta haura dakinta.

Tana shiga ta yi wurgi da jakar, ta fada gado ta fashe da kuka, wata zuciyar ce ta
mata, "yanzu haka zaki zauna wannan matar ta yi ta mulkarki a cikin gidanku gidan
mahaifinki. Impossible!" Zabura ta yi da nufin ta dauki wayarta ta kira Papa sai
dai wayam babu wayar a ma'ajiyarta babu dalilinta, sake fashewa ta yi da sani sabon
kukan, ko bata tambaya tasan Anty Esther ce ta daukar mata waya, dan kuwa babu mai
ikon shigar mata daki cikin ma'aikan gidan matukar ba ita ta bukaci hakan. Zamewa
tayi kasan tiles ta jingina da bed din ta tana matsar kwallah.

Tsawar da Anty Esther ta daka mata aka ne, yasa ta mikewa a firgice, cike da masifa
ta ce "Kukan uban me kike yi, iye nace kukan Uban me kike yi." Cikin son hadiye
kukanta ta ce "Kiyi hakuri Anty." "Rufe min baki munafuka kin zo kin zauna kina
kuka saboda tsabar sangarta da fitsara kamar wacce aka daka ko aka zaga, maza ki
cire wadan nan kayan ki fito ki yi lunch."

Tana tsaye a kanta ta cire uniform ta sauya na gida, daga haka ta tasata a gaba
zuwa dining, dinning din shake da abinci kamar wanda mutum goma zasu ci saboda
almubazzaranci. Uban abinci tayi serving dinta tuli wanda tasan ya mata yawa, ta
tasata a gaba wau sai ta cinye shi, tana ci tana kuka ita kuma tana antayata zagi,
"Yarinya duk anbi an sangarta ki, kina yiwa mutane fitsara iri iri, babu tarbiya,
to ni nan zan gyara miki zama kafin Mom dinki ta dawo." Da kayar ta iya cin rabin
abinci, ta shiga kakarin amai, ganin haka yasa Anty Esther kyaleta, tana sharar
kwallah ta mike zata wuce daki, hanata tafiya Esther tayi ta sakata ta zauna ta
mata massage.

Ranar haka Joy ta wuni cikin wahala da zagi da tsamgwama daga wannan ta shiga
wannan , ba ita ta samu kanta ba sai wajajen karfe goman dare, duk wannan wahalar
da gajiyar da tayi tana samun hakarkarinta ta kasa tunanin Al'ameen ya mata
sallama, Babu abin da yafi tsaya mata a rai irin kyakkyawar murmushi sa, ta tuna
ranar da Fatima ke ce mata duk duniya babu wanda ya kai Yayanta iya murmushi, a she
da gaske ne. Ta sake tuno daddadar muryar sa lokacin da yake ce mata "I'm sorry!
Ban yi don na cutar dake ba." Murmushi ta yi tare da kai hannu ta shafi goshinta
dai-dai gurin daya d'an kuje har yayi jini tana sahafawa tana murmushi, bata san
iya tswon lokacin data kwashe a haka ba kafin barci barawo yayi gaba da ita...


***********

Masu bukatar shiga group na joy su tuntube ni kai tsaye .


09116099486
[12/29, 2:38 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀


~FARHAT~

DAGA ALƘALAMIN👉
*AyshaNalado*

ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiya Writers Association*


*PAGE 20*


Washegari wajajen bakwai da rabi na safe, Anty Esther ta fad'o mata dak'i, tana
cikin barcinta mai dad'i wanda ya d'auke ta dakyar gabanin asuba cike begen
Al'ameen ta ji an d'ad'a mata duka a cinya, a zabure ta farka zata zunduma ihu
idanunta ya sauka akan Anty Esther, tuni ta ja bakinta ta tsuke tana zare ido.

Harara Esther ta watsa mata ta d'aura da "Sannu isasshiya, karfe bakwai da rabi
kina kwance ki na barci, wa kike jira ya tashe ki. Common get up, stupid girl!" Ta
karashe maganar a tsawace tare da mi'ka hannu kamar zata kai mata mari. Da gudu ta
mik'e ta fad'a toilet ta rufo kofar ta murza key, jingina tayi da kofar ta fashe da
kuka k'asa-k'asa don kar Anty Esther ta jiyo ta, sai da ta yi mai isarta babu mai
rarrashi ta samu tayi wankan dakyar, a d'arare ta turo kofa ta lek'o, ganin Anty
Esther bata d'akin yasa ta k'arasa fitowa da sauri, sharp-sharp ta shirya cikin
uniform dinta ta sakko downstairs dauke da makeken school bag d'in ta mai tayoyi.

A dining ta tarar da David gaban shi shake da abincin kala-kala ya ci wannan ya
ture ya janyo wannan, Harara ta watsa mishi a fakaice a ranta ta ce "Shege
mayunwaci babu a hause anzo an samu na banza." Muryar Anty Esther ta jiyo daga
hanyar kitchen tana tahowa,sai masifa take da hargagi da alama da kuku's take yi.
Da sauri ta ja kujera ta zauna, cikin dan karkarwar jiki ta shiga kokarin had'a
tea, David na kallon ta yana mata murmushin keta.

Bata wani ci abin kirki ba ta mi'ke, ganin David ya gama don kar tayi laifi, du k
da haka bata tsira ba sai da Anty Esther ta zage ta tas, wai tsabar iskanci ta zuba
abinci ta barshi bata ci ba. Kuka take son yi amma babu dama, Tana kallo David ya
kwaso kayan kwalama dangin su cake, ice cream, chocolate, ya tula a jaka, sannan su
ka fita sabon driver'n Mom ya d'auke zuwa school.

A cikin mota ta samu damar yin kukanta, kwantar da kanta a jikin kujera ta yi tana
shesshekar kuka kasa-kasa, David dake gefenta ya kalleta yayi murmushi, cike da
izgili ya ce "Yarinya ki kwantar da kai a gabana ki roke ni abin da kike so, zan
taimaka miki." Harara ta watsa mishi ta dauke kai wani irin mugun haushin shi take
ji. D'age kafad'a ya yi ya ce "kin huta."

Yau ma kamar jiya babu abin da ta tsinana a school d'in har sukayi closing.

Koda su ka koma gida yau ma bata huta ba, haka Anty Esther ta sakata a gaba kamar
jiya, ko garden ta ki bari ta fita ta sha iska, wayarta take bukata ta kira Papa
amma tsoro ya hana ta tambaya, tana ji a gabanta Anty Esther da Mom suka yi waya,
amma Mom bata ce a bata ba, sai ma cewa ta yi wai a ci-gaba da tsareta kar a barta
fita ko compound ne idan ba school zata je ba, kuma koda wasa kada a kuskura a bata
waya, har sai ta dawo, daga nan kuma suka ci-gaba da wasu maganganu wanda tuni ta
daina fahimtar komai saboda kukan da ya ci karfinta.

Kamar jiya tana samun kanta tuni ta manta da duk halin da take ciki, ta tsunduma
tafkin begen abinda zuciyar ta ke bege.


**************

Bayan wasu kwanaki.

Sosai Amira ta dage da zuwa daukar karatu wurin Al'ameen, sai dai hakan ba abinda
ya kareta da shi sai wani irin mahaukacin kaunar shi, a duk sanda zasu zauna karatu
zuciyarta sake narkewa take da soyayyar shi, haka zata yi ta kallon shi wani bin
sai Fatima ta ta'ba ta zata yi firgigit ta dawo hayyacinta, zuwa yanzu Ummi ta soma
fahimta wani abu game da Amiran sai dai ta bar abin a zuciyar ta a tunda hasahse ne
kawai take bata da tabbas. Shi kam Yaya Ameen bai fahimci komai ba, saboda kwata
babu wata aba wai soyayya a gaban shi, sai dai ya kan rasa wani irin kallo ne
yarinyar ke yawan bin shi da shi haka.

Ita kam a bangaren ta sosai lamarin ke damunta, duk wani salo da iyayi da zata yi
don Al'ameen ya gane halin da take ciki ta yi amma a banza, hakan yasa ta sake
tarar Zainabu da maganar, zee ta bata shawara kamar yadda ta saba, ta yi na'am da
shawarar don a yanzu yadda take jin soyayyar shi, bata ki kowa ya sani ba don ta
k'una bata tsoron kauri.



Yau ma kamar kullum ta shigo gidan bayan sallar isha'i, kasancewar an wuni ruwan
sama gari yayi sanyi, yasa Ummi basu zauna a tsakar gida kamar yadda suka saba ba,
a falo ta same su gaba dayan su harda Al'ameen d'in da dawowar shi gidan kenan, ya
mutsa fuska ya yi lokacin da ya ji sallmarta, baya jin dadin jikin shi tunda rana
karfin halin kawai yake yi, ga wani sanyi-sanyi da yake ji yana shigar shi.

gaban Ummi ta zube ta kwashi gaisuwa, sannan ta juyo bangaren sa, cikin wata irin
narkakkiyar muryar ta ce "Ina wuni Yaya Ameen." Ya amsa da "Lafiya kalau." Yana
dauke kai daga gareta don take kamshin wannan mayataccen turaren nata na ran nan ya
mashi sallama, dafe kanshi daya fara Sara mishi ya yi.

Fatima ce ta gaisheta, ta amsa cike da kulawa kafin ta samu waje kusa da ita ta
zauna, ta saitin shi yadda zata samu damar satar kallon shi hankali kwance.

Ya fi minti uku a haka kafin ya dago, carat idanunsu ya sarke dana juna ba tare da
ta ankara da zai dago ba, da sauri ta kawar da kanta don bazata iya jurar hada
idanu da shi ba, muryar shi ne ya dawo da ita hayyacinta "Amm! Amira ki yi hakuri
kike gida yau baza mu saka yin karatu ba, Bana jin dadin jikina."

Jin haka yasa Ummi kallon shi da sauri, ta katse shi da cewa "A'a yayan Fatima baza
ayi haka ba, tunda ta riga ta zo, ka koya mata ko kadan ne."

Shiru ya dan yi kafin ya amsa da "To Ummi." Baya iya mata musu matukar akan abinda
bai fi karfin shi ba ne.

Mikewa yayi ya kalli Fatima ya ce "Ku muje dakin zaure taskar gida a kwai sanyi."
Daga haka ya fice, Ummi ta so tsayar da shi suyi karatun a falonta ganin ya riga ya
fice yasa ta kyale shi.


Fatima ce a gaba Amira na biya da ita suka shiga dakin bayan ya amsa musu sallama,
lumshe idanu Amira tayi lokacin data shaki daddadar kamshin turarensa da take
maitar son ji kullum. Dakin tsab da shi a tsabtace kamar ba dakin saurayi ba.

Cike da karfin hali da jarumta ya fara koyar da su, sai dai ko minti goma basu
dauka ba ya fara neman fita hayycinsa, rintse idanu ya yi, yana jin yanayin shi na
canjawa, gefe daya ga wani shu'umin kamshin turaren da yake shaka na neman hallaka
shi.

Babu shiri ya dakata, ya kalli Amira da kyar ya ce "Amira kije kawai gobe ki dawo,
bana jin zan iya karatu yau, na so na koyar da ke kamar yadda Ummi ta saka ni amma
bana jin zan iya."

Cike da matsanancin tausayin shi ganin yadda idanun shi suka rine, ta ce "Toh
Yaya, Allah ya saukawake." Da kai ya amsa mata don baya jin zai iya bude baki ya yi
magana, a rude Fatima ta shiga jeromai sannu, da kai ya ke amsa mata, tuni idanunta
ya ciki da kwalla, da hannu yayi musu alamar su tafi kawai, jiki duk a sanyaye suka
mike, har sun kai kofa, cikin wata irin wahalalliyar murya ya kira sunan Fatima,
duk dakatawa suka yi, ya ce "Kar ki gayawa Ummi halin da nake ciki bana son hankali
ta ya tashin, kin ji ko. " ta gyada kai tana sharar kwalla, cikin shesheka ta ce
"Yayana to kasha magani." Ya ce "zan sha yanzu nan." Ta amsa da "Toh ."suka fice.

Da kyar Amira ta tafi gida ranar, barci kuwa kaurace mata ya yi juyi ta dinga yi,
tana ji kamar ta koma ta kara duba shi duk da dare ya tsala, karshe dai ta lallaba
tayi alwala ta yi nafila ta shiga nema mishi sauki a wajen Allah, tare da mika nata
kokon baran.

Kwanar wahala Al'ameen ya yi a wannan dare, tunda

11 / 23