Author : NONE Category : African Stories & Novels
sanda yaje koda na kwana uku ne sai ya kawo tsaraba na ayana kuma me shegen tsada yake kawowa.
silent war dake tashi atsakanin ibaad da uncle moh din yasaka ayaana a wutar tsakiya, ibaad ya dawo yana mata tsauri, akan tsafta, bacci, ko ana kallo zaizo ya koreta acikin yan uwanta ya hade rai yace taje bacci, dole tay karatu hadda zai takurata wani bin tanayi bakinta na bari. duk sai ya zamo bata samun sauki face wajen mujaheed.
har karya takeyi ma uncle moh dan karta karbe abun hannunsa dan ta samu sakin fuska awajen ibaad koda rana dayane amma sam sam yaki shidakansa saiyaje ya bawa hajy mairo yace ai abu kazan nan na ayaanah ne a ajiye mata ita kuma da zuciya daya take daukar abun haka zata kira ayana tasata karba dan dolenta babu yadda ta iya msmn ma da yanzu yafara hadawa da yaransa yana siya musu duk dama baikai wanda yake bawa ayaanah a idonsu, da kuma bayan idonsu ba.
abubuwan dake faruwa sunyi affecting din ibaad sosai,
musmn daya gane cewa wann ƙarin daukaka da sabon budin da uncle moh ya samu na kudaden larabawa shine ya saka izgilinsa ya karu sosai yake yin abunda yagadama
,ynxu duk gidan babu wanda ya isa ya hanasa yay abunda yaga dama koda sau nawa ammi karama zata masa magana baya daukar maganan ta da mutunci a idonsa bare kuma matarsa da tunda ya samu karin daukakar yake balain manipulating inta da soyayya yana baza mata bakin aljihunsa busines dinta tana wasa da kudinsa aciki duk ya rudeta ta zama koda taga abu marar kyau bata wani daukar abun serious kuma daga yay mata bayani kadan sai ta shashantar. hakan sosai ya kashe ma ammi karama gwiwa, ita kadanta tasan cewa ayaana kwata kwata batason komi dayake faruwa tskaninta da uncle moh, amma ganin ya rufe ma matarsa da yaransan ido duk basu korafi tarasa ya zatay, gashi alkwari tay bazata kyale ibaad ya tunkare case din ba, dan tasan duk randa tabarsa yay magana akan ayaaana bala'in da uncle mohd zai kunce agidan basu san karshensa ba...sam sam bataso ibaad yay fada da uncle dinsa musmn akan ayaana gani take kamr zaiy affcting abubuwa dayawa agidan.
ibaad ya shiga wani yanayi wanda har yakany amusing din zainab arifa, wani bi, she enjoys the bully da takurin dayake ma ayaana,dan duk sanda taga ayaana tana takure ko tana kuka sanadiyar masifar ibaad bakaramin dadi hakan yake mata aranta ba.
within 2 months it became so clear that uncle moh yana opressing din lamarin ne da kudi, dan yasan ata nan ne kawai ibaad ko wani agidan bazai iya taka mai burki ba.
business din da ibaad yake cewa saiya gama 2nd semester dinsa ne zaiyi sai yaji yafara shiga ransa cos he feel he had to do sumting to get ayaanah out of that complicated situation da uncle moh yake kkrin cusata aciki
yana cikin wann nazarin suna daf da fara shirin exam zainab arifah ma tafara nata makircin, inta zo gidan taga ayaanah atakure tana karatu ita daya ko an hanata fita sashen su anty safera sai tadinga cewa ai ayaana tana bata tausayi, haka zata bita har daki tana pity petting inta, wann wkdn din ana zuwa tazo ta same ibaad da kinibibi tafara ce masa yadda take takura ma rayuwar ayaana ynxu tana bata tausayi dan haka tana so ya bata permission zasu je shopping hala ta samo mata farinciki acan" he was so pissed wai har da ce masa tausayi yarinyar take bata..yace atleast she is grounded. zainab tace but she is just so vulberable i kind of pitying her. yace you dont pity urself da everything u want weda good or bad u must get it? tace excuse me how is dat a bad thing?
yace mata abar tausayi ai itace wanda aka traineta batasan darajar kanta ba. maganan ya mata zafi sosai ranar da fushi ta koma gida. ranar gabaki daya ransa a mugun bace yake, ayaana tana lura dahshi yau ko abinci baici ba...wani tunani tay, can da yamma bayan ishai kafin su wuce gida, taje kitchen ta debo abincin ta kawo masa har dakinsa, wanda dakyar da wahala ya kulata. haquri ta dinga bashi ita kanta bata san asali meyasa take bashi hakurin ba. dayaga tay masa kuka sosai kuma yasan hanklinta sam ba akwance yake kwana biyun nan ba sai ya hakura ya sauko sun jima a dakin nasa yana mata nasiha cewa kwata kwata tadena amshar wani abu awajen wani namiji koda shine yake bata abu excessively haka kartana karba sabida one day wnnan abun zai zamo mata trap ko wani abun gori. har ransa baiso da ya gaya mata hakan a fili ba duba da age inta, amma ji yake kamr uncle moh ba tsakani da Allah yake mata wasu abubuwan ba. kuma yana amfani ne da matsayinsa akansu yake yin abunda yaga dama dan yasan yana da bakin da zai iya magana hajiya mairo ta amince dashi kai tsaye.
kusan ma akan uncle moh ya mata fada amma da wayo kuma sosai ta fahimce shi duk da ma bai ambace suna ba. since that day datay shagwaba ta rarrashe yayanta suka dawo dede ya dena fushi, a satin gabaki daya sai ta fara wani irin silent rashin kunya, daga zaran uncle moh ya saya mata abu kai tsaye sai tace masa atambaye yaa ibaad in yanaso ta karba...
tunda tafara masa haka na daya na biyu dayaga abun nata dagaske ne tuni yaji ya fara mugun hatsala, ranar jumaa da sassafe ana fita a sallan fajr ya kada jallabiyarsa ya wuce sashen hjy mairo da zimman kai karar ibaad game da wann magana da ayaanah take furtawa....
# atattauna monday in sha Allah zamu tashi da zafin tsiya.....💋❤️
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*
*WATTAPAD @SURAYYAHMS*
*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[01/12, 11:42] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahm.
⏯️3️⃣4️⃣
Tun gari bai gama wani washewa ba uncle moh ya karaso cikin sashen hajiya mairo, lkcin ita kadaine azaune acikin sashntan tamike sawun kafafunta akan wata lallausar sallaya, tafin kafar nan ya gama jin bakin lalle asalin na gagajiya sai sheqi yake yi,cikin sashen banda qamshin turaren sandal balls babu abunda ke tashi koina ya dau tsafta da qamshi
lazimi take bugawa da katon carbi a hannunta tana Allah Allah tagama tajawo wann hadadden herbal tea dake tashin kayan qamshi gabanta da surkuwnta fatima ta kawo mata a flask yanxun nan, tana cikin wann yanayin taji an doka mata sallama..
"salama alaikum
jin muryan autarta ne yasa maza ta gyara zama tun bai karaso ba tace"muhammadu??
sai da har ya shigo da baqin jallarbiyrsa snn yace naam hajiya nan take ya zube kasa ya zauna da ladabi yace "hjy an tashi lafiya? tanata kallon murdadn fuskansa tace "kalau, mohammadu yaya kake, yaya kuma yan jikokina? tun be amsa ba cikin kyabe baki tace jiya anan nan yarka kulthum tazo ta shanye min madara na kuma nace mata bata isa ba wallah saita biyani, wai haka kuka rainesu ne in zasu sha conflaks sai sun zuba kusan rabin kwankwanin madara a kofi? yara basu san maleji ba, basu gaida me maleji, hm yyl haka kawai ana zaman kalau bazaku turo yaranku suna kassara ni bazai saku ba
..cikin karkadai tare da katseta ahnkli yace "wai har kayan madarar taki ya kare ne mama? tace o,o nifa bance maka yakare ba wnn tsakanina da jikokina ne kasan dai fada baya karewa amma dai ya kamata ku koyawa yarku kulthum maleji wani shegen namijin ne ynxu zataje gidansa tana masa irin wann barnan madaran baikoroto ba hmmm..
yaja ajiyan zuciya cike da ji dakansa yace koma yaya ne zuwa anjima zansaka akara stocking miki kayan shayi tunda ke da jikokin naki kike sha, mama in kulthum bata sha madara yanxu sai yaushe zata sha? ..kyabe bakinta tay tace toh toh shikenan, ai yarka ce banawa ba. kudai dake barnan kudi dama baya muku wuya..ohhh ni mairo Allah na tuba yaushe ma aka kawo wnn din baifi sati biyu ba inbanda shegen kwadayin yara inama nake da lkcin shan wayanann abubuwa,.. hmm toh ya aikin naka kuma ince dai komi lafya?
fuskarsa ba asake sosai ba yace lafya kalau hajiya...bari na zuba miki shayin ki kisha dan wata magana nake tafe da shi kuma sauri nake zanje na shirya naje aiki .
cikin kwalo ido game da dafe kirji tace tohhhh..ince dai ba wani aure zaka jajibo mana ba muhammadu..ku fa maza ba dama kuga matayenku sunyi bulbul suna walwala agida caraf saiku kawo batun mata kishiya..yaushe ma safeeran ta gama haifa maka yaya da har zaka fara batun dankara mata kishiya kai jama'a..
jawo flask din yay yanakan zuba mata shayin a cup a nitse yace "hjy bance miki fa aure zanyi ba dan Allah karki kaini gaba..
tace amma ai zakayin ko? nifa uwarka ce duk naga take taken ka wallah..
dan karamin murmushi yay yace ehh tohh idan zaku bani mata agidan nan ba..
dan dariya tay tace "mata agidan nan? kaji wani maganan banza yo safiya yar cikinka zaka aura,.. ko kuma waye kagani ya dace dakai agidan nan, zaidu dai ya rigaka furtamin sunan fatima..kai da Allah gayamin meke tafe dakai kawai bana son shashanci.
sauke ajiyan zuciya yay ya kalleta with serious face snn yace "hajiya bawani abun tashin hankalii bane..kawai dai yadda abubuwa suke tafiya agidan nan ne basu min dadi, kar nay magana ace na tsane wani yaro wani ina fifita shi Dan haka gaskiya ni zan gaya miki abunda ake min agidan nan bana jin dadinsa dan na lura kamr yaran nan gabaki daya basa ganin girmana kuma iyayensu mata ne ke daure musu gindi...inba haka ba harnine za'a dinga min gadara agidan nan,wai ace na bada yarinyarnn kyautar abu sai taki karba tace wai sai wani wawan yaro agidan nan ya bata izini akan shi waye ne? zaman aure ne a tsakaninsu ko kuma shine ubanta, ni sam bana so na ja wata magana, amma tun da yarinyar nan dai jikarki ne, kece zakiyi masa magana dan duk gidan nan wallh babu wanda zai iya dukana acikin yaran nan, dan haka banaso akaini bango na harzuka na ci uban yaro acikinsu babu wanda yafi karfin duka wajena.
aje kofin shayi tay cikin
katsesa tace kai kai kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun haba haba haba muhammadu..wai kai da waye haka kake wann masifa da boye boye, banason mita kmr matar mamaci kawai fito fili, waye ya rainaka? waye kuma tantirin marar kunyar acikin yaran nan da suka hada meeting sukace zasu bugeka suna hauka ne da zasuce maka zasu casaka? wai waye yay maganan nan gaya min nikaina saina ci ubansa
cikin harde ransa yace hajiya aikinsan waye ne basai nakama suna ba amma inhar kinaso na kama sunan shikenan akan ibaad da ayaanah nake magana.
rike baki tay cikin sassauto da murya tace tohh shikuma rayyanun meyay maka muhammadu Allah sarki naga bayama shiga harkan ka meye hadinsa dakai kuma
adan hatsale uncle moh yace" a'a..hajiya dakata min, dan Allah karki wani fara bin bayansa da wann irin pretence din dan ko ke nan kinsan anjima ana nuna min ban isa da yarinyar da kika kawota gidan nan ba, yakaiga maman safiya saitana tsare ni dawasu irin maganganun banza kamar tamaidani yaro bansan menakeyi ba dan ina bawa ayaana kyautuka ya zama ana kallona kamar mutumin banza, duk sabida ke nake yin hakuri na shareta sann ina bata girmanta kasncewarta ex matar yayana amma bafa tsoronta nakeji, bana son raini, bazan kuma lamunci raini musmmn daga wajen marar kunyar Ɗanta dake neman shiga harkata akan yarinyar nan ba..wai tukunma ma ni a'ansa ne? gaskiya hajiya kija masa burki, ya kyale yarinyar nan tunda shi ba ubanta bane kuma ba aurene tsakanin su ba..kar ya kara hanata karban abu awajena idan ba haka ba wallah agaban yarinyar saina ci masa mutuncin da bzai kara iya daga ido ya kalleta ba bare ni...
cikin hade fuska tace kai subhanallah toh ya isa haka
..shi rayyanun ne yace ma ayaana tadena karban abu awajenka baki da baki ya gaya maka haka?
yace "aa baifada min baki da baki ba,amma ai kullum nabata abu sai tacemin wai inje intambayesa kenan shine yahanata karba, nifa wallah munafurci ne banaso...a fito fili mana, inkema bakisone in saka hannuna akan yarinya ne akigaya min saina san anware ni, saina bar muku yarku dama ai gwaninta ni bai karbeni ba, wani abun da akeyi agidan nan na rainin wayo ai ba isa ayi ma yaa zaidu ko yaa zayyanu ba saini da aka raina ma wayo
juyowa tay ta kallesa tace kai muhammadu wallah kafiye fadin rai abu kadan saika fara hada kanka da yayunka shi zayyanu ma ina ruwansa shidaya tsine ma uwarsa? zaidu kuma kasan baya mita girma ya kamashi kaine dai kake halinku na yan auta haryanxu..
...shikenan kaje, naji korafinka bari shi rayyanun yazo ni da shi zamuyi magana kaima sai akai zuciya nesa. banason ayi abun kunya yadda rayyanu yake zuwa gidan koyan dambe (gym) yana dada buduwa yana kato kowani rana, ai da kuyi abun kunya dashi gara duka kawai ahakura da rainon abarmin yarinya kawai zan maidata ma zaidu sai shiya riketa agidan sa, dan wallh haka kawai bazaka kama dambe da yaran cikinka ba..Allah na tuba wallah dukanka rayyanu zaiyi kaine dai baka kallesa da kyau ba toh wallh ahirrrrr dinku nahana wnn magana, wanda yake zuwa gidan dambe kam bazaimin asarar haihuwa ba gara shi uwarsa bata tsufa ba koyau tay aure zata iya sake haihuwa.
da dan bacin rai a fuskan uncle moh yace "Allah ya kiyaye ya dake ni, ohh ashe dama tsoron sa kikeji kenan ko hajiya? zatay masa magana a zafafe yace toh wallh ba'a isa dai akan dan wnn maganan a daga yarinyar nan agidan nan ba..kawai ki masa magana inba wai tsoronsa kikeji ba..ko so kike ki gwada ma duniya maganan da ake fada game da ke akan uwarsa fatima ya tabbata gaskiya, dama ance kwata kwata baki kaunar lefin fatima kusan kowa ya san da haka
..toh wallah bazaiyu ba, akan shi waye...?
cikin daga mai hannu tace "toh naji. yanxun nan zan kirashi zaizo zan masa magana kuma koma miyene zakaji ayi hakuri akai zuciya nesa.
daga haka suka karkare maganan bayan ya dan zauna da ita na wani lkci ya ciro cheque na kudi wanda ya shirya tun jiya ya bata yace toh ga goron jumaa hajiya"..daukar cheque din tay tagani kudi ne meyawa tana murna tafara saka mai Albarka daga nan ya tashi yakoma sashensa domin ya karya ya shirya ya fita.
Tun bayan haka hajiya bata sake dago wnn maganan ba, har saida taje shago ta zauna kafin ta dinga kiran ibaad awaya yanata ringing bai dauka ba karshenta basu hadu ba sai har washe gari ranan asabar, kowa ya taho, su ibaad ne farko farkon zuwa gaisheta aka gaisa lafiya ana zama kenan tafara dago maganan acikin mutane. ga bappa zaidu, gasu maheer da mujaheed da su anty safeera, kananan yaran ne kawai basu nan
kamar maganan arxiki tafara nasiha cewa tana alfahari da kokarin kowanne acikinsu, sai kuma ta murda zancen ta dawo cewa ita bata dauke ma wani kyautatawa ko kulawa da jikarta ayaanah ba, dan haka karda hakan ya zamo silar da wani zaiy gadara ma wani. tay dogon wa'azi akan kyautatawa..tunda ta fara maganan ibaad kallonta kawai yake da mamaki..
dan yagama lura da cikin gidan gabaki daya, bama hajy mairo ba, kusan gani suke kamar tsaurin da yake ma yaran akan tarbiya da karatu kawai takurawa ne da mugunta. kowa ya tofa awajen shi baice komi ba
hajiya tace wai a saukake ma jikokinta su more zama agidan adena tsorata su bakowani dispcline bane akeyi da zafi da tsauri, bataso taji ana yawan duka, ko ana hanasu hutu, tunda duk suna kokari snn duk abu na kyautatawa da nuna gata indai agidan nan za'a basu kyauta ba nawaje ba kar ana hanasu tunda gidan nan duk ba cutar dasu za'a yi ba.
yanajin yadda uncle moh yay maza ya haura kan maganan harcewa yake su ibaad din ma ai tarbiya da nitsuwa bai gama ishensu ba dan haka basuyi girman da suma zasu takura ma na kasa dasu ba...
kusan kowa ya tofa albarkacin bakinsa atakaice dai hjiya mairo da uncle moh suka justifying komi which sunhow make sense to odas, sabida kowa gani yake toh meye lefin da ana bada ayaana ko wata yarinya kyautuka agidan nan, ibaad yay shiru ransa ya gama bashi cewa uncle moh ne yakai kararsa wajen hajya sai bai tanka kowa ba har aka sallamesu dukansu uku suka fita..
maheer yay kmr zai fahimce abun amma kuma sam ibaad yaki ya bashi fuska suyi maganan, mujaheed ne ma yaso shima yay korafi da dabiar baban nasa, saidai sanadiyar maganan nan sai shima ya dada zulmuwa yafara ganin abun as normal tunda dai gidane kuma babu cutarwa acikin kyautatawa.
kin cewa komi da ibaad yay yasaka maganan yay sanyi kowa ya cigaba da abunda ke gabansa har yamma yay, da zasu wuce gida hajy mairo ta kirasa uwar dakinta tafara masa magana privtly shikadai akan maganan rayuwar ayaanah
she din't even ask him what is hapening kai tsaye tay assuming cewa murdadden halinsa yasa yake so lallai ayaanah tadena karban abu daga wajen yayanta...sai cewa take inda muhammad ba dan cikina bane da sai nace kareta kakeyi, toh yaushe kuma alheri ya zama mugunta? ynxu inba shi ba waye agidan nan yake saya mata kayan gayu. wallh har tausayi muhammadu yake bani ka dubafa yadda yake nuna ma ayaana so da gata, harma fiye da yayan cikinsa, wnn ma ai abun alfahari ne garemu, kuma haka Allah yake son mutum yaso dan wani kamr yadda zaiso nasa toh ahir dinka rayyanu da nemansa da fitina nide bana son tsugudidi da tashin hankli...kaji na gaya maka kenan
tunda tafara maganan latsa wayarsa yakeyi idonsa na kallon wayar har ta gama baice mata uffan ba kuma bai dago ya kalleta ba. har saida
tay shiru ya miƙe tsaye ahnkli cikin danne abun aransa yace "toh, hajiya kiyi hakuri..inkin gama ni zan wuce gida kaina