Author : Aysha Nalado Category : African Stories & Novels
cikin kunnuwansa, "Ya Rabbi! Kaga
niyyata ka dafa mini." Ya furta a bayyane wayar shi ya dauka ya yi dialing lambar
Hayatuttdeen, kamar yadda ya tsammata kiran bai tafi ba, kife wayar ya yi akan
table, shima ya kife kanshi tare da lumshe idanu.....
***********
Da wani irin fushi hadi da bacin rai ya fito daga asibitin, jefa kafa yake yi duk
in da ya samu, idanun shi a rufe, ikon Allah ne kawai ke rike da shi, bai san ina
yake nufa ba, don zuciyarsa ce kawai ke jagorantarsa kwkwalwarsa kam ta dau zafi a
lokacin da bazata iya tantance komai ba.
Wani irin mugun horn ne hadi da taka burki suka ziyarceshi lokace daya, sai dai
kafin ya yi aune tuni motar ta ture shi, duk da ba wani mugun turi bane don direban
yayi iya kokarinsa wajen kaucewa hatsarin, sai da ya fadi kasa.
Gigitacciyar kara ta saki a matukar razane. ba ta san yadda a ka yi ba, ta shiga
komar tunanin shi kamar yadda ya zame mata ibada, kawai ta ji direbanta ya taka
birki, a firgice ta dogo kafin tayi aune kamar kiftwar idanu taga motarta ya ture
shi.
Ita da direbanta rige rigen fita a mota suka shiga yi, kusan a tare suka isa inda
yake, bata tabbatar shi din ba ne, don duk a tuninta gizon da ya saba mata ne, sai
da ta fito daga mortar ta ganshi ra'ayil aini.
Cikin rawar jiki Peter ya isa gare shi don ya taimaka mi shi ya mike, abin mamaki
da daure kai dakatar sa shi yayi ta hanyar daga mishi hannu cikin karfin hali da
jarumta ya dafa kasan titi ya mike tsaye, bai ji mugun rauni ba sai dan kujewa,
sai dai ga dukkan alama ya bugu a kafafun shi ganin yadda tsayuwa ta so gagararsa
da fari, amma yayi ta maza ya cije lips ya tsaya cak.
Tuni ta fashe da wani irin kuka tare da karasawa garesa, a gabansa ta tsaya cikin
kuka take cewa "Na shiga uku na lalace! Yaya Alamen ka yi hakuri, Peter mu kai shi
asibiti, Yaya Alamen ka zo muje asibiti pls jini yana zuba a jikinka." Riko hannun
shi ta yi ta soma kokarin jan shi, gaba daya ta rude bata cikin hayyacinta......
Ku yi manage pls.
Masu comment nagode kwarai ina alfahari daku, jiya kun faranta min sosai dana bude
data naga ruwan comment na shigowa group di na pls Ku ci gaba hakan shine karfin
gwiwata ina sonku sosai masoya mabiya.
[12/29, 2:41 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
~FARHAT~
DAGA ALƘALAMIN👉
*AyshaNalado*
ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiya Writer's Association*
*PAGE 25*
Fashewa ta yi da wani irin kuka, da gudu ta k'arasa gare shi, a gaban shi ta tsaya
cikin kuka da kid'ima ta ke cewa "Na shiga uku na lalace! Yaya Alamen ka yi hakuri,
Peter mu kai shi asibiti, Yaya Alamen ka zo muje asibiti pls jini yana zuba a
jikinka." Riko hannun shi ta yi ta soma kokarin jan shi, gaba d'aya ta rud'e bata
cikin hayyacinta.
Duk da yana cikin halin ciwo, sai da ya ji Yarrrr!!! A jikinsa lokacin da
hannunta ya sauka a kan nasa, da sauri ya saka hannusa d'ayan ya 6an6are hannunta
daga nasa.
Jin haka yasa ta dago da jikakkun idanuta ta sauke a fuskar shi, karaf! Suka su ka
sauka cikin na shi kaifaffun idanun da suke rine, tuni zuciyarta ta shiga wani
irin dokawa da wani irin speed,wasu irin sinadarai masu kama da surkulle ke fitowa
daga idanun shi suna shiga na ta direct ba tare da wani shamaki ba, kasa janye
idanu ta yi daga cikin na shi, duk da irin kaifin da suka mata.
Kayataccen murmushinsa ya sakar mata, ya girgiza mata kai, murya kasa-kasa ya ce
"I'm ok' ba sai kin kai ni hospital ba thank yhu for Ur care." Daga haka ya juya ya
ci gaba tafiya yana d'ingisa kafarsa ta hagu.
Kamar a sume kuma ba a sume ba, haka ta dinga jin kanta, bata farga da ya bar wajen
ba sai da ta tsinkayi muryar Peter yana cewa "Miss ar u ok." Firgigit ta yi ta
kalle shi, ta sake kallon hanyar da al'ameen ya bi, ji ta yi wani kuka mai karfi
ya taho mata from no where, da gudu ta wuce shi ta bude motarta ta fada tare sa
fashewa da kuka.
Jiki a matukar sanyaye Peter ya bude motar ya shiga mazauninsa, ya tada motar suka
bar wajen, zuciyarsa cike da tausayin uwar dakinsa.
*************
Karfin hali da jarumta ce kawai da kuma taimakon Allah suka karasa da shi gida,
zuwa lokacin tuni kafar ta kumbura, baya son ya tadawa su Ummi hankali hakan yasa
bai nufi cikin gida ba ya tsaya dakin shi.
Karar taba kofar dakin ne ya jawo hankalin Fatima dake tsakar gida, da sauri ta
leko don ganin ko waye tunda dai ta riga ta san yayanta ya fita, kuma muddin ya
dawo sai ya shigo cikin gida kafin ya nufi dakinshi, sai dai ga mamakinta shi din
ta gani tsaye idanun shi a rintse ya cike lips yana kici kicin soka key a jikin
padlock.
"Yayana." Ta furta tana karasawa gaban shi, sai lokacin idanunta suka kai ga
kujewar dake gefen fuskar shi da gwiwar hannun shi da ke zubar jini, zaro idanu ta
yi a rude ta ce "Subhanallahi! Yaya me ya sameka?" Kafin ya bata amsa ta hango
kumburan da kafar shi ta hagu ta yi, "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Na shiga
uku!" Da sauri ya bude rinannun idanunsa jin zata yi masa kwarmato, cikin karfin
hali ya yi mata alamar shiii! Da hannu, girgiza mishi kai ta yi tana hawaye sai
kuma ta juya ta runtuma da gudu, "Ya Salam!" Ya furta akan labbanasa, ya fahimci
gaba daya ta rude ne kuma yasan Ummi zata je ta gayawa, sam baiso ba sanin da ya yi
Ummi bata jin dadi yau.
Allah sarki uwa! A kwance take amma jin abin da Fatima ke fada tuni ta mike zaune,
kafin Fatima ta kai aya, ta mike kan kafafunta, ta yo gaba, Fatima ta rufo mata
baya.
"Subhanallahi! Yayan Fatima me ya faru haka, innalillahi wa inna ilaihi rajiun!"
Ta fada cikin tashin hankali ganin yadda kafar shi ta kumbura, "Fatima amshi
makullin ki bude kofar." Fatima dake sharar kwalla ta amsa key a hannun Al'ameen ta
bude kofar, dakyar ya iya daga kafa ya shiga ciki, Ummi da Fatima suka rufa masa
baya, kwanciya yayi, don bazai iya zama ba, Ummi ta sake cewa "Ko dai asibiti zamu
je Al'ameen?" Dakyar ya girgiza mata kai yana cike lips Cike da azaba, sannu suka
shiga rige-rigen yi masa.
Sake kallon kafar Ummi ta yi dakyau ta ce "Wannan kafar taka akwai targade, Yayan
Fatima. Binta yi maza ki je gidan Mallam Surajo mai dori ko yana nan"
Da gudu Fatima ta fice, Ummi kuma ta zauna tana yi masa sannu, daurewa kawai ta ke
yi kar ta zubar da hawaye.
Minti sha biyar Fatima ta yi sallama, Mallam Surajo biye da ita, fitowa Ummi ta yi
a dakin suka gaisa sama-sama ta ce "Mallam yaro ne ya shigo yanzu da kafa a
kumbure, shine nace ta kira ka ka duba ina ganin kamar targade ne." Ya ce "Assshha!
To bari a duba, Allah kiyaye gaba." Daga haka ya shiga dakin Al'ameen din.
Kamar yadda Ummi ta yi hasashe targaden ne kuwa. Babu bata lokaci Mallam Surajo ya
hau aikinsa, duk da cewa kafar bata yi mugum tsami ba, Al'ameen yaji jiki, rintse
idanu kawai yayi yana ambaton sunaye Allah.
Ummi kasa tsahuwa ta yi a baki kofar jin hawaye na shirin zubo mata da sauri tayi
cikin gida, Fatima kam kuka take wiwi ta aza hannu aka.
Bayan wasu mintuna Mallam Surajo ya kammala aikinsa, fitowa yayi ya tarad da
Fatima, ya ce "Yan mata ki gayawa innarku an gama." Ta amsa da to , ta shiga ciki,
tare suka dawo da Ummi.
"Mallam ashe har an kammala, to mungode Allah ya saka da alkhairi, ga wannan ayi
hakuri." Cewar Ummi tana mai mika mishi naira dubun dake hannunta, amsa ya yi, ya
ce "Nagode Hajiya, an kammala an daure kafar nan da kwana hudu zan zo a kwance, an
ma yi sa'a baiyi tsami sosai ba ku ka kira ni, Allah ya bashi lafiya." Da "Amin ya
Rabbi!." Ummi ta amsa mishi, suka yi sallama ya tafi.
Jiki a sanyaye Ummi ta tura kofar dakin ta shiga, cikin hukuncin Ubangiji barci ya
dauke shi, sai dai kallo daya zakasan barcin azaba ne, duk ya hada uban gumi.
Labulen window ta dage ma shi don ya samu iska, daga haka ta fice daga dakin.
Awa biyu ya kwashe yana barci kafin ya farka, zuwa lokacin zafin da bacin ran dake
tattare da zuciyarsa game da abinda Dr Abdul ya yi masa ya ragu kaso hamsin cikin
dari. Shiru ya yi yana tunanin abinda ya faru da shi yadda accident din ya afku da
abinda ya biyo bayan afkuwarsa, bai san dalili ba sai ya samu Kansa da sakin
tattausar murmurshi a fila ya furta "Matsociya." Sallamar Fatima ya katse ma shi
tunani, ganin shi a farke yasa ta saurin karasowa cikin dakin, a gabashi ta zauna
tare da cewa "Sannu Yayana ka farka ya jikin?" Murmushi ya yi mata a hankali ya ce
"Alhmdllh kanwata." Mikewa ta yi tana cewa bari na gayawa "Ummi ka farka." Tare
suka dawo da Ummi, gefen katifar shi ta zauna, cike da tausayawa ta ce "Amintacce
ka farka, yaya jikin?" Ya ce "Ummina da sauki." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Garin
yaya kaji ciwo haka?" Shiru ya dan yi kafin ya ce "Accident na samu mota ce ta
kade ni, amma ba wani mugun kadewa ba kawai dai abin yazo da tsautsayi ne." Girgiza
kai ta yi cike da alhini, ta ce "A ina ne?" "A cikin unguwa ne, na kamo anya ina
dawowa gida." "Asshha!Ubangiji ya kara kiyayewa."
Ranar Al'ameen a gida ya wuni Ummi da Fatima na jinyar shi ko kwakkwarar tari ya yi
su yi ta rige -rigen tambayar shi lafiya me yake bukata, tausayinsu ya kara lullube
zuciyarsa, ya kara tabbatarwa duk duniya bashi da kamar su.
***********
*Amira*
Yinin ranar haka ta yi cikin rashin walwala da faduwar gaba, kullum da tunanin shi
ta ke wuni, sai dai yau duk sanda ta tuno shi sai gabanta ya yanke ya fadi, yau
kimanin kwana uku kenan rabon da ta saka shi a idanunta, takan shiga gidan kullum
kamar yadda ta saba sai dai ta lura kamar yana kaucewa haduwar su da gangan ne,
yau kam tana jin idan bata saka shi a idanunta ba baza ta iya rintsawa, hakan ya sa
ta shirya abin da zata fada a gida don a barta fitowa.
Misalin karfe takwas na dare ta yi sallama a tsakar gidan, Fatima na wajen
Al'ameen don haka Ummi kadai ta tarar a daki, zama ta yi a saman dardumar da ke
shimfide a tsakar dakin, a mutunce kamar ko da yaushe ta ce "Barka da dare Ummi mun
wuni lafiya." "Lafiya kalau Amira, ya dare ya exam." "Alhmdllh Ummi, an gode
Allah." "To Allah ya dafa ya bada nasara." "Amin Ummi nagode." "Ya su Maman Amira,
da sauyan yan uwa." "Duk suna nan kalau." "Ma sha Allah kya isar min da gaisuwa."
Daga haka su ka zauna shiru na dan mintoci, Ummi ta yanke shirun ta hanyar cewa "Ya
akayi ne Amira naga kamar ki na son yin magana." Kasa ta yi da kai ta ce "E Ummi
dama wajen Fatima na zo kuma naga kamar bata nan." "Ayyo Fatima na wajen
Yayanta, da yake dazu ya samu tsautsayi a kafa." Rass! Rass! Haka gabanta ya
yanke ya fadi, bata san sanda ta dafe girji da sauri ba, cikin rudewa ta ce
"Subhanllahi! Na shiga uku! Meya same shi, Allah yasa ba mummunar rauni ya ji ba?"
Shaf ta mance da Ummi take magana.
Ganin yadda Ummi ta zuba mata idanu yasa ta ji wani kunya ya lullu6eta, da sauri ta
yi kasa da kai don gani ta yi kamar Ummi taga abinda ke zuciyarta, basarwa Ummi ta
yi ta ce "Wallahi d'azu ne yana dawowa gida mota ta kade shi har ya samu targade a
kafa, amma da sauki an gyara an daure kafar."
Dakyar ta iya ce wa "Allah sarki! Ubangiji ya ba shi lafiya." Ummi ta amsa da
"Amin." Daga haka shiru tayi zuciyar ta ya raunata ji take kamar ta zubar da kwalla
amma ta daurw saboda a gaban Ummi take, ranar kasa sakin jiki ta yi suyi hira da
Ummi kamar yadda su ka saba ta yi,duk da yadda Ummin ta dinga kokarin jan ta da
hira, ita kanta Ummi ta fahimci tana cikin tashin hankali.
Zaman mintuna ka dan ta kara ta mike ta na cewa, "Ummi bari na je." Ummi ta ce "Har
zaki tafi, to shike nan Amira sai da safe, ki biya dakin Yayan Fatiman, Bintan tana
can daga nan ma kya gaishe shi da jiki." "To Ummi nagode." Ta fada tana ficewa.
Ta kusa minti biyar a bakin kofar dakin ta kasa shiga, dakyar ta yi ta maza ta yi
sallama a hankali Kamar wata mai koyan magana, karfin jin da yake da shi yasa ya
jiyo ta, Fatima kam bata ji, a kan labbansa ya amsa, haka kurum ya samu kan shi da
da faduwar gaba. tsoron shi daya kar ace ta fesa wannan shu'umun turaren na ta.
Minti biyu ta kuma kwashewa kafin ta sake yin wata sallamar ta karo na biyu, wannan
karon da dan karfi, sai a lokacin Fatima ta ji, amsawa tayi , tare da ce wa "Anty
Amira ce Bismillah! Shigo mana."
Kamar wata munafuka haka ta bude kofar net din ta shigo, daga dan nisa da shi ta
samu waje ta zauna, idanunta na kan kafafun shi dake daure, wani irin tausayi shi
ne ya lullu6eta, ji take kamar ta zubar da hawaye, a sanyaye ta dago ta saci kallon
fuskar shi, cikin sa'a su ka hada ido, da sauri ta dauke idanunta daga cikin na
shi, ta mayar kan kujewar dake gefen fuskar shi, don baza ta iya jurar ci gaba da
kallon kwayar idanun shi ba, a haka ta bude baki dakyar ta ce "Ina wuni Yaya Ameen,
ya jiki, ashe abin da ya faru kenan Allah ya sauwake yasa kaffara ne." A jere ta yi
gaisuwar ba tare da ta jira sai ya amsa ba.
Kusan hada baki suka yi shida Fatima wajen amsa mata da "Amin ya Allah." Daga haka
su ka gaisa da Fatima, tana kara tambayarta ya mai jikin, ta amsa mata da
"Alhmdllh."
Zaman shiru na yan sakanni ya gifta, Fatima ce ta katse shirun ta hanyar jan Amira
da hirar islamiyya, kasa sakin jiki ta yi su yi hira kamar yadda su ka saba.
Al'ameen na jin su, amma ya lumshe idanu kamar mai barci, a zuciyarsa kuwa hamdala
ga Allah yake da bata feso wannan bakin turaren na ta ba.
Hirar bai yi wani tsayi ba ta mike ta ce zata wuce, Fatima tace "Kai Anty Amira tun
yanzu, ki dan kara zama mana yanzu fa 8:30 ta yi." Kin zaman ta yi don jin ta take
duk a takure.
Ba don Fatima ta so ba su ka yi sallama, sake satar kallon shi ta yi ganin idanu I
a lumshe ta samu karewa kyakkyawar fuskarsa kallo, har da dan sakin ajiyar zuciya
irin mutum ya samu relief din nan, sai da tayi ma'ishi sannan ta mike tana cewa
"Fati ya samu barci in ya farka kya kara gaishe shi, sai da safe."
Duk abin da take yana kallon ta ta kasan ido har ta fice daga dakin.
Bayan tafiyarta Fatima kimtsa mi shi dakin ta yi ta kashe mishi wuta ta fice don
duk a tunanin ta barcin gaske yake.
Ya dade yana tunane-tunane kafin barci gasken ya yi awon gaba da shi, koda ummi ta
zo sake duba shi itama ta tarar ya na barci ne, gyara mishi rufa tayi ta yi addua'a
ta tofa mishi sannan ta fice ta kulle kofar gidan tunda yau me kullewar na kwance
babu kafa.
Daga nan itama ta wuce ta naimi makwanci asuba ta gari.
********
*JOY*
Daga wurin da accident din nan ya faru direct gida su ka wuce don dama akan hanya
komawa suke, ta je shopping ne.
Har su ka iso gida kuka ta ke yi, Peter duk ya rude sai hakuri yake bata, zama
tayi a mota dakyar ta samu ta tsaya da hawayenta, ta goge fuskarta sannan ta fito
ta nufi Cikin gida, tuni kayan shopping dinta sun isa ciki, daki ta ta yi niyar
shigewa ba tare da ta bari sun hadu da Mom ba, sai dai hakan bai su ba, don a main
parlor ta tarad da Mom, a rude mom da yanzu take nuna mata wani irin soyayya mai
karfi, ta tare ta ganin yadda manyan fararen idanunta su ka rune su ka kankance,
sai dai tambayar duniya ta mata ba amsa data takura mata sai hawaye, a rude Mom ta
sama aka kira mata Peter, a bakin shi take jin abinda ya faru, amma bai gaya mata
cewa Al'ameen ba ne, ba tare da nuna alhini ko tausayi ba take tambayar ina wanda
su ka bige din, nan ya kwashe yadda su ka yi da mutumin ya gaya mata, kuma ya
tabbatar mata dan unguwar nan don ya san gidan su. Cike da jin haushi Mom ta ja
tsaki ta ce "Mitsiyacin banza shi ya sani ai, ya yi wa kansa" daga haka ta ci gaba
da rarrashin yarta.
Wani irin yini ta yi ranar mai matukar azabtuwa ga ruhinta, a duk sanda ta tuno
lamarin kukanta saboda fil yake komawa, hakan ya haifar mata da ciwon barin kai,
sai dai ta yi ta dauriya bata bari Mom ta sani ba gudun kar ta saka mata ayar
tambaya, dakyar da rarrashi ta iya tsakarar abinci haka ta wuni a kwace kamar
ruwa.
Bata gane lamarin ya girmama a gareta ba sai da dare ya yi, kememe barci ya
kauracwa idanunta, don a duk sanda ta rintse idanu shi take gani,cikin raunika da
yadda yake dingisa kafa cike da azaba, haka ta kusa raba dare tana hawaye, dakyar
barci barawo ya saceta, sai dai ko awa biyu bata cika ba ta farka a firgice ta yi
mafarki wai Al'ameen ya mutu, ta shi ta yi daga kwance ta zauna da duwawunta a
tsakiyar gadon ta rafka tagumi tana ta tsiyayar hawaye ji take kamar ta yi
tsuntsuwa ta je taga halin da yake ciki, ya zama dole gobe ta je ta duba ba shi
idan ba haka ba hankali ta bazai taba kwanciya ba.............
Gashi nan harda na jiya😬
Gamai bukatar shiga group ya tu tubeni kai tsaye.
09116099486.
[12/29, 2:42 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
~FARHAT~
DAGA ALƘALAMIN👉
*AyshaNalado*
ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiya Writer's Association*
*PAGE 26*
No editing ayi ta hakuri🙏
Washegari haka Ummi da Fatima su ka tashi da hidamar Al'ameen, abin ma yazo musu da
d'an sauk'i ne saboda shi d'in jarumi ne, bai sakar musu ragamar komai ba, yakan yi
iya k'ok'arinsa, idan ya kasa sannan ya naimi taimako, yanzu ma Fatima ce ta