Chapter 23 Reading Abunda Ke Boye Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Abunda Ke Boye Complete Hausa Novel

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 88

66K to 69K   out of 262.2K words

ne daya dauke shi gabaki daya agaban mahaifyarsa ya zauna agidan san, ko hala yarage mai freedom din sa nayin rayuwa irinta yam hutu kmr age mates dinsa duba da bashine asali ya haifesa ba amma he wants nothing but the best for him cos deeply in his heart yanajin kamr he is more than just a uncle to him, arayuwar sa yakanji kamr yafiye ma ibaad din kallon dan cikinsa daya haifa fiyeda alakar kanin uba dayake tsakaninsu kamr yadda ya lura shima ibaad din kmr amatsayin uba kawai ya ajeshi.

maheer ne ya soma gaishesa cikin nitsuwa da ladabi, ya tattaro hanklinsa duka cikin bashi kulawa ya amsa shi cikin nitsuwar shima..

ajiyan zuciya me sanyi ibaad ya sauke cikin gyaran murya Yace" bappa..katashi lpya?.

ya amsa da lpya kalau ibaad masha Allah ya hanya kuma?
Yace alhamdullhi..

nan ya hau tambayar sa akan abubuwan da suka asalin faru a anguwar tudu dan hajiya mairo sama sama kawai tadan tsakura mishi awaya kuma tafi zakewa ma akan batun zuwan ayaanah cos she deeply want them to create a safe space for ayaanah's new life with them.

cikin nitsuwa ibaad ya fara fayyace masa komi yadda ya faru bai boye musu komi ba face wajen auren daya sakaya bai fito fili ya gaya musu cewa batun aurene yafara hadasa da ayaana ba, since d weding is void and invalid a musulunce sai baiga ma amfanin kawoshi cikin zancen ba. shide kawai ya musu bayanin cewa ahanyar zuwansa tudune ya fara samunta akasa tasuma cikin ruwa, snn bata da lafya kafin nan kuma sai yan kauyen suka kama shi suka tafi dashi acan akauyn suka bashi yarinyar ya taho da ita wajen hajya mairo.

maheer yanata kallon ibaad da mamaki dan ko kadan bai tsakura masa wayannan maganganun ba, he told them how he met ayaanahs mother da duk yadda sukayi da ita akan batun rayuwar ayaanah bai boye musu komi anan ba.

duk jikinsu sai yay matukar sanyi tare da jin matsanncin tausayin labarin taawure da duka yaranta..

nasiha bappa zaidu yay musu sosai, snn yace zai kira lawyersa inya je office zasu tattauna dan ayi wani abu legally akan zamansu da ayanah dan tazamo tana da full legal custody na zamanta awajensu sabida nan gaba kar mahaifinta juma yazo yace yana da cikakken ikon karbanta a hannunsu ko tafiya da ita. tun anan suka yanke hukuncin cewa ahannun mahaifyar ibaad wato ammi karama zata zauna na din din amma sai bayan ta gama jinyarta anan gidansan ta warke sosai.

maheer bai wani so hukuncin da aka yanken har ransa ba amma sanin baqin hali irinna mum dinsa da ganin yadda haryau take cin mutuncin ibaad kawai yasaka ya haqura duk da bai san ayanah ba tukuna yaso ace ayaanan agidansun zatay rayuwarta har tagirma ko dan kanwarsa sultana ta samu soul sister itama. dan sultana ita daya take rayuwarta anan, bata da wata abokiyr hira saina schl sabida duk su ba sa'ointa bane gashi tana mugun jin shakkar ibaad intagansa yawnci tsorata takeyi jikinta sai yahau rawa rawa, shiyasa most time batason saukowa kasa ta sake jiki sai lokcin cin abinci ko in sunfita schll basu nan, acan gidan kuma akwai kulthum da kuma safiya they had each oda all the time, nd mujaheed being the eldest is kinda cool guy asalinsa baida wani matsala da duka kannensa.

Hira suka taba kadan bappa zaidu yanayi yana hada musu da nasiha sosai, shi sam baiya iya zama da mutum walau nashi ne walau bana shi ba, face ya tsinci kansa cikin tunatar dashi kalmar Allah da manzonsa tare da zurfafa musu tunani akan muhimncn zumunci a tsakaninsu.

karfe bakwai yana cikawa suka bar wajen sa, ibaad ya sanar da maheer akan yaje ya kawo masa aron kayan sultana da zai bada ayaanah ta saka just for today inyaso insun dawo daga asibiti zasu dawo musu dashi, maheer baice komi ba yaje dakin sultana ya sameta tana zaune da farin glasses a idonta tana kan solving algebra akan reading table dinta, cikin ladabi ta rusuna ta gaishesa ya amsa batare da ya mata bayanin komi ba ya umarceta akan ta bashi complte spare cloths aro zai dawo mata dashi.

mamaki ya cikata amma dayake tasan basu fiye wasa da ita ba yasa ta tashi da sauri ta bude wardrobe tq dauko masa sabon spare pants da bomb shot sabbi kall daga ledarsu da wata loose abaya mai kyau peach colour mai igiya, baima tsaya duba yanayin tsayin kayan dakyau ba ya amsa yafice duk sai taji she is confused, koma waye za'a bada aron kayanta oho dai ta cigaba da karatunta bata kara kulawa ba...

yana isowa sashensu ya samu ibaad a bakin kofa yana jiransa suna hade ido baice masa komi ba ya miƙa masa kayan cikin sauke ajiyan zuciya yace "can i see the girl? fuska ba yabo ba fallasa ibaad ya bashi short "no..as answr. dan shiru maheer yay snn yace "i just want to see what she looks likes . ibaad yay kwafa yana kallonsa ahanlkli yace "she is sick nd scared maheer, dan Allah kabari sai na fito da ita zaka ganta, gyada kai maheer yay ashashance yace fine toh bari naje na shirya i think i have 9:30am lectures amma zan fita da wuri inada wani business da abdll gaffar

..cikin gyara tsayuwa ibaad yace wai harkun bude shop din naku ne, see i pity u ranar da bappa zai san kana wann abubuwan abayan idonsa. kyabe baki maheer yay ahnkli yace "isit a bad thing? sana'a fa na budewa kaina witout asking for his help he shud be proud of me, ibaad yay murmushi me sanyi cikin gyada kai yace "yeah he shud.,i am proud of you too,kayi kokari sosai...but he shud also scold u abit for squandering millions of naira over a secret investmnt witout his knowledge.

dariya me sanyi maheer yay yace inda a america muke fa da yanxu bama gidansa.. suka dan fashe da dariya"yace toh ibaad da kudi fa ake neman mugayen kudi, i want to be rich as early as possbile dan wallah aure zanyi da wuri...kuma in sha Allah befr i graduate my law schll in few yrs to come i will be a multi millionaire u just wait nd see...ibaad yay murmushi yace i trust you on that..u're a go getter!

dariya yay yace "so yaushe kai zaka fara setting naka business din ko likitoci basa kasuwanci ne? yafadi hakan yana zura maa ibaad ido batare da ko kiftawa ba..

ibaad ya kallesa da kyababben baki yace "seriously? ohh pls, not now mana.. saina settling a karatuna kadan kafin na fara tunanin me zanyi da rayuwata nan gaba. cikin rolling idanu maheer yace "ok fine, but the earlier the better. see yhu at d table. gyada kai ibaad yay har saida maheer din ya wuce part dinsa snn shima ya bude kofar dakinsa ya shiga ahnkli kuma cikin nitsuwa hoping to see ayaanah tagama wanke jikinta ta fito waje tana zaune akan kujera caraf saiyaga wayam snn dakin ya dauka da wani irinn shiruuuu kamar babu kowa aciki kusan ma yadda yabar dakin haka yazo ya sameshi..

kirjinshi har yana bugawa ya aje duka kayan akan gado da bala'in sauri sauri yay kofar bathrum din ya bubbuga da tunanin koma suma tay awajen yana can waje yanata bayani baisani ba...

kusan sau uku zuwa hudu ya buga dabaiji ta amsa ko tay motsi ba hannunsa harna rawa rawa wajen sauri da karfin tsiya ya bude kofar yashigo ciki adan gaggauce wanda karar budewa da shigowarsan ne yasaka ayaanah bude lumsashun idanunta data rufesu tamm tabi ta takure kanta akasa awani lungu tay shiru idonta nakan zubowa da hawaye.

yana hangota akasa arakube kusa da sink yaji ransa ya mugun baci, kai tsaye ya haɗe ransa kmr bai taɓa murmushi ba cos despite his bathrum floor is sparkling clean nd dry sam sai baiga dalilin da wani zaiso yazauna akasa acikin wajen ba...

tsawa yay niyyar daka mata sai kuma yaji ya kasa yin haka ya dan tsaya cak sabida rauni da tsoro dayake hangowa ajikinta sosai....kallo daya kamata zakasan cewa she is u can still grieving the loss of her sister inayah.

tunda ya shigo kallonsa takey a mugun kasale cikin jin tsananin tsoronsa ta kankame jikinta tareda jin matsanancin fargaba tana nishi nishi kmar wacce take shirin sumewa.

akanta yatsaya tareda zuba mata manyan hazel eyes dinsa that are sharp nd piercing, baice mata komi ba for a minutes sai can cikin tattaro makansa nitsuwa ayayinda fuskarsa take a mugun dore ya daga kirarsa sama yace "keee, menace miki kiyi? kanta ta sauke kasa ahnkli bakinta na rawa rawa tace "kace nayi fitsari'yace dakikay fitsarin sai kuma nace miki kizauna anan akasa wai ke wata irin kazamiyace iyeee daga kiyi fitsari ajiki saiki zauna a toilet?

shiru ta masa hawayenta na diddiga gwanin ban tausayi,

cikin sauke sihirtaccyar ajiyan zuciya yace toh "tashi"

a daddafe ta miƙe tsaye kanta na kallon tiles din, baice mata komi ba ya juyo wajen towels dinsa yasa hannu ya dau blue colour me kyau ya miƙa mata ta karba, ya dauki spare brush dinsa yasa tooth paste ya aje mata akan sink snn yay setting showersa zuwa warm yajawota gabansa kamar yar tsana giving her sound stern warning cikin zare mata ido yace "ki cire kayan jikinki, ki aje acan, snn ki daura wann towel din dana baki ajikinki, kishiga shower can kiyi wanka snn kidawo nan ki yi brush..kina gamawa ki fito..do not allow me to come back here for you for the scnd time.

shi baisan ma kotana jin turanci ba amma ganin yadda take gyada mai kai da sauri sauri cikin jin mugun tsoronsa yasaka ya kyaleta ya fita waje.

bayan ya rufe mata kofa kai tsaye ya fara kimtsa dakinsa kamr yadda ya saba, ayaanah stood for a while tana bin inda yabin da kallo, can kafin nan ta share hawayenta ahankli ta aje towel din ta kunce zaninta ta cire kayan jikinta duka ta ajesu agefe kamar yadda yace mata tayi

wani irin sanyi ta dingaji
sabida akwai A.c har a toilet din dakyr ta shiga shower sabida bata taba wanka aciki ba komi tanayine da tsoro tsoro har saida ruwan dumi yafara malala ajikinta sann taji kamr hanklinta yafara dawowa jikinta sosai.

she saw all his expensive gels nd soaps collection dake ta iya karatun turanci sosai kuma tana da ilimin ganewa amma dake batasan ya ake amfani dasu ba sai batay gigin taba masa abunsa ba.

acikin shower tay tsarki ta tsuguna ta wanke koinanta sosai da ruwa tafita tass, ta murda wani abu taga ruwan ya dauke sai tazo gaban sink din tay brush ta wanke bakinta, tay alwala tabi ta dauki dankwalinta ta rufe sumanta daya jike shataf jikinta na ɓari sosai ta bude kofar ta fito...

samunsa tay a zaune akan reading chair yana duba wani katon text book na anatomy and physiology sama sama sabida duk sun wuce basics din a private club dinsu...

irin kallon daya ma fatar jikintan ryt from head to toe yasaka ta sunkuyar da kanta can can kasa jin yay shiru ahankli muryanta na rawa rawa tace "uhmm mai mota...cikin katseta da mugun kallo yace "kee??? arazane ta kallesa yace uban waye mai motar ki? wani irin kankame dankwalinta tay zata fashe da kuka yaja tsaki yace"kar in sake jin kin kirani da wannn sunan now go on nd tell me meye matsalarki

bakinta na bari tace "na gama wankan ne..

yana miƙewa tsaye da sauri ta ja baya ta mannu da kofar a mugun tsorace tana hawaye

baiko kalle ta ya wuce ya shiga bathrum din kallo daya yamata ta karaso ciki, a miskilance yace "go back in der. ya kara nuna mata shower. snn yace kijje ki kara wankan and dis time use soap on ur body kingane me nake fada? da sauri ta gyada masa kai tunma bai fice ba tay sauri ta koma cikin shower ta tsaya, she read all the product on scrolls, har saida tagane wanne zata dauka aciki, koda ta rarumi katon shower gel dinsa tafi mintin biyu tana kokawar budewa, dakyar tazo tagane inda abun yake da yadda ake amfani dashi tana matsawa da karfi kuwa ya fantsama mata a fuska sauran yabi ya zube all over the floor, wanda ya zube ajikinta ta karasa mulkawa sann ta saka ruwa ajikinta wani dan uban kumfa da qamshi da tsantsi atake ya rufeta tana gama dauraye jikinta ta jawo towel din ta dora batare da ta lura ba tana saka kafa waje kuwa wani uban tsantsin gel din data zubar ya jawota waje suuiiiiii ya fetta ta akasa wani dan uban ihun razana ta zuba shikansa baisan sanda ya turo kofar agaggauce ya shigo ciki ba..

ganinta akasa yasa bai yi wata wata ba ya karaso wajenta yace meye faru? kuka take rabzawa dakyar ta nuna masa kasar floor din yaga duk gel dinsa ne akasa ya karkada kansa ya dauketa cak ya fito da ita ya ajeta akan chair snn yadan tsuguna agabnta ya kama kafarta ya dudduba koina yana mammtsa shi tsabar dadin dataji ita dakantan ta dena kukan tay shiru... dabai ga komi ba ya miƙe tsaye yay wani lungu after few mins ya dawo da white bathrobe dinsa ya lullube mata ajiki dashi snn ya umarceta data tashi ta karasa sawa sai ta bashi wet towel din, cikin saibi tamike ta aiwatar da hakan tana bashi towel din yace mata ta zauna, tana zama ya tattara jikakken suman ta duka acikin towel din ya daure mata shi tam tam snn ya kunna room heater acikin dakin for about 5 min, ya je ya dauke men hair dryersa ya kwance mata daurin kan ya fara bushar mata da gashinta yadau lokaci sabida yawa da tsayin sumanta har saida ya gama busharwa tsaf,lokacin ayanah kallon kasa kawai takeyi dan ko motsi batay iyayi bare tari.

tunda ya gama bushar mata dakai taji dumi ya dan gaurayeta daganan sai bai sake kulata ba, kyaleta yay anan for a while yaje ya wanke cikin bathrum dinsa ya tattaro kayantan data jika da fitsari yazo yasaka a engine ya wanke ya matse kafin nan ya dauke body oil insa ya bude yazo yana zuba mata kadan kadan a hannu tana shafawa a hannu fuska da kafarta, daga inda suken ya mata nuni da kayan sawanta akan gado yace yabata 3 mint ta saka kayan ajikinta ta jirashi yana zuwa, tun kafin ta amsa taga har ya fice abunshi, he went out of the room for a while, at exctly 3nd half minutes saigashi nan yadawo yazo ya sameta har tasaka sabon pant din da short ataciki da doguwar rigar da ya dan mata yawa kadan amma baiwani damu ba

suna hade ido tadan sunkuyar dakanta can kasa, ahnkli tace "umm.. zanyi sallah"yq kalleta da mamaki kafincan ya gyada kai kasar wuyarsa yace good for you. wucewa gaba yay barta a tsaye ya dau sallayarsa ya shimfida mata yana tsaye yana kallonta har ta cusa gashinta ciki ta dauresa gamgam sosai sabida yanada tsantsi snn ta gyara zaman mayafin gown in akanta tafara sallanta a nitse,

da gefen idonsa yake kura da ita she really looks pale nd light weigh, kamar jiri jiri yana janta har dai ta idar, tay adduarta hawaye ya cika mata ido ta juyo da sanyin murya tace mishi ina kwana?? sosai ya sha mamakin unxepected halin nitsuwarta daya soma gani sai kawai ya amsata da kai...adan dakile yace mata"are u done? tace uhm. yace "tashi ki biyoni..

babu musu ta miƙe yay gaba tafara binsa abaya tafara takawa ahnkli ahnkli kamr wacce kwai ya fashe mata ciki dan bakaramin rashin karfi da matsancin rauni takeji a zuciyarta da jikinta ba.

kan steps suka bi direct sashen bappa zaidu yakaita kusan kowani takawa sai taji kirjinta ya buga hardai suka iso wani mayen falon da bata taɓa ganin irinsa a kyau da girma ba suna shiga bappa zaidu ya bude kofar masters bedroom na gidan already ya gama shirinsa yay kyau cikin wata dakakkiyar coffe brown shadda ya dora matching colour borno cap mai kyau da kyalli wanda ko ba agaya maka ba kasan naira yay kuka ga designer cover shoes dinsa sai shinning take qamshin turarensa na original hugo boss tuni ya cikke falon da dadin qamshi..

ayaanah na baya baya har ibaad ya karaso da ladabi yace bappa ga yarinyar nan, i tot i shud bring her since she is ready.

kan ayaanah na kallon kasa bappa zaidu yadan lekota ganin ta kyakkwan gaske yasa yay murmushi yace masha Allah.. shigo ciki mana yan mata..

tana karasowa gabansa ta sulale kasa ta durkusa bisa ladabi da sanyin muryanta dake rawa rawa tace "i..ina kwana...?da fara'a sosai bappa zaidu yace lafya yannan tashi. tashi ki zauna akan kujera mana ai nan kamr gida ne...tana zama da tausayi a muryansa yace "ya jikin naki..kamar zatay kuka tace..lafiya..da sauki..

daga nan yafara mata gaisuwar ya hakuri snn ya tambyeta wasu abubuwa game da mahaifyrtan kadan kadan take amsashi a raunace

ibaad yay excusing dinsu ya koma dakinsa feeling relieved tunda ya damƙata ma bappa ita kuwa ganin ibaad ya tafi baiko kalleta ba tuni sai taji tsoro da raunataccen kuka yazo mata tafara ma bappa zaidu hawaye sosai. ibaad kuwa yana shiga dakinsa baiy wata wata ba ya faɗa wanka baikara sanin me suke ciki anan ba.

daga falon kuwa babu irin nasiha da hakurin da bappa zaidu bai bata ba dakyar tay shiru ta dena kukan, after assuring her to calm down, kuma shima kmr ubane agareta snn ta dauka nan kamar gida tazo suduka zasu riketa har saita cimma duka burikan rayuwarta..

dakyar nasihansa ya shiga kunnen ayaanah har taji dan dama dama aranta ta sake jikinta kadan dashi, ganin ta samu nitsuwa ta kuma fahimce shi sai ya miƙe tsaye da niyyar shiga cikin dakinsa domin dauko babban wayarsa, yabarta ita daya a falon tana zaune da hot cup of herbal tea daya bata tana shansa ahankli ahankli.

yana shiga daki ko minti biyu baiyi ba ayaanah taji motsin mutum abayarta wani irin faduwa gabanta yayi dake ba'ayi sallama ba duk saita dauka ko ibaad ne yadawo da sauri ta

23 / 88