JOY by Aysha Nalado

Author :  Aysha Nalado Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 23

6K to 9K   out of 68.8K words

kimani shekaru goma sha biyar ba.

Saga da marwa ta tashi yana yi tare da tunanin me ya kamata ta yi, wasl zai taimaka
mata, cak ta tsaya lokacin da kwkwalwa ya hasaso mata mafita.

Kamar zararra haka ta rarumi wayarta ta fara dialing lambar Papa.

Daidai nan kuma Joy ta karaso dakin, tana tangad'i kamar yar maye tsabar bata cikin
hayyacinta, motsinta yasa Mom saurin dagowa ta kalli kofar, gabanta ne ya fadi
ganin yadda Joy ta fita hayyacinta idanunta sukayi luhu luhu cikin kasa da awa
daya, kwarai rauninta yaso ya bayyana a lokacin, saboda ba karamin so take ma Joy
ba, a duniya Joy ce kadararta Joy ce arzikinta Joy ce rufin asirinta, dakewa ta yi
ta dauke kai daga kallonta ta mayar kan wayarta,

Halin da joy ke ciki yasa bata kula da yanayin yadda Mom din ke rude ba, zubewa ta
yi akan gwuiwowinta daga bakin kofar don tana jin tsoron karasawa kusa da Mom, ta
hade hannayenta alamar roko sannan ta sake fashewa da kuka Wanda dama cikin sa
take, ba ta ce ko mai ba sai kuka da takeyi ba saurarawa.

Kiran waya Mom keyi amma gaba daya hankalinta na kan Joy, kukanta na matukar ta'ba
mata zuciya, har ta fara daina fahimtar abin da take yi, zuciyarta ce ke
azalzalarta akan ta rungume Joy ta jawota jikinta ta rarrasheta ta hanata kuka, sai
da ta yi da gaske ta yakice wannan tunanin daga ranta, dan idan yayi wasa ta bari
rauninta ya bayyana ta bazan ta comma burinta na taba Joy da Fatima cikin sauki
ba, juyowa tayi a fusace ta kalli Joy cikin tsawa ta ce "ki fita ki bani waje Joy
bana son ganin ki." Joy data kara tsorata da lamarin Mom ta dago murya na rawa ta
ce "I'm sor!!!" Kafin ta karkare fadin abin da zata fad'a Mom ta sake daka mata
tsawar data fi na dazu " I said get out from here." Ta karashe maganar tare da
yiyowa kanta kamar idanu waje, da gudu ta fice daga d'akin tana rizgar kuka.


**********


Ko da Fatima ta isa gida, a daki ta samu Ummi, ta dan kishingid'a akan darduma da
alama sallah tayi ta idar, Sallamar ta yasa Ummi da barci ya fara kwasarta ta bude
idanu, ganin haka yasa Fatima cire takalmi ta karasa shiga dakin ta na cewa "Ummi
sannu da gida."
"Yawwa Fatima kin dawo."
"Eh Ummi Allah ya dawo dani."
"Maza ki debi ruwa ki dauraye jikinki ki kimtsa ga abincin ki nan a kitchen ki
dauka.

Bayan Fatima ta fito wanka dakin ta shiga ta kimtsa jikinta ta canza pad, wardrobe
ta bude ta dauki kayan da zata saka, har ta ciro Riga da zani sai idanunta ya
sauka akan wani Riga da siket na kanti da take da shi na gwanjo, ta Dade ma rabonta
da sakawa, haka nan ranar taji tana sha,awar saka kayan, cirowa ta yi ta shirya
cikin su, kayan sun mata kyau sai dai sun kamata tsam dai dai jikinta sabanin da
da suka mata dan yawa yanzu har skirt din ya d'angale mata don iyakarsa 'kaurinta,
amma dai sun bala'in yi mata kyua.

Abincinta ta dauka ta ci , ganin Ummi ta samu barci yasa ta yi kwanciyarta a daki,
tare da Ciro wani story book data amsa hannun Joy ta fara karantawa, tana fara
karatun itama barci ya kwashe ta nan ta yada book din ta tintsire.

Kiran sallar la'sar ne ya farkar da Ummi, ta shi ta yi ta fito tsakar gida
dan ta dauro alwala ta na cikin zuba ruwa a buta Al'ameen ya shigo cikin gidan,
shima kiran sallar ne ya tada shi ya shigo don ya daura alwala ya lallaba ya tafi
masallaci,

"Sannu Ummi." Cewar Al'meen kallon shi Ummi ta yi lokacin ta zuba ruwa ta tsuguna
daga bakin makwarari zata fara alwala ta ce "yawwa yayan Fatima ya jikin." "Da
sauki Ummi." Ya ce yana shigewa makewayi, koda ya fito Ummi ta idar da alwala ta
shige daki don ba Iya kama ruwa yayi ba, sake diban wani ruwa yayi a drum ya
tsuguna ya yi alwala, sannan ya fice zuwa masallacin kusa da gidan jin ana haramar
tada sallah.

Sai da Ummi ta idar da sallar ta tashi Fatima, akan taje ta wura wuta ta daura
ruwan tuwo tunda yau alhamis basu da islamiya.

Bayan Al'meen sun idar da sallah fitowa yayi daga masallaci, kallon yanayin garin
yayi, ko'ina shar haka kawai yaji yana sha'awar yad'an zazzaga, Abokin shi Aliyu ne
ya fad'o mai a rai murmushi yayi a fili ya ce "dan duniya nasan yana gida yanzu,
bari na mike kafa na kai mishi ziyarar bazata." Kallon jikin shi yayi, ganin,
kananan kaya ne a jikinshi wandon jins ruwan kasa da T shirt fari mai layilayi
bakin, bai ciki son fita da kananan kaya ba, amma ganin rigar bai matse shi ba
yasa ya kama hanyar unguwar su Aliyu a kafa kasancewar basu da nisa unguwa daya ne
a tsakanin su.

Stadium junction nan ne unguwar su Ali, a kofar gidan ya tsaya ya aika aka mishi
sallama da shi, Aliyu ya fito yana waige waige, daga bayan shi yaji an ce "Aliyu
timekeeper." Da sauri Ali ya juyo jin muryar da bai zata ba, a d'okace ya nufe shi
ya na fadin" A'a ustaz! ustaz! ustaz! ustaz!!!! namu." Hannu Al'meen ya bashi suka
kashe suna dariya, Al'ameen ya ce "Babban timekeeper babban timekeeper" suka sake
kwashewa da dariya.

Sunaye ne da suke kiran junan su tun a makaranta, hakan yasa koda aka gama karatun
aka rabu ba'a bari ba, haka suke kiran junan su dama sunan makaranta ya gaji haka,
hakan dabi'a ce ta dalibai duk Inda aka had'u komi tswon zamani kuma duk komin
munin suna haka za'a kira juna, Ali ya ce "gaskiya ka shammaceni ustaz ban taba
zaton kai ba ne." Al'meen ya ce "Ai baka da mutunci Ali, baka da kirki baka
zumunci." Ali ya ce "Wai talle ne zai ma Audi gori ba gara ni ba ma ina kira a waya
a kai a kai kuma ko last time na haduwar mu ni naje gidanku ko ka manta ne na tuna
maka." "A'a fa Ali ka dai sake tunawa." Cewar Al'ameen, haka dai bayan sun gama yar
musu as ka gaisa da tambayar ahalin juna daga na suka nemi waje suka zauna kan
dakalin kofar gidan su Ali suka shiga hira suna kwasan dariya.
Al'ameen bashi da aboki sama da Ali don shi ba mai yawan kwashe kwashe bane , tare
suka yi makarantar primary nan IBB Inda bayan sun gama suka wuce maitunbi secondary
school tun jss 1 ajin su daya har suka kammla gasu kuma yan unguwar kusan daya,
hatta iyayensu sun san da zaman juna, yanzu da aka gama secondary kowa ya kama
gaban shi shine zumuncin yayi wuya duk da suna tare a waya Bini Bini saduwace dai
sai a hankali.

Fira ce ta barke sosai, Aliyu ya siya musu awaran waken auya da pure water suka ci,
sun sha fira sosai suna ba juna labarin makarnata da karatu, shi shi Aliyu direct
university ya tafi yanzu haka FUTmin yake zuwa yana 200 level yana karanta
languages, inda Al'ameen ke juwa JEFLA yana karantar bangaren Islamic low shima
yana year 2 ne kamar dai Aliyu, sun Dade suna hira kafin Al'ameen ya mike yace zai
wuce ganin biyar da Rabi ake nema.

Taka mishi Ali yayi suna tafe suna ci gaba da hira, sunzo dai dai get din stadium
wasu yan mata su uku suka fito daga cikin wajen kowaccenau cikin matsatsen JC kai
ba dankwali daya da jakar baya goye a bayan ta dayar kuma hannunta kwallo ne suna
tafe tana buga shi fa titi tana cabewa, da ka musu kallo daya zaka san yayan arna
ne.

Tsaki Al'ameen yayi tare da dauke kanshi a zuciya yana ambaton Allah da neman
tsari daga shaidan, kallon shi Aliyu yayi ya ce "Ustaz namu har yanzu kanan nan da
tsantsenin ka akan irin wadan nan matan." Al'meen yace "To ina amfanin wannan Abu
haka don suna yayan arna sai su rika yawo haka suna fidda tsiraicin su, kamar wasu
awaki, ya kamata gamnati ta dauki mataki don naga abin masgaba yake kara yi."
Aliyu ya ce "waya gaya maka a zamanin yanzu yayan arna ne kawai suke irin wannan
dressing, yanzu ai abin babu arna babu musulmai, don idan kaga wata yar musulman
sai ka zubar da hawayen takaici yanzu haka wadan nan ma in ka bibiya musulmai ne."
Da sauri Al'ameen ya ce "kai haba Allah ya sauwake, wadannan yayan arna ne babu
hasken musulumci ko kadan a tare da su." Kafin Aliyu ya kai ga amsa musa suka jiyo
muryar d'aya daga cikin yan matan bahaushiya rass tana cewa "Aisha, maryam pls Ku
jirani na sai ruwa." Dariya Ali yayi yana cewa "you see ustaz me na gaya maka."
Takaici da bakin ciki ya hana Al'meen amsawa, Aliyu ya ce "Hmmm alamarin yanzu duk
sai a hankali fa kalli wasu ma." Ya Nuna mishi wasu yan mata dake sanye da atamfa
amma ya matukar matsesu kamar in suka yi kwakwaran nishi zai barke, girgiza kai
Al'meen yayi cikin takaici da wannan yanayin suka rabu da Aliyu ya kama hanyar
gida.


*****

Tunda Joy ta bar dakin Mom ta komawa dakin ta kan bed ta fada yana kuka ga ba ci ba
sha, har kusan karfe biyar na yamma hakan ya saukar mata da zazzafan zazzabi mai
hade da ciwon kai kafin shidda na gamma ta gama fita hayyacinci dkyar take sauke
numfashi, Abu ne da bai taba faruwa da it's ba run tasowarta jinshi take yi sabo a
gareta ,bata saba da hakan ba a kullum tsakanin vta Mom kulawace na musamman da
Nina kauna haka ma Papa shiyasa duk ta wahala ta kasa sukuni......


Share pls kuma a dan ringa taba comment ko babu yawa, ta hakan ne zan gane kuma
bite dani ko A'a


Me bukatar shiga group a tuntubeni ta wannan lambar
09116099486
[12/29, 2:30 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

*BY*
*AYSHA NALADO*


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

*LITTAFI NA ÆŠAYA*


*PAGE 5*


Da takaicin wad'annan y'an matan Al'ameen ya kamo hanyar gida, daf magriba ya iso
k'ofar gidan su, ganin ana shirye shiryen yin salla yasa bai shiga ba ya nufi
masallaci, koda suka idar bai tashi ba zama yayi a cikin masallacin yana addu'o'i
tare da neman Allah ya kareshi daga sharrin ta'bar'barewar zamani, bai fito daga
masallacin ba sai da aka idar da isha'i, daga nan kuma bai zame ko ina ba sai gida.

A tsakar gida ya samu Ummi zaune kan shimfidar babbar tabarma, tana sauraren
labarai a redio kasancewar mace mai yawan sauraren labarai, zama yayi a gefen
tabarmar bayan Ummi ta amsa mishi Sallama, "Ummi sannu da gida." Ya fad'a yana
gyara zaman shi da kyau, "Yawwa yayan Fatima ka dawo dama yanzu nake zancen ka a
zuciya, ashe kana tafe." "Eh Ummi na tsaya na yi sallah ne gaba d'aya." Ummi ta
ce "yayi kyau. ya karfin jikin." Ya ce "Alhamdulillah Ummi naji sauki sosai, da
nayi sallar la'asar ma na kaima Aliyu ziyara ne." Ta ce "Allah sarki Aliyu yaron
kirki makaranta ya boye shi, yana lafiya." "Yana lafiya Ummi yace yana gaisheki
sosai, "
"Allah sarki Aliyu d'an gidana ina amsawa ." Murmushi Al'ameen ya yi tuna tsakanin
Aliyu da Ummi.

Fatima Ummi ta kwalawa kira, daga can kuryar d'aki ta amsa tana tasowa daga kwancen
da take har zuwa lokacin riga da skirt din nan ne a jikinta, ji ta yi Ummi na ce
wa "Ki zo ki kawowa yayanki tuwon shi ga shi ya shigo." Jin haka yasa da d'aukinta
ta koma d'aki ta d'auko ledar yalon data siya mai d'azu a hanyar makaranta ba ta
samu ta ba shi ba, ta fito fuskarta washe da fara'a, tana ji dadi zata farantawa
yayanta, hankalin shi na kan daddana yar wayar shi buttus, ya tsinci muryar Fatima
na cewa "Yaya sannu da dawowa." 'Dagowa ya yi yana amsa mata da "Yawwa Fatima ya
gi." Sauran zance ya ma'kale lokacin da ya sauke idananun shi a kanta, ran shi ne
ya baci ganin shigar dake cikin ta, ta ke ya had'e rai yana binta da wani irin
kallon da yasa gabanta fara dokawa.

Lokaci daya fara'ar dake fuskarta ya juye zuwa tsorata, ta ke ta fara ja da baya,
bata kaunar ganin wannan fuskar na yayanta, firgitata yake yi, ya kan mata irin
wannan kallon ne a duk sanda ta yi wani abu ba dai dai ba, tunda ta ke da shi bai
taba d'aga hannu ya duke ta ba, sai dai ya kan ladabtar da ita da hanyoyin data
gwammace gara ya faffala mata mari akan su.

Ummi bata san meke faruwa ba hankalinta na kan rediyonta tana kokarin canza channel
ta tsinin ci muryar Al'ameen cikin kaushi ya na cewa "Zo nan Fatima." Ya karashe
maganar yana nuna mata gaban shi.

Bata iya mishi musu run tasowarta, hakan yasa ta shiga matsawa a hankali kamar
kazar da kwai ya fashewa a ciki, nesa kaÉ—an da inda yake nuna mata ta tsuguna, ta
re da duƙar da kanta kasa, a banza ma wani lokacin bata iya haɗa ido da shi balle
yana cikin iri wannan yanayin.

Ummi dai da ido ta bisu su bata tanka ba a ranta tana kunfi kusa.

Ciki muryar shi mai dauke da amon bacin rai ya fara cewa "Fatima wannan wacce
irin shiga ce kika yi haka kina yar musulmai," tsuru tsuru ta yi tana zare ido,
cigaba yayi da cewa "Ashe ba na hana ki saka kayan da zasu bayyana surar jikinki
ba, ina duk tarin suturunki na mutunci da nake dinka miki? Shiru tayi ba amsa ya
cigaba "Ok na gane tarayyarki da yar arna abin yayi 'kamari har kin fara
kwaikwayon dabi'u da shigarta ko?."

Tuni Fatima ta fara girgiza kai tana kuma jin abin da me fitowa daga bakin
yayanta, "ina tambayarki baki bani amsa ba kina kuka, nace tarrayyarki da yar arna
abin yayi kamari har kin fara dauka dabi'unta ko, to wlh ba a nan gidan ba, kuma
zan yi wa tufkar hanci, tunda ke naga alamar bakin jin magana, don bazan zuba ido
ke kadai yar uwata da nake da ita a duniya ta lalace ba, zan dauki kwakkwaran
mataki akan ki dake da ita wannan yar arnan, domin hakkinane na kula da
tarbiyarki."


Ya kai minti ashirin yana mata fad'a ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba
haushi da takaicin daya kwaso na yan matan da ya gani a hanya, da kuam haushin
kawancen ta da yar arna da yake ji, duk Sai da ya sauke mata su, kafin ya tsagaita
yana kallonta yana huci.

Zuwa lokacin kuka Fatima keyi kamar ranta zai fita, daga yadda take jin amaon
sautinsa tasan ba karamin baci ran shi yayi ba,ko daman bashi hakuri bata samu ba,
jin yayi shiru yasa cikin shessheka ta ce "Yaya ka yi hakuri walla..." Dakatar da
ita yayi da cewa "rufe min baki mutuniyar kawai, kuma ki bace min da gani."

Dasauri ta tashi tana toshe bakin ta saboda sabon kukan da ke shirin kwace mata,
ta kai bakin kofa ya d'aga muryar ya ce "kuma ki ciro kayan ki kawo mi yanzu
yanzu."

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke, bata ce komai ba, a ranta Sai hamdala take da tasbihi
ma ubangijinta tasan ko yau ta fadi ta mutu Fatima baza ta tagayyara ba in dai har
da Al'ameen a gefenta, kallon shi tayi shima ita yake kallo, kallon tuhuma, saukar
da kai kasa yayi cikin taushin muryar ba irin wanda yama Fatima magana da shi ba ya
ce "Ummi kinga abinda nake gaya miki, kinga abin da nake so ki hango amma kin kasa
hangowa Ummi tararryar Fatima da yar arnan nan wlh na tabbata babu alkhairi a cikin
sa, Sai sharri Ummi ki buba wannan lamari dan Allah."

Murmushi Ummi ta yi a ranta ta ce "yaro yaro ne kuma duk abinda babba ya hango
akace yaro ko ya hau rima bazai hango ba."

Jin Ummi bata ce komai ba sai bin shi da kallo da take yi yasa ya mike ya nufi
haryar zaure ran shi duk ajagule.


*********


Joy na barin dakin Mom dakinta ta koma, ta fada kan bed ta cigaba da kuka har zuwa
lokacin ko takalmin makaranta bata cire ba bare uniform haka ta wuni a daki ba ci
ba sha, har wurin karfe biyar na yamma hakan kuwa ya saukar mata da zazzafan
zazzabi mai hade da ciwon kai, kafin shidda na yamma ta gama fita hayyacinci
dakyar take sauke numfashi ko idanunta bata iya budewa.

Abu ne da bai taba faruwa da ita ba tun tasowar ta, jin shi take yi sabo a
gareta ,bata saba da hakan ba a kullum tsakanin ta da Mom kulawa ce na musamman da
nuna kauna duk girman laifin da zata yi cikin rarrashi ta ke nusar da ita, haka ma
Papa shiyasa ta ke ganin abin da girma.

A bangaren Mom kuwa rudanin da take ciki ya shallake tunaninta, hakan yasa bata bi
ta kan Joy ba.
Karfe shida da rabi dai dai motocin Papa suka yi parking a counpound din gidan,
fitowa yayi bayan daya daga cikin escort biyu dake biye da shi ya bude mishi kofa,
fitowa yayi jacket din suit din shi a kafad'a hannushi rike da briefcase din
shi, entrance din gidan ya nufa zuciyar shi cike da bege da kewar iyalan shi,
ma'aikatan gidan sai kwasan gaisuwa suke yana amsa musu da fara'a,

Koda ya shiga main parlour babu kowa bai damu ba, upstairs ya haura yana kiran
sunan baby kamar yadda yake kiran Joy, yayi mamakin da har ya 'karasa hawa saman
ya isa babban kayataccen falon daya fi na kasan kyau da kayatuwa, baiga ta fito da
gudu ta tare shi ba kamar yadda ta saba, to ko dai bata gidan ne? Ya jefawa kanshi
tambaya.


Bai samu wannan amsar ba Mom ta fito daga dakinta, sakar ma juna murmushi suka yi
wanda ita nata iyakarsa la'b'ba, bud'e mata hannayenshi yayi ta fad'a jikinshi suka
rungume juna cike da soyayya,cike da kissa take mai sannu da dawowa yana amsa mata
da zuciya d'aya cike da kulawa, amsar jakarshi da jacket din shi ta yi ta kama
hannunshi zuwa dakin shi.

Wanka ta taya shi yayi, ya shirya cikin kayan zaman gida, zama yayi a falon wanda
ke hade da bedroom din shi, yana amsa called, fita Mom tayi ta dawo dauke da ruwa
da lemon five alive a tray, zuba mishi ta yi ta mika mishi amsa yayi yana murmushi
ya ce "thank you Sweetie." Itama murmushin ta yi ta zauna a gefen shi ta maida
idanunta kan TV duk da kallo kawai ta ke yi hankalinta baya gurin, sama da minti
talatin Papa ya kwashe yana waya da wani tsohon abokin kasuwancin shi wanda suke
shirye shiryen had'akar Samar da wani kamfanin sarrafa 'karafina a Lagos.

Ko da ya ajiye phone din Mom bata kula ba, muryar shi ta tsinta yana cewa "Hala
baby bata nan ne?" Ta amsa mai da "tana nan, tana dakin ta." Murmushi ya yi ya ce
"yau mulki take ji baza tazo ta ma Papa

3 / 23